Share this page
dan ya gane meke faruwa cikin suna fadin ina kwarton? Aciroshi muci ...... Me gadi ne yace laha'ila ha illallahu Alhaji karami meke faruwa? ban gane ba. Aunty maryam fashewa tayi da kuka tana nuna ni da luba dake kuka a lungu dan bata taba ganin ran aunty maryam ya baci ba. Ita abinda yafi bata tsoro kar a wauwaska Mata Mari irin na aliyu saboda ta balla famfo. Nace Allah bansan meke faruwa ba kawai gani nayi tana kuka ni bacci ma nake zazzabi gareni taba....! jifana aunty maryam tayi da wani kwalba hakan ya datse min magana ta yayinda take fadin ba dole kayi zazzabi ba? Aliyu na daukeka Lamar kani ashe kai kura ne cikin farar ajiya? shege tsinnenne saina fadawa baban nana. Waya tahau dannawa yayinda na fara salati ina fadin wai karde har yanzu mafarkin nake kode mafarki nane ya zama gaskiya na shiga uku ni aliyu. Sassabata akayi sama dani wani yana fadin baka shiga uku ba sai an gicce maka....... dan kaza Kazan ka yar kanwar matan wanka zaka lalata?fyade aliyu? Jibgata aka farayi yayinda mafarki na ke zuwa mini tar kamar a gaske domin ko gani nake ilhama akamin. Fadi nake wallahi ni ban Mata FYADE ba suna karya kake. Ga dai abinda na gani a mafarki *Innalillah wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku Aliyu FYADE kake Mata? Abban nana kawo agaji. Ihu akayi masa makwabta suka shigo nan aka rufesa da duka kamin aka sassabesa akayi waje dashi domin a gicce masa girman sa yayinda yake salati yana fadin wallahi ba laifi na bane yarinyar ce tayi min FYADE bani na Mata ba.* *Wani ne yace zama ka tsara ne idan kaka babu gaban ka.... (CHAPTER 1)* Salati kawai nake Dan babu sarki sai Allah kuma shi zai iya mini. Waje baki daya suka fitar dani anata duka na gabaki daya jini yamin kaca kaca tun ina ihu da salati har na koma fadin WALLAHI YARINYAR CE TAMIN FYADE bani na Mata ba! Danko zuwa yanzu naga mutuwa kawai neman tsira nake. Fadi suke yi mana shiru Dan munafuka. Tsabar na daku kasa magana nayi dagabaya. Tayar mota aka dauko ana kokarin a konani yayinda nake fadin kar kuyi gaggawan hukunci ku tambayi luba kamin a kashe ni daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba. LUBA'S POV Ni duk gaba daya tsoran kar a daukeni nake Dan tunda uncle aliyu ya karba toh nima bazan tsira ba abinda wani mutumi ya fada ne yasa naso na gane meke faruwa dukda ban tabbatar ba saboda wasu kalmomin ban taba jinsu ba. Kodai wani ya fadi abinda nayi ma ya aliyu ne ? Dama yace idan aunty maryam zata mishi duka idan taji toh amma menene abinda za'a yanke. Tunowa nayi da wani film da aka yanke kan wani da sauri na Mike ina fadin ku barshi karku yanke shi zanbi bayansu da gudu Dan sun Riga sun fice nikam banason na rasa abokina. Ihu nakeyi wasu Mata na rikeni ko yaushe sukazo oho. Nide fadi nake kar a yanke shi har na suma. AUNTY MARYAM'S POV Lullubi na nema Mata domin jikinta ya soma nuna alamun girma dukda ko YARINYACE. Hankali ne ta shigo min ganin yadda bataso aji masa ciwo na fara nazari. Amma AI irin wannan lamari yaran tsoron mutumin dake musu sukeji amma ita hana dukanta take. Wannan lamarin harda kisa fa, balle ansan halin aliyu na kirki karfa muje kuskure ne! Toh amma ai na KAMASU babu suturar arziki. Amma kuma AI bawai na KAMASU suna tsaka sa aikatawa bane. Ko zina dole a kamaka dumu dumu sheda hudu kowa ya gani. Anya banyi kuskure ba? Da sauri na fice........ πŸ₯ΊπŸ₯ΊπŸ˜’😭 YAU ALIYU NA YAGA TA KANSHI ALLAH SARKI BSBU ABINDA YAKAI KAZAFI CIWO😭😭 KU BIYONI DAN JIN YA ZATA KAYA, WAI SHIN AUNTY MARYAM ZATA ISA KAMIN A KONASHI KO KUWA LOKACI ZAI KURE MATA? TAKUCE KARAMARSU BABBARSU DAN ALLAH ACIGABA DA COMMENTS HAR SAI KUN KARAR MIN DA DATA πŸ˜‰ INA JIRAN COMMENTS FA! miss untichlobanty πŸ’• 15th June,2020. [6/16, 2:42 PM] My Samsung: *πŸ†πŸ†YARINYAR CE TAYI MIN FYADEπŸ†πŸ†* πŸ₯‡ *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* πŸ₯‡ 🌹by miss untichlobanty 🌹 Feel free to contact me on : WATTPAD miss_untichlobanty INSTAGRAM miss_untichlobanty TWITTER, miss_untichlobanty TELEGRAM miss_untichlobanty Your little sis loves you and don't forget to follow me! *Hajiya surayyah wannan shafin naki ne* πŸ€ *CHAPTER 15*πŸ€ AFWAN FOR THE TYPING ERRORS.... Not edited AUNTY MARYAM'S POV Gudu nake kamar kafata zai fita abban su nana da ya shigo yana fadin wai dagaske abinda shegen yaronnan yayi kenan? Mangajeshi nace bantabbatar ba garin waige nayi Tuntube na gurje guiwan hannu da kafa amma a haka na Mike Dan ciwona ba komai bane akan rayuwar aliyu. Saida hankali ya dawo min ma na fahimci kashesa zasuyi ni duk na dauka dukarsa za'ayi. Tabbas dukda bani na Kira mutanen nan ba na rafka babban kuskure Dana daga murya har aka jiyoni. Toh amma kusa kanku a kafata, idan kuna zargin kanin mijinkida lalata yar kanwar ku wadda kuke sonta kamar yarki, amma bakiyi komai ba saboda kina ganin zargi ce kawai kuma yaron nada hali mai kyau kwatsam kukayi arkabo da abinda na gani zaki iya natsuwa? Kema kinsan bazaki iya ba. Yanzu ko zargin wata ake da yin sata sai akaje gidan biki itama taje akayi sata kowa ita zai soma zarga. Wasu ma gar da gar zasuce ta fito musu da abinsu...... Dai dai ana shirin kesta masa ashana na cafe ashanar tare da cewa ku barsa kuskure ne bashi ya aikata ba wanine sannan ya daura masa amma itama yarinyar babu abinda aka Mata kawai tsorata tayi. Ba fadi haka ne Dan na wanke musu suna dukda ko nasan zai iya zama gaskiya ko karya. Salati suka rafka suna fadin da munyi kuskure, kuma duk rashin bincike yaja mana domin ko da mun tsaya munyi bincike kamin mukayi masa wannan duka. Wani mutumi yace tabbas munyi mamakin cewa malam Ali zai iya aikata irin wannan Abu amma toh ganin daga gidansu aka fadi yasa bamu musa ba. Ciccibarsa sukayi suka hada ruwan dumu sukayi masa wanka akan zasu dawo dashi a Kira masa likita yayinda na koma gida ina yiwa kaina Allah ya isa dukda ko nasan abinda nayi daidai ne amma dukda haka nayi kuskure ciwon dake kafata ne suka soma ciwo ina shigowa gida na duba naga ashe dayan kafar kwalba ce ta yanke ni. Sanda likita yazo duba lubabatu da nurse ya taho nan ta dinke mini kafar tawa. Yana cikin yi mana bayani akan cewa tsoro da firgita yasa luba sumewa saboda yarinya ce kwakwalwarta bai shirya da daukan kayan firgici irin haka ba aka shigo da Aliyu take suka shiga dubashi nikam nama rasa abin yi bansan sanda ummi kanwata suka iso ba sai ji nayi tana kuka tana bani hakuri. Yinin ranan kowa jugum muka wuni su nana ko gidan kakanninsu na wajen uba aka kaisu. Dakin aliyu akaje aka taru lokacin daya farka dan bazai iya tafiya zuwa parlour ba yayinda na dauki luba. Mijina ne ya bude mana taron da addu'a sannan ya kalli aliyu yace ya fadi komai daya sani luba kuma ta saurara dakyau idan yayi karya ko guda daya ne ta fada kar taji tsoro za'a siya Mata kwalin biscuit Kato. UNTICHLOBANTY'S POV A hankali aliyu ya tsara musu komai daya faru saboda ciwon dake gefen bakinsa, tun daga haduwarsu had zuwa yau iya abinda