fili dan har muby sai da ya ɗan kalle sa ta cikin madubi sai dai idanun sa rufe ya same su.
A ɓangaren shatou kuwa tafiyar ta ta chanza salo sillo sillo kamar wata hawainiya dalilin hakan ne ya san ya Mahaj jan tsaki saboda akan idanun sa ne ta fara iya Shegen na ta kamar ta san cewa sune a cikin motar sai dai ta zargi cewa ta gane cewa sune dan haka ya kashe motar ya fito dan rarrashin ta, ta lala ma ko zata janye.
Koda Muby ya fita ta ƙasan ido Mahaj ya bi shi da kallo wanda ya ƙara tsumewa a kan seat kamar mai bacci.
" Shatou "!
Muby ya ambata yana sakin murmushi yana ɗan Gyara tsayuwar sa daga bayan ta .
Ɗan juyowa tayi a hankali ta sauke duban ta kan sa a kallo ɗaya ta gane shi dan haka ta ƙara tsuke fuskar ta.Ta ƙara haɗe rai.
Ɗan kallon motocin tayi na kusan daƙiƙa ɗaya kafin ta mere baki ta juya ta cigaba da tafiyar ta tana gunguni da jan tsaki a cikin ran ta,da mamakin yadda aka yi wannan mutumen ya san sunan ta.
Murmushi Muby yayi ya ƙara ɗaga ƙafa ya bi bayan ta.
Bibu dake gefe matsowa yayi yana furta " Adda SHATOU dan Allah ki janye kar su taka ki mutanen birni ne ".
Ya kai ƙarshen zancen yana riƙo hannun ta,fisge hannun ta yi ta ɗan harari Bibu.
Kafin ta ce a hasale " Nifa ba zan janye ba tunda ƙauyen mu ne kuma ba nan ne kaɗai hanya ba ai da za,a takura Ni sai na matsa na bada hanya ".
Ɓata fuska Bibu yayi da jin furucin ta ita kuwa ko a jikin ta duk da ta lura da Muby dake ta sakin murmushi daga gefen ta amma taƙi bari su haɗa ido.
" Dan Allah ki bamu hanya mu wuce Shatou"
Muby ya faɗa kamar wani wanda yake magana da wata Babbar mace yarinyar da bata wuce ya ɗauke ta ya jefar gefe ba.
Wani ne daga cikin masu tsaron sa ya sauko daga motaa yana zare ido kasancewar sune baya sai an fita wajen garin sai kowannen su ya koma mazaunin sa shida yake tsakiya ya koma tsakiyan dan haka suka biyo hanya shigowar su nan ne ya suka sauka wannan tsarin ko shi saboda yace suje hakan.
Sheƙeƙe Shatou ke kallon basamuden mutumin wanda ko kaɗan bata manta fuskar shi ba shine wanda ya tashi zane ta a haɗuwar su ta farko aiko cike da rashin tsoro jin yana furta wa da turanci " Sir let us deal with her "
" Babu uban da ya isa ya saka na bar hanyar nan Ni da ƙauyen mu " Ta kai ƙarshen zancen tana Hararar sa duk da bata san abinda ya ce ba amma jin her ta san cewa da ita yake.
Aiko basamuden nan bai jira ta kai cike da jin Haushin ta ganin ƙaramar yarinya na raina musu hankali domin shima bai manta abun da ya faru a wancan lokacin.
Hannun sa ya sanya yana ƙoƙarin ɗaga ta sama ya ajiye gefe sai dai chik haka ya ji an ruƙe hannun na sa kafin ƙamshin turaren sa ya bayyanar da wanzuwar sa wajen sai kuma Muryan sa mai sanyi da amo da ya furta " Don't touch her " Cikin kakkausar muryan da sai da Muby ya zuba masa ido haka yaron na sa ma.
" Sir yarinyar ta cika zama stubborn ".
