Share this page
da ya sake ba su mamaki da tsoro jin shiru babu wani al'amari da shi, don dama tun hawansa mulki suke jin raɗe-raɗin ana cewa shi ma Dikko hatsabibin kansa ne. Tun daga wannan lokacin suka bayar da kai bori ya hau, suka zame masa tamkar raƙuma da akala saboda yadda suke yi masa biyayya sau da ƙafa. Shi kuma Diko ya cigaba da murza kambumsa yana yin sarauta yadda ya ga dama, saboda hatta dattawan ciki fada shakkarsa suke yi. Babban tashin hankalin da Sarki Dikko ya fara fuskanta akan haihuwa ne, ba don ba ya haihuwa ko iyalinsa ba sa haihuwa ba. A lokacin da uwar gidansa ta fara haihuwa sai ya zama duk yaran da take haifa masu nakasa ne, daga makafi sai masu shanyewar ƙafa da hannu. Waɗansu kuma masu taɓin ƙwaƙwalwa ta yadda ba za su mori ba. Da farko sai ya yi tsammanin daga ɓangaren uwargidansa ne, don haka ya ƙara aure sai dai ita ma tana zuwa ta haifo masa jariri mai shanyewar jiki. Amma duk waɗannan al'amarun da suke faruwa, Sarki Dikko bai taɓa bari labarin haihuwar masu nakasar da yake yi ya fita ba. Saboda killace yaran yake sa wa ayi, tare da yi wa masu tsaronsu bazaranar matuƙar zancan ya fita sai ya hallaka su. Da al'amarin ya fara ci masa tuwo a ƙwarya, sai ya sa amintaccansa wato Waziri. Da ya nemo masa hatsabiban bokayen da su iya warware masa matsalarsa, kuma duk ƙiyayyarsa da addinin kiristanci sai ya amince da a kira malaman addinin a sirrance domin su kawo masa ɗauki. Amma kowanne da ya jarraba maganinsa sai ya ga aikin bai ci ba, don haka ya cigaba da bada ƙarfi a ɓangaren addininsa na gargajiya. Aka cigaba da nemo masa bokayen da ke aiki da ruhin magabata, amma sai lamarin ya girme wa tunaninsa. Sarki Dikko (1835) Cikin damuwa yake duƙurshe a gaban tsohuwar bukkar da aƙalla za ta kai shekara hamsim, Waziri da ke gefe ya sunkuyar da kai cikin damuwa. Hatsabibin bokan ne ya ratso ta jikin dutsen da ke kallon bukkar, sannan ya ƙarasa gabansu ya zaune a kan shurin da ke fuskantarsu. Waziri ya ɗan russuna ya ce, "Ran boka ya daɗe, fatan shekaru masu yawa irin na dabino. Ina mai ja da aikinka ya zo a nuna masa ƙarshensa, ba don ka hana a bauta maka ba da babu mahalukin da ya isa ya hana mu fara bauta maka ya kai boka Tsumbur." Jin irin kirarin da Waziri yake yi wa Boka Tsumbir ya Takawa jin ɗaci a zuciyarsa, saboda shi mutum ne mai tsananin kishi. Don ba ya san ko kaɗan ya ga al'umarsa na fifita wani fiye da shi. "Ya kai shugabana, a yau tare nake da Sarkin masarautar Zulwara..." "Sarkin da yake ƙyashin fifikon wani a kansa, sarkin da yake gabana amma yake jin ban isa a ba ni matsayin da ka ba ni ba. Sarki da yake fama da matsalar haihuwar masu nakasa, kuma a yanzu ma kun zo gabana domin na taimaka muku a kan haihuwar masu nakasar da aka yi masa da asubar yau." Boko Tsumbur ya furta yana ƙura wa Sarki Dikko idanu, a sanyaye Sarkin ya sunkuyar da kai ƙasa. Duk sai ya ji kunya ta kama shi, don duk a kalaman bokan babu wanda ya yi ƙarya a ciki. Saboda lokacin da Waziri yake masa kirari ji yake kamar ya ƙarasa ya shaƙe shi, Waziri ya katse masa tunanin da cewa. "Tuba yake uban kowa, tuba yake mai taimakon kowa." Boka Tsumbur bai tanka masa ba, ya miƙe a gabansu ya saki fitsari a saman shurin da yake zaune. Sai kuma ya mayar da ganyen jikinsa ba tare ya yi tsarki ba, ya ya ɗebi kasar shurin da ta jike da fitsarin ya