Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
itama tana sauke numfashi. Ganin lokacin Sallah ya na neman gotawa wasu har sun fara sallame sallah hakan ya sa Baffa na da Bibu suka yi sauri suka fice bayan sunyi Alwallah aka bar Inna ni da shatou suma ɗin alwallah suka yi dan shatou yanzu wuta Inna ni ke saka mata akan ibada ko da ma chan tana matsa mata bare yanzu,kuma shatoun gwargwado tana iya iya ƙoƙarin ta,tana tsayar da biyar ɗin nan sai dai wasu lokuttan musamman da asuba sai Inna ni tayi Dagske bayan ficewar su Baffa na masallaci. Kamar tambayar arziki bayan gama sallahn su Shatou ta kalli Inna ni cike da ƙuruciya ta furta " Wai yaushe zaki haifa mini ƙanwa Inna ni,ni nikaɗai ce mace gidan nan fa " ? Zuba mata idanu Inna ni tayi kafin ta ce " Ni kuma wando kika ga ina sakawa ba ". Dariya shatou ta kece da ita dan haka kawai ta hango Inna ni cikin wandon Baffa na hakan ya sa ta ƙara tintsirewa da dariya har sai da ta kai ƙasa. Inna ni kuwa murmushi kawai ta saki ta cigaba da jan charbin ta tana jin wani sanyi Aranta ganin yadda shatou ta koma lokaci ɗaya,sai dai kuma ƙasan ranta tambayar ta shatou na ɗaga mata hankali dan ta san ta da shegen nacin tsiya yanzu ko Baffa na idan ta ga dama zata iya tsirewa da wannan tambayar,batun yau take maganar ayi mata ƙanwa ba sai dai Inna ni ta watsar da ita da shirmen ta Amma har ƙasan ranta tana jin tsoron wani mataki da za,akai shatu ta iya fahimtar wani abu,ko ta samu Baffa na da zancen. Sai da ta gama tun tsutsar dariyar ta sannan ta ƙara furta wa cike da ƙuruciya " Nidai Inna ni idan ba zaki mun ƙanwa ba Allah ya sa na haifu da ciki na na samu ƙanne sai na haifa Miki goma " " Ke uku ,Ni biyu,Baffa biyu,Bibu biyu ,Sai kuma biyu na ".. Sai ta yi ɗan alamar tunanin wanda zata bawa. Baki taɓe dan babu wanda ya faɗo mata a rai face MAHAJ. Sai ta ce a zuciya (" Wallahi bazan ba masu jajayen kunnuwa "ya 'yana ba koda kuwa kuwa masu kyaun sa ne ") Tsakin da ta ja a fili ne da murguɗa baki bayan katse maganar zucin ya sa Inna ni da ta zuba mata idanun ta da suka sauya ne lokaci ɗaya sauke numfashi kafin ta iya furta komai sai ta kara tsinkayar Muryar Shatou na furta " Mai gari ɗaya,Amina,da Jawairiyya ɗaya,dan ba zan ba Ramata ba ta saka musu warin baki ". Ta kai ƙarshen zancen irin Dagske take zancen ta kuma kallon da Inna ni ta mata ta fahimci daga ƙasan zuciyar ta zancen ya fito dan haka cike da son danne abun da ke ta so mata ta ce " Ke fa Shatou wani sa'in sha sha kike,Wani cikin ne zaki haifa yaya goma dashi a lokaci ɗaya,kuma da uban me zaki shayar da biyun da zaki riƙa " ? " Gashi nan " Ta buɗewa Inna ni shafaffen cikin ta da yake fari sol sai walƙiya yake yi kamar wadda take gyaran jiki dan dama haka duka jikin ta yake kamar na Inna ni kafin ta fara ƙokarin kai rigar sama kan yan ƙiran dangin ta sai kuma taƙi buɗesu tayi murmushi irin na kunya ta ce " Wannan zan basu " Kai Inna ni ta girgiza tana ɓalla mata Harara,Ga kayan haushi ga abin