Share this page
ni,“na tuna wace ce ni ” shi ne abin da ta furta mini.Cike da jin daɗi na ce “kin tuna? Kai wannan babban abin farin ciki ne amma ya na ga ba ki murna?” Idonta ya kawo ruwa tana mai cewa “na fito a yankin da aka haramta maita da kuma tsafi,ba tare da shuwagabannin sun yi la'akari cewa ba babu wani babban tarihi da magabatanmu suka shuɗe suka bari kamar Magic,ita Maitar ma ba ta fiya ƙarfi ba. Surukina kafin mutuwarsa ya yi matuƙar ƙoƙarin wurin ganin ya daƙile duk wata baƙar shirka,sai dai abin takaici Mayun ne suka haɗin gwiwa wurin kai shi barzahu.Wannan ya fusata mijina har ta kai shi da yin wani tsari shi ne kafa masarauta,yasa an gina babban wuri tare da yin shelar duk wanda ya shirya karɓar addinin gaskiya to ya shigo a cikin sabon ginin da aka yi.Ta wannan hanyar ce aka yi walƙiya aka gano mayu da matsafan cikinmu,sai ya soma yaƙarsu har ya yi nasara a kansu.Sai dai abin da bai sani ba ita maita bibiyar jini take yi,ga shi dai ya kashe tushenta amma bai cire inda ta yabanya ba.Sannu a hankali lokaci na tafiya mace-mace ya fara yawaita a daular,a bisa binciken wani mai bayar da magani ya gano cewa cutar maita ce sai kuma aka ƙara ƙarfafa tsaro.Tun ana yi wa mutum afuwa in an kama shi da cutar maita har aka zo zamanin yarona inda ya yanke ɗanyen hukuncin cewa duk wanda aka kama da laifin maita ko tsafi kisa ne kawai” tana kawowa nan ta yi shiru tare da kamo ni tana cewa “zo ki zauna hakan za ki gaji sosai,ya kamata ma Banah ya nemo miki sanda mai kyau” Kan kujerar da aka sassaka da icce ta zaunar da ni kafin ta ci gaba da bani labarin. “Mahaifin matar ƙanen mijina shi ne mutum na farko da ɗana ya fara cirewa da hannunsa saboda laifi mafi muni da ya aikata ya kashe mahaifan hadiminsa wanda ya ɗauka tamkar amininsa.Ƙarfin wannan raɗaɗin ya saka ita kuma matar ƙanen mijin nawa ta ɗauki tsanar duniya ni da ɗana ta ɗora mamu” nan ɗin ma shiru ta yi tana kallona tsakiyar ido da dukkan alamu akwai wani sirri mai nauyi da take son sanar da ni wanda baki ba zai iya furtawa ba. Ta idonta kuwa ta shaida mini cewa “ni mayya ce! Ina ɗauke da kambun Maitar prophecy” sai kuma ta yi saurin janye idonta daga cikin nawa kafin ta je da sauri ta shige ɗakinta.Na lumshe idona tare da buɗe su kafin na yunƙura dakyar ina dogara sanda na take mata baya. A zaune na tarar da kan shimfiɗarta,na ajiye sandar hannuna ni ma na zaune tare da kamo hannunta.Sai ta ɗago ta dube ni tana wani irin murmushi da ya fi kuka ciwo kafin ta ce “ban taɓa yin maita ba,ban taɓa cin ɗan wani ba kawai dai abin da na sani wani lokacin ina rikiɗa na zama kifi a irin haka ne har ita Dadda ta ganni cikin wannan siffa shi kenan ta je ta sanarwa sarki ai ni ma mayya ce.Ba tare da maganar ta fita waje ba aka titse ni sai na faɗi gaskiyar magana,in kuma na yi shiru na ƙi faɗa gobe gaban al'ummar gari za a yanke mini hukuncin kisa bayan an tabbatar shi ne kawai na yanke shawarar bin dare na gudu.Amma duk da haka bai ishi Dadda ba sai da ta jefe ni da baƙin tsafi ta haukata