Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [29/03 09:54] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCRW☀️ ____________________________________________ 01 Cikin duhun dusar ƙanƙara wata mata mai ƙusumbi ke ta ɗangala sanda cikin sauri har ta isa wani ƙaton kogo mai cike da hayaƙi kamar an yi gobara.Tana shiga kogon ya fara rawa yana fitar da wani sauti,baƙin bargon da ta luluɓe kanta da shi ta sauke kan kafaɗunta hakan ya bayyanar da shafafar fuskarta wacce babu ido,babu tsinin hanci sai iya baki kawai.Bakinta ta buɗe tana yin wani gurnani mai fitar da magana cikin wani yare na ƙarnin baya “ uleja naho kajulu ramhakaya fyayal!” cak kogon ya tsaya da rawar da yake tare da ɗaukar wani irin shiru kamar mutuwa ta ratsa,babu jimawa kuwa wasu fararen halittu suka fara shawagi ko ta ina. Da sauri ta zube kan gwiwanta tana mai buga gundulalun tafukan hannunta a ƙasa tana mai daɗa furzo wasu kalaman. “Za ki iya gabatar da abin da ke tafe da ke” wata murya ta ratso iska ta bata umarni. “Naomi!” ta furta cikin rawar murya. “Alƙaluman doka sun riga da sun ƙafe babu wani canji da za mu iya yi miki” aka bata amsa. “Ita ɗin yarinya ce ƙarama ƙwaƙwalwarta ba za ta iya ɗaukar wannan hatsabibin tashin hankali ba” tana gama rufe bakinta wata tukunyar ƙasa ta faɗo a gabanta ,“ki bata waɗannan ruwan ta sha daga nan komai zai tafi kan tsari” Tukunyar ta ɗauka kafin ta gyara luluɓinta sai kuma ta fito,bai wuce tako uku da ta yi ba sai ta furta wani furuci wanda ya haifar da wata hatsabibiyar guguwa tashi ta zo ta zagaye ta tana fitar da wani iska,sannu a hankali guguwar ke daɗa yin sama da ita a haka ta ɓace ɓat kamar walƙiya ba ta bayyana ko ina ba sai a ƙofar gidanta. Ina zaune ina ƙulla garin magunguna na ji motsi,da sauri na ɗago kai sai na hangi Maa na daidaita rufin ƙyauren gidanmu.Murmushi ne ya wanzu a fuskata ba tare da na ce mata komai ba na ci gaba da kallonta har ta ƙaraso ta zauna kusa da ni tana mai miƙo mini tukunyar hannunta.Na karɓa,sanyin haɗi da wani shock suka ratsa ni yayin da na ji kwaɗayin shan ruwan ciki.Baki na kafa na soma shan abin da ya kasance a ciki don sai bakina ne kawai ya iya tantance mini kallon kitse na yi wa rogo don kuwa ba zallar ruwa ne ba. Ina ajiye tukunyar sai na ji tamkar wacce aka yi wa wankin ƙwaƙwalwa,wasu abubuwa da suka keɓancin mahaifiyata nake son sani. “Maa me yasa ake kiranki da mayya?” “Saboda ababen bauta sun mallaka mini baiwar da ta keɓanta da ta sauran mutane” “Kina nufin makantar ido?” “Eh! ” “Amma ai kina gani duk da babu gurbin ido a fuskarki ” “Naomi??” muryar ƙawata ta katse zaren tambayoyin da nake yi wa mahaifiyata wacce ta kasance jigona,bango abin jiginata. Miƙewa na yi da sauri ina ƙara gyara zaman fatar dabba wacce ta suturta tsaraicina ina mai duben Debora wacce ke sanye da wani tsohon bargo duk ta yane jikinta da shi.Murmushi ta sakar mini kafin ta yi mini alama da hannu,Maa na duba ina mai cewa “zan yi wa Debora rakiya ne” “To kar ki jima saboda lokacin zuwa farauta ya kusa” Maa ta bani amsa,ba tare da na ce komai ba na kama hannun Debora muka fito ƙofar gidanmu wanda ya kasance na kara. “Ya meke labari?” na tambaye ta . Kamar munafuka ta yi ƙasa da murya ta ce “zo mu je na nuna