An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[4/5, 3:04 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J?mode=gi_t
*UWAR AGOLA*
NA
MAMAN AFRAH
Labarin mai cike da abin dariya
*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222
🅿️1️⃣
Malam Nura ne tsaye a tsakar gidansa ya sha babbar riga yana baza ƙamshin turarensa da ya bankaɗa, sai wani ɗaɗɗaga kai yake tamkar ƙadangare, taku biyu ya yi ya ja ya tsaya yana hura hanci ya shiga kwaɗawa matarsa uwar gidan kira.
"Haule" Kira ɗaya ya yi a na biyu ta amsa ta fito daga ɗaki ta zo ganinsa yana cika yana batsewa ta nemi kujera ƴar tsugunno ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido. Ko kallo bata ishe shi ba ya shiga kiran ɗaya matar tasa.
"Kuluwa, Kuluwa, Kuluwa" Shiru kake ji wai malam ya ci shirwa tamkar ma bata gidan, kallon Haule ya yi ya ce
"Kuluwa ta fita ne?" Wani takaici ne ya turnuƙe ta amma ta danne abin da ta ji ta ce
"Haba Malam ka tambayi agwagwa hanyar rafi, ai kaza za ka tambaya kansha labari" Tamkar ta watsa masa garwashin wuta haka ya zaburo ta da masifa yana faɗin
"Dakata Haule ni fa Kuluwa kawai na tambaye ki ba wai baƙar magana ba, ke ga mai bakin aku daga an tambaye ki abu sai ki tsiri karin magana ke ga wacce ta yankewa ƙasar Hausa cibiya" Banza ta masa kamar bata ji ba, ganin haka ya ƙara cewa
"Wai ba magana nake miki ba Haule? Wai ku mata mai ya sa bakwa kiyaye aljannarku da za ku samu a ƙarƙashin ƙafar mijinku ne? Yanzu ya kyautu ki wofantar da ni?" Haule a ƙufule ta ce
"Ka tambayeni na baka amsa ka ce baƙar magana na faɗa maka, kai ba kuturu ba ba kuma makaho ba, ba gaka ga ɗakin Kuluwar ba baka zuwa ka duba ko tana nan, a ce kana mijinta amma kana tamabayata ko ta fita, idan fitar ta yi ma ai kai ba za ka kasa sani ba, dole za ta sanar maka... Tun kafin ta kai aya ya tari numfashin ta da faɗin
",Ai ka ji, to ni bani da lokacin ɓatawa taɗi zanje wajen amarya dan haka idan neman magana kike sai ki yi ke kaɗai tun da kare ma ba ya haushi shi kaɗai" Ya faɗa yana juyawa ya shiga baza babbar rigarsa ya nufi ɗakin Kuluwa tun kan ya ƙarasa yake ci gaba da kiranta tun yana faɗin Kuluwa, har yake kiran ta da sunan ta na gaskiya wato Hauwa amma shiru.
Kuluwa kuwa duk abin da ake tana jin su kawai niyya ce bata yi ba shi ya sa bata amsa ba, yana zuwa ya ɗaga labulen ɗakin idanunsa suka sauka a kanta tana zaune a tsakar ɗakin da kwanon silba a gabanta hasken fitilar ta ya gauraye ɗakin. Kallo ɗaya ta masa shi ma na raini ta sauke idanunta a kan kwanon gabanta, garri ne take sha da gyaɗa a ciki dan haka sai da ta ciko luday ta kai baki ta sha, kafin ta haɗiye ya ce
"Kuluwa yaushe na zama sa,an ki ne?" Bata ce ƙala ba sai da ta haɗiye ta saka ludan a kwanon ta miƙe tsaye ta ce
"Wallahi idan ka sa na ƙwaru sai na kai ƙaranka wajen mai gari ka biya ni diyya?" Saroro yake kallon ta ya ce
"Kashe ki na yi da zan biya diyya" Tana muzurai ta ce
"Ni dai na faɗa maka hawainiyarka ta kiyayi ramata wallahi, dan ... Hanzari ya katse mata da faɗin
"To uwar ƴan kishi ki fito ina da magana da ku, ita ta fito amma ke da bakya iya danne baƙin kishi shi ne za kike ɗaga jijiyar wuya, to dan ki sani aure babu fashi, da ba a aure ba zan aure ki ba" Yana faɗar hakan ya juya fuuuu ta biyo bayansa ranta in ya yi dubu ya ɓaci, daman ya san a rina wai an saci zanen mahaukaciya!.
