bata amsa da "Ban san su ba, amma Hajiya akwai hatsari bamu san me suka zo nema ba" Goje ya matsa kusa da ita yana kallon ta
"Mai dawa wannan ce ƙuruciyar? A hotun kamar bata kai haka girma ba, ƴar firit da ita kamar benu, nan kuma an ci kuɗin jama'a an sha madara da milo an yi ɓulɓul" sai ƙarewa Fiyya kallo yake ita kuma ta yi tsaye tana jin yadda warin wiwi ke dukan hancinta kamar za ta yi amai amma taƙi matasa saboda taurin kai irin na Safiyyerh Abdu Marafa da rashin tsoro. Tsaki ta yi kawai ƙasan zuciyarta kuma tsoro ne fal ga ƙirjinta dake bugawa kamar zai fito waje sai buɗe manyan idanu waje take yi.
"And what is my business with you? Me kuke nema a wannan kamfanin kun zo sai warin ganye kuke mini" Mutallab ya sake buɗe manyan idanunsa jin sautin muryarta zaƙwai a cikin kansa ya kalli bakinta dake motsawa cike da masifa duhun dare ne amma kamfanin haske tar tar ko'ina. Mangal ya lailayo ashar ya dannawa Safiyyerh "ke dan ƙaniyarki mune muke warin ganyen, su waye sila idan baku ba, ƴar wahalar yarinya idan ban bawa tiger namanki ɗanye ya cinye ba"
Safiyyerh ta juya ta kalli tiger daya hauro ya zauna kusa da Moh, yana zaro harshe waje ta nuna karan da hannu ta ce "abin da ya fi namana ɗanye, banda rainin hankali jikin nawa zaka ɗauka ka bawa shegen karan naku, idan kuɗi kuke buƙata na baku don nasa na yin caji kuke nema, stupid" Goje ya juya ya kalli Mai dawa ya ce "ba zamu rage wa yarinyar nan tsayin harshe ba kuwa? Kauɗinta ya yi over, ka je ka zauna matsalar idan ka sha wannan ƙwayar baka gane komai yanzu babu mamaki jinka kake a saudia"
Moh ya lumshe idanunsa ya sake buɗe su a kan Fiyya duk motsin da take yi a kan idanunsa sai dai ba wani fahimta yake ba muryarsa a cunkushe mai ban tsoro ya shafa kan tiger ya ce "shiit"
Tiger ya diro shima ya diro ya tsaya a kan ƙafafuwansa hannunsa ɗaya yana murza gashin kansa wanda ya zama wani iri ba kyan gani na shegun shahararrun ƴan daba ɗin nan.
"Mai jeji ƙirit ka ankare ba lokaci ka ɗaƙkota a kafaɗa mu fece kafin kwalawa su kawo kai dan akwai kimini a nan wancan mai fararen kayan" ya nuna securityn wajan wanda shi kaɗai ne kawai ya rage. Safiyyerh ta ja baya tana juya idanunta ta ce "ban gane ya saɓo ni kafaɗa ba kamar wata ƴar iska ko mara gata, kai naga alamar kai ne shugabansu ko? To wallahi ba wuƙa ba ko bindiga ce bana tsoro kana taɓa ni sai na raba ai an ce ba wani ƙwari ne daku ba" ta ƙare maganar tana kallon cikin idanun Mutallab wanda tun ɗazo shi take kallo shi kuma yaƙi furta komai.
