Share this page
Nafisa kar ki tafi ki bar ni ki jira har Abbas ya dawo,bari na kira Mamar na shaida mata” haka suka yi kuwa,tun suna jiran Abbas har ƙarfe sha biyun dare bai zo ba a tare suka fito suka rufe gida da ko ina sannan suka je suka kwanta. A can asibiti kuwa bayan fitar Sakeenatu,Gwaggo Rahamu ta yi wani kishingiɗa ga kujera kamar mai bacci nan kuwa ruhinta ne ta soma fitar wa daga gangar jikinta.Sawun Sakeenatu ta bi,hasali ma ta rige ta zuwa gidan duk abin da take yi akan idonta hanyar farko da ta soma bi shi ne tafiya ta shiga tunanin mai kula da nepa na unguwar ya ɗauke wuta ba tare da shi kansa ya san dalili ba a cikin wannan duhun ne ta yi ta yi wa Sakeenatu mugunta.Da ta koro ta da addu'a shine ta biya wurin wasu miyagun ƙawayenta ta basu address suka je a siffar gafiya,su ma ba su bar gidan ba sai zuwan Nafisa. Abbas na daga can gefe Mamuh na yi masa hira tana murmushi saboda duk abin da ke faruwa ita tana gani saɓanin shi Abbas ɗin.Bayyanar esprits biyun yasa yanayin shaƙar iskan ɗakin ta sauya saboda tsabar muguntar su, wannan karon hatta Abbas sai da ya ji wani iri.Har yanzu Gwoggo Rahamu ba ta farka daga baccin ƙaryar da take ba,cikin hirarsu ta ƴan duniyar ɓoye suke bata labarin yadda suka firgita Sakeenatu tana ta yin kuka. “Na gode sosai ƙawayena,kar ku manta in kun gama yawon Maitar dare ku biyo ta nan mu sake komawa mu uku mu haɗa ƙarfi mu shayar da ita mamaki” baƙin ruhin Gwaggo Rahamu ya faɗa ,suka yi dariyar mugunta tare da ɗaukar mata alƙawari kafin su bar wurin.Cikin ƙwarewa ta dawo da ruhinta a gangar jikinta,ta dubi Abbas tana mai cewa “ bacci ya ɗauke ni duk yau ban rintsa ba,ina sauran waken ni ma na ci yunwa nake ji” Shi Abbas sam ya manta da wani zancen wake saboda yadda Mamuh ke masa hira,sai yanzu ya tuna Sakeenatu ta je gida dafawa.Da ya duba agogon hannunsa ransa ne yayi mugun ɓaci,“ uwar tamu ai ba ta dafo ba tana can tana gantalin da ta saba,ah to dama su likitoci ba su da kamun kai tsakaninsu da abokan aikinsu suke neman juna in aka ce miki tana can asibiti wani ƙato ya taushe kar ki yi gardama” Mamuh ta faɗa ,yayin da Gwaggo ta karɓe “ i sosai ita ma wannan shegiyarta ta ai shugabansu ne ya ɗirka mata cikin ya bar yaronmu da wahala,wai Abbasi wai ya ƙaƙaba maka aurenta?” Kasa cewa komai yayi,haushi goma da gomiya tara ya rasa da wane zai ji abin ka kuma da zuciyar namiji sai ya ji zargi ya ɗarsu a ransa.Da ya nuna zai je gida Mamuh ta hana shi tafiya ta hanyar amfani da tsafinta,haka suka dinga kwaso sharri iri-iri suna yaɓa ma Sakeenatu sosai kuma suke samun gurbi a zuciyarsa.Can waje ya koma ya kwanta kan wani banci yana ta tunanin rayuwa baya yadda neman aurensa ya kasance yadda sam Sakeenatu ba ta samu shaidar ƙwarai ba ga mutanen unguwa amma ya rumtse ido ya ce sai ita . Ƙarfe biyu da rabi na dare ƙawayen Gwaggo Rahamu suka biyo mata,kafin su yi tsinke gidan Sakeenatu.Sai da suka shiga kitchen suka cinye kaf abincin da ta dafa sannan suka dawo falo suka fara shawarar abin da za su yi mata,suna dariyar mugunta