a zuciyata, ba Nazifi da abin da ya dangace shi ba, hakan ne kaɗai yanzu abin da ke saka ni zubar da hawaye a kowacce rana amma ba akan Nazifi da takaicinsa ba, haka ina ji ina gani mahaifiyata ta kwana uku babu lafiya amma Abbaa ya ce in har na zo gida babu ni babu shi, ranar ban iya runtsawa ba, ban iya shan ko da ruwa ba, amma a haka muka yi waya da mahaifiyata tana bani haƙuri da shaida min ta sami lafiya bacin na san kawai ta faɗa ne saboda in kwantar da hankalina, ƙarshe sai yaran ne su ka zo suna ce min sunje duba Ummani har ma ta basu sabuwar atamfa a ɗinka musu, suna ta murna abinsu suka bani na aje musu na ce su kaiwa Kakarsu.
Yashaik kusan duk sati biyu sai ya zo gidana, ko in bai zo ba ya kirani a waya ya ce in ba su, da kansa zai saka yaran a gaba da tambayar ina yi musu wani abun ne, wannan kuma na san sawar Kaka ne, to da yake dai ƴan sharrin basa kansu sai suce masa bana musu komai, ban sani ba ko da na fita a sabgarsu ne yasa su ka fara sanyi da makircinsu oho, ni yanzu abu ma idan ina da buƙata Ummani na ke kira, ita ke tura min kuɗi in kashe sabgar gabana da yake yaga idan na tambayi fita yana bari.
kuma dalilin rashin zuwana gida duba Ummani Maman Yasmin ta kira ni a waya, na zayyana mata duk abin da ya faru tace ashe shiyasa Yashaik yaƙi haɗa kayan sallah da ni wannan karan, ta tuna ranar har itama sai da yay mata masifa, nan fa ta hau min faɗa da ke jarababba ce itama shiyasa ita ɗaya ke iyawa da jarabar mijinta, kafin ta shiga roƙona akan in aje haƙurina da sanyina a gefe na ɗan wani lokaci in fara rama abin da ake min hakan zai saka duk su saduda, amma wannan haƙurin da na ke shi ke basu lasisin ci min fuska har shi mijin. saboda haka na aro rigar rashin mutunci da masifa da bala'i in saka in zama kamar wuta saboda zafin rai, in ci kutumar uban duk ɗan iskan da yay min ko da kallon banza ne balle ya nemi ya gaya min magana, ta ce harta uwarsa kar in raga mata, ƙarƙari in koyi kissa in yi kaman zan mata sujjada a gabansa amma a bayan idonsa in nuna mata karrr na ke bani da mutunci ko ƙwas, idan na fara hakan za su rabu da ni su kama abun da yake gabansu nima in huta.
na ji shawarartata na ɗan hau kan wata, tun da lallaɓawa na ke kar na zaƙe da yawa ya kuma kai ƙarata gidanmu in shiga uku. yanzun dai yadda nake haɗe rai idan na gansa har shakkar yi min magana yake, na fita harkarsa gaba ɗaya na cire tsoro sai ya fara mamakina hakan kuma ya dame shi, ya fara neman shishshige min yana neman shiri, ni kuwa sam naƙi basa fuska na nuna masa nima mutum ce me zuciya a ƙirji. ko fita zai yi bana damuwa da in bisa in masa a dawo lafiya, sai ga shi in yaga dama wani lokacin idan zai fita ya zo yace min zai fita, ba kuwa na ɗaga ko gashin gira na kalli inda ya ke, hatta ɗakinsa yanzu tsakanina da shi in kai masa abinci da na gama gyara kuma sai washegari, karatu ma sai na so nake zama yay min, ranar nan babu yanda bai da ni ba akan in zo ɗakinsa cikin dare nayi mursisi naƙi zuwa, domin na ƙudurci ni da zuwa ɗakinsa sai ranar da ya san darajata.
To haka dai na ke ta zaman babu daɗi, duk wani nawa da ya kamata ya zo gidan in gansa inji daɗi Abbaa ya hana domin da kansa yasa aka kira masa me gadi da shi Nazifin ya faɗawa me gadin duk baƙon da aka yi ya tambaye shi wurin wa ya zo, in dai wurina aka zo to kar ya bari a shiga. to Yashaik ɗin ma da yake zuwa ya daina, in ya zo dai faɗa ne ke kawo shi to amma a haka na ke farin ciki.
ta ɓangarensa yanzu ba na da wata matsala tunda babu abunda ke haɗamu, daga wajen Iyam ne dai da kuma ƴan uwan nasa abun babu sauƙi matsalar ta tsananta har tafi da, sun matsa min sosai cin mutuncina su ke yanda suka so. duk abunda su ke min haka nake shanyewa in hana kaina damuwa tun da dai haihuwar ba ni zan bawa kaina ba, haka kuma shi da su ke yi akansa ɗin ba ya yi min, tunda ba shi su Atika ya rage nuna damuwa akan rashin haihuwar.
