jiki ba kwari don har yanxu bata gama recovering daga marin da ammah tai mata ba, mami ta dube ta cikin kulawa tace “morning jasmine how’s your night” “Alhmdllh” ta fada takaice, mami tace taje kitchen akwai breakfast dinki acan, godiya tai ta tashi tana jan kafa ta bar gun, mami ta maida duban ta kan nazli dake pressing phone din ta tace “je ki ki duba omair tun da ya dawo jiya be fito daga room din sa ba” haka nazli ta mike tana turo baki don jiya se da ya kusan mammake ta akan ta batai masa knocking ba. Tana shiga parlon sa taga baya nan, don haka tai yunkurin nufa dakin da tasan definitely yana can, daidai ta taba handle din kofar se gashi nan ya bude kofar, sanye yake da wani hoodie white color wanda sosai yai kyau fatar sa me kyau da sheki ta kara bayyna wanda hakan ya sanya nazli furta “woow brother kaga yanda kai kyau kuwa?” Ta fada tana kara admiring brothern na ta. Cikin dacin rai omair yace “what?” “Ba komai u just look good ne as always” ta fada tana turo baki, juya kyawawan idanun sa yai gamida sakin wani karamin tsaki kafin yace “what brought you here?” “Ohh mami ce, she said I should call you tana downstai..” be jira ta karasa maganar ba yai banging kofar tasa wanda saura kadan ya hada da nata face din, ayko ta koma gun mami tana hade rai kamar wanda aka daka. Cikin natsuwa yake taka stairs din idanun sa na kan smartphone din dake hannun sa, fuskar nan tasa a hade but looking handsome as always. Zama yai a kasa kusa da kafar mami ya gaida ta cikin harshen Turkish despite ya gaishe ta daxu da subh, amsa masa tai cikin natsuwa tace “are you not hungry? Na san jiya ma tun Fettuccine Alfredo din da kaci baka kara saka komai a bakin ka ba se coffe” without looking in to her eyes yace “I wasn’t hungry yesterday shisa, but I will make tea right away” yana fadin haka ya mike ya nufi haryar kitchen. isowar sa bakin kitchen din yai daidai da fitowar yasmin wacce ke rike da jug of pineapple juice a hannun ta, duk cikin su ba wanda ya lura da wani coz duk idanunsu da kuma tunanin su basa a tattare da su, wanda hakan ya sanya su yin kicibis da juna, ayko nan take drink din dake cikin jug din ya xube jikin white hoodie din nasa “ Subhanallah, Im so sorry I didn’t mean to, I didn’t see you.. I” yasmin ta fada cikin tashin hanakli. Uffan be ce da ita ba se ma stepping back da yai slightly gami da kurawa stain din dake jikin rigar tasa ido wanda ya kara saka ta feeling so guilty coz expression din face din sa was unreasonable yet distant cold. Ana haka se ga mami ta karaso, bayan fuskantar abun da ya faru ya sanya ta maida kallon ta kan yasmin kafin tace “jasmin, are you okay badai ki ji ciwo ba ko?” Ta fada very gently, “ehh mami, Im sorry ban kula bane ba shine na..” Shiru tai da maganar ganin Omair ya bar gun without a single word, tai kasa da kanta tana Jin ba dadin abun da tai masa, muryar mami ce ta tsinkaya tana fadin “karki damu kanki kinji, don’t bother your self kinji? Coz it was an accident, ba wanda ya wuce yin haka” jiki a sanyaye tai nodding head din ta kafin tace “toh mami, bari ma gyara gun” tana gama fadin hakan ta bar gun ita kuma mami ta koma gun zaman ta fuskarta dauke da murmushi. Se da lokacin sallar juma’ah tai sannan ya fito don xuwa masallaci, don tea din nasa da breakfast din sa ita da kanta gai masa don tasan tunda ya koma baxe kara fitowa ba se abu me amfani sosai, mami ta dube sa kafin ta ce da shi “har ka shirya kenan?” A takaice ya bata amsa da “ehh” daga haka yai mata sallama ya nufi downstairs a ranta tana ta faman jujjuya maganganun da hajja da aunty fiddou suka kira ta suka gaya mata yau da safe. Duk da yasmin na son komawa gida ammah haka ta daure ta jira har habu ya dawo daga masallacin jumaah sannan mami ta barta ta tafi, ko da ta isa parking lot wata mota ta gani a parke very close da wacce habu ya saba daukar ta da shi, motar se faman kyalli take, daidai ta nufi motar da zata maida ta gida don habu ya ce ta shiga ta dan jira shi yana xuwa se kawai taga an bude wannan motar da batai zaton akwai mutum a ciki ba, saurin yin baya tai don ta tsorata sosai, kallo daya yai mata ya dauke kai gamida barin gurin, da sauri ta shige cikin motar tana maida numfashi don ta tsorata sosai….
