gashi ya bude kofar, kallon sa ta shiga yi sama da kasa, sanye yake da dark brown jallabiya, ajiyar xuciya tai kafin tace “ba zaka fito ka gaida dad din ka ba?” Bace komai ba se nufar kofar fita da yai ita ma ta mike ta bi bayan sa, daidai ze murda handle din kofar aka budo kofar, daddyn sa ne ya bayya na fuskar nan tasa a hade wanda sosai kaman sa da omair din ya bayyana, matsawa yai baya sannan a shake yace “welcome bac..” ayy daddy be bari ya karasa ba ya dauke shi da wani marin da nan take fararar fatar sa ta koma jajir, ko hannu be sa a face din nasa ba coz beyi mamakin hakan ba, da sauri mami ta nufi daddy tana fadin “dan Allah ka yakuri, calm down please ka bar” da sauri ya daga mata hannu yana huci hakan ya sanya ta yin shiru tana me girgiza ma omair din kai alamun he should not act bad. Da kakkausar muryar sa ya fara magana cikin fada yana fadin “who the hell do u think you are ehh? You broke an engagement with your sister just like that, do you think our family is a joke? Ko an gaya maka cewa kai ka haife mu ne? To bari in fada maka wani abu tittle din da kake ji da shi kake kuma daga kai saboda shi ni na baka shi and if I wished zan iya amshe shi a ynxn nan. saboda kai ba wanda ya isa da kai shine har zaka je ka samu yarinya kace mata wai ba zaka aure ta saboda tsabar baka da kirki kai burin ka kawai ka kunya ta ni a bainan nasi koh? Baka taba Jin magana ta if nace kai abu indai be maka ba toh kai ba zaka taba yarda kai ba for goodness sake me aybun suhaila da xe ce wai ba xe aure ta ba bayan duniya ta gama sanin wannan hadin eh?” Ya fada looking at mami da idanun ta suka kada sukai jajir sannan ya dauke ido daga kan ta yace “what am i even expecting from you bayan kece kika kitsa masa all these? ke ce kika ja komai kece dan hak..” calmly omair yai interrupting dad din nasa da fadin “all I said was am not marrying suhaila because Im not interested and I believed that I have the right to do so, so please sir stop blaming my mom coz she knows nothing about dis,” baki bude daddyn nasa yake kallon sa kafin daga bisa ni yace dashi “alrigh then, kaje ka auri duk wacce ka gadama if you wish ma ka zauna a haka but I promised you that bazan kara saka ka dole ba, ita da take saka duk hakan se ta san yadda zatai da kai” yana fadin haka ya fice daga dakin a fusace. Mami ce ta kalle sa kafin tace “why omair? Why would you talk to him that way? Mesa zaka ma masa magana bayan kasan duk hakan be kamata ba ehh? Kaga dai yanxu me ka ja for talking back koh?” Without looking at her yace “Im so sorry mother but I can’t resist seeing him blaming you for what is not your fault” ajiyar xuciya mami tai kafin tace “your grandma and others are coming by in the next one hour, dan haka please ka kama kankan ay komai a hankali kaji?” nodding kansa kawai yai without uttering anything coz ba abun da xe hana sa magana more especially yaga ana neman disrespting mom din sa….
