Share this page
mata kirari, ba ta iya tanka musu ba. Sai ta wuce sashenta a gaggauce, don kanta ba ƙaramin cushe mata ya yi ba. Ta jima tana kai wa da kawowa, har ta zauna tana nazari kamar wacce aka tsikara sai ta miƙe ta fita ta kira Baiwa Lawisa ta ce mata ta gaggauta kira mata Jakadiya. Ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba, Jakadiya ta ƙarasa jiki a sanyaye. Don tun bayan mutuwar Fulani Khadija, zuciyarta a cike take da zullumin yadda makomarta za ta kasance. "Allah Ya taimaki Fulani, Ubangiji Ya tsare gabanki da bayanki. Ke kaɗai ce zarah a cikin taurari, hutawarki lafiya ranki shi daɗe." Jakadiya ta furta tana sake dunƙule hannunta cikin jinjina, A ɗan gaggauce Fulani Zainaba ta ce. "Jakadiya ina son sanin asalin tarihin Sarki Gambo, tarihin masarautar nan da kafuwarta." A ɗan razane Jakadiya ta ɗago, cikin in'ina ta ce. "Amm... amma... ranki shi daɗe me... yake faruwa haka?" "Ba na buƙatar tambayoyinki, amsa kawai nake buƙata." Jin furucin Fulani Zainaba ya sa Jakadiya ta sauke gwaruwar ajiyar zuciya ta ce. "Allah Ya taimake ki tarihi ne mai cike da tarin al'ajabi da ƙalubale, ki gafarce ni ranki shi daɗe. Amma duk abin da zan sanar da ke harsashe ne, ko kuma labaran su kasance masu haɗe da rashin cikakkiyar gaskiya ko tabbacin waɗansu abubuwa. Amma akwai wani kundi guda ɗaya, wanda aka buga hatiminsa da rubutun ajami, bangon jikinsa da fatar tsohon zaki Guzugu, sai dai a yadda na ji labari. Mutum ɗaya ce ta san maɓoyar wannan kundin, kuma ta san mafi yawa daga cikin sirrin masarautar nan." "Wace ce ita?" Fulani Zainaba ta furta kai tsaye cike da zaƙuwa, Jakadiya ta yi ƙasa da murya tana ɗan waige. Sai da ta ƙara matsawa gaban Fulani Zainaba, ta yadda wani ba zai iya jin abin da suke tattaunawa ba sannan ta ce. "Sunanta Kursum!" "Kursum!" Fulani Zainaba ta maimata sunan tana nazari, ta sake duban Jakadiya ta ce. "Wace ce ita? Kuma a ina take? Mene ne alaƙarta da masarautar nan? Kuma a ina zan same ta?" Jakadiya ta sake russunawa cike da girmamawa ta ce, "Allah Ya huci zuciyar Fulani, tuba nake abisa kalaman da zan furta. Amma kalamar ban sani ba, ita ce kalamar da duk wani mahalukin da ke zaune a cikin masarautar nan zai sanar da ke." "Saboda me?" Fulani Zainaba ta jefa mata tambaya, Jakadiya ta ce. "Saboda babu wanda ya san yadda aka haihu a ragaya, amma a wani labari da na taɓa ji, na ji an ce akwai wasu ɓoyayyun wasiƙu da Mai martaba yake da su a turakar sirrinsa." Wannan karon a bayyane Fulani Zainaba ta sauke gwauron numfashi, haɗe da jinjina kai saboda yadda take jin baƙin al'amura daga bakin Jakadiya. Fulani ta sake kallon Jakadiya ta ce. "A ina turakar sirrin nasa take?" FULANI SADIYA Tun lokacin da aka aikawa Fulani Sadiya tagwayen marigayya Fulani Khadija, ta ji kamar ta shaƙe musu wuya su ma su mace har lahira. Amma gudun zargi ya sa ta haƙura, ta cigaba da nuna musu kulawar yaudara don tun dangin Fulani Khadija suna ɗari-ɗari har suka saki jiki da ita. Amintattun bayin Sarki Gambo biyu aka ware masu yi musu hidima da kulawa da su, don haka yaran ba su cika rigima ba tun da gari yana wayewa ake tatsar musu nonon akuya su sha. SARKI GAMBO Sarki Gambo ya jima a yana jiran Malami ya ƙarasa surukullen da ke gabansa, sai da ya kammala tsaf sannan ya dubi Sarki Gambo ya ce. "Ban yi tsammanin