wa mijina afuwa idan har akwai kuskuren da ya aika..."
"A shekarun da suka gabata, an ce mahaifiyata ta yi irin wannan roƙon da bai amfane ta da komai ba. Zainaba! A matsayina na mijinki, kuma shugabanki. Ina umartarki da kada na sake jin bakinki a wurin nan."
Najibullah ya furta cike da ɗacin zuciya, jin haka ya sa Zainaba ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Ajiyar zuciya Sarki Gambo ya sauke, yana jin ɗaci a zuciyarsa. Ya ɗan russunar da kansa kaɗan, ta yadda ba kowa zai ji tattaunawarsu ba ya ce.
"Haƙiƙa tarihi yana ƙoƙarin maimaita kansa kenan Najibullah, sai dai ka sani. Idan har kai ka rayu, abin cikin iyalinka zai zama matacce, iyalinka kuma..."
Sai Sarki Gambo ya saki murmushi, sannan ya ɗago. Sai da ya dubi ilahirin mutanen da ke wurin, sannan ya ɗaga takobin hannunsa yana sakin dariyar ƙeta ya datse kan Najibullah da shi.
A razane Zainaba ta ƙwallah wata irin gigitacciyar ƙara, lokaci ɗaya ta faɗi a wurin babu numfashi. Tsoho Sulaimanu ya sunkuyar da kai ƙasa yana zubar da hawaye, jin abu ya gangaro jikin ƙafarsa ya sa shi buɗe idonsa. A nan ya ci karo da kan Najibullah, a razane ya janye ƙafarsa. Sarki Gambo ya sake kallon Ɗanjuma, ganin haka ya sa Ɗanjuma ya ƙarasa ya kunce tsoho Sulaimanu.
"A umarce shi da ya kawo mana kan wannan ƙasƙantaccan ɗakin gabas, ita kuma matarsa muna buƙatar a bata kulawa har zuwa lokacin da za ta haife cikinta. A tabbatar da an kawo mana jariri ko jaririyar da za ta haifa, ita kuma a killace mana ita." Sarki Gambo ya furta, sai ya fara takawa cikin izza fadawa suka rufa masa baya haɗe da yi masa kirari.
Lokacin da Sarki Gambo ya ƙarasa ɗakin gabas, a zaune ya samu Malami yana duba wata fatar ɓauna wacce take cike da ƙananan rubuce-rubuce. Zama ya yi a kujerar da take kallon ta Malami, Sarki Gambo fuskarsa ɗauke da annushuwa ya ce.
"Komai ya tafi daidai yadda muke muradi."
"Amma kuma tsugunne ba ta ƙare maka ba."
Malami ya furta yana cigaba da karatun ba tare da ya ɗago ba, da mamaki Sarki Gambo ya ce.
"Ai na ɗauka na yarda ƙwallon mango zan huta da ƙuda? Malami ina son ka fitar da ni daga duhu."
Malami ya ninke fatar hannunsa, sannan ya ce.
"Kana neman ka yi kitso da kwarkwarta Sarki Gambo." Cike da damuwa Takawa ya ce.
"Ban fahimce ka ba Malami, na fi so ka warware mini zare da abawa."
Miƙa masa fatar hannunsa ya yi ya ce, "Akwai wanda ya san duka tanadin da kake yi a cikin masarautar nan, domin kuwa a yau da safe na tsinci wasiƙar sirri zuwa ga abokan adawarka." Hannun Sarki Gambo yana rawa ya karɓi fatar ya duba, sai ya ci karo da cewar.
_Kada shirun da ka ji ya sa ka dakata da shirinka, akwai sauran rina a kaba. Domin kuwa ƙoƙofi ukun da kake muradin buɗewa ana shirin haramta maka su. Ba sai ka damu da sanin fatar dabbar da aka yi rubutun ba, kawai ka yi abin da ya dace._
Da mamaki Sarki Gambo ya ce, "Malami ban fahimci komai ba, shin mene ne amfanin wannan rubutun?"
