Share this page
9 / 9
ga wani nishadi datakeji Wanda rabonta dashi tamanta mikewa tayi taje gyara labulen window dinta seta hango abinda ke faruwa a garden dasauri tadauko takalminta tayo waje Dan ganin meke faruwa shiko anwar fashewar kaskon keda wuya yaji gurin yadume da wari dasauri yawaiga seyaga nafeesat ce agurin danshi yadauka ilham ce karasowar ilham keda wuya nafeesat tafara tone tonen abinda tayi musu mamakine sosai akan fuskar anwar sabanin ilham wacce tasan dama zaa rina afusace anwar yayi kan nafeesat yafara duka yana kuka yana fadin kincuceni kinsa nakauracewa Matata Allah yaisa tsakanina dake dakyar ilham ta kwace nafeesat ahannunshi kokarin janshi takeyi yakoma cikin gida sabida jin haysniyarsu yafara janyo hankalin security nagidan nafeesat ko kuka take tana rokonsu suyafe mata nasakeki saki uku muguwa inji anwar ba nafeesat ba har ilham seda tafirgita anwar yaci gaba Kuma 30minutes nabaki kibarmin gidana daukar sultan yayi yayinda ilham tadauki sudeis anwar yarike mata hannu suka wuce cikin gida suka bar nafeesat agurin Tana kukan bakin ciki [3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Zahra Muhammad mahmud *Wannan page nakine suhaila nagode da kulawarki gareni kece mutun ta farko acikin daruruwan members na groups dina data fara kirana awaya nagode Allah yabar kauna* *Page 85-86* Suna shiga cikin gidan falon ilham suka wuce Ajiye su twins sukayi suka rungume juna suna kukan farin ciki anwar se neman gafarar ilham yake rufemishi baki tayi tace nadade dayafemaka kuma nima Don Allah kagafarceni laifukan danamaka kissing din bakinta yayi sannan yace nadade da yafemiki my happiness Alwala sukayi hardasu twins sukayi nafila rakaa biyu dan nuna godiyarsu ga Allah Nafeesat kuwa dakyar tashigo tahada kayanta nasawa taba driver nagidan yasa amota sannan itama tashiga yajata se Kano koda isarsu da kuka tashiga part din mahaifiyarta hankalin mamanne yatashi inda tashiga tambayarta ko Lfy Kwashe duk abinda yafaru tayi tasanar da mahaifiyartata Kusan fitsarine yakusa kubcewa mamarta Agigice tace Saki uku nashiga uku yauni na lalace nafeesat duk laifinkine meyasa kika ajiye agidan meyahanaki tafiya daji ki ajiye aygashinan kinjawomana zagi agari koda akasanar da mahaifinta ansaki nafeesat hankalinshine yatashi Amman basu fadi metayiba kiran Mr President yayi yana tambayar me nafeesat tayi mezafi haka da anwar zesaketa har saki uku Hankalin dady ne yatashi danshi har ga Allah besan zancanba Hakuri yavashi sannan yace Bari yakira anwar din yaji Lokacin dawayar daddy tasami anwar suna tsaka da soyayyarsu da ilham dakyar yadaga wayar Gaida daddy yayi sannan daddy yace yazo gida yanzu yanason ganinshi Amsawa yayi Dan yasan dalilin kiran wanka suka shiga shida ilham bayan sunfitone tayiwa su twins suma Anwarne yace tashiryasu yanzu harda ita zasuje gidansu daddy Ilham taji dadin zuwan dazatayi Dan dama takwana biyu rabonta dazuwa gidan tunda abokiyar hirarta tayi aure wato ihsan Karfe takwas nadare suka shiga gidan daga mommy har daddy sunyi farinciki daganin ilham Gaishesu sukayi sannan ilham tabasu guri Daddyne yace anwar meyasa kasaki matarka nafeesat Cikin kwanciyar hkl anwae yayi mishi bayanin komai sosai abin yabasu daddy mamaki yayinda tausayin ilham yasake kamasu lalle ilham tayi