kallon mahaukaciya sukemata bare yanzu data cire hijab dinta acan inda tasha kunu gashin kanta awaje yake gashi da yawa har gadon bayanta .tayi tafiya meyawa har tazo dai dai gadar yankura anan tayada zango ajikin gadar daga gefen titi baccine yasake dauketa agurin ba ita tafarkaba se da garin Allah yawaye shima tafarkane asakamakon hayaniyar mutanen dataji akanta bude ido tayi ahankali sannan tamike zaune tana kallon mutanen dakowa yatoshe hancinsa asakamakon warin kashin datakeyi domin kuwa kashi tayi akwance
Korarta mutanen suka farayi haka tamike tana kuka ko tausayinta basujiba wata bayarabiya harda marinta tana harkadata. Jinsaukar marin akumatuntane yasata sakin kuka me tsanani gami da kwasa da gudu ay tana fara gudun mutanen suka fara dariya sabida gudun abin dariyane koni naso nadara kawai dannasan wacece ilhamne shine yahanani gudune irin naguragu tana fara gudun tafadi kanta yaji ciwo amma bata damuba burinta kawai tagudumma matar domin tunda tazo duniya baataba marintaba se ranar
Seda taci gudunta me isarta Wanda duk inda tawuce da gudun dariya jamaa keyi dan gudun abin dariya ne sannan ta tsaya tana haki yunwa tafaraji danhaka tafara neman abinci tahanya bin guriguri tana kuka kofar wani restaurant ta tsaya tana kuka to aciki akwai costomers suna brakefast acikinsu akwai Wanda yafara amai sabida ganin ilham dayawa daga cikikuma fita sukayi suka bar abincin ganin haka yasa matar me gurin tasowa takama ilham da duka bata barta seda tamata shegen duka sannan takoma ciki tadauko ruwan wankewanke ta kwaramata zuwa lokacin inka kalli ilham bazakace itabace sabida gaba daya fuskarta ta kumbura dan duka
matarce tafara balai dan ubanki gobe ma kikara zuwa kofar shagona ki korar min costomers mayya kawai wuce kibani guri. ilham nakwance agurin sabida jikinta yayi tsami ga yajin ruwan data watsamata yashigarmata ido da duk inda taji ciwo kuka kawai takeyi ganun ilham Bata da niyar tashi yasa matar janta akasa seda tayi nisa da ita sannan ta wurgar da ita cikin wata kwata Allah sarki ilham marainiyar Allah.
love you all 😘maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
_writting by Zahra Muhammad mahmud_
*Page 27*
*Bayan shekara biyu*
Zuwa wannan lokacin duk Wanda yasan ilham baze ganetaba sabida gabada takoma tamkar mahaukaciya sabida datti gashin kantama yadankare akanta kamar bata dashi
Rayuwace takeyi me cike da tausawa sabida ko abincin dazata ci yanzu yakoma sede tabi bola tasamu hakanne yasa duk Wanda yaganta yaga mahaukaciya
Har yanzu atiti take kwana ko kangon da baa gama ginashiba.
Yanzu shekarunta sha uku kuma awannan lokacinne Allah yakawomata jinin al'ada(wayyo Allahna)gaba daya jinin yagama bata mata jiki sabida jinin irin me rushing dinnanne ga azababben ciwon mara Wanda inya murda mata sede taita birgima har Allah yayayemata kuma koda jamaa sunga tana birgimar babu me bi takanta dan azatonsu duk acikin haukarne
Shiyasa yanzu warin datakeyi namusammanne ko ina tabi korarta akeyi babu me Jin kanta kuma lalurarta se abinda yakaru basauki sena Allah.
***********
Zuwa yanzu ameera na js2 sabida megari yamaida ita makaranta kuma har yanzu bata manta da yar uwarta ilhamba shiyasa kullum megari cikin bada cigiyarta yake sabida megari idan akwai abinda yatsana shine ganin ameera cikin damuwa Sam baya kaunar bacin ranta dan inkaga ameera yanzu bazaka taba cewa ba yarsa bace kuma suma matansa kowacce cikin kyautatamata suke ba banbanci. Rayuwar ameera de se sonbarka matsalarta daya ce rashin yaruwarta ga doctor kullum cikin yimata ayke yake duk week-end kuma yana hanya dan yanzu sunsaba dashi kamar dan uwanta haka tadaukeshi shima kuma zallar tausayintane aranshi dakuma wani abu Wanda yabarma ranshi sezuwa lokacin dazata mallaki hankalin kanta.
