Shugaban ƙasar Nigeria,na rantse da Allah sai ya yi dana sanin zuwan sa ƙauyen nan,Amina kun jin yadda kuke wari wallahi haƙƙin ku ba zai ta fi banza ba sai ya san ya taɓa ƙawayen SHATOU ".
Sai dai bata rufe baki ba wata motar tayi mata wankan kwata a fuska sage hannuwan ta ta yayi tana runtse idanun ta cike da hargagi tana tofar da yawu take furta " Allah ya isan mu,Allah ya isan mu Azzalumai ɓarayi,masu kuɗin jini ".
Cikin dabara ta samu ta goge fuskar ta dake ta wari sauƙin ta ma basu kai cikin baki ba ruwan iyakar su akan leɓen ta. kafin ta yanka da gudu ta cimma asalin motar da ta watsa wa Su Amina kwata da tarin duwatsu a hannun ta da ta tsinta a yanzu cikin hasala da wani irin zafi da zuciyar ta ke na wulaƙanci da aka musu ba,a kuma tsaya aka basu haƙuri ba ......✍️
# MMG#
# SHATOU#
# IRO#
# LINA SSS#
# REENA SSS#
# BILAL SSS#
# SAMIRA MAI BILLIONS.
Wannan littafi na kuɗi ne.akan farashin 1000
Page ɗaya ya rage a free pages da na muku alƙawari dan haka duk wadda ta shirya yin payment ga details a ƙasa.👇
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Idan ba shaida kika tura ba kar kimini wani zance pls serious one nake buƙata,ga komai nan a sama na ajiye muku.
Last free page on Monday.
Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh 💞
*_Typing_*
*💋KURMAN ƘADDARA💋*
*©®Faiza Almustapha Murai*
*FA'EEH BG*✍️
*BOOK ONE*
__Paid__
*_Last free pages👌_*
P..1️⃣2️⃣
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Posting room link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn
*LITAFFAN MARUBUCIYA*
*A MAFARKI NA SANTA*
*RAYUWAR MU A YAU!*
_*Ina yan kasuwa Manyan Hajiyoyi masu Capacity ga damar ku tazo domin kuwa muna tallata muku hajar ku a farashi mai sauƙi idan ki/ka na buƙata,sai ku tuntuɓe mu wannan lambar +234 808 750 4734 dan tallata hajarku.Sai mun ji ku.*_
✨🕳️💦🕳️💦✨
Cike da masifa ta fara ƙoƙarin jifar motar sai dai bata kai ga yin jifar ba aka daka mata tsawa inji ɗai daga cikin garda garda dan masu tsaron sa dake tare da shi wanda suka diro daga kan buɗaɗiyar motar su su biyu kasancewar sun hango abun da take shirin yi.
Zare mata idanu suka yi suna jifar ta da mugun kallo.
" Hey girl what are you up to ? "
Wani daga cikin su ne yayi tambayar yana kallon hannayen ta da suke rawa jiran take ta samu dama ta jefi motar yadda zata yiwa na ciki rauni.
Aiko cike da rashin tsoro itama zaro idanun ta dan bata fahimci abunda ya faɗa ba.Hararar su ta dinga yi ɗaya bayan ɗaya kafin ta faki idanun su ta yanka a guje ganin haka ya sa suka bi bayan ta tana isa dai dai ta wajajen motar ta ja baya ta saita danƙon kafin ta saki dutsen na ta da ta saka a kan danƙon da ta fito dashi a ɓoye wanda ita kan ta bata san dalilin da yasa ta ɗauko shi ba ta saka aljihun.Sai yanzu.
Tasss haka glass ɗin ya bada ƙarar tsagewa saboda yadda dutsen ya dake sa na farko kafin na biyu ya ƙara hawa kan sa sai da tayi harbi uku sannan taga ta tarwatsa glass ɗin ta dakata ganin sun kusa isowa wajen ta dan ta musu nisa.
