Share this page
1 / 9
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Compiled by Princess Aysha Muhammad [3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *Bismillahirrahmanirraheem* *Nagodewa Allah mekomai me kowa daya bani ikon rubata wannan littafi nawa me suna *Allah gatan bawa, ina rokon Allah yasa littafina yasamu karbuwa agurinku masu karatu,innayi kuskure kusanar dani da gaggawa domin in gyara ,dan adam ajizine nagode.* *Page 1-10* Azaune take akan dakalin kofar gidansu hannunta dauke da kara tana wasa dashi yayin dasauran yaran makwabtansu suma suke nasu wasan ita kuma tana binsu da ido domin ita Bata da yencin shiga cikinsu tayi wasan yarinyace yar kimanin shekara takwas da haihuwa wacce Allah yajabceta da lalura irinta zubar da miyau sanna kafarta daya dahannunta daya duk ashanye suke intana tafiya tana jefa kafarne yayin da hannun yake makale a kirjinta wannan lalurarce tasa yara da sauran mutanen garin kyamatarta ko wasa basayi da ita sede tazauna agefe tana kallonsu *Asalin labarinta* Ilham bukar shetima shine sunanta na aynihi mahaifinta malam bukar shetima hafaffen garin medugurine acikin garin bama inda fadace fadacen daakeyi ayankinsu yayi sanadiyyar mutuwar iyayensa hakanne yasa yayanke shawara shiga cikin ayarin yan gudun hijira domin yin hijira daga yankinnasu. Bashi kadai bane agurin iyayannasa su biyu ne shida dan uwansa mesuna imamu amma rudin dagarin ke ciki yasa suka bacema juna yayi kukan bakin cikin mutuwar iyayensa da kuma bacewar yayansa Wanda besan awanne hali yakeba shiyasa yarungumi kaddara yayi hijira Acikin ayarin yan gudun hijirarne yahadu da wata budurwa wacce itama ankashe iyayenta( Bata da kowa )me suna maryam tunda suka hadu yake tausayamata sabida ita macece shiyasa yashiga dawainiya da ita har suka shigo garin kano bayan ansaukesu asansanin yangudun hijirane washe gari yakirata gefe inda yashawarceta dasuyi aurene zefi kulawa da ita sabani basu da aure Batare da Bata lokaciba ta amince inda dattawan cikin yan gudun hijirar sukadaura musu aure bayan yabata sadaki nera dubu biyar tundaga lokacin yadukufa gurin kwadago acikin gari har Allah yataimakeshi yakama masu hayar gida me daki biyu acan garin wudil sabida beda halin kamamasu acikin gari be kaunar zamansu acikin sansanin "yan gudun hijirarne shiyasa yakamamasu haya bayan tarewarsu badadewa Allah ya albarkacesu dasamun karuwa ta cikin suncigaba da kulawa da cikin har zuwa haihuwa inda Allah yasa maryam tahaihu lafiya tasamu "ya mace yarinyar kyakkyawace ajin farko sabida daga uwa har uban shuwa arabne sede kallo daya zaka mata kafahimci Bata da lafiya maana nakasasshiyace basuyi kasa agwuiwaba suka samata suna inda taci sunanta ilham bayan suna ilham iyayenta sundukufa neman magani amma duk inda sukaje amsa daya akebasu bazata warkeba tunda da lalurar aka haifeta hakan yasa suka hakura suka mikama Allah lamarinsu ilham na dada girma lalurarta nakara bayyana ahaka har aka yayeta bayan yayetane Allah yasake basu wata 'karuwar inda wannan haihuwarma tasamu mace suka samata sunan mahaifiyar bukar fateema suna kiranta ameera bayan haihuwar ameera basu sake haihuwaba har zuwa yanzu da ilham kede shekara takwas ameera kuma biyar rayuwa suke mecike da tsanani sabida malam bukar me karamin karfine wani lokacin ko yafita bayasamun dakon haka yake dawowa ahaka yakokarta yasa su ilham awata makarantar gwammanti ta pramary ilham na aji uku ameera aji biyu duk à tunaninsu ilham bazata iya komai amakarantaba amma Allahyataimaka yasa tana ganewa sede ko tambayarta akayi bazata iya fadaba sede gwaranci dan harshenta akarye yake. ko amakaranta tsokanarta suke yara sede ameera tatunda taremata dukda itama bawani wayo garetaba ita ilham kuwa sede taita dariya miyau nazuba tadauka wasa suke