dariya dan wannan shirmen na shatou abun dariya ne musamman yan ƙiren dangin da ke manne chan da ake cewa sune za,a shayar da ya yan da su. Kafin Inna ni ta sake cewa komai ta ƙara tsinkayo maganar Shatou "Nidai Inna ni kimin Addu'a Allah ya bani yan goma ".ta faɗa da iyakar gaskiyar ta. Baki Inna ta saki tana ƙara ware idanun ta akan shatou a karon farko. " Shin a ruwa zaki sha cikin ne da zan Miki addu'a dan uban ki da kika fara isa ta da Surutu ". Cike da Hasala Inna ni tayi zancen. Baki shatou ta tura gaba kafin ta ce "eh ai a ruwa ake shan sa dama,ba dole sai ka matsa kusa da maza ba tun da mamassu Ramata basu da maza gidan har baban su ramata baya nan,sai dai ya shigo ya bar ƙauyen amma ta haihu a bun ta kuma a ruwa Ramata tace ta sha ".Ita ana ta tunanin tun da an musu karatu da su daina kula maza suna matse musu dan da kin balaga kina iya haihuwa shine ta ɗauki zancen.Ba tare da fahimtar komai b. Salallami Inna ni ta ɗauka tana fatan kar su Baffa na su shigo su ji wannan magana dan haka babu alamar wasa akan fuskar ta,ta kira sunan ta. ........."Shatou!" Kallon ta Shatoun tayi wadda ke ta sakin murmushi kafin tayi karaff tace. " Addu'ar ce zamu yi Inna ni " ?? Ta ɗaga hannayen ta sama cike da jin daɗi a iya tunanin ta addu'ar samun yan goma ɗin Inna ni zata mata.Tun da ta san amakarantar Arabia da boko ance Addu'ar iyaye karɓaɓɓa ce. Inna ni bata tan ka mata ba sai ma. Kai data girgiza kafin kuma ta mai da kallon ta kan shatou ɗin da kyau. Ta ce " Shatou ke wata rana sai na ganki kamar mai hankali,Wata rana sai ki zama babu komai akan ki,bana son zancen cikin nan daga yau tun da ke sha sha ce,anan ƙauyen idan baki sani ba,Duk aka samu mace da ciki koda na ruwa ne korarar ta wasu daga jama'a suke yi musamman idan ya kasance a lokacin da ake gab da damina ne,manoma sukan kori kowacece ,Dan haka sai in kina da Aure ne aka gan shi dashi ba,a ce Miki komai koda na ruwa ne bana son ko kaɗan naji zancen ƙannen nan,keda kike da tarin ƙanne da yawa ke kika faɗa da bakin ki ". Shiru Shatou tayi ba wai dan ta fahimci wani abu mai ma'ana ba amma dai ta ɗauki gargaɗin Inna ni,dan tana jin tsoron rabuwa da iyayen na ta dan haka dole ta bar zancen. Shiru Inna ni tayi ganin shatou na kallon ta kafin ta ce . " Tarin ƙan nai kuma ".? Fahimtar suɓutar bakin da Inna ni tayi ne ya sa ta furta " eh ina nufin Bibu da Amina ai kin ce kamar dubu suke a gare ki ". Murmushi Shatou tayi tana gyaɗa kanta kafin ta ce " Ba zan ƙara maganar ba nikam,Bana son ƙannen ma ". Tayi zancen da iya kar gaskiyar ta.Sai dai a lokacin ƙuruciyar ta bata damar tunanin tambayar Inna ni dalili ba. Kallon ta Inna ni tayi tana sauke Ajiyar zuciya kafin ta saki murmushi ganin yadda SHATOU ta narke fuska. Sallar Isha'i ce da aka kira ta sanya Shatou miƙewa dan chanza Alwallah dama Inna ni taji warin tusa dan haka da yake su biyu ne ya sa bata ce mata ƙala ba dan ta san itace.Tana zuba ido taga idan lokacin Sallah yayi ko zata miƙe tayi.Sai