Dariyar farin ciki ta kece da ita cike da jin daɗi dan ba haka ta so ba ma so tayi ta ta zubar da shi duka ta ga asalin ɗan ikon da ke ciki zaune wanda da alama babba ne dan ta ga yadda ake ƙoƙarin kare sa tun da ga waɗan chan gardawan.
Motocin chak suka tsaya dai dai saitin ta kasancewar umurnin da suka samu na dakatawa.
Dai dai lokacin su Amina sun ƙaraso cike da tsoro sai zare ido suke yi ganin abun da ta aikata dan su kan su basu san ta fito da danƙo ba.Tun da gardawan nan suka biyo ta.
Ƙoƙarin kama ta bodyguard ɗin suke yi dan hasale suke sai dai maimakon ta gudu sai ma riƙe ƙugu da tayi tana jifar su da kallon banza cike da masifa ɗayan ya ɗaga hannu yana batun kai ma ta mari sai dai ƙamshin turaren sa da yaji a akusa da su ne ya sa shi dakatawa yana kallon sa cike da mamakin uban gidan na su dan bai ma san fitowar sa ba.
Itako SHATOU bata juya ba sai ma rufe idanun ta da tayi tana jiran saukar marin da take ganin idan aka yi shi sai kowa ya mutu cikin su saboda yadda zata addabi rayuwar su.Duk da taji ƙamshin wajen ya sauya da wani daddaɗan ƙamshi hakan bai sa ta yi ƙoƙarin juyowar ba still sai ma buɗe ƙofofin Hancin ta da tayi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin tana jin ta kamar ta faɗa wata duniyar dan take taji bacci na son ƙwace mata ta gurin.
Sanyayyiyar Muryar sa ce mai cike da Izza ta daki zuciyar ta yana furta " Bike Stop this She's young ".Yayi zancen yana ƙare mata kallo ta ƙasan ido cike da mamakin rigimar ta ta dan tun farkon fara rigimar yake ɗan hango su ta madubi.
Dai dai lokacin ne kuma ta buɗe idanun ta tar akan sa kasancewar ya dawo gaban ta yanzu.
Ƙirjin ta ne yayi muguwar faɗuwa ganin mutumen dake gaban ta Bature sak har wani kashe ido yake yi yana sanye da baƙin yadi mai taushi sai dai babu hula akan kwantaccen gashin sa da ya sauka har akan wuyan sa.Kyakkyawa ne fari mai ɗan jiki kaɗan bai wani tara irin muscles ɗin nan ba dan da alama yanzu yake tashe yaro ne shakaf wanda ba zai wuce Shekara ishirin ba da uku a duniya.
Yana da tsawo sosai da faffaɗan ƙirji,Kyakkyawa ne dai na asali,Irin asalin kyawon nan na turawa masu kyau da suka samu surki da fulanin mu,Yana ɗauke da manyan idanu masu haske da gashin gyara wanda yake cike tabb akan gyaran sa ga dogon Hancin sa da ya ƙara ƙawata Kyakkyawar fuskar sa bakin sa na ɗauke da red lips masu kyau da suka ƙawata ƙaramin bakin sa.Sai da ta gama ƙare masa kallo sannan ta sauke numfashi dan ya ɗan bata Tsoro,ganin sa take kamar ba mutun ba,Samun kan ta,tayi da galla masa harara bayan haɗa idon da suka yi yanzu tuno da shine cikin motar da ta yiwa su Amina wankan kwata.
Masifar ta ce ta dawo sabuwa inda ta fara girgije girgije kamar wadda ke ɗauke da wani abu aƙirjin ta tana furta " Wallahi sai kun ba su haƙuri sannan zan haƙura na bar ku ku wuce ko na ƙara sa fasa muku glass ".
Idanun sa ya lumshe a hankali yana ɗauke idanun sa a kan ta dan tsafff yake kallon ta ta gefen ido yana kallon duk abun da take yi.
" Is that all " ?