miƙa wa Sarki Dikko. A tsantsance Sarkin yake kallonsa, Boka Tsumbur ya zuba masa daƙwa-daƙwa idanunsa sannan ya ce. "Ka yi imani da wannan ƙasar shurin ita ce mai rayawa kuma mai kashewa. Sannan ita za ta sa na taimaka wa duk matsalar da kake ciki, kuma sai ka yi imani da wannan shurin ya fi abin bautar da kake bautawa." Jim Sarki Dikko ya yi, cikin sauri Waziri ya ce. "Ya amince tabbatacan boka." Sarki Dikko kallon Waziri ya yi, ya fakaici idon Boka Tsumbur ya matsa hannunsa alamar ya ce ya amince. Cikin muryar takaici da ganin gazawarsa Sarki Dikko ya ce. "Mun amince." Wata mahaukaciyar dariya Bokan ya saki sannan ya fara yi wa kansa kirari, "Sai ni bokan da har gobe babu wanda ya kai ni, sai ni Tsumbur jikan maguzawa masu abin mamaki. Sai ni waraka ga duk wanda ya raɓe ni, sai ni mai abin bautar da babu wanda ya kai ni." Sai ya waigo ya dubi Sarki Dikko ya cigaba da cewa. "Matsalar 'ya'yanka ba daga matsalar iyalinka ba ne, wannan matsalar tana da alaƙa da kisan da ka yi wa Boka Damina. Don haka ko yanzu matanka suka tara da wani namijin za su haifi lafiyayyun yara." "Zafin kishina ba zai bari na saki mace ta yi wani auren ba, babu wanda ya isa ya aikata wannan mummunan aikin a kan macen da na santa." Sarki Dikko ya furta a fusace, murmushi Boka Tsumbur ya yi ya ce. "Ƙarfin zuciyarka yana matuƙar birge ni Dikko. Sai dai ka sani daga nan har ka mutu ba za ka taɓa haihuwar lafiyayyun 'ya'ya ba." A razane Sarki Dikko yake kallonsa, Boka Tsumbur ya cigaba da cewa. "Sai dai waɗannan jariran da aka haifa maka za mu iya warkar da su." "Ka taimaka mini Boka Tsumbur, wallahi ina cikin tashin hankali domin a yanzu babu ɗa ɗaya ƙwaƙƙwara da zan ɗaga wanda zai gaji karagata." Boka Tsumbur ya ɗebi ƙasar shurin ya watsa a wutar da ke ci a gabansa, sannan ya ce. "Za su warke matuƙar ka lamunce da sharaɗin da za mu kafa maka." Cike da rashin dogon nazari Sarki Giɗaɗo ya ce. "Kowanne irin sharaɗi ne a shirye nake da na tunkare shi. Na amince da sharaɗinka Boka Tsumbur." "An haifa wa Sarki Gambo tagwayen mata, adaidai gaɓar da iyalinka ta haife maka tagwayen yaranka mace da namiji. Macen da aka haifa maka makauniya ce, shi kuma namijin ƙafafuwa da hannuwansa a shanye suke." Sarki Dikko ya sunkuyar da kai ƙasa cikin takaici, boka Tsumbur ya cigaba da cigaba da cewa. "Don haka za mu musanya lalurar 'ya'yanka zuwa kan 'yan tagwayen da Sarki Gambo ya haifa." "Amma me ya sa sai Sarki Gambo? Boka Tsumbur ko ka san ni da Sarki Gambo kamar wuta da ruwa muke, idan har sarki Gambo yana ƙaunata. Ko kuma idan ina ƙaunar Sarki Gambo to zan ƙaunaci mutuwata, ta yaya 'ya'yana za su yi amfani da surar 'ya'yan maƙiyina?" Boka Tsumbur ya yi saurin katse Sarki Dikko da cewar. "Saboda ba ka san jinin wace ce a jikin 'ya'yan Gambo ba, da ace ka san wace ce mahaifiyar yaran nan. Na tabbata da ka zabarce ta cikin rayuwarka tun kafin mutuwarta, kamar yadda wani ƙudurin Sarki Gambo ya sa shi aurenta ba don yana sonta ba." Ajiyar zuciya Waziri ya sauke, ya yi ƙasa da murya yana yi wa Sarki Giɗaɗo raɗa. "Ranka shi daɗe ka ajiye batun gabarku a gefe, ka fuskanci abin da yake gabanka. Wannan wata dama ce ta idan ta kuɓuce ba lallai mu sake samun ta ba, kada ka manta ranka shi daɗe. A ƙalla yau shekara biyar kenan ina bibiyar Boka Tsumbur a kan ya ba mu damar ganinsa, amma sai yau ya