Share this page
damu na san ba a baya yanzu ina so" "Wai Dr Hash da ya kewa Fiyya? Ban sani ba gaskiya Yaya why not ka tambaye shi?" Wata tsawa ya dakawa Awais yana cewa "Get lost mumu" fita ya yi daga cikin gidan gabaɗaya. Har ɗaya saura Safiyyerh na kwance a bedroom ta yi shiru tana jin ciwon na yi mata zafi ta yi kuka sosai na rashin sanin dalili har bacci ya ɗauke ta. Cikin bacci ta ji an buɗe ƙofar an shigo ta yi saurin rufe idanu yana sanye da kayan bacci farare ya ƙarasu ya duba magungunan yaga ko ɗaya bata sha ba, ya ƙarasa bakin gadon ya zauna shi gabadaya ya manta cikakken sunanta na gaskiya rashin sanin ne zai ce kawai ya saka hannu ya janyo ƙafafuwanta zuwa ƙasa ta matso dab da shi da sauri ta buɗe idanu, suna haɗa idanu ta tura baki tana juya fuska "Zan saka bindiga na harbe ki a iska kina juyawa" ta kalle shi ta ce "To yaya ciwona ka fama mini" kallon da yake mata ya saka ta miƙe zaune "kin accepting auren?" Ta jinjina kai ta ce "Na yi kamar yadda ka yi na san daddy yana da nasa dalilin damuwata ɗaya na rashin sanin gaskiyar ni ce ƴar daddy ko kai, amma aure tun kafin na zo duniya Allah Ya rubuta wanda zai zamo miji gare ni ina da sani daidai gwargwado zan zauna ƙarƙashinka duk da baka so na, ko kana so na?" Ya girgiza mata kai alamar "A'a" "Ni ma,sai mu koyi son juna" ya kalleta kawai sai ya ce "Muga ciwon" "Yaya a wajan ƙirjina ciwon yake fa" da rashin fahimta ya kalli ƙirjin ya kalleta kuma ya nisa ya ce "Kuma mene a ƙirjin?" Ya faɗa yana yaye rigar. WE'LL SOON END OF THE FREE PAGES. Ku hanzarta biyan 500 domin karanta Mutallab posting za mu babu ɓata lokacin ba lallai ku fahimta a yanzu wanda suka shiga paid group sune da batu ko rabin book 1 babu shiga ba. Tsakiyar labarin akwai muke, mene ya faru a farko me zai faru tsakiya ba zaku taɓa sani ba ko a sashe. MUTALLAB. Book 1, 2 &3 500 Naira 0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385 [1/7, 9:33 PM] Sis Fauzy: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 12 *Bright pens..2nd batch* Hannunsa ta cire da sauri ta ce "ciwon fa a wajan ƙirjin yake yaya" da mamaki Captain ya kalleta ya kalli ƙirjin, da gaske bai san mene matsalarta da hakan ba. Ya ɗauki lokaci kafin ya ce "kuma mene special a ƙirjin?" "Baka sani ba?" Fiyya ta buƙaci jin amsa ganin har lokacin kallon ta yake da alama processing ƙwaƙwalwarsa take yi shi dai ya san wajan da aka caka mata wuƙar kawai zai gani. Bai sake cewa komai ya miƙe tsaye ya nufi fita, Fiyya ta bisa da idanu tana jinjina rainin wayon Captain yana abu kamar baya fahimta. Ta yi shiru bayan fitar tasa, ta ɗan jingina da jikin gadon thinking me ya sa abubuwa suke juyawa tare da faruwa ne? Ba wani tsanar Captain ne a zuciyarta sosai ba, kawai yadda yake abubuwansa ke ƙular da ita amma kaf yayyanta tana matuƙar so da ƙaunar su. Damuwar bai shige dalilin daddy na aura mata Captain ba, bayan shi blood brother ɗinta ne. Yanzu ita ce ba jinin daddy ba ko Aliyu? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Da sauri ta riƙe ƙirjinta jin zuciyarta na harbawa, duk yadda take ƙoƙarin ko a cikin bacci ta sake ganin gilmar reflection ɗin shi ta gagara, ko sautin muryar tasa ma ta mata sai kuma tunanin mahaukacin daya caka mata wuƙa ya faɗo cikin ranta wai shi Mutallab? Who is he? "Who is he?" Muryarta ta sauka a tsakar kanta tana nanata mata tambayar da zuciyarta ta yi mata a fili. "To ya ɗauke ni ya yi mini me? Safiyyerh Abdu Marafa ai ba sa'ar yara bace, bata zama teddy ba, the whole manager anya ya san me yake ce mini? Ba sai ya sake ganin ko inuwar fiyya ba balle ya aiwatar da abin da ya yi niyya a kaina, aikin banza aikin wofi don ma dai ban san ya zaro wuƙar bane zuwa gaba Captain zan lallaɓa ya ara mini bindigarsa problem solved" Ita kaɗai take ta yin mita ta zubawa madubi idanu bayan ta miƙe tsaye. Wanka ta yi tare da alwala bayan ta idar da sallah ta ɗauki skin products mai kyau dake sa fatarta laushi ta yi ta ƙyalli, tana son amfani da kayan Aisha s bayero skin care nd herbal medice, ta ɗauki riga mara nauyi saboda ciwon jikin nata. Kasa bacci ta yi ta ɗauki system ɗinta ta fara dannawa hannunta riƙe da ruwan zafi ta jima suna tattaunawa da Md da Secretary ta email kafin ta rufe system ta yi addu'ar bacci ta kwanta sai dai ciwon ya dameta da zafi har zazzaɓi ya saka ta. Washegari da ƙyar ta yi sallar asuba don bata yarda ta shige ta, ta rufe jikinta da duvet ta girgiza kai da ƙyar baccin ya sake ɗauke ta. Har 12 bata fito ba, sanin abin da ya faru da ita ya saka ba'a nemi ba'asin rashin zuwan nata kamfani ba. Wajejen ƙarfe biyu ta buɗe idanunta dalilin ƙamshin da ta ji da kuma goshinta da ake murzawa a hankali, ta juya ta kalle shi taga waya ya ke yi muryarsa ƙasa tana jin yadda yake magana one by one jin ana kallon shi cikin sauri ya ce "i will call you later" Ya juya suka haɗa ido a hankali ta ce "Ina yini?" Ya yi mata shiru yana kallon kanta da sauri itama ta kalla sai yanzu ta lura kan nata yana cinyarsa ne shi kuma hannunsa na gefen fuskarta "ɗaga ni" "Yaya bani lafiya fa" ya harareta kawai ya yi shiru shima ya ji zazzaɓin ta juya masa baya tana sauke kanta idanunta rufe zafin zazzaɓin na ƙaruwa ji tayi ya ɗago ta zaune kamar wacce zai zaunar a cinyarsa ya faki idanunta ya damƙe gefen cikinta ta yi ƙara tana riƙe shi "Ki dai na yi mini sauti haka, za ki je zaman barrack lazy" ta haɗe fuska tana ji yana taɓa cikinta yaga wajan ciwon na jini ya saka hannu ya shafi ciwon ya taɓo jinin da hannu can ya miƙe yana juyawa. "Captain jini wajan yake yi ka fama mini na shiga uku" idan ba kuskuren ji ta yi ba, muryarsa ta ji ya furta "Allah Ya ƙara" Cikin dare ne yana tsaye ya fito daga cikin motarsa sanye da manyan kaya na alfarma da fuskarsa rufe da facemask ya dubi yaran da suke gabansa ya ce "Ina buƙatar aiki cikin gaggawa bana son wani mistake idan aka samu akasi ina cikin taraddi, kuna kallo abu ya taho lokacin na neman cimmana" Ya buɗe idanu yana sake dudduba inda yake tsaye gani yake kamar ana ganinsa za kuma a iya gane