Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ga aman ruwa, kwata kwata na rasa me ya ke min daɗin a duniyata, ban isa na tuhumi ubangijina kan jarabawa da ƙaddarar da su ke ta ƙwallo da ni ba tun aure, sai dai zan roƙe shi da ya bani ikon cinyewa zuwa matakin nasara. bayan nayi sallar magriba ina zaune jugum, lokacin na kira wayar Hubbi yafi sau goma bai ɗaga ba duk saboda naji ya jikin Atika, hatta ita Yaya da Iyam sai da na kira su amma babu wanda ya ɗaga wayata, ban san wanne asibiti ba ne balle na bi bayansu, sai Lubabatu na kira tace min duk suna asibiti itama an barta ne da yara a gida, amma sun yi waya ance jikin da sauƙi. ajiyar zuciya na sauke don sai a sannn na sami relief, na kwantar da kaina gefen gado ina jan carbi, cikin tunanin da na ke zuciyata ke faɗa min ya kamata in kira mahaifina mu gaisa don mun kwana biyu bamu yi waya ba. duk da ina fargabar in kira shi saboda yacca zai saurin gano damuwar da ke kan muryata, haka na daure na danna kiran saboda ko ba komai waya da shi ɗin zai yaye min damuwar da na ke ciki. nemo lambarsa nayi, nafi ƙarfin minti uku ina saƙa da warwara akan in kira ko in fasa, can kawai na danna kiran ya tafi, kamar yanda ya saba duk lokacin da na kira shi yauma hakan ce ta kasance, ya katse kiran nawa sannan ya biyo baya. da adu'a na samu raunina ya ɓoye da na ɗaga wayar nayi sallama. "Salamu alaikum Abbaa". "Wa'alaiki salam da ma'aikaciyar lafiya, Ƴar albarka ya aka yi saƙon zuciyata ya iso gareki da wuri haka, yanzun na ke cewa bara nayi sallar isha'i na kiraki, ina fatan lafiya kike da ke da mai gidan na ki ko?". wani sanyi ya ratsa ni na farin ciki da jin muryar mahaifina. nayi dakiyar danne kukana na ce,"muna lafiya lau Abbaa, fatan kuma lafiya ku ke?, ya kasuwa?". "lafiya lau fa Sa'ida, komai lafiya kinji, ba dai ki da wata matsala ko?". kamar ina gabansa na ɗaga kai alamar ehh,"babu matsalan komai Abbaa". "to ma sha Allah haka ake so ai, Allah yayi muku albarka gaba ɗayanku, Allah ya ƙara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya kauda duk wata fitina da saɓani a tsakaninku, Allah yay miki albarka kinji Sa'ida, Allah ya ba ki nasara da sa'a a rayuwa, mafi alkhairi yay ta bibiyarki. ki tura min lambar akawunt ɗinki zan saka miki ɗan abin da ya sawwaƙa". "tom Abbaa na gode, Allah ya ƙara arziƙi ya ƙara muku lafiya da tsawancin kwana". "amin ya hayyu ya qayyum, ya makarantar tahfeez ɗin na ki kuwa, ba dai kya wasa da zuwa ko?". "ina zuwa Abbaa". "kema da ke cikin masu saukar ta bana ne?". "a'a sai wata shekarar Abbaa". "to Allah ya bada ilimi mai albarka, ki gaida mijin naki. yanxu ina masallaci sai in na koma sai ta kira ki". har nayi haka zan kashe kiran sunana da yay ya dakatar da ni. na amsa masa sai naji yay shiru, tunanin ko kiran ya yanke ne hakan yasa na kalli screen ɗin kafin na kuma mayarwa kunne in sake cewa,"hello Abbaa". ajiyar zuciya naji ya sauke, shiru bai ce komai ba sai can yay nisa ya ce,"kina jina Sa'ida". na ce,"ehh Abbaa ina ji". ya ce,"walwala ta burin zuciyar ɗan Adam tsakanin abubuwa guda biyu take, farin ciki da baƙin ciki. idan abin farin ciki ya ratsa zuciya fuska zata nuna, za ta yi ƙyalli, zata sake sosai wajen bayyanar da farin cikinta, daga nan kuma murmushi da dariya su ziyarceta. idan kuma baƙin ciki ya ratsata sai tayi baƙi, ta turnuƙe, idanu suyi jajur su cika da ƙwalla, idan ya tsananta hawaye su jiƙa fuska, murya ta bada labarin yanayin da ake ciki...