ba mu wannan damar." Shiru Sarki Giɗaɗo ya yi yana nazari, cikin zafin nama ya ce. "Mun amince Boka Tsumbur." Dariya Bokan ya saki marar daɗin sauraro, sai ya saka hannunsa a cikin wutar gabansa. Ya ɗauko wani allon farin ƙarfe, ya soka a jikin shirun sannan ya fara biya ɗalasiman tsafi, yana kiran sunayen manyan aljanun da suke yi masa aiki. Wani ruwa mai kamar jini da ke tafasa ya ɗiba ya watsa a kan allon, nan take hoton jariran Sarki Gambo da ke kwance Unguwar zoma tana yanke musu cibi suka bayyana. Daga gefe kuma jariran Sarki Dikko ne kwance a saman gadon mahaifiiyarsu, ruwan ya sake watsa musu lokaci ɗaya jarirai huɗun suka fashe da kuka jikinsu yana wata irin karkarwa. Har sai da Sarki Dikko ya tsorata da ganin abin da yake faruwa da su, Boka Tsumbur ya ɗago ya dube su ya ce. "A yanzu haka duk irin tawaya da nakasar da ke jikin jariranka, sun koma yaran Sarki Gambo. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba." Da sauri Sarki Dikko ya dube shi yana shirin yin magana suka ji tsibirin ya yi wata irin tsawa mai razanarwa. *Ummmou Aslam Bint Adam*🌚 07062062624 [24/11, 15:59] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA SHIDA Masarautar Kajjura A haukace Sarki Gambo ya ƙarasa cikin zafin rai, ya maƙure wuyan Fulani Sadiya har sai da ta fara kakari. Murya a kausashe ya ce. "Saboda me za ku kashe mana iyali? Saboda me za ku raba mu da uwar 'ya'yanmu?" Fulani Sadiya ta tattara ƙarfinta ta fisge hannunta da ƙyar, sannan ta gyara zaman rigarta ta ce. "Saboda har yanzu ba ka gama karantata ba, saboda har yanzu ba ka tantance maƙiyin ɓoye da na zahiri ba." Ta yi jim tana shafa wuyanta da har lokacin yake yi mata raɗaɗi sannan ta cigaba da cewa. "Ranka shi daɗe! Kana tsammanin zan kashe Fulani Khadija sannan na bar 'ya'yan da ta haifa? Me ya sa ban haɗa har su na hallaka ba? Mai martaba! Yana da kyau ka nutsu domin ka san wanɗanda suke zagaye da kai. Amma Allah Ya taimake ka, ka san ba zan taɓa cutar da kai ba." Fulani Sadiya tana zuwa nan sai ta fara zubar da hawaye, jikinsa ne ya yi sanyi. Ya riƙo ta a jikinsa, sai Fulani Sadiya ta sake fashewa da kuka ta ce. "Na yi mamaki da har kake tsammanin zan iya cutar da Fulani Khadija, a duk tsawon shekarun da muka ɗauka. Ban taɓa tsammanin za ka yi mini mummunar shaida ba, ko don ban haihu ba kake yi mini haka oho?" Ta sake fashewa da kukan kissa, nan take tausayinta ya kama shi. Cikin tattausan lafazi ya ce. "Ku yi haƙuri Fulani, mutuwar Fulani Khadija ta gigita mu." "Ina yi maka ta'aziyya ranka shi daɗe." Fulani Sadiya ta sake furtawa tana kwantar da kai. A gaggauce Sarki Gambo ya fita daga ɗakinsa, ya koma rumfar ya zauna. Abin duniya goma da ashirin ya haɗe masa, dafe kansa ya yi da hannuwa biyu yana nazarin al'amuran baya da suka shiga tsakaninsa da Fulani Khadija. Unguwar Zoma Lami tana zaune tana yankewa tagwayen Sarki Gambo cibi, ta ga jikinsu ya fara wata irin karkarwa. A ɗan tsorace ta ajiye su tana kallo, tana cikin haka Jakadiya ta shiga ɗakin tana wurga mata tambaya. "Me ya faru Lami? Me ya samu jariran nan? Lami kada ki jefa mu a masifa mu shiga uku, kin ga dai uwarsu a hannunmu ta mutu. Yanzu idan wani abin ya samu yaran nan me za mu cewa Mai martaba?" Jikin Unguwar zoma nan take ya cigaba da karkarwa, bakinta yana rawa ta ce. "Wallahi ban san me ya faru da su ba