Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
carpet na ajiye musu su ka zauna su ka fara ci ni kuma na juya kitchen ɗin don zubowa su Yaya na su. kiran Hubbi ya shigo wayata na ɗaga ya ke shaida min ga masu furnitures ɗin nan sun zo. na fita na hau saman na shaidawa su Yaya, sai sannan na ke ƙara ganin ashe ma basu kaɗai ba ne har da nasu baƙin wanda su ka zo da su suyi musu gyaran. cikin su biyun dai babu wacca ta tanka min bayan waɗancan da su ka gaishe ni. na juyo na sakko ina faɗawa me gadi yaywa ma'aikatan iso, ai na fita hakkinsu tun da na sanar musu za'a shigo. ina ɗakin Hubbi na jiyo muryar Yaya na kwakwazon faɗa,"mene haka na ke ganinku zaune a ƙasa kamar wasu almajirai, don me Nazifin ya siyo wancan dining ɗin ya ajiye, ko dama na kwalliya ne?, kai ku tashi ku koma can ku ci abinciku, kar a ƙara baku abinci ace ku zauna kan kafet ku ci. ba baƙi ba ne ku, nan gidanku ne gidan Babanku, kuyi yanda kuke so yanda ku ka ga dama kar ku ji shakkar yin komai, duk abin da ku ke so kuyi magana da Babanku, idan Antyn tayi muku wani mugun abun ku dinga faɗa masa kun ji ko". sai kuma Anty Aisha ta ɗora da faɗin,"umm ni dai Yaya ban da kin ce wallahi yaran nan ba za su zauna ba. ji fa don Allah yanda aka barsu su kaɗai a falo kamar wasu marayu, wallahi ko baƙo aka yi sai ya ce ƴaƴan ruƙo ne bana gida ba, don an bambamta ƙiri ƙiri. to ni dai har ga Allah ina ganin wani canji da ban gamsu da shi ba zan zo in ɗauke yarinyata, ba zan cutar da kaina ba akan yiwa ƙanina kara". da babbar murya Yaya ta ƙwala min kira, kamar wacca aka hankaɗo daga ɗakin sai ga ni na fito jiki sai ɓari ya ke yi. a dabarbarce na ce,"kun sauko, ga abincin...". "ke dilla can dakata banza mara mutunci, ba yunwatattu ba ne mu, da fari ma in tambaye ki, nan gidan waye?". kaina a ƙasa murya na sarƙewa na ce,"gidan aurena". tayi wani makirin murmushi da sake cewa,"to gyara zancenki, domin ko yanzu ba sai anjima ba kina iya barin gidan nan ki tafi a fanko, nan gidan Nazifi ne, Nazifi kuma ƙanina ne, ba ƴan uba mu ka haɗa ba uwa ɗaya uba ɗaya tafi gaban wasa, duk abin da yake mallakina yana da iko da shi kamar yanda duk mallakinsa ina da iko da shi. soyayyar da mu ke yi masa da tausayinsa yasa mu ka ɗauki ƴaƴanmu mu ka ba shi, wannan yaran da kike gani ba bare ba ne yanzu, ba ki da ikon kallonsu ki ce nan ba gidan ubansu ba ne balle kiyi musu iyaka da shi, yanzu Nazifi ne uwarsu ubansu, su kuma ko yau Nazifi ya faɗi ya mutu sun zama magadansa. saboda haka kinga kuwa sun fi ƙarfin ki ci mutuncinsu, ba marayu ba ne ba ƴaƴan kishiya ba ne ba kuma ƴaƴan tsintuwa ba ne. ko da kika ganki matar gida ba wai ke aka bawa su ba, mai gidan aka bawa, don haka ki tsaya iyaka matsayinki". ni dai take takensu da na lura yasa naja baki ban ce kanzil ba, don haƙurin ma idan na bayar zai iya zama wata rigimar, ƙarshe ma ƙanin na su ya dawo su haɗa masa ƙarya da gaskiya, shima ya juye min nasa rashin mutuncin. yaran su ka tashi daga inda su ke suka bi bayan budurwar da Yaya tasa ta kwashe abincin nasu ta kai musu kan dining, can su ka ci gaba da cin abincinsu. yayin da su kuma su ka koma saman don ƙarasa gyara ɗakin yaran. ni dai tun da nayi komawata ɗaki ban ƙara fitowa ba, ina jin duk wani kai komo na su da su ke yi, ba wasu yawa gare su ba amma yanda ka san masu jeran kayan amarya duk sun cika gidan da hayaniya. qur'ani na ɗauka ina karantawa