Cikin raunin murya kamar za ta yi kuka ta ce "Me za ka yi da wuƙa haka?" Ya buɗe ido sosai sai bai magana ba, a hankali ma ya bi gefen ta zai huce ta yi saurin riƙe masa hannunsa tana faɗin "Ni ɗin ma? Yau za a ji kan mu da kai, kar ka faɗa mini sauyin da ka yi ya zagayo har kai na?"
Ya ɗago kai ya kalle ta ya kalli hannun data riƙe shi da shi, hannunta fari tas saɓanin nasa da yake mai kauri kuma baƙi irin na majiya ƙarfin nan wanda suke tashe akan shekarunsu. "Don Allah ka tsaya mu yi magana, ni ko gidan ba zan shiga ba wajanka na zo" ya cije bakinsa ya mai da kai gefe cikin muryar mai kauri ya ce "Kin ci darajar Ɗan Amina, mene sakin?" Ta girgiza kai kawai tana duban gefe dakalin dake wajan ta gani ta je ta zauna akai, ta yi masa alama ya zauna amma ko motsi bai yi ba, ta san cewa yana jinta amma hankalinsa na kan hanya sai waige-waige "Mutallab ka kalle ni bafa wani zai kawo maka farmaki ba" ta nisa idanunta cike da ƙwalla ta ce "Don Allah kai ne ka kashe ta? Ba zargin ka nake ba Autan Ammo ni me iya rufa maka asiri ce idan ya zama kana da laifi ka faɗa mini gaskiya na maka alƙawarin ko Ammo ba zan faɗawa ba, ka kashe matarka ko ba kai bane?"
Ya juya da wani irin sauri yana kallon fuskarta da take kallon shi cike da damuwa, idanunsa ya yi jajur naman jikinsa na motsawa ya kasa furta komai. Miƙewa Anty Hameeda ta yi tana girgiza kai kuka na cin ƙarfinta "Ko minti ashirin ba mu yi da kai maka matarka ba, sai labarin mutuwar ta muka ji da kisan wulaƙancin da aka yi mata. Mutallab kai ne fa muka gani tsaye akan gawarta, kai ne fa riƙe da wuƙar da aka kashe ta da ita jikinka duk jinin matarka innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na kasa yadda ka kashe ta, daman soyayyar da ka nuna mata na iya fatar baki ne?" Wani irin ihu Anty Hameeda ta yi tana kaiwa jikin bango ganin ya ɗaga hannunsa ya yo kanta sai kuma ya tsaya cak, a hankali da baya da baya ya dinga ja yana ƙare mata kallo sai kuma ya taune bakinsa idanunsa kamar zasu zazzago don girma kallo ɗaya idan ya yi dasu sai an razana da ƙyar ya iya ware laɓɓansa biyu da sukai masa nauyi sosai ƙasan zuciyarsa na ta fasa banda cewa Anty Hameeda ce tabbas da sai ya karya ta gida huɗu.
"Ni na kashe ta, ta cancanci haka ne" ya juya da sauri Tiger da spider da rainbow suka bi bayansa kamar zai tashi sama haka ya sha kwana. Zubewa Anty Hameeda ta yi a wajan tana rushewa da kukan baƙin ciki, su waye suke da saka hannu wajan lalacewar Mutallab? Ba komai ta sani ba ita ba ma'abociyar zaman garin bace ita da mijinta ta dinga kuka da ƙyar ta rarrashi kan ta, ta miƙe tsaye kamar zata shiga gidan nasu sai kuma ta fasa tana ƙoƙarin barin wajan ta ji Malam ya ce "Hameedatu me kike anan ina mijin da yaran naki?" Kanta a ƙasa ta ce "Suna gida, ina yini Malam?" Ya jujjuya yana kallon hannunta ganin babu komai ya ce "Ba za ki shiga bane?" Ta girgiza masa "Zan juya wajan Mutallab na zo" ya jinjina kai domin ba wannan ne a gabansa ba.