A daidai inda Haule take zaune ya ja tunga ya tsaya ita ma tana ziwa ta kama tsantsa da hannu biyu ta tsaya tana wani karkaɗa kai, irin na mai jiran kule ta ce casss. Malam Nura bai yi wata-wata ba ya ja wata doguwar gyaran murya ya ce
"Ba tare da ɓata lokaci ba dan ina da wajen zuwa, domin wajen amarya mai jiran gado zan je, yauwa na tara ku ne a kan na faɗa muku sati mai zuwa ranar asabar za a ɗaura mini aure, kuma ina ƙara jaddada muku duk mai son zaman ta ya ci gaba da wanzuwa a cikin gidan nan to ta tabbatar ta yi biyayya ga maganata sannan ta shirya tarɓar sabuwar amaryata" Ya faɗa yana washe baki a daidai inda ya ambaci amayarsa tamkar an masa bushara da gidan aljanna.
Haule ta yi wata ƴar dariyar rainin hankali ta ce
"Ubangiji Allah ya sanya alkairi, ya bada zaman lafiya, ya kawo ta lafiya" Tana kai wa nan ta miƙe abin ta hankali kwance za ta bar wajen, Malam kamar an warto maganar daga bakinsa ya ce
"Haba Haule kamar wani wanda bakya sona, ina faɗa muku batun ƙarin aurena zan muku kishiya amma ke hankalin ki kwance, kamar an tsoma tsumma a randa?"
Wata ƴar shewa ta yi ta ce
"Wallahi har ka bani wata ƴar bazawarar dariya, haba Malam in da sabo ai na saba, wane dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwarsa, ni kishiyata ai in ban manta ba ina ga goma sha takwas kenan" Da sauri Malam ya ce
"Goma sha takwas fa kika ce?" Tana gyaɗa kai ta ce
"Ƙwarai ma kuwa" Ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce
"Tabbas na tuna haka lissafinki yake, wallahi na ɗauka goma sha bakwai ne, ashe fa sai da na auri Ladiyo sannan na auro Kuluwa, da yake Ladiyo kwanan ta uku a gidan nan muka rabu shi ya sa nake mantawa da ita a lissafin matan nawa...
Haule ta tari numfashin sa da faɗin
"To ka ga kuwa wacce aka yi wa kishiyoyi goma sha takwas mai zai ɗaɗa ta da ƙasa? Ai ni ƙarin aurenka shan ruwa ma ya fi shi wahala"
Wani murmushi ya yi sai dai Kuluwa da ta hayyyaƙo masa ya sa maganar da ya yi niyyar yi ta maƙale, tana huci kamar wacce ta yi tseren gudu ta ce
"Daman ya za a yi ta damu, ai kishiya ko sau dubu aka taɓa maka sunan ta kishiya, kuma dole za ka ji ciwo, ai ta san cewa ba ita za a yi wa kishiya ba ni za a yi wa shi ya sa bata damu ba" Haule ta haɗe rai ta nuna Kuluwa da yatsa ta ce
"Ahir ɗinki ki fita idona in rufe kuma hawainiyarki ta kiyayi rama ta, domin wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa ni ba kanwar lasa ba ce, sannan bakin rijiya makaho ba ya yin wasa a wajen!" Tana kai wa nan ta juya tana kallon Malam Nura ta miƙa masa tafin hannu ta tana faɗin
"Bani sallama, wato kuɗin toshiyar baki na faɗar kishiya" Kamar wanda yake jira ta tambaye shi da sauri ya saka hannu a aljihun babbar rigarsa ya ciro dubu ɗaya ƴan ɗari biyar-biyar guda biyu ya miƙa mata guda ɗaya ta karɓa ta juya, ta nufi ɗakinta, Kuluwa yana miƙa mata ta ce
"Dan tsiya naira ɗari biyar ce kuɗin faɗar kishiyar?" Yana mata kallon kin rainawa kanki hankali ya ce
"In za ki karɓa ki karɓa ki rage zafi, saboda wannan ma na bada mai yawa ki tambaye ta ki ji wataran idan zan ƙara aure klin nake bata ƙanana ƴan naira hamsin guda biyu kuma ta gode mini" Ya faɗa cike da ƙafafa.
