Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
san ita Zaliha sam ba ta damu da soyayya ba." ya yi dan murmushi "Ai kuwa ta huta da wahalar duniya." Ya fada yana satar kallon Asma'u. Itama ta yi masa wani irin kallo da gefen ido "Masu yi ma ai wahalar ba kashesu ta yi ba." Ya yi shiru bai tamka mata ba, sannan ya ce "Muma muna da biki Yola Karshen wannan watan, zan fi so ace. dake bikin domin ni ba 7an halacci bikin ba zamu yi tafiya da Daddy, kuma na tabbatar Mina za ta zo wurin bikin, kin ga in kin je za ki samo min rahoto." "Gaskiya nima zan so zuwa bikin nan in dai bai zo lokaci daya da bikin mutuniyar tawa ba, dan nima ina son ganin Mina amma dai ko mun hadu ba Jallai ne ta gane magana ta ba, tun da ka ce ba ta jin Hausa sosai." "Duk da haka za ta fahimce ki, bare ma an ce inda ta yi aure garin Hausawa ne." wannan lokacin ne suka Karaso gate din makarantar, Salim ya tsinkayo wani (lecturer) dinsu ya danno hancin motarsa, ya yiwa Asma'u nuni "Ga fa mutumin na ki." Ta dan tsuke fuska "Ina ruwana da shi ka manta da shi Kawai shirmensa yake. Ran nan ma ya bi ni har gida amma ina ganin abin da na gaya maza zai yi tasiri." "Me ki ka gaya masa?" Salim ya yi tambayar yana dubanta. hakun kai zan aura." Ya Kura mata ido sannan ya dan girgiza kai yana dariya "Ki daina yi min Karya dan ni na fara gajiya da iin wannan Karyar da kikewa samarinki, shi ya sa mutane suke dauka soyayya ce tsakaninmu. Ya kamata ki daina Karya, tunda kin san ba hakan bane." "A'aha da so kake su dauka Kiyayya muke?" "Haba Malama ba haka nake nufi ba." daidai lokacin da suka isa harabar wurin da aka tanada' musamman dan ajiye motoci ta yi fakin. Tana shirin fita daga motar wayarta ta yi Kara, ta dan ja tsaki saboda Ta dan kanne ido tana dariya "Cewa na yi ya yi ganin ta kusan makara, yatsine ta zuge jakatacirokan wayar, amma ganin mahaifiyarta ce sai ta fadada fara'arta gami da kara kan wayar kunnenta, sannan ta dan rusuna tana gzyar da ita tamkar gabanta take. "Momy ina kwana nima ina nan tafe da mun sami hutu. Salim zai kawo ni Kaduna....Mommy ina Abbana? Jina na nemeshi waya amma na ji rufe." Sai da suka gama surutai akan abinda ya shafesu sannan ta mikKawa Salim kan wayar suka gaisa da Mommy daga nan ta rufe ta nufi aji hanzarce, saboda makarar da ta yi, dan tun kan ta Karasa ciki ta tsinkayi malamin nasu tuni ya fara lecture tana shiga ta nemi wurin zama ta bi sahun dalibai, 'yan uwanta ta nutsu ta fara sauraren bayanan lecture din. Gaba daya ta maida 66 hankali akan lecture da yake yi musu ko baa fada ba an san karatun likitanci karatune mai wabala, wanda yake Lakcar su ta yau dai ta debesu tsawon awanni biyu sannan suka tashi suna fitow aba ta tsaya galsawa da dalibai ba kai tsaye ta nufi gindin motarsu, inda Salim ke zaman jiranta, babu abin da ya dameshi ya saka kida ya nutsu sosai yana sauraren sauti, tun daga nesa ya zubawa Asma'u ido yana yaba kyan halittar da Allah ya yi mata tana Karasowa ya bude mata Kofar motar sai da ta fara cilla jakarta cikin motar sannan ta shiga ta zauna. "Wash! Na gaji wallahi." Ta fada wahalce gami da dan lumshe ido. Ya dan rage sautin kidan sai da ya tada motar sannan ya jeho mata tambaya gami da watsa mata iadanu