"Ba wata mutalla da zan iya samu a wajanki na siyo wainar rogo?" Ta buɗe jakarta ta zaro kuɗi tana irgawa ya yi maza ya fisge ya ce "Mene na lissafi? Maza jeki wajan yaranki kuma na ja kunnenki babu ke babu yaron nan idan ba su kike watarana ya ja miki masifar da za ki ƙare rayuwarki a gidan ɗan kande ba" bata ce komai ba sai data juya zata tafi ta ce "Duk lalacewar Mutallab kai ne ka haife shi, jininka na wanzuwa a nasa" tana kaiwa nan ta yi gaba abinta saboda ɓacin rai da damuwa ko gabanta bata gani sosai.
Moh na kwance a saman wani dutse idanunsa a rufe tun bayan barin shi wajan Anty Hameeda ya zo wajan ya kwanta, zuciyarsa a cunkushe take babu gurbin samun sauƙi a cikinta duk yadda ya ke son tuna waye shi me ya sa ya zama haka sai ƙwaƙwalwarsa ta yi hooking, ya ɗauki zafi sosai ta yi ta processing ya ji Ammo ɗinsa kawai yake son kasancewa da ita yanzu. Ya motsa kaɗan zazzaɓi ne sosai a jikinsa saboda saran da aka yi masa bai gama warkewa ba, baya kuma shan magani wacce zata iya kula da shi baya jin zai iya zuwa wajanta. Ya ƙanƙame jikinsa sosai abubuwa da yawa baya son tunawa sai ya cimma muradin zuciyarsa sai ya ɗauki fansa na abin da aka aika, sai ya bayyana abubuwa da dama tunda har suka bari ya shiga cikin gidan yari ya kuma yi shekaru uku a Cid ya rayuwa cikin masu aikata manyan laifuka. A sama ya ji an kira sunansa
"Mai dawa, sarki mai jeji" bai buɗe idanunsa ba, bai kuma ɗauki murya ba haka baya buƙatar sanin waye don hakan babu abin da zai ƙare shi da shi. Ya nemi waje ya zauna yana furta "Ka saɓe Mai dawa ka basar, fansa kake buƙata ba raunin zuciya ba, ka ajjiye tunanin baya ka fuskanci burinka ka zama abin da kake muradi kafin aga bayanka" har lokacin bai buɗe idanu ba, ko inuwarsa bata motsa ba. Mangal ya ɗaga kai yana busawa samaniya hayaƙin sigari "Idan kana son yin bacci cikin nutsuwa ka manta komai ya kamata ka sha wannan" ya zaro abu a aljihu yana kalle-kalle sai a lokacin Mai dawa ya buɗe rinannun idanunsa ya juya ya kalli mai maganar irin kallon waye kai? Mangal ya ce "Ka dake musulmi akul musulmu, zuwa na yi na taimaka maka"
"Riƙe wannan tiramol ce, ko doki ya sha sai ya gane barno gabas take kana afawa za ka ji zam-zam komai ya zama labari" Mai dawa zubawa ƙwayar idanu shi bai taɓa shan ta ba, bai taɓa shaye-shaye ba ya juya ya kalli Mangal "Da gaske zan yi bacci?" "Darr ne ai aikin wannan kamar yankan wuƙa ne, mai ƙirin ce da ƙyar aka bani ita ina karɓa na doƙu nan" jikin Mai dawa na rawa ya amshi ƙwayar guda ɗaya ya cilla cikin bakinsa, yana runtse idanu ya yi shiru. Mangal ya zubawa Moh idanu a ransa yana jin wani daɗi da kuma farinciki bai taɓa yin aikin da za a bashi kuɗi masu yawan da aka ce ba irin na yau, gashi ya yi nasara Moh ya sha ƙwayar. Jikin Moh ya ɗauki rawar zafin zazzaɓi duk da irin dariyar da yake da ita, gashi duk inda ya motsa ciwon shi jini yake babu wani wanda zai iya duba lamarinsa sannu a hankali ya fara dafe kan shi da wani irin gurnani yaga sama na jujjuya masa ya ɗaga hannu da niyyar ya tare sama ya faɗo daga saman dutsen sai saka hannu yake yana tare sama a hankali kuma jikinsa ya fara saki yana jin wani shuu a tsakiyar kansa yana game jikinsa gabaɗaya zuciyarsa da tunaninsa suka dinga kissima masa kawai ya kashe kansa ko ya cinnawa gidansu huta gabaɗaya kowa ya mutu har shi.