ko da ta isa gida ta tadda innah ce ita kadai a gidan se su hafsa da suka dawo daga makaranta tuntuni, ammah ta tafi tun safiya kaima su abby abincin kalace, itama innah yasmin din take jira ta dawo ta rakata can asibitin, ba yadda innah batai da ita ba akan da ta zauna ta ci abinci ammah se tace mata she’s Ohk ta ci a can inda take ayki, dan haka ko 10mins basu kara a gidan ba suka wuce asibitin. Da mamaki shimfide kan fuskar yasmin take kallon tilin kayan fruits, ruwa, drinks da duk wani abu da marar lafiya ke bukata a space din da abbyn yake, tambaya fall a bakin ta mah kuma ta kasa don bata fiya son yin dogon magana ba more especially da waenda suka girme mata. Jikin abbby yayi sauki sosai, ita dai da ido take ta bin gurin hoping ko zata ga hakeem ammah shiru, tanata zauna agun tana ta faman tunane tunanen da ita kanta bata san dalilin yun su ba. Muryar inna ce ta dawo da ita daga tunanin da take don ta tambayi question din dake makale a ran yasmin din tun daxu “lawal wa ya kawo duk waennan kayan alaton nan gun iye? Ko dai na waencan bayin Allahn ne suka baki ajiya?” Ta tambaya tana satarwa kallon gadon wani tsoho da familyn sa suka kusan cika dakin. Kawu lawal ya kara gyara zaman sa kafin yace “wannan dai likita dan albarka wanda ya biya kudin magani shine jiya bayan kun tafi ya jido duk kayan nan, Wallahi yaron na da matukar kirki sosai don badan shi ba da jiya yunwa ta kashe ni, se guraren 10 sanna ya bar nan gun, Ashe shima likita ne, wallahi sosai yaron ya kwanta mun a rai sosai, dabadan mariya saura wata 2 bikin ta ba ay da na nema ma mata auran sa da kaina in xe yarda kenan” ya karashe zancan yana washe hakoran sa da goro yai wa lahani. “tirr ammah dai lawal akwai ka da son xuciya wanna yarinyar taka me gutsurarren hanci zaka hada shi da ita? ina lefin ma yasaamin er kyakyawa da ita son kowa kin wanda ya rasa” hade rai ammah da kawuawal sukai Jin abin da innah ke kafa, ci gaba da magana inna tai “duk ma ba wannna ba amma gsky wannan yaro dan aljannah ne in sha allahu, jifa kaya kala kala, ya kyauta sosai Allah dai ya biya sa” duk suka amsa da ameen banda yasmin da haka kawai taji xuciyar ta na dukan uku uku. Guraren karfe 1:15 yasmin na zaune kan daddumar da innah ta aro masu gun ahalin wannan tsohon tana laxumi bayan ta idar da sallah se ga doctor sambo nan ya xo duba abby shi da wasu nurses guda biyu, ko daya gama yai ma abby ya jiki sannan ya juya dan barin gun, inna ce tai saurin dakarar da shi da fadin “dakta yaushe wannan dan albarkan ze xo ne? Wallahi ka ganmu nan duk shi muke jira ya xo mu kara masa godiya ammah kaji sa shiru” ta fada tana yake hakoran ta da suka ga duniya, Murmushi dr sambo yai kafin yace “wai doctor hakeem?” Inna tai saurin noddding head din ta ya yin da yasmin ta kara baza kunne tana jiran ta ji me dr sambo xe ce, “ayy iya laraba da alhamis kawai yake shigowa nan asibitin don a asibitin mahaifin sa yake ayki a ragowar kwanakin ammah dai zaku iya ganin sa ya xo nan din if Allah ya nufa” yana gama fadin hakan ya bar gun suma nurses din suka rufa masa baya. Haka kawai ta tsinci kanta da bacin ran da bata san dalilin sa ba, guraren bayan la’asar suna shirin komawa gida kwatam suka jiyo sallamar sa, dago kai yasmin tai da sauri ayko suka hada ido ya sakar mata murmushi