yunwar nan "
Ɗan shiru yayi kasancewar ya dakata yana sauraren ta sai dai bai juyo ba.
"Nop I'm full " ya furta mata a taƙaice kafin ya fice cike da natsuwa.Bayan yayi mata sai da safe.Dan ita da sake ganin sa sai in ya fito zaije Sallah,ko Allah ya Fiddo dashi cin abincin idan yayi ra,ayi.
Da Harara dukkanin su suka bi bayan sa babu ma Kamar SAJIDA Salma kuwa mugun tsaki ta ja cike da ƙunar rai,sun rasa abinda suka kashe masa da bai iya ko amsa gaisuwar su sai ya ga dama a iya binciken su sun kasa gano laifi guda da suka yi masa da ya saka bai kula su ko dan basu haɗa jini dashi ba kamar Samrah.Haka dai suke ta yiwa kan su tambayoyin nan sai dai su gaji suyi shiru sannan Amma ta rarrrashe su.
" Ku riƙa zuba masa ido tunda bai buƙatar magana da ku,kun san halin mutun dan me zaku riƙa damar da kan ku ne,na sha faɗa Miki Sajida ku fita iskan sa bakwa ji dan haka Ni kar wacce ta ƙara kawo mini ƙarar sa " .
Baki suka Turo gaba ba tare da sun ce ƙala ba sai dai abun na ransu ba sa jin zasu bar zancen haka.Sun fi son ya je ga Abbu.
Sashen Hajiya ya faɗa cike da natsuwa Sai dai bata cikin falon hakan ya sa kai tsaye Bedroom ɗin ta ya wuce dan ya san chan ne kaɗai zai same ta dan haka direct ya tsayar da ƙafafun sa ƙofar tare da ɗan yin knocking.Shiru ba,a amsa ba ba,a basa izinin shiga ba,Ƙara maimaita Sallamar sa yayi cike da sanyin da Muryar sa ta ƙara yi,dan ya san tabbas tana jin sa wata rana haka take masa.
Ya ɗan jima tsaye kafin ta bada izinin shigowar sa fuskar ta babu annnurin murmushi.Sai ma karkace kai da take faman yi gefe jiki mace ya durƙusa ƙasa ya gayar da ita.
" Ayyah Barka da dare,Ina wuni "
"Barka,Lafiya "
Kawai ta bashi amsa ta cigaba da jan charbin ta.Zaune yayi ya ta ƙwashe ƙafafun sa wajen kan sa sunkuye.Ya ɗauki kusan mintuna goma a haka bata ce masa ci kan ka ba.Cike da rashin damuwa dan ya saba da hakan yana shanye duk wani abu da zata masa,tun ba yanzu ba tun yana ƙarami,kuma yana mata uzuri ne dan itace ya buɗe ido ita da mahaifin sa ya sani sune uwa uba na sa.Tun chan farko ya san bata bashi kulawar da ta dace duk da itace ta riƙe sa.Amma a koda yaushe bayan yin wayan sa yakan yi tunanin dalilin da ya sa wata rana take juye masa izuwa wacce bata son shi,wata rana kuma ta nuna masa ƙauna fiye da komai kamar yadda ya taso hannun ta ya taso cikin wayen nan fuskokin biyu nata sai dai har yanzu ya kasa samun dalilin ta ɗaya,da take nuna masa haka,A duk lokacin da ya tambayi Abbu kuma ya kan nuna masa babu komai ƙila yanayin tsufa ne.Ya kan ji nauyin sanar da shi dalilin da bai zamo abun da zata ɗaura masa ƙiyayya ba.Yace masa me akan me.Sai dai wasu lokuttan yana ji tana dan gan ta abun akan mahaifiyar sa da bai san fuskar ta ba sai a hoto,wadda kuma bata ma cikin duniyar mu gaba ɗaya.
" Idan zaka riƙa cin abinci ka riƙa ci,dan babu ruwa na ciwo ya kama ka ace ban riƙe amana ba ahto ".