love you all 😘maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
_writting by Zahra Muhammad mahmud_
*page 28*
*Anwar umar mutallib*
Dane ga shugaban kasar nigeria meci ayanzu wato Alhaji umar mutallib manumfashi.shekarunsa basu wuce 35 ba dane daya tamkar dubu agurin mahaifinshi subuyu Allah yaba iyayenshi shine nafari agurin iyayenshi se kanwarsa mebinsa khadija wacce taci sunan mahaifiyar alhaji yasa suke cemata ihsan.
Mahaifiyarsu hajiya zainab ita kadaice agurin mahaifinsu shiyasa tazamana itace first Lady of Nigeria. Hajiya zainab macece kyakkyawa domin ita asalinta mutanen labanonce tsayawa fadin kyau irinna hajiya zainab zezama kauyanci sabida duk wani abu da ake kira kyau ga y'a mace takai karshenshi don kyannatane yake karasawa mijinta kaunarta.duk da kyau irinnata se Anwar yace bata iyaba domin yafita kyau nesa bakusaba mutumne shi miskili naajin farko kasaita gareshi kamar jinin sarauta yayi karatunshi tundaga pramary zuwa secondry school a turkish school dake abuja inda yawuce da karatunshi na jamia a can kasar mascow har zuwa yanzu daya hada masters dinshi akan fannin petro chemical engenearing
Zamansa akasar waje yasa yafara neman mata tun yanayi kadankadan har yakai matakin daze hada mata uku akan gado daya kuma yayi amfani dasu batare daya gajiba sabida Allah yayoshi acikin jerin maza mabukata koya shaawa tamotsa masa baya iya hakura seya biya bukatarsa
Abokanshi nacan sunyi iya yinsu wajen ganin sunkoyamasa shan giya da coccane amma abin yaci tura domin shi baya kaunar abinda zegusar masa da hankalinsa. Anwar Wanda akafi sani da the most handsome domin haka kowa yake kiranshi sabida kyan Anwar ko ajinsin Larabawa da indiyawa se an tona zaa samu irinshi (kunsanme ? Duk kyansa bekai ilham ditaba)yana da gashi akansa metarin yawa yanayin gashinnasa tamkar arnav din kushi koya yamotsa bakinsa se beauty point dinshi yafitu sosai farine shi sosai kuma yanada tsayi amma bacanba sannan yanada faffadan kirji Wanda yake amurde hakan yasamo asaline asakamakon daga karfe daya keyi arayuwarsa baya kaunar komai sama da iyayensa da kuma kanwarsa kuma duk abinda zeyi yana bashi lokacine lokacin nafita shima yabar abin misali inze gana dawani zece yabasa minti biyar tofa dazaran minti biyar tacika tashi zeyi yafice yabaka guri baya wasa da lokaci hakane yasa baya wasa da ibada duk iskancinsa baya barin sallah
Anwar mutumne shi Wanda beba soyayya muhimmanciba ko matan dayake hulda dasu basonsu yakeyiba kawai for personal used yaajiyesu dan ko numbarshi basudashi
Ko bayan yagama karatu mahaifinshi yayi yayi dashi yadawo gida amma yaki kullum ansa dayace am on my way dady very soon tun mahaifin namishi uzuri har abin yafara Bata mishi rai dan haka yasa masu bincikamasa me Anwar yakeyine daya hanashi dawowa gida duk Wanda yasa binciken ansa daya suke Bashi neman mata yakeyi wannan batu bakaramin tada hankalin mahaifinshi yayi ba domin dede gwargwado suna iya bakin kokarinsu gurin ba yaransu tarbiyya dagashi har mahaifiyarsu kudi da mulki besa sunyi wasa da tarbiyarsuba hakannema yasa bekai ihsan karatu kasar wajeba don yana gudun zamani amma yau abinda Anwar zemasa kenan. Hakanne yafusatashi yakirashi awaya yana gaisheshi amma ko amsawa beyiba illa cewa dayayi cikin muryar fushi wacce Anwar bedauka dad dinsa yanada itaba. Duk abinda kakeyi anan inada labari kuma wallahi duk hukuncin dana dauka akanka ka kuka da kanka dan hukuncin baze maka dadiba danhaka duk abinda kakeyi kabarshi kabiyo jirgi ranar asabar kasauka a kano sabida nima zanje kanon wani taro semu taho abuja tare kuma wlh inbaka tahoba daga yau kanemi wani uban niba mahaifinkabane.yana kaiwa nan yakashe wayarshi yana huci
zuface tashiga karyowa Anwar kamar ruwa domin iya tashin hankali yashigeshi jifa yashigayi daduk abinda hannunsa yakai kai yanayi yana fadin wayyo allahna wanne munafikine yahadani da dad. Hakade yagama dan matashin haukarsa yafara shirin barin kasar domin saura kwana biyu asabar din tacika.
