akwai buƙatar na je, ina da meeting da ma'aikata ba zan jima ba" Ummi bata san damuwar Fiyya dole a hankali ta ce "Allah Ya tsare ki dinga kula ke dai macace ba namiji ba, kina lura da abubuwa da kike yi" Fiyya ta yi dariya tana yin waje ta ce "Kuma ki saka tsoron Allah a ran ki Fiyya ban da wulaƙanta jama'a, al'umma ta Annabi ce" Ummi ta girgiza kai kawai ta ce "Wato kin haddace kenan"
"Dole na Ummi"
Cak ta tsaya tana riƙe kan ta Ummi ta ce "Subuhanallahi Fiyya kina lafiya? Ba za ki haƙura da zuwa aikin nan ba?" Ta ɗan ya tsuna fuska da nuna alamar ba komai ta ce "Kawai na ji kaina kamar an saka mini shocking" gaban Ummi ya faɗi sosai sai bata nuna ba ta kama hannun Fiyya suka sakko ƙasa.
Dr Hash ne ya fito shima sanye da farar riga ta likitoci Fiyya na kallonta ta ce "Likita bokan ture, kuma fiɗe ku ɗinke"
"Kamar wasu mahauta" ta yi murmushinta mai kyau tana lumshe idanu "Barka da safiya Dr" ya yi mata murmushi "The whole Manager in the world" Ta buɗe ido shima ya buɗe kafin su ce komai J ya fito shima yana cewa "In the world mana, wannan kamfanin nan ku ina ne basu da reshe ni dai watarana zan zauna ki bani labarin kamfanin sosai na ji ai na yin wanda yake da shi" "Kai Yaya J nima ban san ko na waye" ya buɗe ido ya ce "Ban gane ba?"
"Da gaske nake Yaya ban san asalin me shi ba, kawai dai na san ni Manager ce"
"Ji nake Ashraf's father is the owner of the company"
Ta tura baki gama tana harar shi "Kuma ka sani kake tambayata" ya ɗaga mata gira ya ce "Zan zo ki nema mini alfarma wajan surukin naki nima ya bani ko messenger ne" bata kula shi ba. Ɗago kai ta yi suka haɗa idanu da shi yana zaune ya watsa mata harara yana ɗauke kan shi gefe "Aliyu ba yau zaka tafi bane" ya yi shiru a hankali kuma ba tare daya ɗago kai ba ya ce "A'a"
"Ok na ɗauka yau ne, ni wallahi duk firgitar dani kake mutum ba walwala kamar a filin yaƙi nan fa gida ne, amma kodayaushe kamar an yi maka dariya ko yaya ne ka dinga murmushi"
"Ban iya ba Ummi"
"Murmushin ne baka iya ba Aliyu? Ka gwada zaka iya" ya miƙe tsaye yana yin waje "Ban san yadda zan ba" "Ina kwana Captain?" Fiyya ta faɗa tana haɗe fuska ko inda take bai kalla ba ya yi waje abin shi. Shi dai J murmushi kawai yake yi halin Captain na bashi malam sosai suka jera shi da Fiyya suka fita. Mota ta shiga yana ɗaga mata hannu shima ya shiga tasa motar kowa ya kama hanyar wajan aikin shi. Fiyya na driving a nutse ta hangi wata mota na bin duk inda ta yi sai ta taɓe fuska ko a jikinta a fili ta ce "Ɗan wahala ko waye"
Daddy dake zaune bayan shigowar Ummi cikin parlon sama ya kalleta ya ce "Me kike cewa Ummi?" Ta damuwa ta ce "Kwana biyu ba a amshi maganin Fiyya ba, kuma kamar ciwon zai tashi" ya ajjiye littafin hannunsu yana saka glasses ya ce "Wani abin ya faru?" Ta numfasa yana faɗin "Irin abin da ya faru kwana ki tana jin kamar ana mata shocking a kanta, ni wallahi bana son ma ta dawo daidai bana fatan ubangiji ya ƙara gwada mini tashin hankali dana gani shekarun baya" Daddy ya jinjina kai "Nima addu'ar da nake a raina shi ya sa ma na matsu kawai a yi ai maganar auren nan, wallahi bana son Maama ta dawo old Safiyyerh"
"In sha Allah hakan ba zai kasance ba"