Karɓar fatar Malami ya yi ya ajiye ta a gefe, sannan ya dubi Takawa ya ce.
"A ziyarar da ka kawo mini jiya, akwai wanda ya ji tattaunawarmu. Wannan wasiƙar za a tura ta zuwa ga ɗaya daga cikin sarakuna biyun da baƙin layi ya shata a tsakaninku. Ana sanar da su ka kusa mallakar kundi ukun da na maka bayani, shi ya sa aka siffanta su da ƙofa. Da aka ce kada a damu da sanin fatar dabbar da aka yi rubutu, ana nufin marubucin ba sai ya bayyana kansa ba."
Malami ya miƙe ya fara takawa, yana cikin haka suka ji an nemi izinin shiga ɗakin. Da kansa ya ƙarasa ya buɗe ƙofar, sai ga tsoho Sulaimanu hannunsa ɗauke da kan Najibullah. Kallon-kallo suka tsaya yi wa juna, tsoho Sulaimanu ya kafe shi da ido yana nazartar fuskar Malami da tsantsar cin amanar da ya yi masa.
A gaban Sarki Gambo aka dankwafar da shi, har zai fara magana Malami ya ce.
"Gambo sai ka sake miƙewa tsaye, domin na fahimci idon masarauta har yanzu yana kanka." Jinjina kai Sarki Gambo ya yi sannan ya dubi tsoho Sulaimanu ya ce.
"Duk wata tambaya da zan yi maka ka riga da ka san amsarta. Najibullah ya san maɓoyar kundi ɗaya, kai kuma kana da sani a kan ragowar. Idan ka sanar da ni, za ka tsira da rayuwarka. Idan kuma ka ƙi, za ka ƙare rayuwarka a kurkuku."
Murmushin takaici tsoho Sulaimanu ya yi ya ce, "Idan na sanar da kai ba tsira zan yi ba, don haka ni ba maci amana ba ne. Ba zan taɓa bayyana sirrin nan ba, kuma ina mai tabbatar maka. Lokaci zai zo da za a ɗauki kanka a hannu kamar yadda ka aiwatar wa Najibullah."
A fusace Sarki Gambo ya miƙe ya yi kan tsoho Sulaimanu, cikin zafin nama Malami ya shiga tsakiya. Sannan ya kai bakinsa saitin kunnensa ya yi masa raɗa, jinjina kai Takawa ya yi. Sannan ya koma mazauninsa, Malami ne ya leƙa ya kira sarkin ƙofa. Bayan ya shiga ya zube a gaban Sarki Gambo ya ce.
"Allah Ya taimake ka ranka shi daɗe."
"A ɗauki wannan tsohon a kai shi kurkukun ƙarƙashin ƙasa, ɗakin da Kursum take rayuwa." Sarki Gambo ya furta cikin taƙama.
"An gama ranka shi daɗe, Aljanna mai masoya da yawa. Sikari ba ka yi farin banza ba, ina gwanin wani ga nawa. Kabari mai ƙulla sabuwar abota, mutuwa mai sa a tuna barzahu. Gaba salamun bayanka salamun ubangidana maganin kukana, ka yi shekaran jiya, ka yi jiya kuma gobe ma da kai za a yi In Shaa Allahu."
Sarkin ƙofa yana gama yi masa kirarin ya tasa ƙeyar tsoho Sulaimanu, suna fita Malami ya saki murmushi sannan ya ce.
"Ka gama da wannan babin, idan har gumi ta yi gumi. Da ka tuntuɓe shi zai bada kai bori ya hau."
"Ai dole gyaɗa ta yi mai idan ta ƙi ta sha matsa."
Sarki Gambo ya furta yana sakin murmushi, shi da Malami sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama.