Ya yi tambayar yana ya mutsa kyakkyawar fuskar sa da rana take ƙarawa haske gashi ranar ma ta ishe sa dan haka yake son su gama abun da ya kawo su subar garin dan tun asali bai yi niyyar zuwa ba Aka tilas ta masa.
SHATOU da bata fahimci komai ba ta cigaba da faɗan ta tana furta " Babu ruwa na ko turawan duniya zaka tara nan,kai ko mamamar ka elibabeth da donath trup wallahi sai kun bamu haƙuri babu ruwan mu da masu jajayen kunnuwa ".
Yanzu kam ido cikin ido yake kallon bakin ta da ke zaro zancen kafin ya koma kan kyakkyawar fuskar ta,ta ƙuruciya da take fitar da wani haske fess.Kalmomin ta sun so saka shi dariya amma shi ba ma,abocin dariya bane dan haka yadda ta ambaci su Elizabeth da donald trump suka sa shi ɗan lumshe idanun sa dan sun bashi dariya matuƙa,sai dai babu dariyar.
Hangame baki tayi tana kallon sa yadda zararan eyelashes ɗin sa suka kwanta akan fatar idanun sa,gashi taga kamar fuskar ta sake ba zata iya kiran abun da yayi da murmushi ba ko wani abu daban.
Ƙirjin ta ne ya ƙara bugawa haɗa idon da suka yi ayanzu karo na biyu kai ta sauke ƙasa jin ƙafafuwan ta sun sanyi.
Lemar da aka lulluɓe sa da ita har ta shiga ciki ce ta kalla kafin ta kalli ƙafafun sa dake sanye da sandals na maza masu shegen kyau da ɗaukar ido da suka ƙara haska farar fatar ta sa saboda suma black ne.Mere bakin ta tayi ganin ƙafafun na sa da ko ita da take mace nata basu kamo na sa haske da tsafta ba cikin zuciyar ta kuwa mai bilicin kawai ta furta sai dai bata san cewa zancen ya fito fili ba
Kawai ta tsinkayi Muryar sa yana furta " Hey bana bilicin,Amma ke kin yi kama da su ai".
Ya kai ƙarshen zancen yana sauke numfashi saboda bai cika magana sosai ba hasalima bai cika yin ta da cikakkiyar Hausar mu ba amma yau an saka shi dole.
Ido ta waro cike da masifa kafin hawaye ya wanke mata fuska duk da mamakin jin Hausa a bakin sa " Wallahi bana bilicin nima,Allah ya isa na duk wanda ya ƙara ce mini ina kama da masu bilicin ".
Bai ce mata ƙala ba sai ƙara lumshe idanun sa da yayi yana ja baya ya bar ta cikin rana dan lemar sa tayi mata rumfar dai dai itama.
Da ido yayi ma sauran alama da suke kallon ikon Allah su wuce ya rage daga shi sai wanda ke kula da motar dashi na hannun da man sa wanda suke mota ɗaya dashi.
Wucewa suka yi kowannen su cike da Haushin da ya ƙunsa dan sun so su nunawa Shatou ƙarshen rashin jin ta,su yi maganin ta dan gobe idan sun dawo ba zata ƙara gigin shiga sabgar mai gidan su ba.
" Mubarak ka ba wa yarinyar nan haƙuri ".
Yana gama zancen ya shige motar sa aka rufe.Bayan ya jefa mata kallon da ta kasa fassara shi dan ƙafafun ta sagewa suka ƙara yi.
Bata samu damar yin magana ba har sai da motocin da suke gaba suka tada motocin sun fara tafiya sannan ta ce cikin ɗaga murya " Wallahi ni ba yarin ya bace kuma ban karɓi haƙurin ba dan kai nake so sai ka bamu haƙuri,kuma Allah ya isa na,mai bilicin kawai ".
Mubarak mai kula dashi wanda ya girme masa sosai kuwa haƙuri ya bata murmushi ɗauke akan fuskar sa sai dai ko kallon gefen da yake bata yi ba dan kalmar yarinyar da ya kira mata ta ɓata mata rai.