Meeting hall ɗin ya yi shiru sai muryarta dake tashi cikin faɗa tana ɗan buɗe hannayenta tare da yin baya ta ce "Wanne irin rainin wayo da hankali ne, file ɗin dana ajjiye shi a office ɗina ina jiran a kawo mini proof hujjar abin da aka fitar aka samu shigowar kuɗi zuwa asusun kamfani kamar yadda Accounter ya faɗa mini shine za a ce wai na yi signature a file aljana ce ni da zan taso da gida na zo kamfani na saka hannu, idan zan saka me ya sa ban yi ba tun da file ɗin ya zo table ɗina?" Ta miƙe tsaye tana kallon su gabaɗaya duka maza ne ita kaɗai ce mace ta koma ta zauna tana juyi a kan kujerar "I need to find out the truth, meke faruwa a wannan kanfanin. Md da kai da secretary za ku kai ni na duba ko'ina a wannan kamfanin yau ɗin nan, kai kuma Director ka kawo mini record ɗin komai daga watan daya shige zuwa yau ɗin nan, ina buƙatar statement yanzu a office nawa" ta sauke numfashi fuska a haɗe sosai "An gama" secretary ne ya kalleta kamar a tsora ce yake ya ce "Manager akwai baƙi da suke jiran ki"
File ta ɗauka ta miƙe tare da ficewa daga cikin meeting hall ɗin. Bata nufi office ɗin ta ba inda suke ganawa da baƙi ta nufa ta tura office ɗin a hankali a hankali ta yi sallama ta shiga. Manyan mutane ta gani su biyu zaune a kan kujera kana ganin su ba sai an yi magana ba ta zauna kan kujera mai cin mutum biyu a ladabce ta ce "Ina kwanan ku? Welcome to FS WORLD INVESTMENT COMPANY i am Safiyya A. Marafa how can i help you?" Wani rushehen mutum ne daya Hakim ce a kan kujera ya dinga kallon ta kamar zai haɗiye ta idanunta dai na kan system tana ta dannawa da aikin tura saƙo can ta ɗago kai suka haɗa idanu ta sake kame fuska ta ce "How can I you? Ta ya ya zan iya taimaka muku"
"Ba ki gane ni ba"
Sarai ta gane ko waye ta ce "Yau na taɓa ganinka"
"To ma sha Allah. Sunana Hon Maɗatai zan saka hannun jari ne a cikin wannan Company"
"Ok, me kake buƙata?"
Ya gyara zama sosai ya ce "Za a dinga bani shinkafa, suger, wake a kan farashin yadda Company yake siyarwa ni kuma zan ɗora kaso 50 domin cin riba amma daga lokacin Company ba zai sake siyarwa da kowa kaya ba sai ni" Fiyya ta dinga kallon shi sosai a ranta tana mamakin son zuciyar wasu ya suke so talakawa su yi da ran su ne? Burin shuwagabanni talaka ya faɗi ya mutu saboda yunwa? Ta yi jim sai kuma ta ce
"Da wata ce matsayin Manager ba Safiyya A. Marafa ba do wataƙila ka samu wannan damar a yanzu ina maka murna da cewar we're not interesting anymore, da wannan zai fi kyau ka buɗe naka masana'antar ka nemi matasa marasa aikin yi wanda suke lalacewa ka basu abin yi" ya dinga kallon ta can ya ce "Kin san waye ni? Ƴan'mata ki bi a hankali fa"
"Ai ba a yi wa Fiyya maimaici Hon Maɗatai ba zamu baka hannun jari ba You can leave" ya miƙe tsaye yana jin ba'a taɓa yi masa wulaƙancin da yarinyar ta yi masa ba "Safiyyerh ko? Ki bi a hankali haɗuwar farko ce wannan, zan tafi amma zan dawo"
Ficewa ya yi rai ɓace zuciyarsa na zafi. Fiyya ta ɗauki kayanta ta nufi office. A hankali take bin bayan Md da Secretary ɓangaren kayan abinci aka kaita kana da mai daga can baya wajan shara inda ake ajjiye bukar kamfanin ta dinga jiyo wari da sauri ta nufi wajan Md ya ce "Manager sharar kamfani ce nan" bata kula shi ta nufi wajan sharar tana rufe hanci da f facemask kamar an ce ta juya idanunta ya sauka akan yatsun hannu guda huɗu da suke a leda ƙuda na bin su.
