ba.
"Aliyu"
Da sauri ya saki hannun nata yana zame ta ya miƙe tsaye Ummi ta kalli Fiyya ta kalle shi ta ce "Ita kuma lafiya take bacci a nan? Yaushe ta shigo gidan ai lokacin tashi bai ba?" Captain dai ya yi shiru ta juya ta kalle shi sosai ta ce
"Lafiya take?"
"Ban sani ba"
"To ya naga kana haɗe rai duka zaka kawo mini me kai komai naka babu walwala Aliyu ka dubi girman Allah ka dinga murmushi shifa yin murmushi sunna ne ta ma'aiki" ya shafa kan shi yana zuba hannu a aljihu cikin gaskiyarsa ya ce "Ban iya ba wallahi Ummi ki koyan"
"Shi murmushin? Allah ya rufa asiri to wannan matarka ta shiga uku" yana dai tsaye bai ce komai ba. "Maama?"
"Ummi"
"Maama ta shi yammaci za ki yi ƙunci ko ciwon kai idan kikai bacci" ta buɗe fararen idanunta suka haɗa idanu ta sha kunu sosai tana tura baki ya zabga mata uwar harara ta yi baya zata koma baccin.
"Kee" ya kira sunanta ta buɗe idanu "Tashi kafin na yi balle da wannan silar ƙafafuwan" miƙewa tsaye ta yi ta murguɗa masa baki bata ce komai ba shi kuma ya yi kamar zai juya ya damƙo hannunta ta ƙwalla ihu daidai nan Daddy ya shigo parlon cikin sauri ya sake ta.
"Da kyau Soja gwara ka nuna ƙarfinka akan ɗiyata, yanzu zaka tattara ka koma inda ka fito"
Captain ya juya ya bar parlon gabaɗaya yarinyar haushi take bashi har zuciyarsa. Daddy ya kalli Fiyya ya ce "Maama, yaushe za ki girma ina ganin wawtar wanda ya ɗauki muƙa min Manager ya ba ki wallahi"
"Daddy kune kuke raina ni wallahi, na girma am matured enough" ya girgiza kai kawai kasancewar t.v. na kunne aka fara karato taƙaitattun labarai. Sunan Scorpio aka fara ambata matsayin wanda jami'an tsaro na hukumar FID Federal investigation department suke nema idanu rufe. Dake t.v a hankali ta juya ta kalli mai karanto labaran matashin ɗan jarida dake aiki a gidan t.v na VOA juyawa ta yi ta ce "Daddy ɗan bani aron wayarka"
"Ki yi me da ita?"
"Wayata zan kira, ina son fita ne wajan Kinal" ya miƙa mata wayar ta ɗan jim tana ɗaga hannunta tare da copy na wasu numbersa sai kuma ta miƙa masa bayan ta yi deleting tana murmushi "La la la na tuna inda na sata"
Ya kalli t.v ya kalleta ya kuma kalli wayarsa, ya dai amsa a ransa yana mai jin tsoro da mamakin kaifin tunanin Maama. Ummi kuma ta ce "Ayi ta neman mutum kamar kiyashi shi kuma ya rasa sunan da zai sawa kan shi sai kunama?" Daddy bai yi magana ba Ummi da abin ke ta cinta ta kalli Fiyya dake shirin haurawa sama ta ce "Maama ta shi me ya yi ne?"
