Share this page
Qualities bata yin abun da za a iya following footsteps ɗin ta, she is a clever girl faɗanta har tsoro yake bashi ga taurin kai da miskilanci har addu'a yake Allah ya sassauta mata sai gashi Ubangiji ya gyara komai a lokacin da bai zato ba. Ya ɗauke kai yana kallon wani gefen "Aliyu yaushe ka dawo?" Idanunsa a kan waya yana dannawa, wandon uniform na sojoji ne jikinsa sai fara t.shirt tas wacce ta kama damtsen hannunsa ya saka p.cap ta sojoji fuskarsa kamar ya ce ya shiga uku can ya ce "Da daddare" "Dare da yaushe? Aliyu kai kana son shigowar dare kamar mara gaskiya?" Captain ya ɗan kalli daddy ya ce "Tun 12" "Kuma baka shigo ba me ya sa?" "Kawai daddy" ficewa ya yi yana cilla wayar a aljihu yana jin Fiyya na gaishe shi ko inda take bai kalla ba. "daddy ni ba zan iya ɗaukan wannan halin ba wallahi bai ishe ni kallo ba zan daina ko gaishe shi ina dalili, Safiyyerh Abdu Marafa na da class babu mai ɗaga mini shoulder, duk wannan abun da ya yi aure a waje ne yake soja" Ranta duk a ɓace ta miƙe tana cewa daddy ta tafi ya ce "Allah Ya tsare Manager ya shirya safiyyerh Abdu Marafa". Kasancewar sauri take yi ta saka ta yi driving kamar zata tashi saman bata wasa idan tana kan titi, tana isa ta buɗe office ta shiga fahimtar da sabuwar envelope a table ɗin ya saka ta sa hannu ta ɗauka tare da buɗewa taƙaitaccen rubutu ne mai ɗauke da jan biro wanda ke nuna rayuwarta na cikin matsala. A hankali ta fara duba consent ɗin da takardar ke ɗauke da shi tana ajjiye waya. “Jarumtarki bai kai ki tsaya bincike akan FS WORLD INVESTMENT COMPANY ba, kina iya ɗaukan rubutun matsayin wasa amma gargaɗi ne da jan kunne ga yara masu rawar kai irin ki. Ki tsaya da binciken da kike you're nothing but a manager” Ta dinga juya takardar a hannu tana jin confidence nata na ƙara hakan kamar wata dama ce aka haska mata na nuna cewa lallai akwai ƙullalliyya a wannan kamfanin, kuma ta shirya buɗe faifai ko da za su yi zubaibai ƙwarya ne, ko da gaskiyar da take ƙoƙarin bayyanawa zai yi silar barin ta numfashinta daga ƙirjinta. Ta yi Addison na cikin abubuwan da take ƙarawa a binciken za ta yi komai ko hakan na nufin fito na fito da surukinta ne. Zama ta yi ta fara duba files na sabbin kayan da aka kawo can ta saka aka kira mata accouter bayan ya shigo ba tare data kalle shi ba ta ce "Accouter kana buƙatar wani abu ne?" "Allah Ya taimaki manager kamarya fa?" Still bata kalle shi ba ta yi baya tana duba maganar da aka turo mata yanzu a waya ta ce "kawai kuɗi idan kana so na buƙatun rayuwa" "Ina jiran lokacin albashi ya yi ai nasan za a sallame mu da wuri" ta ɗago idanunta masu sanyi ta zuba a kan shi sai ta cillo masa ƙaramin file ta ce "na saka hannu ka yi signature as a accouter ka cire 1m a asusun kamfani na baka" da mamaki ya ce "Ni kika bawa kuɗin?" "E, ko baka so?" "To na ga ban yi wani aikin da na cancanci 1m ba kin sa na fara jin tsoro ba zan iya cin abin da ba haƙƙina ba" ta ɗan yi murmushi ta janyo files ɗin ta yaga ta ce "meye cikakken sunanka ma?" Rainin