Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
duk yanda ka yanke ba ni da ja akai daidai ne a wurina". Ya kalleta ya ce,"Zahra'u ke fa?". Tayi shiru na ƴan sakanni kamin ta ce,"ba kwana biyu ne ake yi ba dama? amma dai kai ne shugaba kai ya kamata ka yanke". Numfasawa yay yana dubanmu ya ce,"na yanke kwana bibbiyu na san hakan ba zai sa wata ta cutu cikinku ba. Sannan ke Sa'ida tsawon sati guda za ki kasance a kitchen, kuma idan kinyi girki za ki ke haɗawa ne gaba ɗaya har da ƴar uwarki. Zata karɓi girki a washegarin rana ita yau wato asabar me zuwa kenan". Ƙwalla ta cika idona nayi ƙarfin halin maida ita na ce masa,"tom babu matsala, asha amarci lafiya. Allah kuma ya bada ikon yin adalci a tsakani". Jiki a saɓule na miƙe na fita bayan mun shafa adu'a. Ai fa tun da na shiga ɗaki kuma sai kuka haka na dinƙa jin zuciyata kamar zata buga, karo na biyu da na raya dare yanda naga rana don sam bacci yay ƙaura a idona, wani azababben kishi na ke ji yana neman haukatar da ni musamman idan na tuna cewa yanzu fa Nazifi tare yake da wata wacca zai yi mata dukkanin abubuwan da yake yi min. da nanata salatin Annabi a raina na samu zuciyata ta fara sanyi har na kwanta bacci lokacin ma gari ya waye. Kuma da safen shi ya zo ya tashe ni a bacci yana tambayata paracetamol, na ce masa banda shi duk kuwa da ina da shi ɗin. zan koma baccin ya ce na tashi inje in ɗora abincin kari ko ban duba lokaci ba ne, Zahra'u na da ulcer kuma shima ai na san ƙa'idar lokacin cin abincinsa, yara kuma za su tafi makaranta don haka tun muna daɗi da shi kar na tsiri abin da zai zo yana mana babu kyau. sai da ya tabbatar na tashi kana ya fita a ɗakin bayan ya kora min kashedin kar na bari Iyam ta buɗe ɗaki ban kammala haɗa abincin safe ba. Cikin kwanakin da suke ta shuɗewa Nazifi da Amaryarsa amarci su ke ta sha na ban mamaki, tun ranar da aka kawota ba ya fita ko'ina idan ba masallaci ba, kullum suna ɗaki maƙale da juna, ko masallaci zai je sai ta raka shi har gate, haka duk lokacin da na fito zan sauka sai na jiyo sautin dariyarsu nuni da cewar suna cikin jin daɗin duniyar, dariyar Nazifi da zan ce na kusa shekara ban jita ba, shi yasa na ke baƙin cikin tarewarsu anan saman domin abin da matuƙar ciwo amma haka na ke shanyewa, sai dai dole ya raba mana ko na koma ƙasa gaba ɗaya ita ta dawo saman ko ni na dawo sama ita ta koma ƙasa, don na lura da gayya su ke abin na su. Rabon da na saka shi a idona tun washegarin kawo masa amaryarsa da ya zo ya bani dubu ashirin ya ce ko da zan buƙaci wani abu da kuma kuɗin makarantar yara idan sun buƙata saboda ba ya son damu kar suke zuwa can wurinsa, tun daga wannan ranar ko abinci na gama zai ce na barsa a dining za su sakko su ci, duk wata magana ta waya mu ke yinta, da kansa zai kira ni da safe mu gaisa, idan bai kira ba kuma shikenan ba dai zan gansa ba ko da inuwarsa tunda aiki ke fitar da ni, da na sauka na gama na dawo ɗaki shikenan yanzu sam bana zaman falo gudun ɓacin rai, shi kuwa yana ɗakin amaryarsa