se da mami tai ajiyar numfashi kafin tace “ni da kike fadama so kike na dake shi ko me? Kin fi kowa sanin halin sa and am very sure ita ma laylan ko bata San halin sa a zahiri ba ta sani a labari, en uwan sa ma na jiki ya ya kare da su talk less of a friend of yours? Nima kaina so nake ya canza wannan halin nasa, Buh ki bata hakuri shi ma kuma ayy next xe dawo i will talk to him not just because of your friend harda sauran abun da yakeyi don nan his family members duk suna nan so baze yu ya ringa treating din su that way ba.” Murmushi nazli tai kafin tace “much better mami, that’s why I love you” ta fada tana me barin parlon bayan tayi pecking cheeks din mamin. Murmushi mami tai ta bita da ido har ta haye upstairs kafin ta maida idunan ta kan yasmin da ta luluka duniyar tunani. “jasmine?” Se da mami ta fada sau biyu kafin ta dago a dan firgice, tace “na’am hajiya” Murmushi mami tai kafin tace baki saba da sunan ba koh? Murmushi Yasmine tai gamida sunkuyar da kanta kasa, mami ta cigaba da fadin “nafi Saba wa da sunan jasmine akan Yasmine though duk meaning dayane so I will be calling you jasmine not Yasmine hope you like it?” Seda ta fadi hakanne sannan ta tuna cewa since se turanci take yi and bata sani ba ko ita Yasmine din najin turancin, Ammah bisa da mamakin ta se taji ta bata amsa da “it sounds good i like it” seda mami ta danyi kamar me son tuna wani abun don cousin din ta dake nan kano ta fada mata cewa me aykin da aka samo mata tayi secondary ammah kuma batayi tunanin tana Jin turancin har haka ba dadin dadawa ba accent take amfani da Shi ba na Nigerian bane ba shisa she was a bit surprised. Tana so ta tambayi Yasmine din abubuwa da dama ammah se ta bari nan gaba ta tambaya. Kallon wrist watch din ta tai kafin tace “yau ba aykin da zakiyi buh akwai list da zan baki zakuje supermarket ke da driver ku sayo groceries” amsa kawai ta bata sa “toh hajiya” girgiza Kai mami tai tace “next time around akwai punishment akan wannan sunan da kika kakabamun” da sauri yasmin tace “yi hakuri hajiya in sha Allah zan” se kuma tai sauri ta toshe bakin ta wanda hakan da tai ba karamin dariya ya bana ammin ba…..
********
wannnan karan ma tunda suka dau hanya xuwa Supermarket habu ke ta faman yi mata zan ce harda tamabayar ta wai ko tana da saurayi, uffan bata ce da shi ba don Sam bata son magan ko a cikin en uwanta mata talk less of shi da yake na miji. Gabadaya tunanin kalar aykin da zata jibga take if ta koma gida, har suka karaso bata sani ba seda yai mata magana sannan ta dawo daga duniyar tunanin da take, ko da suka shiga cikin dankareren supermarket din habu ne ke fada mata me za ta dauka tana saka masa a basket don list din na cikin wayar sa, seda suka shafe tsawan minti 20 suna abu daya don sosai suka cika cart manya manya har guda 3, daga bisani kuma suka nufi gun biyan kudi.