ZAINABA
Sarki Gambo yana fita, Dogari Nalami ya sallami ragowar mutanan. Ya bayar da umarni aka yayyafa wa Zainaba ruwa a fuska, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fara bin tsirarun mutanen da ke tsaye a kanta. Uwar bayi ce ta shiga ɗakin ta riƙo ta suka nufi can sashensu na bayi, Zainaba tafiya kawai take yi kamar wacce aka zarewa laka a jiki. A wani ɗaki aka ajiye ta mai ɗauke da mutane biyar, wata mai ciki ɗaya ta gani sai ragowa mata da yara. A gefe ta zauna, tana tuna al'amarin da ya faru da mijinta a kan idonta.
Sannu a hankali ta fara jin mara da bayanta suna yi mata ciwo, ta shiga yarfe hannu tana cije baki saboda a zaba.
"Ki tabbatar kin saka wa matar nan ido, Mai martaba ya ce tana haihuwa a kai masa abin da ta haifa ita kuma a killace ta. Kin san fa a yadda na ji an ce mijinta yana da tsohuwar tsattsamar alaƙa da Takawa, wai shi ya sa ya kashe shi. Kuma an ce kashe jaririn ma zai yi."
Ta ji muryar matan da suke tattaunawa daga wajen ɗakin, tagar ɗakin ta kalla ta ganta 'yar mitsitsiya. Ta ga ƙofar ɗakin a rufe ballantana ta nemi mafakar guduwa, tana cikin haka naƙuda ta ciyo ta gadan-gadan. Tun tana daurewa har ta fara kiran sunan Allah ƙasa-ƙasa, ɗaya daga cikin matan da ke ɗakin ce ta leƙa ta tagar ta ce.
"Wannan matar fa naƙuda take yi."
Dam! Ƙirjinta ya buga, tana nan zaune ta ga uwar bayi ta shiga ɗakin sannan ta sa aka fitar da ƙananan yaran. Yanayin da Zainaba take ciki ne ya tabbatar mata da ta galbaita, kuma har lokacin haihuwa shiru sai jinin da take zubarwa. Uwar bayi ce ta fita, domin ta sanarwa da Takawa abin da yake faruwa. Don ba ta fatan abin da zai sa ta ɓata wa Sarki Gambo rai, musamman da ta fahimci Zainaba na da matuƙar muhimmanci a wurinsa.
Bayan da aka shafe lokaci mai tsayi, Zainab ta haifo jaririnta namiji ƙato. Shigowar uwar bayi ɗakin tare da unguwar zoma ya sa ta ƙarasa wurinta da sauri, jaririn ta yi saurin ɗauka. Sai dai ganin ba ya numfashi ya sa jikinta ya yi sanyi. A ɗarare ta nufi wurin Sarki Gambo, ta zube a gabansa tana sanar da shi abin da ya faru. A tsammaninta ba ƙaramin faɗa zai yi mata ba, amma sai ta ga ko ajikinsa. Ya karɓi jaririn ya ajiye, sannan ya ce a yi gaggawar kawo masa Zainab. Uwar bayi tana fita, Sarki Gambo ya shiga uwar ɗakinsa. Daga ƙarƙashin gadonsa a kwai wani tsohon kabari, ya yashe ƙasar da hannunsa kamar yadda Malami ya ba shi umarni sannan ya tura jaririn ciki ya binne shi.
A daidai lokacin da aka kawo Zainaba dare ya fara yi, kuma a sannan Malami ya sake dawo wa wurin Sarki Gambo. Ta galabaita sosai, hatta idanunta da ƙyar take iya buɗe su. Ƙuri Malami ya yi mata da ido, sannan ya zura hannu a ƙasanta. Duk da yanayin da take ciki hakan bai hana ta kare kanta ba, cikin zafin nama ta bige hannunsa. Ta ɗago shayayyun idanunta tana jifansa da mugun kallo.
"Idan kin ba ni haɗin kai, ba zan wahalar da ke ba. Amma matuƙar za ki yi mini gardama, sai na wahalar da ke sannan kuma na gudanar da binciken da yake gabana."