"Ummi ina zan sani, idan kika ɗauke yadda ake juya biyar ta zama goma ba abin da Fiyya ta sani" tana cewa haka ta haura cikin sauri tana nanata numbersa dake kanta cikin sauri ta yi wanka ta shirya cikin abaya ta yi rolling tare da fesa turare sauri-sauri take a haka ta sakko hannunta riƙe da waya ko jaka bata ɗauka ba. Daddy ya dube ta ya kalli lokaci "Wai zuwa wajan Kinal baya tashi sai yamma? Ita Kinal ɗin nan ta dinga zuwa mana zai fi"
"Daddy ba jimawa zan yi ba, na jima ban je ba mun gaisa ba"
"Maama bani da nutsuwa haka kawai idan kika fita gari ya hargitse bani number Kinal ɗin nan na kira ta" kafin ta yi magana J ya yi saurin ƙwace wayar Fiyya ya ce "Bari na kira maka ita Daddy" babu sunan Kinal a jerin wanda ta yi waya dasu yau cikin sauri ta amsa ta ce "Number Kinal a kashe yaje fa J wai ni yarinya ce na san yadda zan kare kai na no body can come and hit me" Ta kalli Daddy da Ummi ta juya ta kalli J ta ce "To tsoran na mene ni Safiyya A Marafa?"
"Allah Ya tsare Maama jeki" amsawa ta yi da amin ta raɗawa J kunne "J akwai gulma yau bari na je na dawo" tana fita harabar gidan mota ta shiga ta yi mata key cikin nutsuwa dake driving har ta fita ganin ta hau kan titi ta dubi bayan motarta ta cikin gilas wata ajjiyar ta sauke mau nauyi ta rufe idanunta ta buɗe sai kuma ta ɗauke hanyar ta nufi wani titin daban a zuciyarta addu'a take yi sosai.
*****
Eng Ali wali na zaune a parlo cikin wani gidansa da yake ganawa da ƴan siyasa masu mara masa baya a kujerar shi. Ya dubi CSP chief Superintendent of Police ya ce "Ina son ku ɗauke idanunku akan yarana, ko me kuke buƙata zan baku idan ɓarna sukai zan ji da komai" Csp ya ce "Hon yaushe za mu cigaba da zuba idanu ƴan dabarka suna yin yadda su kaga dama a garin nan musamman a unguwar Birget gashi lamarin na shirin haddasa faɗa tsakanin ƴan cikin gari da su ƴan Birget, mu jami'ai ne mun san gaskiya muke take ta"
"Ku cigaba da takewar su wannan yaran suna da wa'adi dana samu na ci zaɓe ko inuwata babu mai gani a cikin su. Don haka ku rufe idanunku a toshe kunnuwa, zuwa gaba har matsayi zan saka a ƙara maka mu yi ƴan dabaru" CSP ya jinjina kai Eng Ali wali ya ɗakko kuɗi mai yawa ya miƙa masa yana cewa "Idan kun kama masu dilar ƙwayoyi da kayan maye na san ana miƙa su hannun NDLEA ko? Ka tabbatar ƙwayoyin na zuwa wajan Jafar shi kuma zai bawa yarana, kar ka sake sunana ya fito daman ai ƴaƴan asara ne ko an kama su ba za su taɓa furta ni suke yi wa aiki ba, lastly magana akan Scorpio ɗin nan yana neman bani ciwon kai bana son ya zama damuwata, idan F.i.d suka riga ku kama shi akwai matsala"
"Karka damu hon mun zuba yaran mu ta ko'ina"
Eng Ali wali ya ce "Lallai Scorpio ya zo hannu kafin zaɓe"
Cikin sauri Fiyya ta fito daga cikin motarta tana shiga cikin wajan data zo a reception ta tsaya na wasu mintina tana zaune ta fito tana murmushi ta ce "Ikon Allah kamar tare kuke?" Fiyya ta buɗe idanunta sosai ta ce
"Wa?"
"Captain yayanki"
Gabanta ya faɗi ta kasa cewa komai Kinal ta zauna ta ce "Wallahi zuwan shi biyu fa, nima dai na yi mamaki amma ya ce aiki yake dubawa shi ne ya leƙo mu gaisa har ma na tambaye shi ke sai bai bani amsa. Amarya ya kike ya sabgogi"
"Good. Yanzu lokacin ku ne Kinal siyasa ta matso ana ta fama da habaice-habaice"
"Kamarya habaici?"