Jakadiya, ki yadda da ni haka na ga suna karkarwa ba tare da komai ba." Unguwar zoma ba ta gama rufe baki ba, suka ga ɗaya daga cikin jariran ta fara jijjiga kai. Nan take wani ruwa mai kamar na ɗaurayar nama ya fara zuba daga idonta a madadin hawaye. Ɗayar kuma ƙafafuwnata suka shiga karkarwa, irin ruwan da ke fita daga idanun ɗayar shi ma ya fara tsattsafowa daga jikin ƙafafuwanta. Jakadiya da Unguwar zoma kallon juna suka yi cike da tsoro, Jakadiya ta yi ƙasa da murya ta ce. "Lami kina ganin abin da idanuna suke gani?" "Ina gani Jakadiya, magana ta Allah na jima ban ga haihuwar da ta zo mini da al'ajabi kamar wannan ba." Lami za ta yi magana, suka ji muryar Shamaki daga dokin ƙofa. A daidai lokacin uwar Bayi ta shiga ɗakin, duk suka yi carko-carko. Daɗin da suka ji a lokacin jariran sun dakata da kukan da suke yi, kuma ruwa da karkarwar da suke yi duk sun daina. A ɗan ɗarara Lami ta ɗauke ta ta cigaba gaba da gyara su, sannan Jakadiya ta ɗauke su ta fita da su. Dangin Fulani Khadija ne suka yi wa gidan sarautar tsinke, mahaifiyarta ban da kuka babu abin da take yi. Koda aka nuna musu jariran ba su bi ta kansu ba, suna shiga da suka ga irin kisan da aka yi mata duk sai jikinsu ya sake yin sanyi. Mahaifiyarta ta dubi mahaifin Fulani ta ce. "Malam dama sai da na ce maka ba na son auren nan na Hadiza a gidan sarauta amma ka ƙi ka ji, dubi yadda makircin masarautar nan ya sa aka hallaka mana ita." "Fatima! Ke musulma ce, kuma kin sani da Khadija ta yi aure a nan da mu aurar da ita a wani wurin ba nan ba. Duk abin da Allah Ya ƙaddara a cikin rayuwarta sai ya faru, abin da za ki yi mata a yanzu addu'a ce. Idan har 'yata Khadija ba ta da haƙƙi a wannan kisan da aka yi mata, na tabbata sai Ubangiji Ya yi mata sakayya." Mahaifin Fulani Kgadija ya furta yana ɓoye hawayen da ke gangarowa daga idonsa. Fulani Sadiya Fulani Sadiya tana fita daga ɗakin Takawa kai tsaye ɗakinta ta nufa zuciyarta fes, sai da ta shiga ɗakinta sannan ta fara kai kawo cikin farinciki ta ce. "Fulani Zainaba ke kaɗai kika rage mini. Tun da har Fulani Khadija ta tafi, na tabbata kema ta ki tana hanya. Sai na tabbatar da na aiwatar da ƙudurina, a kan duk wanda zai ba ni matsala a doron ƙasa koda kuwa Sarki Gambo ne." Motsi ta ji daga cikin ɗakinta, da sauri ta ɗaga labule ta shiga. Cikin girmamawa Baiwa Sakina ta zube a ƙasa ta ce, "Barka da shigowa ranki shi daɗe." "Tun yaushe kike a nan?" Fulani Sadiya ta furta da sauri, saboda ba ta yi tsammanin akwai wani a ɗakin ba. "Allah Ya taimake ki kafin fitarki kin manta kin saka ni gyaran ɗaki. Amma idan na yi laifi ki gafarta mini ranki shi daɗe." Baiwa Sakina ta furta tana sake russunar da kai ƙasa, saboda yadda gabanta yake faɗuwa. Domin wani irin tsoron Fulani Sadiya ne ya mamaye ta. "Sakina!" Fulani Sadiya ta kira ta da wata irin murya, a sanyaye Baiwa Sakina ta amsa. Sannan Fulani ta cigaba da cewa. "Ki ji kamar ba ki ji ba, idan kika yi yunƙurin furta kalma ɗaya daga cikin abin da kika ji. Na rantse da girman Yesu mai ceto, sai na sa an yi miki azabar da ba a taɓa yi wa wani mai numfashi a cikin gidan nan ba, sai na wulaƙanta ruhinki ta yadda za ki dinga yagar naman jikinki kina ci da haƙoranki." A razane Baiwa Sakina ta ɗago, sai ta rarrafa a guje zuwa gaban Fulani ta ce. "Ki yi mini afuwa Fulani, Na tuba wallahi ba zan taɓa aikata