Ganin laɓɓansa na motsawa alamar yana magana ba'a ji sosai ya saka Mangal matsawa tare da kafa kunnensa a bakin Mai dawa cikin mawuyacin hali yake furta "Safiyyerh... Safiyyerh...Safiyyerh" Mangal ya maimaita sunan a fili “Safiyya?” wace haka? Ko ita ce wacce ta mutun wacce aka kashe? Ya miƙe tsaye ya ɗauki wayarsa wata number daya haddace ya saka ya kira ana ɗagawa Mangal ya ce
"Sakin nan ya kammalu, yanzu zan zo a taya na amshi fararen" shiru ya yi yana sauraren mai maganar kafin ya ce "Jira jira jira nifa cikin uwata aka haifan ba ɗan zina ba, na maka al'ƙawarin dole zan bawa Mai dawa ƙwayar kuma da sannu zai zama namu. Sai dai na ji yana kiran sunan wata ɗawa wai Safinu ko Safiya?" Ya ƙara yin shiru ya numfasa ya kalli Moh dake kwance a wajan ya ce "A'a Oga ni bana sabga da masu ɗan kwalin nan. Da ƙirin ka oga kanka baya kullewa a fice kake sai na doƙu yanzu" Kashe wayar Mangal ya yi kuma ya goge kiran cikin sauri kuma ya bar wajan.
Baya tantance halin da yake ciki, sai dai yanayin na yi masa daɗi sosai shi ba'a sama ba shi ba'a ƙasa yana fatan ya dauwama har ƙarshen rayuwarsa. Duk da a cikin giyar maye yake bai hana shi gano fararen kyawawan idanunta masu matuƙar ɗaukan hankali ba, a lokacin da take masa wannan duban ji yake kamar ba zai taɓa aikata abu makamancin haka ba amma ƙuruciya da wawta ya saka komai ya wakana a lokacin da duk su biyun basu ankara ba. Gani ranar yake kamar yanzu a cikin idanunsa ya juya da ƙyar yana buɗe idanu zuwa gefe guda sai fara hango kansu su biyun a shekarun da suka huce suna tsaye tana jifansa da wani irin kallo.
Suna tsaye za su shiga practical a lokacin, ya jingina da jikin bango ƙafarsa ɗaya a jikin bangon ɗaya a ƙasa ya harɗe hannayensa duka biyun a ƙirji students ɗin yake kallo yana mamakin abin da ya saka ƴan mata ke burge wasu mazan, as a man kuma good man kawai ka nemi kuɗi ka yi arziƙi ka shahara a duniya shi ya fi, ka zama mai iƙo da faɗa a ji, ka zama wanda zai iya samun abincin da zai ci da safe kuma ya ci da rana ya ci kuma da dare ya bawa ƴan'uwasa da duk mai jin yunwa ya zamana kuma ka kasance mutumin da ake shakka duniya ta san da zamansa bawai kana namiji ka ƙare a wajan wata yarinya ba. Yana cikin wannan tunanin ya ji an ja mugun tsaki ya buɗe idanu ya ganta sosai ya buɗe idanunsa da suke a rufe kodayaushe cike da gashin idanu masu tsayi.
