Share this page
bisa umarnin RAUDA wace kasa kasa sosai ta ce" Baba buga masu kofar Atu tace Akoy kare , idanma daga nan zamu sauke masu mu juya fine" Tana kiransa da baba ne saboda yana dauke da sunnan mahaifinta, sannan mutun ne mai daraja dan Adam, a kulun idan ya dauki Atu sai ya biya ya daukota ya ajiye su a makaranta, tun tana kiyawa har Atun ta kai kararta wajen Mamanta sai ta mata fadan a kan me zata ki shiga a kaisu da kawarta? A dole take shiga har ya zamo kamar yar gidan du inda zasu je tare ake kai su a motar Bugawa ya yi ya fi a irga , gannin ba'a bude ba ya dawo yana fadin" HAJIA Rauda Inaga sai an yi kira ko kawai mu tura mu shiga?" Rauda ta girgiza kai ta ciro karamar wayarta tana masa alamun tana zuwa Numbar mijin Atun ta dannawa kira Wayar na fara ringin ya daga yana fadin" Da girman kujerarki aminiyar aminiyata" Murmushi ta yi , da salon muryarta ta ce" Muna kofa fa aminin aminiyata" Mikewa ya yi da wayar a hannunsa daga cikin mutanen da basu wuce su shida ba, dan kuwa a dole ya tsame daga cikin taron hayaniyar jama'a ya kilace Wadinnan, domin mutanensa ne na kusa sannan abincin da za'a kawo daga gidan su amaryarsa yake so a kawo masu su, dan na jama'ar da aka yi ya tabbata da wahala a dadada masa rai, duba da ba kowa ke maraba da auren nasa ba Da kula ya masu ja gaba har baban falon, yan matan amaryar saura sunne a gaba, sai Rauda dake rike da wani kula madaidaici tana tafiya cikin yannayinta na sanyi sanyi da kuma tsarin salon tafiyar da Allah ya haliceta da shi har ta karaso kan dokin kofar daidai direba zai juya da kula ta ce" Baba kar ka yi nisa, ba jimawa zamu yi ba" Angon ne da kansa ya juyo yana fadin" Haba aminiyar aminiyata, ya koma idan muka gama ci sai a maidaku gida ko?" Ajiyar zuciya ta sauke ba dan ta so ba tana jin dari darin shiga falon, bata yi tsamanin a falo zasu samu angwayen ba maimakun filin gida, sai dai bata ki shiga ba gannin ba ita kadai bace mace a cikinsu, kuma ita dai ba jimawa zata yi ba gaskiya Takalminta ta cire a kofar dakin, kasa kasa tana binsu da kallo ta yi salama sannan ta sako kafarta mai haske da tsafta tana taka tiles din ta nufi wajen da aka ajiye abincin ta ajiye coolar ta sake juyowa dan neman wajen zama Idannuwanta suka sauka cikin na Ishak da Nafisa Shi Ishak din ba zata iya tantance kallon da yake yi mata ba, ama na Nafisa zata iya ajiye shi a matsayin kallon jin haushi ko na laifi? Allah masani, abinda take hangowa dai kamar tarin jin haushi ne, ta yiwu laifi ta yi mata bata sani ba? Ko ita dinma a wajenta bakin jinnin ta dauko? Dan kuwa ta kasance budurwa mai bakin jini a cikin yan mata, ba kowace budurwa ke mata magana ba, akan ce wai ta cika girman kai , da sauransu, ita kuma tana rayuwarta ne daidai misali Kujerar da ta nufa da nufin zama ce ta ga wata tanfatsetsiyar waya ajiye, a hankali ta dauke dubanta ta dan juya dan zaunawa a wani wajen tana dan sakin murmushin abokin ango na mata tayin gefensa Idannuwanta ne suka sake sauka bayan wani saman salaya, hannayensa harde a kirjinsa, kansa sade kasa , a hankali ta dauke dubanta a kansa ta juya ta karasa saman kujerar dake facin din wace ke dauke da wayar ta zauna ta maida dubanta wajen angon dake miko mata ruwa na cikin jarka yana mata fira a ranta kuwa ta ayana' Na tsani na ga namiji har namiji yana Sallah a daki, dan rashin mutunci ko yana aikin uban