Karfe 5 dot motar su hajja ta iso gidan, dis time around da uncle ameen wanda ake kira da Dr kuma kani ga daddyn su omair mahaifin sulhaila and yusra se matarsa aunty fiddou da kuma hajja baba da karama, ko da suka shio gidan se faman hura hanci take har suka isa cikin baban parlon daddyn, haka nan aka shake su da kayan ciye ciye kala kala ammah ko kalla ba suyi ba gabadaya jira kawai suke daddyn ya fito suji me xe ce akan wannan alamarin daya faru. Ko da ya fito ya gaida hajja ta amsa ciki ciki, ita ta fara maggana tana share kwallar da ta xubo mata “surajo mesa kai da danka kuke gudun hada jini da xuri’ata ehh? Haka shekarun baya kai wannan abun yanxu kuma tarihi ya kara maimaita kan sa? Ko dai kaine ma kace masa ya fasa ko kuma matar ka ce tai hakan don ta hada sa da waennan en uwan nata dake kama da aljanu? Toh Wallahi in ma ita ce ko kaine dukan ku baku isa ba don aure kam se anyi shi wlh..” daidai nan omair ya karaso cikin parlon, zama yai a kasa ya gaida su, ba wanda ya amsa masa se uncle din sa da hajja da ta amsa kamar bata so, ita ko aunty fiddou ji take kamar taje ta hada kansa da hango don tama fi er tata shiga tashin hankali da wannan abu daya faru, ita kuma hajja karama bata ma san me take ji ba don ita xuciyar ta da brain din ta ma baya tare da su don ko tuni ta tafi tunanin abin da ya faru shekarun 32 da suka wuce iwal haka. Dr yai kasa kasa da voice din sa sanna “hajja me ya kawo wannan maganr pls? be kamata Ana maimaita abun da ya faru baya ba let’s bygone be bygone mun? Beside ya fadi ra’ayin sa ne kawai so ba lefi yai ba ne ba, she’s still his sister ko ya aura ko be aura ba ba abinda xe canza hakan kuma…” cikin zafin rai hajja ta da katar da shi da fadin “anya ameenu ba’a canza mun kai a asibiti ba? er taka kake so ka bada gudu nmawar ballawa xuciya se kace ba jinin ka ba? Toh Wallahi kar ka kara saka bakin ka anan in dai kasan ‘baraka zakai” tana gama maganar ta maida kanta kan omair da tuni yaji kansa ya wani yi masa nauyi tun bayan da hajja ta fara daga murya don sam be son hayaniya kuma duk sun san da hakan don tun yana yaro da wannan dabi’ar ya tashi. “Omair” Hajja ta fada lowering her voice, “na’am” ya amsa ba tare da ya kalle ta ba, kowa na parlon kallon sa kawai yake banda mami da tunda tai kasa da kanta bata sake dagowa ba, daddy kam ji yake kamar ya gaggaura masa mari “gaya mana mesa baka son auran suhaila kuma? tayi maka wani abun ne?” Kusan 10 secs be ce komai daddy da haushi ya cika sa yace “ba magana ake maka ba” da sauri hajja ta daga masa hannu kafin tace “ba ruwan ka surajo ka daina masa tsawa” “she did nothing wrong, kawai bana so ne kuma..” daga haka yaja bakin sa yai shiru. Dogon numfashi hajja ta ja kafin tace “ka tabbatar da abinda ka fada gaskiya ne ba wani abun kuma a kasa?” Gyada mata kai yai kawai, daga haka hajja tace ”ya fadi iya gaskiyar sa don haka wannan magana babu ita yanxu tunda yace be so ay nasan ita suhailar na da masu son ta koh? Se ta kawo wani ai mata aure da shi” da sauri aunty fiddou ta dago kai tana kallon hajja da wani expression a fuskarta, sam batai zaton haka daga gun hajja ba, don se da ta kira ta na kusan kwanaki ta ringa xugata akan cewa mami ce ta hada komai kuma ita hajjar sosai ta hau ta zaune, don she tot ma zata saka a daura auran a nan cikin gidan daddyn ammah se gashi ta canza direction? She never saw that coming sam daman