Maman Yasmin kuwa ranar ta saci hanya tazo ta dinƙa faɗan maita da rashin zuciya irin nawa ne yasa na ke zaune a gidan, in bar musu gidan mana rabuwa da Nazifi ai ba shi zai hana ni ƙara yin aure ba. na ce mata sam ba rashin zuciya ba ne ina gudun bakin mutane ne da kuma ɓacin ran iyaye, domin duk ranar da Abbaa ya tashi zai ce min babbar biyayyar da zan masa ita ce na zauna gidan mijina, Ummani kuwa da ta tashi yi min nasiha zata fara ne da haƙuri sannan ta tafi ga batun babbar suturar Ƴa mace shine aure, kuma gidan miji shine mafi daraja wajen ƴa mace.
Yau ya kama lahadi, na tashi da sha'awar yin jan lalle, dama zan je kitso in sha Allah daga can zan wuce ayi min ko iya hannaye ne, da yake muna da taron suna ranar laraba jiya Ummani ta kirani take faɗa min Asiya ta haihu ƴar ƙanwar su Abbaa wacce su ke uba ɗaya, haihuwar sosai ta sakani farin ciki kuma a sannan nima na cire tsammani akan ba zan taɓa haihuwa ba, domin kuwa Asiya ta riga ni aure ita shekara goma kenan sai yanzu Allah ya kawo haihuwar, babu irin tsangwamar da bata sha ba don zan iya cewa har gwara ni, tunda ita sau biyu mijin na sakinta, ga kishiya da ta sanyota gaba, da yake Allah ne mai bayarwa komai kuma Lokaci ne sai ga shi yanzu Allah ya bata, ni ma Allah yasa ina da rabo, ya bani ko don masu goranta min da ganin ni na gaza.
bayan na shirya na fito domin naje na yi ayyukan da zan yi, a falo na tarar da su gaba ɗaya a zaune, dama tun zuwan Iyam gidan duk ranar Lahadi yini su ke a falo gaba ɗayansu, in ba yaran ne za su wuce islamiya ba, shi kuwa tun can asali lahadi ranar hutawarsa ce da lokacin iyalinsa balle yanzu da mahaifiyarsa ke gidan, in ba masallaci ba ko ƙofar gida ba ya leƙawa. ni dai in ka ganni a falon to zirga zirgar aiki ce don ba na zama balle raina ya ɓaci, idan tana zaune na zo na zauna don tayata hira in ba ya nan sai ta kama faɗin kana zama tare da surukarka waje ɗaya saboda rashin ɗa'a, idan kuma shine zaune a falon babu ita na zo na zauna sai ta kama bambamin ai bani da kunya ba ni da tarbiya dole sai na nuna mata ƴar zamani ce ni, ina faman liƙewa miji alhalin na san tana zaune cikin gidan saboda dai ba na son zamanta so na ke ta bar gidan. ranar har ce tayi da shi ita akan lamarina na ƴan iskan mata sai ta iya tattarawa ta tafi, banda tana ganinsa kusa da ita kullum hankalinta na kwanciya ai tuni ta kama gabanta, yay ta bata haƙuri ni kuma ya sameni yace ko magana na ke son yi da shi in ke iske shi ɗakinsa kar in ƙara zuwa gareshi idan suna tare da mahaifiyarsa.