me aka yi sallar aka barshi?' Salamce sallarsa ya yi a hankali ya sada kansa yana addu'a har ya gama ya shafa sannan ya mike ba tare da ya kalli kowa ba ya nufi wajen zamansa ya dauke wayar dake ajiye ya zauna yana sake hade rai gannin natacen kallon da yan matan nan suka bi shi da shi, kai subahanalah ya ki jinnin irin wannan hadin da ake yi yan mata da maza, su ba yara ba, ba komai ba ama sai a hadu wai a ci abinci a biya yan matan su tafi, shi kam idan ya tashi dauko hudun nan ba za'a yi wannan badalar da shi ba, yan matan kowace zata yanka ainahin abinda take so a biyata sai a biyata ba sai an zauna ana rainawa junna hankali ba Dubansa ya kai wajen daya daga cikin abokan ango mai sunna Idriss a lokacin da ya miko masa ruwa yana fadin" Biya maradi Allah dai ya kaimu ranar aurenka, a wannan rana ban san wa zai iya amsa sunnansa ba, Allah ya karra lafiya namu" Yannayin fuskarsa bai cenza ba daga daurewar ya amshi jus din ba dan zai sha ba ya ajiye gefe kasa kasa ya ce" Ku salame su mana bafa ba son damuwa" A lokacin da yake furta kalmar "ku salame su mana...." a daidai lokacin ne ya sauke dubansa a kan wace take face da shi tak tak kamar an ajiyeta ne hankalinta sam ba a kan kowa ba, tana rike da goran ruwa bata bude ba , kuma bata ajiye ba Dubansa ya so daukewa tashi daya daga kanta, sai ya samu idannuwansa da dawowa suka sake sauka a kan fuskarta a daidai lokacin da take karanta sakon Bara'atu wace mijinta ya sanar mata mutuniyarta fa gatanan ta daka fuska bayan harda biya maradi a taron, shine ta mata msg din da ya sakata sakin tautausan murmushin da ya saka gefen idannuwanta kadan suka lotsa hancinta ya sake dan budewa kadan sai kuma ya koma yannayinsa saboda gimtse murmushin da ta yi ta dago dubanta a hankali ta kai kan angon kasa kasa ta ce" Kai ko?" Dariya angon ya yi yana fadin" Eh, ba zaki dago mu yi fira ba? Zan kuma kai kararki ne " Murmushi ta yi tana dauke dubanta ta juyo da nufin kallon hanyar kofa, dan mamaki ke neman kasheta na abokanan tafiyar tata, yaya za'a yi su zo waje su wani saki jiki haka a gaban mazan da basu sani ba su ringa fira haka da iya yi? Tun ba'a ce su raba abincin ba har sun bubude sun shiga zubama abokan angon a plate plate sai wani irin iya yi suke yi da Gwali, ita abin har daria ya so bata, ina ajin? Ina jiji da kan? Zamani ya zo mana da sabon salo mai wuyar fasara, ace yanzu mace itace zata yi iya yin da namiji zai gane ta? Lalle wahala bata bar wasu matan ba, WALAHI tsakaninta da namiji sai dai ya bita ba dai ta bi shi ba! A hankali idannuwanta suka sauka a kan fuskarsa, sai dai abin mamaki ko second biyar bata yi tana kallon gefen da yake zaune ba ta dauke kanta tare da nunin alamun bata san da zaman dan Adam a wajen Bama bale ya isheta kallo Mamaki ya kama shi mai girman gaske Har angon da wanda ya sanarwa a salami yan matan suka dawo dan waje ya ja shi ya sanar masa sakon *YUSEF* din cewar a salami yan matan nan baya son takura Rasa yadda zai yi ya yi, a dole cikin murmushi da basu daraja ya ce" Amare, har kun fara raba abincin? Ai da baku ba kanku wahala ba, so nake a maida min ku da wuri ku shirya min hajiata a kawota da wuri wuri, sai kuma na ga har kun fara hidima da mu? Nafisa ce ta yi gagawar dagowa tana sakin fari hadi da murmushi ta ce" Haba elhajinmu, ai ba dawainiya, an riga an zama daya, mun fara ai bari mu gama ku ci