Daga wannan furucin Ayya bata ƙara furta komai ba.Sai ma miƙewa da tayi ta shige wata ƙofa ta bar shi nan zaune.
Wani abu ya haɗiye mai nauyi da ɗaci kafin ya miƙe jiki a sanyaye ya bar bedroom ɗin.
Yana fita Sashen Abbu ya nufa.
Abbu dake duba wata tsohuwar jarida ne da yake adanawa a duk bayan lokaci ya kan ɗauko ta ya yi ta kallo yana Murmushi bayan karanta abinda ta ƙunsa.
Yau ma kamar kullum ya same sa riƙe da ita ahannun sa sai dai shigowar ta sa ya sa ya mayar da ita gefe da sauri yana ɗaura wayar sa akai yana ƙakalo murmushi.
MAHAJ da ya ga komai dan ya riga ya saba da ganin hakan dan haka ya nemi waje ya zauna ƙasa kusa da Abbun yana sauke ajiyar zuciya domin wani mashi da ya soke zuciyar sa na kewar mahaifiyar sa,A duk lokacin da Ayya ta masa wani abun mahaifiyar sa ce abu farko da yake fara tunowa da sai yaji wani irin rauni ya ƙara mamaye zuciyar sa.
Lumshe idanun sa yayi yana buɗe su kan Abbu da ya zuba masa idanu kamar ya samu Tv.Dan kobai faɗa ba ya san daga inda ya fito.Tabbas yana ji da Ayya ba mahaifiyar sa ba ce da tuni ya sata ta bar rayuwar ɗan sa amma uwa ce har gida ya so chanza mata ta yadda babu yadda za,ayi taga MAHAJ ɗin abu ya gagara rabi da kwata ahannun ta ya tashi amma har yanzu ta kasa ajiye makaman ya ƙin ta wadda take yi dan ta ta fi,amma hakan bai sa ta chanza ba,bai da dabara baida iko dan haka ya zuba ma Ayya idanu tare da fatan Allah ya kawo haske a cikin rayuwar ɗan sa.Farin cikin da ya rasa Allah ya kawo masa cika makon sa.
Murmushi ya ɗan ƙakalo kaɗan kar ya sanya Abbu a cikin damuwa ko ya ƙara masa ita.Abbu shima murmushin yayi da yake ƙara bayyanar da kamar su ta asalin fatar su da take iri ɗaya sak dan ba zama kace jinin Ayya bane dan ita chocolate ce.
Abbu fatar Mahaifin sa ya biyo ta sak asalin Bature na Australia sai dai duk da kasancewar sa Bature ya banbanta da saura kamar yadda muka san ko ina akwai musulmi akwai Christian.Domin kuwa kakan Abbu Musulmi ne kuma ba Nigeriye,kakar sa ce Baturiya..Wannan kenan.
" Kaci abinci kuwa "
Ajiyar zuciya MAHAJ ya sauke jin Furucin na mahaifin sa.
Kai ya girgiza masa a sanyaye."But"
Miƙewa Abbu yayi ya cire kan sa dake kan ƙafar sa,bai bari ya furta abun da yake son furtawa ba, ya bi wata ƙofa sai gashi ya shigo da fruit wayen da aka yayyanka,da wayen da ba,a yanka ba.Tare da ruwa mara sa sanyi.
Inda Abbu yabi yake kallo har ya ɓacewa ganin sa kafin ya sauke ajiyar zuciya yana ƙara lumshe idanun sa.
Fitowar sa ce ta sanya shi ware su kan sa.Yana sakin guntun murmushi a cikin zuciyar sa.
Zama Abbu yayi kusa dashi yana murmushi sannan ya miƙa masa pock da ya ɗauko wani irin apple mai kyau daga nin sa kasan zai yi daɗi.
" Haaa "
Haka Abbu ya ce harda buɗe na sa bakin kamar zai cida ƙaramin yaro.
Murmushi ne ya suɓuce masa wanda bai yi niyyar yi ba wanda kuma bai wuce na jin daɗi ba saboda,hakan da abbu yake masa sai yake tuna masa lokacin da yake ƙaramin sa.kafin ya kai haka.
