kira kowannen su daga kakanni na sa har iyayen sa ya basu haƙuri na rashin sanar da tafiyar sa,ya sanar da su tafiyar gaggawa ce ta same su.
Sai shige da fice suke yi an chaɓa ado idan ka Kalli fuskar Ummah sai ka ƙara kallawa tayi kyau har ta gaji saboda tarbon mijin na ta dan yau sashen ta yake kafin ya yi tafiyar itace dan haka kai tsaye nan zai sauka kafin ya zagaya ya gano sauran.Ko Ina ya amsa a estate ɗin SSS zai dawo kowana cike da farin ci,sai kai komo suke yi ana ta gyare gyare dan kowane sashen suna cike da farin cikin Dawowar sa.
Su ALINA ma sun sha kyau matuƙa cikin shigar jeans da t shirt shigar ta su iri ɗaya dan duka kayan su iri ɗaya ne.Sun yi kyau sosai idan ba ka sansu ba zai yi wahala ka iya tantance ALINA ko SARINA a tsakanin su kamannin su suka ƙara bayyana masu cike da kyau da haiba da zallar Hutu da yake ƙara musu kyau da annuri.Koda kowaccen su ta ga iri ɗaya suka saka sai aka koma kallon kallo murmushi ne ya suɓuce ma Rina bayan ƙare ma yar uwar ta kallo dan ta riga ta fitowa.Ita kuma boss ɗin ɗaure fuskar ta tayi dan kar ta raina ta,dan tunda Umma tace ta riƙa sassauta mata kodan saboda tana babba ba ƙarfin su ɗaya ba..
Ummah ma murmushi ta yi tana janyo hannayen su ta zauna tare da su bakin ta washe kamar gonar Auduga.
***
" Hmmm wai kin san Hamida duk saurin nan da nake yi na gama exams na je Hutu wajen Ummah ashe ya koma gurin aiki tun daren da ya kawo ki da safe ".
Matashiyar budurwa ce ke zancen wadda a ƙalla zata kai shekaru ishirin a duniya tana zaune akan makeken gadon royal mai kyau
Murmushi Hamida dake zaune gaban fankacecen madubin da ya ƙara ƙawata ƙaton bedroom ɗin na su ta ce " Yaya Samira ke dai ba zaki raba kan ki ba ko,kin fi son Ya BILAL yana disga ki,kin san dai abun da kike yi baya so ".
Budurwar da aka Kira Yaya Samira ce ta galla ma Hamida Harara kafin ta ce "Ai Ummah na so dan bata taɓa ce mini komai duk da ta lura da abun da nake yi dan haka babu ruwan ki,idan kika matsa mini kuma yanzu na sassaɓa ki kina haɗa ki da Ummu " ta kai ƙarshen zancen tana jan mugun tsaki.
" ai da na sani da ban faɗa Miki ba,kuma ma gashi ya koma sai kije ki ƙara "...
Hamida ke zancen ƙasa ƙasa.
" Me kike faɗa "
Cewar Samira.
Baki Hamida ta turo gaba bata tanka ma Samira ba.
Ƙara jan dogon tsaki Samira tayi tana saka earpiece a kunnen ta.
***
" Amoh ta ƙi karɓan abincin ta nayi nayi ta ƙi karɓa har Sagir ya shiga ya bata ɗazu ta ƙi karɓa,gashi Nurse ɗin ta bata zo ba ".
Shiru Babbar matar da aka kira Amoh tayi wadda ke zaune cikin ado na alfarma daga nin ta ka san akwai dukiya a jikin ta,Numfashi ta sauke sannan ta furta " Suhaila kodai kiran Suhail ɗin zamu yi duk da na san akwai ayyuka gaban sa,yau suna ganawa da patient ".
" Bari na gwada idan bata karɓa ba sai musan abunyi dan yunwa zata iya yi mata illa,gwara ya bata ko zata karɓa ".
Kai matashiyar budurwar da aka kira Suhaila ta girgiza fuskar ta cike da damuwa.
