ta fara sharewa tana Murmushi dama haka suke kullum kuma Indai yana gari shida Ibrahim sun dinga rigima ta kaka da jika kenan suna tsokanar ta.
Ƙarshe anan wasan yake ƙarewa dan duk sun san yadda take ƙaunar kilishin duk da Babu wasu haƙora sai an buga mata shi.Sannan sun san an hana ta cin irin wannan Jann nama amma saboda tsufa da tausayin su ke jin Gara su bata abinda take so kar gaba suna kallo gashi babu ta gabansu shi ya sa shima Sir d dada suke ƙyalewa yanzu sun san ba,a mutuwa sai lokaci yayi kuma Mahaifiyar su ai tayi tsufa mai kyau tun har takan iya cin abu mai nama nama ba ruwa kawai ba.Shi ya suke ƙara gode ma Allah.
"Kaji ɗan Albarka,Allah ya jiƙan magabata,Allah ya jiƙan Dam rayuwa "
Sai kuma ta fashe da kuka.Jikin su ne yayi sanyi har su Leena tunda sun san wanda take cewa Dam duk da basu yi rayuwa da shi ba amma sun san shi a bakin a halin gidan kuma sun san hoton sa dan suna ganin sa asasan gidan.
Rarrashin ta yayi da ƙyar kafin jiki mace jin ta tado masa da wani Miki haka cike da ƙarfin hali haka ya fara daddaka mata kilishin sai da yayi rugub akan haɗaɗɗen dustsen da ake daka mata irin wayen nan abubuwan kafin ya fara bata ya na cewa " Ya isa Maama ci " Yana saka mata acikin bakin ta da ke ɗauke da da sa shi kawai sai yan haƙora da basu wuce biyar ba tsufa duk ya sauke mata su dan haka ko maganar ta ba irin sosai ake ganewa ba sai su da suka saba da ita.Ta nata magular abun ta.
Hajow tunda Mamaaa ta fara maganar ta miƙe tsamm ta shige ɗakin ta.
Shi kan sa Sir ƙarfin hali yake yi.
Abba da ya lura da yanayinsu bai matsa ba ya cigaba da bawa Maammaa tana ci suna taɓa fira har da su Leena tare aka cinye kilishin dan wanda suka rage mata kaɗan ne.Koda su ya gama bata dai dai an fara kiran Sallah hakan ya sa ya miƙe yana sanar da ita zai wuce amma zai dawo sai su wuce tare da su Leena ɗin.Dan Sir shima ya bar falon ya bi bayan matar sa.
Dai dai shima Sir ya fito haka ma Hajow a bayan sa sai dai babu wanda ya bari Ya haɗa ido da Abba.Numfashi kawai ya sauke bata re da ya ce komai ba sai dai ya saka mahaifin sa gaba suka fice a tare zuciyar sa cike da wani irin ƙunci mara daɗi da duk lokacin da Mamaa tayi maganar Dam sai dukkanin su sun tsinci kan su a damuwa dan kafin su warware sai an ci lokaci Abubuwa da dama ke dawo musu a tunani soyayyan su da suka rasa ne suke musu riƙo a zuciya mara wuyar sauka saboda dukkanin su kamar wani irin bango ne ko ginshiƙi a gare su na farin ciki.
Anan Falon Hajow ta yi Sallahn Isha tare da su Leena haka ma Mamaa da take yin Abar ta zaune saboda ƙafafun ta babu lafiya yau dan duka haka suke fama da su har Hajow ɗin Dada ma sune ciwon sa ko Sir ma haka sai dai na shi bai kai nasu ba dan in ya tashi ko tafiya ba su iyawa Uwani ce kawai da suke kira (Ummu)take da lafiyar ƙafafu.
" Nidai yunwa nake ji Inna ni ".
Murmushi Inna ni tayi kafin ta ce " kin ji abinda zaki ce Malama ba wani gajiya ba ke da farauta ɗaya biyu zaki zo min da zancen kin gaji ".
Dariya SHATOU ta kece da ita dan harda dungure kan ta Inna ni tayi.
" Akwai sauran abincin Baffann ku na nan ki ɗauko tun da bamu kai ga na rana ba,dan yau ma tuwo ne zanyi".
Ido Shatou ta ƙwalalo waje kamar wadda ta ga wani mugun abu ko ta ji ta ce " Inna ni tuwo,nikam dai ba zanci tuwo ba yanzu ma fa shine zan ci ragin ɗumame wai so ake yi sai Na zama kamar tuwo ne a riƙa kira na tamalmatu ".
