Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
murmushin kawai yayi. " Ke zo nan ma na huta da shirmen ki riƙa mun aikin nan ". Cewar Inna ni dake aikin Yankan ganyen Alayyahu na miyar sahur. Baki tunzure ta miƙe ta matsa ta ɗauki kabewa ta fara feɗewa sai dai Inna ni na lura da ita yan kan kabewar da ƙeta ake mata shi dan cizgar ta take yi kamar Allah ya aiko ta da wuƙa mai kaifi da aka heƙo musu ɗazu dan haka duk ta kusa zabce rabi da nufin tana ferewa ita kuwa Inna ni kai kawai take girgiza wa tana mamakin yadda za,ayi ace kamar Shatou bata son yin A zumi duk da ba laifin ta ba ne na mahaifin ta ne domin kuwa da ace ya saka mata hannu tun chan da,ai da tuni ta gwane,ta saba da juriya Amma yanzu budurwar yarinya da jinin ta da komai balagus duk wata ace a tana rakin a zumin da ko ɗaukar sa ba,a yi ba.Har take iƙirarin ba zata yi ita dai ba. Kai Inna ni ta girgiza tana sakin murmushi a cikin zuciyar ta idanu ta zaro da ƙarfi ganin yadda aka mayar mata da kubewa yar ƙarama yar cika aiki ta zabce rabi aiko babu arziki ta ce " Ta shi je kai geron dawo na furan gobu, wannan aiki dai babu niyyar yin sa Nagde " . Summ summ haka shatou ta saka hijab ɗin ta, tana turar baki tare suka fice Da Bibu sai dai ko kafin su isa ta wartsake ta saki jiki fushin ma na Inna ni ya sauka.✍️ Maganar gaskiya ba zan ɓoye muku ba Maman Abba na so na ƙwarai da gaske.🥺 Ita kawai ta damu da shiru na na kwana biyu.Ta zata ko ciwon na wa ne ya tashi lallai wannan itace soyayya ta gaskiya. Naji daɗi sosai lokacin da naji muryan ta. Ina godiya sosai uwata rubutu ya bani mutane masu daraja da ƙima a rayuwata. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana ya raya Miki zuriyar ki.I Love you uwata wallahi ina jin ta kamar mamata da ta haife ni Allah ya bar mu tare har a gidan aljanna.✨🙏❤️❤️💕 To subscribe yours contact this number 08069059746 _*KURMAN ƘADDARA*_ *_©®Faiza Almustapha Murai_* _*FA'EEH BG*✍️_ P________4️⃣ 6️⃣↔️4️⃣7️⃣ *BOOK ONE* *_FREE_* *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eehBg* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t _*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_ 💫✨💫✨💫 # Shatou/Iro # Aiyah # Mahaj # Abbu # Faiza Almustapha murai# # fa'i✍️ Suna kai geron suka kamo hanyar gida. A tare suka shigo gidan Bibu a gaba ita a baya suna dariya. Da gardamar wanda zai je ya karɓo dan Bibu ne yaɗauki geron yanzu da zasu fita. Ganin su haka ya sa Inna ni shanye murmushin ta na yar maganar da suke yi da Baffa na dan kar shatou ta samu damar ta.Ta ƙara samun damar wata magana. " Inna ni mun dawo " Cewar Bibu. Ɗan kallon sa ta yi ta saka murmushi kafin ta ce " Allah yayi muku albarka ". " Amin Inna ni ". Shatou ta amsa da ƙarfi tana sakin murmushi. Inna ni dai bata bi ta kan ta ba sai yar hararar da ta sakar mata.Kafin ta ce " Kamar fa jiya ne aka gama Ramadan Baffa na,Yau gashi cikin ikon Allah wani ya sake zuwar muna lallai lokaci babu wuya wajen Ubangiji,Allah ya nuna mana ƙarshen sa lafiya,ya yaye muna damuwowin mu ya kawo muna ƙarshen su ". Ta kai ƙarshen zancen cikin wata raunatattaciyar zuciya wani shuɗaɗɗen lokaci na dawo mata da take ta ƙoƙarin ɓoyewa kan ta. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan ƙaƙalo murmushin ya ƙe jin shatou na furta " Kuma Allah ya sa Inna ni ki haifa mini yar ƙanwa ".Ta kai ƙarshen zancen tana dariya.Haka ma Bibu. Baffa na ma ɗan numfashi ya sauke fahimtar duk inda addu'ar ta ta nufa da kuma abun da yake masa kai kawo a kullum da take ɓoyewa da yake ƙara shigar da ita damuwa. Amin ya amsa cike da tausayi. Kiran Sallah ne ya fitar da su daga gidan shida Bibu.Basu dawo daga masallaci ba sai bayan Sallahn Isha'i sannan suka dawo . Koda suka dawo Su Inna ni sun gama komai har tuwon ta tuƙe abun ta wanda ta sha fira har ta gaji dan shatou kamar an buɗe bakin ta. Sai kuma ta koma firar kayan Sallahn su da ke wajen ɗin ki da kuma irin wankan da zata yi ranar. Kafin kuma aka koma bata labarin Mahaj da ake kira Bature tana yi tana Harare Harare " Wai ni zasu yiwa turanci,nace musu turatu uwar Turai ai nima na iya"... Shiru tayi jin Inna ni na cewa " You are not serious shatou ".Kafin kuma a hankali ta ƙara furta " You are too funny ". Zuba ma Inna ni ido tayi kamar yau ta saba ganin ta kafin kuma ta buga tsalle ta ce " Inna ni turanci kika yi fa kema yau ". Wani farin ciki ne ya ƙara bayyana kan fuskar shatou ita kuwa Inna ni ɗaure fuskar ta tayi kamar ba ita tayi furucin ba kafin tace " ke ban son shashanci,ni da ko aji ban ta ɓa zama ba ina zan ji Yaren Bature ai sai ku ". Ɓata fuska shatou tayi kafin ta ce " Na fa jiki Inna ni ". " A gidan wa kika ji ni shatou ".? " Me na ce " ? " Ce wa kika yi yom no siriyes sai kika saka suna na gaba " Shatou ta yi maganar tana dariya dan ta kasa faɗa,itama ta san shirme ne ta haɗa duk da kalmar ta ɗan shiga kan ta. Dariya ce Inna ni tayi wadda ta jima bata yi ba. Kafin kuma ta ɗaure fuska ta ce cike da tausayin Shatou " Gaskiya ba ki ji dai dai ba shatou ". Ɓata fuska shatou tayi jin furucin Inna ni. Shiru tayi kamar mai nazari chan kuma sai ta ce " Haka fa kika ce to sai in Aljannun ki ne ko Inna ni ". Baki sake Inna ni ke kallon ta kafin ta ce. " Yau naga ta kaina ni matar salihin Bawa yau ni ce ake cewa mai Aljannu ". Tsuru tsuru da ido shatou tayi wadda ta san ta kwafsa,tana tsoron Inna ni ta riƙo ta,dan haka ta zuba mata ido tana sauraren Inna ni dake ƙara furta " to wai gidan wa na same su " " Ai ni ban ce fa kina da su ba,a gefen ki ƙila suke tsaye ". Ɗan ja baya Inna ni ta yi kamar irin ta ji tsoro aiko shatou ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa " Wallahi Inna ni kina da su " Ance duk mai tsoro yana da aljanu ". Inna ni ma Murmushin kawai ta yi kafin ta girgiza kan ta sannan ta ce " Lallai ko ƙila sune kan,kiyi addu'a to". Ai ko addu'ar ta fara dai dai lokacin kuma su Baffa