Haule wacce take dab da shiga ɗakin ta juyowa ta yi ta ce
"Ai idan ana cin ɓaure ba a tona cikinsa, kai kake batun klin ai wannan an bani da daraja, ai in ban manta ba akwai lokacin da ya bani ƙuli-ƙulin naira hamsin lokacin zan yi kwaɗon yakuwa na tambaye shi kuɗin ƙuli-ƙuli ya ce bashi da kuɗi da ya fita ya siyo ƙuli-ƙulin hamsin ya kawo min ya ce in karɓa a matsayin abin faɗar kishiya, lokacin da zai auri Hafiza ƴar gidan ƙanin mai gari, haka na karɓa na masa fatan alkairi, ni da kike ji da gani na ga jiya na ga yau kuma zan ga gobe a cikin gidan nan, ba a banza ba kowace mace take zuwa ta tafi ta barni" Tana kaiwa nan ta bankaɗa labulen ɗakin ta ta shige.
Malam Nura ya dawo da kallonsa kan Kuluwa ya ce
"Idan kin ji ana damo sarkin haƙuri to Haule ce shi ya sa duk auri sakin da nake yi saki ba ya biyowa ta kanta saboda ba ta ɗaga mini hankali idan zan sake aure... Kuluwa wacce tun lokacin da ya ce zai je wajen amarya mai jiran gado ranta ya ƙara ɓaci, tana ganin wato ita yanzu ta zama amarya mai murabus sabuwar amaryarsa ce mai jiran gado, kamar ta kai masa duka ta ce
"Wato shi ya sa ka ce za ta je wajen amarya mai jiran gado, wato an samu sabuwa ni yanzu na zama tsohon hannu, ka gama shanye mangwaro ka yi jifa da shi ƙudaje su baibaye shi ko?"
Yana wani ƙanƙance idanu irin na ɗan duniya ya ce
"Ƙarya na yi?"
Baki ta saki ya layar mai tafiya, kafin ta samu zarafin bashi amsa ya miƙa mata ɗari biyar ɗin, da sauri ta warta tana warta ta yayyaga ɗari biyar ɗin wajen gida takwas ta yaga, da sakakken baki ya bi ta cike da mamaki ya ce
"Kin yi wa kanki amma dai ki sake tabbatarwa aure babu fashi"
Cike da masifa ta ce
"To ni ka sake ni, ba zan iya zama ba"
Yana mata dariyar kin rainawa kanki hankali ya ce
"Haramun ne dai mace ta nemi saki, sannan ki sani babu saki tsakanina da ke har sai kin zauna na tsawon lokaci a gidan nan, in kin manta in tuna miki, auren biyan bashi aka mini da ke, ina bin mahaifin ki dubu takwas ya hanani ya bani auren ki, aka ranta masa dubu takwas na cika dubu biyu aka biya sadaki dubu goma dan haka ba zan yi asarar dubu goma ba duka watan ki biyu fa a gidan nan" Ya faɗa yana mai juyawa ya kama hanya zai fita domin zuwa hira wajen annurin zuciyarsa amaryarsa wacce yake kan ganiyar soyayyarta da kwaɗayin auren ta.