Surfe ki ka yi ko sussuka?" "Ba daya." Ta bashi amsa ba tare da ta dubeshi ba. "Haba Malama mene ne na gajiya daukar lecture daya? kai kake ganin haka." Suna fita daga harabarjami'ar ya dauke kan motar suka nufi titin da zai kai su asibiti, tafiyar da ba ta wuce minti goma ba ta sadasu da asibiti da yake nan ne asibitin da iyalan gidansu Salim suke zuwa basu sha wata wahala ba suka ga babban likita, bayan bincike da 'yan gwaje-gwaje Doctor Hashim ya rubutawa Asma'u magunguna da kuma shawarwari da wasu dokoki da ya kafa mata daga bisani kuma ya dan nuna ra'ayinsa kanta ganin zai dameta sai cewa ta yi. "Lah, Doctor ina fa da miji." buKatar nutsuwa. 67 "Kai ban yarda ke matar aure ce ba." Ya dan dubi Salim "Ya abokina ina fa ciki, ina fata za ka bani Kanwar taka." Asma'u ta ce "Doctor ka yi kuskure, ai wannan shi me Mal cidan nawa." razane likitan ya kai dubansa ga Salim "Ka yi aure ne?" Ya yi dan murmushi "Kwarai ita ce amarya ta." Murmushi kawai likitan ya yi amma sam bai yarda ba. saboda ya lura da lokacin da suka hada ido suna dariya. Suka fito jere likitan ya taka musu har gindin mota, da kansa ya budewa Asma'u motar shige, ta zauna, sannan suka yi sallama ya koma bakin aikinsa. Salim ya bar Asma'u cikin mota ya koma gefe ya kunna Sigarinsa ya gama zuka, bayan ya sha tabarsa ta isheshi sannan ya dawo cikin motar. Asma'u ta kama yi masa dariya, ya kalleta kawai ba tare da ya yi magana ba, sai da ya laluba wurin da yake ajiye alawar tom-tom dinsa, ya ji ba ko daya ashe Asma'u ta shanye, girgiza kai kawai ya yi gami da dan murmushi sannan ya tayar da mota suka tafi bai nufi igida da ita ba sai ya dauki hanyar gidansu. Ta dan watsa masa fararen idanunta "A'aha haka muta yi da kai?" Ya ce "Wai da ina nufin mu je gidanmu ki dan huta in kin gaida su Mommy da yamma sai na maidaki gida, kin ga yau Daddy ma yana gida sai ku gaisa." Da yake bata son yi masa musu sai ta yarda, suna isa yaran gidansu Salim suka tarbeta da murna da komai duk suka rirriKe mata hannu, ta isa falon Mommy ta 68 gaida ita ta dan zauna suka fara hira, ta dubeta cikin murmushi. "Asma'u kin yi wuyar gani yanzu sam ba kya son zuwa gidanmu, ba kamar da da kike yawan zuwa ba?" "Lah Mommy wallahi karatu ne ya Boye ni, amma tun da zamu sami hutu sai kun gaji da ganina." "In ce dai wannan yaron ya gaya miki maganar bikin diyar yayata da za mu yi Yola?" "E Salim ya fada min kuma in sha Allahu zan je." daidai wannan lokaci ya shigo, ya dan dubi Asma'u "Ki taso mu je ki gaida Daddy." Ta mike cikin nutsuwa ta bi bayansa har falon mahaifinsa ta dan rusuna ta gayar dashi. Daddy ya dan fadada faza'arsa "A'a diyata Asma'u yau ke ce gidan namu? Ya ya karatu? Ya mutanen gida, duk lafiya? In ce dai ana maida hankali karatu?" Salim ya ce "Daddy ka yi mata fada tana yawan sa tunani ranta, gashi nan yanzu damuwa ta haifar mata da ciwo." Ya dan dubeta cikin murmushi "Wai haka ne diyata?" Ta sunkuyar da kai tana amsawa kunya ce "Dadd ba haka bane kawia fa Kirjina ne yake ciwo, kuma mun je asibiti." Ya dan fadada murmushinsa "To shi kenan Allah ya sawwake dinga maida hankali akan karatu, kun dai sani karatunku na buKatar nutsuwa." Daga nan suka yi sallama da Daddy suka fito daga sashensa. Salim ya cewa Asma'u "Ki jirani zan je na yi wanka." 