Tunda ya nufu layin su tiger na biye masa baya hannunsa riƙe da gora yara suke watsewa sai waje ake bashi hatta almajirin Malam sai da wasu suka bar wajan banda Ɗanyaro dake zaune yana danna sabuwar wayar daya siya sosai Malam yake ji da shi yanzu lokaci zuwa lokaci yake yi malam alheri na kuɗi ga nama da yake kawo masa, sai dai cikin dare Ɗanyaro zai lallaɓa ya gudu ba zai dawo ba sai safiya. Moh na ƙoƙarin shiga gidan Malam ya tare ƙofar ya ce "Na haifi yaro sunan shi Muɗallabi amma yanzu bani da wannan yaron na bar wa ƴan iska shi da ƴaƴan banza tunda ya zama shaiɗani ba zaka ja mini masifar da zan mutu a gidan ɗan kande ba" Moh zuciyarsa ta fara tafasa har wani hayaƙi ke fita ta cikin bakinsa ya dinga kallon asawan nasa ya kasa cewa komai ya leƙa surar gidan ko zai ga Ammo amma sai Inna Binta dake suɗe tukunya tana faɗin "Matsalata ɗaya a duniyar nan abinci idan na ci na ƙoshi Mufee ta ci ni fa ko a jikina" Juyawa Moh ya yi kamar zai yafi sai kuma ya nufi saman katanga ya kama ya dire ta cikin gidan Inna Binta ta zabura tana faɗin "ƙulna naru ƙulni bar dan wasalamun Allah Ibrahim, auzubillahi" jikinta sai rawa yake masifar tsoron Mai dawa take kamar ran ta sauran jama'ar gidan duk suka shige ɗaki banda Mufee da ta yi tsaye tana kallon shi sosai idanunsu yake iri shi bai san wace ita a gidan ba, bai damu daya sani ba yara ne kamar yaƙi wasu iyayensu basa cikin gidan.
Labulan ɗakin Ammo ya ɗaga ya ganta zaune tana ninke kaya ya fi minti goma tsaye kamar zai juya sai kuma ya shiga cikin ɗakin idanunsa akan kwanon abinci sosai yake jin yunwa idanunsa na rufewa ya miƙa hannu zai ɗauki abincin Malam ya ce "Kana ci zan maka Allah Ya isa ka tashi ka bar mini gida tsinannen yaro" da sauri Ammo ta kalli Malam sai kuma ta ɗauke kai.