Yanzunma kallo su ke yi sai dai ita da shi suna hira jefi jefi, yaran ne hankalinsu ya tattara ga tv, nayi sallama su ka ɗago su ka kalleni, a daƙile Iyam ta amsa shi kuwa sai tsareni da ido yay, sannu da hutawa nayi mata domin mun rigada mun gaisa tun ɗazu, na tambayeta abinda take so a dafa da rana tace faten tsaki amma yaji gyaɗa da ganye na ce to, miƙewa nayi na wucewata kitchen ban bi ta kansa ba da bakinsa da naga yana son magantuwa da alama. tun zuwanta na daina dafa son ran kowa sai na tambayeta me take so a girka, har ga Allah jinta na ke yi kamar uwata, kullum ƙoƙarina in kyautata mata amma sam ba na tsira, komai na yi bana burgeta balle yay mata daɗi, burinta ta kushe ni kawai, ku san kullum sai ta faɗa min bata sona bata son zamana da ɗanta, maganar tun tana damuna ma har na daina jinta, takurawar da baiwar Allah nan ke min yayi yawa, ta hana ni shan iska kwata kwata, ta hana na huta na sake, magana tsakaninta da ni daga gori sai cin mutunci da zarafi, kuma duk wannan abubuwan da take min daidai da rana guda ban ji ina so na mata rashin kunya ba ko na ƙi bin umarninta, uwa ce ita ko bata haife ni ba ta haifi mijina.
ina tsaka da aiki sai ga shi ya shigo kitchen ɗin, tun kallo ɗaya da na masa na watsar, ya shiga dube duben da zai yi, ni na san babu abinda ya shigo da shi sai don dai yay min magana kawai.
kusan minti ɗaya yana faman bulayin iska ganin na basar da shi sai ce yayi,"babu abunda ake buƙata?".
kamar bazan amsa shi ba sai can na ce,"babu".
"komai akwai?".
na ce,"ummm".
shiru yayi na ƴan sakanni sannan ya sake cewa,"ki saka daddawa da yawa a ciki bata son fate babu daddawa".
na ce,"na sani ai".
ina jin kallonsa a jikina har ya fice a kitchen ɗin. bayan na kammala girkin Iyam na fara zubawa na kai mata ɗakinta, na zo ina zubawa yaran nasu sai ƙwala kiranta naji, naje da hanzari gareta cike da ladabi da girmamawa. flask ɗin abincin ta turo gabana tana cewa,"wannan abincin na ki ai kin cika tafarnuwa tayi wani bauuu, ni kuwa kin san idan tayi yawa bana iya ci. ɗauki kije kawai idan anyi na dare na ci".
shiru nayi na kasa motsi, wai tafarnuwa! ni da rabon da nayi girki ma da tafarnuwa har na manta, tun farkon zuwan su Atika na daina amfani da ita saboda Rumana bata ci, kawai dai saboda ta janyo min faɗa wurin ɗanta, kuma yanzu na san ba komai yasa ta yin hakan ba sai ganin zan fita ne, tunda a gabanta na tambaye shi ya ce naje amma kar nayi yamma, to fitar ce bata so idan na ɓata lokaci sai yace in fasa ranta yay fari.
na sauke numfashi na ce,"to me zan ƙara dafa miki?".
"a'a ke da kike sauri za ki fita ai bana ƙara sa ki wahala ba".
nayi murmushi na ce,"fitar ba ta fiki muhimmanci ba, in dai fita ce kam sai na haƙura da ita akanki. don Allah ki faɗa min me zan dafa miki babu wahala ga aikin uwa".
"soya min wainar fulawa, amma kar kisa taruhu me yawa kuma albasa taji sosai".
na ce,"tou". kana na miƙe na tashi na fita. har na sa a raina na haƙura da fitar sai ga shi kuma na gama suyar da wuri. na kawo mata fuska babu yabo babu fallasa tace an gode Allah yay albarka, naji daɗin adu'ar da tayi min karon farko tun zuwanta gidan. na fita na koma kitchen ɗin na kwaso nasa kayan abincin sannan na wuce zuwa ɗakinsa. yana shirin fitowa muka yi kiciɓis tray ɗin hannuna ya kusa faɗuwa yay saurin tareni. bai bani hanya na wuce ba ni kuma ban ce masa kanzil ba tunda dai ai yana da ido, hannuna ne dai ya ƙage saboda nauyin kwanukan cikin tray ɗin, yay tsaye akaina kaman wani sanda, ganin tsayuwar tasa ba me ƙarewa ba ce na raɓa ta ɗan tsukukun gefensa na wuce, na shimfiɗa carpet ɗin da yake cin abinci akai tukunna na ɗora masa kayan abincin.