hankalin Manager mamaki yake bashi sai kawai ya ce Wazeer" da hannu ta ce ya je yana fita ta saka aka kira mata MD abin da ta yi wa Accouter shi ta yi wa Md cikin sauri ya ce "Yanzu kika ɗakko hanya manager da za ki haƙa ramin da za ki iya binne kan ki ciki ai duk sai na raina wayonki wallahi da ajin nan naki ko mene a ƙasa ba ruwanki mind your own business rayuwar nan kana kallon wasu abubuwan kake yi kamar baka sani ba, to a haka cibiya ta rai ne mu kuma yanzu hankalin jama'a da yawa na kan siyasa, matasa na neman hanyar karatu, wasu na can suna bautawa ƴan siyasa, wasu sojan baka wasu rayuwar social media wasu bangar siyasa wasu kasuwanci. Safiyyerh da yawa ana yin abin da ya samu ne ko yazo hannu ba wanda kake ganin cancnatar shi ba, ba a duba capacity na abu ko a siyasa kana ji kana ganin wanda ya dace amma kake rufe idanu ka ɗauki baragurbi saboda yana watsa maka hatsi mu ɗin kamar ka ji suka ɗauke mu, think big Fiyya ke macace babu mai ce miki don me, akwai kuɗin da shi kan shi Alhaji Baihaƙi bai sani" "Kana son siyasa" Md ya yi murmushi ya ce "Safiyyerh siyasa yanzu ai kusan a jinin kowanne matashi take, kinga muna da jam'iyyu uku ɗaya ce mai ƙarfi saboda ita ke riƙe da muƙami ma'ana ƙasar a nan Hon Maɗatai yake neman takarar kujera, sai jam'iyyar su Eng Ali wali sai last jam'iyya wacce mutumin cikin ta ya fi kowanne nagarta kuɗi masu dame shi ba, da ƙyar aka taushi zuciyarsa yake muƙamin kusan matashi ne matasa na son shi amma kasancewar yana cikin jam'iyya ƙarama kusan sabuwa ya sa ba a yin maganar shi ma kuma da ba musulmi bane" Safiyyerh ta jinjina masa kai ta ce "Ka bawa accouter ya yi signature a baka 2m, enjoy yourself MD, but sunan wanda kake bani bayani yanzu?" Ya washe bakinsa ba ƙaramin jin daɗi ya yi ba ya ce "Abraham Denial David, shine ɗan takarar" "Yana da hannun jari a nan ne?" "A'a, i don't think zai saka hannun jari a nan gaskiya" a hankali ta ce "Me ya sa?" "Kar ki zurfafa a bar maganar, za mu yi aiki tare" sallamar shi ta yi tana jin zata yi amfani da Md da accouter Md zai taimaka wajan sanyawa ta san sirrin kamfanin cikin sauƙi accouter zai taimaka wajan bayyana komai. A gefe guda tana jin kamar ta shiga batun siyasar Abraham ɗin kawai ta ji ya yi mata she just want to help him. **** Su da kan su sun kwana biyu basu saka shi a idanunsu ba, ba kuma su samu labarin inda yake ba sai yanzu da suka ganshi kamar walƙiya kwance a ƙasa idanunsa buɗe yana kallon sama Darma ya ce "Sai godiya wanda ya ce zai bi sawunka ya wahala, ɗan malam yaƙi halin malam dafinka ƙarinka masifa ne idan ka taɓa mutum da shi" "Darma" "Ka dake Mai dawa ka jima ka yi lastin irin na dabino, wa kake so a taka a kashe ko a yi masa fiɗa" Darma ya ce yana buɗe hannu sama tare da karkatar da baki hannunsa riƙe da ledar pure water ya nannaɗe a hannu yana kaiwa baki tare da zuƙa. Mutallab ya sake buɗe idanu a sama ya kasa cewa komai tunaninsa ya tafi wani wajan. Goje ya ce "Sai godiya matsalar goge ce ko wato ka kayan lantarki" "Zaman gidan yari