Da sauri da ɗan gudu ya koma motar su yana mamakin halin wannan yarinya da uban gidan na su da yakan yi sati bai yi magana ba sai dai alama ta ido yau gashi da yin magana ta kusan seconni,a tsakiyar rana.
Daga chan cikin mota kuwa bayan sa ya jingina da seat yana sauke numfashi tare da ajiyar zuciya dan kansa ya fara sara masa da hayaniyar ta ga rana ya san sai ya kwanta ciwo wannan ranar da ya shiga mai zafi.
Kalaman ta ne da suka gama ratsa kunnen sa suka sake dawo masa " Wallahi ni ba yarin ya bace kuma ban karɓi haƙurin.... "....
Katse tunanin yayi yana jan mugun tsaki kafin a hankali ya furta " witch " saboda haɗa idon da suka yi babu abun da ya hango face Zallar masifar da take son sauke musu da bai jin zai iya ɗaukar ta dan yanzu haka kan sa ya fara juya masa.
Idanun sa ya lumshe a hankali yana cire duk wani tunani a kan sa,yana janyo wata hadaddiyar kwalba kamar zinari sai walƙiya take yi tana ɗauke da shisha flavour,ya fara zuƙar ta yana ja da sauri kamar zai haɗiye hayaƙin gaba ɗaya.
Mubarak dake gaban mota kallon sa kawai yayi ta madubin yana girgiza kan sa.
A ɓangaren Shatou kuwa kuka ne ya ƙwace mata saboda yace mata yarinya kuma yadda yayi zancen cike da rainin wayau hakan ya sa ran ta ya ƙonu matuƙa dan haka ta fashe ma su Ramata da kuka abun da basu ta ɓa gani ba sai yau tattare da SHATOU kowaccen su ta kasa iya furta komai sai ma yar kallon kallon da ake yi tsakanin su kowaccen su ta kasa furta komai.
Jawairiyya ce ta yi ƙarfin halin furta " SHATOU kiyi haƙuri idan ma dan haƙurin ne mun yafe masa ".
Wani irin kallo ta jefawa Ramata da hawayen ta jage jage a kan ido kafin ta ce " wallahi ba su ci ban za mugu kawai mai jajayen Kunnuwa dama an ce Turawa mugaye ne basu son baƙar fata ".
Tayi zancen tana share hawayen ta da suka tsaya chak.
" Ai nida ke ba baƙaƙe muke ba inda ma su Ramata kika ce ".
Amina tayi zancen tana kallon SHATOU.
Suko su Ramata kallon ta suke yi cike da harara.Itako murmushi kawai tayi dan ta san gaskiya ta faɗa ba ƙarya ba.
" Yanzu dai muje fara zuwa gidan su Ramata daga nan kowa ta je gida ta chanza kaya Ni na wanke fuska ta kar malam ya muna faɗa bamu dawo da wuri kar baƙin su zo muna nan,dama ina son na ga wani Shegen ne aka saka mu wahala saboda shi ".
Ranka ya suka yi zuwa gidan sai dai kafin su isa Shatoun sai jini take yi wai kamar ita wani mai jajayen kunne zai kirama yarinya ita da Inna ni ta daɗe da yaye ta.
Nan dai su Amina suka fahimci kalmar ce ta saka ta kuka.Suko sai yaba kyaun sa suke yi cike da santi kowa na faɗin albarkacin bakin sa,har da faɗin ba su zaci yana jin Hausa ba.Ita kuwa tana kushe sa tare da zagin uwayen sa da ta manna masa su Elizabeth da donald trump wayen da ta ɓa jin su a wani karatu da aka musu ana bada tarihin ƙasashe shine ta riƙe sunayen kuma sai aka yi rashin sa,a ba dai dai ta riƙe sunayen ba.