"Kai ai babu macen da zata soka a school ɗin nan, sai dai kaga ana soyayya" bai taɓa tsayawa ya tanka ta ba sai lokacin har zai mata shiru sai ya ce "Ok" ta haɗe fuska "Saboda macen abinci ce ko iskar shaƙa daya zama dole Mutallab ya amfana dasu?" Ta yi masa sheƙeƙe tana nuna masa ɗaliban makarantar da kana ganinsu zaka san iyayensu nada arziƙi sosai kowanne a students ƙuruciya da tashen balaga na ɗawainiyya da su. Ta ce "Mata ai sune jin daɗin maza, kai fa mace ko kiss bata taɓa yi maka ba a school ɗin nan" Mutallab ya yi ta kallonta daga sama har ƙasa "Matar Moh zata zama mai irin halin MOH" har ya juya sai yaga bata ci bulus ba ya tako har inda take ya zuba idanunsa cikin nata kamar yadda take kallon tsakiyar nasa idanun yana sake matso da fuskarta "About the kiss, ƙilan Moh ya ji ƙan ki ya yi miki don naga shi kike buƙata"
Tsoro ya kamata amma ta dake ta fara ja baya ya yi saurin saka ƙata ya falleta kamar zata kita ya saka hannu ya cafko gaban wandon uniform ɗinta ya dawo da ita dab dashi yana sauke mata numfashi a hankali kuma ya ɗora fuskarsa..... "Mai dawa" kiran da aka yi masa ya saka bidiyon abin da ya faru a baya saurin gogewa a idanunsa har lokacin idanunsa na kafe waje guda sosai yake son sake tuna abin da ya faru a lokacin ya gagara. Goje ya ce "Nan ka auno kenan, na samo sha ɗayan gayen nan. Ya naga kamar a buge kake?" Goje ya faɗa yana tattaɓa jikin Moh ya ji zafi sosai idanunsa kuma ya kaɗa ya yi ja ya san babu abin da zai fahimta koda ya yi masa bayani "Mene haɗin mafarauci da shaye-shaye?" Shi dai ya yi shiru kawai zumbur kuma ya miƙe tsaye kamar wanda ya tuna wani abu ya juya idanu wuƙar da ya gani a jikin Goge ya fusga duk yadda Goje ya yi da shi amma ya kasa amsar wuƙar cikin sauri kuma ya mara masa domin ganin me zai aikata?
Tafiya suka dinga yi har suka kawo titi ya tsayar da mai napep ya faɗa shima Goje ya faɗa ciki. Shi kansa bai san ina za a kaisa ba. Tafiya suka sosai har suka ƙarasu daidai wajan wani ƙaton kamfani wanda kaf Kano babu wanda bai san zaman wannan kamfanin ba. Iya haɗuwa ya haɗu ginin kamfanin ma abin sha'awa ne ga masu tsaro ta ko'ina. Ya tsayar da mai napep ɗin ya sauka "Kuɗi na?" Ya buɗe ido sai ya share "Malam haƙƙina na daƙƙoka daka waje mai nisa ina da wajan zuwa" Goje ya ce "An cinye"
"Kut, ni da haƙƙina daman tunda na daƙƙo ku na ji kuna warin wiwi na san cewa ɓarayi ne ku, cikakken ɗan zamani ne nima ku bani kuɗina yanzu ku na daki kuɗin" Goje ya ce "dan babarka zo ka daka idan ka haifu" mai napep ɗin ya share shi, ganin Mai dawa ya yi shiru yana kallo kamfanin ya nufi inda yake ya damƙi wuyansa ya ce "Kai ka tsare ni ai....," kafin ya ƙarasa maganar Mai dawa ya damƙi hannunsa ya matse ya bada sauti ƙass har lokacin ya kafe kamfanin da idanu. Mai napep ɗin na ihu yana neman ɗauki Goje ya zaro wuƙa yana bubbuɗe jajayen idanu hakan ya saka ba wanda ya zo wajan kowa saurin barin hanyar yake gudun kar tsautsayi ya faɗa masa. Mai dawa ya saki karyayyen hannun mai napep ɗin ya ƙara damƙar ɗayan zuciyarsa na tafasa har yanzu ba komai yake ganewa ba, ya sake karya hannun daman ba tare daya sake shi ba ya ce
"Goje"
"Mai dawa sarki mai jeji, sai godiya"
"Kamfanin meye wannan? Na waye kuma?" Goje ya kalli tafkeken kamfanin da manyan motoci ke ya shiga da fita kafin ya ce "Sai godiya, ciki ne a kan sabgar nan bani da ilimi akan wannan massarafar"
Mai dawa ya saki mai napep ɗin da ya karya masa duka hannunsa biyu yana ja da baya a hankali ya ce "Ina son shi, ina son ya zama mallakina" cikin sauri Goje ya ce "Me kake so?"