Malami ya furta a ɗan fusace, Sarki Gambo ne ya take hannunwanta biyun. Duk yadda ta so ƙwacewa fir ta gagara, don haka Malami ya saka hannu ya dangwalo jinin ƙasanta. Ya shafe a jikin farin ƙyallen da aka shafe da shi da turaren jan Burhum, sannan ya dubi Sarki Gambo ya matsa ya fara yi masa raɗa a kunne. Wata mahaukaciyar dariya ya ƙyaƙyace da ita, sannan Malami cigaba da cewa.
"Ka tabbatar da ka bi kowacce hanya da kake ganin za ka bi, wacce al'umma ba za su yi saurin fahimtarka ba. Ka dakatar da masallatai biyun da ake gudanar da ibada a ciki, idan ba haka ba. Akwai miyagun al'amuran da za su cigaba da biyo baya."
Cikin damuwa Sarki Gambo ya ce. "Mene ne dalilin yin haka?"
"Idan ka aiwatar zan yi maka bayani daga baya."
Malami ya furta. Har yana gab da fita Sarki Gambo ya ce.
"Bayan waɗannan matsalolin, sai kuma rashin haihuwa da muke fama da ita Malami. Abin yana damunmu, domin a ƙallah mun doshi shekara goma babu haihuwa ni da Fulani Sadiya."
"Idan har ina numfashi za ka haihu Gambo, sai dai ba da Sadiya za ka haihu ba. Yarinyar da za ka aura jinin musulmai ce, wato Khadija. 'Ya a wurin Malam Ubaidu, limamin masallacin yamma. Iya bayanin da zan iya yi maka kenan, zan bincika maka yanayin gamuwar hallitar burujin tauraronku. Idan ban manta ba tauraronka kamar Aƙrabu ne, amma kuma a binciken da na yi kwanaki kamar Jadyu ne ɗabi'a nari. Kada na ja da nisa, ina buƙatar ganin tafin hannun yarinyar domin na karancin ilimin tafin hannunta, ina fatan dai ɗabi'arta ba za ta kasance Nari ba."
Malami ya furta yana shirin fita, har Sarki Gambo zai sake magana sai ya ɗaga masa hannu ya ce.
"A yau jawabin da zan yi maka kenan, ita kuma wannan ta gabanka ka aiwatar da abin da na sanar da kai tun lokaci bai ƙure ba." Yana gama maganar ya fita.
Malami yana zuwa bukkarsa ya samu Fulani Sadiya a tsaye, murmushi ya sakar mata sai ya ga ta sake haɗe fuska tamau. Kafin ya fara magana ta katse shi da cewa.
"Zuwa yanzu na gaji da gafara sa ban ga ƙaho ba."
Malami sai da ya zauna a kan buzunsa sannan ya ce, "Me kike ci na baka na zuba Fulani?"
"Lokaci yana tafiya, kwanakin Gambo suna ƙara tsayi, har yanzu ba ka hallaka shi ba. Ni kuma a kullum ruhin mahaifina yana sake azabtuwa, idan ba za ka iya ba zan aiwatar da kaina." Ta furta a fusace. Malami ya furzar da iskar bakinsa ya ce.
"Idan Gambo ya mutu yanzu babu ribar da za ki tsinta, rayuwar Gambo a tafin hannuna take. Amma ki sani, gaggawa ba za ta haifar miki da samun ɗa mai ido ba."
*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
07062062624
[23/11, 22:02] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA UKU
https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?mode=r_t
🛍️Assalamu Alaikum – Hafsat Collection ce!
Kinason kayan masu inganci masu kyau kuma cikin sauƙin farashi? To ba ki da matsala! 🥳💃
📌 HAFSAT COLLECTION ta kawo muku: ✨ Kayan gyaran gida
✨ Kayan ado da kyalliya
✨ Kayan mata da maza masu kwalisa
✨ Kayan kitchen masu kyau da karko
🔥 Duk a cikin farashi mai sauƙi!
📦 Muna a Kano, amma muna aikawa zuwa ko ina cikin amincin Ubangiji! 🙏
Maza ki shiga group ɗinmu yanzu:
👉
📌 Kasance da Hafsat Collection – Sayan daidai, ko sari!
https://chat.whatsapp.com/Gy2EPyKkG3IHqSxSzf0aCl?mode=r_t
Jim Fulani Sadiya ta yi kamar mai nazari, sai ta kafe Malami da wani irin kallo tana nazartarsa sannan ta ce.