mata, to ko sundawo gidama yaran unguwa bakyaleta sukeba shiyasa mahaifiyarsu batason ilham nafitowa sabida ko ina hantararta akeyi tun mamansu na magana har tadena sabida tasan *Allah gatan bawane* *Cigaban labari* tanana zaune yaran suka fara tsokanarta itako se dariya take harda kwantawa miyau nazubowa daga bakinta, jiyo hayaniya da mahaifiyarta tayine akofar gida yasa tayi saurin lekawa daki inda tabarsu suna wasa da ameera ga mamakinta ba ilham sede ameera datakeyin homeworke dinta dasauri tadauki hijab dinta tasa tayi kofar gida sabida ta tambatar da ilham akeyi ayko ilai tana fita tayi tozali da ita tana dariya yara natsokanarta suna watsamata kasa bakinciki besa tayi yunkurin hanasuba illa iyaka dauko ilham datayi tashiga gida daita itako baabinda yadameta se dariya take . love you all maman yusuf✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ [3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ _Writting by Zahra Muhammad mahmud_ *Page 11-20* Suna shiga gida kai tsaye toilet tashige daita tsifa tafara yimata sannan tawankemata kai Wanda yasha kasa sannan tayimata wanka tafito daita daki takaita sannan tayimata shafa tasauyamata kaya karkuso kuganta à time din kamar kadauka kagudu sabida kyan datayi. Abinci tazubo mata tafara Bata abaki Wanda ita ilham har zuwa lokacin dariya takeyi sabida intafara dariya tana jimawa bata denaba itako mahaifiyarta kwalla kawai take sharewa natausayin diyar tata ************** Yauma kamar kullum suntaso daga makaranta, ameera narike da hannun ilham suna tafiya yara suna tsokanarta ameera sekuka take musu tana dan Allah kudena metayimuku Wanda agefe daya ita wacce abin yashafa inbanda dariya baabinda takeyi ganin hakane yasa yaran suka cigaba da tsokanarta ahaka har suka karaso gida babansu suka tarar akofar gida yana alwala zashi masallaci ganinshine yasa yaran komawa da gudu sabanin da dahar cikin gida suke binsu Sannu baba mundawo cewar ameera sannunku mamana kushiga gida ina zuwa bari nayo sallah yafadi tareda shafa kan ilham wacce takafeshi da ido ba um ba umum Dashigarsu gida dakin mamansu suka shiga suka tarar da ita ta kabbara sallah ameerace tayi kokarin zuwa daukar buta itama tayo alwalar tazo tabi bayan mamanta sukayi sallah. Tare da yima ilham adduar samun sauki.itako ilham kiciniyar cire safa take har suka idar bata cire KO guda dayaba ameerace taamsa tacire mata sannan mamansu tacire musu Uniform Wanda gaban rigar ilham jike yake da miyau Wanda hakanne yatilastawa rigar kodewa daga gaban wanka tamusu sannan tajika musu garin rogo suka sha bayan sungama sha ne malam bukar yashigo gida fuskarsa ba walwala kan tabarmar dasuke zaune yazauna cike da kulawa maryam take tabayarsa malam meke faruwa naga ranka abace. Yace haba maryam dama haka yara suke biyo ilham baki taba sanar daniba kamar sunga dodo Sun m'aida ita kamar abin wasa haba maryam kinyimin adalci kenan. Maryam wacce tunda yafara magana take zubar da hawaye dakyar tabudi baki cikin kuka tace haba baban ilham menene amfanin insanar dakai indaga hankalinka yarannan badenawa zasuyiba konakai kara gun iyayensu basa kwabarsu to yazanyi ilham de ba ita tayi kantaba Allah ne yayi ta kuma shi dayayita ahaka nasan yanasane daita kuma nayi imani shine gatanta danhaka kaima kazubama sarautar Allah ido inda rabon musha kallo nangaba zakace nafadamaka takarasa zancan tana kuka. Jin maganganunta yasanya jikin bukar sanyi cikin sigar rarrashi yafara magana nafahimceki maryam kuma nima zanyi yadda kikace amma kinsa ba dadi adunga tsokanarta tace hakane amma bamuda yadda zamuyi sede mufadawa Wanda yayita haka sukai ta tatyaunawa agame da matsalar ilham har akakira sallar laasar suka tashi domin bada fatali. love you all 😘 maman yusuf [3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ _writting by Zahra Muhammad mahmud_ *Page 21* *Bayan shekara uku* Kwanci tashi bawuya agurin Allah yaune ranar dasu ilham suka gama pramary school ita da ameera sabida tun suna aji hudu akayima ameera jumping takamo ilham.cike suke da murna daganin ranar dagasu har iyayensu murna suke harda ilham wacce batasan meyakawo murnarba.atamfa 'yar leda babansu yasiyamusu akadinkamusu Riga da siket ba laifi sunyi kyau kuma sunji dadin kyautar da babannasu yamusu na atamfar, ********* Yau watansu ilham daya dagama makaranta suna zaune atsakar gidansu suna wasa yayin da iyayensu suke hirar rayuwar duniya. Yarone yashigo gidan da sallamarsa bayan Sun ansa yagaishesu sannan yadubi malam bukar yace baban ilham ana sallama Dakai akofar gida wani mutumi gabanshine yafadi sannan yace kaje kace ganinan zuwa yaron yamike yafita yayin da malam bukar shima yamike, da sauri maryam tasha gabanshi tace "abban ilham yanaga daga cewa ana sallama dakai hankalinka yatashi kode akwai matsalane. Hannu yasa yashare gumin daya keto masa yace "Maryam banfada mikibane amma wallahi tun watanni uku dasuka wuce kudin hayarmu yakare kuma megidan cemin yayi yabani wata biyu inkawo masa kudin inba hakaba zesa wasu agidan kuma kinga yanzu har wata uku shida yacemin wata biyu nasan yazo karbar gidansane shiyasa kikaga hankalina yatashi. Cike da damuwa take kallon mijinnata tace "meyasa bakason sanar dani damuwarka abban ilham ni aganina abokin kuka shi ake fadawa mutuwa meyasa kaboyemin ? Kiyi hakuri itace kalmar daya iya furtawa yafita kofar gida dan ganin me sallama dashi abinda yaguda shiyatarar megidan yagani atsaye dashi dawasu katti guda biyu tun kafin yayi magana megidan yarigashi yafara magana cikin fushi "sannunka mallakau wannan ay ko gadona gareka se haka ko ancemaka abanza nasamu gidan dazan barka kaita zama batare dakabiyaniba cikin muryar tausayi malam keba megidan hakuri har kasa yaduka yana bashi hakuri amma shi KO ajikinshi karshema wainnan katti yacema sushiga gidan sufito masa dakomai da kowa nagidan kafin malam yayi magana tuni sunshige gidan umma (sunan da ameera ke Kiran mamansu kenan)tana zaune à inda malam yabarta seganin katti tayi suna shigowa kafin tayi magana taga malam yashigo yana share hawaye tambayarsa tashiga yi "malam meke faruwane ? Cikin muryar kuka yace "maryam megidanne yace mufitarmasa daga gida wainnanma dakikaga sunshigo fitardamu da kayanmu yasasu suyi,jeki kidauko mayafinki juyawa tayi jiki ba kuzari tadauko hijab dinta dama kayansu nasawa agana must go suke dan haka dauka kawai tayi tunkafin takai ga nade katifarsu kattinan sunrigata wurgota kofar gida haka suka shiga wurgi da komai n'a gidan tsinke basu bariba daga karshe suka taso su malan bukar agaba shida iyalansa zuwa kofar gida bayan sunfitone sukaga kofar gidan cike da yan kallo manya da yara.makulli megidan yasa yakulle gidansa yawuce shida yaransa kota kansu be biba ganin jamaa nakara yawa akofar gidanne yasa malam bukar fara tattara sauran tarkacensu kama daga tukwane bokiti dadai sauran kayan tarkacen gida yakulle acikin wani buhu katifarma yasa igiya yadaure dama taji jiki yana gama daure katifar yadorama ameera ummansu kuma tadauki gana must go din kayansu tarike hannun ilham har zuwa lokacin kuka sukeyi dukansu harda ameera sabanin ilham datake tafaman sanaartata wato dariya malam bukar buhun kayan daya daure yadauka yace sutaho sutafi sudena zama agurin suna tarawa kansu mutane tafiya suka farayi dauke da kayansu suna kuka yaran garin kamar jira suke suka bisu abaya suna musu ihu sekace sunyi wani laifi kuma manyan gurin bawanda yakwabesu sabida makwabtansu suntsanesu badan komaiba sedan kawai Allah yabasu ilham haka suka cigaba datafiya yaran namusu ihu karshema suka fara jifansu seda sukayi