Ɗan Buɗe bakin sa da yayi Abbu ya shammace sa ya ɗaura masa shi kan Leɓen sa.Idanu ya ɗan zaro a hankali kafin ya buɗe bakin gaba ɗaya ya tura apple ɗin yana zare shi daga pork ɗin.Farin ciki ne ya mamaye zuciyar Abbu koba komai ya saka ɗan sa farin ciki a yau ko iya wannan murmushin zai gani akan fuskar sa yakan ji daɗi matuƙa rayuwar da ya taso mai cike da kewa yana rage ƙunci.
Taunawa yake yi a hankali yana lumshe idanun sa dan ba zai iya nuna wa Abbu cewa bai da ra'ayin cin abincin ba.Dan chocolates ɗin da ya ci sun ishe sa dan haka bai rabuwa da su a cikin fridge na sa.
A haka Abbu yayi ta cida MAHAJ kamar wani ƙaramin yaro.Ya ɗan ci kaɗan su kankana da su abarba apple ɗin sannan ya janye bakin sa.Bayan Abbu ya miƙa masa gwanda da ta nuna sosai sai tashin ƙamshi take yi.
Sai da ya janye bakin sa Abbu ya lura da abun da ya ɗauko shi ya mama manta ya sako da ita.Shi ko MAHAJ Har tsikar jikin sa ta tashi.Gefe abbu yayi da ita.
Ruwa ya ke kallo sai dai bai furta komai ba.
Hakan ya sa Abbu fahimtar abinda yake nufi dan haka ya tsiyoyo masa ruwan da suke da ɗan ɗimi kafin ya miƙa masa cup ɗin karɓa yayi babu musu ya sha rabi sannan ya ajiye cup ɗin.
Murmushi Abbu yayi bayan ya miƙa masa tissue ya goge bakin sa.
Sannan ya shafa kan sa a hankali yana furta " Ni wai ba zani zan nema na fara goya ka ba MAHAJ ko yaushe ɗan ye shakaf kake komawa shekaran ka fa cikin na ishirin da ɗaya zaka shiga idan ban yi ɓatan lissafi ba ".
Murmushin gefen baki yayi kafin ya ce " I'm still your little son " .
Dariya Abbu yayi kaɗan sannan yace " Na tabbata hakan,bari na fara neman zanin goyo,ƙila kai da girma sai ka tara iyali MAHAJ,Allah ya kawo muna haske a cikin rayuwar ka ".
Bai ce Amin ba sai ma rufe idanun sa da yayi bayan yayi wa Abbu kallon ƙasa ƙasa dan duk lokacin da yayi zancen nan yakan ji wani iri dan baya jin akwai wannan burin na tara iyali nan kusa,dan bai shirya ɗaukar duk wata hayaniya ba yadda yake rayuwar sa ta private life haka yake son ya cigaba da gudanar da Abar sa babu takura.
Abbu dake lura dashi hannun sa ya riƙo yana furtawa a sanyaye.
" Baza ka ce Amin ba MAHAJ "?
Idanun sa ya ware kan abbu kafin cike da rashin son takura ya gyara bakin sa sannan murya ƙasa ƙasa ya amsa.
Abbu sai dai hango yadda jajayen laɓɓansa suka motsa yayi.
Samun kan sa yayi da yin murmushi kafin kowannen su yayi shiru.
Kiran Sallah ne na Isha ya tayar da su Alwallah kowannen su ya ɗaura sannan suka fice daga part ɗin zuwa masallacin estate ɗin kamar wani wa da ƙane dan abbu har yanzu jikin nan na sa bai chan za ba sai kaɗan baka taɓa cewa ba ya'yan MAHAJ bane saboda yadda Hutu ya ratsa sa.
*KAR KU SHAGALA KUNA KARATUN LITTAFIN KURMAN ƘADDARA*✍️
Tare da Fa'eeh BG.