don shi zai mantar da ni babinsu, sai bayan sallar la'asar na daina jin motsi, a sannan ne na fito na lura da sun tafi, tafiyar da ko arziƙin sallama ban samu ba. ɗakin yaran na buɗe na leƙa, zaune na gansu kan gado ɗaya suna kallo. Atika tayi murmushi da ganin nawa ita kuwa ɗayar ta haɗe rai tana juyar da fuska gefe. na ƙarasa wajen na su, ɗakin na su yay kyau, gadon yara ne guda biyu aka saka kowacce da nata, sai drowern kayansu ma kowacce da nata, ɗakin ya burgeni sosai kam dan dama in ta ɓangaren gyaran gayu ne Anty Aisha ba daga nan ba, zama nayi cikinsu ina masu hira wanda har sai da Rumana ta saki ranta, dama ita ce me bakin magana, nan kuma aka shiga bani labarin ƙawayen makaranta da malamarsu me sa kamun kunne, har tana faɗa min tun da sun dawo nan ga makarantar da zan ce Yaya Ƙarami ya saka su. a haka Hubbinya dawo ya same mu, annurin fuskarsa kaɗai ya shaida min yana cike da tsananin farin ciki, sai naji tausayinsa duk ya kama ni, ya kenan yau in ace ɗansa ne na cikinsa?, hannu na kai saman cikina ina rufe idanuwana tare da roƙon Allah ya azurtamu da haihuwa kafin mutuwa. farin cikinsa ya kasa ɓoyuwa, abin da ya siyo musu ya basu suma sai murna su ke yi, wayarsa ya ɗauko ya kira Yaya yana ƙara yi mata godiya da alkhairinta gare shi, Anty Aisha ma ya kirata daga baya. ya tambayi yaren sun ci abinci suka ce masa ehh, yace to su taso suje ɗakinsa, a tare muka fita gaba ɗaya muka bi shi, haka naci albarkacin yaran walwalarsa gareni ta dawo, mu ka ta hira kamar ba shi ba da ya canja ƴan kwanaki, bini bini ya tambayeni me ya kamata a siyawa yaran, ni dai abin da na fara cewa shi ne akai su makaranta da wuri gudun kar ayi musu nisa a karatunsu. bayan ƴan kwanaki da safe na fito a wanka, turus nayi ganin Hubbi ya shigo ɗakin wanda rabonsa da ɗakina har na manta. kallonsa na tsaya yi wanda shima ya ke bina da kallo, to da yake dai tun zuwan su Atika ya ɗan sakko tsoronsa ya ragu a raina, muryata a hankali na ce,"ina kwana". ciki ya ƙaraso yana zama bakin gado. "kin tashi lafiya". "lafiya lau, mun je ɗakin ai na tarar baka tashi ba. na ɗauki ɗari biyu a wallet na bawa su Rumana kuɗin makaranta". na ƙarasa gaban madubi na ɗauko takarda ƙarama na miƙa masa ina daɗa cewa,"jiya aka basu a makaranta wai sun manta ba su baka ba". ya kalli takarda yana cewa,"ta mece?". "ban duba ba". karɓa yay ya duba ya ajiyeta. sai kuma ya kishingiɗa da gadon yana danna wayarsa. ni dai tun fitowata daga wankan na ke jin tasirin kallonsa na shiga jikina. tun da aka bamu yaran nan naga ya dawo hayyacinsa, kuma alamunsa sun nuna ya gaji da ƙauracewa junanmu, so ya ke ya kasance da ni sai dai ni ɗin kuma na ƙi basa dama da fuska, don ko jiya da naga take takensa na agwiwa ya ke ɗaki na gudo. yi nayi tamkar na mance da shi a ɗakin, na buɗe wadrobe na ɗebo kayan da zan saka, sannan na ƙarasa na zauna kan kujerar madubi, ta cikin madubi na hasko shi idanuwansa sun kafe a kaina. cikin natsuwa na yin komai nawa a hankali na ɗauko man shafawa ina shafawa, tun da na shafa humra na hasko ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya. na ƙarasa kimtsa jikina da turaruka cikin salo na jan hankali, ina gamawa na wuce zan saka kayana sai naji muryarsa a kasalance yana cewa. "zo". ɗago ido nayi na kallesa naga yanayinsa duk ya sauya. rigar nayi ƙoƙarin sakawa ya sake dakatar da ni da cewa,"ki zo na ce fa". ina