Share this page
kwashe-kwashe ka rasa wacce za ka auro sai wadda ta gama yawon duniya ta tsiyayar da duk ƙwayaƙwayin haihuwarta a titi.To ban yarda ban lamunce wannan tinkiyar ta zauna a gidan nan ba” Mamuh ke faɗa cikin masifa ita kuwa Ma'idah tuni ta soma kuka musamman irin abin ban tsoron da take hangowa a fuskar Mamuh. Abbas ya sunne kai ya ce “ a dai yi haƙuri Mamuh dukkan bawa bai wuce jarabawa,Ma'idah ita yarinya ce ba ta san komai ba” “Wallahi sai ta bar gidan nan” Mamuh ta faɗa cikin ƙaraji, Sakeenatu kuwa banda kuka babu abin da take yi . Hannun Ma'idah ta kama da niyyar jawo ta,ita kuwa baiwar Allah cike da tsoro ta ɗauki cokali mai yatsu ta caka ma Mamuh ita a ido da zumar ceton kanta ga dodo. Wani uban ihu Mamuh ta yi tana cewa “wayyo idona! Ƴar daba ta kashe ni” jikin Abbas na rawa ya je ya kamo Mamuh wacce tuni idon ya soma fitar da jini,hankali tashe ya soma goge jinin wani na zubowa a doli ya kama ta zuwa asibiti. Bayan tafiyarsu ne Nafisa ta soma tofa ma Ma'idah addu'o'i saboda yadda take wani irin kuka tana firgita,cikin kuka Sakeenatu ta ce “ Nafisa ki ɗauke ta ku wuce gida don Allah” “Ke kuma a nan za ki zauna? ” “To ina zan je Nafisa? Haƙuri zan yi dama aure ya gaji haka sanin kan ki ne a can gidan ba wani jituwa muke ba ni da Mama ta ɗauki ƙiyayyar ɗan farin ta ɗora min” “To amma dai ki kula da kan ki,in kin ga abin ya yi yawa kawai ki tawo gida” Kuɗi ta basu sannan suka bar gidan,ita kuma ta ɗauki waya ta kira Abbas don jin asibitin da suke shi da Mamuh yana shaida mata ita ma ta fita ta je.Tuni Mamuhn ma ta yi bacci an naɗe idon nata da bandeji ga kuma ƙarin ruwa an saka mata. Jikinta a sanyayye ta ce “ ka yi haƙuri” Abbas ya kamo hannunta ya ce “ dama haka Allah ya tsara,ina Ma'idah?” “Nafisa ta koma da ita can gida” “Don me? Zan rarrashi Mamuh na san za ta amince ta zauna da mu” Ta sakar masa murmushi ta ce “ na gode sosai da kawaicinka gare ni” wani kallo yake aika mata yana mirza tafin hannunta,da ido ɗayan mai lafiya Mamuh ke kallonsu tana jin wani irin haushi da takaici. “Mine ne haka? A asibiti fa muke ka bari har mu koma gida” Sakeenatu ta faɗa tana janye jikinta daga nasa ganin abin zai wuce gona da iri. “Mu je gidan to tun da kin ga Mamuh ta samu bacci ,sai mu dawo daga baya” Abbas ya faɗa yana langwaɓar da kai saboda ba ƙaramar kewar ta yayi ba. “To ai na farka” cewar Mamuh tana mai tashi zaune haɗi da hararen Sakeenatu,da ɗan sauri ya miƙe yana tabayarta jiki.“ Ka kira likita ya cire min ƙarin ruwan nan sai mu wuce gidan tun da uwarka ba za ta barin ka cikin salama ba” cewar Mamuh a zafafe,Abbas ya fita don kiran likita. “Duk tsiyarki dai ba za ki iya canza ma tuwo suna ba,Abbasi ɗana ne ba naki ba don haka ni ke da iko da shi ba ke ba.Kuma wannan shegiyar taki sai ta san ni ta caka da cokali sai na shayar da ke mamaki” Da wani mugun sauri Sakeenatu ta je gaban Mamuh ta tsuguna ta ce “ don girman Allah Mamuh ki yi haƙuri , Ma'idah yarinya ce ba ta da wayo ko me za ki yi to ki yi min amma kar ki taɓa ƴata” ta