Share this page
kayan arna,ƙusumbin tsutsotsi maƙale a bayanta,idon sharrinta na fitar da gubar tsafi ” “Naslam na sha faɗa maka ita ɗin ba aljana ba ce,wakiliyar duk wasu sheɗanun Mayu da matsafa ce.Ita ce aka damƙawa kundin prophecy domin cika wani baƙin ƙuduri nasu.Amma da ka gan ta wane yunƙuri ka yi?” “Abih ta ya zan iya yin wani abu? Yanzu dai ina so a shirya dawakan yaƙi su ƙara komawa can domin binciko mini ita” Shiru sarki yayi kafin kuma ya fita,cike da bayar da umarni ya sa aka shirya dawakai majiya ƙarfi da kuma dakarun yaƙi . Jakariya Ali shi ne ya shugabanci tawagar,sai dai sama da awa biyar suka kwashe ko kusa da ruwan sun kasa zuwa saboda tsantsan tsaron da aka shimfiɗa musu a dole ya jawo su suka dawo gida a lokacin tuni yarima Naslam ya kasa sukuni ya sa an kawo masa farin ƙyalle haɗi da abin zane haka ya zauna ya zana Naomi kai ka ce ta gasken ce . Ido ya tsura mata cike da tsana yana tambayar kansa a zuci ‘ wace ce ke? Me yasa tun da na shiga zangon balaga kika addabi rayuwata?’ Jin an banko ƙofa yasa shi barin zancen zucin tare da maida idonsa kan ƙofar shigowa.Jakariya Ali ne sanye da kayan yaƙi,zanen ya fara kallo kafin ya cewa yarima “babu wata nasara dangane da tekun can,amma wai don Allah me yasa ka damu? ” Cikin zafin rai ya ce “aljanar mafarkina ce” “Amma fa ita ce ta cece mu lokacin da Mayu suka fara sarrafa tsafi ” jakariya Ali ya faɗa . “Bayan ta yi silar cutar da ni,Ali na tsani aljanar nan tun ba yau ba na fahimci cewa ita ɗin rauni ce a rayuwata” “Yarima a duk lokacin da na ji kana irin wannan zantukan sai na dinga jin cewa kai ma fa tamkar kana ɗauke da ikon prophecy ” Kafin yarima Naslam ya kai ga yin magana wani irin iska mai sanyi ya fara ratso ɗakin yana shigowa,babu abin da ya motsa sai zanen hoton Naomi shi ma ɗin cike da abin al'ajabi yadda bakinta ke ɗan buɗewa tana murmushi..... [05/04 11:18] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 03 Zanen fuskar Naomi bai gushe yana murmushi ba suka jiyo sautin wata waƙa wacce yarima Naslam ne da kansa ya haramta ta saboda kalaman da ta ƙunsa na tsafi da kuma kirari zuwa ga tawagar dabar Mayu da matsafa. Jakariya Ali ne yayi saurin tsayuwa kusa da window ta inda ya fi jin sautin na fitowa.Wata makauniyar tsohuwa ya gani a durƙushe riƙe da sanda tana rera waƙar tana wani jinjina kai haɗi da murmushi. “Ina ga mun yi baƙuwa ne ,ba don haka ba ai ka haramta raira waƙar nan” jakariya Ali ya faɗa . Yarima da ya cika yayi fam kamar zai fashe ya ce “a kama ta” Da wani irin gudu kuwa jakariya Ali ya fita ,babu jimawa yasa wasu dakaru biyu suka damƙe matar tare da kai ta can ɗakin ajiyar masu laifi ya kuma bada umarnin a ƙara tsaro sosai. Shi kuwa yarima Naslam zanen ya naɗe tare da adana shi ƙarƙashin pilow .Sai a lokacin kawai ya tuna akwai sallolin da suka hau kansa waɗanda bai yi ba,tsuki ya ja a fili yana cewa “duk sharrin aljanar nan ne” Cikin ikon Allah sai ga jakariya Ali ya dawo ,shi ne ya taimaka masa zuwa banɗaki ya yi ɗahara haɗi da alwala sannan ya fito ya soma gabatar da sallolinsa. Bayan