Yana dab da shiga zauren gidan, Kuluwa wacce ya bari da ƙamshin turarensa ta ɗaga murya cike da takaici ta ce
"A haka za a ƙare dai!. Da wani turare mai warin gawa, ai wallahi amaryar ma bata da aji tun da ba a shafa turare ɗan fesawa sai madarar turare" Har zai tafi, sai kuma ya juyo yana nuno ta da yatsa ya ce
,"Ki taka a sannu bar ganin kin tara ki kiyayi mai nema, kuma ba don biyan bashi aka mini da auren ki da tuni na sake ki wallahi dan ni sakin mace tamkar in je jigon dabobi ne in since rago daga ɗaurin da aka masa" Yana faɗa ya fice .
Kuluwa wani takaici ne ya mata dirar mikiya, kallon ɗari biyar ɗin da ta yaga ta watsar ta yi haushi ya sa ta juya da gudu gudu ta shige ɗakin ta taje take kuka dan hatta garin kwakin da take sha ji ta yi duk ya fita daga ranta, ƙafa ta saka ta yi ball da kwanon garin, tamkar dai shi ya mata laifin sai da kwanon ya kife garin ya malale a ƙasa ta yi zaman ƴan bori a tsakiyar ɗakin tana tunanin mafitar hana auren Malam Nura dan tana ƙaunarsa kuma ba ta so ya auro wata ta hana ta rawar gaban hantsi, daman ta daɗe tana jin raɗe raɗin yana neman aure duk da shi daman auri saki shi ne sana,arsa.
Malam yana fitowa ya nufi, wajen Idi mai gashin tsire sai da aka cika masa ƙatuwar takarda da tsiren ya cake kuɗin ya bayar, ya ratsa shagon Abbati mai kayan sanyi ya sayi lemon kwalba guda biyu masu sanyi. Yana ta jin daɗin zuwa ya ga masoyiyarsa ya kama hanyar yana hango irin cin tsiren soyayyar da za su yi da bazawarar tashi, domin shi ya sa ma ko tuwon gidansa bai ci ba.
Sallama ya sa aka yi da ita dan yana ta kiran wayar ba a ɗauka ba, gabaɗaya sai haɗiyar yawu yake kasancewar ƙamshin tsiren da cika masa hanci alla-alla yake ta fito. Jim kaɗan babu ɓata lokaci kuwa sai gata ta bayyana. Tun da ta fito ya mata ƙuri da ido har ta ƙaraso, irin takun da take yi shi ne yake ƙara narkar masa da zuciyarsa a kanta yana son ganin mace cikakkiya, ɗaurin ɗankwalin ta turo ka ga tsiya shi ne ya fi tafiya da Malam Nura bai san ya washe haƙora ba sai da ya ji muryarta ta karaɗe kunnuwansa da faɗin
"Kallon fa?" Da sauri ya dawo hayyacinsa yana faɗin
"Ai ke ɗin ce kullum kamar sake miki halitta ake yi" Ya faɗa yana kafe ta da kallon ƙurilla.
Dariya kawai ta masa ba tare da ta ce komai ba, shi ya gaishe da ita ta amsa a maimakon ta fara gaishe da shi, kujerar da ta fito da ita a hannunta ta zauna a ka shi kuma yana rakaɓe a jikin katangar, har ya saba idan dai zai zo zance ba ta bashi abun zama. Ledar hannunsa ya ajiye ya ɗakko wani dutse a can gefe mai ɗan girma wanda zai isa ya zauna a ka ya zauna, har lokacin yana ta washe baki.