"Kamfanin"
Tana zaune akan kujerar dake haɗɗan office ɗin, cikin nutsuwa dake danna system ɗin gabanta files da yawa cike saman table ɗin hankalinta na kan aiki sosai kana kallon fuskarta zaka san serious ce ita akan aikinta bata da wasa ko kaɗan. Brown suit ce a jikinta mai riga da wando ta yi rolling kanta da mayafi zagayayyiyar fuskar ta fito sosai ta saka wani shade a idanunta baƙi. Wayarta ta fara ƙara alamar kiran ta san tunda ya fara ba zai daina ba, cikin nutsuwa ta murja kujerar ta yi ba, suu kuma ta kujerar zuwa inda wayar take ta ɗaga kiran tana sawa a hands free
"My manager" ta ɗan buɗe idanu ta cikin glasses ɗin ta yi shiru tana ta danna system a hankali ya ce "Maamah" ya kira ta kamar yadda suka ce mata ta sake yin shiru domin bama ta jinsa sosai "Fiyya ina miki magana?"
"Yaya J yaushe zaka fara ɗaukan aikinka very serious, ina kan aiki fa" ya yi murmushi mai kyau tana jin sautin shi a kunnenta "Sanda kika so na zama Mamaa"
"Uhm kiran fa?"
"Kin ci abinci, nina manta Captain ya saka na kira na tambaye ki" cak Fiyya ta tsaya da abin da take ko dai bata ji daidai ba "what?" Ya ce "Kin ji ai" a taƙaice ta ce "Na ci" ya ce "Good, ƙarfe nawa za ki tashi?"
"Ina da meeting Yaya J ka biyo ka ɗauke ni i can't drive cikina ciwo" cikin sauri ya ce "Subuhanallahi! Bari na zo na duba ki ko kawai mu tafi gida" kashe wayar ta yi domin ba wani ciwon ciki da take so take ta saka kanta busy sosai ko zata manta da wasu abubuwan. Knocking aka fara tana ji ta yi shiru can ta ce "In" ya buɗe ya shigo idanunsa ya sauka a jikin sunanta dake manne a table ɗin “SAFIYYERH A. MARAFA” ya ɗauke idanunsa yana rusunawa ya ce "Good day Maa"
Da hannu ta yi masa nuni ya zauna bayan ya zauna, still idanunta akan system tana danna keyboard ta miƙo masa file ya ɗauka ya ce "Wannan fa?" A nutse ta ce "I have to ask, daga ina file ɗin nan? Wanne kaya aka fitar aka samu ruɓanyar kuɗi kashi wajan goma cikin awa guda Accounter?" Ya ɗan shafa kai ya ce "Maa ni ma haka na gani, kawai aka ce na kawo ki saka hannu"
"To ba zan ba" ta ce a taƙaice. "Maa ya zama dole fa"
A hankali ta ɗago idanunta sai kuma ta cire glasses ɗin idanunta manyan fararen idanunta tas a kan shi ya yi saurin ɗauke nasa idanun saboda kwarjin da ta yi masa "Ni ce Manager, ka faɗawa duk wanda ya turo ka cewa ba zan ba, ina buƙatar explanation me aka siyar a kamfanina nan har aka samu shigowar kuɗi kimanin 5.1B cikin awa guda, ba details na abin da aka siya sai file na zuwan kuɗin kuma yanzu ana buƙatar fitar dasu daka account ɗin kamfani? This is complicated" zai yi magana cikin tsawa ta ce "Out of my office accouter" cikin saurin ya miƙe tsaye yana ficewa daga officer ɗin. Numfashi Fiyya ta sauke ta rufe idanunta da sauri kuma ta buɗe jin an shigo ba tare data bada umarnin a shigo mata officer ba. Cikin sauri ta miƙe tsaye tana ɗan ja baya ta shiga ƙare masa kallo daga sama har ƙasa ta yi mamaki to babu security a ƙofar office ɗin nata ne? Da ƙyar ta ja numfashi tana saukewa ta ce.