Ƴata kar ki manta da wanda kike waya, mahaifinki ne mai iya gane halin da kike ciki ko bai kalle ki ba, Sa'ida saki kukan da kike ta dannewa tun a sallamar farko, yi kukanki yacca kike so ba zan hanaki ba kuma ba zan tuhume ki dalili ba, domin shi kuka hanya ce ta rage raɗaɗin da ke cikin zuciya, sai dai ina so na tuna miki cewa kuka ba ya maganin matsala...yi kukan iyaka iyawarki ina sauraronki". zuciyata naji ta matse wani abu ya daki ƙirjina, Abbaa da kansa yau ke bani izinin yin kuka, mutumin da sauyawar yanayina kaɗai ke tada hankalinsa amma yau shi ke ce min nayi kuka iyakar yina, shin ya san matsalar da na ke ciki ne?. lokaci guda dauriyata ta ƙwace na fashe da matsanancin kuka me taɓa zuciyar duk me saurare, kamar yanda Abbaa ya faɗa sam bai yi ƙoƙarin hanani ba, bai kashe kiran ba haka bai ce komai ba, sai dai ina jiyo saukar numfashinsa, haka nayi kukana na gode Allah, murya a dusashe na ce,"Abbaa na gama, amma babu wata matsala, dama kukan soyayyarku ne kawai na ke yi". murmushin manyance naji yayi, bana ganinsa amma ina da tabbacin sai da ya gyaɗa kai kafin ya ce,"yaro yaro ne". kana ya ƙara cewa,"na sani soyayyar da kike mana zata iya sawa ki zubar da hawaye musamman idan kika tuna cewa akwai wani tabbataccen lokaci da dole mutuwa zata raba mu. sai dai ba hakan ne musababbin kukan na ki ba, muryarki kawai ta shaida min akwai matsala, haka ne?". na rumtse ido nace,"haka ne Abbaa". "to me yasa za ki ɓoye min?". "kayi haƙuri Abbaa". yay shiru na ƴan sakanni kafin yay gyaran murya. "saurare ni da kyau Sa'ida. mu iyayenki ne, babu wanda zai tsaya miki tsayin daka a duniyar nan sama da mu bayan mahallicinki. adu'armu a gareki kaɗai ta isa ta magance miki kowacce matsala da kike ciki, kuma ki sani adu'a na canja ƙaddara". yay amfani da kwantaccen lafazi wajen faɗin hakan. murya na rawa na amasa,"haka ne Abbaa, ba wai na ɓoye muku ba ne saboda tunanin ba zaku iya min komai ba, kawai shiga damuwarku akan hakan yasa Abbaa, amma kayi haƙuri Abbaa, adu'arka kawai na ke so". nayi maganar da muryar kuka ina me share hawayena. "Sa'ida ni mahaifinki ne, ba lallai sai kin ɓoye min kina cikin matsala da damuwa ba, muryarki zata bayyana min. ba zan tsaya shiga sha'anin aurenki ba, sai dai ina so na tuna miki duk lokacin da tsananin rayuwa ya dame ki, abu na farko da zai sa ki farin ciki shi ne ki tuna ke musulma ce kuma Masoyiyar Manzon ALLAH [S.A.W]. Duk tsananin da kike ciki ki tuna cewa akwai wanda ya fiki shiga tsanani, Ki tuna cewa kinfi mutane da yawa jin daɗin rayuwa. wannan rayuwar tamu ta duniya da kike gani gaba ɗayanta jarrabawa ce, Sa'ida aure