ɓata fuska na ce,"Hubbi bari na ƙarasa saka rigar...". sai da na saka sannan na je wurin nasa, ya ɗago fuskata yana kallona ya ce,"Habibty fushi kike da ni?". kai tsaye na ɗaga masa kai, sai kuma hawaye ya sakko min. kwanto kaina yay saman kafaɗarsa da cewa,"ba kya kewata?". cikin muryar kuka na ce,"idan ma nayi kewar taka ya zanyi Hubbi, ka mayarshe ni tamkar ba matarka ta so ba, ka ƙi faɗa min dalilinka na ƙaurace min, duk na baka haƙuri ka ƙi haƙura, ban san laifin da nayi ba ka daina sona". ya zago da hannayensa ta ƙuguna ya ce,"to kiyi haƙuri na san na miki ba daidai ba, afuwan kin ji". yay maganar ƙasa ƙasa da muryar lallashi. na ƙara cewa,"to me yasa hakan Hubbi?". numfashi ya sauke ya ce,"saboda ina so inga na sami ɗa sai dai ke kuma shiru, naga kamar rashin haihuwar bai damunki, shiyasa na ke ganin mu'amalar tamu ma bata da wani amfani. amma yanzu da na sami yarancan sai na ji kaso saba'in ya yaye na damuwar rashin haihuwar da bamu yi ba. amma kin sani ina sonki, matsayinki bai taɓa canjawa ba daga gare ni, don haka kar ki ƙara cewa na daina sonki kinji ko, ni na ki ne na har abada, ke ɗaya jallin jal Sa'idan Nazifi". murmushi nayi ina kallonsa, jin maganganun nasa nayi kamar daɗin baki, sai dai kuma ba hakan ba ne, tabbas shi ɗin mai tsananin sona ne duniya kanta zata shaida hakan. sabuwar soyayyarsa naji ta kamani, sai dai na kasa amayar da duk wata magana da ke narke a cikina. duk tarin baƙin cikin da ya ƙunsa min naji ya gushe, tabbas ina son Hubbi, ina ƙaunarsa, kuma sonsa da ƙaunarsa ne yasa zan ci gaba da haƙurin rayuwa tare da shi ɗin, domin a ƴan kwanakin nan kaɗai na lura soyayya da komai nasa da ya tattare ya ɗora akan yaran can zai iya haifar min da babban ƙalubale. "ya kamata mu sha soyayyar da zata mantar da mu komai da ya faru, komai ɗin ya zama tarihi". ya katse tunanina da faɗin hakan. kuma lokaci ɗaya naji yana tattare rigata zai cire. lokaci guda ya fara aika salonsa ga jikina, tuni kuma na biye masa muka faɗa cikin duniyar jin daɗin ma'aurata, mun daɗe kafin mu sami natsuwar da muka rasa na tsawon watanni. da mamakina muna gamawa ya tashi ya fita a ɗakin ko wanka bai tsaya yayi ba, saɓanin da anan yake wankansa, wataran ma tare mu ke yi, mamakin hakan ya tsaya min a rai. na miƙe cikin gajiyar jiki na shiga wanka, ko bayan fitowata kasa komai nayi sai kwanciya saboda ba ƙaramin gajiyar da ni yay ba, sai da ya ƙosar da kansa da yunwar watanni da yawa da ya ɗiba. Cikin wucewar wasu kwanaki lamari ya ƙara taɓarɓarewa tsakanina da mijina, abun ya koma tamkar sa hannu, bai barni da yunwa ba zan ci in sha, amma babu zaman lafiya sam, na rasa kwanciyar hankali da jin daɗi daga gare shi, komai nayi ba daidai ba ne, abinci idan na yi ba ko da yaushe zai ci ba, magana idan nayi sai yaga dama zai amsa min, makarantar tahfeez ɗin da na ke zuwa ya soketa ya ce in har da aurensa akaina na gama zuwa makaranta. idan na zo masa da buƙatar wani abu ranar sai yayi tamkar ya tashi gidan da wuta, ya dinƙa masifa ban da aiki sai shegen tambayar a bani a bani kamar don ni kaɗai ya ke neman kuɗinsa, kullum a nurƙufanci ya ke fuska ba wata walwala, ya dinƙa ƙunci da ɗacin rai, ba zan san fitarsa ba haka ba zan dawowarsa ba. zaman haka na ga ba zai kai min ba na tambaye shi jari, dalilin haka har kuka nayi saboda cewa yay na sakawa dukiyarsa ido, ban da godiyar Allah sam, menene ba ya yi