ni” Na ce “don me yasa kika gudo kika bar ahalinki? Me yasa ba ki zauna ba ki sanar da su babu wata baiwa a duniyar nan da ta wuce maita? In ma ba ki son a sani ai sai ki ɓoye kayarki ” Kai ta girgiza mini tana mai cewa “akwai wani garin magani da ake shaƙawa mutum a hanci muddin yana da ɗigon maita a jininsa to zai bayyana cikin ɓoyayyar siffarsa ne ya dinga tonawa kansa asiri” Na ja dogon numfashi kafin na ce “shi kuma yaronki fa,kin yi tunanin halin da zai shiga bayan tafiyarki? Me yasa ba ki taho da shi ba?” Wani murmushi ne wannan karon ya suɓuce mata bai bayyanar da tsantsar farin ciki da dukkan alamu tana mugun son ɗan nata.Ta ce “Ba fa yaro ne ƙarami ba,ko a lokacin da na bar masarauta ya haura talatin da ɗaya kawai dai a idona ne nake ganinsa ƙanƙane” “Me sunansa?” Kai ta girgiza cike da kunya tana mai cewa “a al'adarmu ba mu faɗar sunan ɗan fari, wannan yasa na yi masa laƙabi da Noor” Samun kaina na yi ni ma da yin murmushin kafin na ce “me Noor ɗin ke nufi?” “Haske!” ta bani amsa. Na ce “zan so na gansa kuwa,da na ji daɗi sosai ni ma zan yi babban yaya” ina faɗar haka sai ta ɗan ƙara matsawa ta jawo kaina ta ɗora kan cinyarta,sai ta cire luluɓin kaina ta soma warware manyan kitson kaina tana mai cewa “wata rana za ki gansa ai ” “Yaushe kenan?” “Ranar da lokacin komawa ta can ya yi,ai zan tafi da ke ne ki ga yayanki in ya so sai Banah ya tsare miki daularki ” Shiru duk muka yi,bayan ta gama warware kitson sai kuma ta ɗebo ruwa ta zuba yaɗo ta wanke mini dogon gashina sannan ta ƙara yi mini wani kitson mai kyau duk da ƙwaya biyu ne kacal amma ya yi kyau.Wunin ranar ne muka ƙara yin wata shaƙuwa ta musamman ni da Ummilo ta dinga bani labarin Yaya Noor lokacin da yana ƙarami da kuma abubuwan da yake so da waɗanda ke saurin saka shi fushi. “Wane abinci ya fi so?” na samu bakina da tambaya. “Gurasa da zuma,yana matuƙar son cin gurasa yana dangwala ta a cikin zuma” ta bani amsa tana murmushi. Na ce “ni ma ina son zuma,kullum in na je farauta sai na je na nemo ta na sha” “Wato yayanki kika ɗauko wajen son zaƙi.Bani labarinki,ina iyayenki suke?” Ummilo ta faɗa . Wani iri na ji duk babu daɗi kafin na ce “dukkansu sun mutu,shi Abbana ban san shi ba ita kuwa Maa a ranar da na karɓi prophecy ɗina ta yi gushewa.Ina sonta sosai,ina jin kewarta a kodayaushe samunki ne ya maye mini gurbinta nake jinki tamkar ke ce ita” na ƙarashe faɗa hawaye na silalo mini masu zafi.Na ƙanƙame ƙafar Ummilo ita kuwa ta shiga shafar kaina haɗi da rarrashina kafin ta ce “ina matsafiyar tarihi sai yaushe za ta zo?” “Ta ce na yi miki sannu da jiki ma tun jiya ” “Ina amsawa,ina ne gidansu?” “Ita ma ba ta da iyaye mahaifinta ya rasu,mahaifiyarta kuma an damƙe ta” “Ayya ki ce ta dawo nan wurina sai mu zauna tare” Ummilo ta faɗa ,sam ban ji zan iya yi mata muso ba hakan yasa ba tare da na shawarci Banah ba na ƙara aika saƙon wasiƙar tsafi zuwa ga Deborah ba ta kuma ɓata lokaci ba ta zo har da ƙullin kayanta.A ɗakin Ummilo na yi mata masauki ,a ɗan wunin da muka yi a tare