Sun ɗan fara taɓa hira kenan ya janyo ledojin ya fito da lemukan tare da takardar yana kallon ta ya ce
"Wannan tsaraba ce siyowa na yi dan na birge ki... Tun kafin ya ƙarasa maganar Hadiza ta saka hannu ta dafe takardar ta saka a leda bai ankara ba ta saka lemukan a leda tana faɗin
"Ina godiya sosai, shi ya sa na fitar da kai tilo a cikin zawarawana, saboda kai na fasa komawa gidan tsohon mijina dan na san zan huta za ka gwada mini gata" Dariyar yaƙe ya yi ya ma kasa furta komai dan ya ga ƙarfin halin nata shi da ya siyo su ci tare shi ma ya mayar da mugun yawu amma ta tattare, a zuciyarsa ya ce
'Aikin uban me kika mini da zan ciko miki takarda da tsire haka, to wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa' Ganin yanayinsa ya sauya ta ce
"Ka yi shiru" Da ɗan sauri ya ce
"Daman siyowa na yi mu ci tare muna hirar soyayya"
A zuciyarta ta ce
'Tashin balagar tsintsaye, idan ka ci nama da lemon nan ka ce ba sunana Hadiza ba'
A fili ta ce
"Ka ji ɗan aljanna bari na buɗe mu ci, ai ina ta jin labarin yadda kake farantawa iyalinka ma" Ya washe baki yana tuna yadda ya biya wanda suka shirya mata ƙaryar nan tun da asali ba a garin suke ba dawowa suka yi.
Yana gyara zaman hular kansa wanda duka haya ya karɓo a wajen Iliya me wanki da guga ya ce
"Duk sati sai an yanka ɗan akuya, kullum kuma ana yanka kaji biyar" Ta lunshe ido ta ce
"Babu mai raba ni da kai sai mutuwa ina son namiji mai kyautatawa iyali"
Ya kalle ta yadda take farrr da ido ya ce
"Ai ni in dai wannan fagen ne bani da matsala ko kayan faɗar kishiya kowacce akwati guda na mata, yanzun nan sai da na musu kyautar dubu biyar biyar" Ya faɗa yana tuno kuɗin faɗar kishiyar da ta basu ɗari biyar biyar da yadda suka sha daru da Kuluwa wacce takaici da baƙin kishi ya sa ta yaga tata ɗari biyar ɗin.
Tana buɗe takardar ta ce
"To ai hakan da daɗi za su ji sauƙin kishin" Ya kyalkyale da wata dariya ya ce
"Ai basu da matsala yanzu ma sai da suka bani saƙon gaisuwa, dan Kuluwa amarya tana ta nannaga cewa kar na manta saƙon gais...
Zuwan Zainaba ƴar kimanin shekaru goma sha uku wajen, shi ya katse masa hanzarin maganar da ya guntso zai fesar, tamkar an jefo ta haka ta musu dirar mikiya, sanye take da atamfa riga da zani, ta ɗaure wani mayafi ƙarami a ƙugunta tamkar wacce aka sakawa wasan dambe.
Zainaba ƴar Hadiza ce yaranta biyu zainaba mai shekara goma sha uku sai kuma Shafi,i mai shekara uku, ita kuma Hadiza tana da shekaru talatin cif.
Kamar ya kwaɗawa Zainaba mari haka ya ji, ya lura yarinya bata da kunya ko kaɗan shi kuma son uwarta ya rufe masa ido yana tsoron ya tsawatar mata a samu matsala, hakan ya sa ya miƙa hannu ya ɗakko naman yanka ɗaya dan ya fara jin haushin kar Hadizar ta ɗaukawa Zainabar naman da yawa.