ganinka a daidai wannan lokacin ba." Sarki Gambo ya sharce gumin goshinsa ya ce. "Dalilin hakan ne ya kawo ni ya kai babban matsafin da nake aifahari da shi." Malami ya saki murmushin jindaɗi, don yana matuƙar son a fasa masa kai. Ya kalli Sarki Gambo alamun ya faɗi abin da yake tafe da shi, sai da ya gyara zama sannan ya ce. "Mun zo ne domin mun san wanda ya kashe mana Fulani, kisa mafi muni da wulaƙanci." "Sanin makashin ba shi zai fisshe ka ba Sarki Gambo, a yanzu babban ƙalubalen da ke gabanka ya ninka mutuwar Fulani Khadija, domin kuwa ita tuni ta mutu. Sai dai mu jira yi ruhinta tun da ya kasance mai tsarki, amma a yanzu tagwayenka sune manyan ƙaddarorin da za su taɗe duk wani burin rayuwarka." A hargitse Sarki Gambo ya ce. "Ban fahimce ka ba Malami, mene ne zai faru da tagwayen da nake fatan su zame mini sanyin idaniya?" "Ba matsalar ce za ta same mu ba, idan har kana tunanin haka ka dakata. Domin idan har matsalar a gaba take za mu iya cimma mata har mu magance ta, ina son Sarki Gambo ya sani. A halin yanzu Hassana da Husainarka sun kasance nakasassun da ba za su amfane ka ko su amfani masarautar nan ba. A taƙaice dai, kai da wanda ba shi da magaji a ɓangaren sarauta ɗaya kuke, ɗaya tana ɗauke da shanyewar ƙafa da hannuwa. Yayin da ɗaya ta samu matsalar makanta da ta ƙwaƙwala, wannan wani mummunan al'amari da zai iya daƙile komai na rayuwarka." *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 07062062624 [25/11, 22:11] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA TARA *MUM NIMRAH'S GRILL FISH AND SHAWARMAR* 'Yar uwata kema kina fama da kwadayin kayan kwalam da makulashe?To ina yi miki albishir da ki garzayo wajan Mum nimrah's grill fish and shawarma don farantawa bakinki, mai gidanki, yaranki, iyayenki da zuciyar ki da haddaden grill catfish or tilapia.😋💃🏻 Sai kuma beefshawarma Akan farashi me sauki. zaki sameta akan number 08140365134 domin yin order a WhatsApp. Location: Kano Sai kun zo💃🏻 Masarautar Zulwara Sai da Boka tsumbur ya gama sauraron tsawar da kogon dutsen yake yi, sannan ya dubi Sarki Dikko ya ce. "Haƙiƙa akwai sabon al'amarin da zai faru a wannan zuwan naka Sarki Dikko, ta wani fannin nakan iya ce maka kai mai nasara ne. Sai dai kuma akwai duhun da na hango yana mamaye da tauroronka, tauraronka ya kasance Himlu don haka nake..." "Amma mun jima da sanin tauraronmu Surdanu ne Boka tsumbur. Kuma wanne irin duhu aka hango mana, shin yana iya cutar da mu ko akasin haka?" Sarki Dikko ya katse boka Tsumbur, bai tanka masa ba ya cigaba da shafa ƙasar shurin gabansa yana wani zane a kanta sannan ya ce. "Tauraronka Himlu ne kuma ɗabi'ar nari, sannan duk wani bincikena bai bankaɗo mini ainahin abin da yake ƙunshe a cikin duhun ba." Ajiyar zuciya Sarki Dikko ya sauke cikin damuwa, yana shirin yin magana boka tsumbur ya katse shi da cewar. "Sarki Dikko kuna iya ba mu wuri, domin a yanzu haka muna da babban baƙo, shugaban rauhanai na ƙarƙashin ƙasa ya ziyarce mu. Matso kusa mu sanar da kai sharuɗɗanmu, da dokokin da za mu gindaya maka." Sarki Dikko kamar yana jira, ya yi saurin matsawa kusa da boka tsumbur. Ya jima yana yi masa raɗa, sai dai tun bai kammala ba gumi ya jiƙe shi sharkaf saboda tsananin fargaba da tashin hankali. Har ya buɗe bakinsa zai yi magana boka tsumbur ya ɗaga masa hannu da cewar. "Mun riga da mun gama zartar da hukunci Sarki Dikko, don haka dabara ta ragewa mai shiga rijiya. Amma muna iya baka shawara, idan har buƙatar hakan ta kama." Jiki a sanyaye Sarki Dikko ya miƙe, suka fita da Waziri yana fargabar sharuɗɗan da boka ya gindaya masa. Sarki Dikko yana komawa gida kai tsaye turakarsa ya shiga, kai kawo ya dinga yi a cikin ɗaki cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali. 