sai kuma muka ƙara ɗinkewa ni da ita muka manta mun taɓa samun saɓani. Da dare muna zaune bayan mun gama cin abincin,Ummilo na ririga Mila da ke yin rigima ta ƙi yin bacci sai ta soma rera waƙa wacce ta saka mu duk nutsuwa.Ba da Yaren da muke magana ba ne,haka kuma ba Yaren tsafi ba ne wani yare ne can daban da ita kaɗai ta san ma'anarsa amma sosai na ji daɗin baitin.Babu jimawa Mila ta yi bacci sai ta shimfiɗe ta tana murmushi tare da cewa “a duk lokacin da Noor ya fitine ni da kuka wannan waƙar nake rera masa ko kuma in ina son saka shi bacci” "Amma Ummilo da wane yare ne wannan?” na tambaya,Deborah da ke rubutu cikin littafin tarihi ta yi karaf ta bani amsa da “Yaran serena ne,yare ne da halittun ruwa ke yi ita kuma waƙar suna yinta ne domin janyo wani ruhi zuwa gare su domin aiwatar da abin da suke buri” Ido na tsura mata ina kallonta ta hasken farin wata,kafin na ce “ ta ya aka yi kika sani?” “Ta ya ba za ta sani ba,matsafiyar tarihi ce fa” Ummilo ta faɗa . Deborah ta yi murmushi tana mai cewa “tun jiya da na yi tozali da Ummilo na cika da mamakin me ya kawo Siren a nan” Na ce “ai na lura da yanayin yadda kike kallonta,to sai da safenku zan je na kwanta” na faɗa tare da lalubo sandata na miƙe na shiga ciki. Kan gadona na kwanta tare da yin shiru ina nazari,can sai ga Banah ya ratso rufin ɗaki ya shigo.Sam hakan bai kuma bani mamaki ba,illa kawai na mujiya da na zuba masa ina kallon yadda jikinsa ya ƙara rinewa kamar wanda ya fito daga cikin rijiyar kunama. Gefen gadon ya zauna tare da miƙo mini wata ƴar kwalba ya ce “shafa mini” ba tare da na miƙe daga kwancen da nake yi ba na karɓa na soma shafa masa sannu a hankali tiririn dafin jikinsa ya soma disashe ganina. ★ Da dare bayan gama bikin baiko sai aka zauna kan teburin cin abinci.Yarima NASLAM ne da dakarunsa masu taya shi yaƙi,suna cin abinci suna raha yayin da shi kuma yayi shiru yana ta juya gurasar da aka ajiye a gabansa ya kasa ci.Jakariya Ali da ke gefensa ya ce “bari na nemo maka zuma in ba za ka iya ci da markaɗaɗen yaji ba” Ya ɗago ya dube shi tare da yin murmushi kawai, Jakariya Ali ya fita zuwa madafa bai wani sha wahala ba don ya tarar da masu aikin kula da abinci ita ta miƙo masa zumar ya karɓa kafin ya zo ya kawowa yarima. Cikin ƙarfin hali yarima Naslam ya karɓi zumar ya soma dangwala gurasar a ciki ya kai bakinsa,sai dai ko kaɗan bai ji wani ɗanɗano ba.Gudun kar ya ɓata wa kansa lokaci sai ya ture abincin, Jakariya Ali ya dube shi cike da mamaki yana shirin yin magana yariman ya miƙe ya nufi ƙofa sai a lokacin ne kuma Ali ya hango baƙin tambarin maita ya fito yau a bayan wuyan yarima Naslam.Cikin bugawar zuciya shi ma ya miƙe ya fita,bai zame ko ina ba sai gidan Barham.Kamar zai ɓalla ƙofa haka yake bugunta,Barham ya buɗe yana mai kallonsa da mamaki yake cewa “lafiya dai ko?” Sai da ya shige ciki tare da rufe ƙofar sannan ya basa amsa da “ina fa lafiya yau baƙin tabon maita ya fito a wuyan yarima sam ya kasa cin abinci” Barham ya saki kofin hannunsa yana mai kallon