ko da zai fito ma ba sani zan ba, ɗakin yaran ya mayar musu ƙasa kusa da na Iyam da wataƙila in ke cin darajarsu idan ya zo dubasu ya leƙo ɗakina. Ita kuwa mun haɗu sau biyu ranar ina kicin ta shigo muka gaisa da fara'arta, tayi min sannu da aiki tana cewa zata tayani na ce mata a'a ba na saka amarya aiki ba ta bari ta gama shan amarcinta, taƙi tafiya ta zauna muna hira da ita jefi jefi babu laifi dai tana da kirki a yanda na fahimta duk da ba lokaci guda ake gane halin mutum ba, har da cewarta yanayina na burgeta ita kam, sai kuma take tambayana ya yanayin cin abinci a gidan ya ke saboda ta san yanda zata tsara lokacinta, hutun sati biyu aka bata a wurin aiki ga shi aikinsu fitar ƙarfe bakwai ne kuma sai huɗu ta ke baro office, na faɗa mata duk lokacin da na ke girkina ta jinjina kai cikin harshen turanci tayi wata magana da ban shaida me tace ba haka kuma ban nuna mata ban gane me tace ba ɗin. Rana ta biyu kuwa da ta yini a ɗakin Iyam ranar ina yiwa Iyam gugar kaya, suna ta hira da ita akan wata mata da ita Zahra'un tace tana yi musu aiki ita kuma Iyam na cewa ai ƴar garinsu ce, shine har ta ɗauko dutsen gugarta ta zo muka ƙarasa gugar tare duk da Iyam na ta ce mata ta ƙyale mini na yi amma tace babu damuwa taga ai na sha aiki. Haka dai rayuwar taci gaba da tafiyar min zaman gidan Nazifi haƙuri kawai na ke yi domin ba daɗinsa na ke ji ba, duk wasu ayyuka da ɗawainiyar masu zama ƙarƙashinsa ni ce, idan na yi kuma kullum a ban iya ba nake a wajen Iyam, wulaƙanci kuwa ban fasa shansa ba sai wanda ya ƙaru ita ta min ƴan uwan idan sun zo suyi min duk da sun rage zuwa yanzu ina ga ko sun bari a gama cin amarci ne. Yawan kuka da sanya damuwa a rai kawai na ragewa kaina saboda gudun kamuwa da wani ciwon, amma haƙurin duk da na ke kam ina yinsa ne saboda abu guda biyu zuwa uku, na farko ina tunawa da rantsuwar Kaka na cewa idan har na fito to ba zan zauna a gida ba sai in ya mutu, da kuma tunanin shin idan auren ya mutu to wa zai auri bazawara irina wacce ke da naƙasun haihuwa? Kuma idan ma auren zan yi wanne kalar mijin zan ƙara aura? don ni tun daga kan Nazifi na sare da duk wani namiji da ita kanta rayuwar auren, ga mahaifiyata da na ke ta son gani amma har wa yanzu Abbaa bai sauka akan bakansa ba. Ranar cikar sati guda da yamma lis ina ɗaki muna chart da Safiyya, Nazifi ya shigo, shigowar tasa kuma ta matuƙar bani mamaki da ɗaure kai gami da tunanin me ya kawo shi, domin rabonsa da ɗakina yau kwana biyar, ni sai naji gabana ma ya faɗi da zuwan nasa. Na gaida shi ya amsa fuska babu yabo babu fallasa, ya ce na tashi na ɗauko masa kujerar madubi zai zauna, na bisa da kallo na ƴan sakanni kamar dai lamarinsa babu lafiya ko kuma yana rashin lafiyar rabuwa da amaryarsa ne oho, na ɗauko na ajiye masa ya zauna ni kuma na ci gaba da danna wayata. Tsakanin mata da miji sai Allah, duk irin yanda na ke matuƙar jin haushinsa da fushi da shi sai yanayin shirun nasa ya dame ni duk da hakan ba sabon abu ba ne, to amma yanayin