Share this page
matarka mu kuma ladidi kukasan ka aura yace eh sanda na auri lubabatu kamin na auri ladidi. Hindatu tace amma toh me yasa ka fara zama da ladidi kamin lubabatu? Yace saboda tana karama lokacin da na AURETA. Hindatu tace ko shin kanada sheda? Shiru yayi tace babu kenan ? Yace akwai ya dago yana kallon idon luba kamin ya dauke Wanda hada idon da sukayi sako ya isar mata. Lauya tace zan iya ganin su yace na farko Allah ne na biyu kuwa ita matar tawa na uku kuma aminina. A ransa ko fadi yake Allah ka gani matata ce amma shedun duk sun manta Dan haka babu wani Abu dazanyi saide na bada shedun karya. Tace ya mai Shari'a zanso ganin shedun daya ambata in an bani dama. Judge yace an baki dama. Kiran luba aka fara tazo ta tsaya. Hindatu tace baiwar Allah ko zamu iya saninki? Goge hawayenta tayi tace nice lubabatu Adam uwar gidan aliyu. Hindatu tace wato kin yarda ke matarsa ce ? Tace kwarai kuwa ya.... ya sanar dani a boye tun bankai haka ba amma yace kar na fada ma kowa. Hindatu tace idan karya ce fa yayi miki Dan yaga ke yarinya ce bakida wayo saboda yayi yadda yakeso dake? Luba tace bazai taba yi min karya ba kuma ba jikina yakeso ba domin da jikina yakeso da sanda nakai masa kaina ina karama bazai kyaleni ba. Hindatu tace wato kin taba kai masa kanki tun a karama bazanyi mamaki ba idan yanzun ma kaikanki kikayi. Samir ne yace objection my lord lauya hindatu tana kokarin tura magana tare da yin kazafi ma matar Wanda nake kara judge yace korafi ya karbu.... lauya hindatu a kiyaye. Hindatu tace zanso naga aminin nasa my lord... yace kotu ta baki dama. Samir ne ya Mike ya zare hulansa na lauyoyi yaje ya tsaya tace wow I see no kake kare abokinka Akan tabar Gazans da yake aikatawa hularsa ya mayar yace objection my lord lauya hindatu tana kokarin tayi cuwa cuwa ta daure magana ne duk sanda na cire kulata ni ba lauyan sa bane ni aminin sa ne kuma duk sanda na mayar da hulata babu alaka tsakanin dashi illa ta lauya da Wanda yake karewa. Alkali yace korafi ta karbu lauya hindatu a kiyaye. Tace mr Samir shin Kaine aminin Wanda ake kara yace eh nine tace ko zaka iya fadamin tun yaushe ka sanshi? Yace tun muna yara muka San juna kuma har yau muna tare. Tace masha Allah abota me kyau! shin da gaske ne abokinka sanda ya fara auran lubabatu kamin ya auri ladidi? tace tabbas wannan babu shakka. Tace toh ko kana wajen sanda aka daura ? Tsarewa yayi kunsan lauya da iya kwantara karya yace tabbas nine ma na karba masa auren a wajen mahaifinta. Daddy ne ya Mike yace karya kakeyi munafiki samiru ashe kaima ka lalace? Alkali yace order order a saura a saura nan ba kasuwa bace ko dandalin yan siyasa. Zama daddy yayi, hindatu tace toh malam Samir mahaifin yarinya yace karya kake ko kanada abin cewa ? Yace ya cadets ne a mazauninsa dan haka wannan bata cikin abinda za'ayi considering. Sannan kuma inada sheda dazai tabbatar da an daura auren ranar haihuwar ta ne. Hindatu tace oh really toh bismillah yace bazan iya aikata hakan ba har sai kin sallame ni na mayar da hulata lokacin na zama lauya kuma zan kare client Dina. Tace ya mai girma mai Shari'a da wannan tambayoyi da nayi da kuma yadda mahaifin yarinyar ba ya karyata su domin babu mahaifin da zaiso kashe auren yarda nake cewa kotu tayi gaggawa daure aliyu na laifin zina da