suka tura ƙofar falon sai dai da zarar sun yi niyyar ɗora ƙafarsu a tile ɗin bedroom sai su ji tamkar cikin garwashin wuta ne suke ɗora su.Gwaggo Rahamu ta ƙanƙance ido tana kallon gefen Nafisa inda kusan kanta ta ɗora wayarta ne sautin karatun Alqur'ani na tashi a hankali wanda ba ma a jinsa sosai,kamar ta san suna nan kuwa sai ta kai hannu ta ƙara volume a tare suka saki wani ihu wanda sai da gidan ya girgiza a firgice Sakeenatu ta farka tana zarar ido... Mai son complete 800 ne via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 10 A wahalce Gwaggo Hajara ke bin bango don isa ɗakinta,fatar nan tata ta tsakaka duk ta yi wani taushi ta fara fitar da wani fanko.A yadda bango ke zuzar fatar cikinta ji take kamar ta yi ta ƙurma ihu sai dai ba dama sata lahira! Tana isa ɗakinta ta ɗauki siffa ta mutum nan ne fa ta yi tozali da yadda duk jikinta ya kumbura yayi ja kamar wacce aka soya,mai ta ɗauko ta shafe jikinta da shi tana matsar ƙwalla tare da jin tsanar Safeenatu na sake feso mata daga can ƙasan zuciyarta. A fili ta furta “ sai na wulaƙanta rayuwarki,sai na saka kin tozarta a duniya,sai na shayar da ke gubar azaba wacce sai kin gwammaci mutuwa akan rayuwarki. Ke kan ki Habibah ba zan bar ki ba zan ɗora miki karatu da alamu har yanzu ba ki ji jiki ba shi yasa kike taimaka wa wata wurin ruguje plan ɗina” shiru ta yi jin an turo ƙofa.Daddy ne ya shigo da sallama a bakinsa,ba ta amsa ba sai ma saurin jawo hijabi da ta yi ta saka duk ta luluɓe jikinta. “Ni kam Hajara lafiya kike? Kin ga yadda fuskarki ta yi suntum sai huci take kamar ƙullun wainar da ya ji yis?” Daddy ya faɗa yana ƙare mata kallo.Wani ƙululun baƙin ciki ne ya ƙara turnuƙe Hajara ta ce “ uwar waina ce....” ba ta ida kai aya ba ta ji yatsun Daddy biyar kan kuncinta,shaye da mamaki take kallonsa nan ta hango wani baƙin tauraro tsakiyar goshinsa wanda ko shakka babu aikin Habiba ne ta tura masa shi. Ba ta gama dawowa daga duniyar mamakin da ta je ba Daddy ya soma magana cikin masifa,“ wato abun naki ya fara zama iskanci,daga tambaya shine za ki zagin uwata saboda kin san yau za ta zo.To tsaya ki ji Hajara duk wata tijararki ki tattara ta ki ajiye wuri guda muddin Hajiya ta koma da baƙin cikinki gida to wallahi akan aurenki.Ki tashi ki ɗora girki tsabar lalaci muna da mai jego a gida amma kin zo kin shige ɗaki kin haye gado tare da saka hijabi kamar matar liman kowacce za ta yi aikin ƙwarai” yana gama faɗa ya nufi ƙofa,sai kuma ya juyo ya ce “ Murjanatu na kan hanya sai ki fara shirin tarben ta” kawai ya fice. Gwaggo Habibah da ke zaune kan kujera a falo ta saki wani irin murmushin nasara,tun da uwarta ta haife ta yau ce ranar farko da ta juya taurarinta na baiwa ta yi aiki da su.Tun bayan da ta yi wa Twins wanka ta shirya su sannan ta bai wa uwarsu abin da za ta ci kawai ta fito falo ta zauna,Daddy na fitowa ta soma yi masa transfer ɗin tauraron ta hanyar kallonsa tsakiyar ido da farko har ya tambaye ta lafiya sai kuma yayi shiru jin sabon abu a tattare da shi. Duk abin da yake faɗa wa Gwaggo