Zainaba wacce babu wanda ta tsana sama da Malam Nura dan ta fi so mahaifiyarta ta koma gidan mahaifinta, gata da shegen kishi kamar ba yarinya ba tsananin kishi take wa ubanta, shi ya sa duk ta tsani zawarawan Hadizar musamman Malam Nura da yanzu shi za ta aura. Da gangan ta je kamar za ta durƙusa ta buge hannunsa naman da yake miƙo mata tsoka guda ya suɓuce ya faɗi, ita kuma Zainaba da sauri ta ce
"Ban gani ba" Ta faɗa kamar za ta yi kuka, murmushi Hadizar ta yi ta ce
"Ba komai kin san shi babu ruwanshi" Wani abu da ya tsaye masa ya haɗiye muduk ya ƙirƙiri dariyar yake ya ce
"To waye bai san yaro ba, bare ma bata gani ba" Zainaba ta faki idon mahaifiyarta ta wurga masa wata muguwar harara tare da murguɗa masa baki ta sunkuya ta ce
"Innata ashe za ki iya cin daɗi ban da mu?" Hadiza wacce take baƙincikin su ci naman tare da Malam Nura ta ce
"Haba Zainaba daman za mu rage muku ke da ɗan uwanki, amma tun da kin zo ɗauki kawai mu sai mu ci girma" Baki sake Malam Nura yake ganin ikon Allah, domin kaf Zainaba ta naɗe takardar ta haɗa da lemukan ta kama hanyar shiga gidan, Hadiza ta ɗan ɗaga murya ta ce
"Kar fa ki hana Shafi'i" Da to ta amsa mata ta shige gidan, Malam Nura da ƙwallar baƙinciki ta kawo a idanunsa da sauri ya yi hanzarin mayar da ita yana washe bakin ƙarfin hali ba ya so ta gane halin da yake ciki, ga yunwa da take ƙwaƙular hanjinsa.
A zuciyarsa yana faɗin
'Wayyo dubu huɗu ta da ɗari biyar'
Tana ƙara turo ɗaurin ɗankwalinta gaban goshi ta ce
"Tun da an yanka kaji ai sai ka ci idan ka koma gidan ko masoyi" Kamar zai yi kuka ya danne ya ce
"Ai kuwa naman kaza yana can don kwanon samira aka cika mini, idan na koma na ci" Ya faɗa yana sauke idanunsa a kan hannunsa ta cikin farin wata sai sheƙin man jikin naman da kuma ɗan burbuɗin ƙuli-ƙulin da ya maƙale a hannun.
Idanunsa ya sauke a kan yankan ɗayan da ya faɗi daga hannunsa wanda Zainaba ta bige masa, kuma shi dai iya saninsa ya san da gangan ta yi don ba sa ga miciji da ita, ido ya ƙurawa yankan naman ya ga ashe har ƙafa ta saka ta murtsuke yadda ba zai amfanu ba, da a nufinsa idan sun yi sallama da Hadiza ta shige gida ya dawo ya ɗauka a ƙalla dai ya rage asara!. Muryar ta ce ta katse masa tunani da faɗin
"Bari na shiga gidan ina son shiga banɗaki" Wani irin washe baki ya yi ta tashi shi ma tashin ya yi ta ɗauki kujerar ta, sallama suka yi ta tsaya masa ƙememe me ta ce
"Au baka bani kuɗin karin safe ba, ko goben da tuwo kake so na karya" Yana kallon yadda ta masa wani farfari da idanun ya saka hannu a aljihu, dubu biyu ya ɗakko ya bata ko godiya babu ta karɓe, juyawa ta yi ta fara takun nan nata da yake so ya saki baki kamar dolo yana kallon ta tana dab da shigewa ta jiyo tare da masa bye-bye, shi ma hannun ya ɗaga mata ta shige ya juya ya fara tafiya ransa a matuƙar ɓace, don ko hirar kirki basu yi ba ga asarar nama da lemon kwalba.
Tun da ya kama hanyar gida ya tsinewa Zainaba ya fi cikin carbi, ya ƙosa asabar ta yi a ɗaura auren Hadiza ta koma gidansa ko ya huta da ganin wannan fitsararriyar yarinyar. Kayan jikinsa ya duba ko zai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 12