yayi sannan kuma a dauresa na FYADE da yayi sanadiyyar ya kasa gabatar da wasu hujja kwarara kuma aci sa tara mai yawa na canja Ma client Dina ladidi halitta da yayi ta hanyar cire Mata hakora. Zama tayi bayan an sallami luba itama ta zauna Samir ya mayar da hularsa alkali yace lauyan Wanda ake kara ko kana da wata sheda da zai tabbatar mana da lubabatu matar aliyu ne ba zina yake ba kuma shin ko akwai wata sheda ta kariya da zaku bayar na aika aikar da yayiwa matar sa? Projector Samir ya kunna yace ya mai girma mai Shari'a zan haske muku hotunan da suka dauka ne a ranan da ta cika shekara 10 kuma aka daura auren. Haskowa ya fara yace ya mai girma mai Shari'a wannan hotan shi da ita minti biyar kamin a daura auren tana kwalliyar birthday dinta duk ta jagwalgwala fuska tayi musu selfie. Hindatu tace ya mai girma mai Shari'a wannan hotan zai iya zama an dauka ne kawai na birthday baiyi proving komai ba. Alkali yace ra'ayinki bai karbu ba tunda lauyan bai gama nuna hotunan ba. Samir ya tafi hoto na gaba ina suna zaune ga damin goro da kudi damin naira dari dari. Yace wannan hotan mahaifiyar yarinyar ce ta dauka ga can maryam yayar mahaifiyar a gefe su kuma maza lokacin ana shirin karbar auren kenan. Wani hoto na uku ya sake nuna wa yace ga kuma hotansu su dukansu harda cousins dinta nana da mama bayan an daura auren. Hindatu tace karfa ku manta ance ranan haihuwar ta ne Dan haka akwai yuwuwar ayi family picture Samir yace menene hadin ranan haihuwa da goro da kalin cingam tare da sisin gwal? Shiru tayi Samir yace ya mai girma mai Shari'a batun FYADE kuma bai aikata FYADE ba domin kuwa shi kansa ba a haiyacin sa yake ba ansa masa kwaya a bin sha Wanda bamusan waye yayi masa hakan ba Ga result nan na jininsa a ranan da abin ya faru ta nuna tabbas akwai kwaya a jininsa kuma a iya sanin duniya,police station har ma da asubiti ba'a taba kamashi da shaye shaye ba. Da wannan nake rokan kotun nan mai albarka da ta wanke mr aliyu daga zargin da ake masa ta kuma sa bangaren da suka bata masa suna su biyashi tara sannan abar masa matar sa. Alkali ne yace lauyan me kara ko kinada abin cewa ? Tace zanso gabatar da shaida na mai gadin gidan tare da mai chemist da kuma mahaifin yarinyar. Alkali yace kotu ta baki dama fitowa sukayi tace bawan Allah zanso sanin ko kai waye yace nine mai gadin gidan malam Ali tace ko zaka iya fada mana abinda ka sani game da shi da kuma matana dake zaune tare da shi? Abinda ya fada ma yan sanda haka ya maimata musu babu ragi babu Kari domin shine iya gaskiyar abinda ya sani kuma ya fahimta. Tace mun gode sannan ta kalli mai chemist tace ko zamu iya sanin ko kai waye? Yace nine malam ubaliyo mai chemist. Tace shin zaka iya fada mana abinda malam Ali yazo siya a yammacin 3 ga wadannan ? Kallon aliyu tayi ya tuna da labarin da yake ji a unguwar cewa matar aliyu ta biyu tana da cikin yan uku dukda baisan sanda aliyu yayi wani aure ba. Aliyu ko yanajin news dadi yasa yi dinga kiran makotansu yana fada musu anata sanya alkairi. A ransa yace yanzu idan ba karesa ba haka yaransa zasu tashi a wahale kuma malam Ali mutumin kirki ne yamin halacci ya bani shago kyauta tare da bani jari sannan baya siyan magani wajen kowa saini Dan ya taimaka min. Nide akwai kamshin gaskiya a maganarta bazan juya masa baya