tsaye take jikin mota su habu da wani ma’aikacin supermarket din suna shigar da kaya cikin boot din motar, ita kanta bata San me ke damu ta ba en kwanakin nan, fada, duka da aykin wahala duk ta Saba da shi ammah bata taba Jin she’s frustrated Akan duk abunda ammah ke mata ba kamar these few days, ji take kamar ta gudu ta koma gidan innna tabarau amma tasan ba hali don ko rami zata shige se ammah ta biyo ta ta zakulota, balle wani gidan inna tabarau da ba bakon ammahn bane ba ba. Tana cikin sake saken ne taga wata tsadaddiyar mota ta xo tayi parking dab da ita, kurawa motar ido tai har after some seconds me shi ya fito daga ciki, haka kawai ta samu kanta da kallon mutumin even though bata iya hango fuskar sa don ya juya mata baya, sanya yake da off white trouser and brown top se kuma boyfriend jacket da ya daura kan top din shi ma off white, tunda take a rayuwarta bata taba Jin kamshi kalar wannan kamshin ba, har wani lumshe idanu tai don a take taji wani natsuwa da kwanciyar hankali wanda ta dade bata ji kalar sa ba ya xo mata, har yanxu she haven’t seen his face, but ta dai San foreigner ne don ba abunda ya suffanta sa da nigerian kama daga kyakkaywan skin din sa wanda yake misalin a xubawa coffe madarar ruwa har ixuwa kan gashin kansa dake kwance baki wuluk, wanda hakan ya kara mata son ganin face din nasa. Yana kokarin rufe murfin motar tasa wayar sa ta fara ringing, hannu ya kai cikin pocket dinsa ya dauko wayar sa kirar samsung ya kara a kunnan sa, duk wani motsi da yake a kan idonta yake don sosai ta maida duk attention din ta kansa, bata san da cewa ana iya samun natsuwa da kallon wani dan adam ba se yau, ko sallma beyi ba taji ya shiga magana da wani language wanda take ji kamar ta taba jin kalar sa, duk da ba ďaga murya yake ba ammah hakan be hanata gane cewa fada yake ba don se faman xura long finger din sa yake cikin bakin gashin kansa, can kuma ya daki jikin motar kafin ya zare wayar daga kunnan sa yana fadin “fuck you nazir” yana gama fadin haka ya shige cikin motar ya rufo kofar da karfi sannan ya tayar da motar ya bar cikin supermarket din da mugun gudu, bin motar tasa tai da kallo kafin ta sauke idanun ta kasa, “me yake damu na ne wai?” Ta fada a fili tana dan dukan forehead din ta, karaf idon ta ya sauka akan wani wallet dake yashe a dadai inda mutumin ya tsaya, kurama gun ido tai kamar me son gano wani abun, tabbas tasan cewa daxu ba wallet a gun kafin ya xo amma yanxu kuma se ga wallet does that mean cewa nashi ne?? “Amma garin ya banyi noticing sanda ya fadi ba?” Ta tambayi kanta, “kina can kin shagalta da kallon sa ta ina zaki gani” wani bangare na zuciyar ta ya bata amsa, a hanakli ta taka ta nufi inda wallet din yake, har ta sunkuya zata dauka se kuma ta fasa tana me tantama “kodai trick aka hada min na dauka na bace daman ance foreigners suna amfani da naman mutane gun hada sausage” ta fada a ranta, (lol da alamu dai yasmine karshe ce gun tsoro). kawar da tunanin tai sannan tai bismillah ta dauka ta mike tana kallon unique wallet din. Ganin habu ya dunfaro inda take ne ya sanya ta bude murfin motar ta zauna tana jiran karaso warsa, a hankali ta bude wallet din, tabbas wannan dollers ne, ta fada cikin ranta don ta tuna sanda tai wining wani competition da sukai 3year ago har wani bature ya bata kyautar 20 dollars amma tunda ammah tai ido hudu da kudin ta amsa bata kara ganin kyallinsu ba, “good old days” ta fada a fili tana murmushi, ko banza a wannna ranar tayi farin ciki sosai ta sanadin hakanne ma ta samu