Share this page
4 / 10
using dinsa da tai as a shield, wani ashar saddiqa tai kafin tace “kina uban me kike yi tai miki kalar dukan nan baki gudu ba ehh? Saboda ke gaki damo sarkin hakuri koh? Toh Wallahi ki jirani a nan in dauko hijabi na akwai abokin masoyi dan hisba ne Wallahi gunsa zamuje mu shigar da report ay zalincin yayi yawa kuma fisabilillahi” da sauri yasmin tace “dan Allah ki bari kinsan banson tashin hankali, lefina na ne ni nai mata lefi dan Allah a bar maganar nan kin ji saddiqa? na barta da Allah kawai” baki bude saddiqa ke kallon yasmin kafin tace “kin fi son ki zauna ta kasheki koh? Toh in ta kashe ki kema kina da xunubi don baki temaki kanki ba, kuma ni wallahi bazan zauna in xuba ido ana aykata barna ban hana ba” tana fadin haka ta juya ta koma cikin gida, ita dai yasmin ta bita da kallo daga karshe ta cigaba da tafiya a hanakali don har yanxu jiri take gani sosai. Daidai inda yai parking jiya ta hango motar, da sauri ta karasa ta bude motar ta shiga, a hankali tace “ina kwana? Na barka kana jira koh” da sauri yace “Lfy kalau emmata, a’a wlh ba komai yanxu ma na karaso” ya fada yana tada motar. Tunda suka fara tafiya take Jin kamar ana rugurguza kashin ta da guduma, hakanan tai lamo jikin kujeran gamida dan rufe fuskarta da hijab dinta, se da taji ya kashe motar sannan ta bude idon ta a hankali jiki kuma a sanyaye ta fice ba tare da tace dashi komai ba. Ko da ta isa bakin kofar shiga parlorn hannu ta kai ta danna bell din jikin kofar, ba jimawa akazo aka bude, wata mata ce wacce a shekaru zatai 40 years fara sal da ita kuma er chubby chubby da ita, kallon juna kawai suka tsaya yi kafin daga bisani ta matsa ma yasmin din ta shigo ciki, a hankali yasmin tace da ita “good morning” da sauri matar tace “morning yasmin” ta fada tana dan Murmushi, da mamaki yasmin ta kalle ta Jin ta kira sunan ta, a karo na biyu matar tace “nice bahar and I believe that kinji magana ta agun mami” sosai mamaki ya kashe yasmin Jin yaddatai hausar kamar bahaushiya, watsar da wannan tunanin tai kafin tace “ehh ta fada mun barka da isowa” daga haka ta shige ciki tabi bayan bahar data danyi gaba, “I have cleaned up everywhere, yanxu abunda zamuyi shine girki, mami tayi list din abubuwan da za’a dafa ma bakin yau and i believe that you will help me make them” with respect yasmin tace “sure” daga haka ta karasa cikin katafaren kitchen din tanajin kamar zata kife kasa don ba karamin jiri take ji ba. Koda suka shiga kitchen din bahar ta mika mata wata piece of paper tace “these are the list of the dishes we are to make ” a hankali ta sa hannu ta amsa, “zobo, dambu, fried rice with roasted chicken, kunun aya, se wasu sunayen abincin da bata ma taba Jin sunana su a duniya ba, mika ma bahar tai kafin tace “toh da wanne za’a fara?” Dan jimm bahar tai kafin daga bisani ta ce, “let’s start with dambu and roasting the chicken, though I have already marinated the chicken and also zobon ma anyi boiling dinsa tiger nut drink kuma was made since in the subh” ta fada tana me fito mata da vegetables, haka nan suka shiga yin girkin ba ji ba gani don she was told by bahar that guest din will arrive by 12pm don haka suke ta ayki ba tsayawa, bahar se hira take mata gamida mata tambayoyi don she was impressed by the girl’s cooking skills, haka dai sukai ta aykin se 11 suka gama, wani iko na Allah se kuma taji duk zazzabin ya barta kawai dai ciwon kai ne ke dan damunta, tunda ta xo bata hadu da mami