'Shin kana ganin za ka iya fita a kan muradin boka Tsumbur? Ta ina za ka fara?' 'Kada ka manta duk abin da ka yi, za ka yi shi ne domin kyawun goben 'ya'yanka. Idan har ka gagara yin haka, sannu a hankali watarana za a shafe tarihinka da irin sarautar da ka shimfiɗa a doron ƙasa.' 'Buƙatar boka ba abu mai sauƙi ba ce, ya zame maka wajibi ka zage damtse domin gujewa kuskure masa.' Ire-iren kalaman da zuciyar Sarki Dikko ta dinga wassafa masa kenan, cikin tsananin damuwa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce. "Ya zama dole mu nemo wa kanmu mafita." Cikin sauri ya buɗe wata ƙaramar ƙofa da ke bangon Yamma na cikin ɗakinsa, wani tsoho ne tukuf a zaune. Sai da Sarki Dikko ya zaune a gefensa sannan ya ce. "Muhimmiyar magana ce ta kawo ni wurinka Babagana." "Na riga da na san haka, domin banza ba ta kai zomo kasuwa." Tsohon ya furta muryarsa tana rawa, Sarki Dikko ya ce. "Ina mai cigaba da ba ka haƙuri bisa killace ka da na yi a nan na tsahon shekaru, duk da na tabbata duniya ta jima da binne shafin rayuwarka." Babagana ya saki murmushin takaici sannan ya ce. "Lokaci zai zo da zan bayyana a idon al'umma, a wannan gaɓar da za ta zo kuwa ina matuƙar tausayinka Sarki Dikko." Sarki Dikko ya zuba masa manyan idanunsa da suka kaɗa jajir, ya dafa kafaɗar Babagana ya ce. "Kafin lokacin mun gama samun biyan buƙatun kanmu har mun hallaka ka." "Lokaci ne zai nuna, don yana gab da zuwa a daidai wannan gaɓar." Babagana ya furta yana sakin murmushi, duk tsahon shekarun da Babagana ya ɗauka a wannan ɗakin bai taɓa jin Babagana ya furta doguwar magana haka ba. Don haka tsoro ya so mamaye zuciyarsa, amma gudun kada ya nuna a gabansa ya sa shi cewa. "Babagana ban san abin da kuka taka ba har kuke ƙoƙarin nuna mana ƙwarin gwiwarku? Shin mene ne abin da kuka taka?" Kamar yadda yake yi akai-akai, haka yanzun Babagana ya fara tari sama-sama. Sai da Sarki Dikko ya miƙa masa ruwa ya sha, sannan ya ce. "Ƙwarin gwiwata tana gab da zuwa, sai dai a wanne lokaci? Ni kaina ban sani ba, amma na sani ba za ta taɓa bari gangar jikina ta mace a hannunka ba." Ajiyar zuciyar Sarki Dikko ya yi sannan ya ce. "Mu ajiye tattaunawarmu a gefe, za mu ajiye mata lokaci domin mu samu tattaunawa." Jinjina kai Babagana ya yi ya ce, "Ina sauraronka, wataƙila ina da masaniya a game da damuwarka." Gyara zama Sarki Dikko ya yi ya ce, "Bayan Waziri babu wanda ya san da wannan sirrin namu Babagana." "Ba iya Waziri ba, har waɗanda ba ka taɓa tsammani ba sun san da wannan matsalar taka, kai dai ka saka ido mutanen da ke kewaye da kai. Hatta shi kansa Waziri ban gama aminta da shi ba, amma wannan ra'ayinka ne ka ɗauki shawarata ko ka watsar da ita." Shiru Sarki Dikko ya yi da jin kalaman Babagana, ya ƙura masa ido yana kallo tare da sake jinjina baiwa da hikimar da yake da ita. Sai da ya gyara zamansa sannan ya ce. "Dattijo Babagana, shin kuna nufin bayan Waziri akwai