Tare suka kama hanyar wani lungu sai gasu tsaye ƙofar wani ɗaki mai duhu ko ina lif lif babu hayaniya.
Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Sai monday idan Allah ya kai mu.
Ina alfahari da ku masoyan wannan labari 🥰💋
Comment and like pls 🙏
_*💋KURMAN ƘADDARA💋*_
_©®Faiza Almustapha Murai_
_FA'EEH BG✍️_
P..1️⃣8️⃣
*BOOK ONE*
PAID
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*
🌙🌙🌙
Zaune take ta takure waje ɗaya jin hasken da ya gauraye ganin ta ya sa ta zabura da ƙarfi tana neman hanyar gudu.Saboda bata son haske ko kaɗan a cikin sa ne take ganin wasu irin halittu kala kala da ban tsoro shi ya sa ta ke natsuwa a duk lokacin da take cikin duhun.Cike da tausayin ta Amoh ta kashe hasken tana jin hawaye na wanke mata fuska kamar Bazasu tsaya ba.Haka ma Suhaila.Ɗaki ne dai mai kyau ko ina tsaf dashi sai tashin kanshi yake yi.
Haka wacce ke zaune ta da kan ta yake hargitse yana walƙiya cikin shigar kaya mara sa nauyi saboda akoda yaushe yana samun kulawa.Dan wasu lokuttan abun yana sakin ta amma a lokacin da duk abun ya motsa ɗakin ma sai ta hargitsa sa da ita kan ta dan kayan jikin ta gaba ɗayan su take yaga su bana ta ba har wanda ya matsa kusa da ita.Kwana biyu an samu sauƙin abun na ta ciwon ya kwanta.Sai dai yau ɗin nan akwai alamar tashin ciwon duk lokacin da taƙi karɓan abinci hannun kowa sai ciwon ya motsa Suhail ne yake mata dole shi kaɗai take shakku a cikin halin da take ciki dan duk tafi sabawa dashi a gidan,idan bata yi niyyar karɓa ba ko Daddy ya zo bazata karɓa ba sai Suhail dan Haka Amoh ta ce bari ta gwada in zata karɓa kafin a tado da Suhail ɗin daga aikin sa.
Ƙara ƙankame jikin ta tayi waje ɗaya tana rufe Kunnuwan ta da take jin wani irin sauti a cikin su kamar na kukan jarirai da wasu halittu.Cike da tashin hankali suka yi kan ta ganin idanun ta na lumshe wa alamar suma zata yi kamar kullum idan abun ya motsa.Sai dai kafin suyi wani abu Numfashin ta ya ɗauke ɗaff da sauri cikin wasu irin hawaye da suka silalo ma Suhaila ta nemi wayar ta dan muddin babu wani namiji a kusa tana farfaɗowa zata ji ma kan ta ciwo ta hargitsa ko ina kuma ta riƙa neman guduwa.
Cike da tashin hankali tayi masa bayani wanda ko jin ƙarshen zancen ta bai yi ya damƙa aikin duba marasa lafiya ga colleques na sa dan suna da ɗan yawa kar ya bar su zaman jiran sa.Bai san ranar Dawowar sa ba suma cike da tausayin sa suka yi masa a dawo lafiya sanin abun da ke faruwa dan muddin ciwon ƙanwar ta sa ya tashi dole sai ya je gidan.
A chan kuwa koda suka yayyafa mata ruwa a fisge ta miƙe tana faman yin wani irin gurnani tana watse komai dake kan madubin babu abin da ke tashi da ke ƙara juyar da ƙwaƙwalwar ta face ƙarar kwalabe. Da Inna ilaiihi wa Inna ilaiihi raji'un da su Amoh ke ambata da sunayen Allah.A lokacin kuma wani ƙarfi ke ƙara tarar mata a jiki kamar wani ƙato dan haka bayan ta gama watse komai na kan madubin ta koma kan jikin ta gaba ɗaya ta yaga kayan jikin ta duk yadda suke ƙoƙarin hana ta amma abun yaci tura Saboda tafi ƙarfin su ƙarshe ma kan Suhaila ta koma tana jibgar ta kamar Allah ya aiko ta tana sakin wata irin dariya dake nuna bata lafiya bace dan mai cikkakken hankali ba zai yi ta ba.Dai dai lokacin Nurse ɗin ta ta shigo kasancewar wani uzuri ya riƙe ta dan ita ke kula da komai na ta har wankan ta,sai kuma wadda take kula da ita idan bata nan itace Nana itama tun da ta ga alamar yanayin na ta yau ta ɗauki uzuri tayi gaba bayan shirya ta.