Jikin Moh ya fara rawa jijiyoyin kansa na mimmiƙewa jin uban daya kawo shi duniya na yi masa Allah Ya isa ya yi ƙasa da kansa idanunsa kamar za su fito waje ya ji babu abin da yake buƙata sai ƙwayar da Mangal ya bashi ya sha, ita kawai zata sauke masa abin da yake ji ya manta da komai, yaushe ne zai zama daidai kamar kowanne mai rai an ci zalin shi an lalata masa rayuwa. Ya miƙe da sauri yana banko ƙofar ya yi waje "Sallamammen yaro Allah dai ya rabani da ƙaddara na huta"
Kai tsaye Moh dabarsu ya nufa yana zuwa suka mimmiƙe Darma na faɗin "sai godiya Mai dawa sarki mai jeji, wani ya ce ba kai ba yanzu mu fito mu yi farfesun hanjinsa"
Yanayin fuskar Mai dawa a bar tsoro ce ya takure waje guda yana jin kamar zuciyata zata fito waje don baƙin ciki. "A sama yake ku bashi sha fara kaga aljan" cewar Darma Mangal ya girgiza kai ya ce "Ba za ta yi masa ba, kawai a yi masa allurar fenta"
"A'a ta yi masa girma yaushe ya faɗo sabgar kar ka luda masa ya yi mana na jakuna yanzu" zaro sirinjin ya yi Moh ya ƙurawa siririn idanu ganin yadda Mangal ke zuƙo ruwan ciki ya fara girgiza kai da ƙyar ya ce "Kar ka yi mini Ka bar ni da tunanin bana son mantawa" kokawa suka fara yi da shi ya ɗauki Darma ya buga da ƙasa Mangal ya faki idanunsa ya caka masa allurar a gadon baya. Jinjiga ya fara sosai cikin ƙaramin lokaci ya yi shiru yana jin shi kamar a samaniya yana yawo yanayin ya yi masa daɗi sosai ya ji zuciyarsa wasai a wannan yanayin bacci ya ɗauke shi. Can cikin dare ya farka kam shi ya yi masa nauyi har yanzu bai dawo daidai ba, babu komai a cikinsa ya miƙe tsaye yana layi kamar zai faɗi Mangal ya ce "Mai dawa"
Ya yi masa shiru yana ɗaukar wuƙa ya soke ya ɗauki fitila ya riƙe "Dare ya yi ba, kana fita waɗancan ɗankokin za su iya kama ka gashi babu da goge a hannu ka zauna, kasan kuma ƴan cikin gari sun shigo sun samu labarin mun yage musu poster bama wannan ba ɗazo an ga gawar wani to ana tunanin mu ne kuma yaron ɗan cikin garin ne fansa suka zo ɗauka,na bibiyi abun shi yaron ƙwacan abar magana ya yi jama'a kuma sun fara ɗaukan doka a hannunsu suka rufe yaron da duka har ya mutu. Su Cokali kuma ba za su haƙura ba kar muna zaune su ci mu da yaƙi"
"Sai godiya"
Ya furta da ƙyar daga nan sake yin shiru yana shirin barin wajan kamar zai kifa "Ina zaka ne? Ka dawo ka kwanta"
"Kai fa ba Malam zan haɗaka da Rainbow"
"Shikenan ina zaka yanzu" ya cije leɓe zuciyarsa na ayyana masa abin da zai yi shi ne daidai allurar sai gaibu take faɗa masa a hankali ya ce "Zan kashe Malam ya baza lahira"
For more information
08164069385
WhatsApp only
[1/7, 9:32 PM] Sis Fauzy: *❤🔥 MUTALLAB ❤🔥*
Page 6
*Bright pens... 2nd batch*
*🔞for the adults and criminal side please 🔥 just take it as a lessons*
Goje daya farka daga bacci ya yi saurin miƙewa yana furta "Malam ɗin zaka kashe mahaifin naka?" Ya yi shiru bai yi magana ba, yana sake riƙe wuƙar a hannunsa da kyau duk jikinsa rawa yake, ga wani irin ciwo da kansa yake yi masa sosai, idan ya tuna abubuwan da aka aikata masa sai ya ji zuciyarsa ta bushe ta kuma ƙeƙashewa. Ya saka ƙafa ya banga je Mangal dake tsaye zai shige Goje ya yi saurin shan gabansa yana ɗaure fuska sosai ya ce "Saboda kana jin kanka a sama ta bakwai kake jin komai za ka iya yi? Me ya sa ba zaka yarda sarki sammai ke yin komai ba, mu fa ba haihuwar ta zubar bane ko yaya ne mun san abin da ya dace kashe mahaifinka ba shi ne mafita ba Mai dawa" ya ɗaga jajayen idanunsa kamar zai ci babu yadda ƙwaƙwalwarsa take faɗa masa ba daidai haka komai na duniyar yake yi masa babu daɗi maƙoshinsa na yi masa zafi da raɗaɗi wani abu ya tsaya masa da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya ce
"Ya zan yi?"