damar yin NECO exams, awards da kuma scholarship wanda ammah ta tsaya tsayin daka ta hanata zuwa makarantar gaba da secondary. har habu ya shigo bata sani ba don har se da taji yace “sorry pretty na barki kina ta jira koh?? Wallahi mami ce ta kira wai a kawai abunda ta manta bata saka a list ba shine fa seda na je na memo sa, cimarsu ce ta can en kasar turkiyaa, kin san rayuwar su gabadaya a can take, se su shafe shekaru kusan 5 basu xo ba, toh se yanxu allah yai suka dawo nan gabadaya, ayy wato in gaya miki ni ayy tun filazal ina ayki a gidan cousin sister din ta dake nan itama GRA amman fa ba girman nan bane ba don gabadaya haihuwar su da girman su a can turkiyan akai amma mamanta er Egypt ce Shi kuma…” “da sauri yasmine tace “muje dan Allah” ta fada kamar zatai kuka don kanta har ya fara mata wani iri saboda surutun sa, ga motion sickness daya dameta tun daxu da ta hau motar. Maida hankalin ta tai kan wallet din dake hannunta, wani tsarsren complementary card ta gani Wanda aka kawata shi da black and golden color, rubutun jiki da italics aka kawata shi, “DOMINION AUTO” ta karan ta a fili, kome ta karanta se ta maimaita sau biyu a haka harta karance gaban card din tass wanda ya hada da location harda kuma email address and the rest, har ta xo mayar da complementary card din se ta lura akwai wani rubutun a bayan card din wanda ya kunshi suna da ceo and chairman’s info, sunan ceo din ta kurawa ido kafin daga bisani ta maida card din cikin wallet din, can ta hango membership card da debit card Wanda su ba wani bi ta kansu tai ba, “tabbas wannan wallet din me amfani ne sosai definitely nasan dole me wallet din will look for it” lumshe idanun ta tai ta jingina kanta jikin window din “adon gari lfy kuwa? kodai zazzabi kike ne??” Habu ya fada yana me leken ta ta mirro, a takaice tace masa “lfy” yace “toh Allah ya sa” daga nan kuma ya maida hankalin sa kan tukin da yake.
Ko da suka isa gida shike shiga da kayan cikin gidan yayin da ita kuma mami ke nuna mata inda zata aje cikin katoton refrigerator wanda ko a tv bata taba ganin kalarsa ba har wani smart screen ne dashi a ciki harda camera wanda mutum xe iya gano abunda yake ciki ba tare da ya bude ba, kofar ma kanta French door style ce, a haka ta ringa xuba wa har ta gama. “sannu jasmine, nasan kin gaji koh?” Murmushi tai kawai ba tare da ta ce komai ba don wannan ko 0.5 na kalar wahalar da take sha be kai ba, cigaba da magana mami tai “ko zaki zauna ki huta xuwa anjima se habu ya maida ki gida?” dan jimm tai kafin “tace toh mami” Murmushi mami tai tace “Yauwaaa jasmine se kije can room ki zauna ki huta xuwa anjiman se ki wuce, ammah bara ina xuwa” ta fada tana mikewa tsaye, ita dai yasmin tunda ta sunkuyar da kai bata dago ba, haka kawai taji matar ta shiga ranta gashi as same time take Jin wani mugun kunyarta. After few mins se ga mamin nan ta dawo da wasu daga cikin abubuwan da sukai shopping na ciye ciye ta aje a gabanta “ga wannan kije ki aje a room dinki if there’s something you need, just give me a call Ohk?” she was lost in words kawai ta tai Shiru can dai tace “na gode mami ammah dis is… “ da sauri mami tace “shhh, dis should be the last tym da inna baki abu zakiyi trying rejecting din sa, just because you are working under me that doesn’t mean I won’t treat you good so don’t do that again kinji? “To mami na gode in sha Allah bazan kara ba” ajiyar xuciya mami tayi kafin tace “good, zaki gane room din??” “Ehhh zan gane” tana gama fadin haka ta kwashi tulin kayan ta bar gun.