ko ta miƙe. (" Mai gari ɗaya,Amina,da Jawairiyya ɗaya,dan ba zan ba Ramata ba ta saka musu warin baki ".) Murmushi Inna ni tayi tuna wayen nan kalaman da suka fi bata dariya duk da ƙirjin ta na ɗagawa akan yadda kwana biyun nan Shatou take addabar ta yau zancen Aure gobe haihuwa,dudu shekarar Shatou nawa da zata fara wannan shirmen koda yake wasu yaran haka ƙuruciyar su take da jajiɓe jajiɓe idan ba shirmen Shatou ba yaushe haihuwar ta zama mara wahala da zata haifi yan goma,abu kamar wasan yaran ai bata mata fatan samun yan goma ko nan gaba ne.Shi Raino harda mai gari..Ta ƙara furtawa acikin zuciyar ta kafin ta saki yar ƙaramar dariya a bayyane dai dai lokacin da Shatou ta same ta,kallon ta tayi ta ce " Inna ni me kike yiwa dariya halan "? " Babu komai Shatou,Addu'a kawai nake yi Allah ya shirya min ke,Ya sa naga Auren ki,ke da yan uwan ki (...da bani tabbas akan su ") ....ta kai ƙarshen zancen cikin zuciyar ta cike da wani irin raunin da take ɓoyewa a lokutta da dama musamman a gaban Baffa na. Sai kuma ta ɗago Afili ta cigaba da cewa. " Amina,Ramata, Jawairiyya Habibu na ga kuma Yar gaban Goshin Baffa nan ta ". Tana sauke zancen ta sauke ajiyar zuciya a ɓoye. " Amin Inna ni,har da nasu Iro ma Allah ya nuna miki ". Shatou ta furta babu kunya cike da ƙuruciya. Inna ni kuwa cike da dariyar da ta bayyanar da wushiryar ta yar ƙarama irin irin ta shatou,cike da mamakin ƙuruciyar Shatou ta kalli yar kyakkyawar fuskar ta da take ɗan ya sharaff da alama zancen har zuci tayi sa wanda ya nuna ma Inna ni cewa shatou bata da riƙo yanzu gashi har da Abokin faɗan ta a cikin wayen da take fatan Inna ni taga Auren ta cike da murmushi ta ce. " Yar mafarauci manya,har da iro alamarin". Kai SHATOU ta gyaɗa kafin Inna ni ta koma sakin murmushi dan yau firar ta da yar ta ƙayatar da ita take yi matuƙa tana samun farin ciki duk da akwai shirme ciki. " Tomh Allah ya nuna muna,ya sa muna da rai da lafiya ". " Amin " Shatou ta ƙara furtawa tana sakin murmushi. Ita ma Inna ni murmushin ta saki kafin ta kalli Shatou tace " ki kabbara Sallah ". Tana gama zancen ta tayar da sallah. Itama shatou haka ta tayar da ita cike da natsuwa kuwa ta gama sai dai duk da Inna ni ta riga ta farawa ta riga ta gamawa. Inna ni kai kawai ta girgiza bata ce mata ƙala ba bayan gama sallahn Tana jin ta tana Yin Addu'a wadda rabi da kwatan sa duk Inna ni ake yiwa da Baffa na. Murmushi Inna ni ta samu kan ta da yi dai dai lokacin da ta gama jan charbin ta tace. "Ke ma fa kina buƙatar Addu,ar nan Shatou,kiyi wa kan ki bamu kaɗai ba da Bibu ". Fuska ta ɓata sannan ta ce " Nidai Inna ni na fi son ku na riga ku mutuwa,Dan nafi son na riƙa ganin ku kusa dani,idan bakwa nan kuma Ni na san bazan ma iya rayuwa ba ". Shiru Inna ni tayi tana zuba mata ido ganin yadda take zancen cike da ƙuruciya da gaskiyar ta, kafin ta saki guntun murmushi cike da tausayin Yar Tata abun son ta wadda take kallo a matsayin sanyin idanun ta wadda bata son damuwa ko ɗigo ce