Ya faɗa yana ƙara zare idanun Sa.Wani kallo Mahaj ya jefa masa dan haka ya yi shiru daga wani sabon furucin da yake ƙokarin yi dan ji yake kamar ya kamo Shatou ya karya yarinyar da ya isa haihuwar ta sai rashin kunya take zuba wa an kasa yi mata komai.
Ƙasa haƙuri yayi ganin yadda take hararar sa ya ƙara miƙa hannun sa zai kamo nata tsintsiyar hannun sai dai hannun na sa bai kai ba ya tsinkayo Muryan sa na furta " This is a last warning akan haka " Yayi maganar da wata irin murya da basu san sa da ita ba a karo na biyu sannan gashi da ƙarfi yayi zancen wanda ke nuna ɗan Abbu ya fara Hasala dan shi mutun ne da yake tsanar duk wata musgunawar da za,a yiwa mace muddin gabansa ne ba zai bari ba.
Gefe wannan mopol ɗin ya koma yana jin mugun ɓacin rai na dabaibaye sa.
Jin Mahaj ɗin na furta masa a natse a wannan karon duk da duk maganar da yake anatse yake yin ta." she's a still a young girl so don't let your anger hurt her ".
Muby dai bin su kawai yake yi da ido kamar ya samu tv yana nazartar duk wani motsin Mahaj ɗin da shatou dake ta Harare Harare har ta mai kare ta ɗin bata bari ba.
Abun na ta abun dariya har da riƙe ƙugu kamar mai shirin dambe.
Yo kodai da ƙaton mopol ɗin nan zata yi U bar ta dashi 😅🤭
*Bibu dai sai kallon mahaj yake yi yana mamakin me wannan baturen kyakkyawa ya zo yi a ƙauyen su.Gashi yana kare Addan su da fitinar ta domin ya san wancan mopol ɗin ko karya ta yana iya yi in aka barshi da ita.
Ɗan satar kallon ta yayi ta ƙasan ido daga cikin glass ɗin sa da ya manna kafin fitowar sa.
Sannan a hankali ya kalli muby ya ce " ka ce ta bada hanya i'm so exhausted "
Kai Muby ya jinjina yana son sakin murmushi kafin ya labarta masa yadda suka yi kafin zuwan sa sai dai duk da turanci suke zancen har ya ƙara masa da " Yarinyar na da taurin kai ko zaka yi mata magana da kan ka ko zata ji nauyin ka ".
Yar guntuwar harara mahaj ya masa kafin ya sauke numfashi karo na farko ya sanya idanun sa cikin na ta ya mata kallo na kusan minti ɗaya sai dai ba zaka ce ita ɗin yake kallo ba a cikin space ɗin na sa idanun sa ya sauke daga kan ta yana yatsine fuskar sa kafin ya furta a hankali " Ki bamu hanya mu wuce ko na saka wanchan ya ɗauke ki daga nan "
Ya yi zancen a natse kamar bada ita yake ba.Yana sauke numfashi na yar doguwar maganar da yayi.
Sheƙeƙe ta kalle sa ta kafe idanun ta tar akan glass ɗin sa da idanun ta wan da take jin kamar yana bin ta da kallo ta cikin sa ne, kafin kuma ta jaa guntun tsaki wanda ya sauka kunnen sa sak sai dai ko alamar hakan bai nuna ba duk da sai da ya ga Zallar ƙarfin halin yarinyar da har yanzu bai riƙe sunan ta ba.
" Ba zan janye ba,turatu uban turai masu tura ma turai,turanci,shine sai da ka gama zage ni nida ƙane na sannan zaka ce mu sauka daga hanya,nida ƙauyen mu dan haka ba zan janye ba a soye ni, kuma bana jin tsoron sa ko wanda ya fisa ka fito zan iya karawa dashi na tumurmushe sa "
Idanun sa ya lumshe a hankali jin yadda yar ƙaramar Muryan ta ke ratsa kwantaresa chau chau da ita ga ta chan ƙasa sai rigima duk da yaga ta ɗan chanza kaɗan.