mijin ta sallamemmme ne don Dr ko me omair ya ce baze taba musa masa ba don yana kaunar yaron tun yana karami, “Hajja mu ne fa manyan sa ba shisa don kawai yace beso se a biye masa? toh me yake nufi damu ehh, gaskiya a kara duba wannan lamarin” daddy ya fada looking so serious don ransa ya baci da wannan abu da tai, “surajo dakar ni, nace tashi ka dake ni tunda ka maida ni kayan banza kayan hofi, dukan ku kunfinison su ne ko me kuke so ku ce mun ehh?” Shiru daddy yai yana huci, something most be done coz baxe bar wannan maganr haka ba, xe daura masu aure ba tare da sanin hajja ba don yasan ita tana son auran kawai dai son da take ma omair ne ya sanyata mance duk kalar son da tai ma auran suhailan da omair din. “Am sorry to say but hajja dis is not fair and zan daura masa aure da suhaila ko yana so ko be so saboda hakan shine ya dace” baki bude hajja ta tsaya kallon sa kafin tace “auhoo ba shakka, ashe surajo ba dadi abun sanda kaje ka auro mana bare ka bar shakikiyar ka kace bazaka aura ba akwai wanda yai maka hakanne ehh? Se kai shaffafe da mai zaka ce kai baza’a maka ba ko? Toh Wallahi kaima se ka dandana kaji daman abun da kai shi za’ai maka, ba uban da ya isa ya daura ma jika na aure se dai in shi yace yana so, haba se kace a garin gaba gaba muke? Yace ya fasa ba se ay hakuri ba wai kai sanda ka xuba naka zamanin haka akai maka ehh surajo? Toh daura masa auran tunda ni ban isa da kai ba” tana gama fadin haka ta figi mayafin ta ta kalli hajja karama tace “xo ki maida ni gida” ba musu hajja karama ta mike ta nufi bayan ta, mami ma ta tashi don yi masu rakiya ammah hajja tace “rike kayan ki ban bukata” Jin haka ya sanya mami dakatawa, har hajja ta fara sauka daga stairs se kuma ta juyo baki bude tana kallon aunty fiddou da har yanxu she’s seating, ji take kamar ta kwalla kara ko zata ji sanyi ranta, yanxu ya zatai da mutanen data gamai wa bragging akan cewa omair suraj owner of dominion outo shine xe auri yarta? Dan gayu dan birni kyakyawa ajin farko wanda ake suma a kansa? A ranta ta ayyana cewa ko komai nata xe kare se ta tabbar cewa omair ya auri suhaila “me kika wani zauna kamar gurguwa?” Muryar hajja ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga, kamar an caka mata allura haka ta tashi fuuu ta raba ta gefen hajja ta wuce ta barta nan tsaye baki hangame. Su hajja na tafiya yai shirin nufa office don daman yana da abun yi wannan stupid zaman ne ya sanya shi be tafi ba. yana fita parlon kasa ya taddata tana saka turaren wuta a parlor kallon daya yai mata ya fice yana jin ransa na kara baci don ganin ta da yai ba karamin kara bata masa rai yai ba…..
Still on free pages…..
INUWAR KADDARA (THE SHADOW OF DESTINY)
By moon🌚
Chapter 9: What If He Walks Away?
*******
After a week su inna suka koma can kauyen su don jikin Abby yanxu da sauki an saya masa reclining wheelchair kuma hakeem xe tura magabatan sa don kai kudin auren sa da kaunar sa yasmin wacce a yanxu ta gama sakin jiki da shi sosai he’s more than a boyfriend to her, he’s her home her safe place, bata Jin zata iya auran wani daban in bashi ba domin shi din me mahimmanci ne a rayuwar ta. Duk da an bashi ita hakan be sa ya yawaita xuwa gidan su ba, bawai don ba ya so ba se don lura da yai cewa ita bata son yawan xuwan nan duk da dai shi din be ki ace ya shafe shekaru yana kallonta ba amma kuma tunda ya fuskanci hakan ya ja burki da xuwan don befi sau 4 ya xo gabadaya ba…
