ne ya kashe Kuluwa ta murmusa bata ce komai ba.
Sai da ya gama gaisawa ya kira ɗaya daga cikin ƙanen Kuluwar, tasowa ta yi ta zo wajensa su Kuluwa sai washe baki ake, ya ɗago ƙullin ya ce
"Mariya ungo wannan kayan yayarku ne ki kai mata ɗaki" ,Daga mahaifin Kuluwa har mahaifiyarta mutuwar zaune suka yi, Kuluwa kuwa zigidim ta tashi tsaye tana zaro ido bata san lokacin da magana ta suɓuce ta fito ba ta ce
"Kayana kuma? A kai min wane ɗaki, mai zan yi a gida?" Ta shiga jero masa tambayoyin domin abin ya razana ta da yawa.
MAMAN AFRAH😍
09025576222
[4/8, 6:27 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/Bu295Z6iGnL3SoKYtgqnbZ?mode=gi_t
*UWAR AGOLA*
🅿️4️⃣
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.*
*Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*UWAR AGOLA*
NA
MAMAN AFRAH
*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222
🅿️4️⃣
Malam Nura ya kalli Kuluwa sheƙeƙe ganin ta hayayyaƙo masa ya ce
"Zama za ki yi a gidan mana" Hankalin iyayenta ya tashi Babanta cike da hasala ya ce
"Nura saboda wulaƙanci ka sako min ƴar shi ne ba za ka barta ta taho ita kaɗai ba sai ka kawo min ita saboda rashin ta ido" Kuluwa har hawayen baƙincikin kishi ya silalo mata domin ta fara tunanin saboda amaryarsa ya dawo da ita gida, ba komai ne ya sanya ta zubar da ƙwallar ba sai tunowa da ta yi da irin barikin da Malam ya nuna mata ta yadda ya yudare ta ya kawo ta gida. Cikin muryar kuka ta.ce
"Wallahi baka isa ba" Mahaifin ta ne ya tsawatar mata, ta ja bakinta ta yi shiru ba tare da son ranta ba, Malam ya ce
"Ya kamata a barni in mutu kafin a binne ni, ni dai babu wanda ya ji na ambaci kalmar saki don haka bam saki Kuluwa ba" Wata nannuyae ajiyar zuciya Kuluwa ta sauke, saboda kalmar nan ta mata mugun daɗi, don ta fahimci cewar har yanzu tana da sauran damar da za ta hana shi rawar gaban hantsi dangane da wannan la,anannan auren da ta tsana, saboda ta san tun da har ya kawo ta gida a kan maganar auren ne.
Mahaifiyarta cike sa takaicin cin fuskar da aka yi wa ƴarta ta ce
"To a kan me za ka kwaso kaya ka kawo ta gida?" Kafin ya furta wata kalma ta juya wata tambayar ga Kuluwa tana faɗin
"Ke Kuluwa ba cewa kika yi gaishemu kuka zo ba? Har kina faɗin yana wajen zai taho da sabulai, amma yanzu muke jin wani sabon al,amari?" Kuluwa ta ce
"Wallahi ba ƙarya na yi ba haka ya faɗa ... Babanta ne ya ɗaga mata hannu ta yi shiru tana goge guntun hawayen da ya zubo ya mayar da kallonsa ga Malam Nura cikin kakkausar murya ya ce
"Nura wane dalili ne ya sa ka dawo da ita gida tun da babu saki tsakaninku?"
Gyaran murya ya yi tamkar wanda zai yi kiran sallah, har sake nannagawa yake sannan ya ce
"Na dawo da ita gida ne ta zauna tsawon watanni uku ko huɗu" Gabaɗaya kowa idanu ya zuba masa, mahaifinta ya ce
"To ina ga ko sakin ta ka yi idan ta yi wata uku ai ta yi idda, wane dalili ne zai sa ka kawo ta gida ta zauna har tsawon wata uku ko huɗu?"
Kuluwa ta yi karaf ta ce
"Wallahi ba zan zauna ba ƙafata ƙafarka" Babanta ne ya nuna ta da yatsa ta koma ta zauna tana jin kamar ta shaƙo Malam ta masa shegen dukan da ko cewa aka yi ga mace ba zai yi sha,awar kallon ta ba ma bare har ya ce zai aure ta.
