shi ne zai bari ta shigar masa turaka a ranar da yake jin sa zai ɓarji amarci da amaryar da ya gama yi wa tanadi a cewarsa.
Fatan samun sa,a ta yi wa Kuluwar ta ja su Kabiru suka tafi. Suna fita Kuluwa ta rufe nata ɗakin ta tafi gidan mai maganin mata magunguna ta lodo ta biya kuɗin ta dawo gida. Tana zuwa ta kai ruwa banɗaki ta salsala wankanta, ɗaki ta dawo ta shafa wani turare mai suna MU JONE turare ne na jan hankalin mai gida da ta siyo an faɗa mata yana da kyau kuma matukar miji ya shaƙi ƙamshin shikenan sai yadda hali ya yi shiga motar mahaukaci!. Wando da riga ta saka domin mai maganin ta ce ta saka kaya na jan hankali, dan haka wani wandon Malam Nura da yake ajiye a ɗakin ta ta ɗauka ta saka sannan ta saka rigarta tshirt kasancewar bata da wanduna.Magani mai suna maƙale mata ta ɗauka ta zuba a nono ta dama ta shanye ta shafa humra.
Wani kwalli idonka idona shi ma duk yana cikin kayan da ta siyo ta ɗauka ta rambaɗa a idanunta. Kanta da yake a tsefe ta shiga tajewa.
A can kuwa su Malam Nura masallacin magriba suka wuce, bayan an yi sallah ya musu sallama duk ransa babu daɗi domin har ya hango zai kwashi amarci amma gashi an samu akasin lissafi. Hudu cikinsa har ciwo ya yi wajen tsokanar Malam Nura yana faɗin
"Wai da gaske abokina duka ka shanye maganin nan kaɗan ka rage, gashi kuma mai maganin ya ce a ranar maganin yake barin amfani, to Allah ya sa ma kai ba gwauro ba ne, ga Haule nan ga kuma amarya Kuluwa sai wacce ka zaɓa" Ko amsa bai bashi ba saboda takaici.
Shago ya wuce yana zuwa ya ce mai shagon ya bashi sufagilu guda huɗu, haka aka ɗakko masa ya bashi kuɗin ya saka a aljihu ya nufi gida.
Kuluwa da ta gama shiryawa tsaf sai kuma ta ce
"Ni da zan je turaka yau, gashi na gama haɗa bom wato na sha kayan gyara, gwara dai in shiga banɗaki in tsugunna don na ji taushen da ta sha ya saka mini ciki" Ta faɗa tana ɗaukan buta ta shige banɗaki ta rufo, a ranta tana ta saƙa yadda idonka idona kwallin da ta saka zai ruɗi Malam, da MU JONE da sauran abubuwan da ta yi amfani zai sanya idan har ta je turaka amarya za ta ƙufula ta ce an wulaƙantata a ranar amarci, in ya so da safe a yi badaƙala a sake ta shikenan ƙurunƙus.
Malam Nura a hanya suka haɗu da Haule da za ta je gidan nasu, take faɗa masa sai Kuluwa kaɗai a gidan ita ma ba yanzu za ta dawo. Da sanɗa ya shigo zaure gidan, yana zuwa ya cire takalmansa ya shigo saɗaf-saɗaf motsin da ya ji a banɗaki ya tabbatar Kuluwa tana banɗaki bokiti ya ɗauka ya koma zaure da sauri.
Yana zuwa zauren ya fito da gabaɗaya sufagilu yana buɗewa yna tatsewa a cikin bokitin wato can ƙasan bokitin amma daga cikin bokitin ba wai daga waje ba. Sai da ya gama tatsewa duka ya saka wani ƙaramin icce ya gyara shi ko ina.
Kuluwa wacce fitowarta kenan daga banɗaki ta cika ruwa a buta za ta yi alwala, tana ƴar waƙarta. Alwala ta zauna a kan ɗan dutsi tana yi amma ta ba ƙofar gida baya. Da ta zo shafar kai ta cire hularta ta ɗora a cinya daman kan a taje yake bata ɗaure ba. Malam Nura ya taso da sanɗa yana zuwa ya kifa mata bokitin nan a kanta, a take kan ya shige cikin bokitin, ya saka hannu biyu ya danna saman kan ta cikin bokitin a take sufagilu da bokiti suka ce sun ga wurin zama a kan Kuluwa, domin babu ɓata lokacin gashin nan ya yi nutso a sufagilu.