iri tai kasa da kanta tana Jin heart din ta na beating very fast gefe guda kuma tana Jin farin cikin da bata aan dalilin sa ba, se bayan da suka gama gaisa wa da su innah sannan tace da shi “ina wuni” ba tare da ta kalle sa ba, amsawa yai cikin sakin fuska kafin ya maida duban sa kan abby dake kwance yace “baba munyi magana da doctor sambo yace gobe za’a sallame ka” se kima yau shiruu yana me adduar Allah ya sa ya yarda da abinda ya xo masa da shi din dan ya kula yasmin gun mahaifin ta ta gado natsuwa da kuma tarbiya gabadayan su idanun su na kan hakeem banda yasmin dake wa sa da fingers din ta ammah kunanta na jiran jin zancen sa, se da ya tattaro natsuwa sosai kafin yace “a asibitin da nake ayki akwai foundation din da suke kula da masu lalurar stroke, in ba damuwa baba zanso ka amince ay transferring din ka xuwa asibitin don kula lafiyar” tsitt kake ji, kowa na mamakin abin da hakeem din ya fada, with shock yasmin ta dago ta kalle sa, he looks so serious, ta kula ba wai don son da yake mata kadai ya sanya yake wa familyn ta hidima ba kawai dai yana yi ne don Allah, da kyar abby ya iya fadin “bawan Allah baka sanni ba ban sanka ba duk da dai ance na Allah basa kare wa ammah wannan dawainiya tayi tayi yawa, i think stroke is my destiny zan cigaba da adduah da kuma godema Allah har sanda zan koma masa kai kuma Allah yai maka albarka” abby ya fada da muryar sa da bata wani fita sosai, yasmin batai mamakin Jin abinda mahaifin ta ya fada ba don ta san halin sa baya son daurawa kowa nauyin sa, “haba malam kai kanka baka Jin dadin yanayin da kake ciki zaka ce a’a? Kadai duba ka gani wannan bawan Allah ya xo zai taimaka ammah kuma kace a’a ay be yi dadi ba abun” ammah ta fada cikin tausasa muryar da yasmin bata taba ji tayi amfani da shi ba, nan su innah ma suka saka baki da kyar abyy ya yarda da bukatar hakeem all in the name of be son ya wahalar da shi. Se da ya tabbatar basu bukatar komai sannan ya mike ya bar gun yana ma abby Allah ya kara sauki. hakeem be kira ta ba se bayan sun koma gida sannan, ko da tai picking call din rasa abun fadi tai dan bata ma son ta Ina zata fara masa godiya ba, tsaf ta gane cewa ba wani foundation ya dai hakan ne don ya taima ki abbyn, “hello your majesty?” Muryarshi me dadin sauraro ya daki kunan ta, a hanakli tace “mun gode sosai Allah ya biya ka da gidan aljannah” se da hakeem ya numfasa kafin yace “jasmine ki daina mun godiya, I did dis all because of Allah kinji? Allah ya bama abby lfy” a hankali ta furta “ameen, toh kaima Kace ameen da adduar da nai maka” Murmushi ya saki me sauti kafin yace “ameen ya rabbi jasmin” daga haka yai mata sallama dan yana da patient din da zai yi attending. Washe gari asabar akai discharging abby, ranar Monday kuma ya koma hospital din su hakeem don duba lafiyar sa kamar yadda hakeem din ya buka kuma har yau be san tana yin aykatau ba don daya tambaye ta mesa ba’a taho da ita hospital din ba se tace masa ambar mata jiran gida ne daga haka kuma be kara tamabayar ta ba har abby yai sati guda yana xuwa asibitin tare da kawu lawal. A bangaren gidan mami kuwa yasmin sosai ta maida hankali ta kan aykin ta, duk wani abun da xe sa tai crossing part da omair se da ta dakile shi don tun wancan ranar har yau bata kara ganin sa ba se dai taga giftswar sa.