jakariya Ali cike da tashin hankali,kafin ya ce “tabo? Wane iri? Baƙi ko ja?” “Na faɗa maka baƙi ne” “Hakan na nufin bayan kambun baka yarima na ɗauke da ɗigon baƙar maita ?” Barham ya faɗa tare da zuwa ya ɗauko wani littafi sai dai duk bincikensa ya kasa samo gamsashiyar amsa ,tsabar firgici goshinsa har ɗigar da gumi yake.Ya ɗago ya dubi Jakariya Ali cike da rauni yana cewa “babu abin da na samu a binciken da na yi” Ali ya ce “ya zama dole mu nemo mafita tun yau kafin gari ya waye ,saboda muddin aka kwana to Maitar za ta rinjaye shi ya fara sarrafa ta ” Idon Barham suka kaɗa suka yi ja,ya rasa meke yi masa daɗi kafin can ya ce “yawwa ina matsafiyar tarihi da aka damƙe?” “Tana can a kulle” ya basa amsa. “Mu je ka kai ni can ita ce kawai za ta bamu mafita” Barham ya faɗa tare da ɗaukar wata takarda.Haka suka dugunzuma zuwa can inda ake ɓoye masu laifi,ko kaɗan babu wanda yayi gigin hana su shiga saboda duk wani dakare a ƙarƙashin ikon jakariya Ali yake shi ne shugaban dakaru gaba ɗaya. Suna zuwa suka tarar da ita a zaune tana yin rubutu a ƙasa,ba tare da ta ɗago ba ta ce “me kuka zo yi? Kun zo tafiya da ni ne a kashe ni ?” Sai suka kalli juna kafin Barham ya yi shahadar cewa “wane laƙani ne ake yin amfani da shi domin daƙile bujurowar baƙar maita tsafi wacce ke bibiyar jini?” Ta ɗago da sauri ta dube su kafin ta ce,“ba zan taɓa faɗa ba ,kamar yadda yake son tozarta al'ummar Mayu da matsafa shi ma sai na bari ya tozarta a idon duniya kowa ya san wane ne shi” Barham ya furta surkullen tsafi sai ga shi tsundum cikin ragar da take ciki,har ƙasa ya zube alamun roƙo kafin ya ce “kar ki dubi wannan ɓangaren,ki dubi matsayinki na babbar matsafiyar tarihi ki sanar da ni laƙanin” Ta kawar da kai tana mai cewa “babu wani laƙani da zai daƙile maitar yariman masarauta ,sai dai a basa magani domin ɓoye ta.Daƙile ta duka kuma dole sai sarauniyar matsafa ce da kanta za ta iya yin haka” “Bani na ɓoyewar” Barham ya faɗa ,ta juya masa baya tana mai cewa “yana can a kusa da duniyar ruwa,fure ne na floris mai matuƙar muhimmanci da zarar ka kai gare shi za ka ji ƙamshinsa na sanar da kai shi ne abin da ka zo nema“ Barham ya miƙe yana yi mata godiya,yana shirin tafiya ta ce “ban ƙare jawabi ba,masu tsaron furen nan fararen fatale ne da ba su aminta da irin tsafinka ba” Barham ya juyo cike da tsoro kafin kuma ya dubi Jakariya Ali ya ce “na gode” Yana fitowa sai kuma suka fara shawarar ta yadda za a yi su fita daga cikin masarauta ba tare da kowa ya gani ba.Jakariya Ali ne ya je inda ake ajiye dokin yarima,kamar yana magana da mutum haka yayi masa bayanin komai kafin ya jawo shi ya fito. Barham ne ya fara hawa don shi ne ya san hanya sannan shi Ali ɗin daga ƙarshe.Cikin amincin Allah suka fita daga masarautar zuwa inda aka shaida musu za su samu maganin,ana kawowa wurin kuwa ƙamshi ya buge musu hanci kafin su yi wani yunƙuri kuma fatale duk sun zagaye su shi kuwa Barham ganin mutuwa a maƙoshi tsautsayi yasa ya furta baƙin tsafi,sai kuwa aka damƙe su aka jefa ɓoyayyar