Ajiyar zuciya ya sauke na gajiya da tsayuwar kafin ya furta a hankali cikin sanyin murya " Haka kika ce,yar ƙauyen ƙayau " ?
Kai ta gyaɗa masa tana cigaba da Hararar sa na kiran ƙauyen su da ƙauyen ƙayau wanda bashi da komai dan haka ta fassara shi.
Muby kuwa murmushi yake ta saki yana dariya cikin zuciyar sa wadda bashi da ikon fitar da ita.
Da hannu Mahaj ya ƙyafato Wannan mopol ɗin da yake ƙara cika yana batsewa ganin yadda uban gidan su yake ta rarrashin Shatou magana cikin sanyi.
" Adda shatou ki yi wa Allah ki zo muje gida ki Basu hanya kar wancan mutumen ya kashe mana ke " Bibu yayi Furucin kamar zai saki kuka ganin abinda Mahaj yake shirin yi.✍️
Masu comments da likes nuna godiya sosai.
Sai kunyi hakuri dan bacci ke cikin ido na na san za,a ga kura kurai mau be ayi haƙuri.🙏da zuwan sa late.
Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800
# _FA'EEH BG CE✍️_
*PAID BOOK 800*
Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin✍️
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔
_*KURMAN ƘADDARA*_
*_©®Faiza Almustapha Murai_*
_*FA'EEH BG*✍️_
P________4️⃣0️⃣
*BOOK ONE*
*_FREE_*
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eehBg*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Posting group link*
https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t
_*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*_
******💕
****💕
***💕
**💕
*💕
Da sauri wannan mopol ɗin ya matso yana jin sanyi a ran sa na damar da yake shirin samu ya yiwa yar ƙaramar yarinyar da bata wuce gwiuwan sa ba hankali.
MAHAJ kuwa gyara zaman rado ɗin sa yayi yana ƙara tsuke fuskar sa.
Muby ne cike da sakin fuska ganin yadda mopol ɗin nan ke ta ƙara haɗiye rai haka ma uban gidan na sa duk da ya san ba lallai ya aikata abin da ya faɗa ba.
" Haba Malama Shatou dan Allah ki matsa mu wuce mai gida na baya son rana tana saka shi zazzaɓi yanzu haka in kin lura ya mutsar fuska yake yi ki taimaka mana ba sai an kai yadda ba,a so ba kar jama'a su tarar mana nan "
Ya kai ƙarshen zancen yana haɗiye dariyar dake neman kubce masa ganin yadda take ta hurar hanci da girgiza ƙirji da Harare kamar zata zubar da idanun ta kuma duka akan sa ne kafin ta koma kan Mahaj dake tsaye hannayen sa maƙale a cikin aljihun sa.Ba zaka iya tantance ainahin yanayin da yake ciki ba sai dai fuskar nan a haɗe take dan ya gaji da lamarin shatou.A ɓangaren Bibu kuwa ganin bata saurare sa ba dan fisge hannun ta tayi tana ce masa barni ka tafiyar ka sai na ga karshen rainin hankali, hakan ya sa ya bar wajen da sauri yana haɗawa da gudu wanda da alama wani zai kira ya raba wannan rigimar.
" Wannan ne uban gidan naka,wannan ɗan Yaron ko ni fa na girme sa kawai dan bana girma ne shi ya sa yafi ni zama ƙato,kuma ma na tuna Bature ance dama haka suke girma kamar biredi hhh " ta kai ƙarshen zancen tana nuna Mahaj tare da ƙara sakin wata yar dariya ta yarinta da rainin wayau da sakarci.
Baki sake Mopol ɗin da ke jiran izini yake kallon ta haka ma Muby sai da ya ƙwalalo idanun sa yana kallon ta tare da furta anya wannan ba aljanna bace a ran sa ga dariyar dake ƙara ta so masa ji yake ina ma a ce Abbu yana kusa ya sha kallon wannan dramar ta su.