juriya tunda koda wasa bata taba kawo kararkaba so sekaji tsoron Allah karike marainiyar Allah bisa gaskiya da amana inji mommy godiya yayi sosai Basu bar gidanba se karfe goma nadare Daddy yayiwa mahaifin nafeesat bayani ranshi inyayi dubu yabaci dangama rufeta yayi da duka dakyar tace mommy ce tasakata yayi hkr Dakyar yahakura yakyalesu Amman da yayi niyar sakin mamannatane *bayan wata daya* hutu anwar yadauka suka tafi aykin hajji shida iyalinsa sunyi adduoi sosai karma de ilham tayiwa iyayenta addua hartana kuka ganin lokacin su huta yazo Amman basa kusa Daga saudiyya yawon honey moon suka wuce inda seda suka shafe wata hudu suna hutawa inda hutun kuwa yayi kyau inda ilham ke dauke daciki natsawon wata biyu farinciki agurinsu kamar me anwar jiyake kamar yamaidata ciki yarasa ina zesa kansa wannan cikin yaga gata sabanin nasu twins hargurin su ihsan da Adnan sukaje inda suke zaune a London Wanda tunda sukayi aure Adnan yahanata zuwa gida yace seta haihu cikinta ko yazufa haihuwa koyau ko gobe tayi murna daganinsu Dan harda kukanta dakyar anwar yararrasheta yayinda shiko Adnan dariya yake mata dakyar anwar yakyale ilham suka kwana agidan ihsan siyayya suka shiga kasuwa ana saura kwana biyu zasu dawo kayan jarirai anwar kediba Kamarhauka ita abin dariyama yabata hakade suka karasa hutunnasu sukayo kasa nigeria koda sugura tazo yiwa aminiyarta barka dazuwa bakaramin farinciki tayiba jin ilham Nada ciki harcewa takeyi Ado gwanja zasu dauko yabugamusu kujerar tsakar gida dariya ilham tashigayi sosai tace haba sis sekace tafari tafari cemana agurinmu dole ke murausaya tunda sunansu twins baayiba ameera ma tazo dauke da cikinta Dan wata biyar dayake batasamu ciki dawuriba sosai tayi murna jin auntyn ta nada ciki fira sukayi sosai inda daga karshe suka tsayar da sati mezuwa zasuje kauyen wudil kaimusu ziyara maman yusuf [3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *Page 87-88* Sati nazagayowa suka tafi Kano harda anwar Da ameera da moneer cikin shiga ta alfarma duk inda suka wuce kallonsu akeyi sabida Sun hadu motocin daake jansu ma abin kallone ga excode gaba da baya ana jiniya Megari yayi murna dazuwansu sosai senan nan yake dasu Kofar gidan megari cika yayi da yan kallo Dan jin cewa ilham gurguwa tazo shiyasa kowa yazo ganinta koda suka fito daga gidan megari rabon kudi suka shiga yiwa mutanen dasuka taru suna kallonsu Ameera ce tamikawa wani gurgu kudin Kai dubanta tayi fuskarsa tabbasa ko alahira aka nuna mata shi zata ganeshi bakowabane illah megidansu daya koresu sanadin hakan suka rasa iyayensu Wani kara tayi sannan ta cukumi mutumin tafara dukanshi iya karfinta dasauri ilham Tayo gurinta tariketa Tana tambayarta meyamata bata da hankaline take dukan tsoho Dakyar Ameera tafadamata kowayeshi Habawa kan kace me tuni guri yakoma se kura Kake gani dangama ilham komawa tayi kamar mahaukaciya gurin dukan mutumin tana kuka ameera natayata Su anwar nacan cikin jamaa se hangowa sukayi kura natashi dasauri sukayo gurin abinda suka ganine yabasu mamaki ilham da ameera ne kedukar wani tsoho gurgu harsun kaishi kasa amma basu denaba jamaa nakallo bawanda yahanasu dagudu suka karasa gurinsu suka amshi mutumin ahannunsu Wanda yadoku sosai Dan hakoran dasuka rage abakinsa tuni sunfice dakyar anwar