ba. Yace tabbas yazo wajena ya siya magani kuma maganin da ya siya kamar wacce ta Saba siya ce ta rage masa sha'awa ga receipt nan na ko wani wata kamar bill haka yake biya. Saide ranan yace na basa mai karfi domin ji yake sha'awarsa ya tsananta a ranan Wanda baisan dalilin hakan ba. Hindatu a ranta tace amma anyi Dan iskan mutumi duk wahalar da nasha lokacin da na ga result din cewa akwai kwaya a jininsa ne na Nemo shagon da yake siyan magani. Kuma ya tabbatar min ya siyenta shine yanzu zai canja zance? Tace malam ubaliyo kwantar da hankalinka ka fadi gaskiya babu abinda za'ayi maka yace gaskiya ta kenan. Cewa tayi mun gode a kufule ta wuce kan daddy tace shin da gaske ne ka aurar da harka ma malam Ali? Yace Sam bansan da wannan zancen ba. Haka daddy ya zauna ya karyata Samir ya rushe musu komai hindatu ko murmushi take tace toh hotunan da ya nuna fa? Yace wannan hotuna munyi amma Gordon da nake gani bansan inda ya samesu ba Dan haka technology yayi aiki dashi ya hada hotan. Tace mun gode malam adamu da wannan nake rokan kotu mai albarka ta gaggauta hukunta malam Ali aka zina da cin amanar matar sa da yayi. Alkali yace lauyan wadda ake kara kanada abin cewa? Tace no my lord babu. Alkali yace bayan sauraran hujjoji da shaida daga bangare guda biyu kotu ta yanke hukunci ko da Aires ko ba aure tsakanin aliyu da lubabatu toh dole su rabu duba da jawabin mahaifinta wannan case mun rufeshi amma kotu har zuwa yanzu bazata daure malam Ali da laifin FYADE ba domin har yanzu ba wata hujja da aka bayar cewa da gangan yayi Dan haka malam Ali na Rabaka da lubabatu saide idan iyayenta ne suka baka aurenta a baiyane, sannan zaka bada taran 250k ma ladidi na hakwara 5 da ka zubar Mata. Na daga case na biyu zuwa 15 ga wata na gaba kamin ya buga guduma luba ta Mike ta ruga da gudu ta rike guduman yan sanda ne sukayi caraf zasu rikota ta zille ta sauko kasa nace kaji taron sakarkaru. Cilli tayi da gudumar ta tsuguna Alan guiwowinta tace mai Shari'a karka rabamu Dan Allah wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba ya kakeso nayi da jarirai alokacin har ana shirin zuba Mata ankwa saboda tayi disrespecting din doka... alkali yace ku dakata me kike fada? Tace ciki ne dani alkali wallahi har cikin yan uku ma kaga hotan yanzu tun kamin a haifesa nakeson ka raba iyayensu. Ban aikata abinda na aikata Dan na Rena doka ba na aikata ne saboda yarana kuma na tabbata kana da yara kuma zaka iya yin komai akansu. Ka duba mana ya mai Shari'a. Yace babu abinda zan iya yi domin kun kasa bada sheda kwakkwara saide ki roki iyayenki da su bashi auren ki abinda kika aikata a yanzu kuma an yafe miki amma ki kiyaye na gaba. Zai buga gudumarsa a karo na ba ladidi tace KU DAKATA MAI SHARI'A INADA MAGANA. GENG! GENG!! GENG !!! ANZO WAJEN GA LADIDI NAN DAI KO ME ZATA CE OHO? SHIN KUNGA LAIFIN LUBA AKAN ABINDA TAYI? ANYA ALIYU ZAI TSIRA KUWA? TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO Miss untichlobanty πŸ’• 13th July,2020. [7/14, 10:31 PM] My Samsung: πŸ†πŸ†πŸ† *YARINYAR CE TAMUN FYADE* πŸ†πŸ†πŸ† πŸ₯‡ *20% TRE LIFE,80% FICTIONAL STORY*πŸ₯‡ 🌹by miss untichlobanty🌹 Fell free to contact me on: WATTPAD miss_untichobanty INSTAGRAM miss_untichobanty TWITTER, miss_untichobanty TELEGRAM miss_untichlobanty WHATSAPP:08146448881 Your little sis loves you and don't forget to follow me! *sister miemie wannan page din naki ne Allah yabar kana!