Ɗan satar kallon MAHAJ yayi da yake tsaye kamar bai san abinda ake yi ba dan ya ma juyar da kan sa gefe ya san cewa ran sa ya fara ɓaci ne sai dai yana ƙoƙarin shanye wa dan shi mutun ne mai shanye komai ba kasafai kake gane yanayin sa ba musamman ma yanzu da shatou ta zamo mace babu yadda zasu yi da ita dan shi kawai yake lallaɓa ta.
" Kai dube ka garjejen ƙato da kai kake kiran wannan abun mai gidan ka chab "
Ta yi zancen irin bani da damuwa da kuma mamaki.
Wannan karon muby murmushi ya saki wanda ya fi na ko yaushe sannan ya ce " Ba wannan ba dan Allah ki yi Haƙuri ki jaye gefe mu wuce ".
Ƙugu ta ƙara dafewa tana hararan Mahaj.
Musamman ganin yadda ya ɗan saka hannun sa akan sa ya cire p cap ɗin sa.
Sai kuma ya taka gaban ta a hankali wanda ya zamo ɗan tazarar dake tsakanin su dan kaɗan ne.
Sai da ya ɗan mula hannun sa ɗaya a aljihu.Ya ɗauki mintuna biyu tsaye gaban ta.Ita kuwa shatou baya ta ɗan ja kafin ta furta " Wallahi Ni ba yar iska bace dan haka ka matsa,ko in fasa maka kai da dutse " ta duƙa ta ɗauki dutsen.
Ƙara takawa yayi inda take dan ganin ƙarshen iskan cin na ta.
Baki ta tura gaba bayan ta zuba masa ido Ganin kammanin Abbu Mutumin kirki ƙiriƙiri a gare sa dan tun ɗazu ta ke hango su wanda sai yanzu ta ƙara ganin su bayyane saboda kusan cin da suka samu,kuma ta tabbatar lallai ya yan sa ne dan shima fatar ta su ɗaya ce sai dai a yanzu ta mahaj tafi ɗaukar ido,ɗauke idanun ta daga kan sa tare da hararar sa ganin sa gaban ta a karo na biyu kafin ta ankara wanda sai da ya ɗan razanar da ita sai dai ta haɗiye dan a cewar ta bata tsoron girman biredi,Cikin zuciyar ta,tayi zancen sai dai bata san cewa ta fito fili ba sak haka maganar ta shiga kunnen sa " Ni bana tsoron Girman biredi ".
Kafe ta yayi da idanun sa ta cikin glass ɗin sa kafin ya ja ƙaramin tsaki da ya sauka kan kunnen Shatou.Wanda ya sa ta ƙara maka hararan da tafi sauran.
" Ai watar da abun da kike shirin yi "
Haka zancen sa ya shiga kunnen ta cike da wani irin isa da kaushin dake nuna ya fara gundura da tsayuwar ta su.
" Zan jefa ka ".
Ta faɗa tana hararan sa tare da turo baki gaba.
Glass ɗin sa ya zare a hankali tare da mayar da hulan sa a kan sa yana zuba mata idanun sa wayen da ya kafe mata har tsakiyar kai yana ƙare mata kallo a fakaice.
" Zan jefe ka fa,ka matsa kafin na ƙirga goma "
Ta kai ƙarshen zancen tana rufe idanun ta.
" Ɗaya,Biyu,uku,huɗu Biyar..."
Ɗan buɗe idon ta ɗaya tayi ganin ko ya matsa sai dai yana nan tsaye kamar dutse ya zuba mata idanun na sa.
Haɗa idon da suka yi ne ya sanya ta ƙara tura bakin ta gaba tana buɗe idanun na ta gaba ɗaya, hannun ta ta ɗaga kamar zata jefa masa dutsen.
Sai kuma ta saki ɗan guntun murmushi wanda ya bayyanar da yar ƙaramar wushiryar ta, murmushin kai da gani ka san akwai Zallar ƙuruciya kan ta babu Damuwar komai a kan ta kamar ma ta mayar da komai shirmen ta.