idan kun gama sai a maidamu, amaryarka kar ka damu kaima ka san tana hannun manya dole ta sha gyara " Sai da ta dasa Aya Rauda ta dago da mamaki ta zuba mata ido A hankali ta lumshe idannuwanta ta maido dubanta kan Elhaji, yannayin muryarta kasa kasa sannan da sanyin nan ta ce" A'a , a maida mu ya fi, sai ku samu sarari ku ci abinci cikin nutsuwa aminin aminiyata" Da sauri Nafisa ta juyo tana kallonta, duk yadda ta so Hanna kanta nuna bacin ranta sai da ta ce" Mu zamu Hanna su sakewa ne? Ko dama an taba yi basu ci abinci ba mu mu juya? Me muka yi Kennan?" Rauda ta sake tsareta da duban dake nunin abinda ke cikin zuciyyarta, ama bata yi magana ba, sai da ta sake bude baki zata yi magana sai ta ga Rauda din ta mike hankalinta kacokam a kan angon da ido ta masa alamun ita fa tafia take so bayan fuskarta ta wani irin nuna lalaci irin na shagwababen yaro , sannan ta masa nuni da agogon hannunta siriri mai ruwan zeba cewar lokacin ta tafi ya yi Daga yadda yake ya sake dagowa ya zuba mata ido a tsayen da take tun daga yalolon jan mayafin dake yafe saman gashin kanta har zuwa yatsutsanta masu ɗauke da abin lalle irin na mata Kansa ya sake daukewa ya kai dubansa kan Ishaq, sai ya ga shi din ma shi yake kallo da kuma wannan dake tsayen Elhajin ne ya samu da dabara ya nunawa su Nafisa ai ba komai sannan ya rako su har wajen motar dake parker ya mikawa kowace embulop da ya zo kan RAUDA ya miko mata Tata du ta fi tasu girma da alamun ta fi tasu nauyi yana fadin " sai mun hadu da dare wajen kawo min aminiyar ko aminiyar aminiyata?" Murmushi Raudat ta sakar masa tana ajiye kudin da aka bata saman cinyarta a saman labanta ta furta" In sha Allah" Direban ya ja su, matashi da shi irin matasan nan masu zuciyar nema dan yaro ne a shagon Elhajin , haka kuma direbansa ne da gidansa baki daya A lokacin da motarsa ta tsaya bakin Danja kunnayenta suka ringa jiyo mata shewace shewacen su Nafisa dake baya, ama sam bata jin abinda suke fada har sai da motar ta tashi suka dauki hanyar gidan bikin kasa kasa ta jiyo magana kamar haka" Ke kuwa, meye a ciki banda gayar tsiya? Itace fa jarin matar marin nata, shi kuma marikin mashayi ne kuma mazinaci!, Wai nan bikin aminiyarta ake yi ta kusa da kusa ama bakin ciki da bakin hali ya hannata ta yi kwaliya irin na sauran yan mata, ki duba ki gani sai hade rai da jiji da kai na banza , isar baka isa ba, ita ba yar kowa ba sai kwonbo da gashi da kuma kirar nan wace a wannan zamani du mai son ajiye kira irin nata tsaf zai ajiye in ya shiga wajen masu magani, aikin banza bata san yanzu maza yan kyale kyalen yan mata ke jan su, ba wai ire irenta ba?" Kanta ta dauke , bata da niyar tankasu, har wace ke maganar tare da Nafisa ta ce" Asalamu alaikum jama'a....mun zo maku da nagartacen ingantaccen maganin Ulcer, magani ne na Hausa jikake wanda Dubai suka gwada suka ji dadinsa, nagartatun tsatatatun itaciyoyin da suka bamu sasake masu anfani ne ake anfani da su, a nan jamhuriyar Nijar a garin Damagaran a farashi mai rahusa dubu biyu yan naija , yan nijer kuwa 1500francs mai bukata ga numbar +227 96897192 , HAJIA RAHAMA 🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶 *AZAL!* 🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶 *SAJIDA NIJAR* *PAID BOOK* _Bismillahir rahamanir-rahim._ *3* *wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍* *TALLAH, TALLAH, TALKAH* _*TOH TO TO!