Hajara sarai ta ji alamun aikinta yayi kyau,ta saki murmushin nasara tana mai cewa ‘ mijinki zai zame miki kumurci,da haka zan raunata muguwar zuciyarki’ “Habibah karɓi wannan ko kuna da buƙatar wani abu sai a ɗauka ciki” Daddy ya faɗa yana mai katse mata tunanin zuci.Ta karɓa tana mai cewa “ Yaya Ɗayyabu na ce bayan biki sai Safeenatu ta koma can gida wurin Hajiya ko?” “Saboda me? Ba a nan za ki zauna ba?” “Eh to ni ma da haka na ce ɗin amma sai na ga kamar anty Hajara ba ta son zamana tun da na zo idonta kamar za su faɗo tsabar yadda take jifana da mugun kallo” Ran daɗi ya ɓace, yanayin fuskarsa ya canza tuni tauraron goshinsa ya ƙara yin baƙi ba tare da ya ce komai ba ya ƙara komawa ɗakin Gwaggo Hajara ita kuwa Habibah har da wata dariyar mugunta ta yi tare da tashi tana taka rawar murna. Daddy na shiga ɗaki ya yi wa Hajara wankin babban bargo,ko ina ana jin muryarsa yadda yake yi mata masifa in ta je yin magana kuma sai ya gwaɓe bakin.Da wannan baƙin cikin ya fita ya bar ta,sai da ta sha kuka wiwi sannan ta fito ta ɗora girki babu jimawa kuwa sai ga Hajiya ta zo .A ladabce Gwoggo Hajara ta gaishe ta wanda sosai ita hajiyar ta yi mamaki don rabon da ta yi mata irin wannan ladabin tun ranar da Ɗayyabu ya kawo mata ita a matsayin matar da zai aura.Cikin sakin fuska ta amsa tare da cewa “ to barkarmu Safeena an sauka Allah raya kan sunnah,kin samu mai taya ki aiki da kuma miji” Hajiya ta faɗa tana murmushi a doli ita ma ta yi murmushin yaƙen a can ƙasar zuciyarta tana cewa ‘ an haifo mana masifa dai aljanar jaririya muguwa wacce ta yi gadon jaraba ’ “Zan shiga daga ciki” hajiyar ta faɗa tare da nufar ɗakin Safeenatu,cike da murna ta zauna tana kallon jariran Gwaggo Habibah ta ɗauki namijin ta bai wa Hajiya ta karɓa tana mai kai masa sumba haɗi da yi masa addu'a sannan ta miƙa shi.Ana ɗora mata macen jikin Hajiya ya ɗau kyarma kamar mazari,murya na ɗan rawa ta ce “ wane suna za a saka musu?” “Basheer da Baseerat ” Habibah ta bata amsa tana murmushi tana kallon mahaifiyarta wacce kambun muguntar Gwaggo Hajara duk ya dabaibaye ta yanzu kuma ya fara barazanar tarwatsewa. Hajiya ta ce “ karɓar ta” tana mai miƙo Baseerat don ruhinta ya soma yin rauni, Habibah ta ce “ Hajiya don Allah ki riƙe t...” ba ta kai ƙarshe ba Hajiya ta miƙe ta je ta shimfiɗe Baseerat a shimfiɗa,sai aka yi rashin sa'a safar da aka saka ma hannunta na hagu ta fita wani mugun haske ya fito ya shiga ƙirjin Hajiya saura ƙiris ta faɗi saboda yadda fitilun idonta suka rufe jiri kuma ya ɗebe ta. Safeenatu dai na daga gefe tana kallon abubuwan ban al'ajabi , Gwaggo Habibah ce ta kamo Hajiya ta taimaka mata ta zauna.Kamar mai cutar huka haka numfashinta ke fita,ruwan sanyi ta nema da sauri aka bata ta shanye ƙatuwar gora. “Habibah bani pilow bacci nake ji” cewar Hajiya ,da sauri ta ɗauko ta miƙa mata ita kuma ta kwanta babu jimawa bacci mai nauyi ya ɗauke ta . Safeenatu ta ce “ Gwaggo Habibah ni fa na fara jin tsoron lamarin Baseerat kina dai ganin abin da ya faru, wannan ai ba zan fita da ita unguwa ba