Share this page
da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA BAKWAI ADVERT *MUM NIMRAH'S GRILL FISH AND SHAWARMAR* 'Yar uwata kema kina fama da kwadayin kayan kwalam da makulashe?To ina yi miki albishir da ki garzayo wajan Mum nimrah's grill fish and shawarma don farantawa bakinki, mai gidanki, yaranki, iyayenki da zuciyar ki da haddaden grill catfish or tilapia.😋💃🏻 Sai kuma beefshawarma Akan farashi me sauki. zaki sameta akan number 08140365134 domin yin order a WhatsApp. Location: Kano Sai kun zo💃🏻 Masarautar Judala Ayarin rukunin bayi ne suke tafe cikin gajiyawa saboda irin doguwar tafiyar da suka yi, ba su ƙarasa cikin masarautar Judala ba sai kusan lokacin da dare ya tsala. A sashen bayi aka zuba su tamkar wasu kayan wanki, a galabaice suke saboda yunwa da ƙishirwa. Don haka suna zuwa a kan ruwa suka fara dira kamar waɗanda suka shekara ba su gan shi ba, bayan da suka sha suka yi ƙat sai ya zamana cikkunansu ya ƙulle saboda rashin abinci. Ƙanan yara maza da mata suka shiga kukan yunwa, da yake ba lokacin abinci ba ne a kan dole iyayensu suka lallashe su don su haƙure wa zuwa wayewar gari. A lokacin da dare ya tsala sosai, a ƙalla kusan ƙarfe biyu da rabi na dare. Fitsari ne ya tashi Indo, don haka ta dubi katafaren filin da suke kwance. Da tarin bushiyoyin da ke zagaye da su, haka kawai ta ji tsoro ya kama ta. Saboda ko a garinsu babban dalili ne yake fitar da ita waje da daddare, don haka a hankali ta miƙa hannu ta tashi Zinaru tana yin ƙasa da murya ta ce. "Zinaru! Zinaru!" Cikin gajiya da magagin bacci Zinaru ta ce, "Tuba muke don Allah ku yi haƙuri ku bar mu a ƙauyukanmu, kada ku kai mu masarautarku mu zame muku bayi." Sake taɓa ta Indo ta yi don ta fahimci firgicin da suka shiga a lokacin da za a kamo su, daga garinsu ne ya sa Zinaru take surutai har a cikin bacci. "Zinaru Indo ce, don Allah ki raka ni na yi fitsari." Sai a lokacin Zinaru ta sake wartsakewa, ta miƙe tana hamma tare da murza idanu tana kalle-kalle. "Yanzu Indo a wannan dokar dajin za mu tafi fitsari, ni fa wallahi tsoro nake ji." Indo da fitsari ya gama matsarta ta ce, "Wallahi ni ma tsoron nake ji Zinaru, amma ko ɗan gabancan ki taimaka ki raka ni." A hankali suka fara takawa zuwa bayan ɗakunan Bayin da suke jere, kasancewar duk mutane ne a warwatse ya sa suka ƙara tafiyar da ɗan nisa. Musamman da ya kasance akwai hasken farin wata, sai tsoron da suke ciki ya ragu sosai. A bakin wata ƙatuwar bishiyar tsamiya Indo da Zinaru suka tsugunna ba tare da addu'a ba, sai da suka gama sannan suka rasa abin da za su yi tsarki da shi. Don haka suka laluba suka ɗauki duwatsu suka shafa a madadain ruwan da ba su samu ba. Miƙewa suka yi suna waigowa suka ganta jingine, a jikin wani ƙaton shuri da ke kallon bishiyar tsamiyar da suke tsaye. Gaban Indo da Zinaru ya yi mummunan bugawa, har sai da kusan lokaci ɗaya suka saka hannuwa biyu suka dafe ƙirjinsu. "Wash! Wayyo cikina da marata, ku taimaka ku zo ku agaza mini." Matar ta furta tana yarfe hannu alamar tana cikin tsananin ciwo, sai a lokacin suka lura da tsohon cikin jikinta. Zinaru ce ta yi ta maza ta ce. "Da me za mu taimaka miki?" "Naƙuda nake yi wash!" Ta furta gumi yana sake tsattsafo mata, kallon juna suka yi, jikin Indo ne ya shiga rawa. Ganin haka ya sa Zinaru ta ja hannunta don su yi gaba, cikin galabaita matar