ƙarashe maganar hawaye na zubo mata saboda zuwa yanzu ta yarda Mamuh muguwa ce. Kafin ta kai ga bata amsa Abbas ya shigo shi da likita,ya ce “ sai kin yi kwana uku sannan za mu sallamar ki” “To ka sanar da uwarmu wacce ta matsa mu je gida” Mamuh ta faɗa a zuciye tana hararen Sakeenatu. Likitan yayi murmushi ya ce “ yanzu yadda za a yi sai ka nemo wacce za ta zauna da Mama,amma gaskiya ba za mu sallame ta ba yau” sai yayi wa Mamuh allurar bacci,duk yadda masifa ke cin ta haka ta haƙura saboda ƙarfin allurar. Shi kuwa Abbas Gwaggonsa ya kira wacce ke nan Damagaram ita ke bi ma Mamuh,babu jimawa kuwa ta zo .Ya ja matarsa zuwa gida,cike da zallar soyayya suka gamsar da junansu. SAFEENATU Tun bayan da kowa ya watse aka bar su ita da Gwaggo Habibah sai ta nutsu sosai kafin ta ce “ Gwoggo ni kam ɗazu wani abin ban mamaki ya faru,maciji na gani ya naɗe Baby girl ɗin nan ina yin ihu ya ɓace kamar aljani ” Gwaggo Habibah ta yi murmushi ta ce “ kar ki wani ji tsoro,sannan ina so ki kwantar da hankalinki duk wani abu da za ki gani ki yi shiru da bakinki.Duk kusan ƴan biyu suna da wannan baiwar,to ke macen ce ke da shi don haka ki shirya ganin abubuwa iri-iri wasu na tsoro wasu kuma na almara” Safeenat ta ja wani numfashi kafin ta ce “ to Allah cire min tsoron” ba ta ida rufe bakinta ba hasken ɗakin ya ɗauke duhu ya turnuƙe shi kai ka ce dare ya tsala.Duk tsit suka yi babu wanda ya ce wani abu,sai kukan jaririyar da ya soma tashi sannu a hankali tsawon minti biyu kafin ta yi shiru.Hasken ɗakin na dawowa Safeenatu da Gwoggo Habibah suka yi ƴar rige-rigen ɗaukar babyn duk suka yi tsaye suna kallon yadda goshinta ke fitar da wani haske yana ƙyalli a gaban idonsu ya ɗauke sai ga shatun haƙoran maciji ya bayyana raɗau .Safeenat ta kai hannu ta shafi wurin sai kuma ya ɓace,ta ja ajiyar zuciya tana mai ɗaukar jaririyar ta soma shayar da ita. Daddy ya yi sallama ya shigo,duk suka gaishe shi kafin a basa babys ɗin ya gani.Sosai yayi musu addu'a sannan ya fita,haka suka ci gaba da yin hirarsu har dare ya tsala.Duk sun yi shirin bacci za su kwanta amma ita Baby kamar ɗiyar aljanu ta ƙi baccin sai ma wani kuka-kuka da take yi. “Safeenat ki bata abincinta mana” Gwaggo Habibah ta faɗa tana shirin tashi ta kunna wuta. “Ina ta ƙoƙarin bata ta ƙi karɓa” cewar Safeenar. Kusa da ita ta zauna tana shirin ɗaukar babyn sai ta lura da yadda hannunta na hagu ke fitar da wani zane mai hasken wuta kamar ta murhu.Wani irin murmushi ne ya suɓuce wa Gwaggo Habibah ba tare da ta shirya ba cike da murna ta jawo hannun jaririyar ta riƙe sannu a hankali har zanen ya fito raɗam letter M ta fito sai a lokacin kuma jaririyar ta yi shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa. A ɗan ruɗe Safeenatu ta ce “Gwaggo mine ne kuma wannan?” Sam Gwoggo Habibah ba ta bata amsa ba sai safar hannu da ta je ta binciko cikin kayansu ta saka wa hannun mai zane.