Dariya Inna ni ke son yi sai dai ta fuske abunta ta cigaba da saƙar kaba da take yi Shatou na gefen ta tana haɗa mata kayan hadin dan tunda suka gama wanchan aikin ta ɗaura girki lokacin ita Shatou ta shiga ɗaki ta duba wani aikin gida da aka basu hankalin ta ya ɗauku.
Kuka ta sakawa Inna ni Dagaske bata cin tuwo ko anyi shi yau dan ba zata yarda ta zama tamalmatu ba dan ta taɓa jin labarin mai sunan an ce daga cin tuwo ta zama haka an mu su irin wannan ta tsuniyar a makaranta inji wani prepect.
Lalllai kammm Sai prefect 🤣
" Wallahi Zan kira Almajiri na bashi ya cinye shi yanzu "
" Ke kuma idan kin gama shiriritar ki sai ki ci na rana ".
Kafaɗa take girgizawa tana cigaba da yin kukan duk da ta na jin sarai abun da Inna ni ke faɗa,miƙewa Inna ni tayi kamar Dagaske take yi dan Muryan Almajirin ta ji a maƙota tunda ta kangar su babu wata girma gare ta dan ma duk haka gidajen na su suke na ƙasa dan ma Baffa na ya ƙara ma ta su girma sai suka ɗan banbanta.
Aiko cike da sauri ta miƙe tana ƙara sautin kukan ta.
Gefen madafar su ta ɗauke shi a inda yake killace cikin wata yar Samira.
Inna ni dariya ke cin ta sai dai bata nuna a fili ba tayi a zuciya sai dai kawai a bayyane ta girgiza kan ta cike da ƙaunar yar ta.
A wannan karon kammm sai da ta yi Murmushi a bayyane ganin yadda SHATOU ke cin Tuwon kamar tana cin kashi sannan ga hawaye jage jage akan fuskar ta.Ga kan ta da take ta langaɓewa gefe cike da Sangarta irin ta ta tana yi tana Sharar hawaye.
Chan kuma mai ta tuna ta ture kwanon baki ture cikin shesshekar kuka ta ce " Ni Bama zan ci wannan ɗin ba,haka kawai a yi ta bawa mutun tuwo,Ai Baffa na suna wajen Farauta na san zai zo da kaya masu yawa shi ya sa nafi son aje farauta saboda mugun Tuwon nan ".
Ta yi zancen tana share hawaye tana Hararar Tuwon Inna ni da yayi kyau na dawa ne sai ƙyalli yake yi ya tuƙu sosai kuma yayi taushi ya sha miyar mu ta kuka mai kyau.
Baki sake Inna ni take kallon ta jin tana kira ma Tuwon ta mugu aiko da sauri ta ƙwala kiran Almajirin.✍️
Damm🤔
Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800
# _FA'EEH BG CE✍️_
Book one free
Book two paid N#800 an samu discount.
Mun kusa kammala Book one masu niyyar biya sai ku biya.
*PAID BOOK 800*
Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin✍️
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔
_*KURMAN ƘADDARA*_
_©®Faiza Almustapha Murai_
_FA'EEH BG✍️_
P________2️⃣9️⃣
*BOOK ONE*
_FREE._
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*
Almajiri kuwa dake kusa da sauri ya kwaɗa sallama bayan jin kiran da Inna ni tayi masa.
Zuru haka Shatou tayi da manyan idanun ta da suke ta wani maiƙo na hawaye tana dakatar da kukan na ta tare da zuba ma Inna ni idanu ganin in da gaske zata aiwatar da ƙudurin ta,ita kuwa Inna ni ba tare da ta ƙara bi ta kan ta ba, ta ɗauke Samiran ta karɓi roban Almajirin ita da kan ta,ta juye masa shi fuskar ta haɗe.
Shatou kuwa Wani sabon babin kukan ya buɗe haka ta zauna ta cigaba da rera kukan ta dan an kyautar da Tuwon da ba lallai ma ta cisa ba Inna ni ta san da hakan amma shine take ta uban kuka haka,Inna ni kuwa har lokacin Sallah yayi bata kula ta ba dan ta lura yan taɓarar sun ƙara motsawa.
Da maburkaki ta kora ta wajen Sallah ai ko tana gama sallahn ta ɗaura daga inda ta tsaya ta zauna inda ta tashi ta cigaba da kukan na ta abun dariya.A haka su Baffa na suka same ta shida Bibu Sai rusar kuka take yi kamar wadda aka yiwa mutuwa.