gudun ta jawo min masifa ace mayya ce ma” Da mugun sauri Habibah ta katse ta “ kar na sake jin kin faɗi haka,saboda ƴarki ba mayya ce ba ƴar baiwa ce” “To amma ai wasu ba za su ganin haka ba ko? Tun yanzu tana jaririya tana haka ina ga ta girma?” Gwaggo Habibah ta yi murmushi ta ce “ Safeenatu bari dai na soma ɗan guntsira miki labaran duniyar ɓoye, kowane mutum da kike gani a duniyar nan yana da matriculation na sama.Ko kuma lambar sirri ta samaniya,da wannan ne in aka sayar da ruhin mutum daga lokacin matriculation ɗinsa ta saminiya sai ta canza.Duk wani ɗan Adam kasance yana da taurari iri-iri waɗanda suke taimakawa wurin gudanar da al'ammuran duniyarsa.Ya zama doli kowa ya kare taurarinsa ya basu tsaro,muddin ka yi sakaci da su kuma to wannan mutumin zai iya zama cikkaken maƙasudi wurin tallafawa masu sayar da taurari su ƙwace masa su.” Safeenatu ta katse ta da cewa “ ta ya za a ƙwacewa mutum taurarinsa alhalin mallakinsa ne?” Gwaggo Habibah ta bata amsa da “ ba ki taɓa jin labarin wata ma'aikaciyar saloon ba mai gyaran gashi? Ki nemi littafin Mrs Sadauki na MAITAR IDO a nan duk za ki samu cikakken labarin.Ki sani cewa matsafa don su kama ruhinka ma abu ne mai sauƙi,abin da suke buƙata shi ne kawai keɓaɓen abu na gaskiya ta atomatik da ke fitowa daga mutumin da ake son cutarwar,kamar gashinsa,sunansa,date ɗin ranar haihuwarsa,zufar jikinsa wato tufafin da ya saka ba a wanke ba,ko kuma jinin jikinsa.Daga lokacin da matsafi ya riƙe ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai iya buɗe katinka na samaniya kuma ya karɓe ƙarfin ikonka wato power daga nan sai yayi abin da yake so” A sanyayye Safeenatu ta ce “ duk Baseerat za ta iya yin wannan? Gaskiya ni dai ban so in kin san hanyar da za a toshe wannan baiwar tata ni dai ki taimaka min don ina ji a jikina muddin aka bar ta da ita a gaba za ta zame mana masifa” Gwaggo Habibah ta yi mata wani irin kallo irin na ba ki da hankali kafin ta je ta ɗauki safar hannun ta saka ma jaririyar wacce ta buɗe ido sai kalle-kalle take kamar mai wayo,kafin kuma ta kafe idonta ga madubi Gwaggo Habibah ta yi kasaƙe tana kallon Baseerat a sannu a hankali ta ga idon yarinyar na sauya kala har suka zama farare tasss babu ɗigon baƙi,wani abu kuma ya soma fita daga bakinta yana bin direction ɗin madubi.Habibah ta ja wani dogon numfashi don kuwa ta fahimci Baseerat za ta yi tafiya ne ko kuma yawon buɗa ido wanda dayawan mutane na yinsa ba tare da sun san mine ne ba.Sai ka ji tamkar jikinka ya zama gawa kana son tashi daga bacci amma ka kasa tamkar an danne ka da dutse,har kwatanta buɗe ido ake amma baka iyawa saboda ruhinka da yayi balaguro ya bar gangar jikinka a kwance. #SAKEENATU Gefen da Nafisa ke ta sharar bacci ta duba kafin ta ɗaga kanta sama tana kallon yadda rufin ɗakinta ke wani lomaƙawa tsabar yadda ake tafiya a guje.Kukan jaki da na kare ga kuma na mage duk a lokaci guda,gefe guda kuma wata siririyar murya take ji tana kiran sunanta.Idonta ya ciko da hawaye,fitsari take ji amma tsoro ya hana ta tashi.Nafisa ta