ya sani be boye komai ba dukda ko yaji kunyar wasu abun. Kallon luba kowa yayi da ido yayi da ummi ta Mike zata falla Mata Mari da sauri daddy ya rikota zaunarta yayi tana zabura hakan yasa luba ta sake fara kuka. Aunty maryam ce ta falla Mata Mari tukunna ta nutsu aka cewa luba tayi shiru ta fadi ko gaskiya aliyu ke fadi ta daga kai. Shiru akayi kamin aunty maryam tace toh ya akayi tasan duka wadannan abubuwa a shekarunta. A Dan tsorace take tana kallon idon uncle Ali Dan neman amincewa ta fada koko murmushi ya Mata ya gyada kai domin shima yana son yasan ta yaya ta San wadannan abubuwa. Itako muryanta har rawa yake Dan uncle aliyu ya fada Mata laifi ne amma tunda yace ta fada kila zai kareta. Komai ta fada musu har zuwa yadda sukazo dakinsa aiko ummi ta kwalla mata mari tana ashar. Shegiyar yarinya wato duk sa min kunne da kike ashe gane me ake cewa kike ? Dama ni nasan baki dena shafa man nan ba wato har tsimi na kika sha ko ? Toh yau sai naci....... yar kaza kaza. Daddyn luba ne ya kwalla ma ummi Mari sannan aunty maryam ma ta kara Mata daya. Aunty maryam tace kaji shashashar Mata duk wannan laifinki ne luba batada laifi ko kadan. Banda karamin kwakwalwa ce dake ya za'ayi kina komai a gaban yarinya kuma har ki kwana daki daya da ita? Bakida hankali ko? Kallon daddyn tayi tace haba abban luba kaima kasan bai dace kuna kwana daki daya da yara ba ya akayi kayi sakaci? Cikin kuka yace wallahi maman nana nayi Mata maganar haka yafi a kirga akan mu gyara dayan dakin da muka mayar store room sai su koma can amma sai tace ai ba hankali ne da ita ba da taga na takura shine tace idan ta yaye kanin ta sai su koma tare Dan kar luban taji tsoro. Kuka ummi ta fara tana fadin sai yanzu na gane kuskure na , na cuci yata ni da kaina sakaci na ya jawo mini matsala. Wallahi ban taba yi da wata niya ba sam ni ban ma dauka laifi ne hakan ba. Dan Allah luba ki yafemin. Luba de kuka take Dan ta maru me kyau. Aunty maryam ne ta kwantar da luba a gadon aliyun kamin ta kewayo bangaren da yake ta tsuguna tace aliyu ka yafe min abinda nayi maka amma ya kamata nina ka fahimce ni! πŸ₯Ί yace aunty ki tashi don Allah ni bakiyi min komai ba haka uwa ta gari ya dace ta zama kawai nan gaba kiyi bincike akan Abu kamin zarar da hukunci kuma nima AI da laifi na da ace nayi aure da wuri da haka duk bata faru ba da na dauko masifa ta na juye kan Mata ta. Dan murmushin jin kunya kowa yayi luba kam tama fara bacci sai hajiyar zuciya take Dan yau taga masifa. Ana cikin yiwa ummi nasiha luba ta firgita ta tashi da sauri ummi tazo gefenta tana lafiya yata? Luba ko fadi take kar ku yanke shi! Karku yanke shi! Ruwa aka yaiyafa Mata a fuska akace babu Wanda za'a yanke yi shiru kinji? Toh tace tayi luf ta kwanta ta rufe ido amma bacci ya kasa daukanta. Bayan an gama da ummi aka jiyo aka jiyo toh saura kai aliyu maza ka fito da Mata kayi aure nan da wata 3. Da sauri luba ta tashi tace nifa ? Bazai aureni ba? Uncle ABBA yace ba kyau shiga maganar manya kinji luba tashi ki fita kuma ke yarinya ce bazakiyi aure ba. Bori ta fara musu itama Allah sai aliyu ya aure ta da suka lallaba sukaga taki saduda sai aka Nemo bulala. Ana dukan ta tana ihu amma fadi take itama sai uncle aliyu ya aureta. Aunty maryam ne ta ceto ta a hannun abbanta tayi Mata magana ta fahimta amma tace Sam fa sai de kawai an yarda zata auri aliyu. Aliyu yace kin Mata me na fada miki ne tace babu ruwanta. Dan itafa gani take auren irin wasa da