ta ce. "Ku ma mata ne, watarana ba ku san inda za ku tsinci kanku ba, don Allah ku taimaka mini." Sosai kalamanta suka tausasa zuciyar Indo, ta tsaya cak wuri ɗaya. Da sauri Zinaru ta kalle ta, Indo ta ƙarasa gaban matar cike da tausayawa ta ce. "Kema kina daga cikin tawagar bayin da aka kawo ne?" Kai matar ta gyaɗa mata a daidai wannan lokaci suka ji ta saki nishi, nan take jaririyar 'yarta ta faɗo. Tsoro ne ya kama Indo, kasancewar bata taɓa ganin an yi haihuwa a gabanta ba. Da sauri ta ƙarasa wurin Zinaru da ke tsaye har lokacin tana kallonsu, cikin sauri ta ce. "Zinaru don Allah ki zo ki taimaka mata ke ce kika taɓa haihuwa." Wani mugun kallo ta watsa mata, cikin masifa ta ce. "Saboda ni ma ba ni da hankali kamar ke ko? Wai Indo ba za ki zo mu tafi ba?" Shiru Indo ta yi, ta waiga tana kallon matar tana yankewa jaririyar cibi. Wani ƙaton ganyen ayaba ta ga tana ƙoƙarin cirowa, da sauri Indo ta ciro ta miƙa mata. Sai ta ga ta ɗora jaririyar akansa, ta dubi Indo tana sakin murmushi a galabaice ta ce. "Sunana Karima kuma a cikin masarautar nan nake, sunan da zan saka wa wannan Jaririyar Batul. Don Allah ki taimaka ki yi mini wata alfarma, ki riƙe mini yariyar nan akwai kayana a bayan shingen can da zan ɗauko." Kamar Indo ba za ta yi magana ba, jiki a sanyaye ta miƙa hannu ta karɓi jaririyar. Zinaru da ke can gefe tana ganin haka ta saki ƙwafa haɗe da yin tsaki ta yi gaba, tana sake jaddada rashin hankalin da Indo take yi. Daidai wurin da Karima ta tashi nan ta nuna wa Indo, sai a lokacin ta lura da mazaunin matar a kan ƙaton gidan tururuwa ta yi shi. Ya jiƙe sharkaf da jini, ga waɗansu manyan tururuwai da ba ta taɓa ganin irinsu ba sun zagaye jinin suna ta tsotsa. "Baiwar Allah zuciyata a cike take da fargaba da ruɗa ni, don Allah kada ki cutar da ni." Indo ta furta zuciyarta tana rawa kamar za ta saka kuka, kama hannunta Karima ta yi, nan take Indo ta ji wani yarr tsigar jikinta ta fara tashi. Ga wani irin sanyi da ta ji hannunta kamar ta tsamo daga cikin ƙanƙara, ta sakar wa da Indo murmushi ta ce. "Ba zan cutar da ke ba, ungo riƙe wannan." Karima ta furta tana miƙa mata abu kamar wacce take shirin ba ta abu. Zuciya ɗaya Indo ta miƙa hannunta, Karima ta zuba mata ido har sai da tsoro ya sake mamaye Indo sannan ta ce. "A duk inda kike zan cigaba da bibiyar rayuwarki, ina son ki riƙe mini Batul tamkar 'yar cikinki. Akwai tarin ƙalulaben da za su afko cikin rayuwarki, sai dai duk abin da ya sha miki duhu. Ki zo bakin shurin nan za ki samu mafita, duk adadin shekarun da zan ɗauko zan dawo gare ki Indo..." "Don Allah me kike faɗa ne? Ban fahimce ki ba." Karima ba ta tanka mata ba, ta tsugunna ta damƙi ƙasar gjdan turuwar, sannan ta damƙi ta saman shurin. Ta shafa a fuskar Indo, sannan ta shafa a fuskar jaririyarta Batul da ke hannun Indo. Nan take Indo ta ji wata irin juwa tana yunƙurin ɗaukarta, tun tana ganin Karima har ta fara yi mata dishi-dishi. Ba ta yi tsammani ba, ta ji Karima ta matso wurinta ta fara yi mata raɗa a kunne mai kama da barin wasiyya.Tana buɗe idonta ta ji jariraiya Batul ta tsanyare da matsanancin kuka, sai dai ba kukan ne ya fi ɗaga mata hankali ba. Rashin ganin mahaifiyar Batul ya fi hautsina hanjin cikinta, tana fara waige-waige ta ji Zinaru ta ce. "Indo ba za ki ajiye 'yar nan ki zo mu tafi ba?" Cikin sauri Indo ta ce, "Ban