miki wani abu” sai kuma ta fara ɗan gudu-gudu tana nufar bayan gari yayin da ni kuma nake take mata baya har muka isa bakin Teku .Da wani irin kallo na bi ta da shi ina mai cewa "me kuma za mu yi a nan?” Da hannu ta yi mini nuni da can tsakiyar ruwa,sai dai sam ban ga abin da take son nuna mini ɗin ba.Lura da hakan yasa ta ce “yi kamar za ki rufe idonki” hakan na yi na lumshe manyan idona kafin na ɗan buɗe su a hankali sai a lokacin na ga wani abin mamaki wanda tunani da hankali ba za su ɗauka ba.Dogon tsani ne a cikin ruwan tare da shata wata doguwar hanya da alamu za ta ɓulle a wani wurin.Umarnin zuciyata ƙafafuwana suka bi ba tare da na shirya hakan ba na ji sanyin ruwa ya ratsa ni.A hankali nake tafiya har na isa kan tsanin na fara taka matakalansa sai dai ban fi tako uku ba na ji kamar an tunkuɗo ni sai ganina na yi a wani wajen na daban ko kuma na ce wata duniyar wacce ta sha banban da wacce na taso na tsinci kaina a cikinta. Wasu halittu ne masu irin siffata sai dai yanayin launin fatarsu da kuma shigarsu ya sha banban da irin ta duniyarmu.A karon farko da na ji tsoro,don ban taɓa ganin irinsu ba .Ƙafata ta hagu na ɗan mayar a baya ina kallon yadda wani mutum ke musayar wuta shi da maƙarabansa,ina daf da na koma cikin ruwa muka yi ido huɗu da shi hakan ya haifar mini da matsanancin faɗuwar gaba tare kuma da rikicewar tunani.Mun shagala da kallon juna ,ƙarar wani abu da ban san me ake kiransa ba ya dawo da ni hayyacina.Sai da na yi dogon nazari sannan na fahimci cewa ta cikin ƙirjinsa ne aka halba masa abar kashe mutane.Faɗuwa yayi ƙasa,wanda hakan ya jawo hankalin tawagarsa kusan su duka na ji sun ce “yalaɓaiii?” kafin su yo kansa,ɗaya daga cikinsu ne ya zube ƙasa tare da ɗora kansa kan cinyarsa yana mai cewa “Naslam?” cikin tashin hankali yake kamar yadda fuskokin sauran suka bayyana. Abokan adawarsu ne suka fara yi musu sarƙa suna gargaɗarsu da su miƙa musu wannan mutumin kawai suke buƙata in kuma sun ƙi za su kashe su duka su tafi da shi. “Rayukanmu fansa ne akan shugabanmu babu gudu babu ja da baya don haka dakaru ku juya ku fuskance su” shi ne abin da ya faɗa yana mai shimfiɗe Naslam ɗin. A wannan gaɓar ce na ga wani al'amari mai shige da irin rayuwarmu ta can duniyar,yadda su mutanen da ke neman ran Naslam duk suka wani zazzalo harshe waje suna sarrafa shi,kafin ƙyaftawar ido sai gawarwaki nake gani suna faɗuwa. Idona na ji suna yi mini ƙaiƙayi ,babu jimawa suka furzo da wani hatsabibin haske wanda ya tarwatsa taron Mayun duk suka faɗi babu rai sai ɗaiɗaiku ne suka gudu. “Naomiiii?” na ji muryar Debora tana kirana daga ta can ɓangare,kamar kifi haka na faɗa ruwa na koma duniyarmu.Ko da na fito daga cikin ruwa jama'ar gari na tarar duk sun cika wurin suna jiran fitowata.Ko kaɗan babu wani damshi ruwa a jikina a bushe nake ƙamas,sai dai a akwai banbanci tsakanin lokacin da na shiga da kuma yanzu da na fito.Kaf illahirin jikina ya rine yayi baƙi yayin da kuma wani abu da nake tunanin ƙusumbi ne ya bayyana a bayana.Fuskokin wasu cike da mamaki yayin da wasu kuma na hango tsoro da hassada a tattare a ciki. “Naomi me kike yi ƙasan ruwa kusan kwana biyu ba ki fito ba?” ƙawata Debora ce ta zo gare ni tare da tambayata. “Kwana biyu ?” na maimaita