nisa dagarin sannan yaran suka koma Love you all 😘 maman yusuf [3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ _writting by Zahra Muhammad_ *Page 22* Tafiya sukayi me nisa sannan suka sami kasan wata bishiya suka zauna domin su huta. Har zuwa lokacin hawaye bedena zuba à idonsuba Malam ne yakai dubansa fuskar ilham wacce ko baa fadamasaba yasan tagaji da hannu yayimata alama datazo kusa dashi.bamusu tamatso hannunta yarike yafara magana "ilham mu munyarda Allahne yayiki kuma yabamuke badan bayason daya daga cikinmuba kuma insha Allahu masu kinki nangaba se Sun huta à inuwarki kiyi hakuri daduniya aduk yadda tazo miki .yafada yana zubda hawaye itako ko ajikinta danma tagajine danasan baabinda ze hanata darawa wani wata sarka yaciro awuyansa yadauramata awuyanta gami da fadin Allah ya albarkaci rayuwarki gaba daya suka amsa da ameen Umma takatseshi tahanyar fadin malam kayi shuru haka Allah nan kuma shine gatan kowa. Tana gama magana tamike malam ne yace inazuwa kuma bayan hutawa mukeyi,tace wallahi kishin ruwa nakeji shine zan tsallaka titincan inga ko zan samo ruwa, mikewa yayi yanafadin haba ina gurin shine ke zaki neman ruwa zauna inje inkawomuku. Haka tazauna badan ranta yasoba shikuma yatafi debo ruwan yanatafiya yana waiwayensu kamar ze jiyo kuma sede yatafi sunanan zaune suka fara jiyo hayaniya abakin titin gaban umma ne yafara faduwa tana tambayar kanta meke faruwa takejin hayaniya haka kamar bazata jeba cam kuma tamike tanufi gurin tana zuwa taga anzagaye ana kallon wani abu karasawa itama tayi gurin yayinda bugun kirjinta yatsananta tana karasawa gurin INNALILLAHIWAINNAILAIHIRAJIUN Malan tagani kwance cikin jini mota tabugeshi kanshi ya rabe gida biyu ko baa fadamata ba tasan malam rai yayi halinsa yanke jiki tayi tafadi kasa sumammiya love you all 😘maman yusuf [3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ _writting by Zahra Muhammad Mahmud_ *Page 23* Mutanen dake gurinne sukayo kanta domin Bata taimakon gaggawa daukarta sukayi sukasa amota tare da gawar malam .sukuwa su ameera suna zaune Jin shirun yayi yawane yasa ameera mikewa takama hannun ilham suma sukayo hanyar titin zuwansu yayi daidai dazaasa ummansu amota dagudu ameera takarasa gurin tana Kiran ummansu mutanenne suka juyo gareta domin Sun fahimce mahaifiyartace har anhada daita amotar Sun fara tafiya sannan ta tuno da ilham dake can gefen titi har zatayi magana sekuma tayi shuru sabida atunaninta ilham ba inda zataje harsuje sudawo tuna hakane yasa tamaida hankalinta kan ummansu wacce ke kwance rai a hannun Allah. Asibiti akanufa dasu umma emmergency aka shiga daita yayin da malam kuma akayi mutuare dashi tagaban ameera akawuce dashi se alokacin hankalinta yakai gareshi wani gigitance ihu tasaki tayo kansa tana ihu nurse ne suka riketa itako ihun Kiran baba take ahaka har aka shige dashi ciki duk wani me imani inyaga ameera se yatausayamata malam yarasu ga umma à emmergency rai a hannun Allah Dakyar nurse din suka rarrasheta tayi shuru abunka da yaro har wasa tafara. Kwatakwata tamanta da wata ilham hankalinta nakan umma tunda ance mata babanta yamutu. Secan da magariba aka fito da umma daga emmergency zuwa dakin 'yan paralyse domin itama umma asanadaiyyar faduwan datayi takamu da paralyse gabadaya barin jikinta daya yashanye har gefen fuskarta .bayan ansa umma adakinne nurse suka kira ameera zuwa dakin likita, tabayoyi yafaramata kama daga sunansu, daga ina suke, awacce anguwa suke (dayake wainda suka kawosu su suka bige malam. Daga cewa bari suyi sallah suka gudu ) sunansu tafadi sannan tafadi anguwarsu. Abinci likita yasa aka Bata daga nan yasa aka maida ita gurin ummanta gefen gadon tazauna sannan tabi jikin ummanta da kallo har zuwa fuskarta ganin yadda fuskar ummanta tasauya yasa