"Who are you? Waye kai.
For more information
08164069385
WhatsApp only.
[1/7, 9:32 PM] Sis Fauzy: *❤🔥 MUTALLAB ❤🔥*
Page 4
Nimcyluv
*Bright pens....Second batch*
Ƙarewa office ɗin kallo ya yi yana buɗe idanunsa akan Fiyya wacce ta ɗan ja da baya tana ɗauke kanta gefe. "Ya Allah i really missed her, Safiyya A. Marafa" ya furta yana kallon makaken photon Fiyya dake cikin office ɗin kafin ya ƙarasa ciki murya a hankali ya ce
"Wa kike tunanin zai zo banda mijinki Fiyya? You're enjoying teasing me" sai a lokacin ta sauke ajjiyar zuciya a ɓoye tare da ɗan yin murmushi mai kyau wanda ya saka shi lumshe idanunsa ya buɗe "Like this.... I missed you completely Fiyya ba shiri na dawo gida fa"
"Ina yini ya hanya?" Ashraf na kallon files ɗin gabanta ya ce "Allahamdulilah. Ya naki aikin Manager?" Ta ce "Lafiya, me ka zo yi a kamfanin ko kana da business damu ne?"
"Eh, babban business ma" tana kallon system ba yabo babu fallasa ta ce "Ohh" kallon ta ya dinga yi yadda take operating system ɗin cike da nutsuwa fuskarta a kame ba wargi hakan bai hana kyan fuskarta bayyana ba ya ja numfashi ya sauke yana jin wani abu sosai na fuskarsa a kan Fiyya ya kalli agogon hannunsa ya ce "Ko gida ban je ba, ina son na samu nutsuwa da kallon fuskarki dear" kamar baza ta ce komai ba sai kuma ta ce "Ok" mamakin halinta na ko ina kula yana damunsa cikin damuwa yana sassauta murya ya ce "Fiyya" ta ɗago ta kalle shi sai kuma ta zame idanunta.
"Na kasa fahimtar me kike nufi dani Fiyya anya kina so na kamar yadda nima nake son ki? I told you na dawo saboda ke amma ki ce mini wani ok? To hell with the ok ɗin na tsani irin wannan ɗabi'un naki, da na yi miki uzurin rashin sabo ne amma for good 5years muna abu ɗaya dake? Idan customers ne kya musu fara'a ki yi welcoming nasu, amma ni da zan zama mijinki kwana kwana nan kike ma haka, ko wanne gardi ya zo office naki kin zama wata kamar jerry abar kallon kowa" ya girgiza kai cikin damuwa da ƙunci yana zare gilas ɗin idanunsa tare da buga table ɗin gabanta ya ce
"A cikin abu biyu dole ne a yi guda"
Kallon Ashraf kawai take ta tabbatar yana da anger issues tama rasa me za ta ce masa don takaici ya zo har office ɗin ta kuma yana yi mata hayaniya, yana ƙoƙarin tara mata jama'a. Ko motsi ba ta yi ba, tana juya kujerar da take kai a hankali idanunta zube a kansa. "Ina ji Ashraf" bata taɓa kiran sunansa ba sai yau hakan ya saka ya kalleta da sauri ransa ya ƙara ɓaci.
