Share this page
yake yi, kar ki daga min hankalinki dan Allah, gan.............." "Yaya, ka fa zo, Hajia na kira" AISHA TA fada sama sama sannan ta juya da sauri ta koma A dole ya katse kiran yana karra tabatarwa maman Yusuf cewar gayanan zuwa, kar ta daga hankalinta plz A lokacin da ya shigo falon Hajia, inda sarki ke kwonce, matansa na nan a dole a irin wannan lokacin, da baban malamin masallacin gidan na zaune daf da shi sosai yana maimaita kalmar shahada, hakan ya sa gabansa ya yanke ya fadi kansa ya sara da sauri ya kai dubansa wajen Hajia inda take zaune kanta a kasa da carbinta tana ja idannuwanta a rintse tana ta ambaton sunnan Allah, dan a irin wannan lokacin ko waye kai dole zaka ji tsoron wanda ya isa ya busa kuma ya janye numfashin bawa, domin kakari na fitar rai shine ya cika falon, duk irin musun da uwar gidansa ke yi bakinta ya mutu ta kafe shi da kallo ta gaza furta koda a, sauran dake zaune kuwa an umarce su su masa addu'a ko su fita dan ba'a bukatar kowa ya daga murya a wajen Sosai kirjinsa ke dokawa ya karaso da sauri ya duka ya rike hannun dan uwansa, wanda ya zamo tamkar ya dafa wani abu marar kasashi, kamar ba tsokar naman mutun ba mai dauke da kasusuwa da nama da jini, a hankali ya amshi hailalar da ake ta maimaita masa idannuwansa na kallon wajen da ya zarce tsayuwar dan Adam, sannu a hankali har yannayin dan rike hannun dan uwansa da ya yi ya saka baki daya hannunsa ya yi nauyi a hannun mahaifin Yusuf Jiki ba laka ya sake damke hannun, wasu irin hawaye suka taru a cikin idannuwansa suka shiga zubowa a hankali saman kuncinsa ya gaza dagowa kunnayensa na jiyo masa furucin malan na sanar da sako mafi dukan zuciyar mahaifiya, Mata, ya'ya, yan uwa, dangi, da jama'ar gari baki daya, cewa RAI YA YI HALINSA Kukan matan ne ya nemi hargitsa masa kwakwaluwa ya ringa jin tamkar ciwon shanyewar barin jiki zai kama shi, a birkice ya dago dubansa yana jin duhu zai mamaye shi, jiki ba karfi ya kama da kyar ya mike ama ina, abin ya zo masa kai tsaye kuma a irin lokacin da bai shirya ko tsamaci haka ba, duk da ita dama MUTUWA takenta kennan, bata zuwa a lokacin da ake tsumayinta dukda babu bawan dake zama yace zo na shirya sai wanda yake cikin halin yau i yau!, Mutuwa dai wannan mai tonon asiri a yau ta dauka, ta katse jin dadin Dubai zata nada na dubai, ta katse shan wahalar Dubai zata dora ta Dubai, mutuwa mai yanke dukan wani farin ciki ko nau'in wahala, a daidai lokacin da ya yi baya zai zube A'isha ta mike ta zuba masa ido abinda ke zuciyarta na zuciyarta, mahaifiyarta ta yi ta yi ta tashi dan ta agaji wanda take yiwa kallon shi ya rage a matsayin wanda zai hau kujerar dan uwansa ko salon kidan ya cenza domin idan har babu ɗaya tsayaye sarauta zata koma hannun kannin riga ana ji ana gani, a lokacin ne kuma Yusuf ya karaso jiki ba laka dan tun a kofa kunnayensa suke jiyo masa hargitsewar da masarautar ta dauka , a dole ya karaso yana jin gaba daya komai ya fice masa a rai, hankalinsa ya tashi, tashin hankali kala kala ya ziyarce shi, ciki harda tunanin mahaifinsa da abinda ke iya damun uban nasa Da sauri ya karasa wajen da liman ya kama mahaifinsa yana masa sannu da nasiha irin wace ake yiwa wanda ya yi rashi ya zaunar da shi daf da mamacin wanda aka rufawa zanin gado sabo dal aka kuma tsawatarwa matan dake kuka kamar zasu tada dakin da hayaniyar kukansu A hankali ya kai hwuiwoyinsa kasa, ya kama hannayen mahaifinsa ya zuba masa ido, a tausashe sosai ya ce" KA yi hakuri Abu, kar ka daga min hankali fiye da halin da nake ciki a yanzu dan Allah" dumin hannunsa dake shiga cikin nasa ya saka shi jimke hannun da karfi sosai hawayensa na ci gaba da zuba tamkar an bude pampo Hajia ta share hawaye a sanyaye bayan ta gama waya da asibiti ta dubi wajen da su YUSUF suke a tausashe ta ce" Ku ne alwalinsa, kunne ja gabarsa, Allah ya masa rahama, ku yi masa shinfida mai kyau, yanzu za'a zo a bashi kulawar da ta dace sai a kwana ana masa sauka, Allah ya jikan ka uban talakawa...." Ta karshe muryarta na rawa sosai wani hawayen na sake bale mata, da kyar ta sake sharewa tana kallon Aban Yusuf da ya karaso da taimakawar Yusuf ya duka a gabanta ya kama hannayenta, kwarai shi ya dan irin radadin da take ji, shi ya san