*_ 🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_ _Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_ Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake _Amarya_Uwar gida_ _Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_ _Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_ INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼 🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI* *🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU* _KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_ _SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_ 💁🏽‍♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻* 💁🏽‍♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI… _MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_ *ADRESSE 94536935 94.53.69.35* *Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER* KARKU BARI A BAKU LABARI🥳 Litattafan marubuciyar Duk karyar kada Yar mahaukaciya Bak'a ce Bani da zabi Daga tafia daukar soja Neman na kaina Kutkale Mage Bani da zabi Idan ka raina inda kake Umughuluk itifal Duk nisan jifa Wata kokowar Ni zan ladabi Dakika biyar Da ciwo a zuciyata Aure yakin mata Alkalamin Kadarata Dutse Daga tafiya daukar soja Makauniyace ND now *AZAL* Kanta ta kawar, bata da niyar tankasu har wace ke firar tare da Nafisa ta ce" FIFI, wai dan Allah baki ga irin yadda mijin aminiyar Tata ke kure mata waje ba? Ke kudinta fa ta yiwu ya fi namu yawa!" Nafisar ta ja dan tsaki ta sake rage murya, domin magana ce suke yi kasa kasa sosai dan kuwa direban dake jan su ko kadan baya jin abinda suke fada , ama ita Allah ya mata karfin ji shi yasa dukkan furucinsu a kunnayenta, kasa kasa Nafisa ta ce" Na zaki gane ba, wannan fa da kike ganninta babbar yar hannu ce, idan kin ga tarin samarinta sai kin sha mamaki, ba za'a ce a'a ba in akace shima yana soyayya da ita din, bata da haram fa, kuma tsaf zata rabaki da saurayinki sai dai ki yi hakuri, gashi ita iyayenma bata da su bale a kai kararta wajensu, iyayenta hatsari suka yi suka mace harda yayarta da kannunta uku, ita dayar nan uwa maya suka bari a hannun kannin mahaifinta, shi kuwa baya hanawa bale sakawa, inma ka kai masa kararta tsaf yake iya daure mata, Ni dai abinda ba zan lamunta ba da ta wulakanta Ishak, ban san waye ke son numbarta ba na amso na bashi ta wulakanta su, ko ji take ba zata samu biyan bukata a wajensa ba?" Da ido dayar ta saci kallonta, gaba take ama tana iya fasara yannayinta, a gaskiya a yanzu da take zaune ba kwaliyar a fuskarta ana iya daukanta a bar su, su da suka shafa hoda da ja gira da su jan baki da gashin ido, to ita gashin idannuwanta kadai sun isheta, danma ba fara bace cen cen din nan, ama yannayin fatar jikinta tamkar ta yan Ethiopia wankaku masu rantsatsen hutu, kai kamanunta kansu tamkar wace ta samo usuli daga su, saima hannayenta da kaffafuwanta, sunna da tsafta da kyan kallo, hannayenta kuwa harda yan faratuna take tarawa na ra'ayi mikaku farare tas tas da su, tana dauke da quality masu fuzga, ba wai manyan duwawu ne da ita ko manyan breast ba, a'a, komai dake jikinta ne dan daidai da tsarin halitar jikinta, sai kuma ta iya saka kaya da wasu yannayin dake daukan hankalin har mata ba iya maza ba, sau tari idan ta halarci taron mata kawai zaka ji ana tambayarta wai gashin idon nan nata ne? Wai me take shafawa? Dan Allah me