ba se da bahar tai using telephone din kitchen din ta kira na gurin ta se gata after few minutes ta shigo kitchen din da shigar alfarma, da ladabi yasmin ta gaishe ta ta amsa mata cikin sakin fuska, harta wuce ta dawo looking at her face kamar me son gano wani abu, ganin kallon da take mata ne ya sanya yasmin din yin kasa da kanta “what happened to you Jasmin? Your face wasn’t like dis yesterday, meya faru?” Dan Shiru yasmin tai tana tunanin me zata ce mata, can tace “faduwa nai” ta fada a takaice, jimm mami tai kafin tace “sannu akwai ointment a room zan dauko miki anjima” “ngd” ta fada slightly, mami bata ce mata komai ba se bude tsadaddun warmer din da ta shiga yi daya bayan daya, nan take aroma ya cika ko Ina da ko ina na kitchen din. “Mami ina kika samu great cook haka? She’s so good ni kaina se kallonta nake kawai don sosai ta birge ni” bahar ta fada tana kallon yasmin da ta sunkuyar da kanta kasa, murmushi tai kafin tace “se dai na gode Allah don da alamu nayi sa’a kam, yanxu kuje ku huta don ba abunda ya rage kume se in sun xo ne za’ai serving dinsu” mami ta fada tana me kai glass of hibiscus drink din bakin ta, ba musu suka nufi hanyar fita daga kitchen din bayan bahar ta daukar masu nasu breakfast din don basu samu Daman yi ba saboda ayki. “tsaya yasmin” Chak ta tsaya ita kuma bahar tai gaba daya breakfast din nasu, mami ce ta karaso kusa da ita kafin tace “meya samu fuskar ki? Nayi noticing ba iya face dinki bane ba and it clearly looks like kamar dukan ki akai, fadamun gaskiya a gida ne aka dake ki haka?” Ta kare maganar a sanyaye, se da tattaro natuwarta sannan ta fara magana don ba abinda xe sa ta fada mata gaskiyar abunda ya faru “a’a ba a gida bane ba a islamiyyah ne aka zane duk en ajin mu” Shiru mami tai tana nazarin abunda ta fada kafin daga baya tace “ammah kuma kuna mata suke maku kalar wannan dukan? Dis is not fear at all look at you face for goodness sake, ya kamata a samu ay ma masu makarantar magana don be kamata ba, zan turo nazli ta baki ointment ki saka” taga haka mami ta fice daga kitchen din. Tana shiga dakin taga bahar takai mata abincin nata don haka ta zauna nan kasan carpet tana sauke ajiyar xuciya don yanxu kuma zafi take ji da yunwa don haka hannu a hankali ta shiga cin lafiyayyen breakfast din da bata taba cin wani abu me dadi kalarsa ba don yaji spicies da sauran Kayan girki da ita bata taba ganin irin su ba. Guraren karfe 12:5 taji ana knocking door din da take ciki, a hanakli ta mike ta bude taga bahar ce, Murmushi ta dan sakar mata, itama bahar tace “mami tace the guest are here” a hankali ta furta “ohh” tana me fito wa daga dakin, gabadaya she’s feeling so awkward kasancewar tana ayki tare da bahar dan a haife bahar ta haife ta shisa ma bata iya kiran sunan ta ko abu take son ta tambaye ta sedai kawai tai mata magana. Tun kan su karasa parlon sama take jin kamshin perfume kala kala iri iri, kanta a kasa take tafiya harta nufi inda dining table din yake ta aje warmer din dake hannun ta, jin bahar na gaida bakin ne ya sanya ta matsa wa kadan ta durkusa har kasa ta gaida su ba tare da ta kalle su ba, su 5 ne a dakin, mata 4 da namiji 1, cikin su kadan ne suka amsa don duk ragowar hankalin su na kan smartphones din su, ganin hakanne ya sanyata mikewa a hanakali ta tashi ta bar gun, muryar wata tsohuwa ta jiyo tana cewa “ke kuma Amina ina kika samo wannan yarinyar ko itama tsintar ta kikai a turkiyan?” Tsohuwar da suke ma lakani