Shi kuwa baki buɗe ya ke kallonta, ta raɓa shi ta wuce har tana noƙe jikinta saboda wulaƙanci, bai san nufinta ba da wannan zaman da ta tsira tsakaninsu, tana ta wani shareshi tsabar raini, ga dai shi tana sakin jiki da mahaifiyarsa wani sa'in ma da yaran, amma shi sai wani nuna halin ko in kula take masa, da sun haɗa ido sai ta haɗe rai tana faman ciccin magani, ta mayar da shi kamar wani ɗan iska sai yake magana tana amsa masa a daƙile, shiyasa yake ganin kaman ba ita ba an sauyata, don mamakinya ke sosai akan canjawarta, kuma ya ɗaga mata ƙafa ne kawai don yaga iya gudun ruwanta, sai dai ya lura idan bai yiwa tufkar hanci ba haka za'a ci gaba da tafiya, zata mayar da shi shashashan miji ta bakin Iyam, kusan satika nawa ko ta hakkinsa ma ba ta bi, ko so take har sai ya nuna mata cewa ya gaji yana da buƙatar kasancewa da ita ne, yanayinta sam ma ba ya nuna tana da damuwa yanzu da shi, tayi wani haske ƙirjinta ya cika, ko faɗa yay mata yanzu sai ta ɗau fushi da shi saɓanin da da hankalinta zai ta shi ta rasa sukuni, lallai yay sake ta yawa.
ina sauke ajiyar zuciya ta gajiya na dubi inda yake na ce,"ga abincinka in zuba yanzu ko sai anjima zaka ci?".
bai ce da ni komai ba, na kuwa miƙe na shiga gyara abunda zan gyara a ɗakin ban ƙara kula shi ba har ya gaji da tsayuwar da yake ya zo ya zauna gefen gado.
sai da na kammala kana na ce masa,"zan wuce gidan kitson".
agogo ya kalla kana ya ce,"ok to nawa zai ishe ki?".
wani kallo nayi masa sannan na ce,"abun da ya samu".
yasa hannu a aljihu ya ɗauko kuɗi, dubu biyu ya zaro ya bani yana ce min wai babu cash a wajensa, kuma na san akwai kawai yanzu ba ya son bani kuɗinsa, tunda Iyam ta ƙyalla ido akan yana ban na cefane bayan yana ajiye komai sai ta fara ƙorafi akan hakan, tun daga haka kam na ce in anyi duniya don manzon Allah ban ƙara tambayarsa kuɗi, in ya bani falillahil hamd in bai bani ba Ummani na tura min kuɗi yanzu.
na fita na bar ɗakin bayan na ce masa na tafi. Allah ya gani ba ƙaramin juriya da ƙarfin hali na ke yi ba akan sharesa, yanda ya ke nuna kaman ya damu haka ni to nayi muguwar damuwa, faɗin na daina sonsa sai na tuna shiga tsakanina da Abbaa ne duk da yanzu Abbaan ya ɗan sakko yana kirana ma wani lokacin da kansa, amma Allah ya sani ina mutuwar son mijina, kawai na fita a sabgarsa ne saboda zaman lafiya da kwanciyar hankalina. sau da dama ina jin na karaya idan ina kusa da shi amma na kan danne na tursasawa zuciyata, in kuwa na kasance ni ɗaya babu tunanin abunda na ke sai rayuwarmu ta baya tun daga haɗuwarmu zuwa auranmu da muka rayuwa cikin farin ciki da ƙaunar juna kafin shaɗan ya shigo tsakani.
shirina na yi cikin sabon hijab ɗin da Alhaji Yayan su Ummani ya aiko min wancan sati, da maƙulli na kulle ɗakina don yanzu ba na iya idan zan fita na barsa a buɗe, duk da ba raya wani mugun abun zai iya faruwa ba amma idan ka kiyaye sai Allah ya kiyayeka, masu zuwa gidan ba ƙaunata su ke yi ba, to ban san iyaka inda manufarsu ta tsaya ba don satin baya da Anty Aisha ta zo ce tayi sai taga bayana a gidan nan.
na sakko ina ƙoƙarin ɗaura niƙab Faty ta shigo da sallama da yanayin gajiya sosai a tare da ita. ita ce autar Iyam a mata, kuma duk ƴaƴan gidan ita da Salaha ne kaɗai Allah ya ci da su rabon karatun boko me zurfi, yanzu tana polytechnic ta nan ɗorayi, satin Iyam uku da zuwa ta dawo itama wai makarantarta tafi mata sauri daga nan, ni dai adu'ana Allah yasa kar zaman nata yay tazarce dan ba mutunci ta cika ba dama ita tun asalinta haka take, ita da Anty Aisha halinsu ɗaya.
fuskata ta washe da fara na ce mata,"sannu da dawowa ƴan makaranta".