"Ki iya harshenki ƴar kanzagi ko na fitar miki da jini yanzu na shata miki bille a wannan fuskar kamar gwada" juyawa ta yi ta ce "Baba wai where are the securities? Where are the rest ka kira su yanzu" kafin baban ya motsa Mangal ya saka ƙafa ya kwarfe shi zuwa ƙasa, ya sake saka ƙafa ya danne masa baki. Darma ya zaro wuƙa ya ce "Ke fitsararriya ce ko? Ba wata uwar muke nema ba ke muka zo ɗauka, don ke muka cikin wannan kamfanin ke za mu yi kidnaping yanzu kin fahimta kin gane ko, ki shige salin alin ko na ɗauke ki yanzu na haura dake wallahi"
Fiyya ta buɗe idanu tana kallon wuƙar dashi kansa Darma ɗin ta yi murmushi zuciyarta kuma bugawa tsoro ya shige ta, ƙoƙarin danna recoding take a wayarta hannunta ya shiga rawa ta dake a ƙasan zuciyarta tana kiran sunan Allah da ƙyar ta furta "kidnaping kuma ni, ni Safiyyerh Abdu Marafa za ku sace, ni Safiyyerh matar soja guda kuna hauka ne ko kuna tunanin mijina zai bari hakan ta kasance?"
Jin furucin Safiyyerh ya saka Moh sake kallonta da sauri yana hana zuciyarsa abin da yake ji, haka kawai ya dinga jin tafasar zuciya ya nufi wajan Safiyyerh jikinsa na rawa idanunsa suka fito waje kamar zasu faɗo da muryar mai ban tsoro mafi muni ba muryar ba ita kanta fuskarsa abar tsoro ce tsaf mutum zai dinga mafarkin ta. Hannunsa riƙe da wuƙa yana kallon cikin idanunta da kyau dab da ita ya ce "Ba mijinki ba ko ubanki Abdu Marafa aka bani umarnin daƙƙowa ko kashewa sai na yi balle ke" ya cije bakinsa ya feshi ya cilla mata ƙatuwar baƙar kunama ta shige ƙirjinta kai tsaye, zufa ta dinga yanko mata saboda tsananin azaba ta kasa ihu ko kuka ga warin da yake yi yana neman kashe ta, idanunta ya juye ya yi ja ta zuba masa idanu tana kallon fuskarsa data yaye,ta miƙa hannu da nufin shafo fuskarsa ta ji ya caka mata wuƙar a gefen cikinta ta yi wata ƙara tana buɗe idanu duk yadda jikinta ke rawa ga jini na zuba mai hanata sake kai hannunta ta shafo fuskarsa ba, daidai nan ya yunƙura zai saɓata a kafaɗa suka ji shigowar motoci na jami'an tsaro, bai niyyar barinta ba yadda Goje ke jan shi da ƙarfi ya saka kawai ya sake ta a wajan yana furta “Mutallab”
Ɗaya bayan ɗaya suka kama katangar suka haure daman kuma kaf kamfanin ita ce ƙaramar katanga wacce babu kwalabe jikinta.
Securities kala biyu ne dana fararen kaya da masu uniform sai shi da yake sanye da wando three qauter da farin takalmi da riga baƙa ko p.cap ɗin kansa babu, ya nufe ta sauran suka nufi wajan baba suka fara ɗaukan statement "Baba kwantar da hankalinka babu abin da zai sameka in sha Allah, bayan waɗannan ƴan daban da suka zo, an bamu tabbacin a daidai yanzu Scorpion ma yana wajan nan ko kuma ya zo" a hankali Aliyu ya juya ya kalli baban jin tambayar da ake masa, sai kuma ya ɗauke kai ya saka hannu ya ɗauki Fiyya zuwa cikin mota bayan ya kwantar da ita ya tsaya yana kallon wanda ke ɗaya motar a tsaye da yake ce masa "Ya akai kuka barta ta fito cikin dare haka? Macace ita fa"
"Sir ƙuruciya, thanks for the call"
"Anything for you Captain Aliyu" suka shiga mota duk suka bar wajan ya rage sai jami'an F.i.d kawai da suke tambayar baba.