“Daga yau kar ki ƙara barin hannunta a buɗe ki dinga saka mata safar hannu ” “Gwaggo ina tambayar ki mine ne ba ki bani amsa ba” “Alama ce ta prophétie/prophecy,da yawan ƴan baiwa tana soma aiki ne in sun kai shekara sha takwas amma ke yarinyarki tun farkon dirowar ta duniya tata baiwar ta fara aiki.Ta ceci ɗan uwan tawaicinta sannan kuma ta ceci ƙawarki Sakeenatu ” Ba don ta fahimci zancen da kyau ba ta ce” mi ya samu Keenat ɗin?” “An yi mata ajiya cikin ruhinta ta yadda esprit zai samu damar yin yanda ya so da gangar jikinta har ya cutar da ita” “Ya aka yi kika sani to?” “Safeenatu yi bacci in lokacin fahimtarki yayi babu buƙatar ki yi tambaya” Da wannan duk suka yi bacci, Safeenatu na tsaka da yin mafarki akan goben ƴarta Gwaggo Habibah ta tashe ta daga bacci.“Ruwan wankan ki na can toilet ta tsakar gida,ki je yi wankan sabulu kafin na zo na gasa miki jikinki da towel” Ta yi miƙa ta tashi a gajiye saboda kwana dare ta yi tana shayarwa,sai da ta ɗauki wani zane da hijabi sannan ta fita ta bar Gwaggo Habibah za ta yi wa Twins wanka. Sakeenatu na fitowa suka yi kiciɓis da Gwoggo Hajara ta gaishe ta sannan ta wuce toilet.Ita kuwa tsabar mugunta yasa ta koma ɗakinta ta yo shirin mugunta yau ma siffar tsakaka ta ɗauka ta yi tsinke can toilet inda Safeenatu ke wanka tun tuni.Da ga can saman katanga Gwaggo Hajara ke ƙarewa surar Safeenat kallo,cikin salon mugunta ta mayar da harshenta dogo sannan ta zuro shi tun daga can sama har ƙasa yana taɓa tile. Safeenatu ta yi wani ihu wanda bai sauka ko ina ba sai cikin kunnen ƴarta jaririya,kwacaaaa Gwaggo Hajara ta faɗo cikin ƙatuwar robar tafasasshin ruwan zafi....... Ga masu son complete na book ɗin nan akwai shi 800 ne via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank . DM +22795045822 [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 8 Da wani mugun sauri Safeenatu ta yi tsalle ta koma jikin ƙofa tana kyarma ,idonta ƙur cikin robar wacce tsakakar ke ta ƙoƙarin fitowa daga ruwan .Ganin ta soma yin girma sosai yasa Safeenatu ta buɗe sakatar toilet ɗin zane a hannu ta fito Allah yayi sa'a babu kowa a tsakar gidan,dakyar ta yi ɗaurin ƙirji kafin ta nufi can ciki da gudu. “Ke lafiyar ki?” Gwaggo Habibah ta yi tambayar . Feenat ta dafe gefen zuciyarta da yake mugun bugawa ta ce “ tsaka...ka ce ta faɗa cikin ruwan da nake wanka” “Shi ne kike wannan haƙin? Kai Allah ya shirya min ke ban san lokacin da za ki girma ba” “Gwaggo ba normal tsakaka da kika sani ba ce, wannan ƙatuwa ce inda kin ga yadda halshenta ke da tsayi ya fi pampo fa” Shiru Gwaggo Habibah ta yi tana kallon Baby girl don kuwa a gaban idonta da tana yi mata wanka wani mugun haske ya fita goshinta tamkar an jefa kibiya. “Allah ni dai ba zan sake shiga toilet ɗin waje ba ƙila ma aljani ne” muryar Safeenatu ta katse mata ɗan guntun tunaninta. “Bari na je na gani ” cewar Gwoggo Habibah kafin ta miƙe ta fita zuwa Toilet ɗin tsakar gida,tun kafin ta ƙarasa ciki take jin nishin wahala . Ido huɗu suka yi da Gwaggo Hajara wacce zuwa yanzu tuni ta galabaita ta yi wani tsamo-tsamo cikin ruwan zafin ta kasa fita . Gwaggo Habibah ta yi wani murmushi tana kallon yadda ruwan suka yi baƙi tsabar