Mahaifiyarta ta ce
"Banda sakarci namiji yana yakice ki, ke kina manne masa, shi kaɗai ne autan maza? Wallahi albasa dai bata yi halin ruwa ba, ni namiji yana cewa kama gabanki nale nufae gidan iyayena don gidansa bai fi na iyayena ba... Babansu Kuluwar ne ya dakatar da ita.
Malam Nura ya ce
"Daman rawar kanta ne ya yi yawa, tana ƙetara maganata a cikim gidan, kuma ita Haule ba haka take yi ba, na basu kuɗin faɗar kishiya ɗari biyar biyar amma Kuluwa tana karɓar kuɗin nan yadda ka san ta samu tsohon tsumma haka ta yayyaga ɗari biyar ɗin wai ta raina"Babanta ya ɗauki salati sai da ya salance kowa yana jiran dalilin salatin nasa ya ce
"Amma Kuluwa an yi ƴar banza, yanzu kuɗin kika yaga naira ɗaiɗai har ɗari biyar?" Ran mahaifiyarta ne ya ɓaci ta ce
"Haba mai gida ina tsiya ina wata ɗari biyar a faɗar kishiya, maganar kishiya ake yi fa wallahi ta min daidai ai ko dubu biyar ce gwara ta yaga" Baban Kuluwa ya ce
"Ai ka ji ku mata daman ku kuke ɗaurewa ƴaƴanku tsantsa, ina laifin ɗari biyar gado ba na uwarka ba aka baka ƙyallan zani ai an mutuntaka, idan bai bata ɗari biyar ɗin ba ma ba wai ƙwata za ta yi ba" Malam Nura ya murmusa alamar jin daɗi ya ce
"Wallahi tana neman takura min ne, kishin ta ya yi yawa, to babban dalilin da ya sa na kawo ta ma, na basu hutun zuwa turaka, ka san abu in ya shafi gidan aure to babu waji ɓoye-ɓoye ko jin kunya, to na ce su haƙura da zuwa taraka har sai amarya ta tare ita ma, to Haule ta yarda don wallahi har naira ɗari na ƙara mata... Baban Kuluwa ya katse shi da faɗin
"Allahu akbar ka ga mai rabo, wata bayan ɗari biyar ɗin ka ga ai ta tashi da ɗari shida" Ran Kuluwa ya kai ƙololuwa wajen tashi, daman ta san babanta yana ja mata raini.
Malam Nura ya ɗora da faɗin
",To ita tana da taurin kai jiya ma a ƙofar ɗakina ta kwana wai sai na buɗe" Mariya da Hinde jin maganar ta fi ƙarfin su cike da kunya suka tashi suka shige ɗakinsu. Mahaifiyarta kuwa sai saƙon harara take aika mata jin zubar da ajin da take yi a kan mijin da ko damuwa da ita bai yi ba
Mahaifinta ya ce
"Wannan kam bai kyauta ba, ke da kika je zaman aure ina ruwanki da aurensa, kuma duk dokar da ya shimfiɗa ai sai ki ce to" Ya juya ya kalli Malam Nura ya ce
"Amma sai ka ce a mata faɗa ba wai zaman gida har watanni ba"
Malam Nura ya ce
"To a mata faɗan don aurena da Hadiza babu fashi" Baki sake take kallonsa tana tuna magangnun da ya faɗa a hanya amma yanzu har ya sauya ashe rami ya mata ta faɗa ba wai fasa auren ya yi ba, ita har da cewa daga gidansu su je gidan su Hadizar a zuciyarta ta ce
'Lallai namiji munafuki ne'
Mahaifiyarta takaici ne ya hana ta sake furta komai Babanta ne ya ringa faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake shiga ba, sai da aka kammala amma Malam Nura da ƙarfin hali sai ya ce
"To amma ta zauna ko sati ɗaya ne ta yi ta koma daga baya" Babanta ganin abun ba na ƙare ba ne sai ya amince Kuluwa tana ji tana gani Malam Nura ya musu sallama ya fita ranta in ya yi dubu ya ɓaci don ta lura kawai so yake sai ya gama ɓarzar amarci sannan ta koma amma duk da haka ya yi gudun gara ne ya tare a gidan zago don ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, don ko a su ko a ita wanna amarci babu wanda zai ci shi ta daɗi!.