wanene shi. "Mai gida wanne kalar aiki ne ya fito da kai cikin duhuwar nan, faɗa taka cikawa tamu sai da kai iya wuya ba wani shege a baya wallahi" ya ɗan yi murmushin jin daɗi yana kallon mai maganar da kana ganin shi zaka san a buge yake cikin maye kamar kullum "Idanun mutane nake so, maza uku mata uku" ya ce yana kallon wanda yake faɗawa maganar ganin yadda ya yi shiru kamar dai ban fahimta ba. "Aiki ja idanun bama na mutum ɗaya ba? Akwai kuskure fa" "Yanzu akwai wani aiki da zan iya sakawa ka yi mini da zai fi ƙarfinka? Kai ɗin amintacce nane na kuma yarda da ƙwarewarka ina jin daɗin business da kai wallahi" ya zaro kuɗi masu yawan gaske ya miƙa masa, ya sake zaro wata ƙwaya kala daban-daban masu kyan gaske da tsada kana gani kasan manya ne ke shan irin ta. "Ka fara riƙe wannan kuɗin nasan kana buƙatar caji a kanka kafi yin aiki yadda ya kamata, idan ka kammala ka sanar mini zan faɗa maka inda zaka ajjiye ko?". "Ka yi ƙarko irin na dabino sai da kai wallahi yau zam dani, ko kan mutum ka ce na kawo maka a yadda ƙwayar nan ke buɗe mini tunani kawowa zan, ba ƙaramin ilimi ne dani ba da tuni fa ni zan yi ministan kuɗi nace na fasa, kaf ƙasar waye bai sanni ba don uwar mutum" sambatu kawai yake na maye ya bugu ƙarshen buguwa, shi mutumin dariya kawai yake basa hakan kuma na yi masa daɗi ainun. Mota ya shiga ya bar wajan shi kuma ya gangara ya shiga lungun titin da suke. Tunda ya tafi ya zauna cikin yan'uwansa mashaya yake tunanin ta ina zai fara? Ina zai samu mutane har ya ƙwaƙwule idanunsu hankali kwance? Ya yi shiru yana kallon sama yana ta furzar da iska mai ɗauke da warin sholi dana bakin gabaɗaya. ***** Mutallab ya tanƙwashe ƙafafuwansa kamar wani sarki ya kuma ɗora hannunsa saman cinyarsa cikin kowacce ƙafa, kallon Abbasa yake tun ɗazo take magana yaƙi cewa komai ko tari kuma bai yi ba, raunukan jikinsa ya kame sai saura, ido biyu za ka yi da shi ba zaka ƙara marmarin kallon nasa ba, babu rahama a fuskarsa nan zaka ɗauka tunda Ammo ta kawo shi duniya bai taɓa yin murmushi ba, ko haɗa hanya da inda fara'a take. "Kalli nan" Ya dubi abin da take nuna masa, zanen kamfanin ne da photon jariran sai kuma kalmar A.M.A "Da fari mu fara gano ma'anar kalmar A.M.A, photon jariran kuma mai sauƙi ne ana nuna maka har jarirai da aka haifa yau ana siyar da shi a kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY, abu biyu ne wanda dole za ka yi ko kusan ukun, da fari sato ita wannan yarinyar ta yiwu a samu wani haske tattare da ita, na biyu kasan yadda duk ka yi ka mallake wannan kamfanin cikin sauƙi, na uku....," sai kuma ta yi shiru ta dinga kallon Moh ciki da bai "Waye Mutallab, waye kai, dole ka faɗa mini asalin waye kai kana ji na?" "To na haƙura" Ya miƙe tsaye a hankali a lokacin ras yake sai abubuwan da sukai masa tsaye a zuciya da maƙoshi "Dole na san waye kai, ko ka faɗa mini ko ba ka faɗa ba, abu na uku sai ranar da asalin naka ya zo kunnuwana zan furta maka shi" bai dai yi magana ba, hannunsa zube cikin alijun kayan da