yadda muguntar da ta shiryo ma Safeenatu ba ƙarama ba ce. “Ƙarshen alawa ƙasa! Yanzu wa gari ya waya? Shi dama ramen mugunta an ce ka gina gajere in kuma ka gina dogo kai za ka faɗa .Ai wallahi ba zan taimaka miki ba sai dai ki dawwama a ruwan zafin nan,in kuma kin ga na taɓa robar nan to wallahi cikin masai ne zan zubar da ku ke da ruwan” Gwaggo Habibah ta faɗa tana wani murmushin jin daɗi. Kamar daga sama tsakaka ta soma magana wacce ta kasance Gwaggo Hajara ,“ ki taimaka min Habibah na yi miki alƙawarin daga yau na zubar da makaman yaƙi” “Kar ma ki zubar ki yi ta riƙon su har sai Mahadi ya bayyana,ba dai maita ita ce jarinki ba? Ki ci gaba da yi wata rana mutuwarki za ki ci” tana gama faɗar haka ta fito daga toilet ɗin,sai kuma ta tuna duk wanda ya mutu a ruwa yayi shahada da sauri ta koma ba tare da ta ce komai ba ta ɗauko robar ta fito da ita tsakar gida tare da juye ruwan ga ƙasa. Tamkar acid haka turɓayar ta soma yin bori tana fitar da kumfa tsabar bala'in da ke tattare da ruwan,a kunyace Gwoggo Hajara tsakaka ta soma jan ciki ta nufi hanyar ɗaki. Ita kuwa Gwaggo Habibah ji ta yi kamar ta sa ƙafa ta laɓe shegiya kowa ya huta.Tana komawa ciki ta cewa Safeenatu “Ki shiga toilet to kafin na juye ruwan yi miki wankan” sai kuma ta fita ta ciko ƙaton bokiti da ruwan zafi,da ɗan ƙaramin towel ta soma yi wa Safeenatu wankan jego ita kuma tana ihu kamar wata ƙaramar yarinya. Macijin jiya ne ya sake bayyana a jikin macen yana wani naɗe jikinta,ita kuma ta buɗe ido taram tana kallonsa kamar mai wayo.Tsawon lokaci ya ɗauka tare da ita yana yi mata wasa kafin ɓace jin motsin su Safeenatu za su fito.Gefen gado ta zauna ta soma shayar da yaran kafin ta kimtsa cikin riga da zane,sai da Gwaggo Habibah ta gama wanka ita ma ta fito ta shirya sannan ta je ta kawo masu abinci suka ci daga nan suka wuce asibiti bayan sun karɓi kuɗi wurin Daddy.Lafiyarta da ta babys aka duba kafin su dawo gida,tuni kuma ƴan Barka suka fara zuwa in waɗannan sun fita wasu sai su shigo. SAKEENATU Tana rungume jikin Abbas ta ce “ Yau tana ɗaya daga cikin ranakun ovulation ɗina,yau na gama period ” cikin tsokana ya ce “ period ɗin ɗaya rana ” ta ja hancinsa ta ce “ eh na dai ji,inda ina jimawa kafin ta ɗauke ai da yanzu ba ka kasance da ni ba don jiya ne na gan ta” Ya gyara mata kwanciya kan ƙirjin nasa yana mai cewa “ Keent don Allah ki dinga bin Mamuh a hankali kin san ta tsufa,ban so kina yin abin da zai ɓata ranta ki guji ɓata mata don farincikina.Ina yi miki wani mugun so ne wanda na san ke ko rabin shi ba ki yi min” “To in sha Allah na yi ma alƙawari zan kiyaye,ai Ma'idar ma an tafi da ita” “A'a za ta dawo,sanin kan ki ne yadda nake mugun sonta ba zan iya yin nesa da ita ba” Wani daɗi ne ya luluɓe zuciyar Sakeenatu,ita ce shaida kan son da yake yi wa ƴarta duk da ta fito ba ta hanyar aure ba.Za ta iya cewa halarcin bai nuna mata ƙyama ba ne ya ɗunguza ta ga aurensa,soyayyarsa ma ba ta jima da samun gurbi a zuciyarta ba. “Ina son ki Keenat!” furucinsa ya katse mata tunani,ta yi