suka wuni a cikin gidan ba tare da sun iya tabuka komai ba, don yau shekara 3 kenan tunda abby ya samu matsarla sakamakon ginin da ya fado masa time din suna gina wani katafren gida, wanda tun daga wannan lokacin komai na rayuwa ya canza masu don sosai rashin lafiyar tasa tai contributing gun duk wani abu da take fuskanta gun ammah don ta san ko me zatai mata abby be isa ya hana ba tun da a yanxu ya nakasa sosai don sanadiyar hakan stroke ya kama sa ga hawan jini me karfi daya damkeshi saboda damuwar abun da ke faruwa a cikin gidan sa gashi ba shida iko ko damar daukar mataki akan hakan. baze iya sakin ammah ba don ita ce rufin asirin sa a yanxu, don ita ke kula da su tun daga ciyar wa da sauran su dan shi danginsa tsaffi ne kuma a kauye suke shine ya dan samu ya fito brini, in ya saki ammah ita kanta yasmin din ba tada yadda zatai don se dai ta koma gun innah a kauye ita kuma inna bata da karfin rike ta yayyin sa kuma aurar da ita zasuyi ko tana so ko bata so, duk da mafarkin ta na rayuwa ya gama rugujewa wannan karan ko ba xe so ya kara ruguza mata mafarkin ta ba, hakan yasa har yanxu be dauki mataki akan ammah ba se ma bawa yasmin din hakuri da yake yawan yi…..
Can yamma ganin dai kamar jikin nasa kara gaba yake ba baya ba ya sanya ammah kallon Yasmin ba annuri a face din ta tace “jeki chemist ki cewa ayuba ya taimaka ya xo ya duba jikin sa” mikewa tai don yin abin da amman ta sata yi, hade girar sama da kasa inna tai tana fadin, “taya zaki ayke ta bayan ga umar a gida ba inda ya je tun da ya dawo daga makarantar boko?” Har ammah ta bude baki zatai magana se kuma tai shiru don tasan halin innah dede take da kugun sa wandon ta don bata wuce tak mata tatas ba agaban yaran nata don haka ta ayka umar wajan ayuba me chemist. Ko da ayuba ya duba jinin nasa yaga ya mugun hawa fiya da ko yaushe se ya dube su yace “gaskiya da damuwa don jinin sa ya ninka na da hawa sosai, kamar ma treatment din sa na da yayi failing, da so samu ne kawai a kaishi asibiti suyi masa check up me kyau” ya fada yana hada kan kayan aykin nasa, kawu lawal ne cikin fushi yace “karyar banza karyar hofi kullum haka dai daga ace wannan se wannan in banda kame kame ba abin da kuka iya, ni dai sisi bazan bada wlh se dai in ku ku san yanda zakuyi dashi” shidai ayuba be kula sa ba don ya kula kamar kawu lawal bashi da seti kuma ba tun yau ya saba yin haka ba kullum ya xo gidan duba mahaifin yasmin se kawu lawal ya suke shi ammah don ganin mutuncin yasmin da na mahaifin ta da yake yi ne ya sanya shi yake daga masa kafa duk da yayi alkawarin cewa wataran se ya gwada masa danyan kai irin na gen Z…..