Abbasa ta basa ya sauya da ƙyar yafi ƙarfin minti ashirin a tsayen yana harhaɗa kalmomin abin da zai ce mata ransa duk a jagole. "Lalacewar Moh bai kai ya sato yarinya ba" "Kuma dole a yi hakan fa" Ya yi waje abinsa yana yana ƙoƙarin ficewa daga cikin bukkar ta ce "Baka da lokaci fa Mutallab, kuma baka da ikon taɓa ta a waje idan ba kana shirin komawa gidan yari bane, kasan yadda za ka yi dai wish you all the Mutallab" Bai ƙara bi ta kanta ba, ya dinga ɗora ƙafafuwansa a ƙasa kamar mai tsoron taka ƙasa sai haɗe fuska yake yana kwaɓewa duniyar ya ji ta yi maza zafi ta ko'ina, ya rasa ina zai je me kuma zai yi sai ɗaga yatsun ƙafarsa yake wanda suke zara-zara matar nan Abbasa ta fara takura masa ko waye ya ce ta yi masa gyaran farce? Yama a ka yi ta samu mai yin aski ya wani kwashe masa suma? Bakin bishiya ya samu ya zauna ya sunkuyar da kansa ƙasa, zufa ta shiga tsattsafo masa ta tsakiyar goshi ya sa yatsa ɗaya yana gogewa ya shafa jikinsa ba kayan garawa ko ɗaya yana buƙatar fita daga yanayin da yake ciki, baya son tunawa ko da wasa. _“One day i will leave you, duk son nan da nake maka”_ Ya ji saukar muryarta a kansa ta sauka har ƙasan zuciyarsa a ɗan lumshe idanunsa da ya yi, ya juya zuwa gefe sai yake ganin bidiyon abin da ya faru bayan kammala assembly, at that time yana can baya zaune ya yi shiru yana kallon students bai san da zuwanta ba sai ganinta ya yi ta baya kamar zata shige jikinsa ya fiddo manyan idanunsa waje yana miƙewa tsaye hannunsa ɗaya zube a aljihu ya dinga kallon ta da ƙyar ya furta "And what is this Safiyyerh?" "Bestie shi ake cewa love mana" ta langwaɓar da kai gefe yana sake kallon yaluwar fuskarta kamar zabiya. "To iskanci za ki mini?" "Iskanci kuma bestie? Me ya sa kake haka ne, son ka kawai nake yi fa why are you doing this to me? Kai ba'a gane maka sam? Ko murmushin masoya ne ka dinga yi mini mana, bafa ni na ɗorawa kai na son ka ba" idanunta ya cika da waye tana jin zuciyarta na yi mata zafi bata ganin komai a idanunta sai fuskar Mutallab. "A love? Shine za a yi wa mutum fyaɗe a soyayyar??" Ta buɗe idanu tana rufe baki jikinta har rawa yake tana jin kamar ta idda abin da zuriyarta ke umartar ta "To ka yi haƙuri idan dai na mutu ka huta, kuma idan baka zo gidanmu yau ba Allah a wajan Ammo zan kwana" fuskar nan a ɗaure ya ja sirirn tsaki ya shige cikin class kafin ya ƙarasa ya ƙara jiyo ta a bayansa tana sake yunƙurin riƙe shi da sauri ta juya sai kuma ta ɗauki school bag ɗinta ta fice daga makarantar tana kuka. *** "i missed the hug" ya furta ƙasan zuciyarsa lokacin da bidiyon abin ya ɗauke daga kusa da shi, ya yi shiru yana tunani har yamma ta yi lis bashi da niyyar tashi daga wajan baya son shiga cikin jama'a yana jin nan ɗin shine daidai da ina ya kamata ya ɓoyewa kwalawa. He feels uncomfortable a cikin jama'a haka nan. Safiyyerh na zaune bayan ta dawo daga kamfani ko ɗaki bata shiga ba idan ta tuna yadda Hon Maɗatai ya sake matsa mata akan hannun jarin da yake son sawa a FS WORLD INVESTMENT