ba daɗi,amma na ji daɗi" "Ka ce ka tuna na jakuna nan cinnaku tsakaninmu da su sai ƙarfe ba ma'ana ka tuna na jakin da suka haɗa maka kenan" "Ina jin zafi a ƙirjina farcuna na da suka cire mini sun ƙi fitowa, zan ɗauki fansa Goje" Kafin su yi magana an yi sallama an ƙarasu cikin sauri Mutallab ya rufe idanunsa jin muryar zabuwa. Goje ya dinga kallon wacce take tsaye "Bayin Allah sallama nake muku fa" Mangal ne ya kalleta sosai ya ce "Yi batu" ta ɗan rausayar da kai gefe ta ce "Amma dai ku musulmai ne amsa sallama wajibi ce" "To alaiki, mene sagin aiki kike so a yi miki?" Kinal ta fito da littafi da biro ta ce "Sunana Kinal ni mawaƙiya ce, har zan shige na hango ku na ji ina son tambayarku na ji ina son na yi waƙa akan ku kasan mu da mu da marubuta kusan aikin mu ɗaya muna da son bin ƙwaƙƙwafi" Goje ya ce "To ina ruwan mu? Fece kafin na yi miki lahani" "Ku ba ƴan shaye-shaye bane? To akan shaye-shayen zan muku tambaya ina yin waƙar zan kawo muku ku ji, idan kun yi shaye-shayen me kuke ji mene dalilin daya saka kuka fara shaye-shaye kuma kuke harkar daba" Moh na jin su ya juya musu baya zaka ɗauka bacci yake, ransa duk a ɓace saboda jin muryar mace da ya ji ya san daya juyo zai iya kashe ta tsaf don bashi da wani business da mata. Darma ya ce "Yanzu yadda muke ji za mu faɗa miki kenan?" Kinal ta yi saurin cewa "E, wallahi na iya waƙa ina da murya sosai babu mamaki idan na yi waƙar na saka a YouTube ta je viral na saka a tiktok ta yi trending" Darma ya ce "To ni dai tun daga sanda a gida na yi...,"Da sauri Goje ya tsayar da shi yana cewa "Kai amma ɗan tsinanniya ne kai, ba haka ake bayani ba" Miƙewa ya yi ya ce "bari na faɗa miki" wuƙa ya zaro a ƙugunsa Kinal ta zare idanu tana yin baya cikin sauri Mangal ya tare bayan jikinta na rawa ta fasa ihu jin yadda Goje ya yanke ta da wuƙa a fuska,ya danna mata ledan wiwin a baki ta fara zare ido tana ihu. Sai a lokacin Moh ya juyo yana kallon yarinyar ya cije bakinsa tare da juyawa exactly irin ihun da Safiyya ta yi lokacin zata mutu. "Gani ya kore ji, idan kin rero waƙar muna dakon ki a nan sata ƴar munafuka" Darma ya dinga tuntsira dariya sosai yana riƙe ciki "Amma Goje baka da imani kamar fa fitsari ta yi a wando gaskiyar kurciyar nan akwai jan ido ga bayani nan kin gani ganin idanunki ai" ya juya ya kalli Moh ya leƙa ga wata cukurkuɗaɗdiyya takarda yake karantawa shi ba wani karatu ya yi ba "Wai wannan takardar mece kamar ta asiri kodayaushe tana wajanka, kamar numfashin shaƙa ka faɗa mana ta mece" cikin sauri ya ɓoye yana damƙe ta a hannu Goje ya ce "Nima sai fakon farar nake na mata karatun makarantar allo, na rasa wacce tsiyar ce a ciki" "Goje" "Sai godiya" "Zan saka maka tsini idan ka taɓa takardar nan ko na saka su tiger cinye ka ɗanye, wallahi zan iya kashe ka akan takardar nan" Kafin su yi magana an zo da babur an cillo wata takarda da sauri mai babur ɗin ya juya, Mangal ya miƙe tsaye ya ɗakko ya buɗe cikin sauri ya kalli Mai dawa dai kuma ya miƙa masa amsa ya yi ya duba, photo na gudu