yayin da kuma cike da mamaki,ɗaya daga cikin tsofin garin ta matso tana mai nuna ni da yatsa tana mai cewa “dama tun ranar da aka haife ki na hango ajalin mahaifiyarki a tattare da ke saboda kin tabbata butulu ki rasa wacce za ki kashe sai wacce ta kawo ki duniya” sai kuma ta juya ta fuskanci mutanen gari tana mai cewa “kuna ta tambayar wa ya kashe Maa to ƴarta ce” Normal mutane ne kawai suka tsorata da furucinta yayin da su kuma dangina masu ido uku suka rufo kaina suna mai cewa “ita ma a kashe ta” sai dai ko kusa da ni ban bari sun ƙaraso ba na yi wani furuci duk suka ƙame ƙyam a wuri guda kamar wasu bishiyoyi. Magana na soma yi sai dai abin mamaki ba muryata ba ce ke fita,ta mahaifiyata ce.Gargaɗi ne mai ban tsoro haɗi da bushara ga waɗanda suka yarda suka miƙa wuya a bisa sabuwar dokar da na shimfiɗa musu.Kamar yadda ake rusunawa sarki haka duk suka zube suna jinjina mini haɗi da gaishe ni,ƙawata Debora ce kawai a tsaye tana wani mayen murmushi mai fitar da tsantsar farin ciki. Hannunta na kama na ratsa ɗimbin jama'ar muka wuce,har muka isa gidanmu ni da ita babu wanda ya cewa wani kanzil.A ɗaki na tarar da gawar Maa a kwance tuni ta fara ruɓewa tsutsotsi na shige da fice ta bakinta.A lokacin ne na ji wata murya daga can cikin ruhina tana bani mafita da shawari,yayin da ni kuma na yi tako ɗaya na aiwatar da abin da na ji.Hannuna na ɗora a goshin Maa na soma yin wani furuci wanda ban koya ba,kawai zuwar mini yayi.Babu jimawa ta soma bajewa tana komawa hayaƙi a haka har ta baje gaba ɗaya sai sautin muryarta da ya soma yi mini bushara “ ina tare da ke a duk inda za ki kasance ƴata Naomi kar ki yi baƙin cikin rabuwarmu wannan shi ne matakin nasararki,hidimar da za ki yi kuma na san mahaifinki zai yi alfahari da ke.Zan tafi na koma asalina,a duk lokacin da kika yi kewata ki je magudanar ruwa ki cilla dutsen karlis zan jiyo sautin kiranki” tana gama faɗar haka aka kece da ruwa mai bala'in ƙarfi wanda rufin ɗakinmu bai iya tare shi ba.Na yi saurin lumshe idona ina jin sabuwar halittata na yi mini wani irin motsi haɗi da ƙara girma wanda silar haka na ji kafaɗata ta ƙara nauyi hakan ya haifar mini da ɗan rusunawa kamar dai yadda mai ƙusumbi ke yi. An ɗauki lokaci kafin ruwan ya tsaya cak ,sai a lokacin kuma na tsinci muryar Debora na cewa “haƙiƙa kin kasance mai babban rabo ƙawata,ina mai sanar da ke cewa nan ba da jimawa ba amon mulkinki zai ƙetare duniyarmu ta ruwa ya tsallaka duniyar turɓaya ” Sai da na haɗiye wasu yawu masu ɗaci kafin na ce “a yau na ga wata duniya ,wasu mutane na gani a siffar tawaga biyu,ɗayar tawagar ta kasance ta Mayu ce yayin da ɗayar kuma ban san ta mece ce ba abin da kawai na iya gani shi ne fuskokinsu na fitar da wani irin haske mai natsuwa haka ma hannuwansu.A goshin shugabansu na ga abin da ya kusan dakatar da numfashina,wani baƙin tabo ne wanda ya ƙawata goshin nasa ya kuma fitar da tsantsar hasken fuskar tasa” “A yadda kika siffanta su sak sun fito a al'ummar nan da ke bautar wani Ubangijin Ka'aba,sam ba su nuna tausayinsu ga matsafa da kuma waɗanda suka saɓa dokar Ubangijinsu” Zuciyata ce na ji tana wata irin tafasa hakan yasa na juyo a fusace ina kallon Debora wacce ita ɗin ta kasance ƴa ga babban malamin ilimin