COMPANY sai ranta ya sake ɓaci, duk dukiyar da Ubangiji Ya bashi bai gode Allah ba, mutane nawa ne a wannan duniyar da basa ci, idan anci na safe ana fargabar na rana, idan na rana ya samu dare kuma sai dai a yi salatin Annabi a sha ruwa a kwanta, masifar rayuwa ta yi wa talaka dirar mikiya, yunwa na neman illata su ga lalura ga rashin aikin yi? Amma hon Maɗatai shi dukiya yake nema idanu rufe ƴan siyasa da yawa kansu kawai suka sani suke ginawa, mene amfanin talaka ya je ya yi zaɓen? Gabaɗaya sabgogin dimokuraɗiyya ya lalace son zuciya kowa yake bi. Ta yi tsaki tana jin ko zata rasa kujerar Manager ɗin ba zata taɓa bari Hon Maɗatai ya saka hannu a kamfanin ba. Miƙewa ta yi ta nufi bedroom bata ɗauki wani lokaci ba ta fito sanye da wando da riga,wandon iya cinya kanta ko ɗan kwali babu da mamaki take kallon Captain ganin ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana danna mata system ga wayarta a hannunsa kafin ta ƙarasu ya kashe system ɗin ya ajjiye har wayar. "Yaya me kake nema a system ɗita kuma?" Ya yi mata shiru ta zauna kawai tana buɗewa bata sake kallon shi ba, ta shiga duba dukkan ayyukan da aka fitar yau da sauri ta kira accouter da number da take amfani da shi na kamfanin tana girgiza ƙafa a hankali cikin faɗa ta ce "Accouter me nake gani a haka? Kuɗi fa kimanin miliyan 500m yanzu sun shigo account na kamfani dana gani a bayanai, bayan tafiyata me aka fitar ne shinkafa ko me?" Faɗa take sosai domin ta iya faɗa ajin ƙarshe ce a fannin. "Manager nifa kina tunawa accouter ne kawai, bani ke da alhakin saka hannu a fitar kaya ko shigowar su ba, kawai ni ke saka hannu a duk wani kuɗi da zai shigo ya fita, i am nothing but a Accounter" Miƙewa tsaye ta yi tana riƙe ƙugu ta ce "Rubbish; ka tura mini ducoment na PDF via email na abin da aka siya har miliyan 500m yanzu yanzu accouter" "Ki yi magana da Md ni kawai kuɗin naga shigowar su babu wani file daya zo officer nawa, trust me manager ba zan ɓoye miki, na san dai bayan tafiyarki Professor Abdu Marafa ya shigo kamfanin" "daddy!" Ta furta da ƙarfi "E, mahaifinki shi" "Kamarya to?" "Shine ban sani ba" sai kawai ta kashe wayar ta ajjiye waje guda, ta sauke numfashi da ƙyar ta shiga uku meke shirin faruwa ya ake ƙoƙarin amfani da ita ba tare data sani ba?" "Yaya" bai amsa ba idanunsa a ƙafarta ta ce "Yaya bacci nake ji" "to ina ruwana" Sai kawai yaga ta ɗora kanta a cinyarsa maimakon ta juya masa baya sai ta juyo wajan cikinsa ta yi shiru tana kallon ƙirjinsa dake buɗe. Ta yi shiru tana sauke numfashi shi dai bai yi magana ba, bai ɗauka haka take da masifa ba yana jin ƙirjinta na ɗagawa a hankali kuma bacci ya ɗauke ta. Cikin baccin ta ji hucin numfashi ta buɗe idanu kallonsa ta dinga yi yadda ya kifa fuskarsa a tata hannunsa ɗaya tamƙe cikin nata "Captain" da sauri ya buɗe idanun ya ƙurawa cikin idanunta ido sai kuma ya ɗauke fuska yana haɗe rai. Fiyya bata ce komai ba ta miƙe zaune shi kuma ya shige cikin part ɗinsa yana taku da sauri sai shafa kai yake