biyu ne ɗaya zanen fuskar wata kamar dai mahaukaciya sai kuma photo jira-jirai, photo me mai magana ga wanda yake da cikakken lissafi a gefe an rubuta FS WORLD INVESTMENT COMPANY. **** Kwana biyu Safiyyerh ta yi busy duk wani family sun zo saboda gobe ne ake ɗaura auren, kamar auren munafurci ba wata gayya ko shagali ɗaurin aure ne kawai ana yi kuma Ashraf zai ɗauki matarsa su tafi. A daren ranar Safiyyerh ta riga data gama accepting auren Ashraf ta yarda bata da wani miji sai shi zata sawa zuciyarta yadda zata zauna da shi tunda tana son shi ko ba can ba. Waya suka yi da Ashraf ya dinga tsokanarta "Har na hango idanun Maama a ɗakin miji, mijin na kuma Ashraf ta yi nasarar samun kyakkyawan saurayi" ta murguɗa masa baki ta ce "Zan fasa" ya yi saurin cewa "Idan ki kaga ba ki auri Ashraf to mutuwa na yi ko ke kika mutu, da gaske Fiyya ina son ki Allah shine shaida duk da ina dalilin auren ki ko saka ni akai na yi hakan amma na yi you're my life partner har janna in sha Allah" "Kamarya? Mene dalilin auren?" "Ke ba ki da wani favourite words ne sai kamarya, zan faɗa miki komai a daren ranar da kika zama halaliyyar Ashraf zan faɗa miki, zan sauƙaƙa miki binciken da kike akan Company" a ruɗe ta ce "Ta ya ya kasan ina bincike akan Company" "Safiyyerh kenan, that's is the difference between man and woman, ina da baƙi sai goben idan na zo ganin matata a wannan lokacin dole na rungume ki halal runguma zan miki Safiyyerh" hankalinta duk a tashe waye Ashraf ne me ya sa daddy ya amince da auren shi? Ta kasa magana har ya kashe kiran sai ya ƙara kiranta video call ƙura mata idanu ya yi taga yana shiri cikin sauri ta ce "Kuma sai ina?" "Inda kika aike ni" ta buɗe idanu "Kamarya?" "I miss you Fiyya shine abin da na manta na ce miki, a nan nake jin motsin ki" ya nuna mata saitin ƙirjinsa, daga nan ya kashe wayar. Daga ƙarshe ta yi zamanta cikin bedroom Awais har bedroom ya shigo ya dinga mata shira "Yaya Aiwas ka ɗan yanke mini farce" "to ban taɓa ganin amarya irin ba tunda nake a duniya" ya jawo ƙafar ya fara yanke mata farce ta rufe idanu. Washegari da sassafe Fiyya na bacci daddy da kan shi ya tashe ta, ta farka da ƙyar saboda kan ta dake ciwo mamaki ta yi ganin kusan family a ɗakin ya kalleta ya ce "Kin dai yi sallah ko?" Ta ɗaga masa kai "Daddy lafiya?" Ya yi shiru ya ce "Junaid je ku fara yin gaba, Captain an kira shi yanzu daga can headquarter, Ummi ɗakko mini hijabin Maama" Hijab ya karɓa ya saka mata ya riƙe hannunta Anty Turai ta yi gaba tana zabgawa Fiyya harara har harabar gidan suka je, abin mamaki gidan shiru ta rasa meke faruwa a motar daddy suka shiga yana baya riƙe da ita Awais na jan motar da Ummi. Motar Fiyya kuma da ita Captain ya yi using wajan fita saboda shi bai Fiyya ɗaukan tashi ba. Fiyya ta yi shiru kan ta a ƙasa,har suka ƙarasu cikin babban gidan mai tarin jama'a daidai lokacin aka fito da shi daddy na riƙe da hannunta ya ce "Mamana je ki masa addu'a" "Addu'a? Daddy waye?" Ta furta muryarta na rawa ta juya ta kalli makarar da