A gidan mahaifiyar Ramata da suke kira Inna faɗa tayi ta musu na rashin kallon hanya gashi garin haka sun jawa kan su wanka da ruwan kwata kwata dan basu yi mata bayanin asalin abun da ya faru ba sun ce mai mashin ne ya zo wucewa ya taka kwatar ta wanke su duk da haka bata yarda ba duk da SHATOU ce ta bada labarin.Wanda su basu san amfanin hakan ba,ita kuwa kar faɗan yayi yawa ne ya sa ta ce haka.
Babu ɓata lokaci suka fito saboda suma sauran sun chanzo kayan makarantar su ramata ce kawai suke jira dan ta fi wankuwa da ruwan dole sai da ta watsa ruwa.
Ficewa suka yi bayan sun mata sun tafi ta musu addu,a da tuna musu da kiyaye hanya.
Tunda suka fito suka yi ta fanfalan gudu dan sun san sun buga latti daga zuwa cin abinci wanda ba ma bari ake yi ba amma suka yi sa,a aka bar su.
SHATOU ce a gaba cikin su dan tafi su gudu nesa ba kusa ba basu dakata ba sai tsakiyar makarantar su dan a sake take babu ko ƙofa bare gate sai filin Allah da take zagaye dashi.Turus ta ja ta tsaya tana ƙarewa motocin kallo ƙirjin ta na sama yana ƙasa tana tuno abun da ya faru ɗazu,tana tsoron a ce sun faɗa ta san in haka ne dole za,a dake su,dan ta san tabbas ƙarar su ce suka kawo,sai dai ta san bugu bai kashewa dan haka ta kwantar da hankalin ta..Haka suma su Amina tsaye suka yi cike da macewar jiki, malam Yusi ne ya hango su daga chan gefe aiko ya taso da sauri bai ce musu ƙala ba sai alamar ido da yayi musu,su shigo a hankali yana nuna musu haɗaɗɗiyar kujerar da yake zaune ya haɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya ita bata ma san akwai irin wannan kujarar a ƙauyen ba bare ma cikin makarantar.Cike da mamaki take bin bayan kujerar da kallo sannan ta na ƙarewa mai riƙe da lemar sa kallo ganin kowannen su a natse,kamar wani abu ya kawo su ba abun da take zargi ba, sai A lokacin kuma ta tuno da baƙin da zasu yi kenan shine baƙon ta faɗa a cikin zuciyar ta.
Gaba ɗaya yaran kowa zuba ma Shatou idanu yayi ganin yadda suma kan su masu tsaron na sa da sauran jama'ar da ya zo da su suke kallon su musamman SHATOU.
Shi dai bai lura da komai da ke faruwa ba saboda hankalin sa na kan abun da yake dubawa, sai da ta tsayu agaban sa, saboda dama tana cikin wayen da ake ji da su anan makaranta ko mai gari zai zo ko baƙo tana cikin ɗalibban da ake ajiyewa gaba saboda tana da tsafta,da ilmi gwargwado ko yanzu tsaf take sai fuskar ta da har yanzu take nuna alamar an jiƙata da ruwa da kuma ɓacin ran da ya taso mata na sa.
Ido cikin ido suka haɗa ido dai dai lokacin da ya gama kallon duk bayanin makarantar da abun da ake buƙata na bayanin da p.a ɗin sa da suka tattara a yanzu bayan gama zagayen da su ka yi yanzu.
Lumshe idanun sa yayi yana sake buɗe su sai yanzu ma ya lura da uniform ɗin makarantar ashe kalar nata ne.Haɗe fuska r sa yayi ganin yadda take buɗe manyan idanun ta alamar ƙiriss take jira tayi rashin kunya nan gurin tun da ta ga ba,a mata komai achan ba.
Su Ramata shan jinin jikinsu suka yi suma kowaccen kamar an tsamo ta a rame tsoro ya cika zukatan su,su tsoron su ace Dagske ya bada labarin abun da ya faru ko ƙarar su aka kawo dan su har yanzu ba su yi zaton shine baƙon ba ganin sa yaro ne ba irin babba da ake magana ba.