πŸ’šπŸ’š* πŸ€ *CHAPTER 36* πŸ€ *AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....* *Not edited* Alkali yace ke kuma wacece kuma me hadinki da wannan Shari'an? Shigowa kotun tayi tace nice ladidi matar aliyu wadda ake ikirarin mijina yayi min fyade. Toh wannan maganar ba haka take ba mijina yayi min abinda yafi FYADE abinda ya ninnika FYADE abinda ba ko wace mace akewa ba. Miji na bai taba kyautata min ba kyautatawa ba halin mijina bane baya kyautata ma matansa. In akace shi mutumin kirki ne an cuceshi. Alkali yace ke mu ba gasar iya magana mukeyi anan ba in kinada abin fada toh in babu kuma kada ki batawa shari'a lokacinta. Ajiyar zuciya tayi tace kamar yadda na fada baiyi min FYADE ba laifi na ne nice na hada tsimi na ajiye a fridge shi kuma yasha lokacin da ya dawo gida ďan ya dauka juice ne kuma batason ya tasheni a bacci. Kallonta aliyu yayi ya saki baki jin yadda ta feso karya amma de yayi tsit baice kala ba. Tace kuma kamar yadda nace ba mutumin kirki kadai bane mijina mutumin arziki ne ga dattako da iya nuna so da kauna Dan albarka abin alfahari na... kamar yadda nace bai taba kyautata mana ba bauta mana yakeyi ni da aunty lubabatu. Aunty maryam haba kawai ta rike luba dake zaune a kasa tana kuka ma kamewa tayi. Toh kode asibitin da taje ya taba Mata kwakwalwa ne. Lauya hindatu tace look mrs ladidi idan har akwai Wanda yake tursasa ki ki fadi wannan magana ne toh ki fada ma kotu kada kiji tsoro. Ladidi tace babu me tursasa ni babu abinda mijina yamin rashin fahimta ce kawai ya faru da mahaifiya ta kuma de shekaru bai wani ja ba bare nace tsufa ce. Alkali yace toh ya batun lubabatu da akace zina suke? Tace haba mai Shari'a? Wace Mata ce zata bari ana zina a gidan ta tayi shiru? Billahil azim ba zina suke ba matarsa ce. Lauya hindatu tace amma ko kina da bayanin abinda ya samu hakorin ki? Tace AI wai hakwara na ? Ranan da suka kawo mana kyakkyawan news ne tsabar jin dadi aljanu na suka tashi to a garin su rike nine ma na yaushe mana jaririn mu kuma anan ne na dinga gwara baki na. Tsumu tsumu lauya tayi wato de ta fadi or what? Alkali ne yace ikon Allah... duba da jawabin da muka saurara daga bakin ladidi kotu tayi wulli da wannan case sannan duk wani laifi da ake tuhumar aliyu da aikatawa ta wanke shi. Malam aliyu Allah ya bada zaman lafiya ya kuma raya yan uku yana kaiwa nan ya buga gudumarsa yace court! A bakin kotu kowa jiki a sanyaye yayinda aliyu ke nazarin wani munafurci ladidi ta tsiro dashi luba ko ganin zuciya take Mata ladidi ta riko hannun luba tace sister wai da gaske yaran mu basu zube ba? Wani tsalle luba ta daka a tsorace Dan ita ba haushi ladidi ke bata ba ganin ta banziya take Mata. Makalewa tayi ajikin aliyu ladidi tazo da yar sandan ta tace yaya aliyu ina wuni murya a sanyaye yace lafiya ladidi daga nan baice kala ba ta riko hannunsa suka fara tafiya a hankali su uku kowa da tunaninsa ladidi ba abinda ke Mata yawo a zuciya sai nadamar abinda tayi. Aliyu ko tausayi ta bashi da tana so da matasa an dauresa a zuwarnan nata amma ta tattare duka laifi ta bashi. Yan jarida da gulma nan sukayi musu ca da tambaya babu Wanda ya kulasu luba ya cicciba yasa a mota ya karbi sandan ladidi ya jingina