Kai tsaye Goje ya ce "haƙuri, ka bi komai a sannu mai dawa ita gaggawa aikin ƴan annaru ce. Kashe Malam a yanzu ba zai rage maka kashi goma a cikin ɗari na damuwar da kake ciki ba, iya wuya iyaye ne su"
"Ba iyaye na bane, ka bari ko ɓalli-ɓalli na yi masa" ganin da gaske shirin tafiya ya ke yi ya ce "Idan kaga ka bar wajan nan sai dai ni za ka fara kashewa" Ya ƙuri da idanu yana kallon Goje har wani hayaƙi ke fita ta cikin bakinsa ya wani cije gefen baki yana karkatar da kai gefe. Kamar wasa Goje ya ga Moh ya nufe shi da wuƙar shima yaƙi matsawa yana ganin kamar wasa ne yana ƙoƙarin kawai Goje sara su kaga mutane kamar daga sama sun zagaye su. Moh yaƙi motsawa sai Goje da ya yi baya ya cake yana zazzaro idanu tare da ɗaga gora sama. A kallon farko Mai dawa ya gane cinnaku ne ƴan'sanda sai ya ɗauke kai shi Goje bai faɗa da labarin ba saboda shigar fararen kaya suka yi.
"Eng Ali wali ya aiko mu wajan ku kawo muku kaya" sai a lokacin Mangal ya ƙarasu yana tale ƙafa ya ce "Kaya sun sauka da zafin su kenan yallaɓai, amma eh kun razana mu shigowa ba notice sai mu ɗauka dire aka yi mana" ɗan'sandan ya yi murmushi kawai ya ce "Kuna da kamar Ali wali za ku ji tsoro? Kune matasan da yake ji daku a yanzu musamman wannan da naga ko kallo bamu ishe shi ba" Goje ya juya ya kalli Mai dawa da yake kallon wani sashi daban alamar baya ma jin me suke cewa "Mai dawa sarki me jeji wajanka aka aiko mu domin aikin bana yara bane"
"Faɗi"
Moh ya ce yana bada faɗi ba tare daya kalli da ɗan'sandan ba. Abu ya fito da shi a jaka ya miƙawa Mangal ya amsa ya ce "Ka a dana kada a je a yi ta sha ana ɓarna, Eng Ali wali ya ce akwai fita ta musamman kuma ƙauyen da za shi basu da kirki dole tafiyar sai daku a ranar zaku cake ku bawa samaniya yazo ta yi hadari" Mangal ya buɗa ya ce "Dar hakan ya yi mana, sai Eng Ali wali ko ana su ko ba'a su ya zama dole don uwatar" Police ɗin ya juya kan Mai dawa a hankali cikin magana mai muƙamin ya ce
"Ka taɓa jin mai suna Scorpio?"
"Wa?" Goje ya ce da sauri yana kallon Mai dawa da sai a lokacin ya juyo ya kalli Jafar shima Jafar ya kalle shi da kyau ya ce
"Akwai matsala ne babba, Scorpio yana yi wa Eng Ali wali barazana, yana da babbar hujjar da zai iya kawo masa matsala a mulkinsa kuma babu shakka ko waye Scorpio akwai alamar ya shirya fito na fito da Eng Ali wali, to muna jami'ai ba zamu bari ba tunda a jikin shugabannin da ƴan dabarun mu muke samun namu rabon. Ali wali yana buƙatar ka taya shi gano waye wannan Scorpio da sunan shi kawai ake ji ba kamanni"
"Kamarya kenan?"