Ɗauke kallon sa yayi daga kan ta a hankali yana lumshe idanun sa kafin ya ware su
Dai dai nan kuma Baffa na ya ƙaraso wajen wanda ke cike da tashin hankalin labarin da Bibu ya kai masa yana kuka kashirɓan ga Addan sa chan zata yi faɗa da mutanen birni zasu kashe ta.
Sai dai yana ƙarasowa wajen ganin Muby sai ya ɗan yi jimm yana kallon sa dan ya gane sa tun da tare suka zo kwanan baya da Abbu, kafin ya mayar da idanun sa kan MAHAJ dake tsaye yana kallon ƙasa kamar mai nazari.
Yan ƙafafun Shatou yake kallo yan ƙanana da su da suke da ɗan datti a cikin silifass ɗin ta,Wani murmushi ne ya nemi suɓuce masa sai dai ya hanawa kan sa hakan.
Ita kuwa shatou dutsen ta yar ƙasa bayan ɗan juyawan da tayi ta kalli Baffa na dake tsaye yana kallon MAHAJ bayan sun haɗa ido da ita.
" Ka ci sa,a Baffa na ya zo wajen nan,Sannan da kuma kaci sa,ar ya yan ka mai mutunci da kamar da kuke yi da sai na fasa maka kai gobe ba zaka ƙara raina ni ba ka zata na manta abun da ya faru ko wai har ni zaka kalla kace mini yarinya,kuma kai da ke bilicin Ni zaka cewa nake yin bilicin ai da ganin ka an san farin bilicin ko ka zata ban san yan bunni na bilicin ba ai Baffa na ya bani labari akwai masu farin mai kuma kaima shi kake shafawa ji fa fatar ka kamar ƙosan iya " Ta kai ƙarshen zancen tana ƙyaƙyata dariya.
Idan ba kuskure yayi ba ya ga alamar murmushi akan fuskar sa wanda sai idan ko lura sosai ne zaka iya fahimtar hakan.
Dan haka ya zuba ma Uban gidan na sa ɗan uwan sa ido.
Ga mamakin furucin Shatou wanda ya tabbatar ba kowa take nufi ba face Abbu shi take kira da ya yan sa.Lallai wannan yarinya Boss ce ya furta a cikin zuciyar sa yana sakin murmushi.
Numfashi ya ɗan sauke Da ke nuna gajiyar sa dake bayyane kafin ya ɗan ja baya kaɗan bayan ya samu haɗa ido da Baffa na da ya zuba masa ido yana Kallon sa kamar ya samu tv.Ga shirmen Shatou da shiga kunnen sa wanda ya ji kamar ya kame bakin ta ya hana ta yin furucin wanda har nauyi tasa ya ji bayan wanzuwar sa wajen.
Kan sa ya ɗauke daga kallon kowa kafin ya kalli wannan Mopol ɗin ya furta masa " is Okey let her be ".
Cije baki mopol ɗin nan yayi wanda kafin yanzu ya yardan wa kan sa shatou bata da lafiyan ƙwaƙwalwa daga yanayin yadda take abubuwan ta.
Dan haka sai lamarin na ta ya so ba shi dariya dan har wani kaso daga Haushin ta ya ragu ganin wanda yake yi dan sa ko ajikinnsa kamar ma yana biye mata su yi ta ƙuruciyar tun da duk kamar sune.
Mota ya koma tare da sauran da suka zagaye su jira kawai suke yi a basu dama su yi wani abu akan Shatou.
Juyawa tayi ta kalli Baffa na ta yi Murmushi tana barin wajen tana komawa gefen Baffa na ɗin.