"Ba na son na fara dasa zargi a kanka Malami, domin ka san duk duniya babu mutumin da na ba wa yarda kamar kai. Ina gudun na sakankance da kai, a kai gaɓar da za ka fara gasa mini gyaɗa a hannu."
Malami ya saki dariya sannan ya ce, "Tun da na binne sirrinki na wurin marigayya mahaifiyar Sarki Gambo. Ya kamata a ce kin watsar da duk wasu-wasin da ke ɗamfare a cikin zuciyarki, Fulani Sadiya ki sa a zuciyarki ni mai lulluɓa wa ruhinki rumfar kariya da binne sirrinki ne. Babu yadda za a yi na ci amanarki, kin sani na sani. Ni da ke muna amfani da Gambo domin mu cikar muradinmu ne, da zarar mun kai gaɓar da muke muradi za mu yasar da ƙwallon mangoro mu huta da ƙuda."
A fili Fulani Sadiya ta sauke gwauruwar ajiyar zuciya, sannan ta ɗora da cewa.
"Tun da haka ne, ina son haihuwa da Takawa. Ko babu komai zan bar magaji a masarautar Kajjura, masarautar da babu mai fahimtar gabanta da bayan har sai wanda ya gane sirrinta."
"Ba za ki haihu a masarautar nan ba."
Malami ya katse ta, ya cigaba da cewa.
"Haka kuma har yanzu ba ki san sirrin masarautar nan ba."
"Me ya sa ba zan haihu ba? Kuma wanne sirri ne ya rage da ban gama saninsa ba?"
Fulani Sadiya ta furta cikin damuwa, Malami ya saki murmushi ya ce.
"Saboda mahaifarki tana soke a dutsen Jaddum, haka kuma sirrin Masarautar nan ba za ki taɓa gane shi ba."
Malami ya furta yana buɗe ƙur'anin da ke gefensa, har za ta sake yin magana. Ya ɗaga mata hannu yana cewa.
"A yanzu ina da uzuri Fulani, kina iya dawowa bayan wani lokaci. Domin a daren nan zan sayi rauhanai biyar da za su yi mini wani aiki."
Sam ba haka Fulani Sadiya ta so ba, tana tafiya Malami ya saki murmushin da shi kaɗai ya san manufarsa. Sai da ya tabbatar da ta yi nisa, sannan ya ɗebi ƙasar sawun ƙafarta. Ya haɗe ta a cikin fatar farin maciji, sannan ya shiga bukkarsa ya ɗora a kan ƙaton shurin da ke tsakiyar gidajen tururwan da ke zagaye da shi.
SARKI GAMBO
Lokacin da Fulani Sadiya ta shiga ɗakinta, ta jima tana kaiwa da kawowa. Kamar wacce aka tsikara, sai ta ƙwala wa baiwarta kira. Cikin girmamawa ta zube ƙasa tana faɗin.
"Hutawarki lafiya uwar gijiyata, Allah Ya ja zamanin giwar sarki. Da yardar Allah Yarima yana bisa hanya, Aljanna mai masoya da yawa. Sikari ba ki yi farin banza..."
"A sanar da Jakadiya ta nemar mini izinin ganin mai martaba."
Fulani Sadiya ta furta a daƙile, jin haka ya sa Baiwa Indo ta sake zubewa ƙasa ta ce.
"An gama ranki shi daɗe, hutawarki lafjya mai farar zuciya."
Miƙewa ta yi ta fita kai tsaye ta sanar wa da Jakadiya saƙon Fulani Sadiya, babu jimawa Jakadiya ta nemi izinin shiga ɗakin Fulani Sadiya. A gaggauce ta amsa mata, don a ɗokance take da son ganinsa a wannan lokacin.