yi. Notification ta gani kamar wancan lokacin saƙo ne ta dm nata. Ta buɗe ba wani magana mai tsayi bane sai dai maganar dab take da rusa tunaninta ta bi saƙon da kallo inda ake cewa. _“bai ci a ce kin yi mantuwa mai nisan haka ba, ki tuna akwai hakƙin wani kan ki Allah Yana kallon ki TIGER“_ ta dafe kan ta to hakƙin waye a kanta waye mai wannan saƙon kuma? Tsaki ta yi ta miƙe ta bar parlon. Bata sake ganin Captain ba har dare ta yi kwanciyarta. **** Cikin sauri take tafiya tana yi tana juyawa sauri take ta isa chemist amsar maganin ga dare ya raba mijin nata ya fita. Kamar daga sama taga mutane sun tsaya gabanta fuska rufe "Su waye ku? Don Allah ku rufa mini asiri magani zan siyo" muryarta na rawa ta yi maganar. Haɗa idanu sukai sai suka ɗaga ta sama tare da danna ta cikin napep ɗin basu tsaya ko'ina ba sai wani kango a nan taga wasu mutanen kwance kamar basu da rai, kuka take tana duk addu'ar data zo bakinta "Don Allah kar ku cutar dani don Allah ku rufa mini asiri da yarana da rayuwarsu" Tana ji tana gani suka danneta tun tana ihu har ta kasa jini kamar an yanka rago babu imani suka cire ƙwayar idanunta duk biyun tare da watsa su cikin aliju da gudu suka fice daga kangon. Bayan ta dawo daga wajan aiki ta shige gidan Anty Turai saboda kiran da ta yi mata, a parlo ta samu Anty Turai da yaranta da kuma wasu ƴan mata zaune. "Ina yini Anty?" "Sannu matar Captain Aliyu Marafa?" Cewar Anty Turai ita dai Safiyyerh idanunta akan waya bata ce komai ba Waheeda ta ce "Mama wai shi Uncle captain ɗin son ta yake yi ne? Ni banga abin so a jikin wannan zabiyar ba sam sam wallahi" Zahiderh ta yi saurin cewa "Ina fa? Captain ne zai ce yana son Fiyya never wallahi, kawai dai auren dole aka yi masa, wannan fari ko na lalura" Safiyyerh dai jinsu take Anty Turai ta ce "Sannu Safiyyerh, ya kamfanin yanzu ai Aliyun ya bar nan wajan Zahiderh ya zo ki dinga haƙuri da shi ya jaddada mini baya buƙatar ki cikin rayuwarsa bai san me zai yi da zabiya ba" miƙewa Safiyyerh ta yi ta ce "To Anty a ɗaura masa aure da Zahiderh ni bani da wata matsala, zabiya kuma ina jira ku halitto irin kalar idan da sauƙi, so kuma ba abin da ya yi mini zafi da shi zan zauna da mijina haka tunda zaɓin daddy ne, wallahi babu wanda ya kai level ɗin ɗagawa Fiyya hankali" Anty Turai ta miƙe tana nuna Fiyya idanunta ya rufe sam bata kula da shigowar shi ba, balle ankarar da ita da su Waheeda suke ta ɗaga hannu zata mari Fiyya dake tsaye tana juya idanunta ta ji an riƙe hannun. Tun zuwan shi ta ji ƙamshin turaren nasa, ya tsaya a bayanta Anty Turai ta kalli Aliyu ta kasa cewa komai ya saki hannunta yana matsawa bayan Fiyya ya zagaye hannunsa a ƙugunta ya jata jikinsa daga baya yana sake kallon Anty Turai "Shekararki nawa Anty yaushe na zo gidan naki kuma? And who told you bana son ta?" Duk a dagule yake maganar yana sake haɗe Fiyya da ƙirjinsa kasancewarta duguwa sosai so ma sha Allah. "Aliyu ni zaka shigo gida ka faɗawa haka?" Bai kalleta ba sai Fiyya daya kalla wacce take shirin