" Wa ya ta ɓa mini Shatouwa ta matar ɗan birni " ?
Baffa na ya tambaya saboda yanzu firar ce suke yi da Bibu yana sanar masa ta ce bata son Iro ita matar ɗan birni ce dan haka bata ma son ko ganin Iro wai ya zo da sunan ko ganin ta ne shi ya sa take ta guje gujen ta cike da ƙuruciya.
Hawayen da suka ƙara silalo mata ta share kafin ta kalli Inna ni tana ɓata fuska sannan a hankali cikin shesshekar kuka tace " Ba Inna ni ba ce ta bawa Almajiri Abincin da ka rage mini,shine nace ina jin yunwa na fara ci ta bawa Almajiri ".
Ɗan murmushi Baffa na yayi kafin yace
"A'ie baki kyauta mini ba,yar amanar tawa zaki yiwa haka ko Tausayin mu ba,a ji "
Ya kai ƙarshen zancen yana share mata wasu hawayen da suka silalo mata.
Inna ni dai bata ce musu komai ba sai ma yar madafar ta su da ta shige tana cigaba da aikin ta fuskar ta a sake dan kamar murmushi ke son fita sai dai ta ƙi bashi dama saboda shirmen na shatou a bun dariya ne.
" Share ta kin ji nama gasasshe ma yau zaki ci dan kamar mun sani muka tsaya muka gasa abun farautar mu tun a chan ungo gashi ".
Wata leda ya Fiddo da ita daga jakar da kayan na farautar su ke ciki da Bibu ya miƙo masa.Wata irin gaashi ce Baffa na suka yi dan dama har gashi suna yi idan sun je chan yunwa ta riƙe su sosai sai su gasa rabin abunda suka samu,yau ma hakan ne dan gashi suka yi na musamman akan abun farautar ta su, tsarkakakken nama ne kamar na kaji kamar kuma na tsuntsaye an banƙare su sun ji gashi mai tsafta sai tashin ƙamshi yake yi.
Take bakin Shatou ya fara motsi jin ƙamshi ya bugi hancin ta tun kafin a ciro shi daga ledar ita sai yanzu ma ta fahimci ta ji ƙamshin tun shigowar su rigimar ta ta hana ta ta tabbatar.
Guda ɗaya Baffa na ya ajiye mata akan wani ɗan madaidaicin filet da Bibu ya ɗauko yana murmushi ganin yadda hawayen Shatou suka ƙafe ƙaff.
Miƙa mata yayi yana furta " Yi Bismillah kici ki ƙoshi wannan duka na ki ne ".
Wani ya Fiddo da ban sannan ya ce " Bibu wannan na Innar ku ne ".
Miƙa ma Inna ni naman yayi cike da fara'a karɓa ta yi tana furta " Angode " dai dai lokacin ta fito daga yar madafar ta su kamar dai ta rumfar kara haka da aka ɗan shinge.
" Inna ni dan Allah mu ji naki ko yayi daɗin nawa "
Mara zuciya ya ji haushi Inna ni ta furta acikin zuciyar ta tana murmushi.
A fili kuwa cewa ta yi " Zo gashi kwaɗayatu "
Cike da jin daɗi kuwa shatou ta matsa ta miƙa ma Inna ni nata zata saka mata baki.Ɗan kallon ta Inna ni ta yi kafin ta ɗauke kan ta ta ce " ɗibi na wan kawai tunda naki baya isar ki "
'' Nidai sai kin ci nawa sannan ki ji yadda gashin sa yake nawa gashin ya fi daɗi "
Babu musu kuwa Inna ni ta yago kaɗan tana neman kaiwa bakin ta.
Karaff Baffa na da ya fito yan zu daga ɗakin sa bayan shigar sa yace " A'ee kar ki janyo ma kan ki rigima ƙyale ta naman ta na farar tantabara ne "
" Naki kuma na ɓaƙa ne,barta ta ci ".
Cike da tsoro kuwa Inna ni ta mayar maa Shatou da shi a cikin filet ɗin tana zuba masa idanu kamar ta ga abun tsoro.
Baffa na kuwa bai ƙara cewa komai ba ya faɗa wajen wanka da ruwan da ya ɗiba yanzu.Ba tare da ya wahalar da Inna ni ba dan wasu ayyukan yana yin abun sa ne ba tare da damuwa ba dan haka ita har ta saba.