Fiyya ta cire gilas ɗin idanunta ta ce "babu abin da mawaƙa suka iya sai habaici wallahi ku zagi wanda kuke so kuma ku yabi wanda ku kaga dama" Kinal ta yi murmushi ta ce "A'a ni ba ruwana idan an kira ni dai waƙa ina yi amma ai ni ta soyayya nake yi tunda a nan na fi kauri, ina nan ina shirya miki ke da Ashraf" Fiyya ta sauke numfashi ta ce
"Ina cikin matsala Kinal ban so faɗawa kowa ba wallahi"
"Subuhanallahi matsala wacce kuma? A kamfanin ko gida ko wani wajan?"
"Kema kin san a gida ba wanda zai mini komai sai mai baƙin halin nan, tunda ya dawo ya uzzura mini ko parlo bana fitowa mutum sai baƙar zuciya ɗan wahala kawai aikin kawai" Kinal dai ta zuba mata idanu kafin ta ce "Mene damuwar?"
"Kwana biyu da suka shige ana bibiyata kullum idan na fita, harta nan wajan da na zo sai da aka biyo ni, ni ba damuwata kai na ina tsoron su Daddy su sani kin san abu idan ya same ni tashin hankali suke shiga. Kinal ban san su waye ba me kuma suke buƙata saboda bani da issues akan kowa wallahi na ji kawai ina son sanin wanda ke following nawa duk inda na je gwara mu yi fito na fito da shi, da na ce ko na yi hayar ƴan daba nima suna take mini baya?" Kinal ta buɗe idanunta sosai ta ce "Daman na fara zargin kina da taɓin hankali Fiyya, ke yanzu ina kika san inda ƴan daba suke bare ki je? Bakya tsoro ko shakka ai matsalarki police ne wannan ina ganin a gayawa Captain kawai" tsaki Fiyya ta yi tana miƙewa tsaye "gwara duk abin da zai same ni ya zaman da dai na faɗawa Captain ni ina da abin yi" "Ƴan daban za ki yi haya yanzu kenan?"
"E" sai kuma ta koma ta zauna cikin nutsuwa ta kalli Kinal ta ce "Akwai abubuwan da bana ganewa kwana biyu kamfaninmu ina son na yi bincike duk abin da na samu ba daidai ba wallahi sai na kaiwa hukuma Kinal yatsun hannun mutum na gani a cikin kamfanin fa?" Kinal ta zare idanu waje ta ce "A'a ki fara samun mai kamfanin ku yi magana dashi tunda ke ce Manager" "Sai yanzu na fara tunani, i wonder aka bani Manager a kamfanina bayan akwai maza da yawa sosai da na yi tunanin ko experience ɗina ne yanzu kawai na ji ina zargi"
"Zargin me?"
Ta ɗaga kafaɗa ta ce "I don't know, na fara bincike dole zan gano gaskiya" Kinal ta ce "To ki bi a hankali Please Fiyya we care about you ni ma zani anniversary na makarantarmu FGC dana shigo Kamfanin gobe, har waƙa na yi mana yanzu haka wani Eng Ali wali na yi wa waƙar da aka saka ni" shiru Fiyya ta yi tana nanata sunan FGC a ranta "Na ji kamar na san makarantar nan fa"
"Ke da ba ita kika yi ba ina za ki sami, ni a can na yi secondary school kinga"
"Haka ne bari na je"
"To ki kula Please kar ki saka kan ki cikin matsala don Allah Fiyya" murmushi kawai Fiyya ta yi tana ficewa daga cikin studio ɗin.