"Aure ko aiki, ya zama dole ki zaɓi guda ɗaya a ciki"
"Ok" ta sake cewa tana miƙewa tsaye tare da ɗaukar jakarta da wayarta da makullin mota ta zaga a hankali zata shige shi ya yi saurin saka hannu ya riƙo nata hannun cikin sauri ta kalle shi tare da jefa masa wata iriyar harara sakinta ya yi ya matsa dab da ita yana sauke mata hucin numfashin ɓacin ransa dake fitowa tun daga ƙasan zuciyarsa.
"Ki bani amsar abin da na buƙata kafin ki fita, aikin ki ko aure"
Ta taune leɓenta tana ware masa manyan idanunta sai kuma ta kalli wayarta tare da buɗewa ta shiga wajan photos pictures ɗinsa ta nemo wanda ya yi kyau sosai ya saka ƙananun kaya lokacin bashi da lafiya ta je duba shi ya fito harabar gidan tana murmushi ta ce "My patient, bari na ɗauki photo as evidence karka mutu bani photon nunawa yarana masoyin da ya tafi ya bar Fiyya" a lokacin juyawa ya yi ya kalleta daga kwancan da yake ya wurga mata harara sai kuma ya miƙe tsaye yana nufar inda take ta yi saurin yin baya tana masa wani irin murmushi ya tsaya yana kallon ta sai kuma ya ce
"To make you clear, ba ki da wasu yara sai na Ashraf, ba ki da wani miji sai Ashraf ba wanda za ki yi wa takaba sai Ashraf.... Ashraf na Fiyya ne Fiyya kuma ta Ashraf ce in sha Allah" murmushi kawai ta yi bata ce komai ba ta ɗauke shi photon yana langwaɓe kai gefe.
Fiyya ta shafa screen ɗin wayarta tana kallon photon kamar yanzu ta ɗauka cikin muryar mara hayaniya idan tasu ta ce "Ya ce wai na zaɓa aiki ko shi, kar ya buƙaci jin amsar daga bakin Fiyya" fisge wayar ya yi "Dole ki bani amsa yanzu ba sai anjima ba" ta gyara tsaiwa tana fuskantar shi da kyau a hankali ta matsa dab da shi ta ce "Allah Ya baka wacce ta fi Fiyya" Ashraf ya yi sak can ya ce "Me kike nufi?"
"Ina nufin na haƙura da auren, na zaɓi aikin" tana kaiwa nan ta fisge wayarta cikin sauri ta yi waje ya bita da kallo zuciyarsa na ta fasa. Tana fita ta kalli security ta ce "Idan ya fito a rufe mini office" waje ta yi ko Elevator bata tsaya shiga ba ta sakko ta bene dake a wajan 5 floor office ɗin nata yake. Sai gaisheta ake yi amma ba wanda ta saurara idanunta har dishi-dishi yake saboda ɓacin rai.
Misalin 1:43 dare ya nutsa ana samawa zuciya nutsuwa ya yinda kowa yake bacci a lokacin ne safiyarsa ta waye. Ya tsaya a ƙofar gidan yana kallon gate sosai ya jima a wajan kafin ya juya ya kalli Goge da Darma cikin hanzari Goje ya shiga buga gate ɗin gidan kamar zai cire shi, sun jima kafin daga bakin ƙofar suji an ce "Waye?" "Buɗe" Goje ya ce yana zare wuƙa tare da matsawa jikin ƙofar mai gadin a ruɗe yake sosai ya ce "Kamarya na buɗe a wannan zamanin da muke cikin insecurity na sani ma ko ƴan fashi ne?"
"Sune" Darma ya ce yana yin muzurai shi kaɗai ne a cikin su yake a buge shi Moh abin da Mangal ya bashi har yanzu bai gama sakin shi ba, shi ya sa ba komai yake ganewa ba. "Wallahi ba zan buɗe ba, babu mamaki kun ji Alhaji Wada ya dawo gari shine za ku yi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 17