ya gama ne,mai magani Barham ya ƙara shigowa ya duba shi tare da basa maganin sha da kuma na shafawa wanda cikin hukuncin Ubangiji sai ya ƙara jin ƙarfin jikinsa. “Zuwa bayan sallar asar zan haɗa maka ruwan magani a bahon wanka sai ka shiga ka yi,amma ina so don Allah ka cire duk wani tunani akan yarinyar da ka zana ” Barham ya faɗa . Yarima Naslam ya ɗago manyan idonsa masu firgita maza ya ɗora kan Barham kafin ya ce “me ka sani game da ita?” Barham ya gyara tsayuwarsa kafin ya ce “ita ɗin ba kamar sauran mutane take ba,an haife ta bayan ɗaukar ran mahaifinta,an raine ta cikin gata da soyayya sannan kuma an damƙa mata muƙamin prophecy a ranar da mahaifiyarta ta yi gushewa wannan dalilin kaɗai ya isa ya tabbatar maka iya tunaninta ma kaɗai ba alkhairi ne ba ga Sarkin goben masarautar nan” “ Ban fahimce ka ba,kana nufin ita ɗin annoba ce ga duniya baki ɗaya?” “A'a! Ita ɗin fa shugaba ce,kamar yadda kake kare Yankinka to ita ma haka jininta ke tafarfasa in aka ce an taɓa ahalin mugaye.Tana da ƙarfin ikon maitar ido,ga kuma baƙar maita ta baki wadda da za a ce ta tofa yawunta a tekun wani yanki da ba nata ba to tabbas da ruwan sun haramta saboda tasirin ƙwayoyin cutar da ke ciki.Na yi magana da jakariya Ali ya shaida mini duk yadda komai ya faru,kuma na gaskata sarauniya Naomi ce saboda abin da na tsinta a yayin yi maka magani” “Me fa?” yarima Naslam ya tambaya. Shiru Barham ya yi kafin ya tako ya iso gun yarima,cikin muryar raɗa kamar mai jin tsoro ya ce “ta jefa maka cutar ayni wato maitar ido, wannan ne ya hana ka motsi ya juye maka tunani ka manta cewa filin daga kake har sai da magauta suka yi nasarar harbin ka” Zuciyar Naslam ce ta fara tafasa kamar za ta faɗo,yana jin ina ma zai ga Naomi a yanzu da babu shakka tabbas da hannunsa zai kashe ta.Haka ya danni zuciyarsa,ya yi ƙoƙari sosai wurin manta wa da ita sai dai kamar abin isimi lokacin yin wankansa na yi na magani idanunsa suka fara yi masa gizon yadda ta kafe shi da idonta masu matuƙar girma da kyawu don tamkar gwal haka suke sheƙi. Jakariya Ali ne ke taimaka masa har ya samu ya shiga ya kwanta cikin bahon wankan,kamar jira ake yi kuwa wani al'amari ya riske shi.Ji yayi kamar an rufe shi bai numfashi kafin ya soma jin wani yanayi wanda sam ba zai iya misalta irin abin da yake ji ba.Jikinsa ne ya ɗauki wata irin kyarma sakamakon wasu halittu da yake gani dishi-dishi waɗanda ya yi imani cewa ba Mala'iku ba ne.Can kuma ya soma wani abu kamar mafarki yana tare da Naomi yana tarayya da ita kamar sauran mafarkansa na baya. Jakariya Ali da ke gefensa tuni ya fahimci abin da ke faruwa,muryarsa na ɗan rawa ya kira sunan yarima Naslam kafin ya ce “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” nan take komai ya tsaya cak.Yarima Naslam yayi wata irin zabura haɗi da nishi bakinsa na fitar da baƙin jini.Jakariya Ali ne ya yi hanzarin goge masa jinin kafin ya taimaka masa ya yi wankan,da ya fito ma shi ne ya taimaka masa wurin saka kaya marar nauyi kafin kuma a gabatar masa da tafasasshen shayi wanda suke yi ko wane dare.Har