Share this page
rikota da hannayensa yana son sai ta nutsu ya ce" Mahmah, ba fa abinda ya sameta, buguwa ce a hannu tana wajen likitocin, ba budurwata bace, adaidaita ne kawai muka hada da ita ina gagawar zuwa na Ganki, Please kar ki cire karin ruwan ke da ba ce lafiya gareki ba?" Sai a lokacin ta kalli karrin ruwan, kai ita fa tunda ya shigo ta ji ta warke daga dukkan wani abu da ya tsaye mata a kirjinta , ko yanzu zuwan su sarki da A'isha Sarkin kawai ta iya amsawa gaisuwar da ya mata, yau shine harda tambayarta jiki? Kwarai ta yi mamaki , A'isha kuwa ta zo din ama bata jin lokacin da ta tambayeta jikinta ba, itama bata bukata, dan ta riga kuma ta rantsewa kanta ba zata kuma daukan wannan wulakancin na A'isha ba! Sai da ya tabbatar da jikinta da sauki sannan ya barta bayan ya sheda mata lekawa zai yi ya ga jikin yarinyar, ita dinma ji ta yi dama zai yarda ta cire karin ruwan su tafi, sai dai ta san yanzu kuma ya zo ba zai yarda da komai ba , sai ta bi tsarin likitoci koda bata so dan ya zauna ya nemi tayar mata da hankali ba komai bane a wajensa a kan lafiyarta Aminu ya samu tsaye a kofar catégorie din da aka saka RAUDA Da sauri ya dan duka yana ba YUSUF din hannu dan a dazu bai san waye ya dauko ba sai yanzu da aka gama komai na lafiyar Rauda aka sheda masa wanda ya dauko din, hakan ya bashi mamaki ainun Da kula sosai YUSUF ya ce" Tashi mana, yaya jikin ta? Ka santa ne?" Aminu ya dan dago din ama ya kasa mike kafadarsa da ta Yusuf din dan girmamawa ya ce" Alhamdulilah da sauki sun sakata barci dai, na santa biya muradi yar anguwarmu ce, Ni kuwa Ni ke mata dan sahu kulun" Yusuf ya bude dakin ya shiga yana sauke idannuwansa a saman kanta, tana kwonce lambak tana barcin da karin ruwan ke sakata, an daure wajen da ta ji raunin an dan sasabto mata rigarta sosai Dauke dubansa ya yi ya kalli Aminu ya ce" Ka je ka sanar a gidansu, tunda da wahala su barta ta koma gida yau" Aminu ya yi tsai ya rasa abinda zai fada, a zuciyarsa kuwa tunani yake yi waye zai fadawa? Babu wanda bai san Rauda da rayuwar da take yi a gidansu ba, ba zai so Maman Rauda din ta zo nan ta wulakanta ba a cikin mutane, dan haka ya ce" Gidan nasu ne ba kowa ai Sir" Ido ya sake zuba masa yana son gane yarensa, wani irin gidansu ba mutane? Kasa hakura ya yi ya ce" Ban gane gidansu ba mutane ba, ina mahaifiyarta ne? In ba mahaifiyarta ai Akoy mahaifinta......ko yan uwanta????!" Fuskar Aminu nan take ta nuna alamu na raunin maganar dake bakinsa, a rayuwa yana tausayawa Rauda kuma yana yi mata fatan alkhairi, shi da ace yana da dama walahi da ya raba Rauda da rayuwar gidansu, Rauda kusan kowa a Anguwar nan na tausaya mata dan yarinya ce mai mutunta kowa, idan zata wuce sai ta gaishe da kai ko me kake yi, fuskarta da sakewa , du irin ukubar da take gani tana matukar jurewa bata bari tana yawan nunawa kowa ba, in dai ka santa ka san me take gani a gidansu ita da kanninta, Rauda tana gannin jarabawar rayuwa kala kala , a da laifinta ake gani saboda mama ta bi kowa ta fada masa bata ji sai yawo sai menene, sai dai yau da gobe ta wuce wasa kowa sai da ya ga asalin wacece Mama aka dawo daga rakiyarta ake kallonta da halinta A raunane sosai Aminu ya ce" *bata da iyaye biya muradi, sun rasu a hanyarsu ta dawowa daga kauye da yan uwanta*" Dukansa ne maganar ta yi? Ko menene ? Bai san lokacin da ya kurawa Aminu ido na yana kallonsa da bugawar da zuciyarsa