wunin ranar haka ta wuni se zubda hawaye take, she cant afford to lose her dad don ganin sa a raye na matukar bata courage a rayuwar ta, guraren karfe 4:30 jikin abby ya tashi sosai don se da ya suma sau 2, ko da ya farfado ma in banda sambatu ba abin da yake, dole kawu lawal da umar suka samo adaidaita sahu don kaishi asibitin malam aminu kano don acan tun farko aka fara masa treatment kafin su watso shi saboda rashin clearing bills din su da basu yi ba. Kuka sosai yasmin take ganin halin da mahaifin ta ke ciki, ganin ta damu sosai ne ya sanya inna cewa ta shigo su tafi tare in ya so kawu lawal ya makale a gefe tunda ita yasmin din ba wani kaurin kirki ke gare ta ba. Suna isa asibitin suka karasa ward din maza suka amso weelchair aka daura shi akai aka shigar da shi cikin ward din, nan litoci suka shiga bashi temakon agaji, xuciyarsa ce tai weak har ta sanya bata iya pumping blood yadda ya kamata ga kuma wani ciwon kai da ke damun sa sosai, tashin farko aka rubuta masu magani allurai da kuma tests iriri wanda kudin yakai 10000, ko da aka mika masu paper din Yasmin ce ta amsa don ita ce ta iya karatu kaff cikin su, duk suka xuba mata ido suna kallon ta duk jira suke suji me zata ce masu, hawayen da suka gani na bin fuskarta ne ya sanya hankalin su kara tashi a haukace ammah tace “dallah malama ki fada mana me suka ce kin xo kin samu gaba kina kuka ko an gaya miki kin fimu sansa ne?” saurin share hawayen nata tai kafin tace “wai kudin magani da tests din da za’ai masa dubu dari, da karfi innah tace “dubu dari? Mun shiga ukun mu yanxu ina muka san zamu samu dubu dari ni halima?” Ta fada tana daura hannu a kanta ammah da ta kafe yasmin da idanu tace “na shiga uku nah ni zulai, hanxu ina zamu samu kudi masu yawan gaske haka?” Ta karashe zancen tana fashewa da mugun kuka, sun shafe kusan 20mins suna nan zaune agun sunyi jungun jungun har se da wata nurse ta dube su tace “auu kuna nan har yanxu baku sayo maganin ba? ana fa bukatar maganin nan da sauran abubuwa da gaggawa in kuma kun shirya fita da gawa ne toh kuyi ta zama” ay ammah bata san sanda ta mike tai kan wannan figaggiyar nurse din ba tana zagin ta ta uwa ta uba harda kokarin kai mata hannu, wasu majinyata ne suka samu suka ririke ammah dake ta faman yi masu tirjiya, ita dai yasmin na can gefe ta rakube kamar wata kaza tana ta faman tunanin yadda za’ai a ceto ran mahaifin ta don ko kaffara bazatai ba innah da kawu lawal ba suda hanyar samun wannan kudin don suma a kauyen ba abin da suka aje se wasu ramammun akuyoyi guda uku wanda su duka ukun ko saida su za’ai basu fi 70k ba don ko nama ba suda shi ajikin su, xumbur ta mike tunawa tai da kudin da hakeem ya bata wanda if she’s not mistaking toh tabbass 10000 thousand naira ne daidai saboda boundle ne guda na kudi. Sadaf sadaf tai ta fice daga ward din da sauri hannun ta rike da takardar maganin, ita dai ta san a cikin aljihun rigarta akwai kudin da xe isheta ta je gida ammah banda na dawowa don saidai ta amsa agun kawar saddiqa, tafiya take cikin sauri kanta a kasa, karo tai da mutum, da sauri ta ja baya gamida durkusawa ta dauki papper din da ya fadi, se dai kafin tai hakan mutumin yai saurin kai hannu ya daukar mata, mika mata yai cikin sanyi tace “yakuri bawan All..” maganar ne ya makale mata a makoshi sakamakon wani bugu da xuciyar ta tai da karfi yayin da tai arba da kaykkawar fuskar sa, wani iko na Allah sam ta kasa janye idanun ta daga kan nasa duk da kasancewar ta yarinya me kunya, shima kuma kallon