aka ajjiye gabanta ɗauke da gawa, ya sake riƙe hannunta da kyau ya jata zuwa gaban makarar ya duƙa tare da yin namijin ƙoƙarin buɗewa. Fiyya numfashinta ta ji ya ɗauke lokacin da idanunta ya yi arba da gawar Ashraf dake kwance cikin makara, jira ya fara ɗaukar gangar jikinta da gaske Ashraf ne kwance ba yau aka ce za a ɗaura musu aure ba shine zai mutu anya gawar Ashraf ce numfashinta ya tsaya cak tana daga tsayen suka ji ta yi wani irin ajjiyar zuciya tare da yin baya cikin sauri a tare daddy da J suka tare ta, ta ƙarasa suma a jikinsu. Bayan sallatar gawar Ashraf da binne shi duk ana zaune ana addu'a daddy ya ce yana neman alfarma don Allah suka ce tame "Kar a tambayan hujja ko dalili a yanzu ina son a ɗaura auren Safiyyerh da Aliyu". *🫠for now na san a ranku za ku yi ta wasu wasu, wasu ma su ce ba su gane inda labarin ya nufa ba😛ku dai nutsu tafiyar kura ce mai tsarƙaƙƙiyya har nishaɗi kuke bani idan ana comment tafiyar da hasashe ku lissafi ba zai taɓa kawowa tunanin mutum ba, kar ku ji kun karaya domin na san dole a gaba zaku buƙaci labarin, har yanzu shimfiɗa muke yi iya shafi 8 mukai* Littafin MUTALLAB na kuɗi ne kuma za a ke yin posting kullum. An fara biya yau domin shiga paid group na MUTALLAB. MUTALLAB. Book 1, 2 &3 500 Naira 0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S.... A tura shaidar biya ta nan 08164069385 ku yi ku biya a sati uku mu kammala 🫠 Domin gyaran nono ❤‍🔥🔥💃 Assalama alaikum Hajiya muna da ingantaccen maganin gyaran nono wadda ya amsa sunansa magani Maganinmu ingantaccen maganine da yake tada jijiyon nonon da suka saki y'ar uwa breast dinki ko yakai silifas saboda kwanciya kikai amfani dashi in sha Allah zakiga amfaninshi acikin 1week maganinmu powder ne yana ciko da breast y gyarasu bashi da illa ajikin mutum munyi amfani da saiwoyi da magunguna gargajiya domin gyaran breast 08063114606 ina garin kano karki sanya y'ar uwa nono yana karawa mace martaba a gurin mai gida maganinmu kowa zai iya sha wadda zatai yaye ko gyara budurwa duk zasu iya sha breast dinki ya ciko yayi bull -bull [1/7, 9:33 PM] Sis Fauzy: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥* Page 9 *Bright pens..2nd batch* "Bani da wani zaɓi sai na hakan, haɗa auren Aliyu da Safiyyerh kar ku tambayan dalili kar a tambayan cikin Safiyyerh da Aliyu waye ba ƙwayar halittata bace ta yi sanadin zuwan shi duniya, hankalina zai fi kwanciya kafin Ashraf ya kwana cikin kabari ya zamana Safiyyerh nada igiyar aure a kan ta" ajjiyar zuciya Sharfaɗi ya yi idanunsa a kan Prof Abdu Marafa ya ce "Me kake jin tsoro da kake so dole ka aurar da ita, Allah Ya gani amintar mu ya saka muka yanke hukuncin haɗa yaran nan aure saboda ƙarfafa zumunci, to kana taka Ubangijin talikai na tashi nasa kuma shine gaskiya, Ashraf ya rasu baya duniya ina tunanin ka bar yarinyar nan ta samu nutsuwa ta duba wanda take so yake son ta sai a yi mata aure, kar a ƙuntata rayuwar yarinya" "Sharfaɗi ba zaka fahimta ba, ka yi mini wannan alfarma ka wakilci Aliyu ni zan wakilci