*****
Kamar an cillo shi haka yaga Mai dawa ya faɗo masa cikin office ɗin nasa da yake tare da manyan mutane sosai tun kafin ya yi magana ya ce "Kowa zai iya tafiya" duk suka fice ya ɗaga kai ya kalli Mai dawa ya ce
"Ka daina zuwa ina nake ni zan dinga neman ka"
"Ka yi ƙarya"
"Ni nake maka ƙarya Mai dawa?" Ya wani haɗe fuska tamau fuskarsa ɗauke da sabon yankan da aka yi masa jiya har yanzu ba'a gyara ba. "Kai ai ba Malam Abdullahi bane da ba zan ce kana ƙarya ba"
Eng Ali wali ya jinjina kai ya ce "Me ya kawo ka yanzu? Har cikin office nawa"
"Ka saka ni aiki har biyu, da kamo maka ɗawar can da nemo Scorpio" ya shagiɗar da baki gefe ya yi fito wanda ya cika office ɗin sosai "Na je gidan asawanta jiya"
"Kana nufin gidan Abdu Marafa?" Ali wali ya ce yana miƙewa tsaye cike da tsoro Mai dawa ya ɗaga ƙafa ya ɗora a saman table ɗin gaban Ali wali "sharaɗin kawo maka ita barewar shi ne mallaka mini kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY, aikin Scorpio kuma ka saka cinnakunka cire hannu daga sabgar ka bar mini ni zan nemo maka shi, bana haɗa aiki da wasu"
Ali wali ya ce "Mene haɗina da kamfanin nan? Karka saka ni rigimar da tafi ƙarfina da ka san ma'anar abin da FS WORLD INVESTMENT COMPANY yake nufi ba zaka haɗa kan da shi ba, wannan Kamfanin ciwon idanu ne" Mai dawa ya ce "Ni Mutallab Tahhb ɗan babana Abdullahi da inkiya Mai dawa bana harin abu na haƙura, wannan kamfanin shi ne burina" Ali wali ya goge zufa ya ce "baka san kamfanin ba shi ya sa a ba ki yake maka wahalar faɗa ni Ali wali sabgar siyasa na sani na saka gaba, ka bar ni a haka ba zaka saka ni a masifa ba"
"Waye mai kamfanin?"
"Sannin hakan daidai yake da tunuwar asirin manyan mutane da dama, ka bar komai yadda ka sani" jinjina kai Mai dawa ya yi ya ce "Zan maka jahilanci ne, ka riƙe amana ka bi sharuɗan da na ce zan maka komai ni ɗan daba ne kai mai neman iko da muƙa mi ni na sare na kashe mu bauta maka shi ne. Batun kamfanin zan yi bincike da kai na, kar ka zama butu don wallahi sai na yi maka daƙiƙanci"
"In sha Allah, daga nan har bayan zan yi maka komai"
"Dar zan doƙa yanzu sai godiya"
Yana fita Eng Ali wali ya ɗauki waya ya kira Csp ya ce "Waye Mutallab yaron da ya fito daga wajan state cid kwanan nan bayan ya yi shekaru uku a wajan su" ta cikin wayar Csp ya ce "Sunan shi dai Mutallab ya kashe matarsa aka aka kama shi, daga baya kotu ta sake shi a zama na ƙarshe ba wanda ya san dalili" Ali wali ya kashe wayar yana sauke numfashi a fili ya ce "waye MUTALLAB?"
For more information
08164069385
WhatsApp only.