ta gan ta atattare da ita,akwai dalilai da dama da suka saka Inna ni bawa Shatou wani waje na musamman a cikin zuciyar ta,mai cike da tausayi wanda ita kaɗai ta bar wa kan ta sani sai lillahi.Ita kan ta Abar tausayi ce sai dai Shatou take ji ma wa. " Allah ya sa mu mutu Muna masu imani kowa ta ɗauka a tsakanin mu duk ɗaya ne dama lokaci kawai muke jira " Shiru Shatou tayi bata bi maganar Inna ni ba wadda ta sauke a jiyar zuciya tana haɗiye wani irin ɗaci a ƙasan zuciyar ta mai girma da ciwo. Shatou kuwa shiru tayi sai dai ta zuba ma Inna ni idanu tana Murmushi kafin ta ce. " Amin " Murmushi itama Inna ni tayi. Sallamar su Bibu ce ta katse ma Shatou wata maganar da take son yi.Dan haka cike da murmushi ta gayar da Baffa na. Amsawa yayi shima cike da sakin fuska da murmushi yana ƙara bin ta da kallo kamar yau ya saba ganin shatoun. Inna ni ce da ta lura ta ɗan yi gyaran murya hakan ya sa ya juya yana kallon ta kafin ya sauke a jiyar zuciya yana sakin murmushi. Zama suka yi a kan ta barman da Inna ni ta shimfiɗa musu tun ɗazu a bincin su ta sauke musu nan kafin ta dawo ta zauna bayan ta tabbatar komai ta ajiye na buƙata dan ta san tare zasu ci abincin dan haka bata wahalar da kan ta da raba musu shi ba. A haka suka ci abincin tare ita Inna ni bata ma ci na ta ba sai dai Baffa na bai ce mata ƙala ba.Cikin natsuwa suka ci suka ƙoshi suka wanke hannayen su kafin Baffa na ya ƙara bita musu karatukan su,kowannen su yayi bita sannan ganin dare yayi suka fara ƙoƙarin miƙewa dan lokacin tara ta buga. Sai dai Shatou na miƙewa Ta tsinkayi Muryan yaro na Sallama wai ana yiwa SHATOU Sallama yadda ta zuba ma yaron da ake tsaye ido haka ma Inna ni, Baffa na ji yayi kamar an masa dabaibaiyi jikin shi ya sauya lokaci ɗaya ya tsinci kan sa cikin wani irin tashin hankali dan haka da ƙyar ya zaƙulo a bun da zai iya furtawa " Wa ya ke kiran ta ".? " IRO ne ɗan gidan mai gari ". "IRO"! Suka haɗa baki wajen faɗa cike da mamaki ita kuwa SHATOU da farko daɗi ta fara ji an fara zuwa wajen ta zance sai dai jin sunan Iro ya sa ta ɓata rai tana Hararar yaron cikin ɗan hasken fitilar da Inna ni ta kunna musu. Inna ni kuwa samun kan ta tayi da sakin murmushi kawai kafin ta bar su nan ta shige ɗakin ta dan ita sai abun ya bata dariya zillau (wai ana yiwa SHATOU Sallama,)sai lamarin ya bata kunya. Ajiyar zuciya Baffa na ya sauke mai nauyi ganin shatou ta wuce fuuu bayan ta furta " Ka ce masa nayi Bacci,idan wani abu na masa ya bari mu haɗu fadar mai gari ".Ta kai ƙarshen zancen tana jan tsaki,irin ita Babbar budurwan nan. Bibu dariya yake ta saki yana kallon Shatou ɗin wadda ta galla masa Harara ya san yadda take yawan faɗin za,a ga saurayin ta kyakkyawan gaske ranar da ya fara zuwa ƙofar gidan nan sai kowa ya suma saboda kyaun sa amma daga ƙarshe sai aka ɓuge da ganin Iro abokin faɗan ta dan haka yake ta sakin dariya yana tuno kalaman na ta. 