kan saka mutum ya yi farin ciki a rayuwa sai dai duk tsananin farin ciki ba shi zai hana ma’aurata fuskantar matsaloli ba. ba abin mamaki ba ne idan a wasu lokuta anata fuskantar matsaloli a auratayya, domin rayuwar aure gaba ɗayanta haƙuri ce, haka kowacce mace da kalar jarabawarta a gidan auranta. ko babu komai ki gode Allah da ya baki miji me tsananin sonki da ƙaunarki gami da tausayinki. ni dai abin da na ke so da ke kar da ki dinƙa barin damuwa a ranki, hakan zai cutar da ke. kamata yayi duk san da kika kasance cikin halin tsanani, to ki ɗaura alwala ki fuskanci alƙibla ki gana da ubangijinki, a gaban mahallicinki ya kamata ki zubda tarin hawayenki, ki ƙaskantar da kanki a gabansa kina me roƙonsa cikin kirari da tsarkakewa, shi ya san halin da kike ciki kuma shi zai magance miki. kuma hakan zai sa ki samu rangwamen komai, tun haihuwarki mu ke miki addu'a kuma ba zamu daina ba har mu kai ga kushewa, kuma ina miki alƙawarin ƙara dagewa akan yi miki adu'a Ƴata. Allah bai hanaki don baya sonki ba, bai bawa wasu don yafi sonsu akanki ba, kema yana sonki kuma zai ba ki mafificin alkhairi cikin yardarsa da amincinsa. Allah yay miki albarka, Allah ya shiga dukkan lamuranki, ya yaye miki dukkan ƙunci, ya kawo miki salama da natsuwa. ayi haƙuri a ƙara haƙuri a kuma ci gaba da haƙuri kinji ƴar albarka, ina faɗa miki hakan ba kuma zan fasa faɗa miki ba ko da yaushe; haƙuri, uzuri, kawar da kai da kuma yafiya, ki kamasu tabbas kin kama makaman nasara da farin ciki, Sa'ida wanda ba ya haƙuri ba ya uzuri ba kuma ya yafiya to shi ne ke samun naƙasun farin ciki, amma me haƙuri da tawakkali da fawwalawa Allah komai wallahi ba ya tawaya, bayan tsanani sai daɗi da izinin Allah". yay shiru, ni kuma kukana ya ƙwace, cikin muryar da ta disashe da majina na ce,"na gode Abbaa nah, na gode sosai, ubangiji Allah ƙara muku lafiya, yaja min da ranku, yasa kuyi kyakykyawan ƙarshe". "amin ya Allah ƴar albarka. amma ki daina kukan, ki kuma yi min alƙawarin ba za ki ƙara ba". "in sha Allahu Abbaa". "zan tura miki kuɗi sai dai kiyi hakuri babu yawa". "na gode Abbaa Allah ƙara arziƙi da wadata" "amin ya Rahman, sai gobe kwayi waya da Ummanin, kar taji ki a wannan yanayin ta hana kanta sukuni, Allah ya sadamu da alkhairinsa, ki gaida ɗan nawa". ya ƙarasa faɗa yana kashe wayarsa, wani sabon kuka na ƙaunar mahaifina ya zo min sai dai nayi saurin toshe bakina tunawa da alƙawarin ce masa ba zan ci gaba da kukan ba. kai na kifa a gefen gado ina lallashin zuciyata da tuna kalaman mahaifina waɗanda su ka fara kwantar min da hankali, tabbas ina mai godiya ga Allah bisa ni'imar barmin su da yay a raye. wallahi ina son Abbaana, ban san ya zan kasance ba a duk san da aka ce ba ya raye, ni na sani ta kowacce fuska nayi dacen mahaifa, adu'ata Allah yasa suci moriyata kafin mutuwarsu, ya kuma sada su da aljanna maɗaukakiya. banɗaki na shiga nayi wanka, bayan shiryawata na shiga laluba jakar makarantata, cikon hukuncin ubangiji sai ga shi na samo wata matacciyar ɗari biyu, hamdala nayi ga Allah ina