duniya. A can masarauta kuwa yarima Naslam ne kwance a ɗakinsa,har aka yi sallar asuba bai farka ba sai da hasken rana ya hudo ya daki tabon maita na wuyansa,wani irin kuka yayi da ya girgiza masarautar.Daidai nan free page ya ida,duk mai son shiga paid group zai biya kuɗin karatunsa 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 *Daga yau discount yake idawa 13.April* *NB:* Da zarar book ya kammala kuɗinsa 1k ne. MRS SADAUKI [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 1-2 #Damagaram Ƙarfe uku na dare agogon ɗakin ya nuna,a sa'ilin da mutane ke kwance suna hutawa a daidai wannan lokacin ne Hajara ta hana idonta bacci saboda yawunta da suke tsinkewa tsabar yadda suke kwaɗayin ɗanɗanon jini. Idonta ta fara rikiɗarwa tun farko kafin ta tura ƙofar ɗakin wacce ta yi sa'a ba a kulle ba,ɗakin cike yake da duhu amma bai hana idon Hajara hango Safeenat ba wacce ke kwance ta tallabe ƙaton cikinta tana sharara bacci. Yawun Hajara suka ɗiga ga ƙasa lokacin da ta yi tozali da ɗan jinjirin da ke kwance a marar uwarsa,ta ɗaga ƙafa da niyyar isa gare ta kawai sai ga wani haske da ba ta san daga ina ya fito ba ya luluɓe Safeenat.Da wani mugun sauri ta yi baya tana zarar idonta da suke jawur kamar wuta kafin kuma ta fice daga ɗakin gaba ɗaya,ba wai don ta haƙura ba sai don ƙara yin wani sabon shirin. “Hajara lafiya kika zo kika tsaya tsakiyar falo?” muryar mijinta Dayyabu ta daki kunnenta,da mugun sauri ta lumshe idonta gudun kar asirinta ya tonu,ba tare da ta amsa masa tambayar ba ta yi gaba ta koma ɗakinta ta ja ƙofa ta rufe.Sai a lokacin ta ja wani numfashi haɗi da buɗe idon, ƙarƙashin gadonta ta je jawo wata tukunyar laka.Banda baƙin hayaƙi babu komai a ciki,wani yare ta yi sai ga shi ta rikiɗe ta koma tsakaka haka ta fito ta fara bin bango ba ta zame ko ina ba sai ɗakin Safeenat a karo na biyu.Har yanzu hasken bai ida gushe wa ba,wannan dalili yasa ta sauka kan dressing mirror ta fiddo harshenta tare da fara zuba yawunta cikin man shafawa da Safeenat ta bar shi a buɗe . Bayan ta gama ne ta ƙara bin bango ta fito mijinta ta gani ya buɗe ƙofar ɗakinta ya shiga ya kuma fito da alamu rashin ganin ta ne yasa haka. Da sauri ta koma ta je ta ɗauki siffarta ta bil'adama,gefen gado ta zauna tana jin har yanzu kwaɗayinta bai kau ba.Haka wannan dare ya kasance daren rashin sa'a gare ta,sam ba ta yi wani baccin kirki ba. Washegari Tun safe Safeenat ta yi wanka ta shafa mai da turare sannan ta shirya cikin doguwar riga kasancewar cikinta ya tsufa ba ta da wata sutura mai yi mata in ba doguwar rigar ba. Cikin sanyin jikin da ya zama tabi'arta ta fito,a falo ta tarar da ahalin gidan kan table suna cin abinci. “Daddy ina kwana?” ta gaishe da mahaifinta,ya amsa cikin sakin fuska yana cewa “ lafiya lau Feenat ya ƙarfin jikinki?” “Alhamdullah!” ta amsa tare da maida dubanta gefen Hajara ta ce “ina kwana Gwaggo?” Hajara ta haɗe rai ta ce “ da ban kwana ba za ki gan ni ? Tsabar munafurci ba ki tashi fito wa ba sai da baiwarki ta gama girki kin fito ki kwashi banza to ban girka da ke ba” Feenat ta sunne kai tana jin wani irin zafi na tasowa daga ƙasan zuciyarta,babban takaicinta kuma da ta ji Daddy yayi shiru bai ce komai ba.Yaran Hajara Munir da Munira suka shiga yi mata dariya,ba ta kula su ba ta wuce kitchen ɗin ta nema wa kanta abin da za ta ci.