ganta ba Zinaru, na shiga uku wallahi ban ganta ba." Kafin Zinaru ta bata amsa suka ga Dogaran sun ƙaraso da sauri suna cewa. "Kai baƙaƙen munafukai, wato da guduwa za ku yi? Allah Ya tona muku asirinku ku wuce mu je." Daga Zinaru har Indo rasa mai bakin magana aka yi, Dogarin da ke gaba sai a lokacin ya lura da jaririyar da ke hannun Indo tana kuka. Cikin mamaki ya ce. "Ke! Dama haihuwa kika yi shi ne har za ki gudu?" Indo da ta rasa bakin magana sai ta fashe da kuka, saboda gabaɗaya tsoro ya kamata ita da ko auren fari ba ta yi ba ya za ta yi da jaririya sabuwar haihuwa. "Ko ba magana nake yi miki ba?" Dogarin ya sake buga mata tsawa, Indo da ta rasa mafita cikin kuka ta ce, "A'a ba guduwa zan yi ba." "To ku wuce mu koma, ƙananan munafukai. An faɗa muku duk girman masarautar nan idan kun shigo za ku iya fita ne?" Zinaru da Indo suka yi carko-carko musamman Indo da damuwa ta cunkushe mata kai. "Indo kin ga irin abin da nake gudu ko? Wai ina uwar jaririyar nan? An ya kuwa ba gamo muka yi da aljana ba?" Kamar Indo tana jira ta ce, "Wallahi Zinaru ban san inda ta yi ba, kamar ƙiftawar ido tana gama yi mini siddabaru na neme ta na rasa. Ni yau na shiga uku." Duk maganganun da suke yi ƙasa-ƙasa suke yin su, shi ya sa ma Dogaran ba su san wainar da suke toyawa ba. "Indo ki faɗa musu gaskiya kawai." Zinaru ta faɗa tana satar waigensu. Indo ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Yanzu wannan labarin mai kama da almara waye ya zai yarda da shi? Idan aljana ce me ya sa 'yarta ta kasance mutum, wallahi ina cikin tashin hankali Zinaru." Indo ta ƙarasa maganar cikin kuka, musamman da ya kasance ita ma jaririyar ban da kuka babu abin da take tsalawa. Sarki Giɗaɗo Tun bayan fitar Galadima abin duniya ya haɗu ya haɗe masa, dafe kansa ya yi cike da damuwa. Ganin ba shi da mafita ya sa ya miƙe ya haye kan gadonsa ya kwanta yana tunanin makomar rayuwarsa, da yadda duniya take neman yi masa atishawar tsaki ba tare da ya shirya ba. Abu ɗaya ya sani yana da gawurtattun maƙiya guda biyu, Sarki Dikko da Sarki Gambo. Wanda zuciyarsa ta fi karkata da kaso casa'in da tara a kan su suke yunƙurin dakushe tarihin zuri'arsa daga masarautar Judala. Kusan duka wunin da ya yi haka ya ƙarasa shi sukuku, jiki babu ƙwari. Sai zuwa washegari ya ɗan saki jikinsa, ganin Fulani Zannira ta shiga matsananciyar damuwa. Da daddare bayan sallar Isha'i, Fulani Zannira da Sarki Giɗaɗo suna zaune suna hira a turakarsa. Shamaki ya doka sallama a bakin ƙofar, yana nema wa Galadima izinin shiga. A ɗabi'ar Sarki Giɗaɗo matuƙar aka yi sallar Isha'i ya rufe ganin kowanne irin baƙo. Amma ga mamakin Fulani Zannira sai ta ga jikinsa yana rawa ya amsa wa Shamaki, sannan ya dube ta ya ce. "Fulani kuna iya shiga daga ciki, domin akwai muhimmiyar tattaunawar da za mu yi da Galadima." Duk da ta yi mamaki, da yake Zannira mace ce mai kawar da kai, amma sai ta saki murmushi ta ce. "Ni mai bin umarninka ce ranka shi daɗe." Martanin murmushi ya mayar mata, ya taka mata har bakin ƙofa cike da ɗokantuwar ganin Galadima. A rumfar (Falo) da Sarki Giɗaɗo yake ganawa da baƙi suka zauna shi da Galadima. Cikin girmamawa Galadima ya ce. "Allah Ya taimake ka, Ubangiji ya ba ka yawan rai ina fatan na same ka lafiya ranka shi daɗe." Sarki Giɗaɗo ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Kun same