waɗanda suka san ina haifar yara masu nakasa?" Gyaɗa masa kai Babagana ya yi ya ce. "Ba ka yi mamakin yadda aka yi ni da nake kulle a ƙarƙashin ikonka a tsawon shekaru na sani ba, sai waɗanda suke rayuwar 'yanci a doron ƙasa? Shi ya sa na ce ka cigaba da kula da hagunka da damanka, domin za ka sha mamaki idan ka ji masu son bankaɗa labulen sirrinka." "Sautari muna mamakin da tambayar kanmu, shin kuna taimakonmu ne ko kuwa mu maƙiyan juna ne Babagana?" Sarki Dikko ya furta yana kallon Babagana, shi ma kallonsa yake sai kuwa ya saki murmushi ya ce. "Kada ka saki jiki ɗari bisa ɗari da ni Sarki Dikko, domin murmushin maƙiyi ba abin yarda ba ne. Duk wani taimako da za ka ga na yi maka, ina yi ne domin na haskawa mai shirin fitar da ni hanya." "Wace ce ita?" Sarki Dikko ya wurga masa tambaya a kausashe, a madadin Babagana ya ba shi amsa sai ya saki murmushi ya ce. "Bari na saukaka maka bincikenka, mace wacce ta kasance tana yawo a cikin rayuwarka. Amma ka rubuta ka ajiye, duk daren daɗewa za ta zo har cikin nan sannan ta tono duk wani ƙulli da ka binne kuma ta bayyana a idon duniya." Haɗiye yawu mai ɗaci Sarki Dikko ya yi ya ce, "Mun ji duk kalamanku, ita ma wannan maganar mu ajiye ta a gefe. A ina zan samu Kursum? Kuma a wannen yanki zan haɗu da ɗan'uwanka tsoho Sulaimanu? Domin Boka Tsumbur yana buƙatarsu a cikin aikin da ya yi mana." "Ba ni zan baka wannn amsar ba, amsarka tana cikin littafin 'Ruwa A Wuta' wanda ka binne shi tare da gawar Sarauniya Humaira." A hargitse Sarki Dikko ya ɗago yana kallonsa, Babagana ya gyaɗa masa kai ya ce. "Domin kuwa ga dukkan alamu tarihi ne yake yunƙurin maimaita kansa." Ajiyar zuciya suka saki su duka biyun, daga haka Sarki Dikko ya miƙe ya ce. "Na bar ka lafiya Babagana, ina fatan za ka cigaba da hutawa cikin aminci." Yana gama faɗa bai jira cewar Babagana ba ya fice daga ɗakin. Sai da ya tabbatar ya rufe ƙofar, sannan ya cire kubar ya wuce maɓoyarsa ta sirri sannan ya zauna ya zabga tagumi. Yana nan zaune babu jimawa, ya ji sallamar Jakadiya daga bakin ƙofa. Sai da ya ba ta izinin shigowa sannan ta shiga cikin girmamawa ta zube a ƙasa tana faɗin. "Allah Ya taimake ka, Ubangiji Ya ƙara maka lafiya. Allah Ya sauki Fulani Hauwa kulu lafiya, sai dai a gafarce ni abin da ta haifa Allah Ya yi masa rasuwa." Sarki Dikko ko a jikinsa, saboda ya san ko babu komai yana da waɗanda za su gaje shi su ɓangaren sarauta a wannan lokacin. Don haka ya ce, "A cewa Shamaki su yi duk abin da ya dace, idan an kintsa Fulani muna buƙatar ganawa da su." Godiya Jakadiya ta yi masa ta fice, sannan ta ƙarasa ɗakin Fulani Hauwa kulu. Sai dai tana zuwa ta same ta a bakin ƙofa, ta zube a ƙasa ta ce. "Allah Ya taimake ki ranka shi daɗe ya ce a sanar da Shamaki ya yi abin da ya dace." Gyaɗa kai Fulani Hauwa kulu ta yi, ta ce. "Ki je kawai Jakadiya, duk abin da ya dace zan aiwatar wa abin cikina, daga haka kuma zan binne shi a ɗakina domin hankalina zai fi kwanciya." Jakadiya tana son sake magana, ganin babu fuska ya sa ita yi godiya sannan ta fice daga sashen Fulani Hauwa kulu. Bayan fitarta Fulanin ta shige ɗakinta, ta shafa cikinta tana sakin murmushi sannan ta ce. "Tun da na gama da wannan shafin, a yanzu ne zan dawo Fulani Karima kamar yadda nake a baya, ba Fulani Hauwa kulun da aka sanni ba." Masarautar Judala Kukan da