min da har sai na zubar masa da ƙimarsa, salon a ce ya gaza wurin kula da iyalinsa, cuta in zan mutu sannu ba zai ce min ba, haka zan ƙara ci ciwona in warke babu ganin likita balle magani, sai ranar ma da ya ɗan ji tausayina ina matsanancin ciwon kai ya siyo paracetamol kwali guda ya bani wai in aje kar in sake ciwo ya kama ni in zo masa da zancen magani ko asibiti, wannan ya ishe ni ko da ciwon ajali na ke. ya daina tambayata ko shawarar duk abin da ya kamata ya aje a gidansa, sai dai ya kira Yaya, abin da ta ce shi zai yi, to yanzu ma ta ce da shi duk su nama da kayan marmari da ya ke ajiyewa ya daina domin ta lura ina masa almubazzaranci da kayan abinci, kuma ɗiba na ke ina bayarwa ba tare da saninsa ba. abubuwan baƙin ciki su ka taru su ka min yawa, shi na rasa laifin me na masa da duk ya ke ƙuntata min. ya hana ni fita kwata kwata, rasuwar da aka yi ta wata kakarmu ya barni da ƙyar ita ma sai da na sha kuka wajen magiya da roƙo, ita ma ɗin kafin ya bar ni sai da ya gama ci min mutunci da cewa ai idan na fita gulma da munafurci ke kai ni, da koyo fitsarar wulaƙanta aure da dangin miji, tun daga wannan furucin na sa kuwa na cirewa raina son fita ko da gidanmu ne. A ɓangaren Rumana da Atika kuwa, zuwansu gidan ban da matsala da nesanta tsakanina da mijina ba abin da ya haifar, yara su ka zamar min annoba, don zan iya cewa ta silar su ne hargitsi ya girmama a cikin gidan aurena, har akansu ina neman na kamu da ciwon zuciya. ya nesanta tsakanina da shi ya kusanta tsakaninsa da yaran fiye da tunani, da su ya ke shawarar duk abin da zai yi a gidan, ko magana zai min wacca ta kama dole sai dai ya faɗawa ɗaya daga cikinsu ta faɗa min, ga yaran sun raina ni, ba wacce na isa na mata magana sai ta min rashin kunya da fitsara, har kallon idona su ke su faɗa min ai Abbansu ba ya sona su ma don haka basa sona, ko abinci na ba su sai su ce ban iya girki ba ba zasu ci ba, idan ya dawo kuma su gilla masa ƙaryar ban ba su abinci ba, ba zan taɓa baƙi ba ƴaƴan nan su ga baƙona da ƙima su gaishe shi. ranar da na tsawatar musu akan ba su gaida Ya Imam ba, Hubbi na dawowa su ka ce ai na zazzagesu na ce zan koresu a gidan, alhalin kuma sun gaida Yayan nawa amsawa ne bai yi ba. ranar na yi kuka na gode Allah, don zagi na cin mutunci da ƙare dangi yay min a gaban yaran. wannan dalilin na cin zarafina da ya ke a gaban yaran sai ya ƙara ba su lasisin yi min duk abin da suka ga dama, ji na ke har gwara kishiya da su, don su idan su ka kunna wata wutar bala'in ba zaka taɓa cewa yara ba ne kuma ba zaka iya kasheta ba. ga sun iya kirsa abin kamar koya musu ake, a gabansa ladabin da su ke yi min kamar uwarsu, amma da zarar an ce bai gidan duk wacca ta ganni ma sai dai tayi min tsaki, ban isa ko ɗaga murya in yi musu ba nayi hakan na shiga uku ranar, idan suka ɓata wuri nasa su gyara sai yaci zarafina. na yi musu faɗa akan ƙin makarantar da su ke hakan sai ya zama tashin hankali har yana faɗin saboda ba ƴaƴana ba ne ba kuma ƴaƴan ƴan uwana ba ne, ina baƙin ciki yayyuna sun kasa sadaukar min da ɗansu ko guda, shi ne shi saboda an ba shi zan takurawa yaransa, to in cire idona daga sha'aninsu tun da ba ni ke ɗaukar nauyinsu ba. ɓangaren ƴan uwansa kuwa sun taso ni gaba da gorin haihuwa, ba su tsaya iyaka nan ba har faɗi su ke wai me ake da auren ƴan talakawa, sam ba su ga abin da aurena ya tsinanawa ɗan uwansu ba, ban da