ta yake with confusion, duk da wancan ranar bata samu ta mai kallon natsuwa ba ammah tabbas ta gane shi tass “yasmin?” ya fada fuskar sa dauke da farinciki da kuma mamaki, saurin sauke kanta tai kasa, kafin tace “good evening” be amsa gaisuwar tata ba ganin kamar tana cikin damuwa don haka yace “what happened my dear? Me kike yi anan wani ne ba shida lfy? Or kinxo dubiya ne?” Ya jero mata tambayoyin gamida kafe ta da ido dan jiran amsar ta yake, bata san sa’addah ta saki wani kuka ba kamar yarinya karama agun har wasu mutane na bin ta da kallo, sosai hanaklin sa ya tashi ganin tana kuka sosai, da sauri yace “ya salam yasmin talk to me, rasuwa akai muku?”ganin kamar hankalin mutane na yi kan su ne ya sanya sa fadin “relax muje ki zauna a can se ki fadan koma mene but pls relax and stop crying” fuskar sa dauke da damuwa ya fadi maganar yana me nuna mata wani seat dake nan gaba da su, samun kanta tai da takawa towards the seat, se da ta zauna sannan ya zauna a kujerar dake facing din tata ya ciro wani hanky me dan banzan kamshi ya mika mata, hannu ta saka ta amsa ta share ragowar hawayen fuskar tata, seda ya tabbatar da ta daina kukan sannan ya kara maimaita mata tambayoyin da yai mata da farko, murya na rawa tace “abby ne ciwon sa ya tashi” ta fada tana share kwallar dake xubo mata, “Subhanallah, meke damun sa?” Ya tambaya, shiru tai ba tare da ta basa amsa ba, doguwar ajiyar xuciya Hakeem ya sauke kafin yace “look yasmin, ki taimaka ki fadan damuwar ki, I promised you in sha Allah i will help you, kuma ma karki manta matsalar ki tawa ce, your dad is my dad too amma if kikai shiru ba yanda zanyi na san me ke damun sa” ya fada cikin sigar lallashi, sosai tai nazarin maganar daya fada a brain din ta after a while tai deciding fada masa duk abin da ke faruwa amman bata mentioning cewa basu da kudin ba. Ko da ta fada masa halin da abby yake ciki sosai yai kwantar mata da hankali sannan ya ce da ita “rakani ward din da aka kaisa” ba musu ta mike suka jera tare har suka shiga cikin ward din, tun shigar sa nurses din gun suka shiga gaida sa cike da ladabi harda ma doctors din, sosai mamaki ya cika yasmin don be ce mata yana ayki a wanann hospital din ba, haka har suka karasa gun da abby yake wanda ba me bin ta kansa don ba su kawo kayan da za’ai masa treatment din da shi ba ganin ba wani taimakon kirki da abbyn yai receiving duk da condition din nasa is worst ya sanya shi calling attention din wata nurse dake duba wani mutun a cikin room din, da ladabi ta nufo sa tana kara gaida shi despite sun gaisa tun shigowar sa, on a serious note ya ce da ita “how on earth ba’a bashi treatment me kyau ba duk da condition din da yake ciki” da sauri nurse din tace “sir an basu takardar magani da sauran abubuwa ammah sunce basu da halin biya daya daga ciki ma ta nemi ta tayar mana da husuma shisa doctor sambo yace a kyale su da halin su” ta karashe maganar tana hararar ammah don har yakushin ta se da ammah tai duk da dai ita er rabo ce bama da ita akai fadan ba. Girgiza kai yai kafin ya ce da nurse din “we are talking about someone’s life here amma zaku a barshi haka? What’s wrong with you people?” ya fada rai a bace da sauri nurse din tace “sorry sir” maida kallon sa kan Yasmin da tai shiru tana sauraron tattaunawar ta su yai, “yasmin” ya fada da wata murya bata iya ce masa komai ba se kara yin kasa da kanta da tai, duk wannan abu da ake su ammah bama su san anayi ba don sun dauka random doctor ne ya xo yake tamabayar ba’asi, hannu