Kuluwa da bata ankara ba ta ji wani abu kamar roba a kanta, kafin ta ankara ta ga ya rufe mata har fuskarta, tana shirin yin magana ta ji an buga abun, abu na farko da ya fara zuwa ranta shi ne aljannu, don ta san dai gidan babu kowa, kuma daman wataran Haule tana cewa idan ta fito fitsari cikin dare tana ganin kamar gilmawar mutum, amma saboda ƙi faɗi irin na Kuluwa da ƙaryata mutum sai tw ce ita bata taɓa gani ba don haka ba za ta yar da ba. Baki yana rawa ta ce
"Subhanallahi waye, mene ne haka, mai na yi muku? Ni ce fa Hauwa Kulu, da aka fi sani da Kuluwa don girman Allah ku yi haƙuri" Ta faɗa jikin ta yana karkarwa idan akwai abin da take tsoro shi ne aljannu. Shiru ta ji hakan ya sa ta saka hannu biyu domin ta cire abun ta cece ranta tun da bata gani bokitin ya rufe mata ido, am a tana ja ta ji gabaɗaya a manne yake da gashin ta, gabanta ne ya faɗi ta tabbatar da wannan aikin aljani ne. A take ta shiga lalume kwaraf ta buge butar alwalar ta, butar ta tuntsura ruwan ya zube, kasancewar wajen alwala ne duk a jiƙe yake kuma har ya yi laka a wajen irin tsantsin nan da ƙasa take idan ruwa yana jiƙa wuri. Da hannu biyu ta dafa ƙasa ta miƙe tana ta salatin da bata iya ƙarasawa take dawowa farko, a zuciyarta tana jin daman ta raka Haule dubiyar babanta. Malam Nura ransa fari rass cike da mugunta yana tuno irin ɗiban albarka da ta yi wa wandon sa ya kai wani ɗan icce ya ɗan soka mata a jikin hannunta, a take Kuluwa ta tabbatar da cewa ta faɗa hannun aljannu domin zaton ta farcen aljani ne aka caka mata a hannun.
Salati take yi kafin ta ƙarasa sai ta kamo hailala, bata gama hailalar take kamo a,uziyya, a haka ta samu nasarar miƙewa tsaye tana baza hannu kamar makauniya ƙafafun ta ta yi wa masauki a wajen santsin lakar nan, a take santsin ya kwashe ta suuuuuu ƙafarta da babu takalmi ta tafi, domin gabaɗaya ta sille takalman wani ya yo kudancin Nigeri,a wani arewacin Nigeri,a ya nufa. Ji ta yi kamar an yi sama da ita sai gata ta faɗi jirif, duk da ta ji faɗuwar amma yanzu ba wai ta faɗuwar take yi ba batun ceton rai ake daga hannun mutanen da su suke ganinmu ba mu muke ganinsu ba. Da sauri ta tashi ta muskuta ta shiga rarrafe domin ta san matuƙar ta sake tashi to faɗuwa za ta yi tun da ba gani take yi ba bare ta taka inda babu laka.
Wata zuciyar tana bata shawarar ta kama hanyar waje a nan ne za ta samu a rabata da abin da aljannu suka kifa mata ya manne mata a gashi, wata kuma tana faɗa mata ta koma ta shige ɗaki ta kulle duk da ta san aljannu har bango suna shiga. A zaton ta ko Haule ko ƴan kawo amarya sa kawo mata ɗauki. Tana sunkuye tana rarrafawa Malam Nura ya lallaɓa ya naɗe hannun rigarsa ya jimƙe ya sakar mata ƙulli a baya saboda bokitin iyakarsa wuya da kafaɗarta. Jin saukar ƙulli rididif har sau biyu ta ji dukan da bambanci da na mutane a take faɗuwar gabanta ta yawaita Malam kuma a zuciyarsa ya ce
',Yadda kika salwantar mini da daren amarcina da Hadiza, da yadda na yi asarar maganin da na ɗaɗɗaka yau, wallahi sai na baki wuju-wuju sai kin gwammace kiɗa da karatu, har da wani saka wandona ke kika san jarabar da kika taka, amma yau yadda zan tsurar da ke sai kin ji daman ƙafafun na guntule miki don har suma sai kin yi Kuluwa, za ki san ni kika yi wa rashin mutunci, kika barni ina yawo da wando kwambileshin (Combination)"
Muryarsa ya shaƙe ta zama kamar ta yara kamar ta tsoho ya ce
"Kuluwaaaaaa" Kuluwa da daman a tsorace take ga kuma bokitin da ya rufe mata kunne wani irin sauti ta ji da wata murya a take a tsure gudawar da take matsewa ta fara ƙoƙarin fitowa!!!.