murmushi mai ɗan sauti ta ce “ na gode” “Ke ba za ki faɗa kina sona ba? Keenat sai yaushe zan ji furicin so daga bakinki?” Ta laƙace masa hanci ta ce “ sai ranar da na haifo ma kyakkyawan Prince mai kama da kai” sai kuma ta miƙe ta je ta shiga toilet,shower ta sakarwa kanta tana tunanin saurayinta mahaifin Ma'idah.Ruwan hawayenta haɗi da na pampo suka haɗu wuri ɗaya suna zuba.Daga bayanta ta ji an rungume ta,da sauri ta juyo suna fuskantar juna kallo guda yayi mata ya hango damuwa a shimfiɗe a ƙwayar idonta.Zuciyarsa kuma ta basa ta yi kuka,bai tsaya tambayar ta ba ya ɗora bakinsa kan nata a wannan rana a kuma daidai lokacin nan Abbas ya shayar da ita zumar ƙauna mai haɗe da yayafin kalaman soyayya masu nuni da sadaukarwa.Ba tare da ta shirya ba ta ce “ I love You Abbas!” numfashinsa ne ya kusan tsaya wa tsabar murna da farin ciki,kamar wani ƙaramin yaro ya soma yi mata kuka saboda kawai ta ce tana sonsa. Shi yayi musu wanka ya shirya su,a ranar a gida ya ja su sallah har ta isha'i .Bayan sun salamce sun yi dogayen addu'o'i ya dube ta da kyau ya ce “ Keenat fatan bayan tafiyata duk salloli kin yi su kan lokaci kuma kin tsare su?” Da sauri ta sunne kai ba tare da ta basa amsa ba,yatsun ƙafarta ya soma ja mata tare da soma yi mata nasihar da ya saba game da mai wasa da sallah a ƙarshe yake cewa “ in kuma na ga kin ƙi yi zan kawo miki ƙanwa ustaziya” a shagwaɓe ta faɗa jikinsa ta ce “ to ai ina yi ko” “Kina yi ko za ki dinga yi?” “Duka biyun! Ba za ka koma asibiti ba?” “Tare za mu koma tashi ki shirya” da “ to” ta amsa kafin ta canza kaya suka fito,sai da ya tsaya ya saya musu fruits sannan suka isa asibitin.Da sallama suka shiga ɗakin Gwaggo Rahamu ce ta amsa yayin da Mamuh ta juya musu baya tana jin wani irin baƙin ciki ya turnuƙe ta saboda a yadda ta gansu cikin farin ciki suna nishaɗi ta san sun keɓe da junansu.Abbas ya ƙarasa yana mai cewa “ Mamuh ya jikin naki?” “Ka damu da ni ne ka sa ƙafa ka yi tafiyar ka? Wato Abbasi matarka ta fi ni ko?” ta faɗa cike da masifa tana juyowa. “Ki yi haƙuri Mamuh Allah dai ya baki lafiya ” ya faɗa kansa ƙasa. Tsabar fitina ta Mamuh sai cewa ta yi “ ina wakena?” Abbas ya ɗago da sauri yana kallon ta yana mai cewa “ wane irin wake kuma Mamuh yanzu da daren nan? Ga ayaba nan da lemu da apple na sayo ” “Na yi da kai na ce ka sayo? Ita waccar abar ai ta san wake nake ci mi yasa ba ta dafo ba?” “Yi haƙuri Mamuh gobe sai a daf....” bai rufe baki ba Mamuh ta saka kuka yana cewa “ shinenan tun da mata ta fi uwa” Da mugun sauri Sakeenatu ta ce “ bari na koma gida sai na dafo mata” Abbas ya ce “ to ki yi sauri” ta yi tunanin shi zai kai ta amma sai kuɗin ɗan sawu ya bata,tana zaune tana hawaye har suka iso gida ta biya shi kuɗin kafin ta wuce ciki. A gaggauce ta soma aikin tana mita “ an yi tsohuwa kamar mayya kullum wake yanzu nan in ban wanke shi ba sai ta sani mtsww ” ta ja tsuki tana dirje waken amma jin ita ma an ja mata tsuki yasa ta zabura tana dube-dube sai dai babu kowa.Watsar da tunanin ta yi ta ci gaba da aikinta