ta yi "A yanzu haka tana rayuwa gidan kannin mahaifinta ne, shi kuwa ba mazauni bane, matarsa din kuwa idan har ta zo nan zata daga hankalin marainiyar Allah ne, idan har ba damuwa Ni sai in kwana a waje da safe zan rakata in fada, Duda ba lallai ta yarda ba ita maman nata" Aminu ya idasa fada yana sada dubansa daga na cikin idannuwan Yusuf A hankali Yusuf ya juyo da dubansa kanta ya zuba mata ido.... Gashin kanta a barbaje yake saman matashin kan da aka dora kanta, Fuskarta a sake take sosai , lipstick dinta har yanzu yana nan saman jan bakin da ta dan shafa Idannuwansa ya janye da nufin juyawa suka sauka a kan kaffafuwanta dake bude, farare tas tas da su har faratunnanta tas tas da su , harta tafin kaffafuwanta a idannuwa kawai idan ka kalla zaka ga mai tsafta ce ita din ko halitarta ce haka, dan luwai luwai suke abin shiga ido Dauke dubansa ya yi ya sake duban Aminu da furucin dake saman lebensa ya ji kamar maganar na neman yi masa nauyi Tambaya ce a bakinsa Tambaya ce a harshensa So yake yi ya yi tambayar So yake yi ya karra jin bayanin abinda bai shafe shi ba So yake yi ya ji me Kennan? Yannayinta na iya tashi tsaye ajiye shi a wata matsaya guda , itace irin ya'yan nan ne sangartatu da iyaye suka lalata take gannin daidai take da uban kowa A dazu furucinta a kan iyayenta ya saka shi tunanin eh lalle iyayenta bata haɗa su da kowa sunna gida ba zata yarda dan ta fito yawace yawacenta a zage su ba! A yanzu kuma sai, sai, sai yake jin kamar numfashinsa zai tsaya a kan son Sannin *WACECE ITA, ME YASA TAKE IRIN RAYUWAR NAN?* , sai dai ya gaza tambayar Aminu, kwata kwata bin digigin nan ba halinsa bane, abin nan bai shafe shi ba A tausashe bayan ya lumshe idannuwansa ya bude a kan Aminu ya ce" Happy juma'at mAh people 🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶 *AZAL!* 🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶 *SAJIDA NIJAR* *PAID BOOK* _Bismillahir rahamanir-rahim._ *11* *wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍* *TALLAH, TALLAH, TALKAH* _*TOH TO TO!*_ 🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_ _Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_ Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake _Amarya_Uwar gida_ _Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_ _Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_ INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼 🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI* *🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU* _KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_ _SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_ 💁🏽‍♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻* 💁🏽‍♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI… _MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_ *ADRESSE 94536935 94.53.69.35* *Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER* KARKU BARI A BAKU LABARI🥳 Litattafan marubuciyar Duk karyar kada Yar mahaukaciya Bak'a ce Bani da zabi Daga tafia daukar soja Neman na kaina Kutkale Mage Bani da zabi Idan ka raina inda kake Umughuluk itifal Duk nisan jifa Wata kokowar Ni zan ladabi Dakika biyar Da ciwo a zuciyata Aure yakin mata Alkalamin Kadarata Dutse Daga tafiya daukar soja Makauniyace ND now *AZAL* A tausashe , bayan ya lumshe idannuwansa ya bude a kan Aminu ya ce" Ka je wajen ka kwana, ina fata kai baka