[1/7, 9:32 PM] Sis Fauzy: *❤🔥 MUTALLAB ❤🔥*
Page 7
*Bright pens... 2nd batch🔞*
The door is open... Ga masu buƙatar ayi musu tallah. Na hango wasu ƙwailaye a conversation group da Mikiya writers 😛Maman Sayed ta ce a faɗa muku akwai maganin gargajiya cikin sati guda komai zai kankama haɗaɗɗan maganin da Fiyyar Ashraf ke amfani da su ta ce a baku numberta ba... 08063114606
Washegari da safe Fiyya na ƙoƙarin buɗe ƙofa ta fito da nufin zuwa office ya rigata buɗe ƙofar, kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kan ta zuwa gefe a hankali kuma can ta ce "Ina kwana?" bai amsa ba sai cewa da ya yi "You told Abba za ki wajan wata, amma kin yi ƙarya ina kika je?" Manyan idanunta ta ɗago ta kalle shi ta ce "Ƙarya kuma?" Ya rufe ƙofar ya tsaya "Idan kina yi mini kamar ba ki gane ba, kwaɗa miki mari zan yi maybe it will help you to understand it very well" ita mamakin shi take yi "Ni fa Manager ce business zai iya fitar dani ko'ina" ya buɗe mata manyan idanunsa sosai sai kuma ya ce "ina kika je" ta tura baki gaba sosai ta yi gefensa za ta shige ya saka hannu ya fisgota kafin ta yi motsi ya ɗago fuskarta ya wanka mata mari ƙwayar idanunsa tamkar zata fito waje yana ihu a saman kan ta ya ce "Idan na sake maimaita miki tambayar sai na tabbatar yatsun hannuna sun kwanta fuskarki"
"Sai dai ka kashe ni" ta yi maganar ko gezau gefen fuskarta ya yi jajur dakakkiyar zuciyarta kuma ya saka ta nuna ko a jikin ta, ƙasan zuciyarta kuma wani zafi da raɗaɗi take ji "ni kike cewa na kashe ki?" Hannu ta saka zata ƙwace nata hannu idanunta cikin nasa ba tsoro ta ce "Me kake so na yi maka? Ka shigo kana tambayata abin da ban sani ba, ka saka hannu ka mari fuskar da kullum nake shafa mata mayuka masu tsada, ni ka mara ban maka komai ba, tunda ka tsane ni ka kashe ni kawai" da ƙyar ta iya ƙare maganar saboda muryarta dake rawa Captain ya saka hannu ya sake ɗauke fuskar Fiyya da mari yana huci ya ƙara ɗaga hannu zai mare ta cikin sauri ya tsayar da hannun nasa ganin hancinta na fitar da jini sosai kuma yaƙi tsayawa.
Ta yi masa ƙuri da idanunta da ruwa ya kwanta a ciki, jinin kuma bai fasa zuba ba daidai nan aka buɗe ƙofar tare da shigowa ciki da sauri Fiyya ta nufi wajan Daddy ta riƙe shi tana fashewa da kukan dake cin ran ta jikinta har wani irin rawa yake yi da ɓari jinin dake fita a hancinta kuma ya shiga ɓata masa farar rigar jikinsa. Daddy ya juya ya kalli Captain daya haɗe fuskarsa "Aliyu me ka yi mata?"
"Ni kuma?" Ya tambayi daddy irin bai ma san me ya faru ba "To ita da waye haka ji bi yadda take kuka hancinta na jini kuma kai na gani a ɗakin, dole kasan mene ya faru" cikin damuwa daddy ya yi maganar wacce sai da ta bayyana saman fuskarsa ya ɗago Fiyya yana duban ta sosai ya ƙara kallon Captain
"Maama wannan jinin fa? Daman kina yin haɓo ne wani abun Aliyu ya yi miki?" Ita dai Fiyya taƙi cewa komai sai shassheƙar kuka take yi numfashinta na yin sama, Daddy duk ya rikice baya wasa da al'amarin daya shafi Maama ko kaɗan a ƙasan zuciyarsa yake jin soyayyarta ya kuma tabbatar ita ce rauninsa Fiyya kawai za a taɓa a iya nakasta rayuwarsa. "Ya isa daina kukan haka nan, Allah Ya nuna mini sati mai kamawa ki tafi gidan mijinki ni ma zan fi samun nutsuwa da hakan zan fi samu nutsuwa idan kikai auren nan Safiyyerh"