miki wannan kuskure ba." Fulani Sadiya ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce. "Daga yau idan kika sake kika ɓoye mini wani abu, wallahi ranki zai yi mummunan ɓaci. Idan kika bari na gano wata manaƙisar da kike ɓoye mini za ki yaba wa aya zaƙinta. Kuma daga yau, za ki fara shiga cikin wasu al'amuran da nake gudanarwa a bayan fage." A wannan karon ma cikin tsoro haɗe da girmamawa Sakina ta amsa mata, daga ƙarshe Fulani Sadiya ta sallame ta. Jikin Baiwa Sakina yana rawa ta nufi sashen bayi, tana mamakin jin miyagun abubuwan Fulani Sadiya take aikatawa. A ɓangare ɗaya ta shiga fargabar rantsuwar da ta yi da Yesu mai ceto, saɓanin Allah Ta'ala da ta san gabaɗaya cikin masarautar suna bautawa. Baiwa Sakina tana shiga harabarsu ta hangi Ridwan zaune a gefe, daga can nesa tsirarun yaran bayi ne suke ta wasanninsu. Ƙarasawa ta yi wurinsa ta ce, "Ridwan!" Ɗagowa ya yi ya kalle ta, nan take ta ga idanunsa sun kaɗa jajir kamar sabon borkono. Gabanta ne ya faɗi, don haka ta matsa kusa da shi ta ce. "Me yake damunka Ridwan?" "Wallahi sai na kashe ta." Ridwan ya furta cike da ɓacin rai, Baiwa Sakina tana shirin sake magana ta ga ya furzar da wani gudan jini daga bakinsa. Tana nan tsaye ta ga ƙasar wurin da jinin ya ɗiga ta rauzaye ta faɗa ciki. Tsoro ne ya sake mamaye ta, duk da ba a wannan lokacin Ridwan ya saba baƙin al'amura masu ɗaure kai ba. Amma na wannan lokacin ya tsorata ta, don jin kalmar kisa da ta yi ya firgita hanjin cikinta. "Ridwan me kake faɗa haka? Duka shekararka goma amma har kake furta kalmar kisa, wa za ka kashe? Kuma a ina ka ji wannan kalmar?" Baiwa Sakina ta kawar da tsoron da ke kwance a saman ƙirjinta, ta furta masa tana kallon yanayinsa. Manyan idanunsa ya ɗago ya zuba mata, har sai da ta ji tsoro ya mamaye ta. Sai ya kawar da kai cike da rashin damuwa ya ce. "Ba ki santa ba." "Kai a ina ka santa?" Baiwa Sakina ta furta cikin sauri, Ridwan ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Tana masarautar Judala, masarautar Sarki Giɗa..." "Kul." Baiwa Sakina ta furta tana toshe masa baki da hannunta, jikinta yana rawa ta ja hannun Ridwan ɗaki. Sai da ta zaunar da shi a kan gado sannan ta ce. "Kul Ridwan, koda wasa kada na sake jin Masarautar Judala a bakinka. A ina ka ji sunan? Ko kana son wani ya kai wa Mai martaba tsegumi a hallaka mini kai? Ba ka san furta sunan masarautar a cikin wannan masarautar kusan daidai yake da hukuncin kisa ba?" Kawar da kansa ya yi gefe yana taɓe baki sannan ya ce, "Haka kawai na ji ba na sonta, shi ya sa nake son kashe ta. Kuma Masarautar Judala ai masarautarmu ce, mahaifata ce..." "Me kake faɗa ne Ridwan? Wa yake faɗa maka waɗannan maganganun?" Baiwa Sakina da ta gama firgicewa ta katse Ridwan, Ridwan ya washe baki cikin rashin damuwa ya ce. "Wallahi Inna wata tsohuwa ce take faɗa mini, kuma duk dare ma a can nake kwana. Ta ce za ta sanar da ni maɓoyar Kundi ukun da sarakuna uku suke son mallaka, amma wai ai sai na ƙara girma." Kusan mutuwar zaune Baiwa Sakina ta yi, tana son sake tambayarsa amma tsoro ya mamaye ta. "Kuma a can na ga an haifi Batul! Ni kuma ba na sonta shi ya sa nake son kashe ta." Ridwan ya sake faɗa cikin damuwa, Sakina ta kamo hannunsa ta ce. "Kana son ka daina ganina Ridwan? Ko kana son na dinga yi kuka?" Da sauri ya girgiza mata kai, Sakina ta cigaba da cewa. "To ka daina faɗar irin maganganun nan, idan ba haka ba waɗannan maganganun za su kai mu har gaban Mai martaba. Kuma zai iya zartar mana da hukuncin kisa." "Shi ma Sarki Gambon ba na sonsa, ta ce mini na kashe s..." A wannan karon da sauri Sakina ta sake toshe masa baki gabanta yana faɗuwa. 