*Saura page 1 mu gama free pages daman na ce muku a 10 za mu gama masu son karantawa har ƙarshe za su biya 700 domin shiga group ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222, *mutanena na Niger ga*
*naku acc ɗin da za ku saka 88630104 nita ko* *amana*
*Issaka issoufou.*
MAMAN AFRAH
09025576222
[4/17, 12:47 PM] MOM MASHKR & AFRAH: *UWAR AGOLA*
NA
MAMAN AFRAH
*Daga marubuciyar*
*Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
09025576222
🅿️1️⃣0️⃣
Iya ƙarfin ta ta bada himma da ƙaimi wajen danne gudawar da take son ɓata mata wandon Malam Nura da ta saka wanda take ganin shi ne makamin da za ta ja hankalin sa har ya kai ga cikar burinta wato kwana a turaka, sannan ya zamana bata yi asarar kuɗin magungunan da ta saya ba. Fasa rarrafen ta yi ta koma daɓas ta zauna ta muskuta mazaunanta a ƙasa tare da sake murza su a ƙasan duk don ganin ta mayar da gudawar da take son ƙwace mata, domin iya tunanin ta ta fara hasashen ba za ta iya matsewa ba. Sau uku tana murza mazaunan duk da faɗuwar da gabanta ya yi musamman da ta ji aljani har ya san sunan ta, duk da tana tunanin ko dai ya haddace sunan nata ne lokacin da ta ce ita ce Hauwa Kulu da aka fi sani da Kuluwa.
Duk da gudawar bata koma duka ba amma dai da dama dama wai kibiya a ido, domin kuwa ta daina matsar ta kamar ɗazu. Hannu ta kai jikin bokitin ta shiga kokawa ita da bokiti saboda tana so ta ɓanɓare shi ko ta samu damar gani da idon ta domin idan tana gani za ta fi samun hanyar tsira saɓanin idanun a rufe.
Ta ja bokitin amma ta ji ya kama kan sosai, ta sake ja ta ji babu alamar zai fita a fili ta ce
"Na shiga uku ni Kuluma(Ta ce Kuluma a maimakon Kuluwa) Ya na ji abu ya zama tif da taya da gashin kaina?"
Malam Nura jin ta kira kanta da Kuluma a zuciyarsa ya ce
'Ai sai kin kira kanki da sunan maza yau, idan aka jima farkon sunan naki ma ba za ki tuna ba sakaryar banza da wofi mai almubazzaranci, haka kawai shaddar dubunnai kika ƙona'
Daddagewa ta yi ta shiga ƙoƙarib miƙewa tun da ta ji ɗif babu motsin kowa, amma sai dai mai tana miƙewa ƙafafun ta hagu da dama santsi ya kwashe su ta koma ta yi zaman ƴan bori a cikin lakar a fili ta ce
",Na ga ta kaina yanzu kayan nan da na saka a raina zan wanki Malam da shi, zan ɗauke masa hankali daga sabuwar amaryar nan Hadiza shi ne nake faɗuwa a cikin laka ya zan yi da raina" Ta faɗa tana shafo jikin wandon domin jin inda lemar ta taɓa.
Malam Nura ya shiga jijjiga kai yana bin ta da kallon tsana a ransa ya ce
"Wato ni za a cuta da wannan wandon da ya miki kamar ƙafar tattabara, ai gashi nan kin zama kamar wacce ta yi nutso a ruwan kwata, amma za ki gane shayi ruwa ne'
Yana faɗar hakan ya zo bayanta ya riƙo rigar daga baya ya shiga jan ta ƙiiiii amma ba wai gaba yake jan ta ko baya ba, kawai yana gewayawa da ita ne, wato round yake yi da ita, Kuliwa wacce ta fara saka rai a samu salama jin bata jin komai tunanin ta aljanin ta gama wadaƙar da zai yj da ita amma sai ta ji ana jan ta ana juya ta tamkar fanka, a gigice ta shiga faɗin
"La haula wala quwwata" Ita kawai take maimaitawa a kiɗime domin zuciyar ta ta gama bata cewar ko dai wani jirgin aljannu ne zai tashi da ita zuwa garin aljannun shi ya sa ta ji yana juyawa hakan ya sa hanjin cikin ta ya karkaɗa da ƙarfi. Malam kuma ƙaimi ya bayar wajen juya ta a cikin lakar nan da cakwalin ruwan alwalar wajen.