ya mika mata alamun ta bashi takardar maganin, a hanakli ta mika masa ya sanya hannu ya amsa daga haka ya bar gun ba tare da yace mata komai ba, sauke ajiyar xuciya tai tana sake sake kala kala a ranta, after a while se gashi nan ya taho hannun sa rike da ledan magani, gefansa kuma doctor sambo ne yana masa magana, tana ganin sun karaso tai kasa da kanta gamida basu guri don aywatar da aykin su, su ammah na ganin doctor ya yi kan abby suka tashi daga zaman bihim din da suke suka nufo sa suna gwale idanu, ba jimawa doctor yai masa gwaje gwajen da zeyi kafin daga bisa ni yace, toh yanxu saura tests wanda in ruwan da aka saka masa ya kare se aje ay masa a nan lab, ya fada yana niyar barin gun, da sauri ammah tace “ammah likita ba ance wai se mun biya kudi kimanin dubu dari ba sannan za’a duba shi ba? Kodai tallafi muka samu ne?” Ta fada tana zazzare idanu, innah ce tai saurin fadin “ke dallah yi mana shiru yanxu inma mantuwa sukai suka duba sa se ki ja su fasa ayy” ta fada tana hararar ammah, ita dai yasmin ji take kamar kasa ta bude ta shige cikin ta, murmushi doctor sambo yai kafin yace “a’a innah ba kuskure bane ba” wani kallo hakeem ya watsa ma doctor sambo don tun farko se da ya rokeshi akan kada yai mentioning name din sa kawai yace wani me hali ne ya taimaka masu ammah se gashi yana shirin bata masa shirin sa, dauke ido dr sabo yai daga kan na hakeem sanan yace “wanan bawan Allahn ne ya biya komai da komai and he’s willing to pay every single naira da za’a bukata a nan gaba” nan fa su hajja suka maida kallon su kan hakeem that was trying to leave the place coz this is not his plan at all ammah dr sambo ya bata masa shiri….. nan fa suka shiga xuba masa godiya harda kawu lawal me bakin hali, shidai uffan ya kasa ce masu se da yaga dai da gaske godiyar tasu ba me kare wa bace ba sannan ya furta “Allah shine abun godiya kawu, ku kara gode masa, Allah ya bama baba lfy” yana fadin haka yai saurin barin gun, da ido yasmin ta bishi har ya fice daga ward din, sosai taji ba dadi da ya tafi don ko godiaya batai masa ba gashi bata ma fito da wayar ta ba balle ta kira sa, ana cikin haka se ga wani gansamemen mutum ya shigo yana korar visitors alamun lokacin visiting ya kare, babu yadda zasuyi haka suka fito suka bar kawu lawal don yai jinyar abby dake bacci har ynx. Ko da suka fita ta ringa ware idanu ko zata gansa ammah shiru har suka tsayar da adaidaita suka bar bakin asibitin…
Suna isa gida kuma se ga en jaje sun fara shigowa don yi masu jaje, ita dai yasmin na shiga gidan daki ta wuce direct ta dauki wayar ta data bari cikin drawer din ta ta shiga dialing number din sa da har yau batai saving din sa ba, ko da ta kira ba’ai picking ba hakan ya sanya ta aje wayar tana hade rai ta fita tsakar gida tai alwala ta tada sallah, idarwar ta ke da wuya taji wayar tata na ringing, da sauri ta nufi wayar tata ta dauka tana kallon numbern nasa at same time kuma juciyar ta na bugawa da sauri, picking tai ta kai wayar kunnan ta bakin ta dauke da sallama, nan daddadar murayar ta ta sauka cikin kunnan sa wanda hakan ya sanya shi lumshe ido yana me jingian a jikin motar sa “ya jikin babah?” Hakeem ya tambaya cike da kulawa, ”da sauki” ta bashi amsa a takaice, daga haka kuma tai shiru don bata san ta ina zata ma fara yi masa godiya ba, can dai tace “na gode sosai Allah ya kara budi, Allah ya bada lada, Allah kuma ya saka da alkhairi” har tana iya jiyo sautin murmushin sa kafin daga bisani yace “stop thanking me yasmin, just focus