a gefe itama ya dauketa ya sata a gefen luba kawai sai suka ga ya fara kuka. Kewayo wa yayi ta bangaren luba yace fito baby a hankali ta fito ya shiga tsakiya ya miko Mata hannu alamun tazo. Shigowa tayi ya kwantar da ita a jikinshi ya kwantar da ladidi ma dukda cewa yana jin haushinta amma yana sonta. Driver yace ina zamuje Alhaji karami? Yace gidana... suna isa suka shiga parlour sake zama yayi a doguwar kujera suka zauna a gefensa kawai sukaga ya dafe goshi ya fara musu kuka kamar yaro. Babu abinda yake tunawa sai yadda ya dinga dukan ladidi kamr bashida imani da yadda suka sha wahala. Rungume shi sukayi dukansu biyu suna tayashi kukan.😭😭😭 Sallama su aunty maryam baisa sun daina ba aunty maryam ke fadin jama'ar Allah ya haka ya zaku mayar damu wasu sususu? Um? Haba aliyu kai haka ake ya zaka dasu a gaba kun wani makale juna kuna kuka? Ummi tace toh lubabatu hamshakiya AI sai ki matsa a jikin Mata da miji ko ? Kara fashewa da kuka tayi. Wai ni me kikemin haka ne bazaku barni na huta rayuwa ba? Toh wallahi ko zaman zina muke saide muci gaba in na haihu a daura sabon aure Dan idan tafiya dani kukazo yi bazan biku ba. Daddy ne zai dauketa da Mari ladidi ta shiga. A take ciwonta ya fame suka fara sallallami itakam murmushi tayi tace karku damu hukunci na nake karba. Zama aunty maryam tayi tare da ajiyan zuciya tayi musu abin tausayi tace don Allah ko zamu samu bayanin abinda ke faruwa? Hawaye ladidi ta goge tace tabbas na kasance me kaunar mijina saide ya kasance me bukata amma dukda haka bai dameni ba. Innayo yar uwata itace ta fara nuna min dole na tashi na tsaya idan ba haka toh tabbas luba zata kwace min shi kishi ya rufe min ido na biye Mata toh sai ta bani sharadi. Idan dai inaso ta hadani da wani boka mai aiki da iyawa sai na soma zina. Salati su aunty maryam suka rafka... sukace ladidi ga shirka ga zina ? Tace na nuna Mata kamar na soma zinan amma babu wani zina Dana soma yi domin inason mijina kuma jarumi na shi daya ma ya isheni. Koda ta kaini akayi mana aikin akace za'a saka luba ta tsaneshi bazata soshi ba ko kadan. Inata jin dadi har akyi min rasuwar nan kace min tafiya zakayi idan baka je zaka samu karayar arziki toh sai naje ayi mana aiki kar mu rasa dukiya 'ya'yan my me zasu ci? Anan boka ke sanar min babu wata tafiya kawai kana tare da luba ne abin ya kona min rai sosai. Anan innayo ta bada shawarar a mantar daku komai naji tsoron hakan domin nasan girman aure amma sai naji na kasa bijire ma abinda tace. Toh tun daga lokacin muka mance komai harda ni kuwa sai dazu ina bandaki boka ya baco min. Ina ganinsa naji tabbas na sandan kuma a take na tuna komai. Boka yace ladidi nasan kina mamakin mai ya kawoni kuma nasan kin tuna komai ban taba yin aiki da nake ta nadama da Dana sani irin naku ba saboda aure na lalata nasa ake yi musu ganin mazinata. Ladidi ki sani ke kanki duk abinda kike yi cousin dinki ladiyo ce tasa na tsafe ki saboda tana son mijinki. Shi yasa ko me ta fada baki yin musu. Ki sani bakida laifi ko kadan a abinda ya faru domin kema ba a haiyacin ki kike ba. Ladidi ni kaina wannan aiki da nake dole ce ta sani domin tunda mahaifi na ya rasu kawu na ya kaini wajen wani malami wai makarantar allo karyace babu wani malami matsafi ne haka na koyi tsafi sai wata 10 da suka wuce na fahimci tsafin