Malam Nuwa kuwa yana fitowa waje ya yi wata miƙa haɗe da yin hamdala a fili ya furta
",Na jefar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda, ina dalili mace kamar cingam, ai wallahi ba don kar na sake ta na yi asarar dubu goma ta ba da sakin ta zan yi, ko kuma in sake ta idan na gama amarcin na dawo da ita?" Ya sake jefawa kansa tambayar, sai kuma ya kaɗa kansa ya kama hanyar zuwa gida.
Yana dab da zuwa gidan kiran Hadiza ya shigo, ya ɗaga ta balbale shi da masifa a kan cewar idan har basu yi maganar kayan da za ta saka a fitar biki ba to wallahi tana iya fasa aurensa, babu yadda ya iya ya shiga bata haƙuri yana faɗin yanzu zai je gidan ya fita wani abu ne.
Ta saki gajeran tsaki irin na kai ya dama ɗin nan ta ce
"Ka turo min kuɗin katin wayar da na kira ka, don ni ba a yi kuɗin katin wayata don kiran namiji ba, shi namiji shi ya dace ya bautawa mace" Shiru ya yi yana nazarin maganar ta, wato shi namiji shi ne wahalalle, bayan ya san kuɗin da take saka katin daga jikinsa take ɓanɓara.
A zuciyarsa ya ce
"Anya wannan za a yi abin arziƙi da ita kuwa in ta shigo gidana, tana titi ma katin waya ma ba za a mora ba to ina ga in ta shigo gidan za take siyan kayan miya idan na bada hatsin tuwo kuwa?' Kansa ya tamabaya yana ta wasi-wasi duk da bai gama yanke hukunci ba amma dai ya san cewar dole a more ta saboda yana ganin duk burga ce ganin tana gidansu amma in ra shiga gidansa sai yadda ya yi da ita.
Haƙuri ya bata ya fasa shiga gidan ya nufi wajen mai siyar da kati ya saya ya tura mata, maimakon ya dawo gidan sai ya nemi waje ya zauna a majalissa ake ta hira.
Kuluwa kuwa haka ta kinkimi ƙullin kayan nata ta nufi ɗakin su Mariya, ranta duk a ɓace sai dai ta yi alƙawarin ko ana mutuwa ana falkowa yau a gidan mijinta za ta kwana!.
Babansu yana jin rediyo yana hamma, can da ya gaji ya kwashi rediyon ya shige ɗakinsa, haka ma mahaifiyarta tun da ta ce ta zubo mata tuwo ta ƙi sai ta watsa yinta, don ta lura Kuluwa ta yi nisa a rakiyar ɗa namiji ba za ta ji kira ba, hakan ya sa ta shiga ɗaki ta hau gadonta ta miƙe ta shiga sakin munshari.
Baba ya taso ya saka sakata a gidan ya koma ɗakinsa, su Mariya ma tun suna hira suna zagin Malam Nura Kuluwa tana kare shi, har kowacce bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. Kiran sunansu ta shiga yi amma ɗif, tasowa ta yi ta fito ta nufi ɗakin Baba tun kafin ta ƙarasa take jiyo tashin munsharinsa, ta leƙe ɗakin mahaifiyarta nan ma baccin take, saɗaf-saɗaf ta koma ɗakin su Mariya ta sungumo ƙullin kayanta ta ɗauki takalmi a hannu ta nufi hanyar ficewa, a hankali ta zare sakatar ta ja musu ƙofar ta saka takalmin ta yi fiyarta.