Su Goje cikin kwalabati suka shige suka ɓoye suna zare idanu da muzurai a hankali ya ce "Akwai matsala jami'an tsaro ne fal yasin, baka dai bar sheda ba kuma me ya saka ka caka mata wuƙa idan ta mutu fa?" Moh ya yi shiru can ya ce
"Ba zata mutu ba"
"A ciki ka soka mata wuƙar fa? Baka kalli yadda jini ke zuba bane da zaka ce wai ba zata mutu ba?" Kai tsaye Moh ya ce "ba zata mutu ba"
"A buge kake shi ya sa, askira ka caka mata fa na ɗauka tsoratar da ita kawai za ta yi"
A firgice ya kalli Goje idanunsa kamar za su faɗo "Goje, idan ka sake maimaita mini cewa na saka mata wuƙa zan maka jahilci yanzu wallahi zan iya kashe ka"
"Kashe ni mana daman ai daba babu wata amana a ciki dole na faɗa, ɗaƙkota aka ce kawai ka yi ba kashe ta ba" Mutallab ya wani juya cikin zafin nama ya damƙo wuyan Goje cikin sauri Darma ya shiga tsakiya ya ce "Sai godiya kar a yi haka akwai amana, kai Goje ka iya bakinka idan ba farkawa kake so ka yi ka ganka a ƙiyama ba" Moh ya cije bakinsa kansa na wani irin sara masa yana girgiza kansa ya kalli sama "duk sanda na sake ganinta sai na kashe ta don uwarka" duk sukai masa shiru sun daɗe a wajan kafin jami'an tsaron su bar wajan suka fito tare da barin wajan suma kallo ɗaya za ka yi wa Moh ka ɗauke kai saboda yadda yake huci ya fiddo da ƙarin jikinsa neman inda zai sauke kawai yake.
The following days.
I. Qasim ya ce "Tunda ta bar I.c.u ai Allahamdulilah, she will soon recovering"
"Dr Qasim ba dai abin ku kuke mana na likitoci ba, ya jikin Maama don Allah ita ce kawai last hope ɗina" Dr Qasim ya yi murmushi ya ce "Safiyyerh zata ji sauƙi in sha Allah, ba'a caka mata wuƙar inda za ta yi mata illa ba ta zubar da jini sosai ne sai kuma zuriyarta data ninka gudun da take yi, ka yi mata addu'a"
"Shikenan Allah Ya bawa Maama lafiya,zan iya shiga ai kwana biyu ba'a barin mu shiga sai na ji kamar har yanzu bata dawo hayyacinta ba" I. Qasim ya girgiza kai ya ce "Daddy kana son Safiyyerh da yawa, shiga ka ganta" har bakin room ɗin da take ciki ya shiga ya shiga sanye da kayan daya dace a shiga aga mara lafiya. I. Qasim ya juya ya fita daddy ya zubawa Safiyyerh idanu tana ƙwace ta sake yin fari a barka da farar mace ta ɗan faɗa an ja mata rigar marasa lafiya zuwa saman ƙirjinta duk da baya kaya a jikin sai iya rigar an buɗe wajan ciwon da akai mata aiki a wajan ya zuba mata idanu ya matsa a hankali yana kama hannunta addu'a ya shiga yi mata sosai ta samu sauƙi zuciyarsa duk babu daɗi idan ya rasa Maama bai san yaya zai yi ba kuma.
"Allah Ya baki lafiya Maama, don Allah ki rage wa kan ki fitina da zaƙewa cikin wasu al'amuran kalli yadda za ki saka rayuwarki ta lalace, Safiyyerh ban shirya ba ban shirya ba Safiyyerh" ya damƙe hannunta yaga bakinta na motsawa amma sam baya jin me take cewa. Ta shi ya yi ya fita yana sake yi mata addu'a a ransa na samun sauƙi da rangwame.
Bayan ya fito waya ya saka ya kira Aliyu yana ɗagawa ya ce "Aliyu kana ina ne, an fito ita daga i.c.u amma babu kai a wajan bana son haka fa, da baya da yanzu ba ɗaya bane matsayin Safiyyerh ya jima da sauyawa"
"Allah Ya sauwaƙe"
Kawai Aliyu ya furta ta cikin wayar daga nan ya yi shiru ran daddy ya sake ɓaci yana jin kamar ya yi kuskure na aurawa Aliyu Safiyyerh na damƙa masa dukkan ragamar rayuwarta da tunanin zai kula da lamarin Safiyyerh amma ba lallai hakan ta kasance ba, sosai abubuwa da yawa ke damun zuciyarsa yana hana shi sukuni tare da rashin isasshen bacci, idan Safiyyerh ta tare a gidan mijinta dole ne ya amshi responsibility da Ubangiji ya ɗora masa na mijinta.