na suka dawo nan suka zauna suna shan iska suna taɓa yar fira shatou na fara saka maganar firan su da inna ni akan turanci da ta ji ya fito bakin ta Inna ni dake lura da ita sai ta tare ta hana kuma duk wannan abun baffa na,na lura sai dai bai san me Inna ni take ƙoƙarin hana shatou faɗa ba,dole haka shatou ta haƙura,suka cigaba da wata firan har lokacin kwanciya bacci yayi kowa ya watse,kafin lokacin ma ta watsar da komai. Koda lokacin Sahur yayi shatou da ƙyar Aka samu aka tashe ta sai da tayi nak sannan ta nemi waje ta kwanta. Yadda kuka san taliya a wannan rana ta ɗai ga watan Ramadana haka Shatou tayi ta lauɗin yunwa kuma Inna ni na saka mata ido sosai ta lura shatou akwai tsoron Allah dan ta ga alamar bata sha komai ba ko cin wani a bu dan yau ma da asuba sai da ta ƙara nusar mata. Yadda kuka san yini biyu haɗe haka shatou ta ga wannan rana. Kowa ya kalli shatou sai ta bashi dariya dan haka ranar babu abinda ta tsinana wa Inna ni tun da suka dawo makaranta take sheme tana jin jiki. Salloli ma da ƙyar take iya miƙewa ta yi su Ita dai Inna ni kai kawai take gyaɗawa cike da takaicin shatou.Da mugun tausayin ta da kullum yake ɗar suwa a ran ta. Koda aka sha ruwa kasa miƙewa tayi saboda yadda ta shaƙe cikin ta tab Da ƙyar ta samu ta yi Magriba da isha'i ai ko,ko Fira yau bata yi ba bare ayi ashamm bacci ya kwashe ta yau ma da taimakon Inna ni ta kwanta,kamar jiya. A ɓangaren Ishaa kuwa tun daga ranar ta ƙara zama shiru shiru babu ko alamar lafiya ajikin ta sai dai ta zuba wa waje ɗaya ido har Suhail da take ganewa yanzu ta daina kula shi dan haka yan kwanakkin nan duk ta fara ramewa saboda kafiya bata karɓan abinci ko kaɗan bare kallon sa.Idan aka matsa mata haukan ta ya ƙara ta shi tuɓuran.Dan haka yanzu komai da dabara ake lallaɓa ta domin babu wanda a yanzu baya yar ƙwalla saboda Tausayin MA'ISHA.Taimako kuwa babu wanda ba,a nema mata wanda ake mata amfani da shi cikin dabara... A ɓangaren MAHAJ kuwa sun koma China kasancewar chan yake a zumi dama mafi yawan lokutta saboda karatun sa. Sai dai ya kan dawo duk bayan ɗan lokaci kafin fitar Ramadana wasu lokuttan kuma ya na yin sa gida. A kwana tashi ba wuya wajen Ubangiji Ramadana ya zo ƙarshe, su shatou an karɓo ɗin ki sai murna ake yi. " Inna ni wallahi kayan nan sun mugun yin kyau ba zaki gane ni ba ranar Sallah ". Murmushi Inna ni kawai tayi tana girgiza mata kai. Tana furta " da wannan ƙashin na ki na wuya sai kace wadda tayi a zumi talatin ciff ". Dariya shatou tayi tana taɓa wuyan ta ta ce " ai ana gama azumi zan cika sa ". " Allah ya sa " Inna ni ta furta tana Murmushi. Bibu ma murna yake ta yi yana gwada kayan na sa kala biyu...Kamar na shatou da hijab ɗaya. Cikin ikon Allah an ga wata yau gobe ake hawan idi ta kowa ne bangare murna ake yi da yi wa juna Barka da Sallah. Mahaj ma gida yayi Sallah sai dai tun da aka dawo Idi ya shigewar sa duk yadda Abbu ya so ya fito ya ƙi fitowa. A ɓangaren