Koda ta shiga dakin a kan empty dressing mirror din dake room din ta daura kayan sannan ta zauna akan carpet ta jingina kan ta da jikin gadon, ji take nan din kamar wani safe place din ta ne, gurin da ba hayaniya ba tsawa and the rest, she doesn’t know for how long mami zatai cigaba da treating din ta dis good, Buh she doesn’t care at all, coz she appreciates the care and the real love data nuna mata for dan zaman nan da tai, yeah real love wanda yana daya daga cikin abunda tai lacking a rayuwar ta, ta hadu da mutane da dama a rayuwar ta wanda is either su sota dan kyawun ta ko kuma su kita don tana da kyau, Buh as for mami’s case bata ga alamun hakan ba. seda ta shafe minti 20 tana tunani sannan ta tuna da wallet din da ta sanya cikin pocket din rigarta, cirota tai a fili tace “dama security guard na bama ajiya da duk ba haka ba yanxu ya zanyi da wannan hakkin?” ta fada kamar zatai kuka, wani da bara ne ya fado mata don haka ta matar da ita cikin pocket din din nata ta zaro er keypad din ta ta shiga laluban numbar kawarta saddiqa don akwai dan Ragowar bonus a cikin sim din nata. kiran na shiga ta dauka, sallama tai mata ta amsa sannan tace “saddiqa dan Allah wani alfarma zaki mun” daga daya bangaren saddiqa tace “to kawalli ina jinki” “dan Allah anjima da rana zan xo ki aran wayarki in saka data in tura sako ta email in ba damuwa?” Tana jiyo dariyar saddiqa kafin saddiqar tace “Allah ya shiryaki yasmin shine harda wani yin kasa kasa da murya, kin san dai ba abunda zaki nema na hanaki sedai in bani da shi koh?, dan haka waya ko kwana kike so tayi a gunki bazan taba ce maki a’a ba” Murmushi yasmin tai gamida sunkuyar da kanta kasa kamar tana gaban ta, tabbas saddiqa nada kirki matuka don ba don ita ba da tuni ciwon zuciya ya kashe ta. “Toh na gode in sha Allah inna dawo nasan kin fara suyar awara se na biyo na amsa na gode” daga haka kuma sukai sallama. Tana aje wayar taji cikin ta na kuka hakan yasa ta dubi kayan ciye ciyen da mami ta bata, kamar ko ta sani ta zabo mata wanda zata iya ci. Wani biscuits me dan girma ta dauka da wani juice, ta fara ci a hankali, se da taci taji ya isheta sannan ta sanya ragowar cikin aljihun ta. Gama cin nata keda wuya taji wani bacci na yunkurin yin awan gaba da ita ayko ta kwanta nan Kasan carpet din ba jimawa ko bacci me dadi yai awan gaba da ita.
“Jasmin!!! A hankali ta bude idanun ta da sukai mata nauyi, ta sauke su kan mami, da sauri ta tashi zaune tana faman rufe dogon gashin ta. “Ashe kwanciya kikai??” mami ta tambaya tana zama gefen gado, gabadaya ta ji ta takure se Kace wacce ta Aykata katon sabo murya na rawa tace “ban sani bane bacci ya dauke ni” Murmushi mami tai don ta kula da halin da ta shiga, “toh tashi kiyi sallah, zan ayki habu se ya maida ki gida koh?” Toh kawai tace sannan ta mike ta nufi inda take da tabbacin cewa toilet ne. Koda ta fito bata ga kowa a dakin ba, tunani ta shiga yi akan inane gabas, tsoron kada ta sallaci inda ba daidai ba ne ya sanyata fita daga dakin. Zaune take a parlor ta mimmike kafa akan kujera se faman pressing phone take, har Yasmin ta karaso parlors bata sani ba don hankalin ta yayi gaba na kan abunda yake yi , tsayuwar kusan 1min tai tana jiran nazli din tai noticing dinta ammah batai ba don haka ta tattaro duk wani courage din ta tace “dan Allah ina ne gabas?” Se a time din ta dago ta kalle ta tace “where is where?” Ajiyar zuciya Yasmine tai kafin tace “where’s the qibla please?” Dan