jaririya Batul take tsalawa shi ya tashi mafi yawan bayin da ke kwance suna bacci, jiki a sanyaye Indo ta ƙarasa cikinsu hannunta rungume da jaririyar. Sai da dogaran suka ga su Indo sun zauna, sannan suka wuce suna cigaba da faɗan kamar yadda suke yi a baya. Ɗaya bayan ɗaya haka suka dinga bin ta da kallon tuhuma, wasu suka fara mamakin yadda ƙaramar yarinya ta haihu lafiya ƙalau ba tare da sun ji nishinta ba. Wasu kuma ganin yadda take raɓe-raɓe, ta sake birkicewa ya sa suka fara zargin ko ba 'ya ce ta halaliya ba. Kallon Zinaru ta yi idonta yana cigaba da zubar da hawaye, Zinaru ta kawar da kai gefe alamar can ta matse miki tana sakin guntun tsaki. "Ke yarinya ki ba ta ta sha mana, wannan ai ɗaukan hakki ne. Ba kya ganin yadda take tsala kuka?" Wata dattijuwa da aka kamo su tare da su Indo ta furta, birkicewa ta sake yi ta shiga inda-inda ganin haka ya sa suka sake tabbatar da lallai haihuwar fari ce Indo ta yi. Saboda sun lura da yadda take jin nauyin shayar da ita, murmushi Dattijuwar ta saki ta ce. "Ƙuruci dangin hauka, yarinya ai kowa kika gani da haka ya fara. Bari ki gani, idan aka ce za a bi ta kunya ai da ke ma ba ki kawo haka ba." Dattijuwa ta sake furtawa, sannan ta miƙe ta isa gaban Indo. Sakata ta yi ta gyara zamanta, ta saka hannu tana ƙoƙarin ciro maman Indo. Wata mata daga gefe ta ce. "To ko ruwan maman ne bai zo ba? Kin san wasu fa dama sai zuwa wani lokaci yake sauka." Kamar Indo ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ta, bakinta har rawa yake ta ce. "Eh bai zo ba." "To 'yar nan ai ba shiru za ki yi ba, yanzu kin ga mu baƙi ne a wurin nan. Ballantana a tatsar mata nonon akuya." A daidai lokacin da dattijuwar ta furta haka Uwar bayi ta ƙarasa cikin gadara ta ce. "Kai! Ba ma son shashancin banza da wofi, lafiya kuka cika mutane da surutu tun asuba ba ta yi ba? Jaririyar wace da ba za ta kula da ita, sai ta hana mutane bacci?" Gabaɗaya shiru suka yi, sai dattijuwar ce ta sake cewa. "Tuba muke yi, dama yarinyar nan ce ta haihu. To kuma yanzu haka jaririyar sai kuka take ga babu ruwa a maman." A wulaƙance Uwar bayi ta dubi Indo da ke raɓe tana zare ido, ta taɓe baki ta dube su ta ce. "Kuma duk cikinku babu mai shayarwa? Ba za a samu wata ta ba ta kafin nata ya zo ba?" Shiru suka yi babu wanda ya iya magana, sai wata busasshiyar mata ce ta ɗaga hannu ta ce. "Allah Ya taimake ki yanzu haka shayarwa nake, idan mahaifiyar jaririyar ta lamunce sai na shayar da ita." A sheƙe Uwar bayi ta dubi Indo ta ce, "Kin ji ai abin da ta faɗa, idan kuma ba za ki ba ta ba sai ki bar ta ta yi ta tsala kuka." Tana gama maganar ta yi gaba, har ta fara tafiya ta waigo ta ce. "Idan na sake jin hayaniya har na sake fitowa, to kuwa za ku yaba wa aya zaƙinta." Tsuru-tsuru suka yi duk tsoro ya sake mamaye su, a hankali Indo ta ƙarasa wurin matar da ta ce za ta shayar da jaririya Batul. Ta miƙa mata ita cikin sanyin jiki ta yi mata godiya, zuciya ɗaya matar ta karɓi Batul ta zauna sannan ta saka mata mama a baki. Batul tana kai bakinta jikin matar sai gani suka yi matar ta yanke jiki ta faɗi. Ummou Aslam Bint Adam🌚 [26/11, 21:49] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA GOMA *AF'S DATA PLUG* _MTN AND AIRTEL DATA AVAILABLE...!!