on dua Allah ya bama baba lfy” ta amsa da ameen kafin tai masa sallama don jiyo muryar amma datai tana kwala mata kira don ta dora kalacan dare. Tana girkin abubuwa daban na mata yawo a xuciya, na farko yadda kaddara ta kara hada ta da hakeem, na biyu kirki da kuma tausayi irin nasa, na uku kuma yadda take kasa daina tunanin sa 24/7 koda tayi kokarin yin hakan, tabbas tana jin wani abu na daban a kansa, wani abu da bata taba ji akan kowa ba se shi... ko da ta kai ma su innah abinci sosai taji ba dadi tunawa da tai abby baya nan, nan da nan kuma xuciyar ta da tunanin ta suka koma gun sa, “ko yanxu ya farka?” ta tambayi kanta, muryar maman saddiqa da ita saddiqar ce ya katse mata tunanin ta, cikin xuciyar ta tai hamdalah don tun daxu take son ta koma daki ammah innah ta hana ta wai ta zauna cikin mutane ba wai zama cikin daki mara haske ba kamar wata bokanya , saddiqa na yima innah da ammah jaje wanda da kyar ammah ta amsa don sam basa ga maciji da ita tun wani fada daya hada su akan dukan da taiwa yasmin ita kuma taje har gida tai mata rashin kunya wanda hakan yasa ko a hanya basa ma kallon juna don fadan har maman su saddiqar se da ya shafa ammah taje har gida itama tai mata diban albarka yanxu ma don ance inna ta xo ne da kuma albarkacin yasmin kuma mahaifin nata bana banza bane amma da duk su biyan ba abunda xe saka su taka cikin gidan. Yasmin ce ta ja saddiqa dakin su don tun wancan ranar da ta je office din wancan watsatstsen take ta so tambaye ta abu ammah bata samu sun hadu ba, “ya jikin abby yasmin?” Saddiqa ta tambaya cikin kulawa, “Alhmdllh da sauki da muka baro shi ma yana bacci ne” “Ohk toh Allah ya basa lfy” yasmin ta amsa da ameen kafin kuma ta gyara zaman ta tace “ummm saddiqa wai wancan ranar da kika ce naje na kai wallet din da wani kalan response aka ce neh?” Jimm saddiqa tai kafin tace waii gaskiya na manta don ni sanda ma aka turo sakon bacci ne a ido na, ammah na taho da wayar ay se ki duba” ta fada tana me mika mata wayar, ko da tai arangama da email din sosai ranta ya baci ammah sam bata bari hakan ya nuna a kan face din ta ba don yana wuya ta nuna bacin rai akan face din ta duk da dai a ranta takan ji zafi wanda hakan ba karamun punishment bane wanda ta sabarwa kan ta dashi tun tana karama. Maidawa saddiqa wayar tai, saddiqa tace “lfy da wani abun ne?” Ta fada tana kallon cikin wayar tata, gwalo ido waje tai kafin tace “kambuu wannan wani kalan mutum ne mara da’ah? Kai amma ban so ma ace kin mayar ba da wallahi se mun gama masa azaba kan mu bashi tun da shi bashi da tarbiyar magana, ay maka magana jaka amman ko godiya babu?” saddiqa ta kare maganar tana huci, murmshi yasmin tai aran ta tace “se kun ma hadu da shi sannan zaki tabbatar da hakan” mikewa tai ta shiga laluban kudin da hakeem ya bata, sosai kirjin ta ya buga ganin ba kudin ba kuma alamun su, ita bawai batar kudin ba, questions din da zata amsa take gudu, sosai hankalin ta ya tashi ta shiga fiddo da kayan nata daya bayan daya, duk abinda take saddiqa dai kallon ta take kawai da mamaki. Wani hamdalah ta saki bayan ta jiyo tudun kudin cikin aljihun wata rigarta, da sauri ta ciro kudin tana kallo, ware idanu saddiqa tai tana kallon kawar tata da kuma abun da ke hannun ta, seda ta mayar da kayan da duka xubo kasa kafin ta koma mazaunin ta na daxu ta damkawa saddiqa kudin, with shock saddiqa tace “a ina kika samu duk wan..” da hannu yasmin tai mata alamar tai kasa kasa “zan miki bayanin yadda aka samu kudin daga baya Ammah dai kudin