Safiyyerh ga jama'a su shaida Please sai a haɗa a yi addu'a har ta Ashraf" J zufa har yanko masa take yi na tsananin mamaki mene haɗin Captain da Safiyyerh da za a yi musu aure? Baya son zuciyarsa ta gasgata abin da yake jin tsoro ko wassafo shi cikin kan shi, Safiyyerh fa and Aliyu? Ya Allah! Shi dai Awais kan shi a ƙasa Dr Hash daman baya wajan yana can duba Fiyya tunda ta faɗi wajan ya yi shiru can daddy ya ce "Kawai alfarma nake nema zan ji daɗin hakan idan ka yi mini" "To shikenan, waye maɗaurin auren?" Daddy ya nuna wani abokinsa, Sharfaɗi ya ciro kuɗi mai yawa a cikin aljihu ya dire ya ce "Ni Sharfaɗi ina nemawa ɗana Aliyu Abdu Marafa auren Safiyyerh Abdu Marafa a wajan waliyi na wannan yarinya" daddy ya saka hannu ya ɗauki kuɗin ya ce "Ni Abdu Marafa uba a wajan Safiyyerh Abdu Marafa na bawa Aliyu Abdu Marafa auren yarinyar wajena Allah Ya sanya musu albarka" addu'a aka yi nan take kuma aka ɗaura auren a gaban shaidu ma ɗaurin ya ce "Aure ya ɗauro a kan sadakin da Sharfaɗi ya bawa dubu ɗari biyu, Allah Ya sanya albarka tsakanin Aliyu da Safiyyerh ya kuma kaɗe fitinar da kan iya wanzuwa a tsakaninsu" duk aka amsa da amin. Daddy ya lumshe idanunsa yana sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya nutsuwar ta saukar masa, bashi da sauran fargaba a yanzu Safiyyerh ta zama matar wani. Kasancewar rasuwar ɗan babban mutum ce kamar Sharfaɗi ya saka manyan mutane zuwa gaisuwa, ƴan kasuwa da ƴan siyasa da wanda dai suke jin kansu wasu ne a garin. Kallo kallo aka shiga yi tsakanin Hon Maɗatai da Eng Ali wali dukkan su cikin shiga ta alfarma, ga mutane da take musu baya kowanne da tarin ƴan jagaliya da ƴan daba gudun kota kwana. Hon Maɗatai ya yi murmushi yana miƙawa Ali wali hannu ya ce "Kwana da yawa Ali wali?" Ali wali ya ɗauke hannu sai kuma ya juya ya ce "Ba yanzu ba ka jira na wani lokaci komai zai haska, za a yi tsawa walƙiya ta bayyana munafukan da suke ɓoye cikin duhun ciyayi" murmushi Hon Maɗatai ya yi kawai yana furta "Allah Ya nuna mana" gaisuwa duk sukai sai dai daddy tsakaninsu kawai addu'a ya miƙewa daga wajan. Bayan yin ta'aziyya Hon Maɗatai ya ce "Allah Ya yi wa Ashraf Rahama, ya taƙaita iya kan shi" Sharfaɗi ya juya ya kalli Hon Maɗatai kana ya kalli Eng Ali wali sai kuma ya ce "Amin, yanzu ba gashi ba gwanin sha'awa a dinga siyasa bada gaba ba sai an fi samun nutsuwar zuciya data ƙwaƙwalwa duk wanda zai samu wannan kujerar Ubangiji ya gama rubutawa kawai dai lalube ake yi cikin duhu ku haɗa kai da hannu kowa ya yi kamfel nasa babban jin daɗin ba jam'iyyarku ɗaya ba" Cikin jinjina kai Hon Maɗatai ya yi murmushi daman shi bashi da wata matsala da Eng Ali wali shi yake haukan shi hankalinsa na kan wanda ya yi shiru, shirun nasa kuma yana nufin babbar barazana a gare shi "Siyasa ai ba zata haɗa musulmi irina faɗa da wani ba, munga jiya mun ga yau muna da tabbacin za muga gobe mai kyau, ni fatana na samu gurbin saka hannun jari a kamfaninka idan aka bani dama an yi mini komai Sharfaɗi" daddy na jin su can aka kira