ya yi sallolinsa bai dubi kofin shayin ba saboda abin da ke damun ransa,bayan sallar isha'i ne sarki ya shigo da kansa ya duba shi. “Gobe ka tura dakaru zuwa bakin Teku su ƙara binciko mini aljanar nan” yarima ya faɗa yana wani kawar da kai gefe. Sarki ya ce “zan so ka manta da batun yarinyar nan ka fuskanci sabon al'amarin da ke shirin tunkaro masarautarmu Naslam.Sanin kanka ne duk abin da ya cika naci to babu alkhairi a tattare da shi,ba tun yau ba kake faɗa mini kana yin mafarki da aljana to ka sani shigowa da ita masarautar nan daidai yake da ruguza duk wani ginshiƙi da ka gina tsawon shekaru” sai kuma ya yi shiru tare da zuwa ya ƙara ɗaukar wani kofi ya zuba masa shayi sannan ya saka cokali yana juya shi tare da miƙa masa ,ba don ya so ba ya karɓa ya soma sha.Sai kuma a wannan lokacin ne sarki ya ci gaba da cewa “gimbiya A'ishah na waje tana jiran fitowar ka ,zan so a ce ku daidaita kanku tun a yau don a samu a wuce wurin,na san daga lokacin da aka ɗaura maka aure shi kenan matsalarka za ta kau”. Ambaton sunan gimbiya A'ishah shi ya wanzar masa da nutsuwar zuciya,don yana mugun ƙaunarta har cikin ransa saboda ba ƙaramar gudunmawa ta bayar ba wurin haɓaka musulunci a masarautar nan ba. A hankali ya sauko daga gadon da yake,sai dai sam ya kasa jurar tsayuwar a dole ya koma ya zauna.Cikin ɗan ɗaga murya sarki ya ce “Ali?” shi kuwa kamar mai jira haka ya buɗe ƙofar ya shigo tare da ƙamewa. “Ka fito da yarima zuwa waje” ya faɗa tare da ficewa.Jakariya Ali ya ɗauko kujera ya taimaka wa yarima ya hau ya zauna sannan ya soma tura shi zuwa can falo wanda ya cika da ahali da kuma aminnan arziki.Tun daga nesa suka haɗa ido da ita,da wani mugun sauri ta yi ƙasa da kanta cikin kunya tana yin wani sihirtacen murmushi.Har aka ƙaraso da yarima ba ta ɗago kanta ba,haka aka shiga jera masa sannu yana amsa wa amma idonsa na kanta. “A'ishah zo ki gaishe da yarima mana kin wani tsaya wuri guda kina sunne kai kamar ba ke ce a yanzu ki ƙi cin abinci ba saboda shi” mahaifinta ya faɗa yana wani murmushi haka ma duk sauran mutanen wurin fuskarsu cike take annuri in aka cire mahaifiyar A'ishah ɗin da take jin kamar ta je ta kama wuyar yarima ta shaƙe shi har sai ya mutu. Gimbiya A'ishah ba ta ko motsa daga inda take ba,sai da mutanen suka dinga fita zuwa babban falo suka bar su iya su uku don duk inda yarima yake jakariyarsa Ali na tare da shi.Ɗan gefe kawai ya koma yana kallonsu,shi dai ko kaɗan bai ga dacewar yarima da ita gimbiyar ba duk da kuwa cewa ita ɗin kyakkyawa ce ta ajin ƙarshe. “Amincin Allah ya tabbata ga shugaban gobe” ta furta tana mai takowa inda yake tana ɗagowa haɗi da yi masa wani kallo mai tsayawa a rai wanda a can da babu abin da ke matuƙar girgiza yarima irin kallon nan amma yanzu sai ya ji sam bai burge shi ba,hasali ma na Naomi ya tsinta a fuskarta. Da sauri ya lumshe ido yana mai amsawa tare da cewa “shi ne ba ki zo kika duba ni ba tsawon kwana biyu ina a kwance” Murya na ɗan rawa ta ce “subahanallahi! Meke damunka yarima? Ai ban san ba ka jin daɗin jikinka ba,saboda tun