soma tayar wa,ita kuwa dakyar ta buɗe ido ta ce “ mine ne ?” “Fitsari nake ji” ta bata amsa kamar wata ƙaramar yarinya,cikin magagin bacci Nafisa ta ce “ ki je ki yi mana” sai ta koma baccinta.A hankali Sakeenatu ta zuro ƙafafunta ƙasa a tsorace ta shiga toilet ko Bismillah ba ta yi ba ballantana karanto addu'a,a tsorace ta je ta haye WC ɗin ta soma fitsari sai kuma jikin ya soma kyarma ganin ruwa na ta ɓulɓulowa ta ƙasan tile suna cika toilet ɗin ko kafin ta ƙyafta ido sun kawo mata a wuya ta yunƙura za ta tashi amma sai ta ji tamkar an saka super glue an manna ta a jikin WC ɗin ta ƙurma wani uban ihu wanda dama su mugayen shine suke jira ai kuwa suka tsaga rufin ɗakin ji kake ƙiiiiii kamar suna yaga zane.Idon Sakeenatu duk a waje take kallon yadda bindi mage,na kare da kuma idon wata baƙar mujiya a daidai wurin da suka tsaka.Cike da mugunta suka diro toilet ɗin wanda yayi daidai da tsinkewar numfashin Sakeenatu..... [13/04 10:28] MRS SADAUKI: MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 11 Duk da Sakeenatu ta suma hakan bai sa mugayen nan sun ƙyale ta ba,haka suka ajiye mata cutar a jikinta kafin su bar ta nan yashe a toilet.Cike da murna suka koma asibiti suka dinga bai wa Mamuh labarin abin da ya faru,cike da mugunta ta ce “ gobe da safe da hannunta za ta dafo wake ta kawo min ,daga nan kuma zan datse alaƙar farin cikinsu ita da Abbas zan maye mata gurbinsa ” duk suka sa dariya suna ƙara tsara mata wani salon muguntar. Washegari Kiran sallar asuba ya tashe da Nafisa,ta sauka daga bed ta shiga toilet nan ta ci karo da Sakeenatu a yashe babu numfashi.Hankalinta a tashe ta cika bokiti da ruwa ta zuba mata,ta ja ajiyar zuciya kafin kuma ta soma kuka cikin firgici.Nafisa ta kamo ta tare da fiddo ta haɗi da tambayar ta,duk a tsorace take wannan yasa ta kasa yi wa ƙanwarta bayani.Ganin haka yasa ita kuma ta je ta yo alwala ta yi sallah,bayan haka ne ta matsa wa Sakeenatu ta je ita ma ta yi sallar.Ko wanka ba su yi ba ta ce “ Nafisa tashi mu je gida wallahi tsoro nake ji” haka suka runguɗa suka je can gidan Mama wacce ke ta ƙoƙarin hura wuta domin ta ɗora ɗumame,tana ganinsu ta san ba ƙalau ba.Kamar wata ƴar yarinya haka ta je ta rungume mahaifiyarta tana wani sabon kukan,“ Subahanallahi! Nafisa mike faruwa?” “Wallahi Mama ban sani ba ni ma na yi ta tambayar ta amma ta ƙi faɗa min,alamu dai sun nuna tsorata ta ake yi a can gidan nata” Nafisa ta bata amsa. Mama ta ce “ to Allah ya sawwaƙa,ku wuce ciki bari na kira malam na shaida masa ” Can cikin mitsitsin ɗakinsu suka shiga,Ma'idah na kwance sai bacci take ba ta farka ba.Sakeenatu ta ɗauki abarta ta rungume ƙam kamar an ce za a raba su,mugun mafarkin da ta yi kan Ma'idar ya dawo mata a kai.Ta lumshe ido ruwan hawaye na kwaranya a kumatunta,ta yi tunanin kakarta ta yanke saƙa,ba ta taɓa tunanin za ta sake yin ƙunci a rayuwa bayan wanda ta yi a baya ba tun lokacin da Abbas ya shigo rayuwarta komai ya dawo mata normal ashe da sauran kallo a sama.Tsohuwar shuɗaɗiyar rayuwarta ce kwanyarta ta soma yi mata