**********
*Asabar*
da misalin karfe goma sha daya nasafe jirgin su Anwar yasauka à filin jirgi na malam aminu kano tun kafin zuwan jirgin airport din cike yake da security takoina sabida Anwar koda saukar jirgin shine mutum nafarko daya fara sakkowa wayyo Allahna sisters kuzo kutayani gani sanye yake cikin blue jins da farar shet sannan yadora katuwar rigar sanyi baka wacce tsayinta yakai har guiwarsa kanshi yasa hular sanyi fara yayinda yanade wuyansa da irin wannan siririn abunnan namaza(bansan sunanshi ba amma wani lokacin har rawani sunayi dashi)red colour inkuka ganshi bazaku so kudauke ido akanshiba domin yahadu saukowa yafarayi cikin tafiyarsa ta kasaita tunkafin yagama sakkowa aka shimfadamasa red carpet yasauko akai yaci gaba da tafiya har zuwa inda aka ajiyemasa motar daze hau wata bakar jeep ce kirar kamfanin Ford tinted ne gilas din motar murfin baya aka bude masa yashiga sannan akarufe sauran motoci kimanin guda goma sha daya suka rufawa motarsa baya yayin da gurin yacika da jiniya duk inda suka wuce kallonsu akeyi yayin da duk ababen hawa nakan titi suke basu hanya ahaka har suka iso govement house koda isowarsu wani kayataccen falo aka saukeshi Wanda ga abincinan na alfarma yaci iya cinshi yabar nabari jus kawai yasha sabida yaci abinci ajirgi nafeesace tayi sallama tashigo cikin falon y'a ce game girma gomnan jahar kano cikin ado nadaukar hankali se kwarkwasa takeyi Wanda shiwanda akeyi dominsa ko kallo bata isheshiba ita kuwa Allah ne yajarrabeta da sonshi tunda dadewa shiko basonta yakeyiba
koda tagaisheshi dakyar yaamsa suna nan zaune akayi ringing bel ita tabada umarnin ashigo wani sojane yashigo yadan kame gami da sarawa sannan yace ranka yadade his highness yanason ganinka mikewa yayi kawai batare da ya amsaba yabi bayansa har zuwa wani falon. Mahaifinshine aciki tare da gomna suna hada ido da mahaifinsa yaji gabadaya kunya takamashi dakyar ya iya gaishesu cikin sakin fuska suka amsa har mahaifinnasa kamar bawani abu dayamasa gomnane yamatso yarungumeshi ajikinshi yajashi har kan kujerar dayake zaune yana fadin haba dan gidan dady yau gaisuwar daga nesace bazaazo jikin dadynba ko shide dukar dakai kawai yakeyi domin beson hada ido da mahaifinsa
bayan sundan taba hira megirma shugaban kasa yamike yace zewuce sabida yau yakeso yakoma abuja tashi akayi gaba daya harda gomna domin masa rakiya zuwa airport jerin gwanon motocine sunkai kimani guda talatin takoina jiniya ke tashi sukayoma shugaban kasa rakiya ga garin akwai hadari sosai anfara yayyafi jamaa kowa yafake sekallon
Motocin akeyi kan kace me ruwa yabarke kamar da bakin kwarya
adede wannan lokacin ilham natsaye abakin titin ruwa nadukanta amma bata damuba sabida hakan sabontane tananan atsaye har motocin shugaban kasa sukazo wucewa
gomna da shugaban kasane abayan motar yayinda Anwar ke zaune agaba shida direba.