Ƙasan tile ta zauna dirshen ta soma tunanin bayan ta gama cin abincin,hawaye suka zubo mata ba ta shirya ba da sauri kuma ta dafe ƙaton cikinta da ke faman juyawa tana jin muguwar ƙaunarsa don a yanzu shine kawai zai rage mata raɗaɗin rashin masoyinta Bashir. “A yi dai mu gani in tusa ta hura wuta! Yo wannan kukan shi zai maido miki mijin? Ai dama duk abin da aka yi shi da cin amana ba zai je ko ina ba.Yanzu da kika yi sanadin hana Bashir auren Murjanatu ina ce ya mutu ya bar ki,kuma ita Murjanatun na can Saudi Arabia cikin gata tana auren farin ciki” Goggo Hajara ta faɗa lokacin da ta tarar da Feenat a kitchen tana kuka.Ta yi kutufo da ƙafafunta ta ce “ ja ki ban wuri na wuce ko kuma na sabanta ki muguwa mai halin uwarta” da mugun sauri ta janye ƙafafunta wani sabon kukan na ƙwace mata. Cikin masifar nan Goggo Hajara ta ci gaba da balbale ta da masifa,“ ki tashi ki fitar min daga kitchen zan ɗora girki ,ki koma can ɗaki ki ci gaba da munafurcinki” Daga bakin ƙofa Daddy ya ce “Hajara ki zo ina son ganin ki ɗakina” Idonta kamar za su faɗo ƙasa tsabar yadda take hararen Feenat,haka ta wuce ta je ɗakin Daddy a tsaye ta tarar da shi ya ba ƙofa baya. “Daddyn yara ga ni ” ta faɗa cike da ladabi. “ Haja ki kiyaye ni,bari gani na ƙyale ki ɗazu kin ci mutumcin ƴata,na yi shiru ne kawai don in nunawa Feenat ba ta kyauta da ta bar ki ke ɗaya ki ka yi aikin gida ba .Amma ba zan lamunci ki tozarta min ƴa ba,nan gidana ne don haka tana da ƴanci sake wa yadda take so.Mine ne na yi mata gori? Maimakon ki rarrashe ta akan halin da take ciki shi ne za ki tsiro mata da wata sabuwar masifar? Ta rasa mijinta wannan kaɗai abun tausayi ne,sannan ga tsohon ciki.Na san tun bayan da Feenat ta auri Bashir ki ka tsane ta,kin manta cewa matar mutum kabarinsa tun can farko Allah bai nufa Murjanatun ce zai aura ba” Cike da munafurci Goggo Hajara ta soma kuka har da jan majina kamar wata yarinya,da mugun sauri Daddy ya juyo tare da jawo ta jikinsa yana cewa “mine ne kuma na kuka? Ke fa uwa ce bai kamata sai an faɗa miki abin da ya dace ba,ɗa na kowa ne ba ka san mai taimakon ka ba” “Amma Daddyn yara ka fi kowa sanin yadda na riƙe Safeenat da zuciya ɗaya amma rana tsaka ta ruguza alaƙar nan don kawai ta ga banda burin da ya wuce Murjanatu ta yi aure” “To ai yanzu komai ya wuce,ba ga shi ta yi auren ba? Jiya ma mijinta ya min magana kan yana so ta dawo gida ta haihu ” Jin ƴarta za ta dawo sai ta manta da zancen kuka ta washe baki ta ce “au ! Madallah! Yaushe za ta zo?” Daddy ya murmusa ya ce “a'a ƴarki ta ce kar a sanar da ke za ta yi miki bazata kawai ki zamana cikin shiri” da wannan Daddy ya fice ya bar gidan zuwan can Company wurin aikinsa. Goggo Hajara kuwa kitchen ta koma sai ta tarar da Feenat ta ɗora girkin rana sai gumi take saboda zafin wutar gas,ta taɓe baki kafin ta fito. Ita kuwa Feenat baiwar Allah sam ba ta ƙaunar tashin hankali wannan ya saka ta ɗora girkin duk don a zauna lafiya.Kafin ta gama jikinta ya soma ƙaiƙayi, soshe-soshe ta fara yi ganin abun na ta yin gaba yasa ta kashe gas ɗin ta fito.