ranar da ka haɗa ni da matan nan nake koya musu karatu daidai da ɗaya rana ban taɓa leƙowa waje ba” Wani numfashi ya furzar yana mai buɗe idonsa ya dube ta,iliminta yana ɗaya daga cikin abin da yake so a tattare da ita,“kar ki damu ai na samu lafiya” Shiru ta yi tana mai ɗagowa ta dube shi,ita sai yanzu ne ma ta lura cewa kan kujera ne yake.Sai kuma ƙwaƙwalwarta ta tariyo mata lokacin shigowar su shi da jakariya Ali, kasancewar kwanyarta dama can ba kullum take tafiya daidai ba shi yasa ne ba ta fahimci hakan ba. Rikicewa ta yi ta zube a gabansa tare da soma jero masa tambayoyi,wanda kuma in akwai abin da yarima ya tsana a tare da ita shi ne yawan tambayoyi da kuma wannan haukan da take yi a duk lokacin da wani abu na ƙi ya same shi. Da wani irin sauri jakariya Ali ya matso yana mai dakatar da ita,yana cewa “don Allah ki yi shiru mana” sai ta ɗago kai tana yi masa kallon tsana saboda tun tuni ta san cewa Ali bai ƙaunarta. Yana yi mata wani mugun kallo ya je ya kama kujerar da yarima ke zaune ya soma tura shi tare da mayar da shi ɗakinsa.Har Ali zai tafi sai kuma ya dakatar da shi yana mai cewa “kai ni wurin matar da aka kama ɗazu” Jakariya Ali ya ce “tana da matuƙar hatsari yarima ,da bari ka yi zuwa gobe in sha Allah ka ga lokacin ka ƙara samun ƙarfin jikinka” “Mu je dai ka kai ni ” ya sake faɗa ,ba don ya so ba ya tura shi zuwa kurkukun har suka isa ragar da aka killace ta. Tana kwance a duƙunƙune cikin wani tsohon bargo,hatta kanta a rufe yake amma hakan bai hana ta ganin yariman ba.Cikin wata irin murya ta ce “barka da zuwa yariman musulmai,ka sani killace ni a nan ba shi ne maganin matsalarka ba.Hakan ma babban kuskure ne ka tabka,ko da yake ba ka san ko ni wace ce ba” ta ƙarashe faɗa tana yin wani nishi sai ga bargon da ta rufa a shi ya yi wani irin sama tare da buɗe ta. Yarima da jakariya Ali suka kalli yadda bargon ya maƙale can sama cikin iska.Su duka biyun sun yi imani cewa tsafi ne ta yi,sai dai a yanayin da yarima yake a yanzu ba zai iya ɗaukar wani mataki ba a hannunsa sai kawai yasa jakariya Ali ya juya da shi. ★ A cikin abin da bai wuce kwana uku ba mulkina ya tsaga kowacce kusurwar yankinmu.Tuni na yi ƙaurin suna yayin da kuma gogaggin matsafa daga garuruwan ƙetare ke kawo mini tayin aure duba da yanayin shekaruna ina buƙatar abokin rayuwa musamman don gudanar da mulki yadda ya kamata sai dai ko kaɗan babu wanda ya kwanta mini a rai. Muna zaune kan kututuren icce ni da Debora ,sai kuwa ga wata baƙar mujiya ta soma shawagi haɗi da yin wani kuka. Debora ta furta kalaman tsafi tana mai buɗe tafin hannunta,sai mujiyar ta sauko tana mai sakar mata wata takarda ita kuwa jikinta har rawa yake yi wurin buɗewa.Rubutu ne reras da manyan baƙi,sai dai harufan na tsafi ne kuma ba su yi mini wuyar karantawa ba.A tare muka kalli juna,kafin na miƙe tsaye ina cewa “to a wane yanki ne aka kama ta?” “Ba ta faɗa ba a cikin wasiƙar,amma ina zaton ɗaya daga cikin garuruwan da suka kawo miki tayin aure ne ba ki amince ba” Shiru na yi ina tunani kafin kuma na karɓi takardar,ina furta tsafi