Rasa abun yi tayi dan abun yafi karfin ta saboda tana da ɗan tsoro Ta juya da sauri kenan dan kiran security sai ta yi kici ɓus dashi fuskar nan tashi tayi Jawur kamar jan tumatir Matashin saurayi ne tsaye da aƙalla zai kai Shekara Ishirin da uku ko da Huɗu a duniya sai dai yana da cikar jiki dan haka zaka iya cewa ma ya wuce shekarun sa,ko zai kai da biyar.Fari ne tass irin farin nan na Fulani kamar sa dai sak irin ta Suhaila da Amoh dan ita suka biyo Rayyan ne ma ya ɗebo mahaifinsu,dan shi bai yi farin su ba.Fatar sa dai kamar ta wadda ke a cikin halin haukar.
Idanun sa ya runste da ƙarfi cike da ƙunar rai bayan ya haɗa ido da ita a lokacin da take ƙoƙarin yaga rigar Suhaila dake ta dambe ta ƙwace kan ta.Ta shammace ta ta cije rigar a bakin ta da haƙoranta wanda kuma babu alamar zata sake su.Zuba masa idanu tayi jin ƙamshin turaren sa da ya garwaye ɗakin wanda ya hana mata yaga rigar sai ma ɗago kan ta dan ganin inda zata gan sa.Murmushi tayi mai kyau kamar yadda ta saba sauka daga yanayin wasu lokuttan cikin ruwan sanyi.A hankali ta zare rigar daga bakin ta tana ɗagawa kan Suhaila tana komawa gefe ta takure waje ɗaya kafin kuma ta saki wani irin mahaukacin kuka mai tsuma zuciya mai cike da sambatu.
Amoh dake jin kan ta na sarawa ne saboda damuwa ta raɓa Suhail ɗin ta wuce haka ma Suhaila cike da wani irin kuka na Tausayin da yar uwar ta ke ciki ta yi anyi magani abu sai gaba yake yi kullum sai zagayen asibiti ake bincikar ƙwaƙwalwar ta da hotuna dan ita yanzu ba likita bace amma har ta haddace yadda hoton kan ɗan adam yake.
Nurse ɗin ta itama jiki mace ta fara ƙoƙarin gyara wajen a dubarance dan cikin kwalaben ta koma ta zauna sai anyi da dabara sannan yanzu za,a chan za mata waje tare da kayan jikin ta.
Numfashi ya sauke mai nauyi kafin ya raɓa ya shige wata ƙofa wadda take haɗe da hanyar da zata sadaka da part ɗin sa.Bai daɗe ba ya fito yana fitowa da syringe a hannun sa wanda yake ɗauke da ruwan Allurar ta dan haka cike da dabara ya shammace ta ya soka mata a damtse cikin kukan azaba ta saki wani marayan kuka mai tsayawa a zuciya.Kafin ta fara fisge fisge tana son ƙwace jikin ta saboda ya bata yar runguma yadda zata natsu kafin ya mai da ita kan gado.A haka bacci ya kwashe ta mai nauyi dan haka chak ya ɗauke ta ya mayar kan gado tare da gyara mata kwanciya.Sannan ya kunna haske dan ya taimaka ma Nurse ɗin ta kula da komai yadda ya dace.
" Mira Komai na hannun ki a gyarata idan ta farka ki sanar dani,Ta samu ta yi lunch ".
Kai Nurse mira ta gyaɗa cike da murmushi tana mugun kaunar yadda Suhail da sauran yan uwan sa da mahaifiyar su suke bawa Yar uwar su kulawa da wasu ne irin yadda take dukan nan ko inda take ba zasu iya matsawa ba.