shi waya da sauri ya miƙe tsaye yana neman uzurin tafiya Eng Ali wali ya bisa da idanu. Cikin dare Fiyya ta farka da wani irin ciwon kai na ɓari guda, ta kasa buɗe idanunta a hankali ta saka hannu ta dafe kan ta duk da halin cewa bai hanata yin addu'a ya yi tashi a baccin ba domin tabbatarwa da kanta ba a cikin kabari ta farka ba. "Sannu Maama" shine abin da Ummi ta iya cewa tana hamdala a ranta domin shirun ya yi yawa ta damƙe hannunta sosai "Ummi kai na ciwo, ciwo nake ji a gefen kaina" jikinta har rawa yake na tsananin ciwo Ummi ta ce "Maama zai daina in sha Allah, bari a kira likita" "Ummi daddy fa?" "Yanzu ya fita, ki yi ta addu'a komai ya yi farko yana da ƙarshe, wannan ciwon kan zai daina miki watarana buɗe idon ki kalle ni" a hankali ta buɗe idanun ganin yadda idanun ya yi jajir ya saka Ummi cewa "Subuhanallahi wannan jan kuma na magani da mene?" "Ummi jimawar da ta yi a kwance da ciwon kan shine ya saka idanun ja yanzu daddy zai shigo Fiyya zata ji sauƙi ki kwantar da hankali" daidai nan daddy ya buɗe ƙofa ya shigo J na bin shi a baya da Dr Hash, ganinsu kuma ya saka komai ya dawo tunanin Fiyya ta runtse idanunta tana jin fargaba na saukar mata. "Da gaske Ashraf ya mutu daddy? Da gaske an binne Ashraf babu Ashraf ya mutu yanzu haka yana kwance cikin kabari mijin da zan aura ranar ɗaurin aurena ya mutu daddy na shiga uku" daddy ya kama hannun Fiyya cikin nutsuwa ya ce "Laa, sam ba ki shiga uku ba tana iya yiyuwa ya shige iyakar shi ne, kuma mutuwa a hannun Ubangiji take idan lokacin ya yi kota wacce siga ce dole wannan rai ya koma wajan wanda ya samar dashi, Maama da gaske mijin da za ki aura mutu ki sawa ranki haƙuri ki yi masa addu'a ki saka salama ki ɗauka bashi ne zaɓinki ko alheri gare ki ba, Ubangiji na yin komai a lokacin ya yi niyya babu mai tuhumarsa hujjar hakan domin shi ishasshe ne ki yi addu'a Safiyyerh Ashraf is no longer alive pray for him" juyawa Fiyya ta yi ta zubawa daddy manyan idanunta wanda yake cike da hawaye da ƙyar ta ce "Ashraf ya mutu ya bar ni cikin zullumi daddy, inama tuntuni aka ɗaura mini aure da shi, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un wayyo ni Safiyyerh" "Zullumi na me kuma Safiyyerh kin ga abubuwa da yawa a rayuwa sai mutuwar Ashraf zai tsaya miki? Ba za ki yi addu'a ki sawa zuciyarki sallama, kuma wani hanin ga Allah baiwa ne kamar yadda aka sanar yau ɗaurin auren ki da Ashraf Allah bai yi ba, haka kuma alƙawarin Allah gaskiya ne igiyar auren wani ta hau kan ki Maama" ta yi shiru don ta tabbatar daddy ba zai fahimce ta ba, ba zai gane me take nufi ba, ta yi missed Ashraf tun ba'a je ko'ina ba ta ji inama ita Ubangiji ya ɗauki rayuwarta ya bar Ashraf ko da bai aure ta ba, babu mamaki ta dalilinsa wani ya san abin da yake ɓoye gashi ta mutu ya barta da wani irin damuwa ba tare daya bar mata ƙofa ko ɗaya da zata gane ba komai ba. "Daddy me ya sa ka haɗa aure na da Ashraf tun fari?" Daddy ya kalli Fiyya cikin kwantar da hankali "Saboda ya cancanta kuma ya dace Maama

Chapter 8 of 17