Mai dawa ya tambaya a taƙaice yana jin ƙirjinsa na buɗewa saƙo ya fara isa kenan a fili kuma ya sha kunu sosai. Jafar ya dafa kafaɗar Mai dawa ya ce "Kamar kai yanzu kowa ya san sunanka Mutallab inkiya Mai dawa saɓanin shi da sunan Scorpio kawai muka sani, babu wanda Eng Ali wali ya yarda da shi sai jami'an Dss ka baza jama'arka su tayaka binciko asalin waye Scorpio akwai kyauta mai yawa idan hakan ya tabbata, kuma ya ce ka faɗi kome kake so zai baka"
Wani irin kallo Moh ya dinga yi wa Jafar na kan kaga biri, biri ya ganka kifi na ganinka mai jar koma sai kuma ya ɗaga kai sama yana kallo sama cikin kumburarriyar murya ya ce "Bayan Dss da shi uban gidan naku waye ka ji yana neman SCORPIO?" Jafar ya ce "Me ya sa kake tambaya?"
"To kuje ku yi aikin da kan ku" ya faɗa yana juyawa cikin sauri Jafar ya riƙo shi ya ce "ka dinga sassautawa zuciyarka da fushi. Bayan Dss akwai jami'ai mafi hatsari da suke neman shi idanu rufe FID Federal investigation department, basu da imani wannan mutanen jami'ai ne da ba zaka taɓa tunanin ta ina zasu cimmaka ba, suna iya zuwa a suffar mahaukata ma ko mai neman taimako, su kakkarya mutum ko su kashe shi ko haukata shi ba wani abu bane a wajan su"
"Suka kasa kama Scorpio?" Jafar ya watsa hannu ya ce "Sannu sannu da zarar sun gane kamanmin su, babu mamaki su ɓullo ta wata hanyar kafin hakan ta fara ka ruga su kai hari,mun gama magana da kai Mai jeji" ya yi shiru bai ƙara cewa komai ba "Ka yi shiru?"
"Ka bada sha ɗayanka, zamu jauwalo ka idan akwai sagi" cewar Goje Jafar ya girgiza kai "Ka bar shi ya yi magana" Moh ya sake kame fuska babu wasa kuma yaƙi cewa komai sai ma fito daya fara yi yana kallon bindigar dake hannun ɗaya ɗan'sandan. Bisa dole suka juya suka tafi ba tare daya tanka su ba,daman Goje ya san ba maganar zai yi ba. Goje ya juya ya kalli Mangal da yake zuƙar wiwi a hankali ya ce "Ka raina musu hankali waye Mai dawa waye Scorpio"
"Ni ne, MUTALLAB TAHHB SCORPIO"
Mai dawa ya ce yana zare idanu waje manya gwanin tsoro da razani har sai da Goje ya ja da baya don bai taɓa ganin halittar idanu kamar ta Moh ba ƙwayar ta juye kamar bata mutane ba kuma sai ƙara ware manyan idanun yake yi.
"Akwai matsala Moh idan suka gano cewa kai ne Scorpio, za su yi maka illa gwara ka ɓace kawai daga yankin kafin komai ya sarara" "Gawata za su iya gani su haƙura da nema na" Ya furzar da iska daga cikin bakinsa kansa ya yi masa nauyi
"Goje an yi sake tunda aka bari na je state cid,ba san komai ba amma a fitar dani. Zan iya haƙura da komai banda abin da yake damuna a zuciya ni da kai na zan bayyana cewa nine Mutallab Tahhb Scorpio da zarar na cika muradina na abin da na yi niyya"
"Mai dawa"
"Sai godiya"
"Ina tunanin ka haƙura ka bar wa Allah komai duk zamu baza mu je gare shi ya yi mana eh hisabi" Moh ya taune harshe yana kaɗa leɓe tare da saka harshe ya kashe wuƙar dake hannunsa "Zafin nake ji a zuciyata zan yi ɓarna, zan sha jini"
"Kamar wani maye? Shi Ali wali ɗin me ka yi masa ne?"