karar jiniyar da ilham tajine yasata firgicewa dan haka Bata bata lokaciba gurin fara gudu gashi ana ruwa. Kamar ance Anwar yawaiga inda take haba mezeyi inba dariyaba dan abin gwanin bandariya dariya yake har rike ciki yana kwanciya Jin dariyarsane yasa mahaifinsa kallonsa da gaggawa Wanda shi tuni yamantama da mahaifinsa yake tafe. Adede lokacin ilham santsi yakwasheta garin gudu tayi samasama tafado kasa haba Anwar ay har ihu ga kwalla data cikamishi ido dan dariya mahaifinsa mamakine yakamasa karara sabida tunda aka haifi Anwar betaba dariyar dazakaji sautintaba se yau
Anwar Wanda garin dariya har pointing dinta yakeyi batare dayasaniba hannunsa mahaifinsa yakalla dan ganin abinda yake yiwa dariya har haka Allah sarki ilham yagani wacce zuwa lokacin harta mike tacigaba da falla gudunta na guragu ay Anwar nagani shima yacigaba da dariyarsa shiko mahaifinsa wani murmushi yasaki Wanda kai tsaye zamu iyan kiranshi namugunta wayarshi yadaga yakira motar bayansu yabada umarnin adauko mishi ilham asa amotar Wanda Anwar dan dariya shibemasan mahaifinnasa yayi wayarba haryadena ganinta bedena dariyaba ahaka harsuka iso airport ko gurin shiga jirgi anriga shigewa da ilham dan haka begantaba ahaka harsukayi sallama da gomna suka shiga jirgi gurin zamansu daya da dadinsa amma koya yatuna yadda ilham tafadi har fadowa yake akujerarsa dan dariya sude security se kallon abin mamaki sukeyi itako ilham tunda akadaukota amota take bacci sakamakon heater dake kunne amotar har akasata ajirgi bacci take shiko mahaifin Anwar kallonshi yayi fuska dauke da murmushi yace aransa my son kenan ay dariya yanzu kosomata
love you all 😘maman yusuf
*ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
_writting by Zahra Muhammad mahmud_
*page 29*
Da misalin karfe biyar na yamma suka Isa Abuja koda saukarsu motocine da jamian tsaro bila adadin suna jiransu karasowa sukayi suka shiga mota zuwa gida
Tun ajirgi dady yaba wani excord dinshi umarnin yakai ilham wani guest house dinshi kuma yatabbatar yasamo matar dazata kula da ita dan haka koda suka sauka Anwar begantaba tafiyar dasukayi bata da tsayi suka iso gida tundaga get kowa ke sarawa har zuwa cikin gida suna shiga falon gidan mahaifiyar Anwar ce abakin kifa tana jiran shigowar gudan jinin nata dagudu yakarasa jikinta yarungumeta yana fadin imiss you mum somuch ita ma hakan take fadamasa karasowar ihsan gurinne yasa yasaki mum yarungume ta itama dad ne yayi gyaran murya sannan hankalinsu yadawo gareshi
Mum ce tafara Isa gareshi tana murmushin dake kara fito da kyanta rugumeshi tayi sannan tace you are highly welcome my spouse dariya yayi sannan yayi huging nata back yana fadin bawaninan bayan duk kun manta dani ta Anwar kukeyi we are sorry tafadi gami dajan hannunsa suka haura sama
Anwar ma dakinshi ihsan taja hannunshi takaishi ruwan wanka tafara hadamishi sannan tace mishi bross kaje kayi wanka inka shirya seka samemu a dinning area na falon dady murmushi yayi mata kawai yashige toilet itako fita tayi tanata murna yau bross nata yadawo bakinta har kunne (amin afuwa banfadi ihsan ko yar shekara nawabace to me karatu ihsan shekarunta ashirin domin da fifting years Anwar yagirmeta)falo takoma tazauna zaman jiran mutanen gidan
Dukansu Sun hallara suna cin abinci sannan suna hirar yaushe gamo da Anwar amma dady bayasamusu baki momy tafuskanci hakan amma tabari sesun kebe ta tambayeshi meke faruwa hakane yasa shima kanshi Anwar yaki sakin jikinshi dasu