wani tsukin ta kuma ji sannan ana magana ƙus-ƙus,gabanta ya faɗi jin tamkar ana tafiya cikin falo.Tana shirin fitowa aka ɗauke wuta,lalubo ta soma yi cikin duhu ko Allah yasa ta ɗauko wayarta ta kuwa yi sa'a ta samu jakarta hannunta har rawa yake ta zuge zip ta ciro wayar sai ta ga saura ƙiris batirin ya mutu alhalin a cike ta bar ta.Tana ƙoƙarin ganin ta kunna fitilar ta ji tamkar saukar huci kusa da ita,ta wani juyo da sauri ta inda take jin abin tare da haska hasken screen babu kowa sai ƙafafuwan ƙofato da ta yi arba da su babu kuma gangar jiki....... Domin samun complet book ɗin nan 800 ne via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [13/04 10:28] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 9 Babu shiri Sakeenatu ta saki wayar ta arta a guje,sai dai ta nemi ƙofar fita ta rasa saboda mugun duhun da ya mamaye gidan baki ɗaya.Cikin ƙanƙanan lokaci duk ta firgice,dakyar ta iya samu ta fito tsakar gida da lalabe zuciyarta sai ƙara tsananta gudu Waige-waige ta fara sai ta ga ashe kaf unguwar ne babu wuta,ba ta gama daidaita numfashinta ba wata baƙar mage baƙa ƙirin ta soma yin kuka miyau!miyau! Kukanta duk ya cika gidan. Ta ɗaga kai dakyar ta dubi inda sautin kukan ke fitowa,ido huɗu suka yi da magen wacce hasken idonta yake kamar na lantarki sai canza kaza suke.A hankali ta sauko daga katangar ta soma nufo inda Sakeenatu ke tsaye da gajiyayun ƙafafunta,Allah ya gani ba ta wani ba wai karatun addini muhimmanci ba dukkan lokacinta da hazaƙarta ta zuba su ne a harakar boko wannan ya sa ba ta iya wasu addu'o'i ba .A halin yanzu da take tsaye ta yarda kuma ta aminta rayuwarta na cikin haɗari,tabbas ta san wannan magen ba normal ba ce muguwa ce cutar da ita za ta yi. Ta na dab da ta kawo kusa da ita ta samu bakinta na furta “ la haula wala ƙuwata illa billah!!!” ƙiiii magen ta wani ci burki tana mai canza salon kuka zuwa na jarirai amma sam Sakeenatu ba ta yi gigin yin shiru da bakinta ba sai ma ƙaimi da ta fara wurin maimaita addu'ar.A gaban idonta magen ta soma mayar da idonta kamar na mutane kafin ta ruga a guje ta yi tsalle ɗaya ta haye katanga,daidai nan kuma aka maido wuta yaran unguwa suka hau ihun murna.Sakeenatu ta ja ajiyar zuciya tana mai yin hamdala ga Ubangiji,bakinta bai gushe ba yana ta furta lahaula wala ƙuwata illa billah a haka ta koma can ciki.Gas ɗin ta kashe saboda muguwar gajiya da ta saukar mata wacce ba ta san dalili ba,wayarta ta ɗauka Allah yayi sa'a babu abin da ya same ta abun mamaki kuma yanzu cajin wayar a cike yake saɓnin ɗazu da aka nuna mata ta kusa mutuwa. Lambar Nafisa ta kira,tana ɗauka babu wani tsaya wa gaisuwa ta ce “ Nafi ki turo min karatun nan da kike saurare don Allah duk dare” “Anty Sakeena lafiyar ki kuwa?” “Ki turo min karatun dai don Allah ina son saurare ” “Ok to bari na hauda data yanzu zan turo miki” “Yawwa ina jira” ta faɗa tare da kashe kiran,ita ma datar ta kunna babu jimawa kuwa karatun ya shigo suratul Baƙara ce ta turo mata sai Yasin .Tamkar abun tsiya network ɗin ya ɗauke ɗif ko