🔥_ Monthly data — valid for 30 days _📶MTN DATA_ • 500MB — 450 • 1GB — 700 • 1.5GB — 1000 • 2GB — 1,300 • 3GB — 1,900 • 5GB — 2,100 _📶AIRTEL DATA_ • 1GB — 750 • 2GB — 1,400 • 3GB — 2,150 • 3.5GB — 1,800 • 5GB — 2,850 • 6GB — 2,900 • 10GB — 5,600 𝙋𝙖𝙮𝙢𝙚𝙣𝙩 : Opay — 7049439332 AFNAN ADAM 𝙒𝙝𝙖𝙩𝙨𝘼𝙥𝙥 𝙉𝙤: 09040772027 _Thank you❤_ Masarautar Kajjura Shiru Jakadiya ta yi kamar mai nazari, saboda sai a lokacin take ganin girman wautar da ta aikata na sakin bakin da ta yi a wurin Fulani Zainaba. Cikin inda-inda ta ce. "Na'am... ranki... shi daɗe, dam... dama na ce a yi mini afuwa ban san wurin da turakar sirrin take ba." Kallon tsaf Fulani Zainaba ta yi mata, ta ƙarasa gabanta murya a kausashe ta ce. "Idan har kika ɓoye mini wani abu, to tabbas sai na haɗa miki tuggun da ba za ki taɓa fita ba. Ko a kan mutuwar Fulani Khadija, ina iya zarge wuyanki har gaban Mai martaba. Don haka ina son ki feɗe mini biri har wutsiyarsa, idan ba haka ba za ki gane ba ki da wayo." Cikin Jakadiya ne ya kaɗa, cike da tsoro ta ce. "Don Allah ki yi mini rai, ki yi mini aikin gafara ranki shi daɗe." Gyaɗa mata kai Fulani Zainaba ta yi ta ce, "Ina sauraronki." Sai da Jakadiya ta waiga, ta ƙara matsawa gaban Fulani har sai da ya kasance suna jin numfashin juna sannan ta ce. "Ranki shi daɗe, wani ɓoyayyan sirrin ɗakinsa ne da ke cikin turakarsa. Idan kika shiga rumfar (Falo) ki tsaya a daidai tsakiyarsa, idan kika ɗaga kanki sama daga jikin azarar za ki hangi wata gajeriyar aska a saƙale a sama, ita wannan askar ta tsafi ce. Ita ce za ki ɗauka, ki shafa jinin sarki gambo a jiki. Saboda a yadda na taɓa jin labari, an ce duk shigar da zai yi ɗakin sai ya yanki jikinsa da wannan askar. Jininsa ya taɓa jikin askar, a haka zai zo saitin tsakiyar rumfar ya fara haskawa da ita. A nan za ki ga daidai ƙofar da take shimfiɗar wurin tana yayewa, da zarar kin soka askar ƙasar wurin za ta dare. Idan za ki shiga ki tabbatar askar tana hannunki na hagu, kuma da ita za ki shiga har cikin ɗakin. To da zarar kin shiga, shimfiɗar wurin za ta haɗe ta koma yadda take." A fili Fulani Zainaba ta sauke ajiyar zuciya, tare da sharce gumin da yake saman goshinta. Cikin damuwa ta ce. "Jakadiya dole sai ta wannan hanyar?" Gyaɗa kai Jakadiyanta yi ta ce, "Ai ba a nan ma gizo yake saƙar ba ranki shi daɗe!" "A ina ne?" Fulani Zainaba ta yi saurin wurga mata tambaya, gyara zama Jakadiya ta yi ta ce. "A wurin fitowar ne, don a yadda na ji labari an ce a yadda Sarki Gambo ya sihirce ɗakin ba ya fitowa a take a lokacin da ya shiga, har sai doshin magriba. Sai dai ina jiye miki tsoron kada Sarki Gambo ya gano ki ranki shi daɗe, domin na tabbata sai ya zartar miki da mummunan hukunci, don an ce ya taɓa hallaka ƙaninsa Galadima wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya saboda wannan ɗakin. To da yake dai jita-jita ce, amma zancan da nake yi miki Galadima ya yi ɓatan dabo har yau ba a sake ganinsa ba. Dalilin haka ya sa ake yi masa wannan zargin, amma Allah Shi ya bar wa kansa sani." Jakadiya ta numfasa sannan ta cigaba da cewa. "Saboda an ce ba iya waɗannan takardun ne a cikin ɗakin ba, ɗakin ya haɗa duk wani babban sirri da ƙudurin Sarki Gambo. Don a wata majiya da na ji, an ce akwai wata doguwar hanya idan aka bi ta har maɓoyar da Kursum take rayuwa. Don har kawo yanzu, babu wanda ya tabbatar da ainahin abin da ke ƙunshe a cikin ɗakin. Saboda babu wanda ya

Chapter 6 of 11