Share this page
ta lakuci kumatunsa ta ce. "Allah Ya raya mini kai Ridwan, sai dai ina jimamin yadda za ka taso a ƙasƙantacciyar rayuwar bautar da muke kai." Kamar ya san me ta faɗa, sai ta ga hawaye yana zuba daga idonsa. Nan take gabanta ya faɗi, tana shirin sake magana Uwar bayi ta ɗaga labulen ɗakin cikin faɗa ta ce. "Sakina kin san duk wani adalci da zan yi na yi miki ko? Yau kwananki nawa da haihuwa, ina ce kin doshi kwana hamsim. Ko kuma don ba ki san zuru ba me shi ya sa za ki cigaba da laƙewa a ɗakina kina rungumar ɗa kina yi masa rawa. Ki fito ku tafi casar gero tun lokaci bai ƙure ba." Jiki yana rawa Sakina ta zame Ridwan da ke cinyarta ta ce. "Bari na goya shi, tuba nake Uwar bayi." Uwar bayi ta saki dogon tsaki ta yi gaba tana cewa. "Daɗina da ku ba ku san harkar mutumci ba, ina laifi adalcin da na yi miki za ki shantake a ɗaki. Ai hutu ba na ki ba ne, tun da Allah Ya ƙaddaro miki rayuwar bauta a gidan nan." Kwantar da Ridwan Baiwa Sakina ta yi, ta shiga uwar ɗaki domin ɗauko zanen goyonsa. Tana fitowa ta hango shi a kwance yana kallon kusurwar bango yana ƙyalƙayala dariya, da mamaki take kallon wurin sai dai ganin babu komai ya sa ta miƙa hannu za ta ɗauke shi. Da sauri ta ja baya, ganin yatsarsa sanye da da wata azurfa mai ɗauke da wani zanen da ba ta fahimce shi ba. A sanyaye ta miƙa hannu tana taɓa azurfar, sai dai jin ta da zafi zau kamar an ciro daga cikin wuta ya sa ta yi saurin yarfe hannunta gefe. "Wallahi idan na sake magana Sakina sai kin yi aikin wata guda babu mataimaki. Iskancin banza da wofi wannan wanne irin wulaƙanci ne?" Uwar bari ta katse mata nazarin da take yi, game da baƙon lamarin da ya faru da Ridwan bayan shigarta ɗaki. Jiki yana rawa ta ɗauke shi ta saka shi a baya, sannan ta fito daga ɗakin zuciyarta fal wasu-wasi. Koda ta je wurin aiki hatta ragowar bayin da suke aiki sun lura da sanyin jikin Sakina, don duk yawan hirar da ake yi sai sun sako ta za ta jefa kalma ɗaya zuwa biyu. Sai da ta ji ya fara mutsu-mutsu alamar yana jin yunwa, sai ta koma can gefen wata bishiyar kuka ta sauko shi tana ƙare masa kallo. Da yake wurin ya yi nesa kaɗan da wurin da suke surfen, ba ta yi aune ba ta ji wata tsohuwa ta yi mata sallama. A ɗan razane ta waiga, don har lokacin zuciyarta ba ta daina rawa ba. Kallon mamaki take yi wa tsohuwar don ba ta taɓa ganinta a gidan ba, amma abin da ya ba ta mamaki ganinta sanye da irin kayansu na bayi. Sai da ta amsa mata sallamar sannan tsohuwar ta ce. "Ɗazu muna filin sassaƙa na ga kin yar da ɗan kunnenki, ban samu damar miƙo miki ba saboda uwar bayi tana wurin." A sanyaye Baiwa Sakina ta shafa kunnenta ta ji babu wari ɗaya, ta miƙa hannu ta karɓa sannan ta yi mata godiya. Sai ta ga tsohuwar tana kallon Ridwan, tana shirin yin magana tsohuwar ta cigaba da cewa. "Allah Ya yi miki babbar kyautar da ba kowa yake yi wa ba, saboda haihuwa babbar ni'ima ce. Idan kika cigaba da riƙe