Suna tsaka da cin abincine Anwar yatuno ilham gurguwa habawa aywata irin dariya yafashe da ita harda rike ciki daga momy har ihsan sunfirgita daganin hakan banda dady dominshi yasan dalilin dariyar momy arude take tambayarsa lafiya sabida ita tahaifeshi amma tasan bata taba Jin sautin dariyarshiba seyanzu dafa shi tayi tana tambayarsa dan gabadaya tafirgice atunaninta aljanune suka shigar mata jikin shi
dakyar yaiya dena dariyar sannan yafara basu labarin abinda yasashi dariya tunda yafara labarin ihsan itama dariyar take momy ko murmushi tayi tace Allah yashiryeka Anwar yanzu dama dankaga gurguwane kake wannan uban dariyar wallahi kakiyayi kanka sabida hallittar Allahce bakyau hakan dakakeyi sabida kaima barawa kayi Allah yayi hakaba
Har zuwa lokacin dariyar taki sakinshi seda ihsan tayi katobara tahanyar cewa kai bross wallahi harna hango ka kaida ita amatsayin miji da mata tafada tana dariya wani gigitaccen mari yadauketa dashi kafin marin yasaketa yakara mata wani yadaga hannu zekara dady yarikemishi hannu shiko nuna ihsan yake da hannu yana fadin ni saankine dazakiyimin wannan mugun fatan keko ihsan wacce irin kiyayyace tasa harkika hangoni amatsayin mijin gurguwa ni yafada yana nuna kanshi yayin da gaba daya jijiyoyin jikinsa suntashi haka gashin jikinshima yatashi idonshi yayi ja ba ihsanba hatta dady seda yatsorata daganin yanayinsa sabida one time yarikide dagudu ihsan tabar gurin tana kuka sabida kotsawa bross nata betaba yimataba Amma shine yau harda marinta daga yimasa wasa kuka tasake rushewa dashi
shiko ta maman tsaye se huci yakeyi momy ce tafara magana cikin sigar rarrashi haba my son meyasa haka wasa fa takema inbanda abinka taya zaka auri gurguwa wacce basake ganinta zakayiba don Allah karage wannan fushinnaka shiko dady kallonsa kawai yayi yace ka kyauta Anwar you Will pay for it kansa yagirgiza yashige daki momyce tashiga yimasa nasiha sosai seda taga yasauko sannan tace yaje yahuta itama tabi megidanta daki
love you all maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
_writting by Zahra Muhammad mahmud_
*this page is dedicated to Zahra Muhammad hausa novels group thanks you all am really appreciated*
*page 30*
Tunda daga wannan rana Anwar yafita harkar kowa agidan kamar yadda kowa yafita harkarshi ko momy tadena bi takanshi sabida dady yamata bayanin abinda yake aykatawa a mascow.
Kuma dady yashaida mata wlh seya dauki mummunan mataki game da abinda ya aykata
Yau lahadi Wanda yay dede da sati daya kenan da zuwan ilham abuja. tun karfe goma dady yashirya yafice agida tare da excord dinshi bazame ko inaba se gidan dayasa akai masa ilham gidan akwai tsaro sosai kai tsaye yashiga falon gidan tare da excord din daya ba alhakin kulawa da ilham wata dattijuwa suka samu zaune afalon wacce shekarunta basu wuce hamsinba matar kallon farko zaka mata kagane tanada kirki matar mesuna inna ladi jiki nabari tasauka akujera tana mikawa dadi gaisuwa Cikin mutunci yaamsa gaisuwarta sannan yasami guri yazauna bayan yazaunane yabada umarnin akawomishi ilham
Domin yaganta inna ladice tashiga daki tafito rike da hannun ilham wacce ko dawasa akacemaka itace bazaka yardaba sabida tin lokacin daaka Daukota ake aykin gyarata asatin datayi a abuja har wata kiba tayi ga haskenta daya fito Wanda ada datti yaboyeshi gashin kanta har kusa da duwawunta yasha gyara bakamar da daya dankareba sanye take da Riga da siket na kanti Wanda suka kara bayyanar da kyanta sede harzuwa lokacin miyau nanan kamarda da sauran lalurorinta