(Firstlady 🙌)
Gimbiyar taskira👑
***
A ɓangaren su Abba kuwa ranka ya suka yi zuwa gida fuskokin su cike da farin ciki,bayan ya Rarrashi LEENA.Tare da Masu tsaron sa da come boy na sa da suke cike da kewar sa suma.Ma'aikatan masu kula da kamfanonin sa,dan suma sun zo tarbon Sa.
Cike da farin ciki dukkanin ahalin suka tarbe sa,Har su Hamida sun zo da iyayen su dan Abba ya ɗauki yan watanni chan.Farin ciki Sir da Hajjo da su Uwani bai ɓoyuwa dan Abba mutun ne mai kula duk da kuwa baya nan yana ƙoƙarin kiran yan uwan sa da iyayen sa,surukan sa.
Ƙaton dinning dake babban falon na Ummah aka baje masa komai da akayi masa duk wani wanda yayi masa abun tarba nan aka kawo masa shi.Dan faranta masa yana mugun son yaga ko ina ahalin sa ne dan haka har su Sir aka zauna akayi ci aka ƙoshi kafin aka ƙara yi masa ya hanya,ya kuma baro Germany ɗin dan chan ya tafi.
Su LEENA da su REENA take aka fara mantawa da wani faɗa aka cigaba da bawa Abba kulawa.Ummah bakin ta kamar ya yage saboda farin ciki sai dai ta wani ɓangaren tana kaƙalo murmushi ne kawai bata san dalilin da ya sa bata son ganin kishiyoyin na ta a part na ta ba.Amma gudun abun magana sai take ƙoƙarin haɗiye komai gashi an shedeta da haƙuri dan Ummah mace ce mai haƙuri da kau da kai.Dan kafin ma kaji ance wani abun ya haɗa su da wani sai an bincika.ta san ta kan ta bata bari kishin ta ko kaɗan ya fita har ya zame mata illa..
Sai da aka watse gaba ɗaya sannan abba ya samu ya je ya watsa ruwa sannan ya dawo falo cikin ya yan sa.Cikin su ya zauna yana biye musu ana bashi labari rabi duk shirme ne dan REENA ce mai bada labarin idan ta faɗi wani abun sai dai yayi dariya ita ko LEENA sai ta galla mata harara.Cikin Surutun nan ne na ta wanda indai tana gaban mahaifin su bakin ta bai iya shiru duk da rashin hayaniyar ta ta sanar da shi Damben da suka yi aschl shekaranjiya.
Yi yayi kamar bai sani ba ya tsaya ya saurare ta kafin yace " Amma ALEENATU Baki kyauta ba gaskiya,Yar ƙaramar ƙanwar taki zaki daka,baki san kin girma ba ".
Ya kai ƙarshen zancen yana sakin guntun murmushi tunda abun ya wuce.
Ɓata fuska Leena tayi kafin ta ce " Ai Abba itace sai ta dinga yin abu kamar bata da wayau Ni kuma sai na dinga jin haushi ".
Kai Abba ya girgiza yana mai da kallon sa kan REENA da ta ke ta Hararar Alina sannan ya furta " Laaa laaa daina kin ji yar gaban goshin Umman ta,harara Anty kike yi,ita wannan Munbar wa BILAL S S ƙanwar sa " ya nuna Alina,nufin sa ita.
Ya ɗan yi gefe da kan sa kamar bai ga yadda idanun ta suka cika da hawaye ba.
" Allah Abba,Ni ta gaban goshin Familyn SSS ce gaba ɗaya nice hasken idaniyar ku,Ni bana son na zauna gaban goshin ya Bilal a bar Ni da kai da Sir da KaKa,Kuma inada Baba Mai bIllions a gefe na ".
Ta kai ƙarshen zancen ran ta ɓace cike da ƙuruciya.
Dariya Abba yayi yana son su tado da zancen sai dai sun ƙi dan haka bai ƙara tada zancen ba.
Sai ma shiru da yayi yana kallon Ummah da tayi shiru kamar mai tunani fuskar ta babu annuri ta zuba ma waje ɗaya ido kamar hankalin ta bai kan su sai dai kuma duk abinda suke yi tana jin su,hasalima wata kalmar da Abba yayi ce ta ɓata mata rai.