ji rauni ba?" Aminu ya amsa masa cewar shi bai ji ciwo ba sannan ya fita ya samu wasu maza dake jinyar babansu ya zauna wajensu yana ji a ransa ba zai iya tafiya ya barta ita kadai a asibitin ba, ko mahaifiyarsa ya fadawa ga inda ya kwana ya tabbata zata tausaya mata, kowama yana son taimaka mata, marikiyarta ce tamkar kwalba wajen Shari, tana iya hada maka wani balakin dan kawai ka taimaki Rauda din YUSUF kuwa bai bar dakin ba sai da ya daidaita abin kusan gadon dake iya shaidawar tashinta, haka kawai ya dan sake zuba mata ido kafin ya fice ya je wajen doctern da ta dubata suka dan tattauna ta sake tabbatar masa a asibitin ana kwana ana leka mararsa lafiya ne, idan ta motsa lalle za'a san motsinta koda abin karaurawar bai yi kuka ba Daga nan ya koma wajen mahaifiyarsa ya zauna saman kujera sunna taba fira har mahaifinsa ya shigo shima ya zauna saman wata kujerar , nan YUSUF ya mike da nufin tafiya sai mahaifin nasa ya umarce shi kan ya zauna , bayan ya zauna din ya zamto mahaifin nasa na dan hiratarsa, hakan ya sa mahaifiyarsa sakewa sosai tana ta yiwa mijin nata fira, dama ance mai d'a wawa , mahaifin YUSUF sai a lokacin ya samu salama da kwonciyar hankali a zuciyarsa yana tuna yadda suka rabu da A'isha, domin a wajen so ta yi ta ci gaba da zazagin Yusuf gaba daya sai ya ki saka baki, karshema sai ya ce ai sai hakuri da addu'a Allah ya shirya mana shi ya fi ALKHAIRI da la'antar, tunda ya fadi hakan sai ta ringa binsa da wani irin kallo , ko na menene? Allah masani, wani lokacin yakan so yarda da wata magana da abokinsa ya taba fada masa, Akoy wani lokaci da suke jaje irin na familly da rashin jin ya'ya dai da sauransu da abokinsa kuma uban gidansa Mai Damagaran, a ranar ne ya ce da shi" HONORABLE, a cikin yayanka ka kiyayi gagawar furtawa YUSUF wasu kalaman, ka kuma yi kokari ka ringa taro rashin jinsa, domin ku so ko ku ki YUSUF sai ya gaje ku!" A lokacin ne yace da shi" Mai martaba YUSUF dai nawa? Ai Yusuf ba zai taba duban sarauta ba, ka ganshi a nan ya fada ya kuma fada cewar mu rike kayarmu, ta yaya muke tunanin shi zai zo ya ringa zama gwamnati na masa albashi? , yace idan bamu sani ba mu sani shi ya wuce jiran dauka da umarni daga gwamnati, cewa fa ya yi tunda ya zama karamin kwari gwamna na iya yin yadda ya so da sarki ya rainawa sarauta wayo, ka san shi matsalarsa duk abinda zai ja masa wani raini ko halin karanta baya ciki, gashi Allah ya taukaka shi a cikin kankanin lokaci, a yanzu idan ka ji wanene YUSUF sai ka yi mamaki, ko mu mun san Allah ya dasa shi, sarauta kam idan da rabon Yayanmu sa hau da wuri ta yiwu sai dai RISLAN" Shine mai martabar ya yi murmushi yace da shi" ba'a cenzawa tuwo sunna komai gyaran da zai sha, gaskiya kuma zanen dutse ce, kai ka san jinnin da ya isa ya hau , tunda kuka yarda muka san da lauje cikin nadi a je a dawo koda kasa ta bini idonmu Akoy kundin labari, arzikinsa kuwa dama haka ake so sai ya ciyar da talakawa da shi, ama fa ya dace kanwarka ta farka daga barci domin *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA* ko ana ruwan muzuru sai ya yi" A hankali Hon BELLO ya dan juyo ya zubawa YUSUF ido A zaunen da yake mayafin Rauda ne a hannunsa yana dan gogawa a wajen hancinsa wanda shi da kansa bai san asalin turaren dake jiki yake shaka ba, shi dai ya rike yama manta na MEYE abin dai a hannunsa kamar nasa haka ya masa rikon gaske Suturar dake jikinsa