take anfani da shi a lebenta? Dan Allah yaya take yi kaffafuwanta da hannayenta suke haka cikin tsafta? Sai dai ta yi murmushi tace haka Allah ya haliceta, kuma haka din ne , sai dai wanka kawai da ta karra, ko kwali na koda yaushe take sakawa ba bale kwaliya, ama a haka din dai take da nata farin jinin da ya tsolewa wasu ido Kasa kasa kawar Nafisa ta ce" Fifi gaskiya Atu ta yi sake, Ni idan nice ba zan taba amincewa da haka ba gaskiya, cap, wannan ai sai ta kwace min mijina ina ji ina gani" Daidai motar ta tsaya kofar gidan su Bara'atu , direban ya sauke madubai sannan ya cire masu sakatar motar A Nutse ta bude bangarenta ta fito sannan ta je gefen da suke ta saka hannu ta bude masu ta kuma tsaya a kan hanyar fitowar ta saka idannuwanta cikin ma Nafisa, wace sai da gabanta ya fadi ta dan samu kanta da dan ja baya tana kallonta lokaci daya tana fadin" Ke kuwa lafiya?" Rauda ta bi su daya bayan daya da kallo, sai kuma ta saki murmushi, cikin yannayin da zaka rantse ba zata iya furta wata kalma sama da hakuri ko hailala ba ta ce" Kina da matsala da Ni ne?" Ba yan matan nan kadai ba, hatta direban nan sai da ya juyo ya zuba mata ido, domin a yanzu ras yana ji dan ya tsayar da amon rediyon motar Nafisa ta sake dubanta da mamaki ta ce" Wai da Ni kike RAUDA?" Rauda ta lumshe idannuwanta da wani yannayi ta daga kafarta ta saka cikin motar sannan ta janyo kofar ta rufo da karfin tsiya ta juyo bayan ta ajiye wayarta a aljihun motar tana kallon yan matan gaba dayansu ta ce" Da ke, da kuma ku nake, Akoy mai matsala da Ni ne? Mu warware ta saboda bana son kwonciya da tunanin wani banza, nace inada matsala da ku ne ta yadda zaku ringa wulakantani a gabana?!" Ta karashe a kausashe tana juyowa gaba dayanta Direban ne da sauri ya shiga yana fadin" HAJIA, kin ga kar ki kula su sauko ki yi tafiyarki, ko me suka maki ki yi hakuri kin ji?" Nafisa ta cafe maganar tana fadin" Karma ta sauka, ta yi mana abinda zata yi!, da ke din nakkkkkkkkkkkkkk" K din kawai ya dan fito a karshen furucinta ta samu kanta da dantse harshenta lokaci daya sakamakon dauke fuskarta da Rauda ta yi da mari sannan ta rike mata wuya harda kokarin daneta a cikin motar Ihu suka kwasa sauran yan matan biyu suka shiga kokarin kwantar Nafisa, sai dai gannin abin na neman zuwa kansu dayar ta bude motar ta fice tana haki har takalminta ya cire saboda yadda ta fito daga motar hankali tashe ta sake duban Nafisa dake kai duka a iska bata samun Rauda din, ita kuma Rauda har idannuwanta sun juye ta rike mata wuya taf tamkar wace zata aikata kiyama Gannin za'a yi kisa ya saka shi fitowa da sauri ya bude bayan ya damko Rauda ya fizgota da dukan karfin da Allah ya bashi, ama cikin ikon Allah sai da ya wartota da dan kunnen Nafisa guda wanda ya yi fitar karfi ya janyo ya ja mata shatinen da ya farke mata da jinni Kusan a tare suka saka ihu, shi direban da Nafisar da kuma dayar kawar da ta kasa fita saboda gaba daya Nafisa kanta ta dane garin fadan Mutane tuni sun fara taruwa a wajen motar a lokacin da ta warce jikinta ta sakar masa harara ta sake ridar motar shi da kansa ya so yin hali irin na mata, wato ya ware muryarsa ya kwala ihun a taimake shi, sai ya ga ta janyo wayarta ne da dan yalolon mayafinta Ido tuni sun kade mata ta dubi Nafisa dake ihun ta yanka mata fuska murya a dake ta ce" Ban maki komai ba cikin tarin abinda nake son