mu kafiya Galadima, tun da muka ji labarin neman isonku muka tabbatar akwai alkairi a tattare da zuwanku." Galadima ya russunar da kai ya ce, "Wannan haka yake ranka shi daɗe, akwai wata ƙasaitacciyar bokanya da muka samu nasarar gano ta. Sai dai ta kasance ƙungurmar kafira, mai bin addinin kiristanci. Sunan da ake kiranta Bokanya Kande, ta kasance hatsabibiya kuma makira. Babban abin farincikin kuma har kawo yanzu, ba kowanne basarake ne ya san da zamanta ba." Nan take Sarki Giɗaɗo ya faɗaɗa fara'arsa, cikin zaƙuwa ya ce. "Galadima a tafi kai tsaye." Galadima ya saki murmushi ya ce, "Allah Ya taimake ka na samu izinin ganawa da hadimanta, sai dai sun sanar da ni babban sharaɗinta ba ta taɓa ganin mutum ido da ido har sai ya yi imani da Allahn da take bautawa, sannan kuma ya amince Allahnta shi ne mai gaskiya, kuma mai zartar da kowanne hukunci. A taƙaice dai, kusan ridda take sa mutum ya yi." Shiru Sarki Giɗaɗo ya yi, yana cikin nazari Galadima ya ce. "Amma fa an tabbatar mini da aikinta tamkar yankan wuƙa haka take yin sa. Kuma tana aiki da mabambamtan jinsin aljanu kala-kala, a taƙaice dai buƙatarka za ta biya ranka shi daɗe." A fili Sarki Giɗaɗo ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Mun amince Galadima." Galadima ya jinjina kai ya ce, "Amma kuma yana da kyau mu yi fitar sirri ranka shi daɗe." "Yanzu haka a shirye muke Galadima, idan babu damuwa za mu iya tafiya. Sai dai ba ma son masarauta ta fahimci ba mu kwana a gida ba." A fili Galadima ya saki murmushi mai sauti ya ce. "Ranka shi daɗe, Bokanya Kande sha'aninta fa ya shallake duk tunanin mai tunani. Saboda a ziyarar da na kai, hadimanta sun ba ni wuridin da zan furta a zuciya wanda za mu buɗe ido mu gan mu a tsibirinta." Daɗi sosai Sarki Giɗaɗo ya ji, nan take ya shiga Turakarsa ya sauya kayan jikinsa. Yana fitowa ba su ɗauki lokaci ba, Galadima ya dafa tsakiyar kan Sarki Giɗaɗo. Ya saka shi suka rufe ido, sannan ya fara biya wuridin tsafin da zai kai su tsibirin da take rayuwa. Wata irin sassanyar murya suka ji tana raira waƙar mai matuƙar daɗi, hakan ne ya alamtawa Galadima sun ƙarasa tsibirin Bokanya Kande. Suna buɗe ido suka ga ƙaton cross a gabansu, Galadima ya dubi Sarki Giɗaɗo ya ce. "Ranka shi daɗe, ni iya hurumin da aka lamunce mini kenan. Kai ne za ka runtse idonka, idan ka dafa wancan gicciyen (Cross) za a biya maka kalmaman imani da Allahn Bokanya Kande. Kamar Sarki Giɗaɗo yana jira, cikin sauri ya matsa gaban cross ɗin ya dafa shi haɗe da runtse ido. Murya da suka ji a farko, ita ta sake karaɗe kunnensa tana biya masa kamar haka. "Ya Ubangiji Yesu, na yarda cewa kai .... Na furta cewa ni mai zunubi ne, kuma yanzu haka ga ni a gabanka ina neman gafararka. Na karɓe ka a matsayin Ubangijina, mai ceton rayuwata. Na buɗe maka zuciyata ka shiga ciki ka ceci rayuwata. Na gode maka da ka ceci rayuwata daga ɓata, Amin." Muryar tana gama biya wa Sarki Giɗaɗo, ya ga ya sake tsintar kansa a wani babban kogon dutse. Ilahirin cikin dutse cike yake da cross manya da ƙanana, wata gajeriyar farar mace ya gani. Daga ita sai ganye a ƙirji da ƙasanta. Sarki Giɗaɗo yana shirin yin magana ya ji ta katse shi da cewar. "Barka da shigowa sabon addini sabuwar rayuwa. Jikinsa yana rawa ya amsa mata. "Barka dai Bokanya Kande." Yana shirin yin bayanin abin da yake tafe da shi ya ji ta ce. "Duk