69 Ta tabe baki "Kai ka &walisa da yawa, ni zan shiga ciki in ka gama ka iskoni (study room) akwai abin da nake son dubawa computer." Tana zuwa study room ta janyo kujera ta kai gaban computer ta shiga danne -danne ta kwashi tsawon lokaci ciki, sannan Salim ya shigo ya duba rubutun da take cikin computer, ya yi 'yar dariya "Malama likitan nan fa da gaske yake yi ya bugo min waya yanzu ya jaddada min bafatarsa. Ta dan kada ido gami da harararshi "To inda gaske yake sai me?" "Kai gaskiya yarinyar nan masha Allahu akwai ki da dankaren farin jini, gashi nan maza sai kawo caffa suke.* "Haba da Allah sai ka ce ni ce kai ga ka nan 'yan gusta sai rububinka suke ka tsaya kana yanga sai faman yankwanasu kake. Cikin murmushi ya ce "Haba yarinya kin dau bashi na data yi miki uzuri daga yanzu duk wanda ya ce yana sonki zan bashi dama." Ta dan marerece "Haba Yaya Salim mijin Mina, ai hama haka da kai. wannan lokacin Shema'u Kanwar Salim ta shigo "Anti Asma'y ki zo ki ci abinci in ji Mommy." Salim ya ce "Je ki ki kawo mata nan." Asma'u ta ce "Anya zan ci abincin nan, lemo kawai za ki kawo min." Salim ya ce "Dame-dame aka yi kicin?" Shema'u ta ce "An tuKa tuwon shinkafa da miyar agushi, kuma akwai shinkafa da salad sannan akwai 70 ragowar farfesu," "Shi kenan abin da aka girka kicin din?" "Ina jin shi kenan amma bari dai na tambayo masu aikin kicin din ko akwai wani abin bayan wannan. Har ta kai bakin Kofar "Ji nan Shema'u." Salim ya ce da ita "Je ki sa hado mata salad ki taho kuma da lemo saboda Antin taki ba ta fiye son cin abinci mai nauyiba." Asma'u yini guda ta yi gidansu Salim, sannan da marece ya maida ta gida. "Yan makarantun jami'a sun sami hutun Karshen zangon karatu wanda shi ne Salim ya kammala karatunsa fannin likitanci, ita kuma Asma'u tana shirin shiga (level three) Kwamishina baban Salim ya shiryawa dan nashi Kasaitacciyar liyafa saboda murnar taya babban dan shi nasarar kammala karatu lafiya, ya gayyaci manyan mutane da dama. Bayan an gama komai, ya shirya musv tafiya Kasar Jamus (Germany). Bayan tafiyar su ne Asma'u ta raka su Momi biki can garin Yola burin Asma'u bai wuce ta ga Mina ido da ido ba, ai kuwa suna isa da kwana daya Mina ta zo lokacin da Mommy ta nunawa Asma'u ita ba Karamin firgita ta yi da ganin yarinyar ba, muguwar kyakkyawa ce, sai ka ce aljana, tsananin kyanta ya zarce duk yanda kake zato ita kam duk yanda Salim ya siffanta mata ita yanzu da ta ganta sai ta ga ta wuce nan, abin sha'awa Mina tana da fara'a da son jama'a gashi kuma ta waye, saboda zaman birni da take yi. Hausarta tana fita sosai, amma kuma Asma'u ta ji labanin wai Mina har yanzu ba ta daina yiwa mijinta tawaye ba, kullum ita kenan guje-guje gidajen 'yan uwa. Asma'u ba ta fi mako daya da dawowa daga bikin Yola ba ta yi shirin tafiya Kano wurin bikin Zaliha Kawarta, tare da gudunmawarta mai tsoka. Lokacin da ta isa Kano ba gidansu amaryar ta sauka ba, dan girmamawa sai ta sauka gidan dan uwan mahaifinta dayake shi kadai ne dan uwansu wanda ya rage garin Kano, wato mahaifin Yusuf mijin da aka aura mata da farko, lokacin da aka sanar da Yusuf zuwan Asma'u da saurinsa ya ZO yi mata sannu da