"Allah Ya taimake ki, Allah Ya tsare gabanki da bayanki. Takawa bai amsa goron gayyatarki ba, a yi mini afuwa ranki daɗe." Jakadiya ta furta tana sunne kai ƙasa, rai a matuƙar ɓace Fulani Sadiya ta ce.
"Saboda me Takawa zai yi mini haka?"
Jakadiya ta waiga hagu da dama, sannan ta sunne kai ƙasa ta ce.
"Allah Ya taimake ki, ki gafarce ni da abin da zan faɗa."
Kallon tsaf Fulani ta yi mata ta ce, "Tafi kanki tsaye."
Jakadiya ta sake yin ƙasa da murya ta ce.
"Allah Ya taimake ki wannan maganar ba za ta faɗu ba, sai dai na raɗa miki a kunnenki."
Kamar Fulani ta dakatar da ita, sai ta gyaɗa mata kai. Jikin Jakadiya har rawa yake yi, ta matsa saitin kunnen Fulani Sadiya ta fara yi mata raɗa a kunne. Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi, amma sai ta kawar da damuwar fuskarta ta ce.
"Jakadiya an jima zan aiko mini da kyautar alkaki, domin ba zan bar wannan albishir ɗin ya tashi a banza ba."
Jikin Jakadiya har rawa yake yi ta zube a ƙasa ta ce.
"Godiya nake ranki shi daɗe, an gaida farar mace alkyabbar mata. Allah Ya taimake ki ina neman alfarmar da a taimaka a rufa mini asiri."
Fulani Sadiya ta saki murmushi ta ce, "Kada wannan ya dame ki Jakadiya, ina mai yi miki albashir da yanzu ma muka fara." Jakadiya ta sake zubewa a ƙasa tana godiya sannan ta fita.
TSOHO SULAIMANU
Lokacin da sarkin ƙofa ya tasa ƙeyar tsoho Sulaimau tafiya mai nisa suka yi a cikin masarautar, sai da suka je bakin wata katanga sannan ya damƙa shi a hannun Sarkin horo da ke tsaye fuska babu ɗigon fara'a. Kallo ɗaya tsoho Sulaimu ya yi masa, ya fahimci rashin imani da ƙeƙashewar zuciya ya samu gurbin zama a zuciyarsa.
"Mai martaba ya bayar da umarnin a killace shi a kurkusun ƙasa, a tabbatar da a saka shi a ɗakin Kursum."
Sarkin ƙofa ya furta, sannan ya damƙa shi a hannun Sarkin horo. Kai kawai ya gyaɗa masa, ya dubi tsoho Sulaimanu da jajayen idanunsa masu kama da sabon borkono. Wanda suka sa cikinsa ya kaɗa saboda tashin hankali, da ƙarfi ya hankaɗa tsoho Sulaimanu. Suka bi ta wata siriiriryar hanya, sannan suka ɓulla gaban wata ƙatuwar ƙofa wacce aka sassaƙa ta da farin ƙarfe. Ilahirin saman wurin a zagaye yake da ƙarfe, sai wasu dogarai da ya ci karo da su fuska a murtuke babu alamar fara'a. A nan ma tafiya suka yi mai ɗan nisa, sannan suka ƙarasa wani wuri mai duhun gaske, harshen wuta ya ga an miƙe wa Sarkin horo. Ya karɓi itacen yana haska musu, a nan tsoho Sulaimanu ya ci karo da waɗansu ƙananun ɗakuna. Numfarfashin mutane ya dinga ji sama-sama, wasu kuma ya ji suna roƙon a taimaka a ba su ruwa.
Tsoro ne ya mamaye shi, har yana jin ƙafafuwansa sun yi wani irin sanyi kamar ba na shi ba. Wata mai tsohon ciki ya hango a zaune, cikin galabaita tana cewa.
"Ku taimaka mini da abinci, yau ne ranar da za a ba ni na ci. Wayyo Allah cikina, ku taimaka mini da ruwa ko cikin tafin hannu ne."
Cikin tsawa ya ji Sarki horo ya ce.