Ummi na kallon daddy da jajayen idanunta ta ce "Ina ta zuba idanu rayuwar yarinyarta na neman lalacewa, ka yi abubuwa da yawa Professor na ja baki na yi shiru da tunanin duk abin da ka yi daidai ne, zuciyata ba zata ɗauka ba Safiyyerh gabaɗaya nawa take ni kawai ta haƙura da aikin wannan Companyn da bana gane masa ai shekarunta bai kai ya kawo ba, ban shirya rasata ba" daddy ya yi shiru yana kallon yadda Ummi ke kuka.
"Ki tashi muje dare na yi" da sauri ta kalle shi tana share hawaye ta ce
"Kuma ban gane muje ba zuwa ina?"
"Ai kin san majinyata basa kwana a wannan hospital ɗin, patient ne kawai yake da alhakin kwana" tun kafin ya kammala magana take girgiza masa kai "i don't think zan iya barin wannan asibitin da Safiyyerh ita kaɗai, ni bana ma ganewa irin haka ka yi musu magana ko a nan zan iya kwana I'll manage" Daddy ya yi gaba yana furta "Kar na sake maimaita miki" dole ta miƙe bayan ta sake leƙa Fiyya ta yi waje.
Kafin a rufe shigowar masu ziyara Yaya J ya daɗe zaune gaban Fiyya yana kallon fuskarta, da kwanakin baya ne zai riƙe hannunta cikin nasa yana ta mata sannu da addu'a yanzu kallon ta kawai ya kasa koda yin addu'ar ma, can ya miƙe ya fice haka Awais da Dr Hash duk suka shigo basu da tabbacin bacci take ko farkowa ne ba ta yi ba. Wajajen 2 na dare ya buɗe ƙofar ya shigo bayan I. Qasim ya bashi damar hakan daman aikin kwana zai yi idanunsa a kanta har ya shigo ya rufe ƙofar a hankali ya tsaya gabanta hannunsa biyun zube cikin aljihu ya ɗauki minti a ƙalla ashirin kafin ya ƙarasa ya zauna bakin gadon har yanzu bacci take ya dubi hannun da ruwa yake shiga ya dubi ɗaya hannun da jini ke shiga a hankali ya kama hannun drip ɗin da yake ɗan mitsi-mitsi ya riƙe cikin nasa a hankali yake murza yatsunta can ya ji ta riƙe hannunsa ya ɗaga kai yaga tana jujjuya kanta sai a lokacin ya lura da sauyin ƙarar da na'urar ke yi.
Safiyyerh tana buɗe idanu ta rufe saboda wani fau ɗin haske daya shige mata ciki sai kuma hawaye ya fara bin idanunta ya ɗan sunkuya yana kallon fuskarta. Ta sake buɗe ido ta kalle shi ta dudduba taga ba kowa ta rufe idon still ta buɗe har lokacin jujjuya kanta take yi "Yaya" ya yi mata shiru ya sake cewa
"Me na yi musu?" Still shiru ya yi mata ta buɗe idanu ta kalle sai ta fashe da kuka sosai ƙirjinta na ɗagawa ya damƙe hannunta
"Yaya"
"Safii..." Ya kira sunanta a hankali ta ce "Kai na zai cire ƙirjina ciwo cikina ciwo yaya mutuwa zan yi"
"Allah Ya yi miki Rahma" sai kuma ya matsa dab da kan nata ta saka hannu ta riƙe nashi ta yi shiru a hankali ta sake cewa "Captain"
"Manager"
"Na ce musu mijina soja ne, wai ko sojan zasu kashe balle ni" ta yi shiru ta sake cewa "Ka riƙe mini kai na ciwo yake mini sosai na shiga uku daddy wayyo" maimakon ya riƙe kan nata sai ya ɗora goshinsa saman nata, ta buɗe idanu ta kalli fuskar Captain kamar zau haɗe da data a nutse ya ce "sun kashe kin?" Ta girgiza kai
"Me ya sa?"