Amma su koda yaushe cikin bata kulawa suke kuma sun kasa haƙura da kashe mata maƙudan kudade dan an rasa gano abinda ke cikin ƙwaƙwalwar ta ta tun fara ciwon na ta dan tun tana da ƙanana shekarun ta aka fara ganin sauyin yadda yara suke abubuwan su wata rana zaka ga tana Harare harare ita kaɗai ko kaga tana huci ko magana ita kaɗai Tun abun bai damun su har ya fara damun su dan harda dariya ta fara yi ita kaɗai nan suka fara bincike asibiti aka tabbatar musu da lafiyar ta ƙalau kuma an kira mai raƙiyya shima babu Aljannu,dan har yanzu kuwa babu wani cigaba na asalin abun da ke damun ta,Kuma hakan bai hana da Anji wani sabon consultant ba mai kula da sashen ƙwaƙwalwa su mata booking aje a duba ta koda kuwa ba ƙasar nan bane...
Tsafff ta gyara ɗakin da sauri saboda kowane irin lokaci tana iya farkawa saboda Alluran ba su wani tasiri a jikin ta.
Dan haka tayi sauri ta gyara komai ta chanza mata kaya tare da gyara mata gashin ta da yaƙara hargitsewa saboda bata bari a taɓa shi ko wankin kan da dambe suke ƙare sa da ita,ita kan ta bata son taɓa kan na ta,bare wani.
Kashe hasken tayi bayan ta gama kimtsa ta.Sannan ta nemi waje ta zauna tana sauke numfashi.Nurse Mira wajen aikin su ɗaya da Suhail shima ya nemi alfarmar ta dan ta riƙa kula da lafiyar ƙanwar ta sa dan tayo special course under sashen brain da kuma abinda ya shafi psycho haka ya roƙe ta tare da albishirin linka mata albashin ta dan haka take ta amsa masa koba komai ai aljihun ta ya ƙara cika,Sannan ta samu shiga Babban gida irin wannan gida na Babban minister.
Cike da wani irin sanyi ta tashi kasala mai nauyi na saukar mata dama haka Allurar ke mata dan haka a hankali ta sauko daga kan gadon tana rakuɓewa a inda ta saba zama.Cikin ɗan hasken da ke akwai a ɗakin wanda ita kan ta Nurse Mira ta saba dashi dan haka ta hango ta dama idanun ta kan ta suke bata motsa ba ko hana ta saukowa sai ma jiran ta zama dai dai ta matso mata da abincin ta.Wanda mafi yawan sa madara ne ko shinkafa da tea.
Su tafi karɓa...
Cike da dabara ta matso kusa da ita tare da kayan shayin da ta haɗa mata mai kauri wanda ya ɗan huce kaɗan.
Zama tayi kusa da ita kamar yadda ta zauna,ta fuskance ta.Ɗago idanun ta tayi ta zuba mata idanu kafin ta ɗauke su kan ta tana sakatar akaifar ta ɗaya daya da ɗaya wanda take tsaftace kuma ba mai yawa ba.
Murmushi Nurse Mira ta saki kafin ta kamo hannun ta.Sai dai da ƙarfi ta ƙwace sa tana zabura tana neman miƙewa tsaye dan ganin ta tayi ta koma mata wata halitta musamman murmushin da ta yi mata yanzu.
Ganin haka ya sa Nurse Mira miƙewa tana jaaa baya.Hakan da tayi ya bata damar komawa ta zauna mazaunin ta.
" Ni ce ko Isha" Bata Kalle ta ba sai ma haɗe ƙafafun ta da tayi waje ɗaya tana saka kan ta ciki alamar bata son ko kallon ta.
Nurse Mira kuwa da ta gane abinda take nufi hakan ya sa ta ɗau wayar ta ta danna ma ñumban da tayi Saving da Dr.Suhail kira.
Ba,a daga ba har ta gama ringing sai dai ba,a wuce minti biyu da gama kiran ba sai gashi ya ɓullo ta ƙofar da ya bi ɗazu yana sanye da kaya marasa nauyi na shan iska.