matsalolinka na gama saninsu. Matanka suna mutuwa duk bayan kwana arba'in da aurensu, a yanzu haka kuma iyalinka tana ɗauke da juna biyu, kai kuma ba ka son ka rasa ta." Gyaɗa kai Sarki Giɗaɗo ya yi ta cigaba da cewa. "Mafitarka ɗaya ce ka nemo mini tsohuwar matarka Karima, ko kuma ka kawo mini jininta wato 'yarta." A firgice Sarki Giɗaɗo ya ɗago ya ce. "Ya shugabata Fulani Karima ta shafe lokaci mai tsayi da mutuwa. Babu yadda za a yi na iya kawo miki ita, kuma a iya sanina da ita ni ne mijin da ta taɓa aure. Kuma a ɗakina ta mutu, aka binne ta a masarautata." "Ba ta mutu ba!" Bokanya Kande ta furta tana zuba masa manyan idanunta farare tas da sha kwalli ya ƙara musu kyau, ji ya yi ba zai iya cigaba da kallon ƙwayar idonta ba. Ta saki murmushi sannan ta cigaba da cewa. "Har yanzu Karima tana doran ƙasa, domin binciken da na yi tauraron rayuwarta yana nan har yanzu. Amma ban gama tabbatar da shin ainihin ruhinta ne, ko kuma akwai wani ƙulumboto da aka aikata ba. Kuma ta haifi jininta a cikin masarautarka, domin tauraron jaririyar daga tsagin tauraron Karima yake, sai dai har kawo yanzu bincikena bai bayyana mini ainahin fuskar jaririyar ba. Sai dai yana kyau, ka binciki masarautarka. Duk sababbin jariran da aka haifa a ciki, ka shafa musu wannan jan garin maganin da zan damƙa maka. Idan har ka ga jini daga al'aurarsa, wala mace ko namiji ko kuma sauran alamomin da zan raɗa maka a kunne, to tabbas jinin Fulani Karima ne." *Ummou Aslam Bint Adam* 07062062624 [25/11, 21:38] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA TAKWAS *MUM NIMRAH'S GRILL FISH AND SHAWARMAR* 'Yar uwata kema kina fama da kwadayin kayan kwalam da makulashe?To ina yi miki albishir da ki garzayo wajan Mum nimrah's grill fish and shawarma don farantawa bakinki, mai gidanki, yaranki, iyayenki da zuciyar ki da haddaden grill catfish or tilapia.😋💃🏻 Sai kuma beefshawarma Akan farashi me sauki. zaki sameta akan number 08140365134 domin yin order a WhatsApp. Location: Kano Sai kun zo💃🏻 Masarautar Kajjura Yadda Sarki Gambo ya maƙure wuyan Fulani Zainaba, abin ba ƙaramin tsoro ya ba ta ba. Don har sai da numfashinta ya nemi ɗaukewa, idanunta suka firfito ta fara fita hayyacinta. Wurgi ya yi da ita ta faɗi ƙasa, nan take tari ya turnuƙe ta. Zuwa ya yi ya tsiyayo mata ruwa a tulunsa, ya ƙarasa gabanta ya miƙa mata. A galabaice ta karɓa ta kai bakinta, sai da ta sha mai isarta sannan ta ɗago tana sauke ajiyar zuciya. Kafe ta ya yi da ido yana kallo, ita ma ta zuba masa idanu tana sake jadadda ƙarfin rashin imaninsa. Sarki Gambo ya ɗago haɓarta, yana bin ta da wani rin kallo mai wuyar fassarawa. "Zainaba ba yanzu zan kashe ki ba." Ya furta a kausashe, kamar ta yi masa shiru. Sai kuma zuciya ta ɗebe ta, tana ayyana mata idan har ta yi shiru zai ga kamar ta fara jin tsoronsa ne. Cikin dakiya da taurin zuciya ta ce. "Rashin kisana da ka yi, yana da nasaba da ganin gawarka da zan yi Sarki Gambo." Ya ji ɗacin maganarta, don haka ya furzar da isa mai zafi ya ce. "Lokaci kawai nake jira, amma mu koma maganarmu ta baya. Me ya sa kike son ɗora alhakin kisan Fulani Khadija a kaina, duk da kina da masaniyar a wurin haihuwa mummunan al'amarin ya faru da ita?" "Saboda na san babu abin da ba za ka iya aikatawa ba saboda buƙatar kanka." Fulani Zainaba ta ba shi amsa kai tsaye. Miƙewa ya yi ya fara