"I love you daddy" Fiyya ta ce a hankali tana rungume daddy ya shafa kan ta cike da soyayya "daddy love Safiyyerh" tuni Captain ya fice daga cikin parlon. Anty Turai da zuwan ta gidan kenan ta ce "Ikon Allah. Yaya kai ne kake ɗaurewar yarinyar nan gindi wallahi ka lalata da soyayya take yin abin data ga dama, ko Aliyu baka tambaya abin da ta yi masa ba ta wannan figaggiyar yarinyar kake"
"Fita daga ɗakin nan Turai" rai ɓace Anty Turai ta fice tana zabgawa Fiyya harara ranta duk a ɓace. Daddy ya kalli Fiyya sosai kamar zai yi magana sai kuma ya ce "jeki wanke fuskarki I'll drop you"
"Daddy daman i missed your drive wallahi" murmushi ya yi mata a duk santa zai kalli Fiyya sai gabansa ya faɗi ya juya a hankali ya dubi picture ɗinta dake gaban madubi sanye da kayan graduation ta yi wani kyakkyawan murmushi ta rungume hannunta tana kallon gefe guda. Ya ƙarasa ya ɗauki photon ya shafa a hankali "Maama na ni kamar na yi ba daidai ba, bani da wani zaɓi ne i am sorry Safiyyerh Abdu Marafa" ya lumshe idanu ya buɗe a kan photon "kina tunanin kin yi girman da za ki iya kula da kan ki, ki kuma yankewa kan ki hukunci? Maama ba kin san komai ba a rayuwa you're nothing but a stubborn girl"
Ya ajjiya photon ya ɗauki wayarta babu wani password a kai dudduba abu ya fara a nutse yana yi yana kallon ƙofar banɗaki can ya sauke ajjiyar zuciya ya ajjiyar wayar daidai nan ta fito. Ya yi waje yana "Ki same ni a ƙasa"
Suna tafe a hanya daddy na driving a nutse ta ce "Daddy" bai kalleta ba yana dai sauraren ta domin program ɗin da ake yi da Eng Ali wali a redio shi ne ya ɗauke masa hankali. "Zan raka Kinal FGC"
Wani burki ya ja a kusan tsakiyar titin Fiyya ta dafe kai tana "Subuhanallahi"
"Mene haɗin ki da FGC Maama?"
"Daddy Kinal zan raka suna yin taro na makarantar zan bita idan na tashi aiki" zufa har fitowa daddy take a saman goshi sunan FGC ba ƙaramin gigita masa lissafi ya yi ba. "ba za ki ba" shagwaɓe fuska ta yi "don Allah daddy wallahi na ji ina son zuwa"
"Wallahi mistakenly kika je shegiyar makarantar nan sai ranki ya ɓaci kuma sai kin daina fita hatta aikin sai kin ajjiye. Wallahi Safiyyerh Abdu Marafa idan kika je za ki san waye Abdu sai na zane miki jiki da carbi ko bulala" ta yi ƙasa da kanta zuciyarta duk babu daɗi idanunta na cika da hawaye tun tana ƙarama take yin biyaya a komai akan abin da ya yi crossing da buƙatar daddy.
Hannunta riƙe da jakarta ɗaya hannun wayarta data kara a kunne suna magana da Kinal, duguwa ce hakan yasa bata fiya saka takalmi mai tsayi ba suit ce jikinta as always fara tas mai riga da wando ta yi rolling da black ɗin mayafi idanunta sanye cikin wani shade glasses mai kyau a hankali take tafiya tana ɗan jinjinawa mutanen kamfanin kai with so much respect tana da girmama mutane kawai rainin hankali ne bata ɗauka "Kinal ki je kawai idan na koma gida za mu yi magana, daddy ya hana" yadda ta yi furucin ya bayyana ainihin abin da take jin a zuciyarta.
"To shikenan nima na zo studio ne zan yi waƙa idan na koma gida zan shirya za mu yi video call na nuna miki cikin FGC ɗin" Fiyya ta ɗan taɓe baki daidai lokacin da take isa bakin ƙofar office nata security ya matsa ta buɗe ta shiga ta buɗe idanu ganin Ashraf zaune a office ɗin "Kinal mu yi magana anjima" ta cire wayar tana kallon Ashraf daya miƙe tsaye yana mata murmushi
"Kuma da permission ɗin wa ka shigo?"