Cup ɗin ta miƙa masa dan dama ta san tunda ta ga bai ɗaga kiran ba ta san cewa yana hanya.Dan wasu lokuttan haka yake yi.
Karɓa yayi cike da natsuwa ya matsa kusa da ita ɗago kan ta ta ke son yi amma saboda ta tuna zafin allurar da ta san shi yake mata ita hakan ya sa ta ƙi ɗagowa ɗin wanda ke nuna alamar fushi take yi dashi.
Murmushi ya saki a hankali sannan ya riƙo hannun ta ɗaya.
Ya furta a hankali " MA'ISHA " ɗagowa tayi ta zuba masa idanun ta da suka ciko da ƙwalla dan shi kaɗai ne yake kiran ta da cikakken sunan ta ko shi kuma ba kullum ba sai lokacin da take cikin irin wannan yanayi,dan tun bata fahimtar shine kaɗa ke kiran ta da sunan har ta gane.Koda kuwa tana cikin ciwon ne tana gane cikakken sunan na ta da kuma ƙamshin turaren sa.
Hawayen ya share mata cike da tausayin ta yana jin kamar ya saka kukan shima.
Cup ɗin da ya ajiye gefe ya ɗauko ya ɗaura mata a baki take kuwa ta fara sha kamar zata haɗiye harda cup ɗin bai hana ta ba,dan ya fahimci tana jin yunwa ne sosai. Sai da tayi rabi sannan ta tsaya kafin ta jaan yo hannun sa tana jan yatsun sa tana dariya cike da yanayin rashin lafiyar ta.
Nurse Mira dariya itama tayi cike da farin ciki.
Sakin hannun sa tayi ta koma kan cup ɗin da ke hannun sa ta juya shi kan bakin sa dan ya san abun da kan iya biyo baya hakan ya sa babu gardama ya ɗan kurɓa kaɗan hannun ta ta haɗa waje ɗaya ta taɓa kafin ta juyo dashi bakin ta ta sha tana leƙo fuskar sa,tana dariya.
Shima yar dariyar yayi sannan ya kafa bakin sa kaɗan ya kurɓa ya mayar mata cije kofin ta yi ta hana shayin shiga bakin ta dan haka duk ya ɓata mata kaya rabi ya bi ta wuyan ta ya ɓata mata kaya.Haka dai aka gama bata shayin rabi shi rabi ita rabi jikin ta.Suna gamawa kuwa da dabara ya miƙe dan wasu lokuttan tare take cewa zasu miƙe dole sai ta bishi gashi bata son haske ko kaɗan ko yanzu ɗan hasken da suka saba dashi ne suke kallon ta cike da tausayi haka itama.Ruwa ya bata wanda ke ɗauke da ƙwayar maganin bacci suma sai da ya sha kaɗan sannan ta sha tana kallon sa tana dariya har da lakato tsinin hancin sa.
***
Tare dukkanin su yaran aka je airport tarbon Sa cike da farin ciki babu ma kamar su LEENA da REENA.
Babban mutun ne mai natsuwa da nagarta wanda Hutu ya zauna masa sosai da ganin sa ka ga cikakken ɗan boko mai ji da dukiya,dan ba zaka taɓa cewa ya ajiye Bilal da su LEENA ba,da Hamrah ba.
Cike da farin ciki Suka rungume sa suna haɗa baki wajen faɗin Abba.Shima cike da murmushi da farin ciki ya shafa kan REENA yana furta " my Baby kece kika ƙara girma haka" .Fuska LEENA ta ɓata kafin ta kawar da kan ta gefe Murmushi ya yi mai kyau yana ayyana wa aransa dama na san arina uwayen rashin haƙuri,dama tsokana ce yayi.Sai gashi ta faɗa.Dan su Hamrah da Ninah ba su nuna komai ba sai murmushi da suke yi suna zagaye dashi.
Amma ita har ta ɓata fuska kuka ma take batun saka wa.