yake kallo har zuwa sarkar dake wuyansa yar siririya mai ruwan ash, ko karfe ce ko azurfa ce? Wa ya sani Damatsunansa da suka shake a cikin rigar nan ya zubawa ido har zuwa ƙafarsa dake cikin takalmi kafa ciki ama ba mai nauyi ba Agogon hannunsa ya zubawa ido da dayan hannunsa dake cikin na mahaifiyarsa a hankali yana kallonta tana ta labari yana murmushi Murmushin ya samu kansa da saki yana dauke dubansa daga kansa Abu daya ya sani shine da wahala YUSUF ya wulakanta a duniya, da wahala ya wulakanta saboda baya haɗa su da kowa, bai taba yarda ya haɗa soyayarsu da ta kowa, rabonsa da siyan shinkafar gidansa har ya manta, idan ya bada kudin cefane niya ya yi dan badangarci, ya jima da dauke masa hidimar kannensa, ya jima da fito da mahaifinsa cikin manyan kwarin kasa, domin a kasar Nijar baki daya a yanzu mutanen dake mu'amala da shi, shi da kansa ya san dan tsaya masan da yaronsa ya yi ne ba dan shi karfinsa ya kai cen ba, domin a yadda duniya ta zama idan kai ba kowa bane baka da fada a ji a gaban kowa hakan ne, shi BELLO yana da damar shiga inda ya ga dama a lokacin da ya ga dama idanma bashi da sanaya da mutumen da zarar ya fadawa YUSUF za'a neme shi ne yana zaune a saman gadonsa, lokuta da yawa shine ke yiwa sarki hanyar halartar wani taron , a yanzu dai a Nijar duk wani baba yana daukan mota ne a park din YUSUF, hakama a wasu kasashen makota, YUSUF ya mallaki park park da dama a garuruwa, kuma duk wata babbar mota yana yi mata nata daban ne, ya jima da shiga cikin duniyar bada kwongila a tsarin gwamnati, mutun ne mai nema ido rufe kuma a kulun habaka kasuwancinsa yake yi , ya ki ya matsa daga Damagaran da garin mahaifinsa ne saboda iyayensa, A hankali mahaifinsa ya ringa jin wani abu mai kama da kunya da jin nauyi Shin dan sun haife shi ne suke wulakanta shi haka? Kwarai matarsa tana da gaskiya ya dace ya fara yiwa kansa wa'azi ya duba abinda yake ciki da yaronsa Daren dai, shi bai samu rintsawa ba, domin YUSUF mahaifiyarsa na yin barci ya KWONTAR da kansa a saman gadon hannunsa cikin nata, dayan kuwa rike da mayafin Nan barci ya dauke shi, shi kuwa ya yi gadinsu har aka fara kiraye kirayen sallar asubahi Farkawa YUSUF ya yi yana yin hama kadan hadi da son bude rinanun idannuwansa ya sauke dubansa cikin idannuwan mahaifiyarsa da kuma mahaifinsa dake daf da ita yana taba goshinta da wuyanta Murmushi ta sakar masa, haka shima ya mike ya nufi bayi yana dan sake mikar da jikinsa dan jin du ya ririke Kulawa ya yi da kansa ya dauro alwallah ya fito yana jin jikinsa du a ririke saboda rashin wanka da brush Yana soke mayafin Nan a aljihunsa mahaifinsa ya karaso ya mika hannayensa yana cire masa sarkar nan dake wuyansa Yana cireta ya saka a aljihunsa kasa kasa ya ce" Mu je masalaci" Kallon fuskarsa yake yi da mamaki harda tunanin toh fa, sabon salo MEYE wannan din kuma? Ko dai shi din ma bashi da lafiyar? Shi kuwa ya yi gaba yana boye yannayin da yaron nasa ya shiga a ransa suka ba Nurse din damar shiga ta taimakawa Mama ta yi wanka da alwallah da sallah , wace ta nuna yanzu kam zata iya jikinta ya warke ba sai an kamata ba, ama Duda haka likitar ta ki tafiya tana kula da ita har ta gama aka gama gyara dakin nata aka saka turare mai sanyin kanshi aka barta A waje kuwa sunna gama sallar ya fito ya je wajen da Ishak ke tsaye da manyan ledoji dauke da kayan abinci da su fruits Nuna masa ya yi ya bashi dan