" Ai kuma REENA ce ta gaban goshin ta Abba bani ba ka tambayi Ummah kaji ".
Zancen Leena ne ya shiga kunnen sa hakan ya sa ya ɗan juyo da kallon sa kan ta yana furta " ai kema ta gaban goshin sa ce ".
Ummah ce tayi karaf ta amshe zancen cikin sakin Murmushi tana furta " Ai dukkanin ku na gaban goshin sa ne,his precious girls,kawai rashin jin maganar nan ne ke haɗa ku,idan kika daina zaki ga Kun shirya ".
Ta kai ƙarshen zancen tana dariya.
Abba dake jin ta kuwa wani guntun murmushi ya sauke kawai bai ce ƙala ba sai ma miƙewa da yayi,ya kama hanyar barin falon dan bacci yake ji saboda kwana biyu bai samu ya runtsa ba saboda yana shirin baro ƙasar..
" Zanyi bacci Barry,kar a tashe ni kowaye ya zo " .
Ya ce wa Ummah.Dan haka yake kiran ta ko kuma Umman su.
" Abba ko Yaya BILAL ne ya dawo "
Reena tayi zancen tana Murmushi.
Kai ya girgiza shima yana son yin dariya hango yadda Leena ke ta Hararar ta.
Saboda jin wani sabon sakar ci.wanda ita bata ɗauke shi komai ba.
yadai suɓuto bakin ta kuma ta fitar.
" Ko shi ne SARINA ai ya san inda na fito ba zai so a tashe da Abban sa ba yana hutawa ".
Hayewa yayi da ɗan sauri Ummah da ido ta bishi bayan ta amsa " TOH a fito lafiya " wani irin abu na tsaya mata arai.
Kafin ta sauke numfashi.
Miƙewa itama tayi ta shige ta kama hanyar bedroom na ta ba tare da tace wa su Lina komai ba.
Ganin haka ya sa suko suka fito suka yi Sashen Uwani.
A chan suka yada zango duk sun cika kaka da surutu gashi ba wata Isasshiyar lafiya amma haka yake biye musu,shida Uwani sai dai suna ta ƙoƙarin ganin an rabu lafiya gudun kar su fara faɗace faɗacen na su dan haka da an kwata Uwani zata tare.
Su waye suka yi missing rigumar Shatou 🤗🤣😂Kar ku damu Nima ina kewar ta zamu je sashen ta next part in Sha ALLAH.
Da ga yanzu update ya koma duk bayan kwana ɗaya.
Saboda na koma school lecture sai a hankali.Allah ya sa zaku fahimce ni.ngd.
_FA'EEH BG✍️_
Book one free
Book two paid#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Comment,share,like pls 🙏
_*💋KURMAN ƘADDARA💋*_
_©®Faiza Almustapha Murai_
_FA'EEH BG✍️_
P_____2️⃣0️⃣
*BOOK ONE*
_FREE._
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*
👑👑👑
___________________Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a ɓangararen.Yau da daɗi gobe babu daɗi.Faɗan su Leena yanzu har gaban Abba yi suke yi sai dai yayi ta faɗa shida Ummah.Tun da haka yarintar su take babu abinda zasu iya yi Musu sai fatan shiriya.
BILAL ya samu kwanciyar hankali shima ya duƙufa aikin sa kasancewar hutun da ya samu ya ƙare masa achan ya ƙarar dashi.Sai dai har yanzu baya neman Leena ko ya kira waya baya zancen ta.Haka itama babu ruwan ta dashi fushi take yi dashi mai zafi dan haka a gaban ta zasu yi waya da Reena bata taɓa cewa a bata su yi magana,wata rana a gaban ta har video call suke yi kuma tana fitowa zai gan ta sai dai bata kula ko nuna cewa ta san abun da suke yi,abun na damun Bilal ɗin sai dai ya zuba mata idanu kawai ya ga iya inda fushin zai tsaya,Ummah kuma da Abba sun zuba musu ido a cewar su sun fi kusa da ya'yan na su zasu ma sauko ne,kowa yayi mamakin fushin na ta dan tana da saurin sauka bisa ga ma Leena da bata da faɗan amma tana da wahalar sauka idan tayi fushi.