Ko da ta je gidan ta shige abin ta ko sallama bata yi ba ta ajiye ƙullin kayana tana mamakin kayan da suke ciki domin ta ji da ɗan nauyi, tana cikin buɗe ƙofa Malam Nura da ya dawo daga majalisa ya shigo ya rufe ƙofar gidan, baki ya buɗe zai kwaɗa sallama, domin ransa fari ƙal Kuluwa tana gida, duk da ransa da sauran ɓurɓushin ɓacin ran kayan da Hadiza ta ambata zai yi mata. Sallamar ce ta maƙale, baki sake yake kallon ta ita da ƙullin kayan ta, Kuluwa kuwa ko kallo bai ishe ta ba ta buɗe ɗakinta ta kinkimi kayanta ta shige. Har ya ƙaraso ɗakin ƙofar ɗakin bakinsa a buɗe shi ya rasa tsakanin Hadiza da Kuluwa waye yake addabar rayuwarsa. Labulen ya bankaɗa lokacin ta kunna fitila tana since ƙullin za ta mayar da kayan mazauninsu.
Yana bin ta da kallo ya ce
"Waye ya je bikon ki?" Ƙugu ta riƙe da hannu biyu ta ce
"Ni ce nan na bikato kaina, kuma wallahi idan ka ce kule casss zan ce, in banda ma maza baku da kunya kai kana da idon da za ka kalleni, ka zauna ka sharara mini ƙarya da daɗin baki ashe dai duk bula ce" Da yatsa ya nuna ta ya ce
"Wallahi kika ƙara ambata cewar ina ƙarya sai ranki ya ɓaci" Ƙaramin tsaki ta je ta ce
"Ya daɗe bai ɓaci ba" Fuuu ya fice daga ɗakin, sai kuma ya dawo ya ce
"Ki shirya ƙunsar takaici idan amaryata ta tare domin da ƙafafun ki za ki fice ki yi yaji"
Baki ta taɓe ta ce
"Ɗan halak ka fasa!.
Yana saka ƙafarsa a ɗakin tamkar da kiran Hadiza ya shiga, sai dai filashin ne ta masa, hakan ya sanya ya doka tsaki yana faɗin
"Uwar son kuɗi ai wallahi kin gamu da gamon ki domin zani ce ta tarar da mu je mu" Ya faɗa yana doka mata kira ya zauna a bakin katifarsa, tana ɗauka ta ce
"Nura wai mai ya sa kake so ka nuna gazawarka ne?" Harara ya galla mata ta wayar ya ce
"Shigowa ta gidan kenan, ina jinki gimbiyar mata, autar mata" Bata tanka masa ba ta ce
"Maganar kayan da na maka, nawa da na ƴaƴanka" Gabansa ne ya faɗi ya fara tunanin ita kuwa mai haɗa ta da sabgar cikin gidansa da har za ta ce ya yi wa yaransa wani kayan fitar bikin ta.
Yana ɗan gyara murya ya ce
"Haba Hadiza su Kabiru duk suna da kaya fa, wallahi ba za su rasa yadin da za a saka musu ba kin ga ba auren fari ba ne bare na ce zan yi ta wadaƙa da kuɗi, wannan aurena na ashirin ne, kin ga Haule ce matata ta farko, kuma na mata kishiyoyi goma sha takwas kin ga idan aka haɗa da ita goma sha tara ke ce ta ashiri... Bai ƙarasa ba ta ce
"Malam Nura ban tambaye ka wannn dogon bayanin ba, ni kaina na sani wannan ne karon farko da zan aure ka, sannan da kake maganar su Kabiru ni ina ruwana da wasu su Kabiru? Ni fa ban san ma ƴaƴanka mata ne ko maza ne ko kuwa maza da mata ba ne, da har zan ce ka musu ɗinki"
Yana sauke ajiyar zuciyar jin daɗin ashe shi ne bai fahimta ba ya ce
"Allahu akbar wallahi zatona su Kabirun kike nufi da kika ce ƴaƴana" Tsaki ta doka ta ce
"Ni da su Zainaba nake ita da Shafi,i" Dakyar ya samu zarafin amsa mata ya ce
"Mai za a musu Hadiza???" Jin tambayar tashi kamar da gayya ta ce
"Bari na maka gwari gwari, kayan fitar biki nawa da nasu za ka mana, ai su ma ƴaƴanka ne ko kuwa ƴaƴana ne ni kaɗai?" Wani ƙululun baƙinciki ya haɗiye ya ce
"Wane mutum in ji mutuwa, ya za a yi in ce ba ƴaƴana ba ne, ai da an mutu har liman, ai ƴaƴanki ƴaƴana ne"
Ta ce
So nake ka mana ɗinki iri ɗaya mu saka ranar ɗaurin aure har kai da kuma su" Karaf ya yi ya ce
"Ki muku a wanann kuɗin dana baki, ni daman na ba Hudu saƙon shadda kano zan ɗinka" Ta ce
"Wato ma ka bashi to wallahi ka bashi namu ya siyo iri ɗaya idan ba haka ba ka zo ka karɓi kuɗinka na fasa auren" Tana kaiwa nan ta kashe wayar.