wannan amanar ta hannunki, haƙiƙa za ki rabauta da lada mai yawa. Tabbas wannan yaron ba kamar sauran yara ba ne, ki riƙe shi hannu bibbiyu Sakina." Tana gama faɗar haka ta saki murmushi ta wuce, da sauri Baiwa Sakina ta bi bayanta. Sai dai tana shan lungun da tsohuwar ta yi ta neme ta sama da ƙasa ta rasa. Kallon ɗan kunnen hannunta ta yi, sai a lokacin ta ga kamar ba nata ba. Ƙura masa ido ta yi, ta sake kallon zoben hannun Ridwan sai ta ga yana ɗauke da irin rubutun zoben hannunta. "Zainaba! Wace ce Zainana?" Ta samu kanta da furta haka, tana cigaba da kallon Ridwan da ke ta tsotsar hannunsa. BAYAN SHEKARA GOMA (1835) Tun daga bakin ƙofar ɗakin za ka fara jin salatinta, cikin galabaita ta dubi Unguwar zoma ta ce. "Lami! Ki taimaka ki karɓo mini tofi a wurin takawa." Cikin girmamawa Unguwar zoman ta ce, "Allah Ya taimake ki, yanzu haka Jakadiya ta tafi wurin Shamaki ta sanar da shi, domin ya faɗa wa Sarki Gambo halin da kike ciki." Cike da zafin naƙuda, Fulani Khadija ta ce, "Ki bi ta Lami, ni na san abin da nake ji. Wayyo Allahna! Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Ganin Fulani Khadija ta fara fita hayyacinta ya sa Unguwar zoma Lami ta fita da sauri, da fitarta babu jimawa Fulani Khadija ta ga an shigo ɗakin. Fuskarta a naɗe take cikin shigar kayan bayi, a daidai kanta aka tsaya ta ɗan ja da baya ta ce. "Wace ce?" Ba a tanka mata ba, aka yarfa mata wani baƙin ruwa a fuska. Ji ta yi kamar an zare mata laƙa, ta faɗi baya yaraf. A daidai lokacin ta saki nishi, nan take tagwayen jariranta mata suka faɗo. Murmushi ta yi tana ƙare wa matar tsugunnen da kallo, sai kawai ta saki wata irin dariya. Cikin shammata ta saka hannunta biyu a saman kawunan jaririn nata, ta fara motsa baki ba tare da ana fahimtar abin da ta furta ba. Ganin ana ɓata mata lokaci matar da ke tsugunne, ta zaro kaifaffan ƙahon da aka wasa ya yi tsini. Ta burma a saitin zuciyar Fulani Khadija, nan take idanunta suka lumshe tana fara motsa bakinta cikin azabar fitar rai. Cikin zafin nama, matar ta zaro zuciyarta wace ta haɗa da mabiyyar jariran ta ɗauka ta fice daga ɗakin. *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 07062062624 [23/11, 22:41] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA HUƊU https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=ems_copy_t Masarautar Judala (1835) Fulani Zannira tana ƙarasawa turakar Sarki Giɗaɗo, bayin da ke biye da ita suna riƙe da alkyabbarta ta baya suka dakata. Cikin girmamawa suka zube ƙasa suna faɗin. "A fito lafiya ranki shi daɗe, Allah Ya ƙara miki lafiya mai zuciyar zinare." Ba ta tanka musu ba, ta tura ƙofar da shiga, sassanyan ƙamshin rumfar Takawa ta daki hancinta har sai da ta lumshe idonta. Cikin takunta na isa da jan hankali ta fara takawa har zuwa turakarsa, sallama ɗauke a bakinta ta shiga tana faɗaɗa fara'arta. A jingine ta hango shi kan ƙasaitacciyar shimfiɗarsa ta alfarma, sai