Janyo ta yayi ganin tana neman barin wajen kafin ya rungume ta yana furta haba " Babyn SSS,Abban ta Yar gaban goshin Ya BILAL SS ".
Ai kamar ya tsokano inda ke mata kaiƙayi take kuwa idanun ta suka kawo ruwa sai kuka.Dariya yayi saboda ya san case ɗin da aka yi dan yana da labarin komai dake faruwa amma bai nuna ma Ummah ba saboda ya san yanayin da take ciki shima bata son ya shige sa shi ya sa bai nuna mata ya sani ba kwata kwata.
Share mata hawayen yayi dan Abba mutun ne mai barkwanci.
Shiru tayi tana sauke numfashi suko su Nina ga dariya ga tsoro sai dai suka kalli junan su kawai suka yi murmushi.Junaid ne,Ayman,Abdul jabbar suka matso suma cike da murmushi da girmamawa suka yi wa Abba sannu da zuwa dan sun tsaya ne matan su fara gama yi masa sannu da zuwan.Sai dai ganin shiriritar LEENA bata ƙarewa ya sa suka matso.
✨✨✨
A ɓangaren MAHAJ kuwa ɗan motsa jiki yayi kaɗan kafin ya wuce masallaci,ya fara gabatar da sallah a cikin jami'in ta kasancewar lokacin ta da ya riga ya kawo.Cike da ƙwarewa ya yi ta buga Basket ball ɗin sa shi,kaɗai sai da ya ji jikin sa ya saki, dai dai lokacin aka fara kiraye kirayen Sallah ta magriba dan haka cike da kuzarin da ya ɗan samu na motsa jikin da yayi ya wuce ɗakin sa direct wanka ya shiga ya ɗauro wanka da alwallah da sauri sannan ya sako Jallabiya mai santsi da taushi maroon color Direct masallaci ya wuce achan ya haɗu da mahaifin sa cike da girmamawa ya gayar dashi,Shima cike da Murmushi ya amsa masa.Mubarak kuwa kai yake ta sunkuyar wa ƙasa ganin irin kallon da yake masa,na tuhuma, wanda shi kaɗai ya san yana yi masa shi saboda ya san duk wani Motsi nasa.Ganin ya dalla masa Harara yanzu bayan sun haɗa ido ne ya sa shi sakin guntun murmushi kafin ya bi bayan su shida Hon Gagara.Da suke yiwa laƙabi da Abbu.✍️
*PAID BOOK 800*
Bayan an haɗa document kuma za,a same sa 1k
8069059746
Opay
Faiza Almustapha
Payment receipt
08069059746
Na rage kuɗin ne saboda complain ɗin wasu daga cikin ku masoya na,saboda irin ƙaunar da nake muku,na rage🥰.Na tabbata kuma in sha ALLAH zaku karɓe shi a hakan,Nasan rage su da nayi ba yana nufin na rage darajar labarin bane..
Masu niyyar saye🥰😘✨ Allah ya bada iko.
Wayen da suka saya dan Allah kar ku fitar mini da littafi.Hakan shine kawai soyayyar da zaku nuna mini.Zan baku littafin amafarki na san ta, ga wayen da basu karanta ba a matsayin Naira 300 ɗin ku Ngde.🙏
Sai kuma labari mafi daɗi💃💃💃💃da zan sanar da ku zan baku complete book one free saboda soyayyar da nake muku,Book two kuma 800.Ongoing kenan.
Complete book Idan an haɗa 1k.✍️
Ina godiya da shawarar ki Maman Abba🥰😘.Uwa ta ta gari Allah ya bar zumunci.🤲
Kk story daban yake,Ba zan ce yafi na kowa ba amma dai zance muku da ban yake.Ku dai kar ku bari Abar ku a baya.