zuwa ganinta ke da wuya duk sai ya rude, saboda irin canje-canjen da ya gani tare da ita. Asma'un da aka yi musu aure tana Karamar yarinya har yana raina shekarunta, amma yau gata ta ama munzalin mace sosai, ta goge ta dada wayewa, boko ya ratsata sosai, gashi idonta ya bude saboda cudanya da masu ilimi, rayuwar ta gaba daya ta. sauya ta samu ci gaba kowanne fanni ta dada kyau sosai, jikinta ya murje, ta yi haske fatarjikinta sai sheki take yi. Kuma abin mamaki ta bashi hadin kai suka gaisa faran-faran cikin mutunci, babu wani alamar raini ko tsiwa. Sai ma girmamashi da ta dinga yi matsayinsa na dan uwanta, sam ta nuna kamar auren dole bai taba shiga tsakaninsu ba, shi kuma ganin haka sai ya fara bullo mata da maganar kome, wai ta yi hakuri su maida aurensu tunda yanzu su ba yara bane, sun mallaki hankalinsu. Dariya kawai ta yi ta shareshi, duk yanda ya so ya shisshige mata ta ki yarda. Da ya matsa mata da zancen soyayya sai ta ce ya yi haKuri dan yanzu shi 72 Yayanta ne, zai fi kyau su rike matsayinsu na 'yan uwantaka amma ya fidda batun komai. Ya kada ya raya ta ki bashi goyan baya, ita abin ma dariya ya bata, sai dai kuma ta yi mamakin shiryuwar da Yusuf ya yi ya zama nutsattsen mutum, ba kamar shekarun baya da yake harkar sharholiya ba da alama yanzu duk ya tuba ya daina shaye-shaye amma koda ta tambayeshi labarin abokinsa Bashir, sai ya shaida mata bashi da lafiya yana nan yana jinya, duk ya fita daga kamanninsa sakamakon kamuwa da cutar Kanjamau (AIDS) da ya yi. Allah ya kyauta abinda ta ce kenan tun da Asma'u ta zo biki Yusuf na tare da ita, duk wata zirga-zirgar zuwa gidan biki shi ne ya ke dawainiyar kaita da daukota, fir ta Ki yarda direba ya kaita bayan haka ta ziyarci mutane da dama har gidan Sunusi abokin Yusuf sai da ta je ya yi aure har da 'ya'yanshi biyu sannan ta je gidan Ahmed abokin Aminu, babu yanda bai yi da ita akan ta daure su gaisa da abokinsa waya amma fir ta Ki yarda ta kawo uzirin wei tana da miji, kuma ta Ki yarda ta kar6i lambar Aminun. Bayan nan ma har. gidan Babar Aminu ta je ta gaisheta, ta kai mata kaya sha tara ta arziki, amma ta Ki fadin garin da take da zama da mahaifiyar Aminu ta matsa mata da tambaya sai cewa ta yi Sudan take aure. Asma'u dai tana cikin kacaniyar bikin Zaliha, Salim ya yi mata waya ya shaida mata sun dawo shima yana nan zai biyota Kanon don haka ana sauran kwana daya gama bikin Zaliha, Salim ya iso sai da ya kama daki Tropicana Hotel ya biya sannan ya yiwa Asma'u waya suka yo suka daukeshi. Zaliha ta yi farin ciki da Salim, ya halacci gurin bikinta koda yake party daya kawai ya samu da yake duk shagulgulan da za yi an yi an gama. Tua da Yusuf ya Kyalla ido ya ga Salim kishi ya masa tsakaninta da Salim dan haka Yusuf sai ya yi zaton saurayinta ne, kishinsa Kin boyuwa ya yi, hankalinsa bai kwanta ba sai loakcin da Salim ya gabatar da kansa ga Yusuf, ya ce shi abokin karatun Asma'u ne kuma shi ne amininta na hannun dama, tun daga nan Yusuf ya saki jiki da Salim duk shi ya kaishi yawace-yawace cikin gari, ya nuna masa gurare da dama cikin Kano. hirarrakin da suka yi da Salim sai da Yusuf ya bashi labarin irin zaman da suka yi da Asma'u lokacin. da ya aureta, da yanda har suka