dai ta lura har ta ƙarasa gabansa bai fahimci ruhinta ya wanzu a wurin ba. "Barka da hutawa sarkin sarakai." Ta furta cikin salo mai jan hankali, wuri ɗaya ta ga yana kallo don haka ta zauna daga ƙasansa. Sannan ta kai hannu ta shafa sajensa da ke kwance luf a zagaye da fuskarsa. Murmushi ta ga ya sakar mata, ya fara ƙoƙarin kawar da damuwar da ke kwance a saman fuskarsa. "Barka da shigowa sarauniya." "Damuwa ba ta dace da gwarzon mazaje ba, nannauyan tunani bai cancanci samun sukuni a tare da kai ba jarumina." Ta furta tana zuba masa idanu, sannan ta ɗora da cewa. "Idan ban takura Mai martaba ba, ina son sanin damuwar da yake ciki domin na samu sukunin kawar masa da ita." Janyo ta ya yi jikinsa yana jin tsananin soyayyarta tana mamaye zuciyarsa, haka kawai yake jin soyayar Zannira ta doke duk ragowar matan da ya aura a baya. Nan take ƙirjinsa ya buga, tausayinta da shi ya mamaye shi. Amma gudun kada ya ɗarsa mata damuwa ya sa shi kawar da damuwar zuciyarsa ya ce. "Akwai baƙin al'amuran da ke shirin faruwa Fulani, kun san jan ragamar sarauta ba abu mai sauƙi ba ne." Kwanciya ta yi a jikinsa, ta janyo hannunsa ta shiga wasa da shi sannan ta ce. "Ni san mijina gwarzo ne, don haka babu gwagwarmayar da za ta dagula masa lissafi. Kai ɗin jarumin namiji ne, zuciyarka tamkar ta dakarun jarumai dubu ce." Yadda a ɗan kwanakin da suka yi da Zannira take ba shi ƙwarin gwiwa abin ba ƙaramin birge shi yake ba, ta kai hannunsa saman cikinta sannan ta ce. "Allah Ya taimake ka wani babban albishir gare ni, ban san da wanne irin tukwici za a saka mini ba." Cikin zumuɗi Sarki Giɗaɗo ya ce, "Duk abin da Fulani take muradi za mu mallaka mata, matuƙar bai saɓa da tsarin masarautarmu ba." "A yau da muka cika kwana talatin da biyar da aure, tun wasu kwanaki da suka wuce na yi ɓatan baƙon watana..." A zabure Sarki Giɗaɗo ya miƙe, cikin zallar farinciki mai haɗe da tashin hankali ya ce. "Da gaske Zannirata?" A ɗan kunyace ta sunne kai ƙasa, ta saki murmushi sannan ta gyaɗa masa kai. Rungume ta ya yi tsam a jikinsa, nan take idanunsa suka fara zubar da ƙwalla. Hawayen fuskarsa ta saka hannu ta share, sannan ta ce. "Ranka shi daɗe, ban yi tsammani har farincikin rabon jikina zai sa ka hawayen farinciki ba." Sarki Giɗaɗo ya ɗago murya a ɗan dashe ya ce, "Dole mu yi hawayen farinciki Zannira, kyauta ce da tun muka zo duniya ba mu taɓa samun irinta ba. Sai dai kuma kash..." Jin ya yi shiru ya sa ta ce, "Sai dai me ranka shi daɗe?" Ya ƙaƙalo murmushin yaƙe ya ce. "Babu komai Fulani, za ku iya tafiya don akwai muhimman abubuwan da za mu duba yanzu." Kallon tsaf ta yi masa tana karantar yanayinsa, cikin damuwa ta ce. "Ranka shi daɗe!" Kallonta ya yi ta cigaba da cewa. "Tun a tsirarun kwanakin da suka gabata, na fahimci sauyinka. Na fahimci kana cikin matsananciyar damuwa, don Allah ranka shi daɗe ka warware mini zare da abawar halin da kake ciki." 