"Yauwa". ta amsa min a ciki tana shigewa ɗakin mahaifiyarta.
shigarta kenan sai ga Iyam ta fito. ganinta yasa na tsaya tambayar,"wani abun za'ai maki Iyam?".
ta ce,"ehhh fa". ta faɗa tana yi min duban sama da ƙasa. "Ce zan yi dama ki haƙura da fitar kawai, kayan wanki ne na ɗebo su, nawa ne da na Faty, kuma yaran naji suna faɗar kayan makarantarsu na gobe ba'a wanke ba, kinga fita kuwa bata kama ki ba, ki bari zuwa goben sai ki je duk inda za ki tunda ba tashin duniyar za'ai ba".
shiru nayi hakan yasa ta ɗaga murya da cewa,"ko kuwa ba za ki ba Sa'ida na ga kin ɓata rai, ina uwar mijinki ban isa na sa ki aiki ba kenan?".
ido na rufe na sauke ajiyar zuciya, murya ƙasa na ce,"ya za'ai na ce ba zan yi abunda kika saka ni ba, don Allah ki bar faɗin haka".
"na ji bana son kissa, yauwa ki wanke yanzu kar ki ce sai anjima yamma tayi su ƙi bushewa har dare su zo suna warin rima".
sai ta shiga ƙwala kiran "Faty! Faty! fito min da kayan nan da na ɗaure, ki tabbatar kin sako duk kayanki na dattinkar daga baya ki zo kina min mitar kin rasa kayan sawa in za ki wuce makaranta".
Fatin ta fito da damin ƙunshin kaya na cullo su gabana tana faman hararata, kallon kayan na yi kawai na san da gayya aka ɗebo su, kuma rabi na san na Fati ne tunda ko cikakken sati banyi ba da yiwa Iyam wanki. abun yana ci min rai yana ƙonan zuciya duk sanda Iyam ta bani wankin kayan Fati, ƙanwar miji fa? ba ma dole yarinyar ta dinga gani na a wulaƙance ba.
maganar Fatin ta katse tunanina tana cewa,"ba ki ba ni abinci ba kuma".
ban ko kalleta ba na duƙa zan ɗau kayan Iyam ta ce,"jin abunda ta faɗa ne ba ki yi ba ko kuwa abincin ne ba ki da niyyar bata isashshiya. ko kin mata gidan Yayanta ne uwa ɗaya uba ɗaya?".
kayan suna da nauyi sosai ban ɗauka ba na ɗago ina kallon Fatin na ce,"amma ai kin san hanyar kitchen ɗin Fati ki shiga ki zuba mana ko na taɓa hana ki. idan ma shiga kitchen ɗin ba za kiyi ba ai ga flask ɗin su Atika nan kan dining ki zuba mana".
"banga zan iya yin duka biyun ba, kece matar gida kece da dafawa da zubawa. saboda haka ki zuban abincina kawai ko na haɗaki da Yaya Ƙaramin shi ai ya isa da ke idan ita Iyam ɗin kin rainata".
kallonta kawai na ke raina na sosuwa har ta wuce ta zauna kan kujera tana ɗaukan remote ta canja tasha. Iyam ta shiga ƙwala kiran Nazifi, gabana na faɗuwa nayi saurin barin wajen ina nufar dining, abincin na zuba mata na ce da ita ga shi nan, kamar bata jini ba haka tayi banza da ni.
ina niyyar barin wajen sai ga shi ya fito daga ɗaki, Iyam na ce masa,"a'a da ce tayi ba zata bawa Fati abinci ba na ce to bara na kiraka ƙila taji maganarka tunda ni ban isa ba".
kallona yayi yana cewa,"bisa wanne dalili za ki hanata abinci? wai ke ki hora mutum da yunwa daɗi ya ke miki ne? wato abunda na ɗanɗana miki kwanaki bai ishe ki ba?".
Iyam ta katse shi,"kaga duk ba wannan ba, Fati dai gata can zaune ma kallonta take, kallon dole don dawowarta kenan yunwa take ji, ka ce kawai ta bata abinci".
"ki bata abincinta karnki ƙara hana wani nawa abinci tunda ba ke kike siyowa ba, don kin dafa ba yana nufin kina da iko da shi ba ne".
muryana na shaida damuwa na ce,"ban fa ce ba zan bata ba, ce nayi taje ta ɗiba. kuma ga shi na zuba mata na ce ta zo ta ɗauka tayi min shiru".