tarihin duniya.Tun da na ji ta ambaci haka tabbas kuma na san gaskiya ta faɗa ,“dama har akwai masu tsanar Magic a duniya? Shin ba su san tasirin tsafi ba ne ko kuwa sun jahilci lamarin ne?” “Ko ɗaya! Su ɗin sun yi imani a kaf duniya babu wanda ke tafarkin gaskiya sai wanda ya kasance ɗaya daga cikinsu.Wannan dalilin ne ma yasa suke shirya yaƙi duk shekara suna shiga ƙasashen matsafa.Kin ga mu bar maganar nan ma saboda ba ta shafe mu ba” “Ta ya za ki ce ba ta shafe mu ba alhalin kin san duniyarmu ba mu yarda da wani addini ba? In fa suka farmake mu?” ban san me yasa na ji tsoro da shakku dangane da mabiya addinin ba, musamman in na tuna fuskar mutumin nan Naslam. Debora ta riƙo hannuna tana mai cewa “masana tarihi sun tabbatar mana cewa yankinmu zagaye yake da ƙoramai ta yadda babu wata halitta da ta isa ta ƙetaro izuwa nan sai da izinin esprit ɗin ruwa,kina tunanin uwayen gijinmu za su lamunta a kawo mana hari ?” wani irin numfashi na sauke ko ba komai kalaman ƙawata sun ɗan rage mini fargaba amma duk da haka ban yi ƙasa da gwiwa ba na yi shela ina son ganin dukkanin matsafan garin domin zuwa kowacce kusurwar ruwa su kai saƙo zuwa ga aljanai da ruhikan ruwa....... [30/03 19:48] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 02 Ƙananun shekaruna ba su hana ni jagorantar tsoffi da kuma dattizai zuwa bakin kowacce kusurwar ruwa ba.A tsaye nake ƙiƙam ina kallon yadda ake masayar kalamai tsakanin aljanun ruwa da kuma matsafa,kamar yadda na faɗa musu tun farko ina son a bai wa garinmu kariya haka su ma suka faɗa sai dai aljanun sun ƙi lamincewa da ƙudirinmu kai tsaye sai da suka kawo nasu sharuɗan.Daga ciki akwai bayar da jinin baƙaƙen dabbobi duk ranar laraba, sannan a kowacce ƙarshen shekara ɗaya daga cikin mutanen yankin zai zama hadiya ta aljanai. Shiru wurin ya ɗauka suna kallona,suna jiran amsata a matsayina na shugaba.Ni ma shirun na yi ina nazari,wanda ban san ashe cewa tazarar lokacin da na ɗauka kafin na miƙa yardata ya fusata aljanun ruwan sun komawarsu. “Sun fusata ba za su sake yin magana ba sakamakon shirun da kika yi yayi yawa.A matsayinki na shugaba ya kamata a ce kina bada amsa ne a kai ba tare da nazari ba” ƙawata Debora ce ta yi wannan furucin idonta na kallon tsakiyar ruwa.Dukkan matsafan sun yi amanna da furucinta,ban ce komai ba sai taku da na fara yi ina ɗaga kafaɗata gefen da ke da ƙusumbi na shiga can tsakiyar ruwan.Tafin hannuna na hagu na kalla ina yin wani furuci nan take ya tsage jinina ya soma ɗiga a cikin ruwan.Duk ɗigo ɗaya ina iya jiyo wani nishi daga can ƙasan ruwa,na ɗauki kamar minti biyu a haka kafin na dakatar da zubar jinin sai kuma na soma yin magana cikin sauti ƙasa-ƙasa “joliho kuntahee namaruju kalmari hanaighar kashmuh balbilancaaaa!” babu shiri na lumshe ido jin yadda wata irin guguwar ruwa ta tashi tana tunkuɗo duk wani masarafin tsafi izuwa gare ni. “Ya ke ƴa ga Bazuka ki sani cewa kowanne tasiri da farashinsa,sannan mu halittun ruwa ba mu taɓa mance duk wata alaƙa da aka ƙulla da mu .Za mu bai wa garinki kariya kamar yadda kika buƙata sai dai ki sani a duk lokacin da kika take dokarmu za mu bayyana miki asalin me ake kira da masifa da annoba ” wata murya da ke kama da ta macijin ruwan ta yi mini