juyawa idanunta cike da hawaye ya yi saurin riƙo hannunta yana "Wait" sai kawai ta kifa kanta a ƙirjinsa tana shassheƙar kukan da bata shirya saboda ganin idanunsa "Anty karki sake mini haka" "Idan na sake me za ka yi Aliyu na ce me za ka yi?" Ya girgiza kai ya rungume Fiyya tsam a jikinsa ya ce "Ban san me zan iya yi ba, kawai dai na faɗa miki, kuma i love my wife" Fiyya ta yi saurin ɗago kai ta kalle shi ya ɗage mata gira "Yes, I Iove You Safii" yana cewa haka ya kama hannunta suka fice. *** Suna zaune a dabarsu ya yi sauri ya miƙe tsaye Goje ya ce "Sai godiya, ina aka nufa don shirwa kake baka jewar banza, ɓauna mai tafiyar ɗaukan rai jeji naka dabbobi naka, a lafiya mai dawa" jikinsa ya ji ya fara kakkarwa tsohon tsuminsa na neman tashi ya yi ƙasa da kansa yana ƙoƙarin hana kansa yin kirari da amsar saƙon Goje, ya bar wannan layin tuni. Da ƙyar yana girgiza kai ya ce "Goje" "Sai godiya, wuya a ina wuya a daji kai ne mai dawa da jeji na Malam Abdu shalelen Ammo, ƙanin Sa'adah da Bafullatana a lafiya aminin Hamida, ɓauna taka mesa taka ba wani bayanka jan biro maganin daƙiƙin yaro Allah Ya ja da ran mai dawa" gabaɗaya jikin Mai dawa ɓari yake yana damƙe hannunsa wajan ganin mai ɗaga su sama ba har can cikin kansa yake jin kirarin. Kawai ya juya ya bar wajan "Wai ina zaka ne kasan yanayin da ake ciki fa akwai cinnaku" "Baka haifan ba balle ka tambayan karka biyo ni" yana cewa haka ya bar wajan ya jima yana tafiya kafin ya ƙarasu gidan sai ya saka maƙulli ya buɗe ya shiga. A ɓangaren su Safiyyerh tunda suka bar gidan Anty Turai suka shiga mota basu ce komai ba ya kuma haɗe fuska itama bata ce komai ba, daidai wani gida a bakin titi taga ya tsaya ya kalle ta "Kar ki fito jira ni nan" ta jinjina masa kai. Fita ya yi ta jingina tana ɗaukan waya, abin da ta fara cin karo da shi a X picture ɗin wani kyakkyawan yaro yana murmushi ya rufe idanunsa saboda hasken da ya yi masa yawa kamar ka taɓa shi jini ya fito, ta dinga kallon picture ɗin sai kawai ta yi skipping zuwa next tweet. A hankali ya buɗe ƙofar ya shiga idanunsa zube a saman tafkeken screen ɗin computer dake jikin bango, gabaɗaya wajan nau'in kayan computer ne kala-kala. Ya ɗan dafa kafaɗar wanda yake zaune akan kujera yana juyawa a hankali, kallo ɗaya zaka yi masa kasan mayen computer ne masanin hakin da duk wani surƙulle. Captain ya ce "Where are you hiding?" Ya ɗaga idanunsa a hankali ya kalli Captain bai ce komai ba kuma ya cigaba da danna wayar, Captain ya saka hannu ya dungure masa kai ya nemi waje ya zauna yana taɓa computer shima. Da sauri ya miƙe kuma jin sautin muryarta da yadda take ƙoƙarin buɗe ƙofar ya yi saurin miƙewa ya nufi ƙofar daidai nan Fiyya ta shigo "Yaya gaskiya yunwa nake ji akwai hadari sosai a gari ina tsoron ruwa" "Muje" Ya yi saurin faɗa yana kama hannunta tare da rufe ta da jikinsa leƙawa take son yi ya saka hannu ya juyar da fuskarta ya jata waje, shima ɗin dake zaune ya juyo a nutse ganin sun fita ya saka ya cigaba da abin da

Chapter 12 of 17