yanda ya sakani a gaba ne kamar akwai damuwa babba, wani abu da na tuna yasa na ɗago na dubesa na ce,"Baka da lafiya ne?". Na tambaya cike da tsantsar kulawa har ina kai hannu na taɓa wuyansa sai dai naji jikin nasa sanyi ƙalau. Ya ce,"Lafiya lau na ke. Ya ƙoƙarinki? na gode". A hankali na ce,"babu godiya a tsakaninmu. Amma sai dai ban yarda da babu komai ɗin ba, ka faɗa min don Allah akwai wata damuwar ne?". Sai da ya gama ƴan kamekamensa kana ya ce,"ina so zamu yi magana ne da ke sai dai ban san ta yanda za ki karɓeta ba". Ina kallonsa sosai da nazari nace,"ka faɗa kanka tsaye ba matsala zan fahimce ka". Zamansa ya sake gyarawa kana ya miƙo min baƙar leda nasa hannu na karɓa. na buɗe ledar idona ya sauka akan bandir ɗin kuɗi ƴan dubu dubu sabbi masu uban yawa, na ɗaga kai na kalle shi ina jiran ƙarin bayani. Ya murza hannunsa kafin ya ce,"Zahra'u ce bata da lafiya don yauma a asibiti mu ka yini, to likita dai yace tana da buƙatar kulawa, kinga ƴan uwanta duk ba anan su ke ba balle a samu wanda zai zo ya zauna da ita. Na san ba ki da matsala Sa'ida shiyasa na ce zamu yi magana da ke ta fahimta ki faɗi farashin da za ki siyar min da kwanakinki na tsawon lokacin da zata ji sauƙi". Yay shiru yana kallona, ni kam har ya gama maganarsa kallonsa kawai na ke yi idona waje tamkar za su faɗo, yayin da a wannan lokacin hawaye sun gama wanke min fuska. Murmushi na yi me ciwo sai dai daga ni har shi zamu iya rantsewa tunda muke tare da juna irin wannan murmushin bai taɓa fita a fuskata ba, cikin wani irin murya da ban san ina da shi ba na ce,"uhmm sai kuma me?". Na faɗa ina haɗiye ƙullutun wani abu me masifar ɗaci. "Nan dubu ɗari biyar ne, idan kinga kina da buƙatar ƙari ki faɗa ko nawa ne a shirye na ke da na ƙara miki muddin kin amincewa buƙatar da na zo miki da ita". Na kaɗu da maganar Nazifi sosai, na rasa me zan ma ce da shi kamar yanda na rasa a wanne sahu zan sanya Nazifi, tunani na ke anya kuwa Nazifi cikin hankalinsa ya ke? Me ya ke nufi da wannan maganar da ya zo min da ita? Idan ni ce bai buƙata mene dalilin da yasa yake zaman dole da ni? Ina tarin ilimin addinin da na sani a ƙoƙon kan Nazifi? Dukkan tunanina ya tsaya cak lokacin da Atika ta faɗo ɗakin tana haki, ɗago idona itama Rumana ta shigo kamar an jefota, kafin nayi tambayar lafiya saboda yanayinsu da ke shaida akwai matsala, sai ji nayi Atika na cewa da shi,"Abba ka je Iyam ta faɗi". Maganar Rumana ta kutsa cikin tata itama tana cewa,"Abba Anti Amarya ce ta mari Anti Fati kuma Iyam taje wucewa hannun Anti Amarya ya bigeta ta faɗi a ƙasa tana can ta kasa tashi, Abba ka taso da sauri Anti Fati tana cewa sai sun yi rigima da Anti Amarya ita kuma Anti Amarya ta ce sai ta faffasa mata baki". Da saurinsa ya miƙe ya fita yaran suka mara masa baya, ni dai idona ya maƙale akan ƙofar ɗakin ina tunanin na tashi na bi bayansu ko nayi zamana?. Zuciyata ta hane ni da tashi na fita, na zauna cikin girgizar lamarin da Nazifi ya zo min da shi, siyan kwanana! bai damu da