NOTE: (Ischemic Stroke shine stroke din daya samu Abby caused by a blood clot blocking blood flow to the brain, wanda bai fiya effecting maganar mutum ba shisa Abby ba wani sosai yake shan wahalar magana ba though yana struggling kadan kadan)….
***********
Soosai sukai sabo me karfi da Hakeem sabon da bata taba zaton cewa zatayi da wani bil adama ba, don duk rashin san maganr ta indai da hakeem ne takan saki jiki sosai saboda he’s very kind and well mannered uwa uba kuma ya iya magana. Indai ba ayki take ba toh tabbas tana makale da shi a waya, a halin yanxu komai nashi ta sani shine dai har yanxu be gama fuskantar abunda take ciki coz yasmin tayi phd a iya nuna komai ba komai bane ba don har yanxu be san tana aykatau ba. A bangaren ammah ko bata samun damuwa da ita sosai saboda inna na nan don koma za tai se dai tai a bayan idon innar. Wata ranar alhamis bayan kawu lawal sun dawo daga asibiti shi da abby da a yanxu ya fara samun sauki sosai don yakan iya motsa jikin nasa duk da yana Shan wiya kafun yai hakan wanda likitan dake kula da shi ya sanar dasu cewa baban nasarace daya fara motsakar arm da leg din sa duk da ko yana Shan wuyan yin hakan sabanin da da sam baya iya yin komai kuma baya ji ko an taba part din nasa ammah yanxu Alhmdllh har maganar sa ma ta fi na da fita, all thanks to Allah and Hakeem. Watarana kawu lawal ya sa aka kira ammah, inna da kuma ita Yasmin din dakin abby, bayan sun zauna inna tace “kai lawal lafiya muna cikin zama zakai mana kiran gaggawa haka? Kodai jikin ibron ne ya kara tashi” ta karasa maganar tana kallon abby da idanun sa ke a rufe. gyaran murya kawu lawal yai kafin yace “Lfy kalau inna don abun alheri ne ya same mu gabadayan mu” Gabadaya suka xuba masa ido banda Yasmin da kanta dake kasa, innah tace “tohh wannan wani abu ne haka iyeeh?” Kawu lawal ya bata amsa da fadin “wannan yaro de likita ya same ni yace yana neman izinin fara neman yasaamin in har ba ai mata miji ba, ni ko nan take na ce masa ba ai mata ba kuma nace na bashi dama ko yanxu yake son a daura aure za’a iya daurawa don yaron ya burge ni daya mutumtani ya xo ya same ni da wannan maganar ya kuma girmamani ya kuma nuna cewa ni uba ne a gun yasamain, haka shima uban yasaamin din yace shi bashida damuwa matukar yasaamin din tace tana so toh ya bada go ahet” ba su inna ba ita kanta Yasmin din tayi mugun mamaki da ya sanya ta dago kai tana kallon uncle din nata coz hakeem beyi mentioning xe aywatar da hakan nan kusa ba though he kept mentioning that he’s very serious about her and he want to marry her amma batai zaton da wuri haka ba don dudu basu fi 2 weeks sa haduwa ba. Inna ce ta rangada buda tana me rungumo yasmin din jikin ta gamida fadin “kai Alhmdllh Allah mun gode maka, daman ance me hakuri shi kan dafa dutse ya kwankwadi roman sa, kai madallah Daman Wallahi ina tai wa yasaamin kwadayin yaron nan dan yaron akwai hankali da mutunta na gaba da shi, toh Allah ya tabbatar da alkhairi don wannan hadi ya ma hadu don ita kanta jikar tawa bata ce a’a ba don yaron masha Allah son kowa kin wanda ya rasa, ita ma baza ma ta fara cewa