jawabi. “Hakan ba zai taɓa faruwa ba,zan kiyaye dukkan sharuɗanku” wannan karon na bada amsa kai tsaye. “Mu ne za mu zaɓar hadiya da kanmu,a duk sa'ilin da lokaci ya yi za mu nuna miki mutumin da muke buƙatar jininsa ta mafarkinki ” “Na amince!” “Sannan kuma haramun ne shiga ruwa ranar Laraba ” “Na amince!” ina furta haka kawai sai yanayin garin ya canza ya ɗauki wani irin launin duhu amma ba sosai ba,sararin samaniya ya cika da baƙaƙen giza-gizai yayin da kuma kukan tsuntsaye da kaɗawar bishiyoyi ya tsaya cak. “Aroroke! Aroroke! Aroroke!” shi ne abin da sauran mutanen da muka zo suka fara faɗa cikin murna saboda dukkan alamomin nan da suka bayyana na nasara ne. A hankali na fito daga cikin ruwan ina mai fuskantar su sai duk suka yi shiru tare da sauke idonsu ƙasa don nuna girma a gare ni. “Daga yau na sama wa garinmu suna za a dinga kiransa YANKIN MUTUWA,duk wanda ya shigo sunansa gawa ba wai mutum ba ko dabbar da ba ta wannan garin ba ta shigo na bada izini kafin a zo a faɗa mini a kashe ta” nan ɗin ma jin daɗinsu suka bayyana a fili kafin na wuce gaba su mara mini baya muka koma can tsakiyar gari inda na sa aka ƙara ƙawata gidanmu. Kan shimfiɗar da gawar Maa ta rushe na hau tare da yin kwanciya.Ina lumshe idona fuskar Naslam ta dawo mini da wani mugun sauri na buɗe su tare da tashi zaune ina jin zuciyata na harbawa da sauri.A fili na ja wani tsuki ina jin tsanarsa da su kansu mabiya addininsa.Yatsun hannuna na murza tare da furta kalmar tsafi nan take ragayar da ke maƙale a tsakiyar iccen rufin ɗakinmu ta yo ƙasa ta zo daidai inda nake wata ƴar ƙaramar takarda na gani mai ɗauke da haruffan tsohon asiri.Ban yi wani dogon bincike ba na fahimci cewa wannan takarda daga mahaifina take,mutumin da daidai da sakan ɗaya ban yi rayuwa da shi ba.Rubutun bai da yawa a ido,amma ma'anoninsa sun isa a rubuta dogon labari.Tsam na miƙe bayan na maƙale takardar a ƙuguna,daidai ƙofar da za ta ba mutum damar shiga uwar ɗaga na zube tare da shafar wurin nan take ya ɗau wani haske yana mai bayyanar mini da jan rubutu wanda aka rubuta da jinin mahaifina. “Finstako Bazaku enfinstako naheee” ina furta haka ƙasar wurin ta tsaye sai ga wata ƴar madaidaiciya wuƙa ta bayyana mai ɗauke da sunan mahaifina,nawa da kuma na Maa.Sai da na tsaga jinina ya ɗiga a kai sannan na samu damar ciro ta.Wani mummunan iska ne ya taso daga sama ya cilla ni gefe kafin guguwa ta fara haɗuwa daidai wurin da na ciro wuƙar.Wata siffa ce ta bayyana a gare ni,tun a kallon farko na ga ne shi ɗin mahaifina ne duba da fuskarsa sak irin tawa ce.Hannu ya miƙa mini,daga wurin da nake zuwa inda yake da ƴar tazara amma hakan bai hana ni ɗora hannuna kan tafinsa ba sai ya janye ni muka ɓata cikin iskan guguwa.Wata tsohuwar maƙabarta ce mai zubin ta kiristoci,kowanne kabari da nasa sunan. “Wannan ce hanyar da matsafa ke bi don kawar da maƙiyinsu ba tare da sun sha wahala ba.Da zarar kin ginawa mutum kabari to lissafin mutuwarsa zai dawo hannunki ,ke ce za ki zaɓar lokaci da kuma yanayin da zai bar duniyar bil'adama zuwa ta matattu” shi ne bayanin da Abbana ya yi mini ba tare da na tambaye shi ba. Kallonsa na yi ina mai cewa “ni banda maƙiyi ko ɗaya” “Shi kuma Prince ɗin da kuka haɗu fa? Kin yi tunanin cewa