nawa hakkin ba! Jiyo sautin muryar Zahra'u a sama na miƙe na fita, har zan sauka na fasa na leƙa ta saman ina kallonsu. ta na tsaye tasa hannu ta matse bakin Fati wacce ke tsaye a gabanta tana faman matsutsun ƙwacewa. Shi kuma yana tambayar ba'asin abin da ya faru. Ran Zahra'un a ɓace babu sauƙi ta ce,"Honey waɗanna irin gidadawan mutane ka ke bari suna shigo maka gida anyhow? Kawai fa na sakko ne zan je wurin Iyam sai na isketa bisa gaban dining tana buɗe flask na abinci, to ni ban san wacece ba tunda ban san face ɗin nata ba dalilin da yasa na dakata na iskota ina tambayanta, daga tambaya kuma saboda fitsararriya ce unguwar zoma bata mata gashin baki ba shine take da zarran yi min tsaki tana faɗin na raina mata hankali, Honey can you just imagine ƙanwata ta kusan huɗu na min tsaki? Impossible i must teach her a lesson ba na tolerating raini ko kaɗan". Iyam wadda ta miƙe da ƙyar ta ce,"To Zahra'u yi haƙuri ki cikata ai rashin sani ne. kinga kwana biyu bata gidan shiyasa ba ki shaidata ba Amma daga yanzu ki shaida fuskarta ƙanwarki ce ita ce ƴar Autata, nan take tare da mu ai, ranar biki ne ta koma can gida". Iyam na yin shiru Zahra'u ta kaɗa kai tace,"Am so sorry to say Iyam amma wannan ba magana kika yi me kyau ba, ba hanyar gyara kuma a ciki, kamata yay ki dubeta kiyi mata faɗa kice ta bani haƙuri before then na saketa, amma ba in ƙyaleta ba gobe taji daɗin repeating ma wani, ban sani ba ko halinta ne haka kuma wataƙila tana yiwa matar gidan tana ɗauka sai dai ni ba me ɗauka ba ce". Sai tayi shiru tana mayar da kallonta ga Fatin ta ce,"yanzu za ki iyama Yayanki Nazifi tsakin da kika min ko za ki iya yiwa Maijidda(Yaya)? To ki sani ba sa'arki ba ce ni, ke imfact ko da shekaru guda muke da ke tunda har Yayanki ya auro ni na wuci ki min rashin kunya biyayyarki dole garen". Ta ƙyasta yatsu da ƙara cewa,"And just for today zan ɗaga miki ƙafa amma for the next time idan kika ƙara wallahi sai na saɓa miki kamanni". Ta saki bakin Fatin da ke aikin zare ido don da alama ruƙon bakin da aka mata ba na daɗi ba ne. Kana ta koma ga Nazifin tana ce masa,"you just kept silent ka ƙi cewa komai. Anyway ka gargaɗi ƙanwarka, idan ma akwai wasu irinta to ka tara su kaja musu kunne, ba ƴar iska ka auro ba so they have to respect me kaman yanda su ke respecting na ka. Kuma zai fi kyau ku yi shari'a da wadda tayi muku rainonta domin bata yi mata tarbiya me kyau ba ta cuceku". Ta kalli Iyam ta ce,"ki yi haƙuri bana sane na bigeki ban san da zuwanki wajen ba ne". Ta na gama faɗin hakan ta bar wajen, kuma yanayinta kawai zai shaida maka zuciya ta kai nesa, ganin tayo saman nayi saurin komawa ɗaki. Abin da ya dameni shi ya damen balle na tsaya fassara yanayin da naji akan abin da ya faru tskninsu. Na zauna na saka kuɗin da Nazifi ya bani a gaba ina kallonsu, kallon da yay sanadin haska min hoton wani lokaci can baya shekaru uku da suka gabata wanda ya haska tarrr a cikin kaina, ina hasko lokacin da na fita na bar gida kafin sallar asubahi