rubutun ya goge sai na soma juya ido ina yin magana cikin raɗa rubutun ya soma rubuta kansa ina gamawa sai na umarci tsuntsuwar ta kai wa mahaifiyar Deborah .Ido na birkice suka koma farare tas ta haka ne nake iya hango gudun tsuntsuwar tana keta sararin samaniya tana wuce ƙauyuka tana shiga wasu garuruwa sai dai tana daf da ƙetara wata tutar wani yanki na ga wata kibiyar haske ta jefe ta ita kuma ta faɗi ƙasa ,duk kuma yadda na ƙware a tsafi ban ƙarashe ganin sauran abin da ke faruwa ba...... [06/04 08:01] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 04 Hankalin Debora sosai ya tashi saboda ta lura da abin da ya faru.Ko kaɗan ban ga laifinta ba saboda na san yadda mutum ke ji in mahaifiyarsa ba ta tare da shi, wannan yasa na damƙo hannunta tare da yin wani irin kalar tsafi na gushe mata da damuwar tare da saka mata nutsuwa na danne ƙuncin zuciyarta. Idonta da suka kaɗa suka yi ja na duba karin na ce “ki sani cewa babu wani sarki da zai gagare ni,ki sa a ranki ummarka tuni ta kuɓuta” Muryarta na fitar da wani irin amo take cewa “ya ke shugabata in ba ki manta ba irin haka ne mahaifina ya tarar da wa'adinsa,silar zaƙulo bincike domin rubuta tarihi ya haɗu da wasu mabiya addini mabanbanta suka kashe shi a ƙarshe sai mahaifiyata ce ta maye gurbinsa domin ci gaba da rubuta littafin kudin binciken duniyar ruhaniya” tana kawowa nan da zancenta sai ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba da cewa “ina jin tsoron kar a ce ita ma Umma nata ajalin ne ya zo” Kai na girgiza mata ina mai cewa “muddin ina raye hakan ba zai faru ba” Rungume ni ta yi tana sauke wata irin ajiyar zuciya,yayin da ni kuma na shiga tunanin hanyar da zan bi na ƙwato Umma ɗin saboda a duniyar nan a halin yanzu banda wani masoyi da na fi so da ƙauna sama da Debora.Cikin hikima na mayar da ita cikin gida gabanin ni kuma na fita zuwa can cikin baƙin jejin garinmu mai cike da aljanai da fatalwa. Cikin tafiyar rauni ta masu larurar ƙusumbi nake tafiya ana take mini baya,ko kaɗan ban san su wane ne ke take sawuna ba kuma ban jin tsoro ko fargaba wani abu.A haka na isa bakin wata iraciyar kuka mai zubin halittar mutum don da baki da hanci gare ta.Ina gama daidaita tsayuwata sai kuwa bisashin ganye suka fara zubowa a kaina kamar ana ruwa kafin ɗanye ƙwaya ɗaya ya faɗo a gabana.Ɗaukarsa na yi tare da tofa yawuna a kai,sai na soma juya ido babu jimawa yawun suka rikiɗa zuwa rubutu.Sai a lokacin na miƙawa itaciyar ganyen mai ɗauke da bayanin abin da ya kawo ni nan ɗin.Tafin hannuna na ji ya cika da wasu duwatsu,ina dubawa sai na ga suna sheƙi akan kowanne dutse an rubuta karlis .Ban yi jinkiri ba na nufi ɗaya daga cikin magudanar ruwa na je na yi tsaye ina kallon yadda ruwan ke a kwance sun nutsu ko motsi ba su yi.Dutse ɗaya na cilla ina sauraren yadda ƙararsa ya ratsa ruwan tare da soma yin gudu har zuwa inda nake son ya isa. Ba a ɗauki wani lokaci ba wata iska mai sanyi ta soma kaɗawa tana fitar da wani ƙanshi irin na gawa.Can sai ga Maa ta ratso ruwa ta fito,fuskarta ta yi wani fari fat kana ganinta ka