masu aiki kuma sun kammala gyara sabon ɓangaren makarantar su shatou a bun ka ga harkar Naira,sannan an samar musu da hanyoyin ruwa masu kyau da tsafta bisa ga inda suke zuwa ɗebo ruwan su. Dan haka Abbu ya saka ranar ƙaddamar da aikin dan fara amfani da shi sallah da sati biyu. A cikin wannan lokaci na bukukuwan Sallah shatou an sha tangaririya ita da su Amina da su Ramata da Bibu dan duk inda za,a je da shi ake zuwa. Kowaccen su ta sha ado ta labta jan baki a baki da ja gira babu ma kamar su Ramata da Jawairiyya. Sai dai A wannan karon itama shatou ta sha Jan bakin ta da Ja gira ta yi kyau a irin kwalliyar ƙauye Inna ni dai in ta kalle ta sai dai tayi murmushi kawai ta girgiza kan ta,da ta so hana ta yi sai ta ga rashin amfanin hakan dan haka ta bar ta ta kashe fuskar ta sai gashi ta ɗan mata kyau,dan kafin su fita Tv ta mayar da ita har sai da Shatou ta kai ga cewa " Inna ni nayi kyau ko" ?.Kai Inna ni kawai ta gyaɗa kafin ta ce " Sosai kuwa kamar amaryar kauye ". ".a'a nikam Amaryar Birni ce ba zan yi aure a ƙauyen nan ba ni da ma zan zama yar sanda Aure na ba yanzu ba ". Inna ni dai a yanzu ma Murmushin tayi kafin ta ce " Allah ya ce " Har suka fice tana kallon Shatou tana Murmushi kafin hawaye kuma ya wanke mata fuska,daga nan ta shige ɗaki ta saki wani irin kuka mai ciwo da ƙunar zuciya sai da tayi mai isar ta sannan ta share hawayen ta daga nan barci ya kwashe ta kasancewar ita kaɗai ce a gidan.Sai su shatoun........ " Uban wa na kama " Muryan sa ta daki kunnen ta ba ita kaɗai ba har ta da su Amina sai da ƙirjin su ya buga jin muryan sa dan tunda aka fara a zumi ko hanya basu ƙara haɗuwa da shi ba wanda sai daga baya suke jin ya shiga birni kai rake. Tsuru shatou tayi da ido tana kallon sa. Shima haka. " Yarinyar nan sai yar shila kike zama ". Maganar sa ta ƙara ratsa Kunnuwan ta. Ya kai ƙarshen zancen yana lasar baki kamar wani maye. Hararar sa ta samu ƙarfin yi sannan ta ce " kai muje " Bibu da ke a tsorace ya riƙe hannun Shatou gamm. Kara shan gaban su yayi kallon kallo aka fara tsakanin ta da su Amina kowa na tunanin abin yi dan sun ma fita tsorata. Dariya abokan sa dake tare da shi suka sanya ganin yadda shatou ke ta zarar ido. Hararar su ta ke ta yi tana jan tsaki. Wani mai zafin nama ne ya ɗaga hannu da zummar kai ma bakin ta bugu Sai dai bai samu damar yin hakan ba domin kuwa hannun sa aka kama da ƙarfi. Ba kowa bane kuwa face Iro da ya sha shaddar sa yellow sa ka wanke sai walƙiya take yi kamar an mata ruwan mai. Wani sanyi ne ya ratsa Shatou.Tana gode ma Allah. " Wallahi da ka taɓa ta sai zaman garin nan ya gagare ka ". Iro yayi zancen yana Harare Harare,Wanda ya je gidan su Shatou aka ce bata nan dan yaje gwada mata wankan san na yau dan yanzu ta ɗan fara sake masa sai dai yana ganin wulaƙanci kuma hakan ya ke shanye wa dan shi burge shi hakan ke yi saboda yana shiga birni,sai yake ganin kamar tana masa irin yadda yan matan birni