mahaifinsa na nan kuma baya so su dagawa mahaifiyarsa hankali a kan wannan Jiki ba karfi Ishak ya bashi ledojin ya koma cikin motar da fatan samun lafiya wa mahaifiyar YUSUF din tare da fadin yanzu direbansa zai kawo masa motarsa da tufafinsa a ciki sannan ya tafi da ky din gidan a hannunsa Yana juyowa ya ga Hon BELLO tsaye kofar asibitin yana kallonsa, zuwa lokacin haske ya fara yi sosai a garin Fuska ya hade dan ya riga ya san yanzu zasu hau sama su fado, domin ya ga Ishak din da yake gudun ya gani Yana isowa kunnayensa suka jiyo masa Muryar mahaifinsa yana fadin" Me yasa ya juya?" Dakatawa ya yi yana kallon mahaifin nasa, ya sake kallonsa da kyau sai kuma ya dan dauke dubansa ya ce" Yana da uzuri ne" Murmushi Hon ya yi ya mika hannayensa ya ce" Kawo na rage maka kayan" Wannan karon kasa boyewa mamakinsa ya yi, har ya dan ja baya kadan yana kallonsa kafin ya ce" Me yake faruwa ne?" Hon Bello ya zuba masa ido ya ce" A ina fa?" YUSUF ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Na ga yanzu Bama gabanta , kuma ka ci gaba da wani abin daban Abu" Murmushi ya yi yana riko ledar dake dauke da jus ya ce" Bani Ni haba ya ina so in taya ka kana wani kiyawa" Baki ya saki yana kallonsa, sai kuma a hankali ya ce" Ina son dibarwa wannan yarinyar da ta kwana a nan" Yana fada ne yana nuna daidai dakin da RAUDA take, daidai lokacin ne kuma Raudar ke cikin fadan a cire mata abinda yake hannunta gida zata je, Aminu sai faman kwatanta mata yake yi ama ta nuna masa ta ji sauki gida take so Samun kansa ya yi da nufar dakin ya murda ya shiga kai tsaye yana sauke dubansa a kan Aminu dake tsaye, da Nurse din dake tsayen itama rike da dan kwanon nan nasu na likitoci, sai RAUDA dake tsaye rike da abin gado sai luuuuuu take yiwa ido saboda abin magani ama fadi take yi gida zata je a salameta "Me yake faruwa?" Ya iya furtawa bayan ya kare mata kallo ya juya yana kallon Nurse din da Aminu Nurse din ta ce" Sir, zuwa na yi dan na cenza mata karin ruwan nan, na tarda ita ta farka shine tace ba za'a saka mata ba gida zata je yanzu yanzu" YUSUF ya kalleta da dan mamaki a fuskarsa ya ce" Ke da baki da lafiya zaki tafi gida?" Idannuwanta ta dauke daga fuskarsa tana saukewa kan Aminu, a raunane ta ce" Ina son gida Aminu, ta yiwa uncle a gida ya kwana yana nemana, Ni gida zan je!" "Ki yi hakuri y'ata a cire maki sai a kaiki gidan, zauna a cire maki" Abu ya fada a tausashe yana karewa Rauda kallo da son karantar yannayinta Ajiyar zuciya Rauda ta ringa saukewa ta zauna saman gadon, hakan ya sa sket dinta tatarewa sosai har kamar cinyarta dake fara sol zata bayyanar da kanta, duk kuwa yadda ta yi dan ta rufe jikinta hakan ya gagara sai kanta da ta sada kasa cike da jin kunya da takaicin zaratan mazan dake dakin a irin wannan lokacin jikinta na son bayana Har dan dukawa Nurse din ta yi wajen amsa umarnin Hon ta karasa ta cirewa Rauda sannan ta saka abin goge jinnin nan ta goge mata ta danne mata da auduga Da kula sosai Abu ya dubi Aminu, zuwa lokacin Yusuf ya fice ya nufi dakin mahaifiyarsa , ya ce" A me kuka zo ne?" Aminu ya ce" Sir, ai da daidaitar tawa ce aka yi accident din, tana nan police station sun ce idan an gama fitar da sakamakon wanda bashi da gaskiya nima sai sun buga min takarda na biya diyyar yawo da ita ba awo, zamu tsayar da adaidaita ne" Hon ya dan gyada kansa ya laluba aljihunsa ya ciro abin saka kudinsa ya ciro kudi