ga matatta ga kuma fararen kaya a jikinta. Cike da soyayya na je da gudu na rungume ta,sai dai kamar na jimƙi iskan gas haka na ji babu wata alamar gangar jiki.Da sauri na ja da baya ina kallonta tana wani fitar da murmushi,wani irin tausayin kaina na ji wanda ko ranar mutuwarta ban ji shi ba. “Me kike buƙata Nao?” don haka take kirana a duk lokacin da take shauƙi ko kuma take son isar mini ƙaunar da zuciyarta ke ƙumshe da ita. “Maa shi kenan ba zan ƙara jin taushin gangar jikinki ba?” ita ce tambayar da na yi mata madadin na sanar da ita matsalar da ta kawo ni. Ta ce “Naomi a zangon da nake na fita daga sawun duniyar bil'adama na koma cikin duniyar matattu,ki kira ni da ruhi kai tsaye” Kallonta na yi,tabbas ita ɗin ruhi ce kamar yadda ta faɗa ɗin.Na kai hannu na shafi kumatuna da nake jin wani damshi,wanda na yi imanin cewa ruwan hawaye ne .Murya na ɗan rawa na ce “mahaifiyar Deborah ta faɗa hannun mugaye shi ne nake son sanin ta ya zan ceto ta?” “Babu buƙatar yin haka,saboda ita ɗin ba kanwar lasa ba ce.Za ta iya fitar da kanta kar ki wani damu kanki” Maa ta faɗa . Na ce “amma kuma ita ce da kanta ta aiko da takarda domin sanar da mu” “Ta yi haka ne domin ku ci gaba da rubuta littafin bayanai ba wai don kawo mata agaji ba.Ki sanar da Deborah cewa lokaci ya yi da ita ma za ta ɗauki muƙaminta na rubuta tarihi kamar yadda mahaifinta ya karɓa gun mahaifinsa,ita kuma mahaifiyarta ta karɓa daga mahaifinta,yanzu kuma ƙaddarar littafin tarihi ta dawo hannunta” Maa na gama furta haka sai ta soma nitsewa cikin ruwa haskenta na tarwatse wa haɗi da disashewa.A gaban idona ta ɓata,na lumshe idona ina mai furta kalaman tsafi tare da buɗe su kuma a nan na tsinci kaina a ɗakina. Deborah na kwance amma ba bacci take yi na.Kallonta na yi kafin a takaice na sanar da ita abin da Maa ta shaida mini,da wani irin sauri ta miƙe ta zauna tana kallona can kuma ta soma furzo da wani irin furuci sai na ji tsafin da take yi ba irin nawa ba ne yana da banbanci kamar yadda Hausar wani gari ba ɗaya take da ta wani garin ba. Babu jimawa sai muka soma jiyo kukan jemage yana wani tsala shi kamar zai fasa gidan,a tare muka fita nan muka yi gamdakatar da wani baƙin jemage baƙi ƙirin da shi ga kuma wani irin girma na ban mamaki. Kan ƙafafunsa ya sauka bayan ya cillo wani tsohon littafi ya dira a tafukan hannun Deborah. Kallo ɗaya na yi masa na fahimci cewa shi ne wanda aka wakilta domin tsare littafin ya basa kariya.A hankali ya soma yin tsalle har ya isa gun Deborah,babban farcenta na ƙafar hagu ya kama ya fasa shi tare da soma shan jininta irin sosai ɗin nan don har sai da ta soma yin wani irin haske irin na rashin jini amma ko kaɗan ban yi yunƙurin tsayar da shi ba har sai da ya gama sha sannan ya tashi sama,sai dai bai yi wani nisa ba ya ɓace ɓat. Sai a lokacin na je na kama ta na ja ta zuwa ciki na zaunar da ita,magani na ɗauko na soma rufe mata yatsan da shi wanda har yanzu yake ɗigar da jini. “Ki kwanta ki huta na san kin gaji” na furta. “Ki soma karanta littafin kafin ni na karanta miki ” ta furta tare da