Daga Alƙalamin
FirstLady 🙌
Gimbiyar taskira 👑
Fa'eeh💞
Comment,share,like pls 🙏
_*💋KURMAN ƘADDARA💋*_
_©®Faiza Almustapha Murai_
_FA'EEH BG✍️_
P.....1️⃣9️⃣
*BOOK ONE*
_FREE._
*TASKIRA WRITERS ASSOCIATION*
*Channel link*
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
*Follow me on*
*Wattpad@Faizamurai*
*Arewabooks@Fa'eehbg*
*Facebook@Fa'eeh Bg*
P...1️⃣9️⃣
Direct Sashen sa ya shige duk da ya san Mubarak na bayan sa hakan bai sa ya juya ba sai ma cigaba da tafiyar sa da yayi inda bai daka ta ba sai da ya tsinci kan sa a ciki ƙaton falon na sa.Zama yayi yana ɗan sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗago idanun sa da suka ƙara yin haske ya zuba su kan Mubarak dake tsaye yana sakin murmushi shi kaɗai dan ya kasa manta badaƙalar da aka sha da SHATOU.kan sa ya kawar bayan ɗan yi masa kallon yan mintuna.Wanda ko bai tambaya ba ya san abinda kallon ke nufi dan haka kai tsaye ya furta ' Eh dama Yarinyar nan ce na tuno da ita a ƙauyen da muka je ".
Sarai ya ji shi kuma take ya fahimci inda yake nufi dan in bama yanzu da ya tuna masa ba shi ya manta da wata halitta Shatou a rayuwar sa.
Bai ce komai ba dama Mubarak bai yi tunanin zai amsa masa ba.Dan haka ya ƙara furta " Dama cewa nayi a gafarce ni,na faɗawa Abbu maganar nan naga bai kamata a ɓoye masa ba shine,na ga ka fahimci komai daga yanayin Abbu ɗin shi ya sa naga Gara na faɗa maka karka ce na munafunce ka !"Ya kai ƙarshen zancen yana sakin guntun murmushi.
MAHAJ kuwa idanun sa ya ɗan ƙara buɗewa a zuciyar sa yana ayyana gayen nan ya ma raina mini da wayau a fili kuwa ɗan kallon gefen ido yayi masa ganin yana Murmushi hakan ya sa bai ce masa ƙala ba,dan dama ya fahimci cewa ya riga ya matsi bakin sa da bai gajiya da magana idan ya tashi.
" I know this will happen "
Ya furta a hankali kamar mai tsoron magana.Mubarak kan sa ya shafa kawai kafin ya miƙa masa wayoyin sa da ya ajiye masa tun ɗazu sai dai ya san bai ko bi ta kan su ba har yanzu yadda ya ajiye su haka ya gan su.
Ajiye mai su yayi nan kusa dashi kafin yayi masa Sallama bayan ya nemi ko yana buƙatar wani abu.
Bayan fitar Mubarak MAHAJ numfashi ya sauke kafin ya miƙe da wayar sa wadda yafi amfani da ita ahannun sa,Babban falon ya fita Sashen Amma ya fara shiga anan ya tarar da su Sajida da Salma da Samrah dake ta buga game hankalin ta yayi nisa.Bayan sun gama sanar da ita irin wulaƙancin da yayi musu yau.
Da murmushi kwance a kan fuskar ta ta amsa masa kamar bata ji komai bakin su Salma ba dan bata cika ɗaukar zancen su serious ba dan ta san halinsa ne,hakan ko samrah saboda tana little sister na sa ne yake ɗan sake mata,kuma duk wannan rashin sakewar ya samo asali daga irin kular da ya samu.
Zama yayi cike da girmamawa anan ƙasa yana cewa " Amma Barka da dare "
Cikin sakin fuska ta amsa masa.
Ya hanya ta yi masa ya amsa da Alhamdulillah kafin yayi shiru ya rufe bakin sa ruf.
Shiru falon ya ɗauka.Su ko Su Salma ganin yanayin sa ya sa suka kasa yi masa magana dan fuskar sa babu alamar akwai wasa acikin ta.Ƙarshe ma idan suka takura sai dai irin wulaƙancin ɗazu ya biyo ko makamancin sa dan sun fuskanci ɗabi'ar ya yan na su ce rashin son takura.
Miƙewa yayi zai fice Amma tace " MAHAJ ba zaka ka yi Dinner ba,Abbun ku ba zai ji daɗi ba,idan kana zama da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 39