Nazifi na kwance yana bacci, na fita cikin mamakon ruwan saman da ake narkawa ina me bara gurin ubangiji yasa na zama ta farko a layin da zanje na kamawa mijina, nayi tafiyar ƙasa tun daga Yakasai har Nasarawa GRA a ƙafa ba tare da na tsaya ko hutawa ba balle tunanin abun sakawa a baki. Na ƙara hasko lokacin da na ke tsugune gaban Alhaji Fari ina zubar da hawaye ina shaida masa halin tsananin da muke ciki na rashin cin yau balle na gobe, ina mai roƙonsa arziƙi da ya taimakawa mijina da jari ko da na dubu goma ne ko kuma idan da aikatau cikin gidansa ya taimaka min. Na ƙara hasko zuwan Nazifi a lokacin da kuma sanda Alhaji Fari ya ɗauko tsabar kuɗi naira dubu ɗari biyar ya damƙa su a hannuna ya ce ga shi yayi mana domin Allah. Na ƙara hasko lokacin da na juya na fuskanci Nazifi cikin tsananin murna da jin daɗi gami da fashewar kukan tsantsar farin ciki ina miƙa masa kuɗin da cewa,"Hubbi ga shi na ka ne halak malak, Allah ya amsa adu'armu Hubbi yaji kukanmu, Allah yasa ƙarshen wahalarka kenan yasa kuma silar ɗumbin arziƙinka ne mara yankewa". Tunanin da na ke ya katse sanda Nazifi ya dawo yana cewa da ni,"me kika yanke? Ko na ƙara miki lokaci nan da anjima?. Dubu ɗari biyar Sa'ida zata iya isarki taimakawa ƴan uwanki, idan ba haka ba kuma na ƙara miki wata dubu ɗari biyar ɗin kinga har Umra za ki iya zuwa abinki". Hannu na saka na goge hawayena da babu su, dan ban san ma sun ƙafe ba. Ina kallonsa fuskata a washe na ce,"Na amince, na baka kwanakina na tsawon wata guda bisa yardata da amincewata, ka kula da matarka yanda ya kamata, ubangiji Allah ya bata lafiya". Murmushi yay na nuna jin daɗi ya ce,"Na gode. sannan ki nemo sabuwar me aiki don Allah saboda kinga Zahra'u ma'aikaciya ce ba zama take yi ba, kinga akwai yiwuwar a sami me tayata aiki a ranakunta". Nayi shiru ban ce masa komai ba kaina na kan cinyata ina kallon kuɗaɗen, na dakatar da shi daga fitar da yake ƙoƙarin yi, na miƙe na isa gabansa na kama hannunsa na damƙa masa kuɗin na ce,"ba na da buƙatarsu ka ƙara a jarinka". Kallona ya tsaya yi ya buɗe baki zai magana na ɗaga masa hannu. "Don girman Allah kar ka ce da ni komai, kaje kawai raina fess ya ke. Daidai ne dai wanda yay ya sani, haka kuma ranar tsayuwa gaban ubangiji na nan tafe". Dogon numfashi yaja ya sauke idonsa akan kuɗin kafin ya juya ya fita ya bar ɗakin hankalinsa kwance. Hawaye ne suka shiga kwaranya a fuskata, sai na duƙe a wajen ina dukan goshina a jikin gado, kafin na ɗago kaina na kalli sama na ce,"Ya Allah dukkan abubuwan da suke wakana kana ji kuma kuna gani, ka fini sanin dalilin da yasa rayuwa ke ta ƙwallo da ni haka, na sani ba don baka sona ba ne, amma ya ubangijina ka sama min mafita nan kusa, ka sawwaƙe min wannan ƙasƙantacciyar rayuwar da na ke ciki, Ya Hayyu Ya Qayyum ka dube ni saboda tsarkakan sunayenka". Sannu a hankali naji ina samun salama a raina, kaina har lokacin ina kallon saman ɗakin na fara tunano rayuwar baya. *WAIWAYE, SHEKARU TARA DA SUKA GABATA.* *MAFARI...