miƙewa na fita cikin ɗan guntun farin cikina na samun kuɗin, wurin me gadi na isa na ba shi na ce ya taimaka ya siyo min maganin ciwon jiki, idan akwai sauran canji ya siyo min awara ko gurasa. cikin mintunan da ba su haura ashirin da biyar ba sai ga shi ya dawo, nayi masa godiya sosai sannan na koma ɗakina, awarar ɗari da hamsin ce ba wata mai yawa ba guda uku, na ci na shiga banɗaki na sha ruwa na kuma sha maganin. har aka yi sallar isha'i ina ta jira ko zan ji motsin dawowar Hubbi amma shiru, ni hankalina ma gaba ɗaya na kan halin da aka ce yaran suna ciki, idan na ɗau waya zan kira shi sai zuciyata ta kwaɓeni akan hakan, daga ƙarshe kawai na aje wayar na kwanta bayan nayi sallar isha'i. wajen ƙarfe biyu na dare na farka firgigit, na sauko da sauri na faɗa banɗaki na yo alwala, sallah na tayar ina ta jero nafilfili kuma cikin kowacce sujjada da tahiya kuka na ke ga Ubangijina, ina mai yi masa kirari da tsarkakan sunayensa, ina roƙonsa da ya kawo min sauƙi a halin da na riski kaina, ya wanzar da alkhairansa a gare ni, ya canja min tsanani zuwa sauƙi, baƙin ciki zuwa farin ciki, damuwa zuwa walwala, tashin hankali zuwa kwanciyar hankali da zaman lafiya. ni dai cikin ikon Allah tun raka'ar farko na fara jin sukuni na ziyartar zuciyata, haka bayan na idar na ɗau ƙur'ani na fara karatu, karatun da ban daina ba sai da na ji an fara kiran sallar farko, wallahi zuwa wannan lokacin sai naji zuciya tayi wasaisai, naji tamkar ba'a taɓa dasa damuwa da ƙunci ba a tare da ni, haka kawai sai na ke jin wani farin ciki da ban san dalilinsa ba yana ziyartata, naji ina mantawa da faruwar komai yana barin jikina yabi iskar ɗakin. har sai da aka yi sallar asuba bayan na gama lazimi na ji bacci ya ziyarci idona, a sannan na miƙe da ƙwarin jikina da bana jin ciwo ko ɗis na hau gado na kwanta, bakina ɗauke da tasbihi bacci me daɗin gaske yay awon gaba da ni. ba ni na farka ba sai ƙarfe goma na safe, yau dai hankali kwance na sakko saɓanin da dana ke sakkowa a gigice idan na farka irin haka a makare, ba don komai ba sai don tunawa da abincin mai gidan, ni ai ko babu komai ma kulle kitchen ɗin nasa yay min rana, tun da ga shi nayi natsatstsen bacci, kuma na huta haka babu ƙorafin ba ki kammala da wuri ba, babu ɗauko ɗauko, maida maida. wanka na shiga nayi, na tsaya gaban madubi ina mamakin irin ramar da nayi, ka rantse da Allah zaftarata ake yi, hannu na kai na taɓa kumburarren ciwon bakina, nayi wata dariyar takaici kawai ina girgiza kaina, hoton dukan da na sha jiya ya haska min tarr a ido, haka zagin da na sha yay amsakuwwa a kunnena, a jiya ina cewa na bar su da Allah ya saka min, amma a yanzu kam na yafe musu babu kuma ƙullacinsu a raina sam, na san zan daɗe kafin na manta abin da suka min amma zan yi dukkan iyawata don ganin na manta ɗin ko saboda kar na dinƙa ganinsu da abin har yasa ni jin ɓacin rai. humra na ɗauko zan shafa, sai dai ina ɗaukowar fuskata ta washe da dariyar da haƙorana suka bayyana, ba don komai ba sai don tunawa da Ummani, duk san da na kirata na