ɗaya babu wanda ya buɗe,juyin duniya ta yi amma sun ƙi buɗewa har wayar ta kashe ta kunna amma network ɗin ya ƙi yi.Cike da damuwa ta sake kiran wayar ƙanwarta,tana ɗauka sai ta rasa abin da za ta ce mata kawai ta fashe da kuka.Daga can ɓangaren Nafisa ta ce “ subahanallah! Anty Sakeena don Allah mike faruwa? Mike damun ki?” Cikin muryar kuka take cewa “ Nafisa tsoro nake ji! A tsorace nake ji nake kamar ba ni ɗaya ba ce cikin gidan nan tamkar ina ....inaaa” ta kasa ida maganar saboda motsin da ta gani ana yi can cikin labule wanda ta tabbata kuma ba ɓera ne ba saboda girman halittar.Ihu ta fasa ganin ƙatuwar gafiya ta faɗo timmm da ƙasa,yayin da kuma wata ta biyu ita ma ta sake fitowa a guje ya kama waccan wacce ta faɗo a gaban idonta suka soma faɗa suna cizon junansu.Babu shiri Sakeenatu ta haye ɗaram kan bed ta na kuka,Nafisa na jin haka ta ziri hijabi ta fito ko Mamarsu ba ta sanar ma ba ta fito ta samu ɗan sahu.Allah yayi sa'a ba wani nisa ne sosai a tsakaninsu ba,da gudu ta shigo gidan tana ambaton sunan Allah daidai nan gafiyoyin suka yi ɓatan dabo hatta. Nafisa ta je ta rungume ƴar uwarta wacce da ace tana da cutar asuma da tuni numfashinta ya fita,“ yi shiru don Allah ya isa yi min bayanin mike faruwa? Ina shi Abbas ɗin?” “Yana asibiti wurin Mamuh,na dawo na dafa mata wake da shinkafa ne shi ne ake ta firgita ni” nan ta kwashe duk abin da ya faru ta shaida wa ƙanwarta. Nafisa ta ja dogon numfashi bayan ta saurare ta,sannan ta ce “ wannan duk sharrin miyagu ne shi yasa a kullum ake son bawa ya keɓe wani lokaci don nemawa kansa kariyar ruhi da gangar jiki ba wai gyaran duniyarka ba kawai.Ni wallahi na fara zargin Mamuh ɗin nan,kina dai ganin yadda Ma'idah ta caka mata cokali da dukkan alamu ta hango abin da idanunmu basu gani.In ba masifa ba cikin daren nan za ki dafa mata wake kamar mayya,ke ƙila ma ita ce.Tashi mu je ki yi alwala ai zama bai gan ki ba tun da kin ji kin gani aure a inda ba a ƙaunar ki” Da taimakon Nafisa ta yo alwala dama ita Nafisar kusan kowanne lokaci tana da alwala mace ce mai riƙo da addini ba ta da sake,hasali ma malamar makaranta ce a wata islamiyya. Karatun Alkur'ani ta soma koya wa Sakeenatu kamar wata ƴar yarinya haka take biyawa inda ta yi kuskure kuma ta gyara mata. “ Ki kasance kullum cikin tsarki bima'ana alwala saboda tana da muhimmanci sosai wurin bada kariya,ko sheɗanu suna shakkar mutum mai zama da alwala a koyaushe,ke ko period kike to ki yi abarki sannan ki riƙe azkhar na safe da maraice” “Amma ai kin san ban iya su ba ko?” “Ki koya mana anty Sakeena ,shi ilimi ai bai da ƙa'ida shekaru ko tsoho ɗan shekara ɗari zai iya shiga makaranta ballantana ke da ko talatin ba ki kai ba” “ Ni rubutun larabcin ne ke bani wuya ” “Zan nemo miki littafi mai fassarar Hausa ,sai na dinga koya miki yanzu bari na tura miki app ɗin Alkur'ani sai ki dinga saurare ” Ta karɓi wayarta ta tura mata tare da saita mata komai ta kunna sautin ya soma tashi,ta ce “ to ni zan tafi gida ko Mama ban sanar ma ba” “ Don Allah

Chapter 8 of 10