'Harara take ta galla musu sai dai babu wanda ya kula ta, su dai abinda ya kawo su suka yi suka samu waje suka zauna,cike da rashin damuwa da yanayin na ta. Tun da kuma suka gaida ita dan amsawar ma ciki ciki ta amsa musu ita dan haka bata ƙara bi takan su ba,dan dukkanin su umurnin Ummah suke bi dan ita ke turo su dole daga su har Bilal gaida matan uban na su da sauran matan yan uwan sa koda kuwa ba su so dan akwai inda suke jin daɗin shiga kamar sashen Hajiya Asma'u da sashen Hajiya Ramlat da sashen Hajiya Maryam mahaifiyar su Samir wadda suke kira Hajiya.Ba su damu da halin ta ba sun saba dan ita kai tsaye take nuna musu tsana dan shi kan shi ma Abba ya sani kuma bai takura mata da dole sai ta so ya yan na sa ba wulaƙanci dai ne bai ɗauka ga kowannen su akan ya yan sa da suke ganin kamar ya fifita su da yar guda ɗayar Momcy da ma su Ninah. Dalilin da ya sa Ummah ta tura su kuwa ganin sun shiga kowanne sashen bayan dawowar su daga shashen Momy da faten waken da ta ce akaiwa Abba wanda Ummah ta karɓa sannan ta ce su juya su je su gaida Hajiya Sa,ada Mamy itama su gano ta kamar sauran. Dan haka da turin baki suka juya.Abba da bai shige ba tukunna ya yi yar ƙaramar dariya yana jin wani irin kaunar Ummah a ransa duk da ya san Yadda Hajiya Sa,ada Ke rashin kulawa da ya yan Ummah bai taɓa ganin damuwa kan fuskar ta ba kai ita ko abokin faɗa bata dashi cikin abokan zaman na ta dan haka yake ƙara girmama lamarin ta duk da suma sauran ba,a cika kama su ba dan suna yin kishi mai tsafta sai dai duk da haka kowaccen su akwai abun da ke ranta tsakanin Mamy, Momcy. Sai da suka kusan share mintuna talatin suna zuba wa tv ido sannan Leena ta zunguri Reena da tayi balance dan ta saki jikin ta sai kallon Cartoon take yi da ta sauya ita kuwa Hajiya Leena da take jin ta kamar a ƙaya ta ɗaure fuska ta mau dan tana jin hararen hararen nan har cikin jikin ta dan haka ta kasa ko ƙara kallon gefen da Mamy take zaune.Dan Umurnin Ummah ne ta ce Sai sun tsaya sun ta ya ta fira saboda ita dai tausayi take bata babu wani yaro na ɗebe kewa a sashen ta daga masu aiki sai ita kaɗai dan haka take tura su sosai a sashen sai dai Allah bai saka ma Mamy ƙaunar su da su har uwar ta su ba,duk da kuwa tana da son yara amma bata kula su ko kaɗan.Tun Ummah bata gane ba har ta gane amma duk da haka baiwar Allah sai ta tura su wannan rashin albarka ba su ba har Bilal yiwa take yi dan ta sha barin sa a falo shi kaɗai ta ƙara gaba shi ko ga sharaɗin Ummah dan haka yake zaunawa har a ɗan ja lokaci sannan ya fice,to yau ma sun ci sa,a ta zauna kuma ta amsa musu sallama. Hajiya sa,ada mace ce irin matan nan masu kaifi ɗaya idan bata son ka bata son komai na ka dan haka saboda rashin kaunar da ta keyi wa Ummah sai ta shafi ya yan ta,Sannan mace ce da bata damu da shiga sabgogin mutane ba sai dai tana da sakewa idan ta ta shi da kuma wanda ta ga dama dan idan ta shiga sashen surukan na ta bama zaka ce ita bace ko a gaban mijin ta,dan suma suna ƙoƙarin bata kulawa Musamman Uwani da ta san zafin rashin haihuwa tun da ta ɗan ɗana