a’a ba ko yasaamin dita?” Ta kare zancan tana kara manno yasmin jikin ta wacce sam hankalin ta be tare da ita coz tama rasa me za tai kuka zatai ko dariya? Da kyar ammah ta hadiye wani abu me mugun daci da ya tsaya mata a makogaro tsabar bakin ciki da takai ci, ko ba’a fada mata ba ta san hakeem dan masu hannu da shuni ne don ko fatar jikin sa ka kalla zaka tabbatar da hakan, ta ina ma za’ai haka ta faru? Ina ai baze yu ba er kishiya ta auri wannan tsalelen mutumin? kuma da rai na da lafiya na? A’a baxe yu ba Wallahi” ammah ta ayyana duk wannan abun a ranta tana me hura dan hancin. Kawu lawal ya maida duban sa kan yasmin da duk jikin ta ya gama yin la’asar kafin yace “ke! Kinji duk abinda muka fada ko? Ina fatan kema zaki saki jiki ki nuna masa kauna don yaron da gaske yake ba yaudara yaxo yi ba don yace ma nan kusa manyan sa zasu xo” shiru yasmin tai don bata san me zata ce ma wan mahaifin nata ba ga idon ammah dake ta mata yawo a jikin ta don kallon ta take kamar zata cinye ta jira kawai take ta ji me zata ce, mikewa tai ba tare da ta ce komai ba ta fice daga dakin, tana jiyo sanda inna ke sakin guda tana fadin “kai wannan abu ya mun dadi dan bakin ciki yau se dai ya mutu” kusan 10mins tana rike da wayarta karar ringing tone din wayar ne ya dawo da ita daga tunanin da take, as expected shine ke kiranta, har kiran ya katse batai picking ba and she doesn’t know why tai hakan. Gabadaya ta kasa bacci she’s feeling a little bit nervous coz se take ganin kamar zaren ba kalar yadin bane ba but still theirs something she’s feeling deep down about him something very strange something she have never felt before. Tun da ya kira sau uku yaga batai picking ba ya kyale ta kawai don be son ya takura mata sam.
Washe gari ta shirya da sassafe kamar kullum habu yai dropping din ta a gidan mami, ita tai aykin gidan kaff coz bahar ba tada lfy, tun da ta xo ta kula da yanayin mami kamar ba dadi don tayi looking kamar ita ma bata da lfyn. Tun bayan dawowar omair Nigeria familyn dadyn su omair suka tada bori sosai gami da sako ita mamin a gaba kan cewa ita ta xuga dan nata ya ce ya fasa auren Suhaila, yau wannan ya kira yai mata kalar tasa dibar albarkar gobe wannan ma ya kira yai nasa don sun so ma su xo gidan mamin amma mahaifin suhailan ya tsawatar musu don ya ce shi baxe saka omair ya auri er sa don dole ba tunda yace be so shikenan a hakura Allah ya hada kowa da rabon sa don shi sosai yake respecting feelings din mutane more especially omair da bama ka gane yana son abu ko baya so ba. A bangaren daddyn nasu sosai ya bude ma mami wuta akan cewa ita ta kitsa komai saboda wani manufa nata daban and yace mata komai omair ke yi ita ke sangarta shi, sosai abun ya bata mata rai don maganar su hajja da sauran en family be dake ta ba amman na dadyn nasu ya taba ta coz ta dauka shi ne mutum na karshe da xe yarda da wannan zancan amma se gashi yana cikin masu sukar ta. Guraren 12 lokacin yasmin na blending fresh fruits da bahar ta fada mata tai blending ta kuma yi storing a fridge taji kamar motsin mutum, da sauri ta juya ayko da saurin tai kasa da ido