"Idan kika sake magana, sai kin maimaita kwanakin karɓar abincinki kafin a ba ki ki ci."
Ba ita kaɗai ba, lokaci ɗaya tsoho Sulaimanu ya ji hatta mutanen da ke numfarfashi sun yi tsit kamar an yi ruwa an ɗauke. Jikinsa a sanyaye suka ƙarasa bakin wata ƙatuwar rijiya, wacce aka sassaƙa murfinta da dalmar baƙin ƙarfe.
Mukulli Sarkin horo ya saka ya buɗe, ya dubi tsoho Sulaimanu ya ce.
"Wuce mu je."
Cikin tsoro, firgici da tashin hankali tsoho Sulaimanu ya ce.
"Ina?"
Tass! Ya sauke masa mari a fuskarsa, nan take ya ji kunnensa ya yi dum! Kansa ya yi masa nauyi, juwa ta fara yunƙurun taɗe ƙafarsa. Bakinsa da hancinsa ne yake zubar da jini, don tun da ya zo duniya bai taɓa jin marin da ya gigita kwanyarsa kamar wannan ba.
"Mu je na ce!"
Sarkin horo ya sake buga masa tsawa, tun bai rufe baki ba tsoho Sulaimanu ya yi sauri zura ƙafarsa, sai a lokacin ya lura da marattakalar benen ciki. A haka Sarkin horo ya tasa ƙeyarsa har suka kai ƙarshen matattakalar benen, sai dai suna gama shiga ya ga tsananin duhun wurin har ya ninka na baya da suka baro. Ƙananun ɗakuna ne ƙuntatattu, gaban tsoho Sulaimanu yana bugawa bai yi aune ba ya ji Sarkin horo ya buɗe wani ɗaki ya hankaɗa shi ciki. Ji ya yi ya ci karo da abu mai gashi, nan take hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi.
Harshen wutar ya ziro musu, sai a lokacin ya lura da hallitar mai zubin mutum kuma mace ce a gefensa. Sai dai gashin da ya lulluɓe kanta zuwa jikinta ya sake hautsina hanjin cikinsa. Cikin muryarsa marar daɗi ya ji Sarkin horo ya ce.
"Shawara ɗaya zan ba ka, idan har wani abu Mai martaba yake nema a wurinka, yana da kyau ka ba shi haɗin kai domin amfanar gobenka. Idan ba haka ba, sai ka fi Kursum lalacewa. Domin ita kai tsaye ɗakin horo aka fara kai ta, taurin kanta ne ya kawo ta zuwa ga wannan matsayin. Kai kuwa tashin farko ɗakin ƙasa Mai martaba ya ce a saka ka, na tabbata hukuncinka sai ya fi naka muni matuƙar ba ka bayar da kai bori ya hau ba."
Sarkin horo yana gama faɗa ya fice daga wurin, sannan ya rufe rijiyar da mukulli kamar yadda ya same ta da farko.
Wani irin tsoro ne ya mamaye zuciyar tsoho Sulaimanu, gabansa yana faɗuwa ya ce.
"Sannu malama kursum."
Shiru ya ji ta yi masa, bai daddara ba ya sake maimaitawa. Bai yi tsammani ba sai ji ya yi ta karce shi da farcenta, wanda hakan ne ya sa shi jin ɗumin da ya tabbatar masa da jini ne yake zuba. A ɗarare ya ja gefe, duk da ba ya iya ganin koda tafin hannunsa. Sai kawai ya fashe da kuka, sannan ya ɗaga hannuwa sama yana roƙon Ubangiji Ya kawo masa ɗauki.
SASHEN BAYI
Tun sassafe da gari ya waye kowacce Baiwa ta kama gabanta, domin gudanar da aikin da ya zame musu ta kamar sallar farilla. Ɗakin shiru babu kowa sai Baiwa Sakina da ke rungume da jaririn hannunta, kallon fuskarta yake ƙir kamar yana tantance surarta. Murmushi ta sakar masa, ta kai hannu