masu dan kauri ya bashi da kula ya ce" Ku shiga ku je, sannan ka sanar min gidan su yarinyar zan zo da dare dan na basu hakuri na sanar masu hatsari ne kuka yi , Ni da YUSUF in sha Allah" Sosai Aminu yake godiya, yana so ya nuna masa ba sai sun zo ba dan kar su ga wulakanci gurin Mama, sai dai ya kasa fadin hakan, Rauda kuwa a lokacin ta shiga wanke bakinta koda da bakin ruwa ne, dan ji take du a takure, Bama kamar jikinta ji take yi kamar kazantar duniya ta tare a kanta Yana ficewa ta fito tana tambayar Aminu wayarta da mayafinta da pos dinta Ya bata wayar da pos din, ama bai san inda mayafin yake ba, dan haka suka fice tana jinta wani iri duda a garin yan mata na fita ba mayafi, ba wani abin bane a garin A cikin asibiti kuwa Abu na karasawa dakin ya samu YUSUF zaune yana ciyar da mahaifiyarsa wace take zaune itama ram da ita tana masa fira yana murmushi Yana shigowa YUSUF din ya zuba masa ido, idannuwansa cike da yannayin son yin tambaya, ama ya gaza yin, shi kuwa Hon karantarsa ya yi tsaf sannan ya nemi waje ya zauna ya bude wani abincin da kula ya yi bismillah kafin ya kai bakinsa ya ce" To wai haka ake yiwa budurwa? Sai ka tafiyarka dan tana rigimar gidansu za'a kaita? Lalabasu fa ake yi ko su dagawa mutun hankali walahi" Dan dakatawa ya yi da son kaiwa mamansa abincin a bakinta ya dan kallo mahaifinsa, kasa kasa ya ce" Ba budurwata bace" "To ama kama sonta ko?" Ya katse shi da son lalle sai ya ja shi surutu Da sauri ya dube shi, sai ya samu kansa da sakin dan murmushi dan sarai ya kula wani sabon salo ke dawainiya da mahaifinsa wanda ba zai sakankance ba sam, a hankali ya ce" Allah ya raba Ni da soyaya, adaidaita fa muka hada, ana ta wani bata hakuri tana shirme ai sai a barta ta yi yadda take so!" Ido Abu ya dan zarro, ya ce" Kai, ikon Allah, aya, Ni kuwa ta bani tausayi, kuma kamar tana tsoron kar iyayenta su ga bata dawo gida ba, sun tafi dai yanzun da dare sai mu je mu na iyayen nata hakuri mu fada masu a inda ta kwana dan ga dukkan alamu bata saba kwana a waje ba gaskiya" Mama ce ta ce" Yarinyar da suka samu hatsari ko Aban YUSUF?" Aban Yusuf ya amsata, ta ce" Nima fa na so gannin jikinta dan nan ya shigo da jinninta a jiki, dole ta damu iyayenka ba cen sunna cigiyarka, Ni da nice ai ba zan iya barci ba sai na ga yara mace ta dawo gefena ta kwonta, karma su daketa su ƙi yarda Ni walahi dama rakata ka yi ranka shi dade" A hankali Yusuf ya sake debo abincin ya nufi bakin mahaifiyarsa da shi a ransa yana ayana' anya kuwa damuwarta gidan ne? Koda yake ance tana da Kani ko?, a da ba zan bi Abu gidansu ba, but zan so na ga marikiyartar nan da idona!' Haka suka ci gaba da fira hankali kwonce har likitan Mama ya zo ya salameta suka nufi gidanta Tafe suke cikin adaidaitar ita da Aminu , dan ba yadda bata yi da shi kan ya je zata zo ya kiya ba, domin bata so ganninsu tare ya jaza masa wata fitinar ama sai ya nuna mata ko daya zai rakata su je tare sai su fadi abinda ya sameta ko dan marikinta kar hankalinsa ya tashi Banki suka je, ta sauka ta shiga dama idan zata fita duk wani abinta mai mahimmanci da ya shafi katin shedar yar kasa ne, katinta na banki ne takan fita da su saboda tsaro , takardun ta na makaranta kuwa dama a gidan inna suke da na haihuwa da sauransu domin akoy ranar da ta taba barin takardun ta na makaranta aka saka masu wuta akace ba'a san an bar fitila mai kananzir

Chapter 8 of 12