'Tabbas ba ki yi ƙarya ba Fulani, a kullum na wayi gari zuciyata cike take da fargabar makomar miyagun al'amuran da ke bibiyar rayuwata. ' Amma a fili sai ya ce. "Idan har akwai abin da yake damunmu kune mutanen farko, da za su fara fuskantar damuwar da muke ciki. Muna buƙatar hutawa Fulani, zuwa wayewar gari akwai kyakkyawan albishir da za mu yi wa mahaifiyar yarima." Murmushi ta yi, don haka ta miƙe tana gyara alkyabbar jikinta. Janyo ta jikinsa ya yi, ya sumbaci goshinta sannan ya sake ta ta fita daga ɗakin. Zama ya yi a gefen gado, ya dafe kansa da hannuwa biyu. Yana ayyana ga ƙoshi ga kwanan yunwar da ke tun karo shi, kamar wanda aka tsikara da allura haka ya miƙe zumbur ya fita. Yana zuwa ya samu Dogari Isiya da ke kula da ƙofar turakar Takawa, Sarki Giɗaɗo ya ce. "A gaggauta kira mana Galadima." Cikin girmamawa dogari Isiya ya ce. "An gama ranka shi daɗe, Allah Ya tsare gabanka da bayanka ɗan toron giwa. Gaba salamun baya salamun uban kowa mai taimakon talakawa." Ɗaki Sarki Giɗaɗo ya shiga, ba a ɗauki lokaci ba Galadima ya ƙaraso yana neman iso. Nan take Sarki ya ba shi izinin shiga, yana zama ya dubi Sarki Giɗaɗo ya ce. "Allah Ya taimake ka, an aiko kana nemanmu. Ina fatan ba wani laifin muka aikatawa mai martaba ba." "Akwai gagarumar matsala Lurwanu, wannan wani sirrina ne da za mu bankaɗa maka. Wanda babu wani mahaluki da ya san da shi. Don haka muke son mu yi magana da akai a matsayinmu na ɗan'uwanka ba sarkin masarautar Judala ba." Jinjina kai Galadima ya yi ya ce. "Ina sauraronka ɗan'uwana, In Shaa Allahu zan ba ka gudunmawa matuƙar abin bai fi ƙarfina ba. Kuma ni mai lulluɓe maka bargon sutura ne, ba tare da na bayyana sirrinka ba." "Duk matan da na aura a baya, waɗanda nake kai wa kurkukun zauren horo. Ba gaskiya ba ne laifin da nake laƙaba musu, kowaccensu mutuwa take yi." A razane Galadima ya ɗago yana kallonsa ya ce, "Ban fahimce ka ba yaya Giɗaɗo." Ajiyar zuciya Sarki Giɗaɗo ya sauke ya ce. "Daga kan marigayya Fulani Karima, kun san mun auri mata masu yawa." Galadima ya jinjina kai, Sarki Giɗaɗo ya cigaba da cewa. "To tun bayan mutuwar Karima, duk matar da muka aura bayan kwana arba'in take mutuwa." A wannan karon Galadima baki da hanci ya saki yana bin sa da kallon mamaki, Sarki Gidaɗo ya miƙe tsaye yana zagaya ɗakin cikin damuwa ya ce. "Babban abin ya girgiza duniyarmu, ya dagula mana lissafi bai wuce Fulani Zannira ba." Kallonsa Galadima ya yi yana son jin ƙarin bayani, Sarki Giɗaɗo ya koma kusa da shi ya zaune murya a raunane ya cigaba da cewa. "Tun da muke aure, babu macen da muka fi so muka fi ƙauna har cikin jikinmu face Fulani Zannira. Kuma a yanzu maganar da muke yi maka, Fulani tana ɗauke da cikin Yarima ko Sarauniya." A fili Galadima ya faɗaɗa fara'arsa, ya ɗaga hannu cikin jin daɗi ya ce. "Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, haƙiƙa na yi matuƙar farinciki. Domin idan lissafi ba ƙwace mini ya yi ba, ka