Tun tana la haula wala quwwata har ta dawo tana cewa
"Wa qulna ya naru kuni bardan wa salaman ala ibrahim" Haka ta shiga maimaita samu fatiha.
Sai da ya ga ta jigata sosai sannan ya sake ta, saka ta ɗin da zai yi tamkar ya tura ta suuuu ta bi caɓalin santsi ya kai ta dab da banɗakin ta rarrafo tana son guduwa ɗaki, jin ta samu bango ta dafa ta tashi tsaye ƙafafun karkarwa kawai suke kamar mazari, ganin hakan Malam ya juya ya ɗakko fanteka a ƙofar ɗakin Haule ya haɗo da wata bulallar maina.
Yana zuwa lokacin ta ji tsoro da tsurewar da ta yi ba za su bar ta ta iya tafiya da ƙafafun ta ba, hakan ya sa ta durƙushe yana zuwa ya saka fantekar ya buga a saman bokitin, wani sauti ya bada wanda Kuluwa ta zaci aljanin yana adawa da kan ta ne, bayan abun da aka kifa mata hallaw ake son raba kanta da jikin ta. Hakan ya sa da sauri ta rarrafa kamar irin guragun nan masu laulayayyar ƙafa idan suna rarrafawa suna wani irin sauri, haka ta shiga sauri tamkar ana tura ta. Malam da sauri ya bi bayan ta ya ɗaga bulallae ya tsula mata, cike da yadda bulallar ta shige ta ta mata shigar sauri ta miƙe tsaye babu shiri, da ta tuno yadda lakar take taɗe ta da yadda ta ji an jujjuya ta ɗazu da sauri ta sake tsugunnawa sai kuma ta sunkuya kamar mai naƙuda tana jiran tsammani don ita gabaɗaya an dagula mata lissafi.
Malam tuno da Hadiza ta ƙi tarewa ne saboda abin da Kuluwa ta masa ya sake ɗaga bulalar ya zabga mata.
Cike da tsoro ta ce
",Ni dai Kuluwa alƙiyamata ta tsaya, ina zan ga Malam kafin in cika in nemi yafiyarsa a kan wandon angoncin sa da ƙona, Malam ka zo gida ka yafe mini ga aljannu za su yi ajalin Kuluwarka" Ta faɗa bakin ta yana karkarwa, wata harara ya aika mata tamkar tana ganinsa.
Ƙafafun wandon jin ya mata jagafgaf ta shiga naɗewa domin gudu za ta yi ba na wasa ba, ko ɗakin Malam ne ta samu ta tsira da ranta saboda abin da yawa wai mutuwa ta shiga kasuwa. Tana tashi tsaye ya saka mata ƙafa cike da mugunta sai gata ta yi sama ta dawo ta rafku da ƙasa cike da ficewar hayyaci ta ce
"Allah ya isa... Maganar ce ta maƙale kafin ta ƙarasa sakamakon tunowa da ta yi da cewar aljannu ne. Saɗaf saɗaf ta fara rarrafawa tana fatan ba su ji Allah ya isan da ta musu ba.
Rabuwa ya yi da ita sai da ta kusa da ɗakin sa tana faɗin
"Allah ya taimakeni gwara in je ɗakin Malam" Ta faɗa maganarta tana karkarwa, sai da ta kusa zuwa tana lalamawa ya saka ƙafarsa ya buga a ƙasa sau biyu, Kuluwa jin wani ƙara didif da ƙarfi sai ta ɗauka sakkowar wani aljanin ne, hakan ya sa babu shiri ba zato da tsammani ta miƙe tsaye ta falfala a guje duk da shamaki da bokitin ya mata da ganin gabanta, burin ta kawai ta shige ɗakin Malam gani take za ta tsira.
Malam Nura a zuciyarsa ya ce
'Kaico Kuluwa ai tun da kika taɓa ni kin taɓowa kanki wallahi' Murya ya maƙe tamkar an shaƙewa biri wuya ya kasa magana haka ya mayar da muryarsa ya ce
"Za ki faɗa wutar aljannu gata nanta cika ɗakin mijin naki sai ci take kamar an watsa fetur...