Ajiyar zuciya MAHAJ ya sauke tare da ɗan shanye narkakkun idanun sa yana kallon Shatou da take ta ya mutsar gashin Bibu tana dariya kamar har ta manta da rigimar da ta gama Badan komai take yi masa haka ba sai dan ganin yadda yake cikin tsoro kamar zai yi wani kuka har yanzu a tsorace yake yana zaton wani abu zai same ta ne kafin su iso.
Kallo ɗaya yayi musu ya ɗauke idanun sa kan su.
Juyawa yayi a hankali ya fara tafiyar sa cikin ƙasaitar sa da natsuwa sai dai ko tako biyar bai yi ba ya juyo a hankali ya ɗan saci kallon Baffa na kafin kuma ya juya ya cigaba da tafiyar sa ko kafin ya isa bakin motar wani ya buɗe masa da sauri. Shigewa yayi suka rufe sa.Jingina bayan sa yayi da seat ɗin yana sauke Jerarrun Ajiyar zuciya tare da numfashi kan sa ne ya ɗan sara masa na gajiyar magana da tsayuwa cikin ranar da yayi.Wani madanni ya danna a hankali inda ya buɗe wata yar ƙofa sai ga drinks ɗin sa wayen da suke favorite na sa a ciki sun ɗauki sanyi mai yawa.Dan wajen kamar fridge ne.
Ɗaya ya ciro kafin ya zuba masa ido kamar mai karantar wani abu a cikin sa,Har ya fara ƙoƙarin buɗe murfin sai kuma ya dakata tuna lafiyar sa da yanzu in ciwon sa ya tashi Abbu ne mai shiga damuwa matuƙa dan haka ya ajiye shi gefe har ya sha iska,ya rage sanyi.
Jingina ya ƙara yi da seat ɗin yana ɗan kallon gefen damar sa sai kuma ya juyo a hankali ya ƙara ɗaga wani abun sai ga wannan yar kwalbar da take ɗauke da shishan sa.
Zuƙa ya fara yi a hankali yana lumshe idanun sa yana fitar da hayaƙin da wani irin style na ƙwarewa.
Idanun sa ya ɗan ɗaga ya kalli gaban motar.
A ɓangaren Muby kuwa dariya yayi wadda tun ɗazu yake riƙewa sai dai yar ƙarama kafin ya matsa wajen Baffa na ya miƙa masa hannu cike da girmamawa suka gaisa.
Baffa na haƙuri ya basa na aika aikar da shatou tayi na ɓata musu lokaci.
Ya ƙara da furta " Ƙuruciya ce ita Tata haka take sai haƙuri Shatou kuma in sha ALLAH zata daina wata rana ka bashi hakuri ".
" Babu komai Baba ai mun ga alama kamm Shatou Badai rigima ba,Zata daina in sha ai komai lokaci gare sa "
Baffa na ya ji ɗan sanyi a ransa duk da har yanzu yana jin wani iri a ransa na ganin MAHAJ ɗin da yake fuska babu annuri.
Kuɗi Muby ya zaro daga aljihun sa ya damƙa ma Baffa na sai dai yaƙi karɓa,kuma a dai dai lokacin ne Mahaj ya sauke idanun sa kan su daga cikin motar kallon su yayi na yan seconni kafin ya ɗauke idanun sa kan su yana cigaba da jan shishar sa,yana ƙara shanye idanun sa tare da kumshe su kamar mai jin bacci,duk da akwai bacci a idanun sa amma hakan Halittar Mazan take nature na sa ne.
Duk yadda Muby yayi Baffa na ƙin karɓan kuɗin yayi wanda kafin ma su lura Shatou sun yi gaba ita da Bibu da gudu suna dariya saboda tace ayi yar rigen gen kuma akan idanun Mahaj suka yanka a Guje.
" Runner girl "
Shine furucin da ya fito daga bakin sa a hankali ba tare da ya shirya wa hakan ba wanda ya fita a iya laɓɓan daga bakin wanda ba kowa zai ji ba koda yana kusa da shi ne kuwa, sai kuma ya ja tsaki na bayyane wanda ya sauka a kunnen Muby da ya riga yayi sallama da Baffa na yana ƙara jin jina ƙuruciya da rigimar Shatou yana sakin murmushi.