da nake ma shirka ce Dan yana kota mana addinine tare da murde wash abubuwan ya koya mana tsafi mu Wanda muka iya yace mu waliyai ne kuma baya bari mu nemi fatawa wajen kowa. Cire gashin dake kansa yayi ya wanke fuskarsa wallahi da na lallashi ashe ma matashi ko yaya aliyu bai kai ba. Anan ya dukusa ya bani hakuri yace ya cire jarabar da yasa ma aliyu domin dama innayo ce tace yace bazai iya ba Dan sanda taje wajena da fari kamin ta kaini. Yace min amma bazai iya tunatar daku ba sai akan sharadi daya sine zaku tuna. Idan har na tona asiri da baki na kowa zai tuna amma dole rayuka guda biyu zasu salwanta idan ko ban fada ba bazaku taba tunawa ba kuma bazaku yarda ba. Aunty maryam tace gara fa da kika gane bamu yarda da taysuniyar nan ba. Ladidi tace zaku tuna karku damu yanzu mu jira zuwansa Dan yace idan na fada jikinsa zai yi masa Saba toh zaizo ya warware sai ya tuba ya kuma nemi Ilimi sadidan me kyau ba wadda akayi Mata mix me cuwa cuwa ba. Kamin ta rufe baki ya baco kamar ba boka ba so handsome dashi ya durkusa ya gaishe su. Aliyu ya kada cewa komai luba kuwa gyangyadi ma take Dan she can't come and kill herself. Yace zan tuna muku kuma ladidi ta bada rayuwa daya wato na innayo yanzu na biyu ne bamu samu ba. Ladidi tace a dauki tawa a na biyun mana a zabure bokan yace Sam bazan iya ba ladidi kinsan irin s..... take yayi shiru kamin yace adai nemi wani. Luba tace indai za'a dena mana ganin mun tana yin zina toh why not a dauki baby daya a ciki na? Aliyu ya bige Mata baki yace ke shashasha rufe mana baki. Shiru tayi tace toh ni gaskiya kar a sake cewa nayi zina. Yace toh ni bari na dauki duk wadda naga dama yana fadin haka ya rufe ido aiko kowa ya Mike mai kai masa damka nati me girgiza kai nayi ladidi tasa hannu zata bude idon nasa kawai sai ga gawa....... 😳😳 KAWAI ME NA SHIGA UKU! ALIYU YA DAUKA KO LUBA? LADIDI? AUNTY MARYAM? UMMI KO DADDY? KODE UNCLE ABBA NE? KO WATA FAN DINA YA DAUKA NE MA? WAIYO ALLAH πŸ₯ΊπŸ˜­ TOH KARDE KU MANTA KUYI VOTING TARE DA COMMENTING SANNAN KU TAYANI SHARING. NAGODE DA KAUNA TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO.... Miss untichlobanty πŸ’• 14th July,2020. [7/16, 1:33 AM] My Samsung: *πŸ†πŸ†YARINYAR CE TAYI MIN FYADEπŸ†πŸ†* πŸ₯‡ *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* πŸ₯‡ 🌹by miss untichlobanty 🌹 Feel free to contact me on : WATTPAD miss_untichlobanty INSTAGRAM miss_untichlobanty TWITTER, miss_untichlobanty TELEGRAM miss_untichlobanty WHATSAPP: 08146448881 Your little sis loves you and don't forget to follow me! *MAKIYA DA MAHASSADA DA MASUJIN HAUSHINA BAN MUKU KOMAI BAπŸ€’ WANNAN PAGE DIN NAKU NE. ALLAH YABAR KAUNA!❀ DAN KAUNA KE KAWO KIYAIYA KO?* πŸ€ *CHAPTER 37*πŸ€ *AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....* *Not edited* Yace toh ni bari na dauki duk wadda naga dama yana fadin haka ya rufe ido aiko kowa ya Mike mai kai masa damka nati me girgiza kai nayi ladidi tasa hannu zata bude idon nasa kawai sai ga gawain wata Mata da na innayo sun baiyana. Cikin kaskanci duk diwa da kazanta na fita daga jikinsu. Ya nuna dayar matan yace kunga wannan matar sunanta jummala itace matar kawuna kuma itace ta bada shawarar a koya min tsafi akayi min karya cewa almajiranta za'a kaini. Bata taba kyautata min ba saide ta kuntata min, ba ta da