'Na shiga uku ni Sakina, me Ridwan yake neman janyo mana?' Ta raya a ranta tana zubar da ƙwallah. "Inna kin ga can fa." Ridwan ya furta cikin murmushi yana nuna mata kusurwar bangon ɗakin. SARKI GAMBO Sarki Gambo yana zaune aka kai masa tagwayen jariransa duka mata, waɗanda ya yi wa laƙabin Hasana da Usaina. Kowaccensu ta saka hannu a baki tana tsotsa. Jiki a sanyaye dogaransa suka sunkuyar da kansu ƙasa, Sarki Gambo ya fara zubar da hawayen tausayin halin da jariransa suke ciki. Ya jima a haka, sannan aka iso aka sanar da shi an gama haɗa gawar Fulani Khadija za a sallace ta. Da ƙyar Sarki Gambo ya iya miƙa wa Shamaki su, ya bayar da umarnin a kai su ɓangaren Fulani Sadiya domin ta kula da su. Sannan ya ce a tabbatar da an tatsi nonon awaki an ba su don gudun kada yunwa ta illata su. Cikin ƙanƙanin lokaci mutane da dama suka sallaci gawar Fulani Khadija, don mahaifinta ne ya jagoranci sallar gawarta. Bayan da aka kai ta gidanta na gaskiya, mahaifiyar Fulani ta nemi da a bata jariran domin ta kula da su. Amma fir Sarki Gambo ya ƙi amincewa, saboda tsananin soyayyarsu da yake ji a cikin zuciyarsa. Kusan wuni guda Sarki Gambo ya yi yana karɓar gaisuwar Fulani Khadija, sai yamma liƙis ya shiga turakarsa. Da shigarsa babu jimawa, Jakadiya ta zo nema wa Fulani Zainaba iso wurinsa. Ya yi matuƙar mamaki, don haka kai tsaye ya amsa wa baƙuntarta. Sallama ɗauke a bakinta ta shiga, sai dai kamar kullum fuskarta a cunkushe take babu ɗigon fara'a. Sai da ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi sannan ta ji ya ce. "Mun yi matuƙar mamakin ganinku Fulani Zainaba, yau kusan shekara goma kenan da shigowarku rayuwarmu. Sai dai ba ku taɓa neman izinin ganinmu a turaka ba, idan ba mu muka nemi ƙeɓewa da ku ba." "Saboda babu buƙatar hakan a tattare da ni, a yanzu ma akwai dalilin da ya kawo ni turakarka." Fulani Zainaba ta furta cikin tsana, Sarki Gambo ya saki murmushi ya ce. "Zainaba ba za ki taɓa sauyawa ba." "Zan sauya Sarki Gambo, amma lokaci alƙali ne yana nan tafe." Ta ba shi amsa kai tsaye, sai kuwa ya ƙura mata ido. Ita ma ba ta janye idonta ba, ta cigaban da kallonsa har sai da ya matso gabanta ya ce. "Dalilainmu masu muhimmanci ne suka sa muka bar ku a raye Zainaba, tun da kun san ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba." Fulani Zainaba ta saki murmushin takaici ta ce, "Ni kuma Ubangiji Ya ja da kwana ne, domin na fahimtar da kai kuskuren da ka tafka a baya." A fusace Sarki Gambo ya ɗago, Fulani Zainaba ta girgiza kai cike da takaici ta ce. "Na zo na ji ya aka yi Fulani Khadija ta mutu? Don ina zargin wani abu a mutuwar baiwar Allahr nan. Sanar da ni, ya aka yi aka haihu a ragaya? Domin a sanin mugun halin da na yi maka tun daga shigowata gidan nan, na tabbata babu abin da ba za ka iya aiwatarwa ba." Da sauri Sarki Gambo ya dube ta, cikin zafin rai ya ƙarasa ya maƙure wuyanta. *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 07062062624 [24/11, 17:29] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna

Chapter 4 of 11