"Ban sani ba" ya ɗan murza mata goshinsa yana kallon cikin idanunta ya ce
"Saboda ke matar soja ce" ta yi shiru kawai tana kallon shi can ya matsa yana sauka ya zauna saman kujera.
Washegari da sassafe ƴan sanda suka shigo room ɗin lokacin tana zaune ta ɗan jingina da jikin gado, statement na abin da ya faru suke tambaya. Sp Ghali ya kalli Safiyyerh data sunkuyar da kanta ƙasa ya ce "Da suka zo sun faɗa miki abin da suke buƙata?" Ta girgiza musu kai.
"Za ki iya gane wani daga cikin su? Suna ko kammani?" Ta ɗago ta kalli Sp Ghali dake tsaye ta ce "Idan na gane kamannin sai me za'a yi to?" "Zamu kira a zana mana fuskar wanda kika gane ne"
"To ban gane ba"
Duk suka tsora mata idanu musamman daddy ta buɗe idanunta itama ta ce "Kamarya? To na gane ne?" Daddy ya ce "Maama wa kija ji ya ce wani abu?"
Sp Ghali ya dinga kallon Safiyyerh yana jin wani irin abu a ransa na motsa masa sai ya yi murmushi ya ce "dear kin ce basu nemi komai ba, ba wanda kika gane ba suna amma haka kawai sai su caka miki wuƙa think Safiyyerh" sarai Safiyyerh ta tuna sunan da ta ji ya ambata na Mutallab sai ta yi shiru a hankali kuma ta ce
"Sp kasan matsalar da ƙasar nan take ciki musamman Jiharmu akan ƙwacan waya, wayata zasu ƙwace ni kuma na hana saboda ina da abubuwa a ciki shine sukai mini haka" ya jinjina kai ya ce "Haka ne dear za mu yi bincike zan gano kowaye za mu hukunta shi ƙarƙashin hukuma bisa kundin da aka wanzar, get well soon dear" ya sake faɗa yana murmushi kan ta dai a ƙasa yake. Sallama sukai dasu daddy suka tafi. Captain na zaune ko tari bai yi ba wayarsa kawai yake dannawa can ya miƙe ya fita daddy ya bisa da kallo haka Yaya J ganin ko sannu bai yi Fiyya ba daman bai jima da zuwa ba.
Eng Ali wali ya dinga kaiwa yana kawowa ransa duka a ɓace ya kalli Mai dawa ya ce
"Yanzu daka kashe ta fa? Wai me kake nufi da wannan abin da ka yi ne Mutallab?"
"Ka dai na yi mini ihu kamar Malam Abdullahi" Ali wali ya jinjina kai kawai ya ce "Kasan ka raina ya ɓaci kake cewa haka? Ya zan aike ka ka yi sato yarinya kuma ka caka mata wuƙa salon ka ɓata mini aiki da sanyin safe ake kama fara ba mai dawa"
"To na fasa"
Ali wali ya buɗe idanu ya ce "Meka fasa ɗin? Ba dai ɗakko yarinyar ba kake nufi?" A taƙaice ya ce "Shi"
"Haba uban mafarauta, kai baka san wasa ba kai kamar ɗa kake a wajena fa" sai a lokacin Moh ya buɗe idanu ya kalli Ali wali yanzu dai normal yake ba'a buge ba "baka haifan ba, san da aka haifan baka da labari" ya yi fito yana miƙar da ƙafa ya ce "To ka kira ɗan naka ya yi maka aikin, mu fa kuke sawa a wahala har a yi zaɓe aci a cinye ka hau kujerar ba lallai yaranka suna ƙasar ba, ba'a rainawa Moh hankali ka bar mu matsayin ƴan daban kawai" Ali wali ya ce
"Ya batun yarinyar?"