Ammah tsaye bakin window tana hangen professional masu ginin dake ayki ka’in da na’in, yau kusan kwana uku da fara sabunta gidan nasu wanda duk aykin hakeem ne wanda shi so yai ma su tashi daga wannan gidan ammah Abby yaki, tabbas tasan cewa xuwan hakeem rayuwar su alkhairi ne ammah a ranta take Jin wannan alkhairin ba kan yasmin ya dace ya fada ba, don tunda a ka kawo zancen cewa hakeem ya na neman yasmin da aure ta kasa cikakken bacci har wani fadawa tai don bakin ciki da takai ci, gashi bata samun bacci me dadi don data kwanta se tayi mafarkin yasmin da hakeem da dansu me kama da larabawa cikin daulaa don haka duk ta tayar da hankalin ta, taya za’ai tana ji tana gani er kishiyar ta ta tafi gidan hutu ta barta da yayan ta a wahale? Da ranta da lafiyar ta bayan kuma ga ita er tata duk da tana da kananan shekaru ammah still ay ita ma zata iya zaman aure kuma ita ma tana da kyan nata ba wai ba tada shi ba. Tunanin hakan ya gama jagula mata rai, hijabi ta dauka ta fice ta nufi hanyar waje, kai tsaye gidan neighbor din ta ta shige maman daddy, tana isa ta tadda ta tana kashe charcoal alamun ta gama girki, kujerar tsuguno ta janyo ta zauna ta zabga uban tagumi, baki bude maman daddy tace “me zan gani haka ni rakiyaa? wannan uban rama da kikai fah? Kinga yanda kika koma kamar bulalar mayu?” Ta fada tana tafe hannu, wani abu me daci ammah ta hadiye kafun tace “wallahi maman daddy ko bacci bana iya yi sam abun duniya ya bi ya isha ni, kina gani fa da gasken wannan asabar din za’a saka ranar auran nan, in akai auran nan shikenan ni na zama gantalalliya marar galihu da ni da yara na” ta karasa maganar kamar zatai kuka, murmshi maman daddy tai kafin tace haba “maman hafsa? Se kace ba ke ba? Yaushe duk kikai sanyi haka har wannan dan karamun abun xe tayar maki da hankali? Ayy ni shiru nai miki inga ko zaki mun maganar ko kuma ke kin yarda ay wannan abu da ranki shisa ma ban miki maganr ba, ammah tun da kin kawo kuka gidan mutuwa to wallahi se in da karfi na ya kare gun nakasa wannan auran.” Ta fadi tana huci. A rayuwar nan ba wacce maman daddy take so in ka cire ‘yayan ta da kuma mahaifiyar ta sama da ammah don tai mata abun da ko en uwanta na jini basuyi mata ba don haka ko me ammah zata ce tana so bata kasa a gwiwa face ta samar mata da solution. Ajiyar numfashi ammah ta ja kafin ta kalli maman daddy tace “toh yanxu me kike gani za’ai?” Kasa kasa maman daddy tai kafin tace “kin tuna labarin wani malami da na taba baki kwanaki sanda uwar miji na ta sako ni gaba?” Gyada mata kai ammah tai tana zare idanu kafin tace mata “ehhh na tuna shi” “toh gun sa zamu” shiru ammah tai for some seconds ganin hakanne ya sanya maman daddy fadin “nasan fa bakya son ayki da bokaye duk abun ki, dan haka ki kwantar da hankalin ki wannan ba boka bane ba malami ne me temakon fisabillilahi” sosai ammah ta yarda da maganar tata don ita bata son ayki da bokaye don tana gudun wannan karin maganar ta Hausawa dake cewa kaikayi koma kan mashekiya, barin ma ita da ta tara ‘yaya mata. “Wallahi har na ji dama dama maman daddy don da in gaya miki bana iya runtsawa saboda wannan lamarin” “karki damu ayy daga yau ma har da munshari se kinyi, toh amma yaushe zamu Je?” Ta jefa ma ammah tambayar “ay ni ko yanxu ma kika ce muje a shirye nake tsaff” dariya maman dady tai kafin tace ahh harda su azarbabi a lamarin naki? Se dai ki bari gobe don se na hada karyar da zan ma baban daddy kin san halin sa da shegen kwakwkwafi” “hakane kam toh Allah ya kaimu goben” daga haka suka cigaba da tsara yanda tafiyar tasu zata kasan ce…