yaja ilham Wanda se kokarin kwacewa takeyi Tana fadin kabarni nakasheshi shima mugu azzalumi dabadan Kai ba dayanzu munatare da iyayenmu cikin farinciki dakyar suka jasu sukasa amota anwar ne yaciro kudi zeba mutumin Dan akaishi asibiti Dan har karyewa yayi ahannu Dasauri ilham tadakatar dashi tace Anwar!!!! Idan kasake kaba mugunnan kudi wallahi zaman Lfy nidakai har abada Jikin anwar har rawa yakeyi yatashi daga gurin mutumin yashiga mota Mutuminne yakaraso dakyar yanacewa Don Allah sugafartamasa tsawa ilham tadakawa direban daya ja motar ayko beyi watawataba yahaura motor bisa kwalta Tafiya suke ilham da ameera se kuka sukeyi danji sukayi mutuwar iyayensu tadawo musu sabuwa dakyar su anwar suka rarrashesu har suka iso Abuja dayake moneer ma yanzu a abujar yake ayki Rayuwa taci gaba da tafiya cikin so da kaunar juna har zuwa lokacin da ilham tahaihu Tahaihu Lfy wannan karoma twins tahaifa sede su duka matane murna agurin anwar bata misaltuwa godiya ko ilham tashashi kwando kwando daddy yayi murna mommy ko harda rawarta Daddyn Adnan har Abuja yazo ganin Matannasa shida mommy ranar suna yara sukaci sunan mommyn anwar da mommyn ilham wato Maryam da Zainab inda suke ce musu mufeeda da mubeena tarom sunan yakayatar Dan dangi nakusa dananesa babu Wanda bezoba media ko ko ina hotunan sunanne sede fatan Allah yaba mejego Lfy ameerama da jima da haihuwa inda tahaifi namiji akasa sunan mahaifin moneer suna kiransa da shahid itako ihsan yaronta har ya iya zama itama namiji tahaifa yaci sunan daddyn adna suna kiranshi da ameer duka family rayuwa suke cike dajin dadi da godiyar Allah kudin ilham da daddy yabata dawanda anwar yake bata hadasu tayi takaiwa baban Sugura tace agina masallatai da rijiyoyi sadakatul jariya zuwaga mahaifanta [3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Last page *Page 89-90* Tenure din daddy yakare Dan haka yanzu lokacine nabuga gangar siyasa Inda jamiyyar su daddy suka tsaida anwar amatsayin Dan takarar shugaban kasa Anwar bayaso sabida Yasan Mulki ze hanashi samun isasshen Time din ilham dinsa Dakyar suka shawo kansaya yarda Daddy ma behanashiba sabida ya yarda anwar yanzu yashiryu kuma mutumne metausayi da rukon amana Dan hakan yashiga karfafawa anwar din guiwa Ilham ma fatan alkhairi tayimasa Hartana tsokanarshi tace to my life yanzu kuma shikenan munci kafar Kare dagani harkai sabida yawon campaign Rungumota yayi yana dariya yace kece de me kafar Kare baniba ko kinmantane intuno miki Dariya tayi Tana kaimishi dukan wasa tana cewa wlh kadena banaso Shima kwaikwayanta yayi yace kidena nima banaso Kara rungume juna sukayi suna dariya Dukansu yanzu bazama yayon campaign suke guri guri inda kowa yake fadin maso uba yaso dansa sukari bakayi farin banza ba bangon sugar kowa yadafaka seyalasa kayi taka kayi tame karafin karfi makiyanka bazasu iyaba Irin wainnan maganganu suke fita abakin alumar kasa Ranar zabe tazo inda koina afadin nigeria ankada zabe Lafiya babu tashin hankali se jiran sakamako gobe in Allah yakaimu Anwar har ramewa yayi sabida zirga zirga kuma duk inda Zashi kafarshi kafar ilham yaran kawai suke bari agida gurin masu kula dasu washe gari aka sanar da sakamakon zabe Wanda tun jiya aka Fara inda alkalin Zabe yabada sanarwar anwarne yalashe Zaben daga jamiyyar