Wacece ita, tun sunna yara sukan yi mamakin jarumcinta, ama mahaifinsu ya taba fada masu, tsarin Sarautar garinsu dole sai da jajirtaciyar mace irinta, dan kuwa a gobe gobe da safe da zarar an birne mamacin za'a naɗa wani sarkin a ci gaba da zaman amsar gaisuwa, abinda zai zamo rikici na mamaki idan har akoy masu harin kujerar, kujera kuwa tabas akoy masu harinta na wajen gida da na cikin gida A sanyaye ya ce" Ba zaki yi kuka sosai ba? Bana so abubuwa na dira maki a zuciya Hajia" Ajiyar zuciya Hajia ta sauke mai karfi tana kallonsa a sanyaye ta ce" Idan na fashe da kuka zai dawo min ne?, yaya zan yi? Aban Yusuf na rasa uwa, uba, miji, yanzu kuma yau na rasa baban d'a, tabas mutuwa tawa ce ban dandana ba, Allah ya musu rahama ya bamu kyakkyawan karshe" Yusuf dake kallon mahaifinsa a tausashe ya zuba mata ido yana kallonta Tabas bata taɓa maganar da ta shiga zuciyarsa irin ta yau ba Kansa ya dauke yana kallo likitoci suka shigo bisa jagorar A'isha, aka dora mamacin aka fice da shi bangaren da za'a kimtsa shi a cen din ne kuma za'a masa addu'a har garin Allah ya waye Sai da aka fita da shi Hajia ta riko hannun mahaifin Yusuf tana kallonsa ta ce" BELLO, ka san me yake jiranka, sai da na hanna fitowar YUSUF, ama ya fito, ka ja shi ku koma gidan nan, sai na neme ku" Wannan karon YUSUF din ne ya dubeta da kula , sannan ba da daga murya ba ya ce" Inaga ya dace ku mayar da maganar buya gefe, dan babu inda zan je ko ya je ga gawa kwonce, duk mai so ya zo ya gwada abinda ya fi iyawa, Allah ne mai komai, idan har Allah ya ƙaddara tare za'a birni gawarwakinmu a gobe buya ba zai hannamu mutuwa ba hajia " Hajia ta zuba masa ido, zuciyarta na dokawa sosai, tana hangen abinda mijinta ya fada a kan yaron da bai ga girmansa ba bai san waye shi ba, ya Allah, ya Allah A tausashe ya sake kama mahaifinsa ya mikkar ya rike shi sosai suka fita ya nufi bangarensa da shi, dan yana so ya fara samun nutsuwa kafin ya je a kwana wajen dan uwansa, Yana fitowa A'isha ta dawo da sauri ta shige ciki wajen Hajia, yaronsa kuwa da sauri ya zo ya talaba masa mahaifinsa suka kama Abu sosai suka fice da shi ba Dar ko tsoron wani ya nufo shi A'isha na shiga ta karasa wajen mahaifiyarta, a daidai lokacin Hajia ta sada kai ne hawaye sun tarun mata a cikin idannuwa sosai tana ta jan carbi tana godiya ga Allah da jarabawar da ta sameta , ta rasa yaronta Bama zata iya tashi ba bale ta je inda gawarsa take, sai dai dadin musulunci addu'a na tarda bawa a duk inda yake Da sauri ta dago jin an zauna daf da ita ta zuba idannuwanta cikin na A'isha A'isha ta dan ja numfashi tana kallonta ta ce" Hajia, waye zai fara shiga kabarin marigayi?" Da mamaki sosai Hajia ta zuba mata ido, da yannayin muryarta da ta fara raunana saboda kukan dake cin zuciyarta ta ce" Dama akoy wanda zai fara shiga sama da BELLO da YUSUF ne?" Da sauri da kuma mamaki ta zubawa mahaifiyar Tata ido, muryarta ta kasa boye mamakin ta ta ce" BELLO? Bellon da ya fada cewar baya ra'ayin sarauta Hajia?" Wannan karon hawayen dake cikin idannuwan Hajia sun samu zubowa, ta saka bayan hannunta ta share tana kallonta ta ce" Fadarsa ce, ra'ayi ne na jin dadin harshe ya fada, kuma koda baya nan inace kin san ya haihu, domin ja gabar garina kin san ko wanene ko?" A'isha ta kasa daidaita tsuguninta saboda kaffafuwanta da suke son neman fitinarta sakamakon tashin hankalin dake son damunta na amsar da ta san me ake nufi da ita wace da wahala idan har ba zata iya yin fito na fito da dangi a kan wannan ba, sai dai da kula sosai ta ce da mahaifiyar ta " dama akoy wanda ya cencata bayan RISLAN ne?, nagartar yana da ita, makaranci ne, malami ne, mai jin tsoron Allah ne, ba'a taba kama shi da wani laifi ba, kuma daidai gwargwado yana da kudi, me ake so a daurawa talakawa? Kar dai ace mashayi mazina................." Harshenta ya datse saboda zazafan marin da Hajia ta sauke mata a saman kuncinta, rai bace sosai ta ce" Asalamu alaikum, alhamdulilah mun tsaya bakin nan a free page, zamu nausa cikin labarin, domin AZAL din na gaba, rikicin na gaba, zazafar soyaya mai rikita zukata na gaba, darasi na gaba, kai ba zaka gane ba sai ka shigo mun tafi tare in sha Allah An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 12 of 12