Iro ne ya shigo da tawagar sa an sha coat hoƙaƙƙu sun sha guga sai buɗawa ake yi shi ga ɗan gayu,dan shi mai gari ya wakilta anann makarantar da kuma zagayen guraren da za,a kafa ma famfon ruwan sha,bai samu zuwa ba sai yanzu saboda ba,a goge masa kayan da wuri ba da ya aro a wani ƙauye.
Tun da ya shigo SHATOU ta ɗauke idanun ta daga kan sa ta mayar da su kan Iro tana sauke masa wata irin muguwar harara mai birkita Idanu ga wani irin zafin sa da ya taso mata.Sai dai dariya ce ta so ƙwace mata ganin yadda yake ta wani lanƙwashe wa,ta ayyana a ranta baka ga wannan ɗan izzar ba daka raina kan ka.
Tana rufe baki kuwa ya kawo dai dai gurin yana ƙare masa kallo.Haɗiyar yawu yayi ganin ko gaba da gaban ta dan sai da ƙirjin sa ya buga dan ya san idan wannan yayi turanci sai dai ya bishi da ido turanci Nigeria ya yaji da shi bare na Nigeria,to amma ai ba turawa aka ce zasu zo ba minister ne da kan sa,wannan shine minister ɗin ake nufi ko me.?ya tambayi kan sa.Maganar zucin sa ne ya katse lokacin da SHATOU ta saki wata irin mahaukaciyar dariya tana ƙara bin Iro da kallo daga sama har ƙasa da ke ta zancen zucin da bai da mai basa amsa,Cike da raina ta sa shigar sai yaji ya muzan ta musamman ganin irin dariyar da SHATOU ke yi kuma ya san dashi take ba shakka.Ran sa ne ya ɓaci take ya bawa Malam yusi umurnin a fitar da ita a hukun ta ta.Haka kuwa aka yi malam Bello dake tsaye ransa ya gama ɓaci da shatou ya taso rai ɓace ya fizgo hannun ta har sai da ta kusa faɗawa jikin sa bai dangane ta da ko ina ba sai ƙasa faɗuwa tayi kamar zata ci ƙasa a gefe har sai da ta sanya hannayen ta,ta riƙe ƙasar.
Tunda ta fara dariyar Tata yake bin ta da kallo
Cike da mamaki dan shi farko ya zata ma spirit ne da ita suka tashi sai dai a hankali ya kalli gefen da ta ke kallo a lokacin ne ya ga Iro kuma ya tabbatar da shi take.
A kan idanun sa komai ya faru har yadda malamin su ya fisgi hannun ta yana kallo ta ƙasan idanun sa.Amma bai tan ka ba sai ma lumshe idanun sa da yayi dan dariyar har cikin kan sa ya ji ta.Jin gina da kujerar yayi yana jin kan sa na ƙara sara masa.
Mubarak ne ya matso da sauri ya ɗan sunkuya yayi magana ƙasa ƙasa wadda bansan abun da ya ce masa ba.Idanun sa ya buɗe yana sake lumshe su dan idanun sa har sun fara sauya wa saboda hayaniya da kuma rana.
Miƙewa yayi ba tare da ya kalli kowa ba cike da izza da sanyin tafiyar sa ya kama hanyar shiga motar sa baya Mubarak ya take masa.
Malam Bello da yake principal na makarantar da Iro suma da sauri suka bi bayan sa.Dakatawa yayi bayan ya cire sun glasses na sa da ya sanya bayan ta sowar sa ya ƙyafato malam yusi Cike da sanyin murya ya ce " Don't let them to hurt her,mace ce ".Malam Yusi da ba wani gane turancin yake ba ya ɗan fahimta hakan ya sa ya gyaɗa kan sa cike da girmamawa.
Da ido yayi wa Mubarak magana.Mubarak cikin aiwatar da zancen sa ya ce " masu construction zasu zo su duba komai,tare da masu ginar ruwa in Sha ALLAH,zasu zo a gobe,kuma idan mun samu time zamu dawo ".