"ohh in magana ki ƙaryata". cewar Iyam
"ni ba ƙaryata ki nayi ba amma yanda kika ce ai ba haka ba ne...".
maganata ce ta katse dalilin saukar marin da naji a fuskata.
"duk ranar da mahaifiyata ta ƙara magana kika nemi ki ja akai sai na mugun saɓa miki, uwata fa tana faɗa kina cewa ba haka ba, me kike nufi in ba ƙaryatata ba".
idona ya ciko da hawaye ina dafe da kuncina. na jiyo shi yana cewa da Fati. "ke kuma zo ki ɗauki abincin".
ta marairaice tana cewa,"Yaya Ƙarami ƙafata ce naji ciwo bana iya takawa inama shirin ce maka zanje asibiti ne".
ya waigo ya kalle ni daidai lokacin da na ke niyyar barin wajen murya a sama ya ce,"na gama magana ne da za ki bar wajen?".
na dakata ba tare da na juyo ba.
"ki ɗauki abincinta ki kai mata kina ganin ai tana da lalura".
na danne kukana na mayar da hawayena, na ɗauki abincin na je na miƙa mata ta karɓa tana ƙunshe dariya, cikin raina na ce Allah ya saka min.
Barinsa wajen na nufi bene nima, gaba ɗaya na manta da batun wani wanki, sai munafukar yarinyar ce take cewa da Iyam wai na tafi na bar mata kaya. ita kuma ta ce ta ƙyaleta da ni zamu zuba. ni kam ban tsaya ba nayi ɗaki ina jin babu daɗi a raina, zama nayi saboda raina ya ɗan yi sanyi amma har ga Allah na jima ban ji ɓacin rai ba irin na yau.
to ni wankinma bai cin min rai ba kamar zuba abincin in kai mata kuma ta karɓa tana min dariya, in wanki ne dama tunda Iyam ta dawo ta hana badawa da guga tace masa gatan yayi min yawa komai sai a kashe kuɗi ayi min banda aiki sai kwanciya, don haka bisa umarninta kar a ƙara bayar da wanki a gidan, kayan wankin guda nawa su ke da ni ba zan wanke ba sai dai ai ta ɓarnar da kuɗi ni babu tausayi saboda ban san wahalar da yake sha ba kafin ya samesu, to in dinga ƙwarara jiki ina motsawa, haka ma fa firij tasa an ɗauke na kitchen an kai ɗakinta, duk su lemo da nama in ya kawo sai yanda ta bani, duk sona da maltina yanzu sai haƙura na ke yi saboda idan naje karɓa ta dinga mita kenan.
Da rana ina cikin wankin sai ga shi ya shigo yana faɗin,"wanne irin rashin hankali ne wannan? Kin bar tukunya zata ƙone kin taho wani aikin na daban, ki bari ki fara kammalawa da ɗaya mana, wannan ai ba dabara ba ce. kin san yanda gas ke kara tsada kuwa, wallahi za ki ja na koma ajiye miki buhun gawayi".
Da alama bai san wankin na waye ba shiyasa, Na tsame hannuna a ruwan da sauri, ta gefensa na wuce na nufi kitchen ɗin, ina zuwa na tadda ruwan zafin ko tafasa bai yi ba, ni dai dama nayi mamaki domin kuwa nayi ƙasa da wutar sosai, kai bawa dai da komai kayi sai ya zama laifi, nufinsa da yay maganar in tsaya masa bayani ya hasala ya gaggaya min babu daɗi. ina kitchen ɗin ya dawo ya sameni, ya ce in fito falo na iske shi, sauri sauri na wanke shinkafar na zuba na fita, yana tsaye hannayensa harɗe ta baya, hannun kujera na zauna ina ce masa,"gani".
kuɗi ya miƙo min tare da cewa,"akwai abunda ya taso min na ke so a taya ni da adu'a, ga wannan dubu talatin ne, idan kin gama aikin sai ki leƙa gidan Malama Hadiza, akwai buhun shinkafa da wake na bayar akai gidan, idan kin je sai ki tambayeta adadin kuɗin da ake buƙata, jallof ne za'ai da ƙosai da kunu ayi sadaƙa".
ina kallonsa na kai hannu na karɓa na ce,"Allah ya karɓa ya biya buƙata".
Ko amsa ni bai yi ba, ya nemi kujera ya zauna ni dai na bi sa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 23