"Na ji" ya ce yana miƙewa tsaye har zai shige ya dawo ya ɗauki bandir ɗin kuɗi ƴan dubu-dubu ya watsa cikin aljihu. Sautin daya ji kamar gurnani kamar kuka kuma ya sa ya nufi ƙofar da yaje jin hakan ya murɗa handle zai buɗe cikin sauri Eng Ali wali ya riga shi ya ce "Haba Mutallab idan iyalina ne a ciki fa?" Moh ya zubawa Ali wali ido ya kalli ƙofar sai kawai ya fice yabar wajan. "Ɗan wahalar yaro ɗan jaraba Allah Ya nufa na lashe kujerar ganina sai ya yi maka wahala"
Hon Maɗatai yana zaune ya kalli Sp Ghali ya ce "Ka lemo record ɗin nasa?"
"Na samu Hon amma cin dai amana ne irin namu na jami'an tsaro amma fidda record ɗin wani criminal ya saɓawa kudin tsarin ƙasa" Hon Maɗatai ya ce "Waye Mutallab?" Sp Ghali ya ce "Nothing serious about him hon, shekaru uku da suka shige an kama shi da laifin kashe matarsa ranar da aka kai masa ita matsayin amarya, kafin nan yana da record na zama gidan yari na watanni sai kuma taɓa guduwa Legas, a baya kuma kafin hakan shi mafarauci ne ma'abocin shiga jeji ya yi farauta"
"Hon akwai matsala ne? Na ga ka yi shiru?"
"Batun Scorpion ba, case ɗin yarinyar nan Manager a ranar ance shima Scorpion ya je wajan" Sp Ghali ya ce "Hon Scorpion da ƴan siyasa irin ku yake da matsala fa, ko mutumin daya kashe last yana da za hujjar kisan mune dai bamu sani ba, waye Scorpion ba wanda ya sani jami'an mu na neman shi haka F.i.d Federal investigation department wallahi suna kama shi wannan kisa ne nan take ko su yi masa allurar hauka" "Al'amarin Scorpion ya yi kama da ɗaukan fansa fa, za mu zuba ido ya kashe mu ne? Ku hanzarta nemo ko waye Sp Ghali"
"In sha Allah Hon"
Aliyu na zaune saman kujera daddy ya ce "Kaji ai ko?" Ya jinjina kai kawai "Zuwa dare sai ka ɗauke ta ku tafi can part ɗin dake gidan daman tuni an zuba komai empty dai yake to ɗazo an kaiwa Safiyyerh kayanta, Aliyu Safiyyerh amana ce idan ka ci amana ba zan yafe maka ba, na yi haƙuri na rabu da kai amma na so kun bar ƙasar gabaɗaya" addu'a daddy ya yi musu sosai duk da Fiyya bata wajan. Aliyu ya tashi ya fita. A daren ranar ƴan jarida suka shigo saboda hirar da za su da daddy. Sosai aka yi hirar inda yake cewa. "har kullum ni Professor Abdu Marafa bana goyan mutumin da bashi da wata nagarta wanda baya duba rayuwar yaranmu matsa wanda kuma zuwa gaba sune zasu gaje mu, duk wanda ya buƙaci ku zaɓe shi ku fara duba nagartar shi waye shi, bane background na rayuwarsa waye shi tun farko? kar a yi amfani da talauci da rashin iliminku a saka ku yi zaɓan tumun dare a wannan lokacin matasa yana da kyau ku yi gangami ku magana da murya ku saka iyaye na gida ƙanne da yan'uwa su zaɓi cancanta, wannan masu gamu taliya gishiri ko masu siyan ƙuri'ar mu basu ne wanda suka dace ba, ƙuri'armu ita ce ƴa'cinmu kana siyarwa baka da damar yin zaɓe ku kalli yadda ake mayar da ƙananan yaran ƴan daba masu bangar siyasa ana basu ƙwaya suna aikata zunubi suna kai kansu inda za'a kashe su, ku faɗa mini ko sau kun taɓa ganin ɗan wani daga cikin ƴan takarkarun nan? no! Sai yaran talakawa wanda basu da ilimi ko basu da sana'a sai a yi amfani da wannan damar a janyo su a kurɓata musu rayuwa a ƙarshe kuma ko gidan yari yaro ya tafi wallahi sai dai iyayensa su yi fafutuka duk da cewa har da laifin wasu iyayen a lalacewar yaran, matasa ku haɗa ƙungiya da za ku dinga taimakon juna kar ku yadda da mulkin kama karya kuna kallon shekaru huɗu da suka shige yadda zaɓe ya kasance"