CPA Murnar dasukayi bazata misaltuba Dan ilham har da kukanta rungume anwar tayi tanamishi fatan Alkhairi tare da adduar Allah yabashi ikon yin adalci yasa mulkin Yayi sanadin shigarsu gidan Aljanna Talakawa ko zan iya cewa sunfi kowa murna ganin anbasu abinda suka zaba musamman matasa suna ganin yanzu suma anbasu yencin tsayawa takarar shugabancin kasar sabanin da da dattijaine sukeyi kasade gaba daya takaure da murnar zaman anwar shugaban kasa *RANAR HANDING OVER* wato ranar rantsar da anwar fans kubiyoni eagles square musha kallo Anwar nahango cikin shiga ta alfarma sanye yake da wata ubansun shadda fara yayin da gefenshi nadama handbag dinshice wato her excellency Hajiya ilham bukar shettima the First Lady for the Federal Republic of Nigeria 👍 sanye take cikin wani farin Material anyimasa adon Goulding fuskarta sanye cikin bakin glass takalmi da Jakarta da gwaggwaronta da dankunne da sarka da agogo duk Goulding colour ne yaransuma abin gwanin Shaawa babu abinda yafi burgeni se lokacin da zaayi handing over tsakanin anwar da daddy wato uba da da sunyi matukar kyau gashi kayan jikinsu anko sukayi hakade taron yaci gaba da wakana har aka rantsar da anwar nafeesat adede lokacin Tana zaune gaban TV Tana kallo Wani bakin cikine yarufeta tasa kuka Tana ganin dayanzu itama Tana gurin amatsayin First Lady gawani uban kyau dataga anwar da ilham sunyi ga yaransuma abun gwanin Shaawa kuka takeyi sosai tanajin son anwar aranta Wanda tasan sede tamutu dashi Dan anwar yamata nisa anwar da ilham basu samu kansuba se wajen goman dare duka sungaji sabida wuni sukayi sallamar baki dasukazo tayasu murna wanka sukayi suka hau Gado domin huce gajiya ilham har bacci yadauketa anwar yace besan zancanba dole tafarka Dan biyamasa bukatarshi kamar kullum yauma anwar kuka yake iya karfinshi araina nace tofa Mr President da kuka wato no easy ilham seda yaci kukanshi yakoshi amma na dadi koda suka tsarkako jikinsu dariya ilham take mishi tace yanzu Dan Allah haka Zamushiga presidecial Vila kana kuka rungumeta yayi yana dariya yace baby bawannan bane abin jinba godewa Allah nake dayasa First Lady tawarke da da yar gurguwa zanshiga dariya dukansu sukayi suka rungumi juna sunayiwa Allah godiya daya nunamusu wannan rana anwar yakama ayki gadagadan yayinda a ministocinsa yaba Adnan minister na health moneer kuma na ilimi yayinda ya rike minister na petur da kansa ilham malama tasamo duk weekend take zuwa gida takoyamata karatun addini rayuwarsu tazama abar koyi kowa sonsu yake gashi mulkinsu suna adalci kowa se samusu albarka yakeyi yayinda soda kaunar junansu se abunda yakaru anwar na kaunar ilham kamar ransa yayinda ko kadan bayason bacin ranta itama kuma haka kudi da mulki besa suna wulakanta mutaneba godiya sukewa Allah kullum daya mallaka musu junansu. *Alhamdu lillahi rabbil alamin. Astagafiruka wa atubu ilaika ya Allah. Allahumma inni as aluka bi annani ashhadu Alla ila ha Illa anta ahadussamadullazi lam yalid walam yulad iyyaka naabudu waiyyaka nastaim* kuskuren dake ciki Allah yayafemin. anan nakawo karshen littafin *Allah gatan bawa*sekuma munhadu a littafina na gaba mesuna 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 written by Zahra Muhammad mahmud An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9