ma tawaya da yaja masa, da sun san haka aurena zai zamarwa ahalinsu masifa da ba su bari ya aure ni ba. idan na shiga cikinsu tamkar mushe haka suke ja baya da ni suna habaici, a ke min gorin wai ai ko da aka auroni haka na zo babu kayan gara. ƙalilan cikinsu ne ma su tausaya min, sauran duk daga kyara sai hantara da nuna ƙyama, shi yasa na kama kaina na ja gefe domin wulaƙancin na su ya fara min yawa, har bana so abun zuwa cikinsu ya ta so, mugun haƙurina kawai ke sawa na sharesu bana bi ta kansu, idan na ce zan fanɗare ba su isa ma su min kallon banza ba, to bana son tashin hankalin iyayena da damuwarsu, sannan kuma ina tsoron abin da zai jawa igiyar aurena samun matsala. duk matsaltsalun da ke ta faruwa da sanin surukata, tun ina zuba ido in ga ta tsawatar akan abubuwan da ƴaƴanta su ke min naji shiru, ga mamakina ma sai na ga tana goyon bayansu, itama ta hau kan layinsu, ƴaƴanta su min, ɗanta yay min, itama tayi min. gaba ɗaya na rasa ta ina ƙiyayyar ta samo asali, na rasa laifina. idan na bada haƙuri sai ya ƙara zama wani babban laifin, abin da na lura da shi ma ba akan rashin haihuwa kaɗai yasa su ka tsane ni su ke tsangwamata ba, akwai wani dalili na su a gefe wanda su ka barwa kansu sani. tabbas babu babban tashin hankali a gidan aure irin ace uwar miji ta sanyo ka gaba, ni a baya ban san wani matsalar uwar miji ba, idan naji ƙawayena suna ƙorafi akan uwar miji sai in ce ku ne dai baku iya zama da ita ba, ku sota tamkar mahaifiyarku sannan ku mata biyayya kamar taku mahaifiyar, to duk sanda na faɗi haka Hassana Tijjani ta kanyi murmushi kawai ta ce Sa'ida ba za ki gane ba, in uwar miji na sonki tana sonki kawai, in kuwa bata sonki to wallahi duk son da ɗanta ke miki zaman auren ba zai taɓa yi miki daɗi ba, in kuwa tana sonki to ko ɗanta bai sonki kya sami ƴar salama, ita uwar miji idan ta sako ki gaba duk wani kalar biyayya da za kiyi mata a banza ne, ashe hakan da su ke faɗa gaskiya ne domin kuwa ga shi ina ga ni, kallon banzanta gareni ya fi tsorata ni fiye da na ɗanta. duk wannan tashin hankalin da na ke ciki iyayena da ƴan uwana babu wanda ya sani, ban taɓa faɗa ba kuma ban taɓa nunawa ba, sai dai kawai fa duk wanda yay min farin sani yana ganina zai ce ina cin matsala, hankalina ba'a kwance yake ba. domin kuwa lokaci guda na fita a hayyacina na ƙara yin wata muguwar rama, nayi duhu duk na sakwarkwace, na zama kamar mara lafiya ƙwaƙwalwa saboda kullum a firgice na ke, haka na ke jin duk rayuwar ta fita a raina, har so na ke dare yayi ɓarawon bacci ya ɗauke ni in sami ƴar salama, don bani da babban tashin hankali sama da wayewar gari, da zarar gari ya waye na shiga fargaba da taraddadi kenan. uhmm so kenan, wallahi duk wannan tsananin da na ke ciki na gidan aurena har yanzu banji soyayyar mijina ta taɓu a raina ba, ban ji ina nadamar aurensa ba, ban taɓa jin ina ma ya sawwaƙe min in huta ba, sonsa na ke da dukkan raina, sam bana fushi da duk abin da yake min, uzuri na ke masa da kuma adu'a, tun bayan aurena da shi ban canja akalar adu'ata ba, kafin na yiwa kaina shi na ke yiwa, ni har na fi so ya zo yana min bambami akan ya shareni kwata kwata babu magana, kuma kullu yaumin bana fasa zuwa neman yafiyarsa da basa haƙuri a kowanne daren rana kafin kwanciyata, zan ta haƙuri ba zan karaya ba, Allah na zan ta faɗawa ya daidaita tsakaninmu, ya kuma bani ikon cinye jarabawar. yau na tashi