tasanya kuka tana jijjiga umman tana fadin umma.gaba daya dakin bawan da betausayawa ameera da ummanta ba tananan har bacci yadauketa ajikin ummannata. ********** Bata farkaba se dasafe se lokacinne tatuna da ilham dagudu tafito daga Dakin tana ihun Kiran ilham karo sukayi da doctor ganinta afirgicene yasa yariketa yana tambayarta meke faruwa dakyar ta iya fadamasa dasauri yadauketa yasa amota suka tafi gurin dayake banisa amma koda zuwansu va ilham ba alamarta sede kullin kayansu juyo sukayi jiki bakwari bayan sungama duba ko ina nagurin ba ilham asibitin suka koma ameera nata aykin kuka. love you all😘 maman yusuf [3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ _writting by Zahra Muhammad mahmud_ *Page 24* Suna isowa asibitin dakin da mama take suka nufa auna ta likitan yafarayi da mamakinsa yaga ba numfashi atare daita hankalinshine yafara tashi yana gudun kar ace ita ma babu ita awo n'a musamman yashiga yimata sede yamakaro Allahn dayayita yafishi kaunarta innalillahi wainnailaihirrajuiun itace kalmar dayake nanatawa zufa ce tashiga keto mishi ta koina dubansa yakai gun ameera wacce har Yanzu kukan rashin ganin ilham takeyi. Tausayinta ne yakamashi Jan hannunta yayi suka bar dakin bayan ya rufe gawar umman wasu nurse guda biyu yagani yabasu umarnin akai gawar umma mutuware Office dinshi yashiga da ameera bayan Sun zaunane yafara magana " kiyi hakuri kinji kowa dakalar kaddararsa ketaki kaddarar Bata da kyau amma kigode Allah kinji .kai kawai tadagamasa sabida Bata fahimci meyake nufiba duba da kankantar shekarunta. Address dinsu yasake tambayarta tasanar dashi Jan hannunta yayi suka sake fita kai tsaye unguwarsu yaje da ita wani makocinsu yasamu mesuna malan sule bayan sungaisane yake tambayar sa shin koyasan wannan yanuna ameera dago kai malam sule yayi yakare mata kallo sannan yace yasanta yar gidan malam bukarce inafatande lafiya. Lafiya kalau likita yabashi amsa daganan likita yakoro masa bayanin abinda yafaru harda mutuwar umma se anan ameera taji ummansu itama tarasu kuka tasamusu me tsuma zuciyar duk wani me imani shikanshi malam sule kukan yakeyi yakara da fadin jiya jiyannan mutanennan sukabar gidannanfa yanuna gidan ashe tsautsayine yafitardasu Kuka yasake barkewa dashi likitane yakatseshi dacewa malam ba kuka zakayiba sonake ka kaini gidan megari inyimishi jawabi sabida asan yadda zaayi da gawarwakin. Tashi malam sule yayi gami da fadin biyoni muje gurin me garin. Kama hanya sukayi likita narike da hannun ameera ,akafa sukaje gidan megari dayake banisa bayan sungaisa dame gari sukayimishi bayanin abinda ke tafe dasu megari bakaramin girgiza yayi da labarinba duk da besan malam bukar amma yatausayawa rai shela yasa akayi agari akan jamaa suzo fada zaayi janaiza sannan yamike yabi doctor suka dunguma zuwa asibitin da isarsu akasaka gawarwakin amota bayan doctor yagama daukar hotonsu awayarsa sannan yayi cikecike a file dinsu. Kai tsaye kofar gidan megari akayi dasu Wanda yacika da jamaa cikin gida aka kaisu akamusu wanka megari yasallacesu aka kaisu gidansu nagaskiya Wayyo rayuwa kowa nagurin yatausayawa wainnan bayin Allah se addua ake musu nasamun rahamar Allah.bayan anyi adduoine doctor yace zewuce sabida yanaso zetafi gida dan shi acikin garin kano yake ayki yakawoshi wudil. yanemi megari daya bashi ameera yatafi da ita dan zamanta agarin zedunga tuna mata danginta tana shiga damuwa.hakuri megari yabashi akan yayi hakuri zuwa Adan kwana biyu sabida karyayi gaggawar bashi ita daga baya danginsu nagurin iyaye suzo nemansu dan haka yayi hakuri aga abinda hali zeyi. Va ason ran doctor yatafi yabartaba wacce harzuwa lokacin daze wuce kuka takeyi ita ummanta dakyar ya rarrasheta bayan yamata alkawarin zekaita gurinta, naira dubu goma yakirgo yaba megari akan