tai don bata son ma tana kallon cikin idon sa me bal’in kwarjini, take cikin din ya dauki kamshin turarensa me mugun kamshi, cikin natsuwa ya fara takawa cikin kitchen din hannun sa dauke da mug din da ya sha coffeen da mami ta sanya nazli hada masa, fuskar nan tasa a hade ko kallon inda take beyiba yai dumping cup din cikin sink har cup din na making sound din da ya sa ta dan tsorata kadan, daga haka ya fita daga kitchen din ba tare da ya kara kallon inda take ba. Yana fita ta koma gun cup din ta shiga dauraye wa tana me turo dan karamin pinkish lips din ta don yadda ya tsorata ta ba karamin bata mata rai yai ba. Fitar sa da kusan 3mins se ga mami ta shigo ita da nazli, shirin wani abinci suka shiga yi wanda da ka gani zaka san ba na nan bane ba, ba wanda ke magana cikin su coz har face din su looks so serious, mami ta saka yasmin din ta yanka mata fruits ayko ba shiri ta shiga yin hakan, dining din sama suka kai komai da komai da sukai, mami tace mata kar ta tafi ta tsaya ita da nazli su daura abinci don anjima kadan zatai baki, haka ko akai ita da nazli suka shiga kitchen din suna girkin ba me cewa kowa komai don nazlin ma playing wani Turkish drama tai a ipad din ta while cooking even though ma duk yasmin ce ke yin aykin. Guraren 3 aka xuge gate din gidan, da sauri nazli ta bar kitchen din ba tare da ta bi ta kan ipad din nata ba, kofar parlor ta bude ta tsaya tana kallon mahaifin nata that was on a phone call, yana karasowa bakin kofar ta nufesa tana murmushi da ya kara bayyana kyawun ta, “Hoş geldin daddy” (barka da xuwa daddy) shima ya mayar mata da murmshin gamida da mata side hug sannan yace “Sağ ol kızım” (na gode daughter) daga haka ta matsa masa ya shiga sannan ta amshi dan karamin trolly bag din sa a hannun habu sannan ta kullo kofar parlon. Se kallon ko ina na gidan yake, A haka har suka karasa upstairs inda mami ke a zaune tana jiran karasowar su, mikewa mami tai ta nufi in da mijin nata yake tai ma masa sannu da xuwa ya amsa mata cikin natsuwa, kallon ko ina yake kafin yace mata “where’s he?” “He’s in his room, but would you mind taking shower, eating and resting before you dive into the matter? Coz I could see that you are tired” shiru dady yai for some seconds kafin yace “alright then” daga haka mami ta amshi trolley din hannun nazli sanan ta ce da ita ta je ta sanar ma brother din ta cewa dad din sa ya dawo. Ko da nazli ta shiga part din na sa ba ta samesa a parlor ba, don haka ta karasa bakin room din sa ta shiga knocking a hankali gamida kiran sunan sa, ta shafe kusan 2mins a tsaye a gun before ta bar gun don ta kula be da niyar budewa, ko da ta koma bata ga kowa parlon ba don haka ta wuce can kitchen in da ta baro yasmin na girki. Har daddy yai sallah yai wanka kuma yaci abinci omair be fito ba shi kuma daddy be kara tamabayar mami ina yake ba, satar jiki mami tai ta nufi part din omair din, ko da ta taba kofar se taji shi a rufe alamun ya saka key ta ciki, nannauyar ajiyar xuciya mami ta sake kafin tace “open the door” tana fadin haka ta koma kan daya daga cushion din parlon ta zauna, ayko bayan 40secs se