A zuciyarta kuma ta ce
'Wuta? Innalillahi kar ta kwaile min mazaunai i rasa wanda zan ke juyawa in amarya ta zo'
Ai ba ta jira ya ƙarasa maganar ba ta ja wani uban birki, ba ta san lokacin da ta yi wata kwana ta juyo ba.
Malam a zuciyarsa ya ce
'Wato kwana ba sai mota ba, mutum ma yana ribas kuma ya yi kwana' ,
Kwanar da ta yi ne ta taho a kiɗime ya sake gyara murya ya ce
"Kuluwa za ki faɗa ruwan maliya" Da kuka ta fashe bayan ta dakata da maganar don yanzu ta fara tunanin ko dai ba a duniyar mutane take ba a duniyar aljannu take.
Zaunawa ta yi a ƙasa take mismis da baki tamkar mai zikiri amma ita kanta ko wuƙa za a daka mata a maƙoshi ba ta san abin da take faɗa ba. Amma dai da fargaba tana sanya ƙirji ya fashe da tuni nata ratattakewa zai yi domin a matuƙar tsorace take ita ba komai ne damuwar ta ba rashin sanin abin da yake a kanta. Ganin ta zauna ɗam ya taho ya saka bulallarsa ya zane ta tsaf duk ya burɗa mata jiki, idan ya tsula a nan ta saka can ta riƙw can har sai da ya tabbatar da ta jigatu kuma ya ji ɗan sanyi a zuciyarsa dangane da abin da ta masa sannan ya ƙyale ta. Sai faman basu haƙuri take har zai fice daga gidan ya fasa ya juyo dan ya ƙara tsorata ta cikin murya mai ban tsoro wannan karon ya yi magana ya ce
"Yanzu za mu kyale ki, amma dai za mu cire miki mashayar ɗa (Breast) Guda ɗaya" Da sauri ta saki wajen ƙafafun ta da take murzawa ta riƙe mashayar da suka ambata tana zare ido daga cikin bokitin cike da murya kamar za ta yi kuka ta ce
"Ku mini rai komai zan baku amma kar ku cire mini mashaya wallahi ban taɓa haihuwa ba ban shayar da ɗana ba, kuma mijina sabon aure zai yi, idan kuja cire mini kar a zo ake mini gori tun da gidan kishiyoyi ne"
"Malam ya aikawa kirjin nata da ta damƙe gudun kar tsautsayi ya rutsa da mashayar kamar yadda aljanin ya faɗa mata a zaton ta, a zuciyarsa ya ce
"Aikin banza abu ba abu ba, akwai ya babu kakar wajen uba, abu kamar ƙwallon goruba amma tana faman tada hankali'
Jin haka ya ce
"Za a guntule miki hanci da fatar baki" ,
A zuciyarta ta ce
"Wannan aljanin maye ne, ta saka hannunta guda ɗaya cikin bokitin ta dafe hanci ɗaya hannun yana kan mashayar da ta dafe.
Yana tunano wata sabuwar muguntar da zai mata sai ya ji alamun tahowa za a shigo cikin gidan, da sauri ya zo ya dilliƙa mata wani uban ƙulli har sai da ta gantsare, a zuciyarsa ya ce
'Ko banza kin ci uwar wuya' Yana faɗa ya yi saurin laɓewa yadda mai shigowar ba zai gan shi ba. Haule da ta dawo ta buɗe baki ta yi sallama, kasancewar ta baro su Alawiyya a gidansu sun ce a can za su kwana.
Kuluwa jin sallamar Haule ta buɗe baki kamar ƙaramar yarinya tana faɗin
"Taho Haule, taho ƴar uwata ta jini ba kishiyata ba, zo ki ga yadda na yi arangama da mutane ɓoye, wallahi na yi zaton alƙiyama ta ce ta tsaya ashe dai za ki zo ki same ni da rai" Ta faɗa tana sharɓar kuka tana miƙa hannayen daga zaunen da take ko sallamar bata amsa ba.