tariya,cikakken sunanta shi ne Sakeenatu Abubakar,ƴar gwagwarmayar rayuwa mai zuciya cike da burin zama wata aba a duniya.Karatun boko shi ne abokin da ta riƙa sannan kuma tubali don gina rayuwa mai inganci,sai dai ƴan magana na cewa rashin sanin ya fi dare duhu.Sakeenatu ba ta taɓa sanin cewa ba sanadin boko ne za ta zubar da mutuncinta ba,zuwanta jami'a shi ya ƙara buɗe mata ido sosai ta waye ta zama ƴar gayu,ƙwazonta a wurin karatu shi yasa ta ciri tuta a wurin malaman makaranta kusan duk maganarta suke suna yabon baiwar da Allah yayi mata banda malam Agali wanda tun ranar da ya ɗora idonsa kanta yake jin mugun sha'awarta saboda ta haɗu ta kowanne fanni.A wata rana Laraba ce wacce ta kasance ranar farko da ya fara ɗana mata tarko da kuɗi,“ki hau taxi” ya faɗa cikin taushin murya a gaban ɗalibai ba tare da ya ɓoye ba kuma ya sakar mata murmushin nan nasa wanda yake haukata ƴan matan makaranta da na wajensu .Ba za ta cewa tana sonsa ba,amma ita ma tana cikin waɗanda yake burge su saboda yadda yake da kyau kamar Balarabe ga baƙar sumar kansa ko wata macen ya fi sannan ɗan gayu ne kullum cikin shiri mai kyau yake.Ƴan matan ajin suka hau yin shewa suna taɓi tare da cewa yau dai an samu wacce ta sace zuciyar Dr Agali,da ido ta bisa kawai lokacin da yake fita daga ajin yayin da ɗalibai duk suka dawo kusa da ita kowacce na tofa albarkacin bakinta.Sakeenatu ta ji wani irin girman kai ya zo mata tare da alfaharin ita ce ta ciri tuta,cours ɗin da aka yi musu na gaba sam ba ta fahimci komai ba saboda tunanin malam Dr Agali.Ba ta buɗe ƴar enveloppe ɗin kuɗin ba sai da ta je gida, kuɗi ne ƴan jika-jika sabbi da su har guda goma.Ta kai su kusan hancinta ta shaƙi ƙamshin turarensa,tuni jikinta ya mutu murus ta na shirin saka kuɗin a jaka ne ta lura ɗaya daga cikin takardun kuɗin an rubuta lamba a jiki.Kamar wacce ake tsikara ta ɗauki wayarta ta loda lambar sannan cike da waswasi ta tura masa saƙo babu jimawa ya kira ta,kamar wani mutumin ƙwarai har da yi mata sallama ta amsa tare da ce masa “ fatan ka je gida lafiya?” Cikin muryar nan tasa ta buzaye waɗanda ba su ida iya Hausa ba ya amsa mata da “ a'a ina wata asibiti an kira ni in tiyata” Ta saki murmushi mai sauti ta ce “ ina son ganin ranar da za a ce Sakeenatu na yin tiyata” “Lokacin zai zo ke dai ki ci gaba da dagewa wurin yin karatu,na ji malamai sai yabon ki suke ashe ba a cours ɗina ne ba kawai kika ƙware” nan ma murmushi mai sautin ta yi kafin ta ce “ burina shine zama babbar likita wacce duk duniya za ta yi alfahari da ita,ana dinga nuno ni a TV” “Kina iya barin Nijar Keenat?” Dr Agali ya tambaye ta,kai tsaye ta basa amsa da “ eh sosai sai in gwamnati bai ɗauki nauyin karatun nawa ba” “To ki fara shiri in sha Allah ni nan zan sa burinki ya cika” “Keee Sakeenatu keee!” Mama ta faɗa tana mai kamata dundu wanda shi ya katse mata tunanin shuɗaɗiyar rayuwarta,da sauri ta dawo hayyacinta tana mai kallon Mama wacce ta janye Ma'idah da sauri tana mai ci gaba da cewa “ kawai ki kama yarinya ki riƙe gam tana kuka da ranta amma