Ɗakinta ta je,direct toilet ta shiga ta soma yin wanka sai dai ba ta canza zane ba sai ma wani ja da fatarta ta yi.Dakyar ta daure ta je ta ida girkin ta zuba a kuloli ta jera kan table,da ta koma ɗaki sai ta ɗauki hoton hannunta inda alamun jan ya fi yawa ta tura wa ƙawarta Sakeenatu tana tambayarta ko mene ne wannan kasancewarta likita .Babu jimawa ta kira ta bayan sun gaisa ne take cewa “ sai dai ki zo asibiti a duba ki ta waya ba a ganewa,kuma ni ba aikina ba sai dai na haɗa ki da likitan fata” Feenat ta ja ajiyar zuciya ta ce “ KEENAT kin san Daddy ba zai bari na fita ba,kuma dama bai dace mace mai takaba ta fita ba” Cike da tausaya wa KEENAT ta ce “ na sani amma ai lafiya ta fi komai ,ƙila kuma kin ci wani abu ne da ya haifar miki da hakan” “Ban ci komai ba fa,ya aikin ana ta fama ko?” “Wallahi kuwa,in sha Allah in na sauka zan biyo nan gida na duba ki” sosai suka yi hira kafin su yi sallama. Daga inda take zaune ta fara kallon hotunan Bashir inda yake sanye da Kakin soja,nan ta lalace wurin kallonsu har sai da Munira ta shigo kiranta .Ta miƙe dakyar ta fita,a falo ta tarar da Goggo Hajara tun da ta fito ta lura idonta na kan cikinta.Ta sunne kai tana mai karanta ‘ Hasbunallahu wani'imal wakil ’ a can ƙasan zuciyarta,cikin nata ne ya soma yin motsi kamar zai fito mata ta cibiya.Tsabar yadda take jin ciwon juyinsa yasa ta kai hannu ta dafe ƙasan mararta tana mai fitar da nishin wahala,ido rufe ta ci gaba da sauraren azabar da ke ratsa duk sassan jikinta. Goggo Hajara ta yi wani makirin murmushi tana mai cewa “ Safeenat lafiya kuwa?” Sai a lokacin ta ware idonta da suka yi wani mugun ja,bakinta sam ba zai buɗu ba ballantana ta iya yin magana.Bayanta da ƙugunta suka ƙage lokaci guda wanda ya haifar mata duƙawa ba ta shirya ba,tuni idonta sun fara ganin dishi-dishi duk da wannan ne cikin farko tuni ta fahimci haihuwar ce ta zo bilhaƙi. Goggo Hajara ta ce “ Haihuwa ce kam,Munira fita waje bari na ɗauko leda ” “Mama in kira mai taxi ku wuce asibiti ko?” Munira ta faɗa tana kallon Safeenat wacce tuni ta fara wani gurnani mai haɗe da nishi. “Uwar mai taxi za ki kira ,fice na ce” Goggo Hajara ta faɗa tana mai shiga ɗakin Safeenat ta ɗauko robar da aka tanadi duk wasu kayan haihuwa. Da kanta ta shimfiɗa leda ta ɗora wasu zannuwa akai kafin ta ce “ Safeenat ki cire rigar nan mai haihuwa ina ruwanta da wata sutura” tsabar azabar da take ji yasa ba ta yi yunƙurin hana Goggo cire mata kayan ba. Yawun Goggo Hajara har wani dalala suke suna tsinkewa lokacin da ta ga kan ɗa ya sawo kai.Jikinta har rawa yake wurin taimakawa yaron ya fito ,babu wani jinkiri ko ɓata lokaci ta fara juya ido tare da soma kai

Chapter 6 of 10