maki, ba kin ce a ce min idan kika ganni sai kin wulakantani ba? Ni zan fada maki gwa da gwa kin ciri katin fada da Ni mai rabamu sai Allah!, dan na maki alkawarin haduwa goma sai na kawo maki hari sai dai ki kasheni, zan nuna maki mayar nake ta kirki idan na riki wuyanki, haka kuma zan nuna maki mai kwacen mazan mutane nake ta hanyar bin duk wani namijin da zai nuna yana son ki, ke sai na zame maki *AZAL* a rayuwa tunda kika zagar min iyayena!, sannan ki je ki sake bincike labarin da kike da ba daidai din bane karamar yar is....." "RAUDA?" Muryar mahaifiyar Atu ta katse ta Tun daga kanta har kafarta dake ja ba takalmi ta bi da kallo sannan ta karaso da dan sauri tana yiwa ya'yan Atu magana kan ya watsa mutanen dake neman yin taron idi a wajen ta sake zubawa Rauda ido sannan ta leka motar da kuka da ihu ke tashi Sai da ta tsorata gannin yadda jinni ya BATAWA Nafisa atamfarta da fuskarta A tsoracen ta ce" Subahanallah, innalilahi wa inna ilaihi raj'une, menene duka wannan? Yanzu RAUDA dama baki daina fada irin wannan ba? Me ya yi zafi haka? Kai Usman maza fitar da mota a kai wannan asibiti, ke kuma wuce mu je ciki wuce, dan Allah kowa ya tafi ku tafi kawai , du kun tsatsaya an rasa mai kama masa a kashe fitinar nan sai da ta zama haka? Subahanallah Rauda yau sai na saba maki yau sai na saba maki Rauda!" Nafisa da ake tarewa tana kuka ita kadai ta san me take ayanawa a zuciyarta, abu daya ta sani in har wannan mahaukaciyar ta mata ila sai ta rufeta dan na zata taba yarda ba, ashe mahaukaciya ce bata sani ba? Da ta san bata da hankali na zata taba yarda su shaki iska daya da junna ba, a irin yadda take kafa kafa da jikinta ita ko fada bata taɓa hada jinni da kowa ba, abu daya ta sani in dai tana fada da kai in ta sakoka a gaba da habaice habaice da harare harare har sai ka ji kamar ka daina fita cikin sa'ani, sai gashi tun kafin abin ya kaisu da haka daga magana wannan mahaukaciyar ta mareta hadi da yi mata rauni? Ba zata iya yafe wannan wulakancin ba Rauda kuwa bata tsaya ko'ina ba sai cen kuryar su Atu Tana shiga ta samu waje ta zauna a kasa ta sada kanta Jim kadan sai ga mahaifiyar Atun ta shigo , tun kafin ta zauna ta shiga fada tamkar zata ari baki, fada take yiwa Rauda irin fadan da uwa ke iya yiwa y'arta cikin fadan ya ce" Ashe bakya jin magana? Inace nan ma maku maganar fadace fadacen nan kuka ce min kun daina, shine zaki hada jiki da mace har ki mata wannan raunin? Ina anfanin wannan abin da kika aikata Rauda? Ya Salam me ya haɗa ki da ita da zafi? Me yasa wani lokacin bakya kwabar zuciyarki ne? Ko menene idan kika yi hakuri ba Shikenan ba? Mai hakuri yakan dafa dutse , a matsayinki na mace a kulun fada maku nake yi ko muryarku ba kowani banza bane zai ji kai tsaye, komai na mace abin a kilace ne a ririta, komai naki daraja ne da shi, har wancen ya kamo ki ya fitar da ke daga mota? Ya Allah haba RAUDA " A hankali Rauda ta dago idannuwanta tana kallon maman aminiyarta wace take kira da Mama itama, a sanyaye ta budi bakin da nufin fadin abinda suka yi mata sai kuka ya kubce mata, domin a duniya idan kana so ka ga hawayenta ya zamto zata fadi wani abin da aka yi mata har ya mata ciwo a zuciyyarta A hankali ta iya furta" ban masu komai ba, har iyayena suka zaga" Jikin Mama ne ya yi sanyi sosai, ta sani abinda ya shafi iyayen yarinyar na rikitata sosai, ko dan

Chapter 2 of 12