* Ta dabo ci gari, garin da ba kano ba dajin Allah, jalla babbar hausa, yaro ko da me kazo anfika, tabbas a duk inda kaji anyi irin wannan kirarin a kaf faɗin duniya, kasan ba da kowanne gari ake ba face garin kano da ake yiwa laƙabi da tumbin giwa, garin da ya amsa wan nan sunan, musamman idan aka yi duba da yawan al'ummar da ke cikin garin, ƴan asali da kuma zuwo daga ƙabilu daban daban, garin da ya tara manyan Malamai, ƴan kasuwa, Attajirai, ƴan siyasa, Dattawan arziƙi, Sarakai, Makarantun boko da na addini, garin da yay shura wajen haɓɓakar kasuwanci da kamfanunuwa. A tarin unguwannin da ke cikin garin kano, unguwar yakasai na daga cikin manyan anguwanni wadda ake kira da Yakasai rabin birnin kano, idan muka tattara zuwa makarantun da suke cikin garin kano da bamu san iyaka adadin su ba, Shekara secondry school na ɗaya daga cikin makarantun sakandire ta gwamnati da ke a cikin anguwar ta yakasai, me ɗauke da ɗalibai maza da mata. Ɗaya ga watan octoba ita ce ranar da duniya ta shaida a matsayin ranar murnar samun ƴanci na ƙasa najeriya, a bisa girman ranar ga ƴan ƙasa yasa hutu ke ta'allaƙa ga dalibai, ma'aikatan gwamnati, kamfanunuwa masu zaman kansu, har ma da wasu daga cikin ƴan kasuwa. A yau da ya kasance talatin ga watan Satumba, daga cikin harabar makarantar sakandire ta shekara, ɗalibai ne ke ta dabdalar shigewa cikin ajujuwa bayan kammala taron asambili da akayi, mafi yawanci fuskokin su ɗauke da farin ciki saboda murnar hutun da aka basu na tsawon kwanaki biyu sakamakon murnar zagayowar ranar ƴanci na ƙasa. tun bayan komawa aji kowanne ɗalibi ka kalla zaka ga zaƙuwa a fuskarsa na son a buga ƙararrawar tashi domin tafiya gida. Ƙarfe ɗaya da rabi dai-dai aka buga ƙararrawar tashi, kuma a wannan lokacin ajinmu SS2 mune muka fara fitowa. Sunana Sa'ida Salman Madobi, shekaruna goma sha biyar a duniya, ina ɗaya daga cikin sabbin ɗaliban da aka kawo watan da ya wuce da na baro makarantar Aisami na dawo nan ta shekara. Ni ɗin ba doguwa ba ce haka kuma ba gajeriya ba ce ina da matsaikacin tsayi me kyau gami da dirarran jiki na jan hankali, ina da cikar halitta ta ko'ina, doguwar fuskata na ɗauke da dogon hanci da madaidaicin baki da kuma irin idanun da ake kira da sexy eyes, ba zan ce ni kyakykyawa ba ce can amma dai ba na cikin sahun munana ina da kyawuna daidai misali, hasken fatata ba irin hasken nan ba ne sosai kuma ba baƙa ba ce ni, sai dai na ɗauko ɗabi'ar mahaifiyata na bala'in haƙuri da sanyi. ban da yawan magana ina son shiru a rayuwata ni kam, dan ina iya zaman minti talatin a wuri ban magana ba duk kuwa irin surutun da ake yi, wannan dalilin ne yasa wasu ke cewa ina da girman kai wasu kuma su ce saboda ƴar gidan masu kuɗi ce, basu san ni ɗin ƴar masu rufin asiri ba ce, kuma ba komai yasa ake min kallon ɗiyar masu ƙumba ba sai dan zubina da irin shigata ta uniform da jakar makaranta da yanda na ke fesfes, da Yayana da ya ke kawo ni a motar uban gidansa idan ya kai yaransa makaranta, wannan yasa da yawa ke