ke yiwa matan su ganin sa abun da take masa yan ga ce. Hannun sa ya janye yana huci kafin ya ce " To uban ya zai sa ta mana tsaki,ita fa wannan yarinyar ji take kamar uban ta ya gina ƙauyen nan,ke ba yar kowa ba babu asali mai kyau amma ke har kin samu damar raina mana mu da ƙauyen mu,wallahi kin cin sa,a da mun Miki figar kaza, Ni da ace nine kika yiwa budurwa ta wannan bugun da tuni na jeme ki amma ko yanzu ba zan bar Shamsu yayi wannan yaƙin shi kaɗai ba ,zaki gane kuren ki ". Ya kai ƙarshen zancen yana jan mugun ƙyafci wanda ke nuna a hasale yake. " Ka kashe ta idan ka ta shi ". Iro ya furta shima cike da hasalaaa. Shatou dai ganin cacar baki ta kaure tsakanin su ne hakan ya sa ta ja hannun su Amina suka yi gaba.Tana ji yo muryan Shamsu na zagin ta da aiban ta ta,da kalmomi mara sa daɗi wayen da yarintar ta ba zata iya bata damar tantance su ba da ma,anar su. " Wallahi sai na mata mugun wulaƙancin da bazata taɓa mantawa da shi ba,ba dai kai ka ɗaure mata ba daga kai har ita sai na jefa ku a masifa,zaka san ka shiga hurumin Shamsu,Shatou sai ta zamo a bar tausayi ka rubuta ka aje ". Wayen nan sune kalmomin da suka mata wani irin tsayi a kunne da zuciya dan dakatawa tayi tana juyawa kadan ta kalli Shamsu dake maganar wanda ya ke zancen yana ƙure ta da kallo yana huci saboda yadda Iro ya tare hanyar ta sannan ya ce idan ma mutun ya cika Shege ya matsa ya taɓa ta sun san halin sa hakan ya sa kowa ya yi cirko cirko,shi ko Shamsu ya ce aka mo masa ita,Amma duk sun ƙi matsawa dan haka ran sa ya mugun ɓaci ya ƙara ƙulla masifar da ke cin zuciyar sa ta ƙiyayyar shatou da ya ɗaurawa kan sa. Haka kawai jikin shatou yayi mugun sanyi har ta ji kafafun ta sun kasa ɗaukar ta. Yawon Sallahn da ba,ayi ba kenan yau dan jikin ta ya mutu mutuss ta kasa ko tafiya da kuzari tayi sauri bare gudun da suke yi idan sun ga ji kafin su samu mafaka su huta suna dariya. Gidan su Amina suka wuce har Bibu. A chan ta ɗan wartsake har ta saki maganganun Shamsu suka cigaba da wasannin su na ɗiyar kara.Sai kusan Magriba suka yi gida ita Bibu kuma ta ce Bibu kar ya faɗi komai game da abun da ya faru yau,ɗan kallon ta kawai yayi bai ce komai ba dan duk da shima ba wani girma gare sa ba ya ji kalmomin na Shamsu sun ratsa kan sa dan haka ya ƙara tsorata ta da shi,tsoron sa idan ba kashe masu shatou zai yi ba.Dan haka yake jin kamar ba zai iya shiru ba sai ya fadawa Baffa na.Sai dai tuna cewa Inna ni zata iya ji kuma sai ta daki Shatoun hakan ya sa ya ji zai iya kame bakin sa. Koda suka isa gida Baffa na bai dawo ba shima daga fadar mai gari. Sun tarar da Inna ni tsakar gida tana sauraren rediyo ana zaɓen Barka da Sallah na gaishe gaishe na sallah ga yan uwa. Suna saka waƙoƙin soyayya na zamani. " Inna ni ma idan na yi Aure wata rana haka zance ina gaida Inna ta ina mata Barka da Sallah da ita Baffa na da Bibu da su Amina,Amma idan nayi Aure nesa ". Murmushi Inna ni tayi kafin ta ce " Ohh amaryar Iro ko kin manta an gama zancen ne ko dan kin ji nayi shiru ne ai magana ta kan kama tuni baffan ku har ya fara zancen kuɗin Aure zai karɓo jibi tunda ke kika bada dama a nemo Miki ". Idanu Shatou ta ƙwalalo ta ce " Dagaske Inna ni " ?Tayi maganar tana dariya. Baki sake Inna ni ta Kalle ta kafin ta ce " Dagaske dai kina son yaron nan ".? " Allah ya raba ni nikamm wallahi sai ɗan birni ". Kai Inna ni kawai ta girgiza tana ɓoye dariyar ta. Ganin yadda ta haɗe rai. " To ai na ga ko ɗazu angon naki ya zo neman ki " " Eh ai kawai gaisawa muke yi Ni bana son sa ina da miji na ɗan birni ". " Dagaske wane ne wannan mai sa,a ". Baki washe shatou tace " ban san shi ba amma dai ɗan birni ne,kuma zai zo nan ya kwashe mu tare da ke da Bibu da Baffa na,kin san Inna ni na taɓa mafarkin na je birni,ƙila ma shi zai zo ya kai ni makarantar yan sanda ". "Hmmm to Allah ya bada mai albarka " Cewar Inna ni idanun na ja sauya wa daga farin madarar su izuwa duhun damuwa da ya fara lulluɓe su. " To me ya sa ki ka bar ɗan mutane a tsaye oh ni Indo ". " Ai shi ne naga yana mun amfani shi ya sa,amma Ni kam bana son sa wanda ko bakin sa baya wanke wa,duk wari yake yi sauƙin ta ma shima yana saka dan turare ko kaɗan ne,Kai saka turare sai Batu.." Shiru tayi ta ƙi kai ƙarshen maganar sai kuma ta ja guntun tsaki ta ce " Maye " A bayyane. " Waye maye kuma " ? Cewar Inna ni. " Da wannan Baturen nake wallahi Inna ni ba a daɗe ba na gan sa a mafarki na kusan sau uku wai yana riƙo hannu na na zo mu tafi ". Cewar shatou. " To fa ku je ina " ? Inna ni ta tambaya. " Waya sanar masa,ai ni da zan ƙara ganin sa da nace masa wallahi yayi wa aljanin sa magana duk na ƙara ganin sa sai na ƙona su,har dashi,dan na san Aljannun sa ne ƙila ".Tayi maganar da iyakar gaskiyar ta. Inna ni dake sauraren ta murmushi kawai ta yi. " A,a shatou mutanen birni kike ƙokarin faɗa da su ki rufa mini asiri ki bar natsuwar da nake da ita yanzu ta zauna kar ki fara kin ji ki bar ni da sauran farin ciki na". Shatou dai sauraren ta kawai tayi ba tare da ta fahimci komai ba na inda zancen Inna ni ya kaɓa. Shiko Bibu sai dariya yake yi yana kallon Shatou dake maganar cike da ƙuruciya yana tunanin taya za,ayi ta iya faɗa da aljani bayan ga Shamsu ma ba ta iya karawa da shi duk yadda take cika baki idan ta gan sa zata masa rashin mutun ci. Inna ni dai bakin ta kawai take kallo tana dariya. Dan labarin yadda ta tare musu hanya ta basu kafin kuma koma bada labarin yadda Mopol ɗin nan yake tafiya da yadda Ogan su yake wani shan ƙamshi harda kwaikwayon tafiyar sa. Daga ƙarshe dai bayan Inna ni ta gama shan dariya ta mata nasiha da kulawa da barin raina manyan ta.Tana bin ta da addu'ar shiriya. Sannan ta ce ta cigaba da Addu'a rashin Addu'a ne ka saka ta yawan wannan mafarkin. Salloli da aka fara ne ya tayar da su daga firan da suke yi ta bikin sallah da suke bawa Inna ni yadda wasu suka yi kyau wasu basu yi ba,wasu