rabu ba tare da ta bashi kamashi duk iya bincikar da yayiwa Asma'u ta Ki gaya hadm kai ba. Sam Salim bai yi mamaki ba, domin ya Za rina wai an saci 7anin mahaukaciya dan yanda Asma'u take son Aminu baya jin akwai wani da namiji da za ta amincewa har ta bashi hadin kai su yi zaman aure. Sai da aka gaba bikin Zaliha da kwana biyu sannan suka tafi, amma abin mamaki tunda Asma'u ta je Kano ta tafi sai Yusuf ya kasa samun sukuni domin ji ya yi duk duniya babu wata 'ya mace da yake so illa Asma'u matarsa ta da. Bayan sun koma Sokoto Salim ya ce "Ya ya ki ka Asma'u ta ce "Gaskiya na ji dadin ganin Mina, domin yarinyar tana da kyau, tana da hankali, kuma tana ga Mina?" If da nutsuwa." yaba da halayenta?" "Kwarai ni ka ta burgeni." "To ko akwai-Wani alamu da kika fahimta wanda za ki yi min albis gashi?"" Ta gyada kai tana murmushi cike da zolaya, sannan ta ce "Na fahimci Mina tana cikin Koshin lafiya kuma tana jin dadin zaman aurenta domin mijinta yana masifar sonta. albishir kuma Mina dai tana da Karamin ciki..." "What?!" Ya fada da sauri gami da Kura mata ido. Ta dan dake gami da tsagaita dariya "To me ye aibi? Ai Raruwa ce, ko kuma kana nufin kun yi yarjejeniya ba za ta haihu ba?" "No, ba mu yi haka da ita ba." "To tun da ka san ba ku yi haka da ita ba sai ka yi Ya yi dan murthushin jin dadi "Kenan kema kin S14addu'a Allah ya sauketa lafiya." Ya sake dubanta razane "Please tell me the true am not joking" (Don Allah ki gaya min gaskiya, ba wasa Ganin rudewar da ya yi ya sa ta dan kanne ido gami da sakin 'yar dariya, "Kai yarinyar nan kin ke ba) shammace ni, amma zan rama bashi kika dauka kin gane?" Yusuf ya rinfa zaryatsakanin Kano da Sokoto shi ala dole so yake Asma'u ta koma amma duk lya Dacinsa kallo ma bai isheta ba, da ya matsawa Goggo cewa ta yi "Ba ruwana ka je can ku Karata ka manta lokacin da ake ik bin ka ana ro€onka kana iya shege?" \. Ya ce "Haba Goggo ki yi hakuri ki manta da wancan maganar ba wai hankalina na yi ta ba na furta furucin ne cikin 6acin rai amma yanzu na fahimci Asmna'u ce kadai matar da nake so dan haka tunda muka rabu kasa yin aure, ita kadai zuciyata ke Kauna." Goggo ta ce "To ni mene ne nawa ciki? Ai ko yaa Asma'u ta amince da kai sai in yi rakiya....." Sai da hutu ya zo Karshe sannan Salim ya kai Asma'u Kaduna wurin Mamanta bayan ya dawo ya fara sturye-shiryen tafiya bautar Kasa, inda zai yi service jibsr Delta. Koda hutu ya Kare Asma'u ta koma makaranta ba karamin kewar Salim ta yi ba, kwata-kwata ji ta yi karatun ma ya gundireta, saboda babu Salim, da yake bata frye shiga cikin Kawaye ba, dama shi ne abokin brrarta, koda yaushe suna tare haduwarjini kenan, Allah ne ya hadasu matsayin aminan juna. Shekarun Aminu hudu da barin Nijeriya.zuwa karatu Kasar Rasha ko sau daya bai taba zuwa ganin gida ba, tun farkon tafiyar shi ya yi alkawarin ya yiwa Niyaeriya adabo dan tunaninsa zai iya zama na dindindin Kasar Turai, to amma ga mamakinsa tun da ya dira aKasar sai ya kasa samun sukuni,saboda kawai fimanin yarinya daya, dan gaskiya rayuwarsa ta gigita saboda soyayyar yarinya daya da ta dinga wahalar dashi ya yi kuka da idonsa ya shiga damuwa iri-iri, ya yi jinya sosai, duk dalilin Kaunar Asma'u bayan ya kammala