koda aka fito da ita dady yayi matukar mamakin ganinta ahaka sabida betaba kawowa ransa akwai wani mahaluki afadin Nigeria daze gwadawa Anwar kyauba segashi yagani atattare da ilham baiwar Allah azuciyarsa yafara magana yana fadin inbanda iskanci irinna Anwar wannan ay baabar dariya bace sabida duk kyan dayake takama dashi wannan tafishi matsala dayace kawai lalurarta yanacikin wannan tunaninne aka zaunar da ilham agabansa dagowa yayi yakalleta cike da tausayawa itako se dariya take mishi hadi da gwarancinta Wanda ko baa fadamasaba gaisheshi takeyi yayin datake magana shikuma miyau yashiga ambaliya ko afuskar dadi babu alamar kyamatarta illa tausayamata dayayi juyawa yayi game kula daita wato inna ladi dan tayimai karin bayani kara rusunawa tayi sannan tafara magana ranka yadade a iya zamana da yarinyarna nafahinci ba mahaukaciya bace kawai dolancine da ita domin har biro da takarda take rubutu bide bansan metake rubutawaba amma nasan duk dan makaranta yaga rubutun zeiya karantawa jeki kawo min rubutun inji dady mikewa tayi taje tadauko takardu wainda yawansu yakai goma daya bayan daya dadi yashiga dubasu abu dayane arubuce duka ajikin takaddun wato
*ilham shetima bukar*dady yayi matukar mamaki kobaaceba yasan sunanta kenan amma daya gwada seyace ilham bukar shetima dasauri tadaga hannu alamar itace kamar yadda takeyi amakaranta dariya duka sukayi anan suka gane sunanta amanarta yakara dankawa inna ladi sannan ya umarceta data share wa ilham miyan bakinta zedauki hotonta haka kuwa akayi inna ladi harda sake shafamata hoda tasamata jambaki wayyo Allah naso ace kuna gurin kuga yarda ilham tahadu ko kusa bame ganinta yayi zaton badaga indiya takeba dasauri dady yamata hoto kala biyu daya tasoma dariya wacce tabayyana hushiryarta me matukar kyau yayin da beauty point dinta shima yafito intakaicemuku ilham tayi kyau matuka
bayan yagama daukar hotontane yamike yamusu sallama yawuce.
koda isarsa gida hutawa yayi bayan yayi sallah yasa momy takiramishi Anwar da ihsan bayan sunzo dady ne yafara magana dacewa abinda yasa nataraku bakomaibane illa akan Anwar gaban anwarne yafadi azuciyarsa yace shikenan tafaru takare muryar dady ce tadawo dashi daga tunanin da ya fada inda dady yadora dafadin Allah yasani tun ashekarun baya nake umarta Anwar daya kawo matar dayakeso domin yayi aure amma yaki to hakanne yasa nidakaina nazabo masa wacce nake ganin tadace dashi ba Anwar ba hatta momy seda tafirgita dajin batun itako ihsan fadi take aranta Allah yakara dasauri yadago yana duban dady amma yakasa magana sabida zafin da zuciyarsa kemasa dady ne yaci gaba nasamomaka matar aure diyar mutunci sede yarinyace karama dan shekarunta basu wuce 14ba what inji momy takatse dady tahanyar cewa haba alhaji me yar 14 years zatayi agidan aure dan Allah kabar wannan maganar shide Anwar nashi ido dan yasan dady baya magana biyu amma azuciyarsa jiyake dama shi aljanine kawai yatashi yabace dady yaci gaba kuma nan da sati biyu zaa daura auren ba wani shagali zaayiba kawai daurin aure zaayi shagalin zaa dagashi zuwa lokaci namusamman. hawayene suka fara ambaliya a kan kyakkyawar fuskar Anwar. dan bakinciki yazaayi yana mazaunin dan shugaban kasa Wanda ahalin yanzu ankai sunanshi majalisar tarayya ta sanatoci da ta wakilai akan su tantanceshi zaa bashi mikamin ministan man petur na kasa amma ace bikinshi bashagali sekace wani mara gata kuka yaci gaba dayi dady ko kallonshi beyiba ita ko momy tundaga kallon fuskar megidan tasan bayason wargi dady ne yadauko wayarshi yanuno hoton ilham yamikama momy yana murmushi yace ga hoton surukartaki dasauri momy taamshi wayar tafara kallon hoton aybatasan sanda tarungume dady ba tanamishi godiya fadi take gaskiya kaiya zabe karfa kasa jamaarka sufarayi dakai tahanyar cewa se kyawawa kuke aure murmushi dady yakarayi yace wato naiya zabe ko ihsance taamshi wayar ahannun momy wani ihu tasaki gamida rungume yayannata