ce Ummani Humra ta kusa ƙarewa zata ce Sa'ida amma shanta kike ko, ko kuma girki kike da ita ne in sa a koma haɗo miki duro guda. haƙiƙa ina son mahaifiyata, Allah dai ya bani ikon kyautata musu a rayuwa. rigar bubu na saka na sanya hular shatali, na ɗan yi tsaki saboda yanayin kitsona da ya tsufa. agogo na kalla ƙarfe sha biyu na rana da ƴan mintuna, na jijjiga kaina da mamaki, har na nufi ƙofa zan fita sai zuciyata ta dakatar da ni da ce min in fita in yi me?, ai kawai in koma in kwanta lokacin hutawa ne Allah ya kawo min, idan har ya dawo gidan ai dole zai zo ya tada ni ko dan ya ci zarafina, musamman da ya zamana laifin nawa tsagin jikinsa na taɓa. kan gado na koma na jingina bayana da filo, ba zan iya kwanciya ba don na gaji da ita, waya na ɗauka na kunna data na shiga wattpad na lalubo sunan Oum Mumtaz da Nana Haleema, nayi saving sababbin littafansu a library, na kashe data nan da nan kuwa na hau karatu, karatun littafin hausa sam bai dameni ba, amma ko da na leƙa wani group ranar nan naji ana ta koɗa littafan nasu na ce ni kam in sha Allahu sai anyi tafiyar da ni, baza'a barni a baya ba, Kwantan Ɓauna da Lokaci ne sai in ban same su ba amma ba abin da zai hana in karanta su kam. da littafin Lokaci ne na fara, kawai sai naji maganar Baba tana dawo min cikin kaina da yake cewa kowacce mace da kalar jarabawarta a gidan aure, tabbas haka ne tunda ga Umaima ma wadda matsalarta da tawa kusan ɗaya ce, sai dai ita nata da lafiya tun da babu tsangwamar dangin miji haka kuma ta samu ciki har ta haife, saɓanin ni da dangin miji suka taso ni gaba, miji babu sauƙi, sharrin ƴaƴan ruƙo, ga kuma nakasun rashin haihuwa da duniya ke ganin shi a matsayin babbar tawaya a gare ni. murmushi kawai na ke me ciwo domin ni ɗaya na san me naji a cikin zuciyata, haƙiƙa jarabawar da na ke ciki tana da matuƙar wahala, amma babu komai na faɗawa Allah daren jiya, ya amsa sai jiran sakamako wanda na ke da yaƙinin me kyau ne. can ina cikin karatun Kwantan Ɓauna ina jinjinawa sha'anin hassada da makirci irin na gidan sarauta, naji cikina ya murɗa har nannaɗewa hanjina yake saboda mahaukaciyar yunwar da nake ji, tun ina daurewa naji ina ba zan iya ba, to amma ya zan yi? na san ko na sauka babu abin da zan samu na ci, amma zanje na duba kan dining wataƙila Allah ya taimake ni in samu ko guntun biredin shekaranjiya ne. abu kamar wasa lokaci ɗaya naji jikina ya kama karkarwa, na yi cilli da wayar gefe na fita a ɗakin a gigice, tabbas yunwa bata da hankali, ji na ke fa kamar zan mutu wallahi. kamar yanda na zata har yanzu kitchen ɗin a rufe yake babu alamar ma an buɗe shi, a daddafe na wuce dining ina zuwa Allah ya taimake ni na samu ragowar yogurt a jarka, ban wata wata ba na ɗauka na kafa kai ban sauke ba sai da na shanye tass. na san ba zai wuce mai gidan ne ya sha ya ajiye ba don ni dai ban san da shi a wurin ba, jiya ban bar komai akai ba da nayi gyara, to ban damu da duk hargagin da zai min ba, ba hauka na ke ba a yanda na ke jin raina na neman fita sanadin yunwa ba zanga