karatunsa laftya tare da dimbin nasarori sai da ya dan dakata ya fara aiki da wani kamfani na zitga-zirgar jiragen sama. Kwatsam lokaci daya sai ya tsinci kansa da rikicewar dukkan al'amura domin abokinsa Ahmed ya warware masa abubuwan da ya boye masa tsawon shekaru hudu game da masoyiyarsa Asma'u dan shi Aminu duk tunaninsa Asma'u na gidan aure, Kila ma ta hayayyafa dan duk san da ya tamkbayi Ahmed labarin Asma'u cewa ya ke yi tana can gidan mijinta. Amma abin mamaki lokaci daya sai Ahmed ya bashi labarin abubuwan da suka faru da Asma'u bayan tafiyarsa duk dai da Ahmed din ya tabbatar masa amma yanzu bai san garin da take ba, gaba daya hankalinsa ya ji ya tashi komai ya kwance masa, ji ya yi tamkar ya yi tsuntsuwa ya taho Najeriya, yanzu kam zaman Turai ya gundireshi in band ya ganshi Kasar shi ta haihuwa babu abin da yake buKata. Gaba daya hankalinshi ya tafi ga auren Asma'u, shi dai ya ganshi yau gashi ga Asma'u, matsayin ma'aurata shi ne cikar burin rayuwarshi. Nan da nan ya ajiye aikinshi dan ba zai jure zama wata Kasa ba, alhali Asma'u na Can Najeriya ba ta da aure, in ya yi haka ma al ya ci amanar Kaunar da ta nuna masa, dan haka &aggauce ya yi shirin baro Kasar Rasha, ya dire Najeriya Kasarshi. ta gado da zummar neman masoyiyarsa Asma'u duk inda take fadin Najeriya. Kwananshi biyu Kano suka zauna shi da abokinsa Ahmed suka tsara yadda zasu fara neman Asma'u da yake lokacin da ta zo gidan Ahmed ta Ki fadin takamaiman garin da tek da zama. Aminu ya sanar da mahaifiyarshi zasu je neman fi Asma'u. Mamaki ya kama babarshi. "Shin Abba har yanzu yarinyar nan tana ranka?" Ya dan shafa kai yana murmushi "To Mama ya ya zan yi tun da Allah ya jarrabi zuciyata da Kaunar yarinyar, kawai dai ki yi min addu'a Allah ya yi min katarin ganinta. Itama ta yi murmushi "To Abba Allah ya bada sa'a. Koda yake ina ganin Kila fa yarinyar nan duk inda take tana da aure, domin lokacin da ta zo gaisheni cewa ta yi mijinta ne ya kawota. oF "Kai haba Karya take an gaya min tuni aurenta ya mutu."To ku yanzu ina kuke zaton za ku sameta?" "E to zamu fara zuwa nemanta garin Sokoto idan bamu sameta ba sai mu nufi Kaduna, inda Mamanta take "To Allah ya taimakeku ku sameta." "Amin Mama, addu'ar da nake so ki yi mana kenan. Gobe ne zamu tafi Sokoton." Washe gari sammako suka yi shi da Ahmed suka nufi birnin na Shehu, suna shiga cikin garin Sokoto sai suka dauki hanyar da za ta kaisu Kauyen (Shodi) da yake babu wani taKamaiman wurin da zasu nemi Asma'u garin Sokoto, dan haka stka yanke shawarar zuwa wannan Kauye dan suna zaton akwai wasu Kakanin Asma'v wannan gari, amma koda suka shiga sai suka yi ta faman bilinbituwa sam gidan da suke nema ya Bace musu, suka yi ta yawo cikin Kauyen suna tambaye-tambaye sai da suka gaji da yawo duk sun karade ko ina sannan Allah ya taimakesu suka sami aure has wani dattijo ya ce ya san gidan da suke nema. Nan take ya rakasu gidan Dudu Kanwar Kakar Asma'u, bayan sun sami gidan sai suka yi rashin sa'a she ita dai Dudu Allah ya yi mata rasuwa, tun tuni kuma duk iya kokarinsu nasu sami koda daya daga cikin ya'yan marigayiyar duk abin ya ci tura, domin dukkansu sun tafi cirani sai da damina suke dawowa gida. Amma koda su Aminu