Yana gama zancen ya shige mota shima dan dama shi ya shige tun bayan gama maganar sa har ya rufe sa.
Glass ɗin gefen da su Iro suke tsaye cirko cirko ya buɗe kafin ya Jefa musu wani irin kallon da suka kasa gane na meye.
Sannan ya danna madanni glass ɗin ya rufe.Sai da suka ɗan tsaya na mintuna kafin ya bada damar tafiya.Yadda motocin suka shigo haka suka bar makarantar ɗauke da daddaɗan ƙamshin sa da ya garwaye ko ina.
Malam Bello da Iro da suka ji duk bayanin da Mubarak yayi ne suka ce Masha ALLAH cike da farin ciki sai dai dukkanin su suna mamakin izzar wannan yaro dan daga nin sa yaro ne da kaɗan zai girmi shi Iron.Sai zancen da yayi na farko da basu gane komai ba,dan lafiyayyen turanci ne yayi amfani dashi ko shi Malan yusi dan yana ɗan ganewa ne kaɗan ya fahimta.Kalmar mace ce kawai suka iya ganewa su ko.
Dan haka suka zuba ma malam Yusi ido dake murmushi dan jin ko zai yi wani bayani.Amma gudun jin kunya musamman shi principal yaji kunya bare ma Iro mai Degree.🤭
MANYA🤣
# MMG
# SHATOU J FARAUTA
# IRO
# LINA SSS
# REENA SSS
# BILAL SSS
# UMMAH SS
# SAMIRA M BILLIONS
Wannan littafi na kuɗi ne.akan farashin 1000.
Mun gama free pages👌duk wadda ta shirya yin payment ga details a ƙasa.👇
Zan baku kwana goma ko biyar zuwa lokacin na san duk mai niyyar biya ya biya.Dan mufa ra sa da wuri kafin school ta mini ɗauri.
Masu tambayar document bani dashi a ƙasa.✍️
Amma zan cigaba da update a Arewa Books mai buƙata sai taje chan tayi following ɗina ta saka kuɗi ta karan ta.
Handle ɗina a Arewabooks shine👇
Arewabooks *@Fa'eeh bg*
Whatsapp dai sai kun shirya,sai mu fara Ngde🙏
Idan ba shaida kika tura ba kar ki mini wani zance pls serious one nake buƙata,ga komai nan a ƙasa na ajiye muku..
*PAID BOOK 1k*
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh 💞
*_Typing_*
*💋KURMAN ƘADDARA💋*
*©®Faiza Almustapha Murai*
*FA'EEH BG*✍️
P..1️⃣3️⃣
*BOOK ONE*
~PAID~
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Follow my account*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*
༼✿☯‿☯✿༽
Bulalar Ummah ta riƙe ganin ya fara zubawa LINA ita,kafin ta rufe baki, idanun sa a rufe dan ko amsar tambayar ta ya kasa bata.Cike da ɓacin rai itama ta ƙara dafe bulalar tana furta '' Me kake shirin aikatawa,duk hukuncin da kake yi mata bai yi ba sai an haɗa da bulala yau she ma ka samo wannan ne,me ya sa ba zaka saka ta kamun kunne ba kamar yadda ka saba ".
Sakin Bulalar tayi tana kallon sa idanun sa sun kaɗa sunyi Jawur zuciyar sa ta motsa dan har jijiyoyin kan sa sun tashi kamar wanda yayi faɗa da mazaje, ta gefe ɗaya LINA kuka take tayi,na abun da ta aikata bama bulalar da yayi mata ba dan bata jin zafin bulala sai ta ɓace,ta takure waje ɗaya,ita kuwa REENA baccin azaba ya kwashe ta tuni dan haka hayaniyar ma ba ta ji ba.
Ƙasa Iya furta komai yayi sai ma sauke kan sa ƙasa kafin ya faki idon Ummah ya cigaba da zuba mata ita a duk inda ya ga shuɗin ta saboda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 39