Haule cike da tashin hankali ta ƙarasa shigowa da ɗan gudu ta nufi inda Kuluwar take, a daidai nan Malam da yake laɓe ganin ta bashi baya ya suɗaɗe ya saka takalmansa da abubuwan sufagilu ɗin ya bar gidan. Tana zuwa ta kwashi salati ta salance ya ce
"Kuluwa aljannu kuma mun shige su, ai daman ina faɗa miki idan na fito fitsari da dare sai na ga kamar wulgawar mutum amma kika ce babu wasu aljannu a gidan nan,... Kafin ta rufe bakin ta Kuluwa ta ce
"Kaico! Haule, taimaka ki gani abun da suka rufa mini yadda kika san an haɗa mayen ƙarfe da jikin ƙarfe haka ya haɗu da gashina ya ƙi ɓamɓaruwa, gashin nan da na tsefe zan ke yin kwalliyar da shi idan amarya ta tare amma kin ga sun maƙala shi a wani abu" Haule da ta ƙaraso cike da rikicewa ta ce
"Kuluwa ai bokiti ne a kanki" Kuluwa ta ce
"Haba Haule wane irin bokiti dan Allah ki taimaka a san yadda za a rabani da wannan abun na kaina, ni ba na ganin komai sai duhu, zatona ma ko matatar man aljannu ce"
Haule ta ce
"Ba waji matatar man fetur ɗin aljannu wannan bokitin naki ne baƙi" Shiru ta yi rana nazarin shin daman bokitin ta ne aljannun suka ɗauka kenan suka rufa mata amma ta kasa gane dalilin da ya sa abin ba ya ɓaaruwa.
Haule ta ce
"Ni na tasa garin yaya ta faɗa tana yaɓa bokitin amma sai ta ji shi ƙamƙa a kan Kuluwa, nan ta shiga ƙoƙarin ɓanɓarewa amma abin ya ci tura!.Tun tana ja abin yana bata mamaki har ya fara vata tsoro.
Tana kallon Kuluwa cike da tausayawa ta ce
"Kuluwa bokitin nan kamar dai tare da kanki aka yi su a mannr domin ya ƙi fita fa" Kuluwa kamar za ta yi kuka ta ce
"Dan Allah ki cire mini, yanzu idan ƴan kawo amarya suka zo sai a mini dariya fuska a rufe," ,Amsa mata ta yi na Kuluwar ta ce
"Bari in dafa ƙasa ki dage ƙarfin ki na bara ki cire mini amma kar ki bari daidai da ƙwayar gashina ɗaya ya tsige garin cirewa, kin san dai gashi shi ne adon mace" Banza Haule ta yi da ita ta shiga ƙoƙarin raba ta da bokitin amma ta ji shi gamgam idan ta ja da ƙarfi sai Kuluwa ta shiga zandama ihu tana faɗin wayyo gashin ta. Ta jima tana abu ɗaya amma ta kasa gane mene ne ya riƙe gashin daga cikin bokitin ganin abin ba na ƙare ba ne sai ta cewa Kuluwa bari ta je ta dubo Malam Nura a waje, har tana tambayar kuluwa daman bai dawo gidan ba ta ce ai ban da aljani babu wanda ya zo tun bayan fitar su, ba ta san cewa Malam ne aljanin nata ba.
Haule hanyar waje ta kama da sauri tana jin Kuluwa tana rangaɗa mata kira amma ta yi banza da ita, don tana faɗar wai kar fa ta tafi ta bar ta aljanin ya dawo ya ida nufinsa na cire mata mashaya, wai ta kama hannun ta su tafi tun da ita ba gani take ba yanzu.
Malam yana fitowa ya watsa gidan sufagilu ɗin a kwata, ya tafi wata majalisa wajen mai siyar da biredi ya zauna suna ta tsokanarsa mai zai kawo sabon ango majalisa shi da zai tarɓi amarya nan dai ya sanar da su cewar sai gobe ne tariyar. Haule tun da ta fito take ta duba shi bata gan shi ba. Tafiya ta shiga yi tana dubawa wani saurayi ɗan maƙotansu ta tambaya ya ce ya gan shi a wajen me shayi da biredi, nan ta ce ya kira mata shi. Tana nan tsaye sai ga Malam ya taho yana ta sauri tamkar bai san mai ya faru a gidan ba yana zuwa cike da nuna damuwa ya ce
"Haule lafiya dai? Ko ƴan kawo amaryar ne suka zo?" Ya faɗa kafin ya ƙaraso, Haule ta ce
"Malam mutanen ɓoye ne suka yi wa gidanka kutse wallahi suna can
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 12