tunanin Abbaana wani Alhajin Neran ne. Sunan Mahaifina Malam Salman, Asalinmu ƴan ƙauyen Madobi ne daga baya kuma karayar arziƙi da mahaifin su Abbaanmu ya samu yasa muka dawo nan cikin kano da zama, tun lokacin ina cikin zani. Abbaana yana kasuwancinsa anan kasuwar kurmi shi da ƙaninsa Baba Sabi'u in da su ke siyar da citta da kayan ƙamshi na abinci, yanzu haka kuma sun koma ƴan tebura anan bakin asibitin Murtala suna siyar da atamfofin leda turmi da falle falle. Mutane da yawa sun shaidi Mahaifina akan kirkinsa da dattakonsa, duk wanda ya san Malam Salman Madobi zai buɗi baki ya ce maka mutum ne na gari wanda ya san darajar ɗan Adam da kyautatawa, ba a taɓa jin kansa da kowa rayuwarsa kawai yake yi shi da iyalansa da ƴanuwansa, ga shi da ƙoƙarin taimako. Mahaifiyata ita ɗaya ce matarsa Sa'adatu muna kiranta da Ummani, ita kanta jama'a na shaidarta da halin kirki da sanin yakamatarta, kowa kuma zai ce maka Ummani bata da wani farin ciki sama da taga ta taimaki wani da ke cikin tsananin buƙata duk da itama ɗin ba shi ne da ita ba, akwai ta da halin kawaici da kauda kai gami da masifaffan haƙuri da ka iya hallakar da ita, amma banda idan aka taɓa ƴaƴanta, duk haƙurinta da shirunta ajiye shi take a wannan fannin ko da za su samu saɓani da mahaifina, akwai soyayya me ƙarfi tsakanin iyayena da kuma fahimtar juna, kyautatawa da rufawa juna asiri. Mu biyar ne a wurin iyayenmu, maza huɗu sai ni ƴar autarsu mace, Sa'id shine Babba wanda mu ke kira da Yashaik saboda tsantsar uztazancinsa amma mutum ne me zafi don shi ya gaji Kakanmu Zakariyya mahaifin Abbaanmu da mu ke kira Kaka, sai Yaya Imam da ke bi masa shima ɗin yana da zafi kamar Yashaik, sai Yaya Al'ameen shi kuma irin Abbaa ne kaifi ɗaya mara magana sosai, Yaya Salman me sunan Abbaa shine na huɗu muna ce masa Abbayo, shi kuma ba gidanmu yake zaune ba a gidan babban wan su Ummani yake, sai ni Autarsu wadda tazararmu da Yaya Abbayo shekaru bakwai ne. Ba masu kuɗi ba ne mu sai dai muna da rufin asiri, Mahaifinmu jajirtaccen uba ne wajen ganin ya tsaya akan dukkan buƙatun iyalansa da kuma ganin ya gina ƴaƴansa kan tarbiya me kyau da kuma basu ilimin arabi da boko gwargwadon iyawarsa, mahaifina bai boko ba amma mutum ne shi me son ganin ɗa na karatun boko shiyasa ya tsaya mana tsayin dka a wannan ɓangaren. Duk Yayyuna maza sun kammala makarantarsu, Yashaik shine me degree da ya kammala BUK in da ya karanci law, sai sauran masu diploma duk polytechnic suka yi, Ya Imam pharmcy Ya Al'amin Science lab, sai dai cikinsu har yanzu babu wanda ya sami aiki. Ya shaik driver ne a wani gida yana kai yara makaranta da kai iyalan gidan unguwa, Yaya Imam kuma ɗinki ya ke yi kuma yana samu sosai, Yaya Al'amin kuma su Abbaa yake bi kasuwa, sai ni yanzu da nake kan karatuna wacca iyaye suka ci burin karatun akaina kamar ni ɗaya ce na fara boko a gidan, duk wani gata ina samu, duk abin da nace ayi min sai an yi min shi duk domin ƙarfafa min gwiwa nayi karatu sosai, domin

Chapter 20 of 23