Mai dawa ya ja idanunsa ya lumshe ko yaya idan ya yi shiru sautin kuka biyu yaje ji a kunnen shi, tare da jiyo ƙarar wutar dake cinye jikin nata hakan ya saka baya iya runtsawa idan ba wani abu ya afa ba haukwata shi ake son yi. "Na yarda da kai Goje, ka ci amanata askira zan saka maka a maƙoshi" "Ni ɗan halak ne. Yanzu ya batun Manager ɗin? Ka santa ne na ji baka bashi amsa ba" jin ya yi shiru ya saka shi cewa
"Ko dai ka san Managern kamfanin?"
"Karka ka daman"
*****
Fiyya na zaune a saman gadonta tunda ta dawo take kwace tunani ne fal a cikin zuriyarta ga wani irin tsoro da bata taɓa jin shi ba, a karo na farko ta ji tana son sanin komai da komai na Kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY, da duk mutanen da suka saka hannun jari a ciki data rufe idanunta yatsun hannun take ganin da aka yanka aka zuba cikin leda sosai taga rubutu jikin ledar amma ta manta bata duba ba. Ta juya a hankali tana kallon wayarta kamar mai tunanin wani abu kuma sai ta ɗauki wayar tana dannawa numbersa ta kira aka danna line busy. Har zata ajjiye wayar sai ta ji an kira ta zubawa sunan idanun kafin ta ce.
"Ashraf..."
Kiran ta ɗaga ta kara a kunne ta yi shiru ta cikin wayar ya sauke numfashi da ƙyar muryarsa a hankali.
"Na ji tsoro Fiyya" ta ɗan tura bakinta gaba kamar yana kallonta muryarta mai daɗi ta ce "He said he was scared" ya ƙara fidda numfashi kamar tana gabansa "Maama kina wahalar dani da kika zaɓi aikin nan na kusa mutuwa, na ji ba zan iya barin ki ba kuma ke ce dai wacce nake so Fiyyar nan tawa"
"Ba na ce ka daina ce mini Maama, why not Fiyya kawai?" Kamar mai raɗa a hankali Ashraf ya ce "I am sorry bestie me"
Dum! Haka ta ji kan ta ya yi masifar sarawa da sauri ta dafe kan nata tana jin kamar wani abu na janta a gigice cikin faɗa ta ce "Karka sake kira na da wannan sunan" ta cikin wayar ya ce "Ba zan sake ba amma lafiya kike? Yanzu kike mini magana cikin soyayya Fiyya me ya sa sometimes kike abu kamar bake ba? Are You okay?"
"Kai na ke ciwo"
Tana cewa haka ta kashe kiran ta cillar da wayar nata zuwa gefe guda. Da sauri ta miƙe babu ko hula a kan gashinta yana tashi sama tana dafe da kanta bata ganin ko gabanta duhu ne a cikin idanunta haka ta dinga sauka akan matattakalar benen. Karo ta yi da mutum cikin sauri ta kama hannunsa tana ɗorawa a kanta "Yaya J kai na zai cire wani abu nake ji, ciwo yake mini kamar ana jana" gabaɗaya ta rikice ta ƙanƙame shi har zufa ke tsattsafo mata.
Kama hannunta ya yi ya jata saman kujera taƙi sakin shi ya zauna a hankali tare da zaunar da ita ta yi saurin ɗora kanta a cinyarsa ya riƙe mata kan yana murza goshinta nata very careful kar ta ji zafi. Sun jima kana ta shiga sauke ajjiyar zuciya numfashinta na sauka ya ɗan leƙa fuskantarta yaga bacci take ya saka hannu ya juyo da fuskarsa yana zuba mata idanu ya riƙe hannunta har lokacin bai ce komai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 17