Shatou kuwa kallon Inna ni tayi ganin yadda ta tsira ma naman ta Idanu hakan ya sa '' Ta ce Bafa duka zan cinye yanzu ba zan ajiye wa su Amina ne "
Numfashi Inna ni ta sauke kafin ta fara tsakurar nata naman da ya ji gashi mai kyau dan har da kayan gashin akwai a cikin sa ba Zallar naman ba ne.
Bibu ma ɗakin sa ya shige ya canza kayan jikin sa kafin ya fito yana bawa shatou labarin yadda suka yi farautar yau dan harda gasa suka yi da wasu yan farautar kuma su suka yi nasara tana ta murna tana cin naman ta sai da ta ga ta ci rabi sannan ta ce " wannan na su Amina ne, Ramata Jawairiyya "
Haka ta raba naman a ledar kowannen da gefen sa ana yi ana suɗar hannu.
Inna ni ma ta tsakuri nata jin cikin ta ya ƙoshi ma hakan ya sa abin cin da take neman zubo musu ta ke neman samun murfin samira ta rufe sa saboda tunda suka yo gashin nan ta san sun ƙoshi dan haka babu buƙatar tambaya,amma saboda tantance wa ta ce " Habibu na na zubo maka abincin ".
Cikin sa ya shafa yana cewa " Wallahi ji nake kamar ma zanyi Amai Inna ni a dai bar shi sai anjima ".
Kai ta jinjina.
Baffa na da ya fito kuwa shima ta tambaye sa lokacin yana alwallah kai tsaye ya ce " Wallahi Mun ƙoshi sai dai anjima "
" Ai dama ɗana ya ce kun taƙe cikin ku,na dai tambaya ne kawai "
Murmushi Baffa na yayi kafin ya ajiye butar da ya gama alwallah da ita a mazaunin ta.
" Assalamu alaikum Wai ance ana Sallama da shatou "
Wani yaro ne ya shigo yana zancen bayan yin Sallama wadda ko amsa masa ba ayi ba ya jero kalamin.
" Inji uban wa "?
Shatou ta tambaya cike da Hasala dan ko ba,a faɗa ba ta san nataccen ta ne.
" Wai inji masoyin ta Iro ".
Yaron ya bada amsa kamar yadda aka umurce sa.
Wani irin ƙololon baƙin ciki ta haɗiye kafin cike da masifa ta ce " tafi kace masa ba zan zo ba nama nake ci,kuma wallahi ko ya fi ɗan ƙuje kwaɗayi ba zan sammi shi ba ".
Bibu kuwa mi zai yi idan ba dariya ba yana kallon ledar naman na ta da ta kusa cinye rabin da ta ajiye wa su Amina dama bai ji a jikin sa zasu samu ragin ba dan adda shatou akwai son nama bare kuma ba irin Tattabara mai irin girman nan ce sosai ba,ta ta wadda aka san zata iya cinye wa aka haɗa ta da ita.
Inna ni ma dake saka marafe ga samirun abincin kuwa murmushi kawai ta ke yi ta re da girgiza kan ta abun haushi abun dariya.
Azo hira wajen ka kana cewa saurayi nama kake ci kuma ba zaka samma shi ba,ai ko bata faɗa ba ya san bata Rabo da cin nama tunda yar mafaraucin daji ce.Dariya ta yi ta gefen baki tana ƙara auna kalaman na shatou da take kallon su da shir me tsantsa.
Baffa na dai tun fara zancen yaron ya samu kan sa da yin tsaye waje ɗaya ƙirjin sa na bugawa duk lokacin da za,a ce ana yiwa shatou Sallama wani irin abu mai kama da nauyi ne ke ɗaure masa jijiyoyin jikin sa su kan hana sa sarrafa harshen sa da gangar jikin na seconni.
Sai dai duk da yanayin da yake ciki kalaman SHATOU sun mugun bashi dariya matuƙa.
Dan haka ya murmusa kaɗan yana cewa " ai ko baki faɗa ba shatou na ya san Gidan nama kike ".
Baki ta tura kafin ta ce " Bibu ta shi ka raka ni wajen mai gari,yasin Inna ni kar ki hana ni,ai shi Baffa na ba zai ce komai ba tunda ya san bana son sa ".
Miƙewa tayi da sauri ta shige ɗan ɗakin ta bata daɗe ba ta fito da wani ɗan guntulallen hijab na ta da aka yi mata kusan shekara biyu da suka wuce,tana mugun son hijab ɗin dan haka ba kullum ake saka shi ba gashi har ya gundule mata kuma ta ƙi bari a bada shi wa wasu.