Duk abun da ƙannen na sa suke ciki yana sane dan har case ɗin Anisa da ta shiga ta yi dambe da Wanda ya daki ƙanwar Anisa ɗin,kamar yadda ta ce sai ta koya masa hankali, wanda kan hakan ya sa Uztas Babba ya zane ta tare da mayar da ita gida suspension na rana ɗaya.Sai da tayi kusan kwana biyar hakan ya sa aka bawa Nina takarda ta kai gida saboda gaba ɗayan su har ita har REENA ya ji suka yi sai dai sun ce hutun kwana biyu aka ba su ana su ajujuwan dan haka Ummah da Abba suka yarda.Sai dai bayan hutun ya ƙare har sun ƙara wani Ummah ta sha kai da zancen komawar su makaranta.Ana cikin haka sai ga Nina da Hamra sun zo da takarda suka ci sa,a Abba ranar a sashen yake dan haka suka damƙa masa aiko ya tara su su duka biyun ya yi ta musu faɗa dan babu abun da aka ɓoye a takardar ga cikakken sunan Leena nan.ALINA SALEH SADA.
Har Reena haka na ta yake rattafe an rubuta nata rashin zuwa makarantar wanda shine laifin ta kawai.
Da haka aka tasa ƙeyar su bayan an musu faɗan da ya bi taɗa yan kunnen leena ya bi ta ɗaya ya fita...
••••••••••••A ɓangaren SHATOU kuwa duk yadda Inna ni take ƙoƙarin ɓoye wa Baffa na sai da ya fahimci cewa yar sa ta girma dan haka addu'o,i kawai ya bita da su cike da farin ciki da mamakin ɗan mutun girman sa babu wuya idan akwai rayuwa wanda ya sa har ya tuno da wani shuɗaɗɗen lokaci da bai taɓa tsammanin shatou zata zama mutun ba.
Sai dai mutuniyar taku babu abinda ta ɓoyewa su Amina.Suka dinga murna suma sun kusa girma kamar Shatou tunda Inna ni tace ta girma nan gaba kaɗan zata zama Babba.
A ɓangaren rigimar ta da Iro sai abun da yayi gaba domin sai da ta rama cin kashin da yayi mata bayan ta tabbatar shine dai wanda yayi rubutu akan allunan makarantar su.
Dan haka ta fashe masa tayun keke gaba ɗaya,fashi kuma irin na babu gyara.
Koda Iro yayi bincike ya gano Shatou ce dan haka ya ƙullaci sai ya wulaƙanta ta,tare da ɗaukar zugar ƙawayen sa.Yanzu haka yar ɓuya ake yi tsakanin su.Dan ita da kan ta ta san tayi masa illa babba wadda kuma take farin ciki har cikin ranta.
Inna ni kuwa mugun daɗi take ji a tunanin ta shatoun ta yi hankali tun ganin kwana biyu bata ɓallo masu wata rigima ba da iro tunda shine abokin faɗan ta.
Sai dai kamar haka ne dan ta rage yawon Sosai,ko farauta yanzu ba kullum take bin su ba.
Tafe Suke a hanya su huɗu,sun kaiwa Maman ramata aiken da ta musu,suna tsalle tsallen su na yara masu ƙuruciya.Ta furta "So nake Ɗan gidan elibabeth ya dawo na rama cin kashin da yayi mini dan ban manta ba " Kai Amina ta ɗan juya tana dariya saboda ta san maganar ramuwa ce dan kwana biyu da suka wuce Shatou kullum cikin jini nin sa take in ta haɗu da shi sai ta masa wulaƙanci,kamar yadda ya wulaƙan ta ta.Tana batun furta wata kalma akan zancen na zuwan sa sai kawai taga SHATOU na sakar mata harara da ta sakata haɗiye maganar ta.Kafin kuma tayi gaba tabar su nan cirko cirko.