suka matsa da bincike sai aka yi musu kwatancen wani tsoho wani dan Kauye gaba kadan aka tabbatar musu in dai suka je gurinsa zai gano yarinyar da suke nema, domin shima dan uwan Dudu ne. ~Su Aminu suka yi mura, suka nufi garin da tsohon yake har da dan rakiyarsu. Bayan sun isa garin suka je-gidan mutumin suka ggaisa sannan suka zayyanewa wannan tsoho abin da yake tafe dasu, suka kwatantama masa Asma'u suke nema. nutse suka gabatar da kansu sai da tsohon ya gama fahimtarsu tsaf kuma ya riga ya gano ko su su waye nan take ya raya ransa wato masifar da ta tafi tun shekarun baya ita ce take so ta sake dawowa, haka kawai muna zaune cikin kwanciyar hankali wannan kafirin yaro ya Zo ya tayar mana da hankali,w ato kenan so suke duk su karkashemu da wannan shegiyar soyayya yanda suka kashe uban yarinyar nan. To wallahr ba zai yiwu ba, yanda suka zo haka zasu koma amma ni ba zan gaya musu inda jikar Yalwa take ba. Su dai su Aminu da suka yi shiru suna jiran amsar da tsoho zai basu amma abin mamaki duk Bata lokacin da suka yi wajen kwatanta masa Asma'u tashi daya sai te ya birkice musu wai shi sam bai gano yarinyar da suke nufi ba, babu mai sunanta cikin danginsu daga Rarshe da suka matsa masa sai ya ce "Ayyo na tuno yarinyar da ku ke nufi, ko ba Ma'u 'yar gidan Marigayi Alhaji Masa''ud na Kano ba?" Da sauri Ahmed ya ce "Yauwa ita muke nufi Baba." Yayin da Aminu muma ta kamashi Allah-Allah yake ya ji abin da tsohon zai fada, shi dai kawai burinsa ya ji garin da Asma'un take amma budar bakin tsohon nan Sal Cewa ya yi. "Allahu Akbar kaico duniya, ai in dai wannan yarinyar kuke nufi ta rasu tun tuni wjaen haihuwar jikar Yalwa ta riga ta mutu da dadewa. Nan da nan Aminu ya dafe kai da hannu biyu cikin Karaji ya ce "Shi kenan ta faru ta Kare, rayuwata ta ruguje.Ya tsuguna gaban tsohon yana rasgar kuka sal ka ce Karamin yaro. Tsohon ya ce "Haba samari hakuri za ku yi ai duk mai rai mamaci ne, mu ai tuni muka yi kukanmu muka "FE hakura. Ahmed duk ya riga ya Kule da haushin tsohon nan, ya dafa Aminu "Ka yi hakuri abokina tashi mu tafi kar ka damu duk inda Asma'y take zamu nemota. Aminu ya dan harareshi "Haba Ahmed ya kake abu kamar wani yaro, kana ji fa bawan Allahn nan ya ce' mana Asma'u ta mutu, in haka ne ina zamu nemota?" Ahmed ya janyo hannunsa "Ni dai kawai ka tashi mw tafi." Ya juya ga tsohon nan "To Baba dattijo mun gode Allah ya ji Kan Asma'u, mun tafi, sai wata rana." Tun da suka shiga motar Aminu babu abi da yake 80 sai Zub da hawayc duk yanda Ahmed ya yi kokari ya ga ya shawo kan Aminu ya yarda Asma'u ba ta mutu ba abin ya ci tura, saboda shi kawai ya da abin da tsohon nan ya fada, tunda an ce dan uwansu ne. Ahmed ya ce "Haba mutumina ka daina kka haka nan ni fa na san Asma'u tana nan da ranta bata mutu ba. Garin da take ne kurum ban sani ba, amma tana yawan kirana waya muna paisawa." Aminu ya ce "Mutuwa fa aka ce ai ka san baya ba ta da kadan komai yana iya faruwa ba mamaki Asma'u ta rigamu gidan gaskiya, kuma gashi ma har an ce gurin haihuwa ta mutu." Ahmed ya tausasa murya cikin KoKarin sa na rarrashin abokinsa 'Amma in ba ka manta ba shi wannan tsoho ya nuna mana wai ta mutu da dadewa har ma an y1 shekaru alhali

Chapter 5 of 7