"Wake neman permission idan ana batun ganin mata, na zo ganin matata ne" ta ajjiye jakar hannunta tana zama saman duguwar kujera "Sannu mai mata" ya miƙe ya dawo kan kujerar yana leƙa fuskarta
"Miji ɗaya gare ki a duniya kuma nine" cikin wasa ta ce "Ai kowa ba zan aure ka don ka ji"
"Funny Fiyya" a yanayinta na rashin damuwa da soyayyar ta ce "How are you?" Yana kallonta yana ji wani abu sosai game da ita "Fiyya na yi kuskure wallahi bana sanin ina shige limit ɗina sai na yi wani abu. Ni na san ba wani sona kike ba amma idan kika yi haƙuri watarana za ki ji son nan ko yaya ne kullum kina ƙara nesanta kan ki dani yayinta zuciyata ke ƙara kusanto kanta gare ki. Komai da lokacin shi idan mukai aure muka rayuwa inuwa guda I'll definitely be honest to you, ina jin kishin ki a ƙirjina ne a nan nake ji kina mini motsi Fiyya" ya nuna ƙirjinsa saitin zuciyarsa sai ya ɗan juya gwanin tausayi
"Amma bakya so na"
"Who told you that?"
Ashraf ya buɗe idanunsa "When are you gonna tell me you love me?" Tana kallon shi tana murmushi ita tana son shi sosai kawai bata san ya zata nuna bane sometimes rigimarsa ke sawa ta bijire itama ta miƙe tsaye tana danna kiran number messenger bayan ya ɗaga ta ce "Call Md for me, ka kira mini Md da Secretary hadda accouter" ta ajjiye ta ce ta haɗa shayi a cup guda biyu ta saka cokali tana miƙawa Ashraf ɗaya idanunta cikin nasa ta ce "San da aka kai ni gidanka matsayin mata" ya lumshe idanu ya buɗe
"I'll wait as far as you're with me. Abin da kawai nake buƙata shine ki so ni. Ki so ni ko da kaɗan cikin yadda nake sonki ne"
*****
Anty Hameeda na sunkuye a madaidaicin parlon gidanta tana duba jarkokin lemon ginger ɗin da take siyarwa ta ji hucin mutum da sauri ta miƙe sai kuma ta yi baya a razane ganinsa tsaye a gabanta yana waige-waige kamar wanda aka biyo ga wani irin yanka a ƙarƙashin wuyansa da alama yanzu akai masa jini ja zuba, ya yi zuru-zuru sai huci yake yi naman jikinsa musamman na ƙirjinsa na motsawa "Ɗan autan Ammo wannan hucin fa kamar an biyoka wani abun ka yi? Wane ya yanke ka haka me ka yi masa?" Bai kula ta ba ya juya ta bi bayan shi kitchen taga ya nufa ba jimawa ya fito da kwanon abinci daidai nan wata mata ta fito tana ganin Mai dawa ta yi saurin sakin butar hannunta ta ce
"Wannan tantirin ƙanin naki uban ne ya zo yi mana a gida? Yaushe ma aka sake shi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un mugun ji da mugun gani Ubangiji ya kare Allah wadaran ƴan daba ya tsine musu albarka ya saka su fita a cikin ajalin su" matar ta faɗa hawaye ya cika idanun Anty Hameeda ta ce "Baba ina laifin ki ce Allah ya shirya ɗa fa na kowa ne bawa kuma sai me shi, ciki ne mai haife-haife baka san me Ubangiji ya ɓoye ba suma fa ƙaddara ce ba wanda ya zaɓi yadda rayuwarsa zata kasance"
"Ai duk wani ɗan daba ƙarshe wulaƙantacciyar mutuwa ce ko idan sun sha ta faɗa musu babu daɗi su kashe kan su, ko kuma su haukace garin shaye-shaye ko garin faɗan daban su a kashe su. Allah wadai" Moh dai bai yi magana ba abinci kawai yake ci hannunsa ko wankewa bai ba duk jini Anty Hameeda ta shige ɗaki bayan ta share hawayen idanunta lemo ta ɗakko
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 17