doshi shekara kusan ashirin da auren fari ba tare da Allah Ya kawo rabo ba." Ajiyar zuciya Sarki Gidaɗo ya yi, ya sake miƙewa tsaye a karo na biyu yana girgiza kai. Murya ɗauke da damuwa ya ce. "Ba a nan gizo yake saƙar ba, domin a yau kwanan Fulani Zannira talatin da bakwai. A ƙiyasin mummunan al'amarin da yake bibiyar matan da na aura, saura kwana uku ta yi bankwana da duniya." Hankali a tashe Galadima ya miƙe, ya matsa kusa da ɗan'uwansa sannan ya ce. "Ya zama dole mu nemi mafita, domin haka kawai nake ji a jikina banza ba ta kai zomo kasuwa." "Shi ya sa muka kira ka, domin ku nemar mana mafita. Mun sha zuwa wurin malaman soro a sirrance, amma kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba. Don haka muke son ku nemo mini hatsabibin bokan da zai magance mana damuwarmu. Don mun tabbata, ba zai wuce kaidi da makircin wancan la'annan Sarkin ba." Galadima ya gyaɗa kai cike da gamsuwa sannan ya ce, "Tabbas biri ya yi kama da mutum, amma wani hanzari ba gudu ba. Zuwa wurin boka sauka daga doron addinin musulumci da saɓa wa Allah ne." "Idan mun saɓa masa Ubangiji mai gafara ne, idan buƙatarmu ta biya sai mu ɗaga hannu mu nemi yafiyarSa." Galadima ya jinjina kai, sannan ya yi wa Sarki Giɗaɗo alƙawarin nemo masa hatsabibin bokan da zai warware masa matsalarsa. MASARAUTAR KAJJURA Baki ɗauke da sallama Jakadiya da Unguwar zoma suka shiga ɗakin Fulani Khadija. Jakadiya da ke riƙe da ƙoƙon tofi ta ce. "Allah Ya taimake ki, Allah Ya buɗe ido lafiya. Ranki shi daɗe ga tofin Shamaki ya karɓo a wurin Mai marta..." Jin kukan ɗaya daga cikin jariran ya sa ta yi saurin ajiye ƙoƙon ta ce. "Lami maza duba kamar fa ta sauka." Da sauri suka ƙarasa wurin Fulani Khadija, a nan suka ci karo da jarirai guda biyu suna wutsul-wutsul a ƙasa. Unguwar zoma Lami ta shiga kiciniyar yanke musu cibiya, Jakadiya kuma ta tallafo Fulani a nan ta ci karo da jinin da ke tsartuwa daga ƙirjinta. "Fulani! Fulani! Innalillahi Fulani me nake gani haka? Lami taya ni gani ko idanuna ne." Jakadiya ta furta cikin tsananin kaɗuwa da tashin hankali. Lami tana ɗagowa ta yi tozali da yanayin Fulani, nan take jikinta ya shiga karkarwa ta ce. "Na shiga uku ni Lami, yau wacce irin baƙar rana nake gani." "Maza-maza ɗaurewa tagwayen cibiya kada su mutu mu sake shiga uku." Jakadiya ta furta a hargitse. Hannun Lami ban da karkarwa babu abin da yake yi, a haka ta samu ta ɗaure musu cibi. Kafin ta ƙarasa Jakadiya ta fita da gudu cikin kururwa ta sanar da abin da ya faru. Kafin wani lokaci tuni labari ya zagaye cikin masarautar, Bayi, Dogarai da masu sarautar masarautar lokaci ɗaya jikinsu ya yi sanyi. Saboda kowa ya shaidi Fulani Khadija mutuniyar kirkice, don haka mutuwarta ta zo musu a bazata musamman da ya kasance kisan rashin imani aka yi mata. Sarki Gambo yana zaune a turakarsa, Shamaki ya faɗa ɗakin babu ko neman izini kamar wanda aka jefo daga sama. Jiki da muryarsa suna rawa