da matsanancin ciwon kai, hakan yasa na kasa fitowa gaba ɗaya, tun da nayi sallar asuba na durƙufa kan sallaya, bacci ma na ke so na koma amma na kasa saboda gabana da ke ta faɗuwa, ga shi ina so na tashi in je in tada yara su yi shirin makaranta sai dai in na tashi jiri sai ya mayar da ni. da ƙyar dai na lallaɓa na tashi a daddafe na fita, ɗakinsu na shiga, na shiga banɗaki na tara musu ruwan wanka, sannan na fito na tashe su kan suyi wanka. su ka tashi da ƙyar kowacce na faman ɓata rai, zama nayi ina lallashinsu da ba su haƙuri akan cewa watarana sai labari, yanzu ne su ke da dama da lokaci na yin karatu, idan basu yi ba nan gaba za su ciji yatsa. na lallama su da ƙyar su ka sauko su ka wuce banɗakin, na jaddada musu da su yi sallah in sun shirya. ɗaki na koma saboda sanyin zazzaɓi da ya rufe ni, ina shiga na ƙudundune cikin bargo ina ta karkarwa, kaina jinsa na ke kamar zai faɗo, haka cikina ma wani bala'in ciwo ya ke min. ban ankara ba kawai naji amai, duk ƙoƙarina na kar in yi akan gadon hakan sai da ya faskara, amai nayi sosai mai wahalarwar gaske. gaba ɗaya jikina sai ya saki, da ƙyar na kimtsa wajen a wahalce na dawo na kwanta, hawaye kawai na ke zubarwa saboda ni ɗaya na san irin azabar ciwon da na ke ji a jikina. ina cikin wannan halin aka turo ƙofar ɗakin, Rumana naji tana cewa,"Anty mun gama shiryawa". fito da fuskata nayi ta cikin bargon kaɗan, bana iya ko ganinsu da kyau, murya a wahalce na ce da su. "wayata na kan mudubi ƙarfe nawa?". Atika ta duba tana cewa,"seven twenty". idona na rufe, har ga Allah ban da wani ƙarfi da ƙwarin da zan tashi in dafa musu abinci. a hankali na ce da su,"Rumana ban da lafiya, ku yi haƙuri kuje kitchen akwai sauran abincin dare a flask ɗin Abbanku ku ci kun ji, na san bai huce ba. abincin makaranta kuma zan bayar a kawo muku". su ka yi shiru ba su ce da ni komai ba duk su ka yi cirko cirko. tsoron abin da zai biyo baya yasa na miƙe zaune cikin tsananin azaba, cikin dauriyata na yunƙura zan sauko Rumana ta ce. "Anty ki koma ki kwanta, a bamu kuɗin makaranta idan mu ka je sai mu siya snacks kafin a shiga class, ba zamu iya cin sauran abincin jiya ba". na san yanzu Hubbi bai tashi ba, don haka nace da ita,"duba ƙasan littafin can akwai ɗari biyar ku ɗauka". ɗari biyar ɗin kenan na ke ta ririta ko da wata buƙata ta ujila zata taso min. ta ɗauko tana faɗin babu canji, na ce suje da ita tun da ba su yi breakfast ba, magani nasa ta miƙo min ta fita ta ɗauko ruwa ta kawo min. nayi musu adu'a tare da a dawo lafiya su ka fita, Rumana ɗin ce dama me sauƙi sauƙin kai, don ko yanzu ita ce tayi min sannu tana Allah ya bani lafiya, amma Atika har su ka tafi fuska a murtuke tana ta ƙunƙuni. ni dai zan iya cewa cikin awa guda na kusa shanye sacet ɗin paracetamol, amma duk da haka babu wani sauƙi da na ke ji a tare da ni, ciwon ma tamkar ƙara shi ake yi, hawaye masu zafi ne kawai ke sauka kan kuncina, idan nayi haka zan ɗau waya in kira shi sai in tuna kashedin da yay min, ba kuma na so in kira gidanmu nan ma ya zama fitina, haka dole na haƙura. adua na ke tayi, da kaɗan kaɗan kuma naji ciwon na ɗan raguwa tun da har ina iya buɗe idona, cikin baccin da ke son kwashe ni naji muryar Hubbi daga can nesa na kiran sunana da amon sautin da ya gigita ni ya firgita ni, zan iya cewa ban taɓa jin tsoro da firgici irin na kiran da yay min a yanzu ba, take

Chapter 6 of 23