abinci in ƙi ci ba, duk abin da zai min yay min na riga na saba yanzu. ɗaki na koma na ɗora karatuna daga in da na tsaya, a hankali naji cikina na motsa min da ciwo, can kuma na fara ji kamar ana ɗaure min hanjin cikina, nayi saurin miƙewa zaune ina riƙe cikina idanuna a runtse, tambayar kaina na fara anya youghurt ɗin da na sha me kyau ne?, ko dai ba Hubbi ne ya sha ya rage ba?, to wa ya shigo da shi?. da ƙyar na samu ciwon ya lafa na kwanta ba shiri, haka nayi ta sauke numfashi ina jin bacci yana ƙoƙarin ɗaukata, dama na ware a.c sanyin sai ratsa ƙashina yake. ban san bacci ya ɗauke ni ba sai ji nayi ana taɓa ƙafata, na buɗe ido a hankali, ido muka haɗa da Hubbi yana tsaye hannayensa zube cikin aljihun wando, ji nayi zuciyata ta motsa, nayi dakiyar ɓoye tsoronsa na ɓata rai ina yin miƙa, zuciyata kuwa ta dunƙa zugani akan in juya masa baya in koma baccina amma sai naji ba zan iya ba, haka na miƙe zaune kamar ina so kamar bana so nama kasa gane kaina. shi dai yana tsaye kamar wani gunki kallona kawai yake yi, ya shirya cikin manyan kaya riga da wando na yadi milk colour, yayi bala'in kyau kansa babu hula. kasa daina kallonsa nayi saboda masifar kyawun da yayi min, ba tare da shiryawa ba murmushi ya suɓuce min yayin kallonsa, kalmar kayi kyau na ke shirin faɗa masa, amma sai dai saƙon da ke a saman fuskarsa yasa na sunkuyar da kaina ƙasa na ce,"Ina kwana". Maimakon amsa gaisuwar tawa sai ji nayi ya ce,"Kafin nan da awa guda ki tabbatar kin tattara kayan ki kin bar min gida, kije gidanku ki zauna har sai san da na neme ki". a zabure na waro idanu waje har ban san lokacin da na sauko akan gadon ba saboda ruɗani, hannuna dafe da ƙirji idanunsa cikin nawa na ce,"Hubbi me ka ce?". ransa a haɗe tamkar hadari ya ce,"Kinji ai ba kya buƙatar na maimata miki, ki tabbatar kafin na dawo kin bar gidan nan in ba haka ba za ki yi karo da abin da ba ki taɓa karo da shi ba, wallahi muddin na dawo na sameki sai na miki wulaƙancin da kare ma ba zai shinshina ba". ya faɗa yana nuna ni da yatsa, kafin ya fita ya barni tsaye cikin maɗaukakin mamaki da tsantsar al'ajabi, haka na ƙame kamar gunki ƙofar kawai na ke kallo idona ko ƙiftawa ba yayi, tashin hankali da firgicin da su ke zuciyata kuwa tamkar zata faso ƙirjina ta fito. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un". na faɗa a bayyane ƙirjina yana harbawa hannayena har lokacin dafe da ƙirjina. "lamarin har ya kai haka?, duk haƙurin da na ba shi?, wanne irin bala'i ne wannan?, in tafi gida fa har sai ya neme ni, me yay zafi har zai yanke tsatstsauran hukunci haka? akan dai iya abin da ya faru jiya ko kuma da wani laifin daban a gefe da ban san da shi ba? to ni kuwa in je in ce da su Abbaa me?". a fili nayi maganar ina jan numfashi sama. daɓas na zauna kan gadon na kafe wuri ɗaya da kallo, cikin kaina na rasa tunanin me zan yi, na kuma rasa inda zan ɗora wannan al'amarin me girman gaske. ban san lokacin da hawaye ya shiga zarya a idanuna ba, lallai ina cikin jarabawa, kuma tabbas na yiwa kaina alƙawarin cinyeta, ba