Da sauri suka bi bayan ta har da haɗawa da ɗan gudu,kamar yadda ta fara gudun itama.
Ramata ce ta furta " ki jira mu Don Allah shatou "
Chak ko ta tsaya saboda jin sunan Allah da Ramata ta ambata,saboda SHATOU akwai taƙawa duk abinda ka haɗa ta da Allah kan sa kagama dan haka su Ramata da sun fara abu ta zille sai su haɗa ta da Allah sai kiga ta sauko anyi komai cikin natsuwa.
Suna isowa kusa da ita suka jera suka cigaba da tafiya kowannen su na sauke numfashi dan sai da suka haɗa da gudu.
Turus tayi ganin Wanda ke gaban ta,kamar an jefo sa, cike da masifa take kallon sa dan duk da ta san ta masa rashin mutunci bata jin zata nuna masa ta ji tsoro dan bai isa ba.
Kallon kallo aka fara tsakanin su,suko yan zugar abokan sa sai wani ciccira suke yi jira suke yi kawai ya basu umurni su hau ta da bugu dan bulali ne hannun su masu girma,ashirye suka zo bayan samun labarin an ga Shatou ta wajajen Layin Audu mai chemist itada su Amina.
Su ko su Amina tsoro ne ya mamaye musu zukata musamman ganin wayen nan bulolin sai hankalin su ya ɗaga matuƙa babu ma kamar Amina.
" Yau dai na kama ki bayan gama ɓoye ɓoyen ki,ke Ni zaki wulaƙanta,yau Bama zan jira hukuncin mai gari ba da kaina zan hukunta ki,kuma in kin isa ki rama ".
IRO yayi zancen cike da gadara da rashin mutun cin da ya zo da shi.
Hanɓare baki tayi bayan ta kyaɓe sa tana galla masa harara cike da rabin tsoron ta.Sai kuma ta saki guntun murmushi irin na rainin wayau kafin ta riƙe ƙuguu tana cewa " Ai dama jiranka nake yi,mu haɗu fuska da fuska,dan na shaida maka cewa ba zan taɓa yafe maka ba,abunda nayi maka bai cire mini zafin abubuwan da kayi mini ba,wai har Ni zaka ƙaryata kai da wayen nan ban zayen abokan na ka,saboda son ranku baka san abun na raina bane ko me,Sannan ka koma ka yi mini wani suna chan da bai da daɗin faɗa ma,kuma ka sake ƙarya ta ni,ai nikaina wannan karon ba sai an je gun mai gari ba "
Duka Idanu suka zuba mata sake da baki ƙaramar yarinya na zaro zance cike da rashin tsoron ta yadda ma take juya ɗan ƙaramin bakin ta yake kallo wasu miyau iro ya haɗa yana ƙarewa Shatou kallo daga sama har ƙasa irin kallon da bai taɓa yi mata shi ba.
Idanun ta da take ƙara juyawa cike da masifa yake ƙara bi da kallo.
Sai dai kafin ya iya cewa wani abu ya ji saukar bulala bulalar nan ba jikin kowa ta sauka ba face jikin Shatou wani daga cikin su ne mara haƙuri wanda yake mugun jin Haushin ta ya far mata saboda ta kira su da wawaye dama wanchan karon cike yake da ita.Cike da Masifa Shatou ta kai ƙasa tana kururuwa kafin ta kwaso ƙasa ta fara auna musu a jiki idanun ta a rufe cike da masifa.
Dai dai lokacin kuma manyan motocin da ke ratsa hanyar suka wuce su.Su Amina kuwa cike da tashin hankali ganin an fara da Shatou suka fara neman hanyar gudu itako babu alamar zata motsa sai dai cikin ikon Allah tayi musu wankan ƙasa yadda take so musamman wanda ya dake ta dan gaba ɗaya idanun sa sun rufe da ƙasa dan bai ankara ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 39