wannan Kennan…………
A bangaren gidan mami kuwa ita da nazli yadda kasan an zare masu laka haka suke rayuwar, karma mamie don omair tun washegarin wacan ranar ya tattare kayansa ya koma apartment din sa na nan kusa da company acewar sa wai ayki ya masa yawa ne shisa ita kuma mami ta gane cewa don daddy na nan ne ya sanya shi tafiya donko ranar da dadyn ya tafi a ranar ya dawo. Sam mamie bata damu da daddyn sa wanda tun da ya tafi be kara bi ta kanta ba wanda if da sabo tuni ta Saba da wannan halin na sa, don indai ba ita ta kirawo shi ba to be taba kiranta if kuma yai picking call din to a dacin rai yake bata amsa, wanda hakan ya samu asaline daga abunda ya faru cikin familyn nasu wasu shekaru da suka wuce. A bakin nazli mamie take Jin cewa suhaila ta dawo nigeria don ta ga picture din su a status din yusrah sistern suhaila, sosai mamie taji ba dadi don tasan aunty fiddou ce ta hana ta kiran ta tsawon wannan lokacin don ba halin suhaila bane hakan don suhaila na son mamie sosai kamar ita ce ta haife ta ita ma kuma tana ma suhailar kallon er ta shisa ma tun a wancan time din ta bada goyan baya Gun hada auran omair din da suhaila don tasan suhaila bata da wani damuwa don sam batai halin maman ta ba.
bayan dawowar omair he noticed that taste din abincin gidan ya canza, although he enjoys mamie’s dishes ammah wannan ma be san yanda xe musalta dadin sa ba, ya haddace signature din girkin mamie wanda hakan ya sanya tun ranar farkon da ya ci abincin ya shaida cewa ba mami bace tai ba ammah se kuma ya samu kansa da kin tambayar wanda yai din don he enjoyed every single spoon na abincin shisa be ma damu da tambayar ba don sosai yake jin dadin sa. Tunda ya dawo be kara haduwa da yasmin da yake ma kallon someone da take Jin kanta kamar ta fi kowa ba se watarana da yamma guraren karfe 5 ya gama ayki a system din sa jikin sa sanya da wata ash singlet wanda ta bayyana muscular body din sa me mugun daukar hankali, bakin window yaje ya tsaya hannun sa daya rike da cup din coffee while dayan kuma ya xura shi cikin gashin kansa wanda ya mugun gajiya da shan gyara yana massaging din sa a hainkali. Kanta idanun sa suka fara sauka tana tsaye jikin mota tana waya tana dan murmushin da ya sanya dimples din ta duka guda biyu lotsawa, samun kansa yai da shiga bacin ran da be san dalilin shiba, gashi kuma ya kasa barin bakin window din on top of that se ya samu idanun sa da binta da kallo, kamar ance ta daga kai sama kawai ta hango sa, ayko nan take idon su suka gauraya cikin na juna kasa tai da idon ta da sauri tana jin xuciyarta na bugun saba’in saba’in don batai zatan ganin sa ba, shima barin window din yai yana me kara saka fingers dinsa cikin gashin sa amman wanna karan ba a hankali ba rather with frustration. Can kasan makoshi ya furta “damnn it”, what am I doing? Ya fada yana me dire coffee din hannun sa kan bedside table, takaicin sa daya data hango shi yanxu se ta dauka kallon ta yake, yaja karamin tsaki yana me kara jin haushin kansa, her presence annoys him, her calmness irritates him her silence feels too present, indai yarinyar nan zata cigaba da zama a gidan nan toh dole se dai ya koma nashi apartment din…..