jimmm nazli tai kafin tace “Ohhh there” tana fadin haka ta cigaba da danna wayar ta, ko second daya bata kara ba ta bace daga gun, ta kula itama nazli tana da saukin hali duk da dai tsoronta ya shige ta tun sanda suka shigo ta bude musu kofa, tana idar da sallah ta fice daga dakin daidai mami na saukowa daga upstairs, “kin idar?” “ehh mami” ta fada tana wa sa da gefen hijab dinta, “iya number din parents din ki nake da banda naki, drop your number here” mami ta fada tana me mika mata tsaddadiyar wayar tata, a hanakli ta saka hannu ta amsa, within seconds ta sanya mata number din nata mami tace “good gobe by 7 habu will come and pick you up coz akwai guests dazanyi and I need your hand” a hankali tace “Allah ya kaimu” kudi mami ta bata tace “ga wannan kisa credit” marairaice wa tai zatai magana mamakin ta hade rai tace “have you forgotten about the promise you made?? Or lemme know if kinyi breaking promise din naki ne” kanta a kasa tace “nooo mami, na gode Allah ya saka da alkhairi” daga haka tasa hannu ta amshi kudin taima mamin seda safe. Seda suka bar layin sannan tace da habu “dan Allah in tambayeka mana? ” jiki na rawa habu yace “laaa ay ba damuwa ina jinki” tsabar zumudi Saura kadan yai balle da wani matashi dake kan scooter din sa, ayko yaron ya kumduma masa ashar, Sam habu be bi ta kansa ba don gabadaya ya tattare natsuwar sa yana jiran yaji me yasmine din zata ce masa, complementary card din ta zaro a hankali ta mika masa tace “dan Allah kasan wannan address din?” amsa yai ya parking can gefan titi sannan ya shiga kallon card din, mika mata yai kafin yace “kwarai kuwa nasan gun ai ko wani matashi kika tambaya a kasar nan harda kewaye yasan wannan sunan, dominion auto ba? gidan motoci kenan ay ko a week dinnan ma se da na kai su hajiya kamar tana da halaka me karfi ita da me gun duk da dai ba wanda yasan fuskar me gun ko a social media sudai nasu posting pictures din motoci sedai customers din sa wanda suka taki sa’a suka xo yana gun ko kuma ya gadaman haduwa da su amman kamar ance lawyer ne sunan sa umar ko omair? Ohoo dai amman dai ya san aykin sa gaskiya don duk case din da ya solver se yai wining haka naji ana fade, suna ma da branches fa har a kasar waje.” Ita duk ba wannan bayanin ta tambayesa ba ammah se faman zuba yake kamar wani parrot, kasa yai da murya kafin yace “motar zaki saya ne kema?” banza tai masa don ya fara bata haushi, ganin dai ba basa amsar zatai ba hakan ya sanya shi fadin “in xuwa zakiyi aise in kaiki don duk hanya ce” shiru tadanyi tana nazarin maganar tasa, da taso kawai ta tura sako ta email din company din, ammah kuma hanaklin ta ya kasa kwanciya da xuwa da wallet din gida kada tsautsayi ya sa ammah ta gani ta shiga uku ta lalace don haka ta yanke shawarar kai wallet din harcan company din ko ma wa ta gani taba wa ajiya tunda akwai suna and lots of information za’a gane koma na waye, don haka ta dago kai a hanakli sannan tace “toh na gode…”
(Anya habu be shiga uku ba da shegen surutun nan nasa ba? Ita kuma hajiya yasmine bakwa ganin don taga fuskar wannan bawan Allahn yasan ya ta daukar wallet din nasa instead ta bawa security guard?? Da gaske ne nazli nafa kirki kode yasmin makauniya ce bamu sani ba? 😂 )
Thank for the love and dua🖤
A cigaba da mun sharing xuwa groups, friends and family pls😫…….
INUWAR KADDARA*
By moon🌚…
Chapter 3: The Wallet That Led Her to Him
*****
Dominion Auto wasn’t just a company It was power.