miƙo mini,kamar ba zan karɓa ba sai kuma na kai hannu na karɓi littafin na ajiye a gefe.Ido ta lumshe ta soma yin bacci mai kama da mutuwa,wanda na yi imani cewa a cikinsa ne za a miƙa mata wasu asirai da kuma power kariyar kai da kuma ta abin da aka damƙa mata amanarsa. A cikin wannan daren ne na soma karanta littafin tarihi wanda ya ƙunshi rayuwar jarumai da kuma irin gwagwarmayar da suka yi fama a kai.Na samu sirrika dayawa,na yaƙi da kuma yadda ake sarrafa maita ta sigogi daban-daban. Wannan littafin ya ƙara saka mawa zuciyata cewa duk inda babu magic to lalle babu rayuwa mai inganci, Magic shi ne komai na duniya a cikinsa ne za ka samu ƴanci da kuma gata.Rufe shi na yi tare da raɓawa gefen Debora na kwanta,ina lumshe idona na soma jin wani irin motsi a cikin kunnena tamkar ƙwaro na tafiya.Ƙara nutsuwa na yi sai na soma jin tamkar ana yi mini magana ne,amma ta ina? Ban sani ba.Ji na yi ana danne ni ana saukar mini nauyi,na furzar da huci mai zafi jin wasu kalmomi daga wata murya da ban san mamallakinta ba. “ A duk inda kike a faɗin duniyar nan sai na nemo ki,ni ne nan zan kashe ki da hannuna ƙaramar matsafiya muguwa mai idanun maciji” muryar namiji ce amma ban san wane ne ba, sannan ban fahimci abin da yake nufi ba har ya ƙara yin wani furucin “ina ma ace annabi sulaiman bai yi wafati ba,da na roƙi alfarmarsa ya tura rundunar aljanu su gana miki azabar da ta fi ƙarfin tsafinki ” Saurin buɗe idona na yi,ina mai tambayar kaina “wane ne kuma Annabi Sulaiman?” sai dai banda amsar wannan tambayar,in akwai wanda zai faɗa mini ita to bai wuce Deborah ba wannan yasa na kasa haƙuri na kai hannu na shafi fuskarta.Ta buɗe idonta tarau a kaina,sai dai babu ɗigon baƙi a cikinsu da alamu har yanzu ba ta dawo daga balaguron ruhi ba. “Wane ne Annabi Sulaiman?” na tambaye ta,idanunta ne suka dawo normal nan take ta tashi zaune sannan ta bani amsa da cewa “ ya kasance ɗa ga Annabi Dawuda shi ma kuma annabin Ubangijin Ka'aba ne.Yana da matuƙar power don a tarihin annabawa shi ne kaɗai ya mulki mutane da kuma aljanai,sannan kuma yana iya yin magana da dabbobi da kuma jarirai waɗanda bakinsu bai buɗe ba.Ya yi mulki cikin hikima da adalci ga al'ummarsa” Zuciyata ce na ji tana wani irin bugawa na jin bayanin da Deborah ta yi mini.Kamar mai tsoron sake jin wata buwayar na ce “amma me Annabin ke nufi?” “Mutum mai isar da wahayi daga Ubangijin Ka'aba zuwa ga al'umma ” ta bani amsa kai tsaye.Ban ce mata komai ba sai tashi da na yi na fito waje ina kallon taurari ina kuma juya kalamanta. Ƙofar gidan na ji ana bugawa,na je na buɗe sai na ga gungun matsafan garin ne da alamu sun fito maitar dare ne suka biyo. “Ranki shi daɗe mun samu baƙuwar fuska a yankin nan,wani mutum ne maharbi mun tsince shi a wata gona yana bacci.Mun ɗaure shi da duk wata igiyar tsafi amma ta ƙi yin tasiri a kansa saboda girman tsafinsa wannan dalilin ne yasa muka zo zuwa gare ki” ɗaya daga cikinsu ya faɗa . Raina a mugun ɓace na ce “me yasa ba ku kashe shi ba?” Kallon juna suka yi kafin wani kuma daga cikinsu ya ce

Chapter 2 of 10