kin ƙi sakin ta” Sam ita ba ta san riƙon da ta yi wa Ma'idar ya cutar da ita ba,cike da takaici da zugin da zuciyarta take yi ta tashi ta fita ta cika bokiti da ruwan ta shiga banɗaki.Wanka take son yi amma tunanin Dr Agali sai ƙara kawowa kwanyarta farmaki yake,abin da ya faɗo mata a rai a yanzu kuma shi ne ranar da ya kira ta ya shaida mata Visa ɗinta ta fito ta zo ta karɓa bai jin daɗin jikinsa.Ba tare da wani tunani ba ta je gidan nasa kamar yadda yayi mata kwatance,duk a tunaninta yana da mata amma sai da suka shiga ciki ne ta ga shi ya bata ruwa sannan ya kawo mata lemu wanda ya zubar da shi a jikinta da gayya har tufafinta suka ɓace.Ta wani rumtse ido don takaicin ganin video yadda Dr Agali ya ɓalle maɓallan rigarta ya cire ta ya bar ta daga ita sai bra ya je wanke mata ita duk ta yi tunanin ƙauna ce ta kawo haka sai bayan ya dawo ne ya soma yi mata wasu zafafan romance.“ Ni fa dama ba zan yi miki komai ba, wannan ɗin ma ban san ya aka yi ya faru ba ki yi haƙuri ba zan sake ba sai bayan aure” Dr Agali ya faɗa lokacin da ta sakar masa kuka. “Anty Sakeena don Allah ki aje tunanin nan gefe ki yi wanka ki fito ga malam nan ya zo” Nafisa ta faɗa daga bakin ƙofa.Sai a lokacin Sakeenatu ta fara wankan ,bayan ta fito ta je ta gaishe da malam wanda ya kasance ƙanen Mama ne.Cikin garwashin wuta ya zuba ƴaƴan habbatu sauda hayaƙi ya turniƙe ɗakin,idon Sakeenatu duk suka fito waje ta soma tari kamar ranta zai fita shi kuwa karatu ya soma nan lamarin ya ƙara yin gaba don tuni ta soma yin kuka .Tsawon lokaci kafin ya bar ta haka nan,magani ya bada wanda za ta dinga shafawa da hayaƙe jikinta da kuma gidan.Bayan tafiyarsa ne ta samu ta ci abinci,wunin ranar dai Mama haka ta ƙare shi wurin yi mata nasiha dab da magrib Nafisa ta yi mata rakiya zuwa gidanta.A tare suka yi gyaran gidan da girki kafin ta yi wanka ta shafa man da malam ya bata ta kuma yi turare. A can asibiti kuwa tun safe da Abbas ya bar su bai koma ba,kuɗi kawai ya bar musu hakan bai yi wa Mamuh daɗi ba.Ana yin sallar magrib ba tare da likita ya sallame ta ba Gwaggo Rahamu ta haɗa tarkacensu suka fito a ɓoye.A bakin hanya suka samu adaidaita wacce za ta kawo su gida ,suna tafe suna hira “ ai tun da kika ga bai dawo ba to tabbas babu makawa da ya koma gida karuwanci ta yi masa kin san halin namiji kan mace sakarai yake zama” Gwaggo Rahamu ta faɗa . Mamuh ta tsuke bakin nan nata ta kasa cewa komai saboda baƙin cikin da ke addabar baƙin ruhinta,gani take yi ma tamkar adaidaitar ba ta gudu. Suna isa gida tun a bakin ƙofa suka canza kalar idonsu daga na mutum zuwa na mugunta,sai aka yi rashin sa'a Nafisa na tsakiyar falo tana hayaƙa hantiti da tazargade .A tare suka shigo,a tare kuma suka saki ihun azaba suna masu faɗuwa ƙasa suna yin wani irin huci a gaban idon Nafisa suka rikiɗe suka zama jibga-jibgan macizai kowa yace shi ba ma matsoraci ne ba to bai ga abin tsoron ba .Da wani mugun sauri Nafisa ta mangal ɗin hannunta mai cike da garwashi,da azama ta nufi hanyar ɗakin Sakeenatu sai dai kafin

Chapter 9 of 10