Baki Sake Inna ni da ta fito daga ɗakin ta take kallon ta.Ita kuwa shatou hannun ta ta ke wankewa cike da alamar da ke nuna sauri take yi Dagaske wajen mai garin zata je.
Baffa na ta kalla kafin ta ce " Baffan su kana kallon wannan shirmen ba zaka dakatar da ita ba " .
Numfashi Baffa na ya sauke kafin ya saki ɗan guntun murmushi yana kallon Shatou da ta laƙƙama kafadar Bibu da yake ɗan waigowa yana kallon Inna ni yaga yanayin fuskar ta dan ya zille ma rakiyar.Sai dai Inna ni, sake fuskar ta, ta samu kan ta da yi jin Baffa na ya ce " Karatu ya dace da shatou ba Aure ba yanzu,kuma yafi dacewa ne a lokacin da gari yayi haske duhu ya yaye raunin zukata ya sauka ".
Wayen nan kalamai na Baffa na da Inna ni ta fahimce su sarai hakan ya sa ta sakin fuskar ta wani irin raunin ta na bayyana a fili wanda take ta ƙokarin ɓoyewa a koda yaushe.
Baffa na ya lura da yanayin da ta shiga sai dai bai bi ta kan ta ba sai ma ficewa da yayi ya bi bayan Su shatou sai dai shi masallaci zai je saboda an fara kiran Sallah Asr dan gabatar da sallah akan lokacin ta, da zummar idan ya fito ya bi bayan su Shatou dan shi a gare sa zuwan case ɗin chan mai sauƙi ne dan haka ya ƙi hana shatou ɗin ta fiya.
A ɓangaren su shatou kuwa Yaron na fita suka bi bayan sa ita da Bibun anan suka tarar da iro ya ɗauko wanka irin wanda ya ɗauko ranar da Mahaj ya ziyar ce su.
Ya banbaɗa humra ta mata sai wani buɗawa yake yi.
Ai ko kallo ɗaya shatou tayi masa ta watsar tayi gaba dan haka fahimtar inda zata je hakan ya sa cike da alfahari da wani irin farin ciki dan tana kwana gidan sauƙi ya bi bayan su.
Dan haka koda Baffa na ya fito ya hango bayan su ne sai shi Iro da ke bayan su yana ta buga ƙwanbo.
" Haba Captain Wai har zaku bar nan ɗin gashi ko ziyara ban samu na kawo maka ba ".
Ta ɗayan ɓangaren ake zancen.
" No Yaqub kar ka damu dama wani aiki muka zo yau zan koma amma ai zamu dawo ko meeting haka,nikaina na so a ce na zo naga patient ɗin ku,amma next time zan shigo in Sha ALLAH "
" Ko yanzu wani issue ne ya taso daga Lagos ɗin ai da ba zan bar Abuja yau ba sai na ƙara ɗan huta wa dan nan ɗin nafi samun Hutu Sosai ".
" Ok captain Allah ya taimaka A dinga zumunci yanzu fa ban gan ka ba da ban ma sanin ka shigo Abuja ".
Ɗan shafa kan shi yayi yana gyara zaman belt ɗin sa da hannun sa ɗaya dake ta walƙiya yace " Haba Yaqub Ai wannnan duka laifin mu ne,Allah dai ya bamu ikon gyarawa ".
Dariya yaqub yayi ta chan ɓangaren kafin ya ce " waton dai ba zaka yarda laifin ka ne ba " ?
Dariya shima yayi mai ɗan faɗi ya ce " Haba na isa,ai Indai gardama ce an bar maka Yaqub dan haka na yarda,dama ko school su Samir ne masu riƙa maka "
Dariya Yaqub ya kece da ita yana tuna rayuwar su a Thailand ɗin mai cike da tarihi sai dai basu watsar da taren ba ta su ba har yanzu dan nisan da ke tsakanin ne kawai amma suna communication ko shi ba sosai ba saboda commitment da yayi wa kowa ya wa.
" Allah ya tsare Captain na gode sai mun yi magana ".
" Amin thanks you "
Kafin suka yi Sallama wayar ya ajiye.Yana sauke ajiyar zuciya.
Wata ƙatuwar jakar sa ya ɗaura a bayan sa yanayin ta sojoji kafin ya kwaso duk wani abu nasa na irin na'urori ya zuba a cikin wata yar ƙaramar jaka itama.Sannan ya kashe hasken Bedroom ɗin ya fice daga ɗakin yana rufo shi.