ya zube a ƙasa ya ce. "A gafarce ni ranka shi daɗe, a yi mini aikin gafara. Tuba nake uban talakawa, tuba nake damo sarkin haƙuri. Tuba nake jarumin sarki mai dakakkiyar zuciya, a yi mini afuwa bisa mummunan furucin da zai fito daga bakina." Kallon da Sarki Gambo yake yi wa Shamaki ya sa shi fahimtar yana cikin tashin hankali, Shamaki yana shirin yin magana Jakadiya ta faɗa ɗakin a hargitse ta ce. "Allah Ya taimake ka, Allah Ya ƙara maka lafiya. Kaina bisa wuyana ubangidana, tuba nake ranka shi daɗe. Ina neman afuwa abisa miyagun kalaman da zan yi, na mummunan kisan wulaƙancin da aka yi wa Fulani Khadija a yanayin da take naƙuda." A razane Sarki Gambo ya miƙe, nan take jijiyon kansa suka fito. Da wata irin murya ya buga musu tsawa da cewa, "Wacce irin maganar banza ake sanar da mu?" Gabaɗaya suka russunar da kai ƙasa, hawaye yana zuba Jakadiya ta sanar masa da duk abin da ya faru. Gani suka yi ya zauna a kujera daɓar, ya sunkuyar da kansa ƙasa cikin ɗacin zuciya. Ganin haka ya sa suka nemi izinin fita, don sun fahimci Sarki Gambo yana cikin kiɗima da tashin hankali. Fulani Sadiya da kawo kanta kenan turakar Sarki Gambo, ta saki murmushi zuciyarta fes ta tura ɗakin ta shiga. "Barka da hutawa Sadaukina!" Bai tanka mata ba, don haka ta matsa gabansa ta dafa kafaɗarsa ta ce. "Ina yi maka ta'aziyya Sarkina." "Ke ce kika kashe ta ko?" Ya wurga mata tambaya, Fulani Sadiya ta fara takawa tana murmushi sannan ta ce. "Eh." Ta yi furucin tana kashe masa ido ɗaya. *Ummou Aslam Bint Adam*🌚 [23/11, 23:14] Ameerah Adam: *KUNDI UKU* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne. SHAFI NA BIYAR Masarautar Zulwara Kasancewar duk ranar asabar ita ce ranar bikin gaida abin bautarsu, ya sa iyalai da dama suke shirya ƙwai da kwarkwarta domin halartar wurin bauta. Kusan tun asuba ilahirin mutanen ƙauyen suke zuwa bakin kogin, saboda kowa burinsa ya isar da bukatarsa domin Allahnsu da suke bautawa ya yi gaggawar amsa musu. Kogin Sutturu shi ne kogi ɗaya tal da yankin Zulwara suke bautawa, kasancewar akwai wata murgujejiyar bishiyar kukar da ke gaban kogin. Dalilin da ya sa suke bautawa kogin da kuma bishiyar kukar, kasancewar a shekaru masu tsayi da suka gabata. Ita wannan bishiyar an wayi gari da ta faɗi a cikin ruwan, da mutanen yankin suka yi yunƙurin tsamo ta daga ciki saboda wucewa a kwale-kwale, sai ya zamana duk wanda ya shiga kogin ba zai fito ba sai da wata nakasa. Ko dai idanunsa su makance, ko ƙafa ta shanye da hannu, wasu ma sai dai a tsame gawarsu daga ciki. Tun daga lokacin mutane suka daina shiga wannan kogin, a hankali sai kuma ruwan cikinsa ya dinga janyewa. Har ta kai ga ruwan kogin ya ƙafe tas. Bishiyar kukar da ke kwance ta ƙone ƙurmus, sai aka wayi gari shuri da gidajen turuwawa sun kewaye wannan bishiyar kukar. Ana cikin haka sai Boka Ɗan Asabe ya yi mafarki, a cikin mafarkin an ce ya je ya ɗebi ƙasar wannan kogin ya yi wa wani