ma basu samu ɗin kin ba take ce musu su gode wa Allah. Masallaci Bibu ya wuce. Tare suka dawo da Baffa na aka sha fira kafin kowa ya wuce makwancin sa. Sai dai fa shatou maganganun Shamsu sun sako ta gaba ji take kamar yanzu yake nana ta su,sai kuma maganar Auren ta da Iro da Inna ni tace mata wasa take yi mata ko maganar bata yi da Baffa na ba ganin ta matsa mata da tambayar bayan sun gama sallah wai dagske take yi.,Bacci ɓarawon ne ya kwashi shatou a yau bayan ta gama Addu'a.Dan musamman maganganun Shamsu sun mata tasiri ƙwarai da gaske.. Yau Sallah kwanan ta goma sha biyu ciff inda ya kasance saura kwana biyu Abbu su shigo wajen ƙaddamar da ayyukan da aka kammala. Shatou ce zaune ta buga ta gumi idanun ta sun zubawa waje ɗaya ido kamar hankalin ta baya jikin ta. Inna ni ce ta fito tana cewa " wai baki wuce wajen Sallahn ba har na gama na fito " Ganin shatou bata ma nuna ta san da ita take ba hakan ya sa ta ƙare mata kallon ƙwass ga wani irin tsoro na kama ta domin kuwa ta lura da shatou cikin yan kwanakkin nan tana yawan yin shiru ko ta makure gefe ta zubawa waje ɗaya ido ga shi ta ƙara yin wata irin rama kamar mai ciwon yunwaaaa... Ajiyar zuciya Inna ni ta sauke kafin ta matsa kusa da ita ta dafa ta ta kira sunan ta. "SHATOU"! Ai ko da sauri shatou ta kalli gefen irin a tsorace take babu zaton nan.zuba mata ido Inna ni ta ƙara yi kafin ta ce " Me ya ke damun ki wai,ke ba Damuwar komai ba amma ki zauna ki yi mini shiru ga ramar da kike ta yi,me yake damun ki ". Kuka ta fashewa Inna ni dashi wanda ke fitowa har ƙasan zuciyar ta sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi shiru Inna ni bata samu damar rarrashin ta ba domin mamaki abun ya bata da tsoro dan tsoron ta kar ace wani abu ya faru da shatou bata sani ba duk yadda take saka ido akan ta. " Me yake faruwa wai ko sai na ƙara saka ki kukan yin kukan mai dalili ". Ajiyar zuciya shatou ta sauke kafin ta ce. " Inna ni ji nake kamar zan mutu kowane irin lokaci,sannan ƙirji na ke bugawa da ƙarfi kullum, taɓa ki ji fa,Ni na san tafiya zan yi na bar ku,ban ga kin haifa mini yar ƙanwa ba ".Ta kai ƙarshen zancen ta na ƙara fashewa da wani irin kukan da ya fi na ɗazu. Ita kuwa Inna ni wani irin rintse idanun ta tayi jin yadda zuciyar shatou ke mugun bugawa da kuma kalmomin ta da suka jefa ta cikin wani irin yanayi na tsoro da firgici duk yadda ta so ta hana hawayen ta zuba a wannan karon gaban shatou sai da suka silalo suka sauka akan kafaɗar shatou da ƙirjin ta yake cigaba da mugun bugu mai hana jiki da ruhi zaman lafiya. Chak ta tsayar da kukan na ta kafin ta ce " Inna ni kin ji ko " " Dan Allah ki mini Addu'a Allah ya sa ba mutuwa zanyi ba,bana son na mutu yanzu na Barki ". Wasu hawaye ne ke ƙoƙarin ƙara sauka akan fuskar Inna ni indata haɗiye su, Shatou kuwa jin hawayen Inna ni jikin ta sai ya ƙara karya mata zuciya sai take ganin kamar Dagaske mutuwan zata yi itama Inna

Chapter 36 of 39