sa suna hajja ta tambaya tana me kai fruit din da ke gabanta baki gamida bin yasmin da ido kamar zata cinye ta, Can kuma facalar mami wacce take auran kanin daddyn su nazli me suna aunty fiddou tace “Kinga mami garin kwashe kwashen nan naki wataran se kin tsinto aljanu don ita kanta wannan ni ina da ayar tambaya a kanta Jibe ta fah? Se a lokacin matashiyar macan da zatai sa’ar nazli da brother dinta wanda xeyi 28 years haka suka dago kai suka dubi yasmin da ta juya baya zata bar gun, can kan cushion daban wata mata ce ta sha shigar alfarma, a shekaru zata kai mami, suna kiran ta da hajiya karama don sunan ta daya da hajja wato safiyyah, wacce tunda ta xo take ta fama pressing phone din ta don ko cikakken gaisuwa basuyi da mamin ba, daman ita waya shine abokin hirarta don takan iya shafa hours tana danna waya ba tareda da tace wa kowa uffan ba, jin maganr da su hajja ke ne ya sanya ta dago kai gamida yamitse fuska tace “wai wata yarinya ake magana akai ne?” Aunty fiddou ta bata amsa da fadin “maid din mami ce na ganta kamar ba mutum ba”" a karo na biyu hajiya karama ta yamitse fuska tace “as in?” Tai maganar a takaice tana kallon bayan yasmin dake sauka daga stairs din, still aunty fiddou ce ta kara bata amsa da fadin “the girl is hella beautiful” bata kara cewa komai ba se maida idon ta kan mami da tai wacce was busy helping bahar gun arranging dining table din don suyi sauri, se da ta ga mamin zata juyo se ta dauke kai ta maida kan wayar ta da take dannawa, “the dining is ready” mami ta fada tana jama hajja kujerar da zata zauna. Gaba daya se yaba abincin suke ta yi banda hajiya karama dat was just playing with her spoon, ba kuma don abincin be mata dadi bane ba, kawai dai halin nata ne ya matso though she’s always moody. Seda sukai nisa gun cin abincin sannan er aunty fiddou me suna yusra fadin “mami where’s nazli? Ko ba tare kuka dawo bane ba” charaf aunty fiddou ta amshe da fadin “ayy ba zata fito ba jira take muje har daki mu gaida ta” mami dai bata tanka ba don tun dazu taje room din taji ta a toilet wai wanka take where as ita da sassafe take wanka duk don kada ta hadu da familyn baban nata shine take using din shiga wanka as an excuse, daidai hajja ta bude baki zatai magana se ga nazli nan ta shigo parlorn kana ganin yadda take frowning face din ta kasan she’s not happy to see them at all, seda ta xo dap da su sannan tace “Good afternoon everyone, sannun ku da xuwa” ta fada tana zama kan dining chair, cousin brother din ta wanda shine da daya agun hajja karama me suna hateem se binta da kallo kasa kasa yake kamar xe cinyata don rabon da su ganta anyi kusan 6years don yanxu ma se da hajja tai magana sannan suka dawo nigeria don sam in akwai inda basu son xuwa toh nigeria ne, suna hada ido da hateem ta galla masa harara don sam bata manta bakin halin sa ba da rashin M din sa don ko yaxo gidan su ma turkey bata ma shiga harkar sa saboda girman kansa da halin shariya irin na mahaifiyar sa hajiya karama daya kwaso. “kaniyarki naazli, nace kaniyarki, mu zaki gaishar a gantale kamar wasu en iska? Halan bakisan matsayin mu a gunki ba ko? Toh Wallahi ki kama kanki in ba haka ba zamu saka kafar buje daya dake cikin nigeria” ta fada tana kankance ce idanu, turo baki nazli tai kafin tace “granny daga xuwa na harkin fara mun fada daga gaisheki” ta fada kamar zatai kuka, mami ce ta daka matsa tsawa gamida hade rai tace “will you keep quiet ko se na baki dirty slap? Hajjar