Zamewa ya yi daga kan katifar ya yi zaman ƴan bori yana jin ɓacin rai, ba komai ne damuwarsa ba yadda ya bada kuɗin shaddar dubu ashirin amma yanzu ana cewa ya ƙara, duk wayar da yake Kuluwa tana laɓe, sai da ya gama ta juya ta koma ɗakinta tana jijjiga kai tana mamakin wannan wace irin amarya ce tana saƙawa a ranta dole ta yi fito na fito da wannan amarya domin ta lura za ta sha gabanta a wajen miji.
Katifarsa ya janye bayan ya rufe ƙofar, ya tashi ya leƙo window ganin babu kowa ya koma ya shiga tona tsakiyar inda ya ajiye katifar, yayi tono sosai sannan kuɗi suka bayyana yan fito da su yana kuka mai cin rai, a fili ya ce
"Ni dai wannan so ya zame mini jaraba ma ba jarabawa ba, ta yaya a ce ƴaƴan bazawara ma sai ka musu ɗinkin fitar biki" Dubu talatin ya lissafo ya ce ita dubu sha biyar yadi uku su ma ƴaƴan yadi uku, ya mayar da ramin ya rufe ya mayar da katifar yana kallon kuɗin gabansa yana faɗuwa yana tunanin da wannan kuɗin sai ya auri kusan mata uku amma wai iya hidimar amarya da ƴaƴanta ne.
Haka ya kwanta da kuɗin a aljihu yana saƙa da warwara. Ko da ya fita da safe zai kai wa Hudu har ya tafi Kanon sai wurin mai pos ya kai aka tura masa ya masa bayanin cewar iri ɗaya zai siyo shaddar, sannan ya kira Hadizar ya ce ya bayar sai dai abin mamaki ko godiya bata masa ba lamarin da ya sanya cikinsa kaɗawa.
Da dare Hudu ya dawo sai dai basu haɗu ba sai da safe, ya basho shaddar blue ta yi kyau sai ƙamshi take, haka ya ɗauki tashi ya kai ɗinki ya kai mata tasu, a haka ma sai da ta karɓa musu kuɗin ɗinki a wajensa, shi ya rasa wane dalili ne ya sa ya zama kamar wani sauna a wajen Hadiza.
Kwana biyu aka ɗinka masa shaddar ta sha aiki ya kai aka goge, sai dai ya saka a ransa idan ya saka ranar ɗaurin aure cirewa zai yi ya samu ya fansar ya karɓi kuɗinsa domin ba zai saka shadda mai tsada haka ba.
Tun daga zauren gidan yake karaɗi yana faɗin
"Ga angon Hadiza nan, lallai Hadiza ta ciri tuta, wannan shaddar ko a aurena na farko nan saka ba, amma sai gashi a aurena na ashirin zan saka, Allahu akbar kabiran" Ya faɗa yana kara shaddar a jikinsa, Kuluwa tana kallonsa ta windown ɗakin ta amma bata fito ba, baƙinciki kamar ya kashe ta tana cin alwashin da ita kaɗai ta sani.
Haule ce ta fito tana ta zuga shi tana wasa shi, haka ya ringa mata ruwan sanya albarka.
Tun da ya faɗi cewa ba za su sake shiga turaka ba, babu wacce ya bari ta shiga, magungunan da aka haɗo masa ne yake ta narkawa cikinsa shi ala dole mai amarya.
Ranar asabar, wacce ta kasance ranar ɗaurin aure, ango kansa ba rawa yake ba gilgilwa yake domin a yau ne sabuwar amarya za ta tare da daddare. Ana shirin tafiya ɗaurin ya baro su Hudu da sauran abokansa, sai wasu makaɗa da duk suka karaɗe layin da kaɗe-kaɗe suna ta waƙe ango suna ambaton sunansa da sunan amarya!.