haka kawai ne kika fita daga duniyarmu ta tsakiyar ruwa zuwa duniyar turɓaya? Ya ke ƴata ki sani daga ranar da muƙamin iko na prophecy ya fara aiki a kanki to abu na farko da uwayen gijinmu suke nuna maka shi ne babban maƙiyinka” Shiru na yi ina nazarin furicinsa ,so nake na san ta ya aka yi Naslam ya zama maƙiyina,don na fahimci sarai a kansa ne yake magana. “Dalilin da yasa kika zama maƙiyiyarsa saboda ta silarki ce aka yi galaba a kansa,ba don a ce ya shagala da kallonki ba to da tabbas magauta ba za su harbe shi ba” ya ƙara faɗa kai ka ce shi ke sarrafa tunanina da har yake sanin abin da ban furta ba. “In dai duk abin da ka furta gaskiya ne,to zan so a ce a duk lokacin da yake tsakiyar fafatawa da maƙiya ya zamana ni kuma na bayyana a wurin ta yadda zan zamo rauninsa,ya gane ya kuma fahimci cewa wutsiyar raƙumi ta yi nisa da ƙasa.Ta hakan ne kawai ba zai taɓa sha'awar farmakar yankina ba” Bai ce mini komai ba sai wuƙar nan da ya cire daga gidanta ya miƙo mini tare da nuna mini wani buɗaɗen kabari wanda a jikinsa aka rubuta sunan Prince Naslam. Hannuna na tsaga jini ya zuba a cikin ramen kabarin,babu jimawa wuta ta soma ci balbal.Daga nan kuma kawai sai tsintar kaina na yi a ɗaki,ba tare da na san alƙawarin jini ne na ƙulla Ni da aljanai ba. ★DAULAR ABU NASLAM Tutar daular ce aka juye alamun babu lafiya a yankin.Dakaru haɗi da hadimai sai faman kai komo suke yi suna jiran tsammani na farfaɗowar jagoransu,madubi kuma gun babbar masarautar musulinci. Sarki Haroon mahaifi gun Prince Naslam a tsaye yake a wata kusurwa wacce ta yi daidai da alƙibla.Idonsa a rufe suke,yayin da kuma ya haɗe hannuwansa wuri guda domin nuna ladabi ga Ubangijinsa.A hankali yake motsa bakinsa,duk da ba a jin furucin amma za a iya fahimtar abin da yake cewa shi ne “Ya Hayyu! Ya Ƙayyum! Wato ma'ana Ya Rayayye! Ya dawamamme!” iya shi kaɗai yake furtawa bai dakata ba kuma sai da ya ji murya jakariya Ali yana cewa “shugaba cikin amincin Ubangiji ka'aba Prince Naslam ya dawo hayyacinsa ” “Shukuran Ya Rabb!” shi ne kawai abin da ya furta kafin yake juyowa yana kallon Ali wanda duk ya fita hayyacinsa tun ranar da suka dawo daga yaƙin tsibirin Mayu. Murmushi sarki ya sakar masa wanda ya haifar masa da samun wata ajiyar zuciya nan take kafin cike da girmamawa ya ce “yarima na buƙatar ganinka” “Mu je!” ya furta kafin sarki ya shiga gaba shi kuma Ali na take masa baya har suka shiga ɗakin yarima Naslam inda yake kwance yayin da kuma tsoho Barham ke kula da lafiyarsa. Suna haɗa ido da mahaifinsa ya yi saurin yunƙurowa da niyyar tashi,sai dai raunin ƙirjinsa ya dakatar da shi da wani mugun sauri ya koma ya kwanta yana mai yin wani irin nishi. Barham ya ce “na yi nasarar cire dattin garin mahalbiya,nan da kwana uku in sha Allah zai iya tsayuwa kan ƙafafunsa” Sarki ya ce “Ubangin ka'aba ya albarka ce ka ya ƙara maka ɗimbin ilimin sanin magani” Barham ya amsa da “ Amin ” kafin kuma ya yi wa Ali alama suka fice suka bar sarki shi da yarima. “Ya jikin naka?” sarki ya tambaye shi yana mai dafa goshin Naslam ɗin.Maimakon ya basa amsar tambayarsa sai cewa ya yi “Abih aljanar da nake baka labari ita ce silar raunin da aka ji mini,na gan ta a zahiri tana tsaye gaɓar teku sanyen da

Chapter 1 of 10