**HAKEEM**
Zaune yake kasan carpet yana cin fruits din da maid din gidan ta kawo masa, saman kujera kuma mahaifiyar sa ce wacce suke kita sa ummi ke zaune cikin shiga ta alfarma tana masa magana cikin sanyin murya “duk da nasan baka damu da zancan mutane ba ammah still ina me kara ja maka kunne da yi maka nasiha, indai kasan you can’t protect her from your family member’s bad mouth gwara ka hakura ka samu daidai hierarchy din ka, Im not againt your marriage ammah kawai ina me kara tuna maka cewa su waye dangin mahaifin ka, kaine kawai gatan ta kaine zaka iya protecting din ta kuma in ka sake ka bada kofar raini to shikenan za’a samu matsala don haka ina me tunatar da kai karin maganar malam bahaushe da yake cewa se bango ya tsage kadangare ke samun damar shiga, Kazama very strict a kan duk wanda xe takura ma matar ka” murmushi hakeem yai yana me biting apple din dake hannun sa kafin yace “I assure you mother bazan taba barin yasmin ta sha wuya ba in sha Allah” “toh gwara dai, Allah yai maka albarka ya kuma tabbatar da alkhairi” ya amsa da ameen sannan ya mike don yin shirin fita ayki. Har ya kusan fita ummi tace “yauwa hakeem na manta i wanted to send you to amina’s house tun jiya amman na manta, yanxu tunda zaka fita se ka kai mata sakon pls” sosa kansa yai yace “nasan na mata lefi don na mata alkawarin sake komawa amman ban kara ba” tabe baki ummi tai kafin tace borin kanya in kaje can ka mata ba ni ba, ka bude deep freezer akwai wasu medium bucket din fura da kuma manya manya na nono ka dauki guda biyu ka kai mata sune sakon nata” tana fadin haka ta wuce upstairs..
Horn yai bakin gate din gidan, after a while se ga gateman ya leko ta karamun gate, ba jimawa kuma ya koma ya bude babban gate din don an sanar da shi cewa ya bude masa gate din. Kai tsaye Hakeem ya nufi kofar shiga parlon ya danna bell din, ba’a wani jima ba me aykin ta bude masa kofar, tai leading din sa har xuwa parlor sannan ya zauna, can se ga matar gidan ta fito, tun daga upstairs data hango sa take murmushi gamida fadin ”wata sabon gani wato dan zaka angwance shisa kake tai mana yanga koh?” sosa kai hakeem yai gamida yin kasa da kansa yana murmushi, har kasa ya rissina kafin yace “ina wuni mami” se da ta zauna sannnan ta ce lafiya lau hakeem ya gida ya su rumana da ummin taka?” “Sunanan kalau kalau Alhmdllh” “masha Allah bara na sa a kawo maka ruwa” da sauri yace a’a mami da kin barshi wallahi i’m Ohk” “to se ka sha” Murmushi yai kawai, tana fadin haka ta mike ta nufi kitchen. Can ba jimawa se ga daya me ayki tata ta taho kanta a kasa tana tafiya hannun ta rike da try din fruit da drinks, tunda ta nufo sa yake kallon ta da wani kalar expression a kan face din sa, “how’s This possible? What on earth is she doing here? Me take a nan gidan?” ya jefawa kan sa tamabayar da be san amsar sa ba, da kyar ya iya dake wa ya ambaci sunanan ta da wani kalar lafazi da shi kan be san cewa yana da shi ba, deep down his heart yake hoping Allah ya sa he’s wrong, Allah ya sa ba itan bace ba, se dai ina dagowar da tai ne ya kara tabbatar masa da cewa ita ce, ita ce ke aykatau a gidan cousin sistern mom din sa? Toh amman me yasa ta boye masa? Hakan na nufin ba shida amfani a gun ta da har take wannan aykin ba tare da ta sanar masa ba?. Ware idanun ta tai sosai after having an eye contact with him, bata san sa’addah ta aje try din ba ita ma ta zauna kasan carpet din warwas kamar wacce aka cirewa laka a jiki, nan take komai da ya saba fada mata ya shiga dawo mata kamar yanxu yake fada mata “Yasmin in akwai abun da na tsana a