asiyamata kayan sawa .yanacikin maganar ne yatuna da kayansu nabayangari dan haka motarshi yanufa yaje yadebo kayan Wanda bawanda yatabasu sabida bawasu kayan kirkibane. Megari yaba kayan sannan yabukaci da à adanasu kodan gaba. Sallama yama megari yawuce, bayan tafiyarsa megari yasa akashiga da kayan cikin gidan shima shiga yayi rike da hannun ameera yana shiga matanshi sukayo kanshi kowacce burinta yabata ita sabida me gari baya haihuwa dan haka dukansu basu da y'aya ganin inyace gawacce yaba abin ze zama da rigima shiyasa yace dukansu yaba kowa nada iko akanta ameera kenan baiwar Allah . jamaa ina labarin ilham ne ? love you all 😘maman yusuf [3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ _writting by Zahra Muhammad mahmud_ *Page 25* Iham tunda ameera tatafi tabarta take tsaye abakin titin bata matsaba tananan har kowa yawatse bata da alamar motsawa. Gungun wasu almajirai sukazo wucewa sundawo daga yawon bara suna zuwa daidai da ita kawai seta bisu dan ita atunaninta gidansu zasuje tafiya sukayi metsayi Sannan suka iso wani dan kauye dayake suna da yawa shiyasa basu lura da itaba tsayawa sukayi abakin titi da alama tafiyar dasukayi sunyitane dan samun ragin kudin mota baa kauyan zasu tsayaba wata motace kirar akori kura tazo wucewa dasauri almajiran suka fara tsaida motar Motar harta giftasu tadawo da baya ina zuwa direban motar yatambaya. Kano suka hada baki gurin bashi ansa gyara parking yayi sannan yafito yabude musu kofar bayan motan dasauri almajiran suka fara darewa kan motar har sungama hawa ilham natsaye sabida ita bazata iya hawa da kantaba direbanne yawaigo yaganta atsaye atunaninshi tafiyarsu daya danhaka batare da Bata lokaciba yadauketa yasa acikinsu bayan yarufe kofarne yace dasu kudin motarsu naira hamsin hamsin basu musaba sukace Allah yakaimu lafiya zagayawa yayi yatada motar sukadau hanya Tafiya sukayi medan tsayi sannan suka iso kano parking yayi agefen titi sannan yasakko yabudemusu kofa kowa inze sauka seya mika kudinsa harsuka gama sauka yarage saura ilham sauko da ita direban yayi sannan yamika mata hannu alamar takawo nata kudin kallonshi kawai take da lumsassun idanuwanta Wanda KO baa fadaba yunwa takeji Ganin Bata da niyar magana yasa yakyaleta yashige motarsa yawuce yabarta agurin sukuwa dama almajiran sundade da wucewa. Tananan tsaye har akafara Kiran sallar magaruba bata matsa a inda takeba amma zuwa lokacin tafara kuka sabida rabonta da abinci tun karin safe kukantane yajanyo hankalin wata mata meseda kunu da kosai kanta .kobaa fadamataba tasan yunwa ce tasa yarinyar kuka dan haka kunu tazubamata kunun da kosai taje gurinta tabata kallon ilham datayine yasa zuciyarta tashi sabida ilham inbanda warin rana da karnin miyau ba abinda takeyi ga wani zarni daya cika gurin asaka makon fitsarin datayi ajikinta Seda me kunun tayi dana sanin bata kunun a robarta. Itako ilham nagani kunu bata tsaya tunanin komai takafa robar abakinta batadamu da zafin kununba tashanye tas sannan taci kosan ay tana gama sha takwanta agurin sebacci da gudu me kunun tabar gurinta domin lamarin ilham yafara Bata tsoro Yarinya dakyau kamar aljana sannan gata nakasasshiya ay bata bata lokaciba tahada kayanta tabar gurin Love you all 😘maman yusuf [3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ _Writting by Zahra Muhammad mahmud_ *Page 26* Tanan kwance agurin kowa yazo wucewa sede yamata fatan samun lafiya domin azatonsu mahaukaciyace Tana gurin har zuwa karfe daya nadare se alokacin tafarka koda tafarka Bata tsorataba cigaba kawai tayi da tafiya duba da yadda garin kano dan musa me kwankwasiyya yawadatata da haske dan haka ilham tafiya kawai takeyi batunanin komai ba mutane sede jefi jefin motoci masu wucewa Duk motar datazo wucewa nacikin motar

Chapter 1 of 9