Wanda tamanta fada sukeyi fadi take bross dady yagama yimaka komai tunda ze aurama wannan hurulinin dan Allah kalli hoton kagani da kamar baze kallaba amma se yadaure yakalla danyaga wanne kyaune wannan dahar yafi nashi da na momynshi kallon hotonyayi dasauri yamike yana fadin subuhanallah wani matsanancin farinciki ne ya ziyarceshi dagudu yakarasa jikin dady yarungumeshi yana masa godiya intakaicemuku Anwar harda yar kwallarsa ta farinciki godiya ko dady yashata tafi kwando dubu Anwar ne yafara magana dady yarinyar waye ita kuma yasunanta ilham bukar shetima sunanta wow gaba daya suka hada baki harda momy dady yaci gaba sanin yar gidan waye kuma wannan betasoba domin mahaifinta amininane dan haka aure nanda sati biyu sekaje kafara shiri rungume dady yakarayi sannan yanemi dady daya bashi contact dinta don su gaisa dady yabashi amsa da bata Nigeria se anyi auran zata taho kuma ba waya ahannunta Anwar beso hakaba amma kobakomai yasami hotonta dan wayar dady yadauka yatura hotunan atashi wayar tun agurin yadora daya akan dp dinshi yayi status da my wife to be shide dady kallonsu kawai yake yana dariya azuciyarsa dady ne yace kuma son kasaurareni dakyau duk ranar daka saki yarinyarna kobayan rainane banyafemaka ba dasauri suka kalleshi sannan Anwar yace haba dady karan haukane yacijeni dazan saki my Princess ay dady mutu karaba murmushi dady yayi sannan yace Allah yasa ameen dukansu suka amsa dady yaci gaba kuma in andaura auran anan zaku zauna zuwa wani lokaci kallon kallo suka fara Eh junansu momy ce kamarya alhaji banganeba hannu yadagamata sannan yace zaki gane senan gaba mikewa yayi yashige dakinsa yayin da momy tabishi jiki asanyaye
Anwar ko ko ajikinshi domin ji yake ko atiti aka ce yazauna da princess dinshi zama zeyi matukar yana tare da ita dasauri yayi wanka yashirya yafita tare da excord dinshi bezame koinaba segidansu wani abokinshi dane ga megirma ministan yada labarai wato bala usman kaita
Naseer bala usman kaita shine babban abokin Anwar tun secondry school har zuwa jamia suna tare tun ahanya yamishi waya akan yana tafe dan haka koda isarsu suntarar yana jiransu awaje Anwar nasauka amota suka rungume juna Jan hannunshi masser yayi zuwa part dinsa ayko ruwa beshaba yafara ba naseer labarin auransa sannan yanuna masa hoton matar bakaramin murna naseer yataya abokinshiva har yana cewa abokina Allah yabaka duniya kayi kokari kasamu kiyama daganan suka shiga shirya yadda bikin zekasance.
love you all 😘 maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
_Written by Zahra Muhammad mahmud_
*page 31*
Lokacin bikin Anwar se karatowa yake yi yau saura kwana uku
Gaba daya Anwar yazama busy sabida zirgazirga yakosa adaura auren yayi tozali da kyakkyawar amaryarsa
Shima dady beda lokaci duba da yanayin aykinshi wani lokacinma baya kwana agida. Momy ce ke cigaba da hidimar komai duk da itama akwai nata aykin but bakamar dady ba
Kayan lefe kuwa tuni anhadoshi daga dubai baabunda babu fadin abinda ke cikin lefen ze cinye data baa gamaba
Bangaran dazasu zaunama tuni komai ansaka inkukaga daular daakasa abangaren da ilham zata zauna zaku dauka bazaa mutuba kayane na nunama saa yayinda shikuma megayya me ayki wato ango tuni yabada hotunan ilham akayimasa enlargemet dinsu manyan size yasaka agidan wasu kuma akayi editen danashi aka hada bame cewa batare suka daukaba abokanshi kuwa kowa yaga hoton amaryarsa murna suke tayashi insuka bukaci yakaisu sugaisa da ita sede yace bata gari wani lokacin har mamakin Anwar sukeyi sabida Anwar miskiline nabugawa ajarida amma yanzu yazama suda sabida auran ilham dazeyi
Ko invitation card na bikin abin