ɗansa mai nakasa magani. Idan ya warke sai ya cigaba da bayar da magani, da farko ya ji tsoro. Amma da ya tuna a mafarkin nasa an ce za a ɗaukaka shi, kuma za a ba shi ƙarin ilimin bokanci sai ya yi ta maza. Ya tara mutanen gari ya sanar da su abin da ya faru, mutane da dama ba su amince da kalamansa ba. Saboda suna ganin kamar yawo da hankali ne a ce su bar bautar rana su koma bautar ƙonanniyar bishiyar kuka. Boka Ɗan Asabe cikin fargaba ya tunkarin ƙonannan kogin ya ɗebo ƙasa, ga mamakinsa sai ya ji ƙasar ta yi sanyi sosai kamar ya ɗebo ta daga cikin kogi mai ruwa. Bayan ya ɗiba ya karyi itacen bishiyar, ya fito daga ciki ya haɗa wa ɗansa magani ya shafe masa ƙafafuwansa. Ko sa'a guda ba ta shuɗe ba, ɗansa ya miƙe garau ya samu lafiya. Wannan dalilin ya sa mutane suka fara gasgata maganar Boka Ɗan Asabe, musamman da wasu nakasasun suka dinga zuwa yana warkar da su. Sai ya zamana duk umarnin da bokan ya ba su tamkar wahayi haka suke amfani da shi, na zartarwa su zartar na aikatawa su aikata. Ana cikin haka Boka Ɗan Asabe ya ce kowanne magidanci ya ɗauki dabba ɗaya daga cikin gidansa ya kaita wannan ƙonannan kogin, da sunan godiya ga sabon abin bautarsu bisa ni'imar da ya fara yi musu. Jin yadda boka Ɗan Asabe yake ƙara samun ƙwarin gwiwa, maganarsa take karɓuwa. Ɗaukakarsa ta tumbatsa ya sa sarkin wancan lokacin ya aika har gida aka hallaka shi, saboda yana ganin idan aka cigaba da tafiya a haka al'ummarsa za ta daina ba shi girma da matsayin da yake kai. Tun da sai abin da Bokan ya faɗa ake zartarwa, saɓanin idan shi da yake sarki ya bada umarni ake tantama a kai. A ranar da Boka Ɗan Asabe ya mutu, a daren ranar Sarki Nomau ya makance. Tun ana nema masa magani har abin ya ci tura aka haƙura, daga ƙarshe aka naɗa ɗansa ya zama sarki. A ranar da Sarki Isa ya hau kan karagar mulki, a ranar kuma ƙoramar da suke bautawa ta fara tsattsafowa, bishiyar kukan da ta shafe sama da shekaru masu yawa ta miƙe. Haka mutane suka dinga turuwa suna ganin abin al'ajabi, ana cikin haka sai Damina ɗan Boka Ɗan Asabe ya gaji mahaifinsa a fannin bokanci. Sanin abin da ya faru ga tsohon sarki ya sa sarki mai ci bai yi yunƙurin kashe shi ko illata shi ba. Haka suka cigaba da tafiya ana zaman doya da manja tsakanin Sarki Najume da Boka Damina. A haka har girma ya cin musu, ajali ya riski sarki Najume bayan mutuwarsa aka naɗa ɗansa Sarki Dikko. Abu na farko da Sarki Dikko ya fara yi a ranar da ya hau kan karaga shi ne rushe tsibirin Boka Damina. Ya sa aka kawo masa shi a gabansa a fada, ya zare takobi a gaban jama'a. Sannan ya bayar da umarnin daga ranar babu wanda zai sake bayar da wani umarni idan ba shi ba, ganin abin da ya faru da Boka Damina ya sa jikin mutane ya yi sanyi. Tsoro ya mamaye su, sai dai a ɓangare ɗaya suka shiga dakon ganin mummunan yanayin da zai faru da Sarki Dikko kamar yadda ya faru da kakansa tsohon Sarki Nomau. Abin

Chapter 3 of 11