itama wanda har yanzu suke cikin raɗaɗin. (Masu neman haihuwa ido rufe Allah ya basu.Rashin haihuwa tabo ne Babba mai raɗadi da ke samun zukatan wayen da suke cikin wannan yanayi,yara abun so ne ga kowa musamman naka kana kallo kana jin daɗi,shi ya sa sai inyi ta mamakin Mazan da ko matan da basu son haihuwa abinda wasun su suke nema ido rufe.Suna nan Dare da rana suna kai kukan su ga Ubangiji.Amma sai kaga ciki ya tasa an hana sa shaƙar iskar duniya saboda son rai.Kyautar da kai baka isa ko wanin ka ya baka ita ba.Allah ka bawa masu neman haihuwa,Iri mai albarka.Amin✍️) Miƙewa Leena tayi wanda ya sa Reena kallon ta kafin ta ɓata fuska tana miƙewa. Dan ta so ta cigaba da kallon ta dan ita fa ko a jikin ta. Ficewa suka yi bayan sun mata sallama sai dai bata ce musu ƙala ba duk da tana jin Reena na nanata Mamy mun tafi. Sai da suka fice sannan ta juya ta harari bayan su tana furta " Ya yan Mayu kawai duk zan yi maganin ku har uwar ta ku uwar munafukai ". Mtsww ta ja dogon tsaki tana kara waya akan kunnen ta. Suko su Leena suna fitowa Sashen Hajiya suka faɗa ganin wata dallaleliyar mota Parkey a gurin wadda ko ba,a faɗa ba sun san ta waye har rigen gen suke yi cike da farin ciki da mamakin yaushe ya dawo haka suka an taya ƙaton falon babu ko sallama,kowaccen su fuska washe babu ma kamar Reena.✍️ # 2025 # Hausa novel # Love,and romance story # Zumunci mai ban mamaki *PAID BOOK 1k* 8069059746 Opay Faiza Almustapha Payment receipt 08069059746 Daga Alƙalamin FirstLady 🙌 Gimbiyar taskira 👑 Fa'eeh💞 Commente,and like pls 🙏 _*💋KURMAN ƘADDARA💋*_ _©®Faiza Almustapha Murai_ _FA'EEH BG✍️_ P_____2️⃣5️⃣ *BOOK ONE* _FREE._ *TASKIRA WRITERS ASSOCIATION* *Channel link* https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y *Posting group link* https://chat.whatsapp.com/L1d9rxjzfMM0pagtLNRfqn?mode=ac_t *Follow me on* *Wattpad@Faizamurai* *Arewabooks@Fa'eehbg* *Facebook@Fa'eeh Bg* ☘️☘️☘️ Da murmushi kwance akan fuskar sa ya tallabi Reena ta dake gaba juya ta yayi kamar yar kaza suna ta dariya haka ma Leena dukkanin su dariya suke yi cike da farin ciki mai tarin yawa mai cike da kewar ya'yan na su.Matashin saurayi ne kyakkyawa kamar dai yanayin sa da Bilal sai dai Bilal ya ɗan ɗara sa ko daga yanayin fata dan shi ta sa mai duhu ce kaɗan. Samir kenan ma'aikacin Custom service kamar yadda muka sani shine ɗa na farko a wajen Hajiya Maryam Uwar gidan Ibrahim Sada Saleh. Samir yana aiki a kano kuma ya kan shigo gida ya ga yan uwan sa idan sun samu hutu ko ya ɗauko hutun. " Yaya Sannu da dawowa, shine ranar da muka yi waya da kai a wayan Ummah,ka ce ba yanzu zaka dawo ba sai bayan an gama a zumi ". Reena ce tayi zancen tana shige wa jikin sa bayan sun zauna a tare a kan ɗai daga Cikin manyan kujerun dake a cikin ƙaton falon. Hajiya Maryam dai da suke kira Hajiya murmushi ne ta ke ta yi cike da dattako da tsantsar ƙaunar ta ga yaron na ta da yan uwan sa take kallon su. " Yanzun ma Reena ba zama na zo yi ba na zo ganin Baby