sa’ar kice?” Mami ta fada kamar zata doke ta, “hmmm daga baya kenan” aunty fiddou ta fada tana kai spoon din ta baki daga haka kuma ba wanda ya kara cewa komai a gun se da suka gama tasss sannan yasmin ta shigo do min dauke kwanukan, cikin natsuwa take xuba su cikin wani medium sized luxury basket, gabadaya ta kagu tai abin da ya kawota ta bar gun, dan gabadaya a takure take a gun, tunda ta fara kwashewa bata yarda ta dago idanun ta ba har ta gama ta bar gun, tana isa kitchen din ta sauke ajiyar xuciya, ta juye plates din cikin sink ta shiga washing dishes din…. ******* Zaune yake kan kujera ta alfarama yana going through wasu sabon motoci cikin mackbook din sa babu wani walwala kan fuskar sa, can gefen sa kuma wani mutum ne ke kwance kan wata tsarariyar cushion 3 seater yana wasa da yo-yo hankalin sa kwance kamar wani karamun yaro, rintse idanu omair yai don gabdaya karar yo-yo din takura masa yake kuma nazir din ya san be so hasalima intentionally yake don ya saka sa magana, “would you stop that already?” Ya fada sounding so pissed up, Jin abinda ya fada ne ya sanya nazir din yin murmushi don abunda yake nema ya samu don haka ya mike zaune, daidai ya bude baki zeyi magana kawai akai knocking door da sauri nazir yace “come in” wani kallo omair ya bishi da shi Jin abun da yace, PA din sa ne ya shigo yace “good afternoon sir” be amsa gaisuwar ba se fadin “proceed” da yai hakan ya sanya PA din fadin “your schedules for today is as follows… 1:00 PM Lunch meeting with potential investors regarding Dominion Auto’s expansion, 2:00 PM Inspection of newly arrived vehicle models in the showroom. 4:00 PM Strategy meeting with senior management, 5:00 PM Preparation and briefing for tomorrow’s court appearance and 6:00 PM Review and approval of pending reports and emails, that will be all for today, sir.” can kuma se yace “also… sir regarding the girl that..” daga masa hannun da omair din yai ne ya sanya shi yin shiru da bakin sa yana me jiran Jin abinda xe ce masa “Cancel the 1 PM meeting, Push the 4 PM to tomorrow and make sure I’m not interrupted” dan Shiru PA yai kafin yace “ohk sir..” ya nufi hanyar fita daga office din kamar daga sama yaji yace “call the receptionist” nan ma ya amsa masa da Ohk sir. Duk wannan abun da ake Nasir na zaune ya saki baki da hanci yana kallon ikon Allah . After a while se ga knocking din receptionist din nan, can kasa kasan makoshi ya furta “come in” nervously take tafiya dan yaune karonta na farko da ta taba shiga office din sa kuma gashi ta san ba alkhairi bane kiran da yai matan ba, after kusan 2mins da shigowar ta ya sauke medicated glasses din sa ba tare da ya dago ba ya fara magana “who came here yesterday?” Ya jefa mata tambayar, Jin ta yi Shiru ne ya sanya shi dago kyawawan idon sa yai mata wani sharp kallo daya sanya xuciyar ta buga wa, kusan a fusace a kuma gadarance yace “I asked you a question.” Murya ba rawa tace “S-sir… a girl came. She said she found your wallet but” “But?” yai interrupting dinta coldly, ta hadiye wani abu daya tsaya mata a makoshi sannan ta cigaba da fadin“She didn’t have an appointment, so I told her you were unavailable.” “She came all the way here… to return something that belongs to me amma you sent her away?” nan ta shiga defending kanta da fadin “sir, it’s protocol. No one sees you without” Protocol?” ya tambaya sharply kafin ya kara da cewa let me make something clear, If someone walks into my company with