Gini ne mai tsawo, an yi shi da gilashi mai kyalli, yana haskakawa kamar yana nuna wa duniya cewa shi ne ke da iko. Sunan DOMINION AUTO an rubuta shi da manyan haruffa masu azurfa a saman ginin—wanda ba za ka iya wucewa ba tare da ka kalla ba, hakanan habu ya danna hanccin motar tasa after ya karbi entery card agun security guard, Koda suka isa parking lot nan suka fara arangama da Motoci masu tsada wanda sukai sahu sahu jere cikin tsari, kowacce mota tana kyalli kamar ba ta taɓa ganin ƙura ba. daidai inda ake parking ya tsaya sannan yace “to mun karaso” a hanakali tace “na gode Allah ya saka da alkhairi” “in biyo ki ciki ne kokuma injira ki anan?” ya fada yana me kallonta ta mirror, Sam bata dago kai ta dube sa ba sema yunkurin fita daga motar da ta shiga yi “a’a nan ma yayi na gode” da sauri habu yace “aa ke dai ki shiga ki fito ina jiranki anan coz hajiya ta dankan amanarki don haka sena karasa aykina sannan” boyeyyar ajiyar xuciya ta sauke kafin tace “ to bara naje na dawo” daga haka ta shiga walking slowly towards the entrance door hannun ta rike da wallet din nasa gam, her fingers were slightly shaking kamar ance za’a kwace daga hannun ta. Cikin ranta ta ayyyace cewa wannan gun it didn’t feel like somewhere someone like her should enter, amma duk da hakan ta kara step daya xuwa gaban glass door din wanda ya sanya glass door din budewa automatically.
nan fa wani cool air yai brushing against her skin, wanda ya sanya ta zare idanun ta a tsorace sannan ta furta “Subhanallah” ganin kofar zata rufe ne ya sanya ta saurin shige wa ayko ya rufe da ita. Shigarta keda wuya wani sanyi me hade da kamshi ya kara dukan ta wanda bata san sa’adda tai folding hands dinta around her body ba, everything looks expensive ga wani Shiru da cikin gun ya dauka like people were afraid to make mistakes. Employees din are moving quickly, neatly dressed, and focused. Murmushi ko digo babu akan fuskar su saboda gabdayan su abu daya suka sani wanda shine “the owner doesn’t tolerate nonsense.”
Dakewa tai ta nufi reception area, inda wata well-dressed lady ke a kewaye da wani table da looked like it cost more than her entire life. The receptionist looked up, her eyes scanning her from head to toe, don yanayin dressing dinta is simple. Too simple for a place like this, Ammah duk da haka tai forcing polite smile Sannan tace
“Good afternoon and welcome to Dominion Auto Please, have a seat while I notify the manager of your arrival. Would you like a glass of water or perhaps some coffee while you wait?” Da sauri ta girgiza kai sannan cikin rawar murya tace “no thank you Im not buying anything, rather looking for someone called OMAIR SURAJ” murmushin kan fuskar receptionist din be dauke ba sedai ya canza ya zama controlled and more distant.“Do you have an appointment?” ta tambayi yasmin din calmly, girgiza kai tayi kafin tace
“No… but it’s very important.” “I’m sorry, you can’t see him without an appointment. Ta fada tana danna keyboard din computer dake gabanta, dan Allah, it’s very important plss ma’am” ajiyar xuciya receptionist din tai kafin tace “look’m sorry but the person you are looking for is the boss here and he is currently unavailable.” Kamar zatai kuka tace “I have his item with me I just want to give it to him and go.” Sam recepnist din bata bi ta kan zancan cewa wai akwai abun sa a gun ta ba, don sam in ba don kyaun da take da shi ba batai kama da wacce boss din su xeyi interacting ba har ta samu item din sa, mutumin da ko yayan governors or ministers suka xo sayan motanci basu isa su gansa ba indai ba suda appointment da shi. Don haka ko me wannan yarinyar ma zata ce mata bazata saurare ta ba balle har taja mata a kare ta a ayki Ana zaman kalau. on a serious note tace “He’s in a closed executive meeting with external partners. No interruptions are allowed.” Tai Shiru se kuma tace “even staff are