ta ne,nayi kewar ku baki ɗayan ku ". Ya yi zancen yana kallon Leena da taɓata rai,dan a tunanin ta Hamrah yake magana dan itace bata kusa tun da duk yana kiran su haka,sai dai ita yafi kiran ta hakan. Yar ƙaramar dariya yayi kafin ya mai da kallon sa kan mahaifiyar sa da take cewa bazai je ya watsa ruwa ba ya dawo ta san rigimar su da Leena yanzu idan aka fara babu ranar ganawa. "Hajiya bari ba lallashi Baby na tayi fushi " Ya bawa mahaifiyar sa amsa yana sakin murmushi. Hannun Leena ya riƙo da kyau yana mata raɗa a kunne ban san a bun da ya furta mata ba take ta washe baki tana furta " Allah Yaya " Kai ya jin jina mata shima cike da sakin murmushi. Hajiya dai bata ce komai ba sai ma murmushi kawai da ta saki tana kau da kan ta bata re da ta damu da shiriritar ta su ba dan ba yanzu aka fara ba tun kan su kai haka,yake biye wa Leena dan sun fi shaƙuwa da shi a cikin yayyen na su,shi ne komai Leena dan haka ta ji zai dawo ta kama murna kenan a wasu lokuttan harda kitso da lalle take matsawa Ummah sai anyi mata saboda Ya Samir zai dawowa idan ya sanar musu, tasan school ɗin su ba,a barin lalle amma haka zata je ayi mata idan ta je su zane ta shi ko Samir da ya gane hakan sai ya daina sanar musu idan zai dawo dan haka har yanzu akan turban yake. Tafawa suka yi da juna kamar wasu sa'o'i. Ita ma Reena rigima ta aza sai ya tafa da ita dan haka cike da farin ciki suka tafa da ita. Shigowar su Abduljabbar ce da Ayman,da suka fita wajen ball suka shigo cike da murna ganin motar sa sai ga Junaid shima a bayan su wanda ya fito yanzu da niyyar fita sai ya ga motar ya yan na su. Cike da farin ciki da girmamawa suka masa sannu da zuwa yana amsa musu da sakewa da murmushi haka suka gama gaisawa yana ɗan musu tambayoyi suna Amsawa kafin kowannen su ya kama gaban sa musamman su da suka dawo daga wajen ball suna buƙatar saka ma jikin su ruwa zafi ya taso musu duk da sanyin Ac dake ta aiki a ƙaton falon. Shima Junaid ficewa yayi yana zuwa kuwa ya sanar ma Ninah cike da farin ciki ta baro sashen Mahaifiyar ta da ta baro da kayan da Abba ya saya musu wanda ta ke ta fama gwaggwadawa ai ta na jin cewa ya Samir ya dawo ta cire kayan da sauri ta fito daga sashen tana dosar sashen Hajiya. Dai dai yana cewa " Girls Bari na watsa ruwa na zo muyi fira dan ba zan ma yi baccin ba sai na sha labari ". Da gudu ya tara Ninah da ta shigo itama a Guje tana kiran sunan sa. Baki washe ya tarbe ta yana rungume ta kafin itama ya ɗaga ta sama yana lilo da ita tare da faɗin " Little naga kin ɗan ƙara girma,Keda Reena,Baby na kawai naga babu wani chanji gata nan yar firit ". Dariya duka suka yi sai Leena da ta tura baki gaba kafin ta fara hawaye tana ɓata fuska tace " Ba yaya B bane ya sako ni gaba gashi harda karya mini kashin baya na yayi,kuma Ni ban yiwa ma Babyn sa komai ba,amma aka mun ƙazafi ". Ta kai ƙarshen zancen kamar Dagaske jawabin nata. Waro idanu yayi shima ya ɓata fuska yana cewa "Wai meya sa ya'ya Bilal

Chapter 19 of 39