aiki sai hada guri a unguwa yau tana can gobe tana can. Aikin kenan. Wannan kuwa ya fada yana nuna ladidi yace inajin ba sai nayi dogon bayani ba itace innayo cousin din ladidi. Wannan da kuke gani shaidaniya ce tazo wajena tace taga mijin ladidi kuma ya Mata amma bataso ta dameshi cikin sauki Dan za'a gane takunta so take a bata ma ladidi suna sai ta rabasu. Batasan cewa tun lokacin akwai lubabatu ba ni ko na sani amma nayi shiru abina. Anan tace na sa duk abinda ta umarci ladidi tayi kuma hakan akayi ban taba aiki ya subuce ba sai akan ladidi lokacin da tace ta soma zina amma ladidi ta kasa saide bazata ketare maganarta ba Dan haka tayi pretending haka innayo ta kawota wajena da duk wani kullu da ladidi tayi bata cikin haiyacinta. Malam aliyu saide kayi hakuri dukda nasan maganar da zan fada bata da wani muhimmanci saide hada guri toh amma yadda ladidi ta kasa cin amanar ka yasa...... sai kuma tayi shiru bakin aliyu na rawa ga hawayen nadamar abinda tayi wa ladidi na zuba mai yace in...ina..ji..jinka. Ajiyar zuciya ya sauke yace wannan dalilin yasa na fara son matarka amma kuma tana da aure ni kuma babu abinda nake darajawa irin aure. Da naso tsafi daya zanyi ladidi ta zama tawa amma bazan iya cin amanar aure ba. Faduwa aliyu yayi gaban ladidi ya kwanta a cinyarta kamar yaro yana gunjin kuka yana fadin ladidi na ki yafe min kinji.😭😭 Babu Wanda bai share kwalla a wajen ba yace tabbas ke din nagar tacciyar Mata ce Wanda samun irinki sai an tona. Bayan wani lokaci boka har yayi tsafi ya watsar da gawan a jeji bayan aljanu sun zukesu sun busar dasu. Tashi yayi jiki a sanyaye yace yan uwana ni zan tafi zanje na kwana ido biyu na warware duk wani aiki da nayi cikin jahilci sannan kuma na nemi tuba kuma na roki Allah ya yaye min son ladidi kar na cutar daku a kanta. Ya bude kofa kenan aliyu yace malam boka... kowa sanda ya murmusa saboda sunan bai zauna ba da gyara murmushi bokan yayi yace musa ne sunan aliyu yace Ayya mallam musa ka bani minti kadan mana muna zuwa aunty maryam son Allah a bashi abinci. Kamo hannun ladidi yayi suka haura sama suna shiga daki ya rungume ta yace ladidi na ... nasan ban kyauta miki ba hakan yasa naji ban canceki ba. Shin ko zaki iya duba girman Allah ki yafe min? Makalewa tayi a jikinsa tace dama can ni ban rike ka ba na yafe ma duniya da lahira. Yace ladidi kinga a sanadin mu da kuma son da bokan nan yake miki yasa ya gano gaskiya sai nake ganin bamu kyauta masa ba idan har muka barshi ya tafi bai sameki ba. Ladidi tace me kake nufi? Yace idan har bazai sameki ba me zai hana na sakeki ki auresa ? Kinga muma sai muyi irinta ansar yadda suka dinga bawa muhajirun matansu kuma sai na bashi aiki a a karkashina karki damu baza ku bar gidannan ba muna tare kinga dama na siya gidan makotan nan namu sai ku zauna a ciki ko ya kika ce? Tace yanzu kenan zan zama ba matar ka ba? Yace ba dole ladidi ni zan zauna dake in baki yarda ba amma bakaga yardar ki shi zaisa mu zaunar da musa tare da mu kinga bazai koma ruwa ba kuma Allah zai bamu lada. Ki duba zuciyar ki akwai ko da dogon sonsa ne idan ma babu kina tunanin zaki soshi? Murmushi tayi yayi dariya yace aiho wato dama kina crushing aure nane ya rike ki ko? A hankali ta daga kai yaja Mata hanci yace haba mu didi ba ko kunya? Kuma

Chapter 14 of 15