"Professor Abdu Marafa kenan a yayin da yake bawa matasa shawara akan su miƙe tsaye domin ƙwatuwa jiha ƴan'cinta. Professor mai ya sa duk maganar da zaka yi akan matasa ne? Da batun shaye-shaye ko daba?" Daddy ya rantse idanunsa yana jin zuciyarsa na yi masa zafi can ya ce
"Ɗan jarida kenan baki abin magana, saboda matasa sune yau, sune gobe haka jibi matasa sune cigaban ƙasan idan har aka tsaya musu aka fitar da iri mai kyau, shaye-shaye kuma....," sai kawai ya yi shiru. Yakasai ya ce "Gabaɗaya abin da zamu iya naɗa kenan a wannan satin, zamu cigaba da bibiyar professor Abdu Marafa domin ganin haƙar tasa zata cimma ruwa ko yaya ne? Ni Khalid A Yakasai nake cewa a huta lafiya"
****
Numfashi Mutallab ke fitarwa a hankali jikinsa duk yanka saboda faɗan da suka yi da ƴan cikin gari bai san adadin mutanen daya sara ya fitarwa da jini ba, bashi da tabbacin ko bai yi kisa bama rabin fuskarsa duk yanka ne wani wajan har ya zame masa tabo. Goje shima cikinsa rauni ne da ƙyar yake fidda numfashi a hankali ya ce "Sun kashe Darma fa, ni ban ɗauka haka zuwa kamfel ɗin yake ba, wallahi sun kashe Darma na yi ƙoƙarin kai masa ɗauki amma ta kai nake"
"Goje"
"Na'am, Sarki"
"Nemi maɓoya" ya ce "Idan na ɓoye kai fa? Naga ba zaka iya tashi ba gwara ni ma kai ma da tuni sun kai ka kushewa, gashi wannan ɗan jakar Mangal ban san inda yake ba, balle a jira Ali wali a faɗa masa koda taimakon da zai mana"
"Wai baka jina idan ba ƙiyama kake shirin zuwa ba ka tashi ka face Goje" da sauri Goje ya miƙe ya yi kwana saboda ƙarar motar kwalawa da ya ji, Moh ya saka hannunsa a aljihu ya danna laya tuni ya ɓace a wajan.
Abbasa ta dinga kallon Mutallab kamar baya numfashi ta girgiza kawai ta kalli mai yi masa treatment ɗin bayan ya gama ya miƙe ta ce "Sannu da ƙoƙari" ya jinjina mata kai ya fice kawai. Ta yi shiru tana sake kallon Ɗan'malam.
Kamar yadda daddy ya buƙata Safiyyerh ta tare cikin part guda da yake gidan daga can baya, ita dai da to kawai take binsa sai kuma idanu ta yarda ba zai zaɓa mata abin da bai dace da rayuwarta ba, ta amince zata zauna da Captain Aliyu zata koyi son shi. Cikin sauri yake gudanar da komai kamar mai tsoran wani abu. A harabar gidan Aliyu na tsaye yana kallon Awais da yake cewa "Yaya ban gane tambayar da kake mini ba"
"Ya sunanka ma?"
Da mamaki Awais ya ce "Ikon Allah Yaya ni fa ƙaninka ne tsayin shekaru baka san sunana ba?" Aliyu ya haɗe fuska ba wasa ya ce "Kuma dole akai na haddace, seriously bana iya tunawa"
"To kai ne Baba captain Aliyu sai Junaid sai Dr Hash sai ni Awais sai Maama" "Ok, shi likitan wanne allura ya ke yi mata ban
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 17