honesty you don’t send them away like they’re nothing.” “I’m sorry, sir..” ta fada kamar zatai kuka Lura da nazir yai ba daina mitar abun xeyi ba ya sanya shi fadin “Kinga dismissed we will handle the situation” shi dai be kara cewa komai ba se maida hankalin sa da yai can smartphone din sa, da kamar kar ta tafi ammah da ta tuna yadda take Jin labarin kusancin nazir din da shi se ta fice don tasan tunda nazir yasa baki toh an yafe mata har gaban abada… “Nazir get out of my office” banza nazir yai masa kamar beji me yace ba, ajiyar xuciya yai ya dauke idon sa daga kallon nazir din, gabadaya friend din nasa sai testing patience din sa yake more especially wanna dawowar da yai Nigeria don he’s just finding any possible excuses da xe yi amfani da shi don ganin yayi getting on his nerves, don dai shi ba biye masa yake ba amma da tuni sunyi hannun riga, shiru ne ya wanxu na kusan 5mins can dai nazir ya maida kallon sa kan abokin nasa yace “look omair saboda wallet zaka ringa acting haka? A zafafe ya juya ya kalli inda nazir ke zaune yace “keep your damn mouth quiet karka karasa batan rai pls, my concern is that my contact card, membership card and my driving license are all inside the wallet and kaima kasan how important those items are” ya fada looking so disturbed and annoyed, er dariya nazir yai kafin yace “toh dai ka yakuri, kama gode ma Allah yarinyar me gaskiya ce coz da ba haka ba da ba abinda xema saka ta taxo nan talk less of emailing you” “look it doesn’t matter” ya fada yana me kallon wani direction din daban “bara zanma KB magana se a bashi address din ta yaje ya amsa, is that Ohk for you?” A takaice yace “no” dafe kai nazir yai yace “Wallahi omair kafi yaro dan karami damuwa, kai ba’a taba birge ka koh? Toh shikenan do what suits you” yana fadin haka ya dau belongings din sa ya fice daga office din, don daman yana nan patient suna jiran sa. Tsaki omair yaja yana jin ransa na mugun baci, saboda batan wallet dinnan nasa jiya se kwana yai a apartment din nazir gashi harta logage dinsa a cikin hotel room dinsa yake don kayan da xe sa ma da wasu kayan amfanin sa se da suka tsaya suka siya a wani supermarket even though nazir yayi insisting da yai using nasa outfits din ammah yace shi sam baze saka kayan nazir din ba duk da ko kayan sabbi ne fill a ledar su. Wayarsa ce tai kara alamun shirowar message, a hankali ya bude kyawawan idanun sa ya daura a kan screen din wayar tasa, tsaki yaja bayan ganin message din nata, daman ya san message din ta ne don tunda ya kunna wayar tasa ita da en MTN suke rige rigen masa message, batai worthing time din sa ba don haka bema bude ya karanta message din nata ba, after a while ya kara tunawa da wallet din sa that’s with a stranger hakan ya sanya ransa kara baci don haka ya kai hannu ya dau wayar direct cikin email din sa ya shiga wanda tun jiya yaga email dinda tai masa amman ya ki yin reply saboda he doesn’t feel like doing so, after a while yai replying da “Ohk, bring it yourself ” yana tura email din ya dire wayar a gefe gami da mikewa tsaye ya nufi kan full body massage chair din dake office din ya zauna yana me adjusting necktie din da ke wuyan sa, sam jiya be samu damar bacci a apartment din nazir ba even though daman tun can shi he’s a night owl ga kuma surutun nazir ya cika shi da shi wanda se da akai sallar asuba sannan nazir din ya kwanta, shikuma 8 ya taho gun aykin ba tare da ya bi ta kan nazir dake ta sharar bacci