treatment din abby ne and I want you keep it with you the money is not safe in this house” ta fada a hankali pleadingly, Shiru saddiqa tai tana nazarin abin da kawar tata ta ce mata kafin tai ajiyar xuciya tace “toh yasmin nasan ba zakiyi abin da ba shikenan ba I trusted u amma gaskiya ajiya kudi me yawa haka a agurina babban risky ne coz if akai finding out a gida na banu and bazan iya mentioning name din ki ba kin sani” ta fada a raunane, shiru ne ya dan wakana na kusan 10 seconds kafin “yasmin din ta ce hakane kuma nima bazan so na saki cikin damuwa ba, don’t worry xan aje a guri na” ta kare maganar tana dan murmushi. Hararar ta saddiqa tai kafin tace “toh kinji nace bazan amsa bane ba?” Ita dai yasmin bata ce komai ba se kallon saddiqa da take kawai da mamaki “ayy ina da banki na OPay se na kaima me pos ya saka kudin ammah fa bana anguwar nan ba daman gobe in muka je kasuwa ni umman mu zamu wuce sheshe gidan aunty murja se a saka mun acan daman akwai wani me pos da ya taba cewa yana sona toh nasan ma ba lallai ya amshi chargis ba” ta fadi hakan tana tura kudin cikin kugun ta, ita dai yasmin se kallon saddiqa take don wayon ta is extraordinary dan bata bari sam kanta ya kulle zata samar da mafita, ana haka maman saddiqa ta shiga kwalla mata kira akan su xo su tafi, haka nan duka fito daga dakin duk su biyun, yasmin ta raka su har kofar gida tana masu godiya, ganin idon innah ne ya sanya ammah yin shiru ammah da se tai mata kacha kacha akan gayyatar mata saddiqa da tai cikin daki. Se gurin 2 sannan yasmin ta kwanta bayan ta raba dare tana yima mahaifin ta adduar samun lfy da kuma hakeem da ya taimake su, a cikin adduar ko har samun kanta tai tana fadin “ya Allah in alkhairi ne bawan nan naka Allah ka tabbatar da alkhairi a wannan lamari, in ko ba alkhairi bane Allah ka raba” ta rufe adduar tata da adduar isthikara…
Still on free pages…..
INUWAR KADDARA (THE SHADOW OF DESTINY)
By moon🌚….
Chapter 8: A Proposal She Wasn’t Ready For….
Washe gari friday ta tashi da safe kamar kullum tai duk gyaran gidan da dumamen abinci, yau sam ba tada niyar xuwa ayki don so take taje ta kula da mahaifin ta. Tana cikin juya ruwan zafi a cikin wani ribabben plass se ga ammah ta fito daga daki tana hamma kamar zata hadiyi babu, direct inda yasmin din take ta nufa fuskar nan tata da taci uban bleaching a hade “uban me kike har yanxu baki wuce ayki ba?” Murya na rawa yasmin tace “daman-daman ina so in ce ko zaki fadawa mami abby ba lfy bazan samu damar xuwa ba se ya..” Marin data zabga mata ne ya sanya ta hadiye zancen nata tana yarfe hannaye, ammah na huci tace “dan ubanki so kike a kore ki a aykin koh me? Toh Wallahi ko mutuwa yai se kin je, dan haka xo ki wuce ko na kara miki wani kin san hali na, daman tun jiya ina ciki dake” ta karashe maganar tana huci. Duk abinda ke faruwa innah bata sani ba har yasmin din ta bar gidan don Allah yayi ta da dan banzan nauyin bacci don tsaf se a sace ta bata sani ba. Tana isa bakin titi taga ba motar gidan mami a inda habu ya saba yin parking, wayarta ta zaro tana kallon lokaci taga 7:48 still da sauran lokaci, tana taye agun can se ga motar ta karaso hakan ya sanya ta yin ajiyar xuciya don ta dauka ya gaji da jira ne ya sanyashi ya tafi. “A gafarce ni yau na makara wlh kin san garin akwai sanyi sosai kuma abun mamaki duk da safiya ce yau amman na tarda go slow” ya fadi hakan yana me figar motar da gudu.
ko da suka isa gidan a parlor ta tadda nazli da mami, har kasa ta durkusa ta gaishe su