zagaye ɗakin yana girgiza kai, sai da ya yi zagayen kamar sau uku sannan ya koma kan kujerarsa ya zauna suna cigaba da kallon juna ya ce. "Tabbas ba ki yi ƙarya ba Zainaba, zan iya aikata komai kuma a kan kowa matuƙar buƙatata za ta biya. Domin dalilin haka ne ya sa na hallaka mijinki Najibullah da jaririn ɗanki." Runtse idonta ta yi da sauri, tana jin wani irin ɗaci a ranka. Saboda duk lokacin da ta tuna irin kisan wulaƙancin da Sarki Gambo ya yi wa Najibullah sai ta ji abin ya dawo mata sabo. Murmushi mai sauti ta ji ya saki, sai a lokacin ta buɗe idonta sannan ta ce. "Abin da ba ka sani ba Sarki Gambo, babban kuskuren da ka aikata a rayuwa shi ne rashin kashe ni a daidai lokacin da ka kashe mijina. Za ka maimaita waɗannan kalaman naka a gaba, kuma ina mai sake tabbatar maka da kamar yadda kake tare da ni saboda biyan buƙatar kanka. Na rantse maka da zatin Allah, ni kaina na jinkirta hallaka ka ne saboda manufar da ke ɗamfare a cikin zuciyata." "Taurin kai, kafita da ƙarfin zuciyarki suna birge ni Zainaba. Sai dai abin da ba ki sani ba, tun da har zan iya juya wa Fulani Sadiya baya. Babu macen da za ta sha a wurina, idan kika tsame tagwayen 'ya'yana da abar bauta rana da ta ba ni." Da sauri Fulani Zainaba ta dube shi saboda jin furucin da ya yi. "Me kake faɗa haka?" Jin tambayarta ya sa shi ɗaga mata gira ya ce. "Kamar yadda kika ji a kunnuwanki." Fulani Zainaba ta miƙe a hankali, sai da ta ƙarasa kan faffaɗar shimfiɗarsa ta zauna sannan ta ce. "Wannan wani salon ne? Ko kuma kana son nuna mini hatta Ubangiji sai ka haɗa shi da waninSa?" Sarki Gambo ya girgiza kai haɗe da cewa, "Ko kaɗan ba yadda kike tsammani ba ne, na kasance ɗaya daga cikin masu bin addinin gargajiya tun asalin iyaye da kakanni. Akwai dalili mai ƙwari da mahaifina ya ɗora ni a turbar nuna wa al'umma ni mai bin addinin Musulumci ne. Wannan furucin da na yi miki, kada ki yi tsammanin zai zame miki hujja da za ki nemi tarwatsa ni, domin har abada ba za ki iya da ni ba Zainaba." "Ai ka riga da ka yi sake ɗan zaki ya girma Sarki Gambo." Fulani Zainaba ta furta tana nufar bakin ƙofar fita, sai da ta gyara zaman alkaybbarta sannan ta waigo ta ce. "Ni daga yau nawa aikin zai fara, domin duk kalma ɗaya da kake furta mini ina ajiye ta a mizanin da ta dace." Murmushi Sarki Gambo ya yi ya ce. "Ina yi muku fatan samun nasara Zainabata, haka kuma a wannan daren muna buƙatar raya shi tare da ke. Sai dai zan ba ku dama domin ku je ku huta, ko za ku samu sukunin nazaratar abin da yake ranku." Ta fahimci sarai abin da yake nufi, amma sai ta kawar da zancan da cewa. "Hankalina bai kwanta da zaman su Hasana a hannun Fulani Sadiya ba." Jim ya yi kamar mai nazari, don haka kawai shi ma yake jin zaman tagwayensa bai samu gurbi mai kyau ba. Amma kuma a yadda ya san Fulani Zainaba ta yi masa mummunar tsana, ba ya jin zai iya damƙa raganar rayuwar 'ya'yansa a hannunta. Don ya tabbata ko ta ɓangarensu ne za ta iya yin galaba a kansa, hakan ne ya sa a fili ya ce. "Ko da su ba jininmu ba ne, mun tabbata Fulani Sadiya ba za ta cutar da su ba. Mun aminta da Fulani fiye da yadda kuke tsammani, idan kuna mummunan tunani a kanta ya kama ku janye." Murmushi Fulani Zainaba ta yi kamar za ta tanka masa, sai kuma ta girgiza kai ta yi gaba. Tun da ta fita hadimai da dogarawa suke zubewa suna jera

Chapter 5 of 11