Zama yayi da kyau kafin ya kunna motar bayan ya saci kallon MAHAJ ɗin da har yanzu yake zuƙar hayaƙin dan har motar ta fara turneƙewa ga hayaƙi da illa ko wani yake zuƙan taba ko wani abun hayaƙi zai iya cutar kai.Dan haka ya kunna abun hurar da hayaƙin da sauri,wanda ke zuƙe sa take.
A ɓangaren MAHAJ kuwa tari ya fara kafin ya ajiye shishan yana rufe ta ya ajiye gefen sa tare da ƙara shigewa seat na motar yana sauke numfashi jin yadda awazzun sa suka fara riƙe masa.
Tafiya motocin suka yi suna barin wajen ajere gwanin burgewa.
Baffa na bai ɗaga daga wajen ba sai da ya daina ganin su sannan ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yana kama hanyar gida.
Su Shatou kuwa koda suka isa gida kowannen su na dariya da sauke numfashi kasancewar a tare suka shiga.Inna ni dake saƙar kaba ce ta ɗago ta kalle su kafin ta ce " lafiya kuka faɗo muna haka yau har da kai Bibu da nake gani mai hankali ".
Yar ƙaramar dariya yayi yana furta " Inna ni mun gaji "
" To dan kun gaji sai aka ce ku ƙi yin sallama mai ya haɗa gajiya da sallama "
" Kai ku koma kuyi Sallama ko na saɓa muku "
Baki Shatou ta tura tana sauke nishin gajiya kafin ta juya ta bi bayan Bibu.
Sallama suka yi suka shigo bayan Inna ni ta amsa musu.
" Me ya faru yanzu a bani amsa Bibu " ?
Ta ƙara tambaya kasancewar bata san komai ba domin A kan hanya ya haɗu da Baffa na ya fito daga gidan, Zashi fadar mai gari.
" Wai fa Shatou ce Inna ni ta tare wa yan birni hanya da sun ture ta sun take ta da mota da ace ban kira Baffa na ba da sun kashe mana ita,kuma har da rashin kunya ta yi ta musu har da wani ƙato ta so yin faɗa ".
Sai da ya kai ƙarshe ayar zancen sannan ya daɗe bakin sa da sauri yana zare idanu kamar wanda yayi ƙarya domin kuwa ya san halin Inna ni yanzu sai ta zane Shatou,tana dadewa bata buga ba amma duk ta Hasala sai ta buge ta take jin sanyi in ta kai ta ƙul bare ma ta sha mata faɗa akan rashin kunya wanda kuma ba kowa take yi wa ba sai wanda Allah ya jefa komar ta kan sa,ta samu waje wanda kuma ma ita bata ɗauke sa komai ba a ta ta ƙuruciyar.
Shiru Inna ni tayi ta zuba ma Shatou idanu ƙirjin ta na bugawa da wani irin sauri jin zancen mutanen birni ga maganar Bibu ta tsakiya da ta ƙara sanya ta kiɗima da yace da sun ture ta sun take ta da mota,sun kashe mana ita.
Ganin kallon da Inna ni take bin ta da shi ne daga sama har ƙasa ya sa Shatou ɗan shan jinin jikin ta.
Ta sowar Inna ni ce daga zaunen da take ta kaɗa hanjin Shatou take ido ya raina fata rashin gaskiya ya bayyana ƙara rara gare ta, ganin Inna ni na tun karo ta ne ....✍️
🙏🙏🙏🙏
Ayi manage haka pls.🙏
Wannan labari na kuɗi ne akan Naira#800
# _FA'EEH BG CE✍️_
*PAID BOOK 800*
Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Daga Alƙalamin✍️
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Like,react,share,and Comment,Vote PLS 🙏🥺💔
_*KURMAN ƘADDARA*_
*_©®Faiza Almustapha
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 39