Baki a washe ya cika roba fal da ruwa ya kai banɗaki, ya dawo ya cika bokiti ya nufi bayin Haule wacce take gyara ɗaurin ɗankwali ta ce
"Ango yau ruwan wankan har makayi biyu" Bokitin ya ajiye ya washe baki ya ce
"Allah ne kaɗai ya san daɗin da nake ji yau Haule, ji nake kamar na ɗaga ruwan gidan nan na sheƙe a jikina" Da dariya ta tuntsure tana faɗin
"Idan ka sheƙe duka ruwan ina muka kama muka riƙe, da wanne za mu yi aikin gidan, gwara dai ka je da guda biyun" Shi ma dariyar ya yi yana ɗauka ya shige banɗaki ita kuma ta shige ɗakinta.
Kuluwa da take leƙosu daga ɗaki tana banka musu harara ganin babu kowa a tsakar gidan ta fito riƙe da ashana a hannunta, da sauri ta nufi ɗakin Malam ta ga shadda a kan katifa tana ta sheƙi ga wayarsa da kwalbar turare a gefe da kuma hula, baki ta taɓe ta ɗaga rigar ta ɗauke wandon ta fito, bayan ɗakinsa ta nufa ta ƙyasta ashanar ta saka a jikin ƙafar wandon, saj da wutar ta cinye gabaɗaya ƙafafun wandon ya koma gajeran wando mai iya cinye sannan ta saka ƙafa ta take, wutar ta mutu ta ɗakko wandon ta linke ta je ta mayar mazauninaa ta fito daga ɗakin ta shiga ɗakinta ta garƙama sakata!.
MAMAN AFRAH
09025576222
[4/9, 6:17 PM] MOM MASHKR & AFRAH: https://chat.whatsapp.com/DDmSp3AUB7gJnJQLnau59V?mode=gi_t
*UWAR AGOLA*
🅿️5️⃣
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
*08032773332.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo Zamzam tamkar yar budurwa.*
*Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*08032773332*
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*UWAR AGOLA*
NA
MAMAN AFRAH
*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222
🅿5⃣
*KULUWA*
Tana shiga ɗakin ta fara tunanin makomar ta a gidan Malam Nura, domin sai yanzu ne zuciyarta ta shiga zulumi da abin da ta aikata na ƙona masa wandon amarci!. Duk da ta san shigowarta ɗakin ba mafita ba ce amma dai ya zama wajibi ta tanadi wani abu da za ta tsira, tun kafin ya fito ya mata tijara.
A can cikin banɗaki kuwa Malam Nura sai da ya saɓa jikinsa sau takwas, yana wankan yana ta ƙiyasta irin kyan da zai yi yau, ya san lallai zai tashi kan mutanen ƙauyen Shabaru, duk da ya gama tsara nawa zai siyar da shaddar idan an kammala biji, don hatta kuɗin ɗinki sai ya fitar har da riba zai ɗora!.
Yana gama wanka ya mayar da riga ya fara shirin buɗe ƙofar banɗakin. Kuluwa tana ta tunanin abin da za ta aikata, wata dabara ce ta faɗo mata a rai, da sauri ta leƙo tsakar gidan daga jikin wata ƴar tula da take jikin ƙofar ɗakin, Haule ta hango tana duba ƙaramin mudubi a hannunta ta nufi ɗaki.
Da sauri ta zare sakatar ɗakin ta da ta saka, ta ɗan buɗe ƙofae kaɗan yadda ba za a ce rufewa ta yi ba, baki Kuluwa ta buɗe da ƙarfi ta shiga yin jiniya irin wacce ake yi wa sarki ko gwamna da sauransu. Malam Nura yana shirin fitowa sautin jiniya ya sauka a kunnuwansa, ɗif ya yi ya saurara don gabaɗaya ya rasa ta ce a zuciyarsa ya ce
'Ikon Allah, lallai wannan ɗaurin auren nawa zai tara mutane, to ko dai a dangin su Hadiza suna da alaƙa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 12