zan taɓa bari na faɗi ba in Allah ya yarda. zuciyata ta fara bani umarnin gaggawar tashi in bar gidan karma ya dawo ya same ni yay min abin da zai zama sanadin bugawar zuciyata a yau, a karon farko naji bana son ganin ko da inuwarsa. haka na buɗe wadrobe ina ɗebo kayana, ina zubawa cikin akwatu ina magana tamkar zararriya. "Me zan ce idan na koma gida? Na ce musu mijina ya ce in je gida sai ya neme ni?, bisa laifin me? da wanne ido zan kalle su in musu bayani? Hasbunallahu wani'imal wakil, Hubbi meyasa! Me na maka a rayuwa Hubbi?". ina kuka sosai haka na gama haɗa kayana, na ɗauko hijabina zan saka wayata da ke kan madubi tayi ƙara, na rufe wardrobe ɗin na ƙarasa da sauri na ɗauki wayar don na shaida kiran Ummani daga ringtone ɗin da na saka mata na Uwa Uwa Mama me share min kukana. sai da na saita kaina da danne yanayin da na ke ciki na ce,"Salamu alaikum Ummani, ina yini". Daga can ɓangaren ta ce,"barkan ki dai Sa'ida, an yini lafiya, ya kike ke da mai gidan naki?." na ce,"Lafiya lau Ummani, duk kuna lafiya?". ta amsa,"lafiya lau, amma ya naji muryar taki kamar ba ki da lafiya." na ce,"Ehh wallah Ummani na tashi da ciwon kai ne yau, yanzu na tashi a bacci ma shisa kika ji muryan nawa haka, dama ina cewa zuwa anjima zan kiraki". na faɗi hakan ina dafe kaina yayin da sabbin hawaye masu zafin gaske ke zaryo min. ta ce,"subhanallah to kin dai sha magani ko?". na ce,"ehh na sha, shi ne ma naji daɗi ai". ta ce,"to Allah ya sawwaƙe. daman maganar zuwa ƙauye zan miki na bikin ƴar gidan Kawu Musbahu, gobe ne tafiyar da safe in Allah ya kaimu, ga shi na ji ki babu lafiya sai dai ki haƙura kya je musu daga baya ko". tamkar anyi min bushara da kujerar makka haka naji maganar Ummani, wani farin ciki ya lulluɓe ni har hakan na bayyana akan fuskata, cikin saurin maganar da ban taɓa yi ba na ce,"lahh ai ciwon kaine fa kawai Ummani, kuma na faɗa miki naji daɗi ma". sautin murmushin manyancenta ya bayyana har ya taɓa zuciyata, ta ce"ke dai kawai za kiyi ƙarfin halin naki da kika saba, to Allah dai ya ƙara lafiya. sai ki faɗawa mijin naki, idan ya barki kin fito da sassafe to mu tafi tare, in bai barki ba kuma kya taho ke ɗaya tun da kuna da direba". na ce,"ai kamar ma na sani muka yi maganar da shi ɗazu, da yake shima yana shirin tafiya za su koma dubai, kin san dama nayi miki magana an gama ginin ɗaya plaza ɗin da ya buɗe. sai na ke ce masa to daga biki kuma sai in ɗan yi kwanaki a gida ya ce babu matsala". ta ce,"ah tou faɗuwa ma ta zo daidai da zama, shikenan to sai kin zo ɗin. kya ce masa ina masa Allah kiyaye". da haka muka yi sallama ina mai farin ciki na samun damar da zan fake da ita ba tare da kowa ya san dalilin zaman da zanyi a gida ba bayan gama biki, wanda ina roƙon Allah yasa zuwa lokacin komai ya saisaita. sai dai kuma a gefe guda zuciyata cike fal da tarin fargaba da tsoro mara misaltuwa. Cikin farin ciki na ci gaba da shirina, har da kayan da zan bayar a ƙauye duka na haɗa, ban san lokacin da zaman zai ɗauke ni ba tun da bai ce ga

Chapter 8 of 23