ba, shine kuma by 11 ya biyo sa nan office din nasa ya cigaba da takura masa…….. Dan Allah wa xe raka ni muje muyi ma Yasmine duka ne? yarinyar sam bata da karsa shi😒 Toh dai ga me wallet ya bayyana Amman fa kamar bakin haki gare sa😒 Gaskiya naso ace saddiqa ta kira en hisba sunyi gaba da ita😏 Su hajja anxo an kwashi girki Harda takeaway amman still ana taba bakin hali….. INUWAR KADDARA (THE SHADOW OF DESTINY..) By moon🌚.. Chapter 5: One Saw a Liar. The Other Saw a Future. YASMINE….. Gama wanke dishes din keda wuya wayarta dake cikin aljihun rigar ta ta fara ringing, da sallama bakin ta ta kai wayar kunne, daga daya bangaren saddiqa tace “ynx email ya shigo, wai yace ki kai masa can din” dan jimm yasmin tai kafin tace “toh shikenan na gode” daga haka sukai sallama, kamar daga sama taga nazli ta shigo cikin kitchen din, ointment din da mami tace ta bata tun dazu ta mika mata ba tare da tace mata komai ba, amsa yasmin tai tai mata godiya, instead of nazli din ta fita daga kitchen din se ta haye kan chair din dake kitchen din ta zauna ta cigaba da danna wayar ta a nan gun, ita dai yasmin ta cigaba da goge gogen ta, after some minutes se ga mami nan ta shigo, turus tai tana kallon nazli that was busy pressing her phone bama ta san da shigowar mahaifiyar tata ba, bata ankara ba taji an fizge wayar tata daga hanun ta, da sauri ta dago kai, hada ido tai da mami dake kallon ta rai a bace tace “get out” ba musu nazli ta mike daga kan kujeran kanta a kasa ta bar kitchen din, mami ta bita da ido har ta fice kafin daga bisani ta maida kallon nata kan yasmin da ta maida hankalin ta kan abun da ke gabanta tace “bahar zata kawo takeaway a xuba ma hajja abinci a ciki” tana fadin haka ta fice ta bar kitchen din ba tare da ta jira amsar yasmin din ba. Se guraren karfe 4 sannan su hajja suka tafi bayan an masu packaging takeaways din a cikin basket, suna tafiya ita da bahar suka kara tsaftace gidan yadda ya kamata suka saka turaren wuta a ko wani lungu da sako na cikin gidan, bayan tayi sallah ta ninke prayer mat din ta aje shi kan bedside drawer, dakin da bahar take ciki tai knocking a hankali sannan ta dan ja gefe ta tsaya, bude kofar bahar tai da alamu itama bata dade da idar da sallar ba don ta hango prayer mat a floor din dakin, “ummm aunty na idar, daman na xo nai miki sallama ne” ta fada tana me wasa da gefen hijab din nata, daman bahar din ita ta sanar mata da sakon mami na cewa if ta gama aykin taje habu ya maida ta gida, murmushi bahar tai tace “toh Allah ya kaimu gobe da safe journey my dear” daga haka sukai sallama ta fice, gabadaya se taji wani iri da taga mami bata wani kulata ba se take ji kamar tayi mata lefi ne, tana fita ta tadda habu nata faman goge daya daga cikin motar gidan, a hankali take takawa kamar bata son yin tafiyan don tana tuna cewa gida zata koma se mood dinta ya kara baci, ko da ta shiga motar se tunanin yanda zata cema habu ya aje ta a hanyar wannan car company din take don so taje ta bayar sannan ta wuce gidan, bata Jin zata iya fada masa cewa ya sauke ta a wani gun don haka tai shiru bata ce masa komai ba. Ko da yai dropping dinta se da ta tabbatar ya yi nisa sosai sannan ta tsari adaidaita ta kwatanta masa gun da ze kaita don akwai kudin da mami ta bata a pocket din ta…. Ta tsaya a gaban Dominion Auto karo na biyu, amma wannan karon xuciyarta tana bugawa da sauri fiye da jiya. Yau batare da kauyanci ba kai tsaye ta nufi gun receptionist

Chapter 4 of 10