A dai dai ƙofar bedroom ɗin ya samu AB na jiran sa wanda shima yake sanye da na sa uniform ɗin cike da girmamawa haka ya sara masa tare da ƙokarin karɓan jakar sa da take goye a bayan sa.
" Nop "
Kawai ya furta tare da Katar da Ab ɗin gefe kuwa ya koma ya bashi hanya ya shige gaba kafin ya bi bayan sa.
Haɗaɗɗun motocin da ke a wajen suka shiga sai dai mota uku kawai suka yi dan su biyar ne suka zo kawai yin meeting ɗin da minister of defence akan wani case da ya shafi tsaron Nigeria.Kasancewar Train suka yi booking saboda shine available hakan ya sa babu wata drivern ya kai su Train station ɗin ba,a jima ba kuwa jirgin ya tashi.
Koda su Sir suka dawo Daga masallaci tare suka shigo su huɗu sun saka Abba tsakiya sai jikan su a gefen Dada Samir kenan, suna ta tsokanar sa yana tsokanar su har Abba na masa jan ido ya daina rena musu iyaye.
Sai yayi dariya ya ce " Ai Abba haka kake yiwa Mamaan mu tsohuwa mai ran ƙarfe".
Sai Ya dungure masa kai dan Abba akwai barkwanci matuƙa shida ɗan uwan sa haka suke da son wasa.
Cike da murna Reena ta faɗa jikin Dada tana cewa " Oyoyo Dadan Ummu Uwani ".
" Wai wace Ummu ɗin ta ku yar nema " ?
Dada yayi maganar yana lakace Hancin Reena dake wasar haƙora.
Ummun su Umma Umman mu ce "
" Aaa ga Umman ku chan "
" Amma mata ta bata isa haihuwar irin ki ba ga dai iyayen ku nan " Ya nuna Ibrahim da suke kira Abba ƙarami.
Murmushi Abba ƙarami yayi yana karasa shigowa ciki dan baya nan bai daɗe da dawowa ba daga tafiyar kwana ɗaya da yayi,dan haka yau koda ya dawo bai samu shiga Sassan iyayen na sa ba, sai a masallaci suka haɗu da sir yana son yaga mahaifiyar su,da rigimammar kakar ta su dan haka ya fara shiga sashen Ummu Uwani ya gaida ita sannan ya yo nan.
" Abba ƙarami ina wuni " Leena ta faɗa kamar wata mai hankali ita kuwa Reena hannun sa ta maƙalkale tana dariya tana cewa " Abba Wai Ummu Uwani bata haife Ni ba ".Dariya yayi ya shafa kan ta kafin ya ce " kin ga ummun ku chan,waccan tsohuwar mara haƙora,gashi kun ƙi saka mata artificial ta samu na cin kilishi ".
" Wacchan ta chan ta mu ce "
Dariya ta yi haka kowa dariya yayi yadda Abba ƙarami ke bayanin kamar irin yana mata wani karatu ne da ake buƙatar demonstration dan fahimtar ɗalibai.
Hajjow ma murmushin ta yi tana masa daƙuwa.
Kan sa ya shafa kafin cike da girmama ya gayar da Su Sir,Dada ,Hajiya Sannan cike da girmama Ya gayar da Abba shima cikin basa girman sa na Babba.
Amsa gaisuwar Samir yayi yana hararar sa.Dariya Samir yayi yana shafa kan sa dan ya san dalilin hararar ta sa bai shiga Ya masa sannu da dawowa ba dan sashen Momcy ya sauka chan,sannan bai faɗa masa zai dawo ba.Sai dai ganin sa yayi ɗazun a masallacin Sallahn la,asar shine har yanzu bai huce ba.
Matsawa yayi kusa da Maama cike da tsokana ya ce " Yar tsohuwa mai ran ƙarfe an buga dake an barki,ni da Yaya Sai zancen Jallof ɗin ki mu ke yi "
Yanzu kam Maaama bata yi kuka ba sai wata harara da ta sakar masa tana ɗauke kan ta da tura baki gaba kamar dai yadda kuka san Leena na yi.
Dariya duka suka sanya har su Hajow haka suka cigaba da tsokanar ta Samir na karewa yana juya abun kan Su Sir Abba ƙarami na masa daƙuwa shida Abba. Lafiyayyar Dinner ɗin da Mai aikin Hajjo ta haɗa suka zauna gwanin burgewa kowa ya ci ya ƙoshi suna gamawa suka fara taɓa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 39