yara keyi na aure ne kuma kunsan yara da naci. Dena kulata sukayi tahau musu kuka, taki cin abinci har abin na damunsu basusan tana kewaya wa ta bayan katanga tasha madara ko yogurt ba. Haka tayi sati sai tasha kamshi tukunna take shan shayi ko abinci. Su suna damuwa ita kuma ta dauki abin a wasa tanaso tayi winning su yarda su kuma sunaso ta ta hakura. Ganin idan ba yarda sukayi ba zata kassara kanta yasa suka kirata parlour lokacin satin gidan su aunty maryam ne Dan ankai wata ana daru da ita. Zama tayi a kujera aka Kira aliyu Wanda already ya samu Mata nafeesa shekarar ta 24 har ansa rana. A kasa ya zauna sukace toh aliyu kaga dai abinda kanwar ka ko harka ne zamuce ta dage akai me kake gani? Yace au ita dama bata bar zance ba? AI ni na dauka wasa take. Kunsan shiriritar ta ku barta kawai. Bata rai tayi tana hura hanci Dan ta kara girma sosai in ka ganta zakace takai shekara 8 race Allah uncle ni ban yarda ba. Aunty maryam ce tace ka dalla yi mana shiru, ya ABBA yace aliyu idan yarinyar nan tayi shekara 10 bata hakura ba toh da ta gama secondary zaka AURETA kaga shikenan ma asiri mu a rufe Dan idan ba haka ba wannan Terere da ya faru in anzo aurensa sai ya taso kasan jama'a da kara gishiri wa zance Dan tayi manda. Dafe kirji aliyu yayi yace ya ABBA aure fa kace? Ya ABBA yace kwarai kuwa zaka AURETA! πŸ™†πŸ»β€β™€οΈπŸ™†πŸ»β€β™€οΈπŸ™†πŸ»β€β™€οΈOH NI UNTO NA BANU YANZU KUMA WANNAN JAGWAL DIN DAGA INA TA BALLO? KAI JAMA'A SHIN KUNA GANIN YA DACE DA SUKA YARDA DA SHIRIRITAR LUBA? KUNSAN FA BA HANKALI GARETA BA ITA A GAME MA TA DAUKI ABUN AMMA KARKU MANTA TAKI KARATU YASA SUKA YARDA. KUNA HANGO JAGWAL A GABA KO BAKU HANGOWA. SHIN ZATA YARDA KO KUWA ZATA FASA IN TAKAI SHEKARA 10 ? KU BIYONI DAN JIN YADDA ZA'A WARWARE WANNAN CAKWAKIYAR. AMMA DAI LUBA TANA RUWA. TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO Miss untichlobanty πŸ’• 16th June,2020. 4 - [6/18, 7:30 PM] My Samsung: *πŸ†πŸ†YARINYAR CE TAYI MIN FYADEπŸ†πŸ†* πŸ₯‡ *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* πŸ₯‡ 🌹by miss untichlobanty 🌹 Feel free to contact me on : WATTPAD miss_untichlobanty INSTAGRAM miss_untichlobanty TWITTER, miss_untichlobanty TELEGRAM miss_untichlobanty Your little sis loves you and don't forget to follow me! *JANNAT,SUMAYYA YARIMA, SA'ADATU TIJJANI, ZAKIYYA and MATAR MANYA wannan shafin naku ne* Allah yabar kauna πŸ€ *CHAPTER 16*πŸ€ AFWAN FOR THE TYPING ERRORS.... Not edited ALIYU'S POV Wannan wace irin magana ce ake min ace in aureta? Taya ma zasu biye shiriritar yarinya ? Ajiyar zuciya na sauke. Dadin abin ma ance in takai shekara 10 za'a sake tambayar ta. Toh ni ince wa nafeesa me? Dukda Cewa tana da hakuri amma ace tun kamin ayi aure a fada ma kishiyar ka? Lamarin nan da sake. Kallon ya Abba Nayi nace Toh Allah ya kaimu nan da shekara 4 Daga nan aka Shiga sabgar biki na. Akwana a tashi har Anyi aure na nida nafeesa Muna zaman lafiya mata me hankali da biyaiya samun irinta Nada mugun wahala. Tasha wahala sosai saboda 'bari da tayi yafi sai 4 Daga nan tahau jinya har Allah ya amshi ranta. Daga nan na auri salma itama a hatsarin mota ta rasu. Kamin kace me na auri mata 6 amma duk babu mai tsawan rai kuma duk na kwarai ne saide abinda baza'a rasa ba. Lokacin da luba tayi shekara Goma muna zaune mu mun mance da zancen ma Dan gani ake shirman ta ne ta manta kawai muka jiyota tana fadin indai zaman nan na batun aurena da uncle Ali ne toh ban fasa ba. Kallonta muka tsaya yi iko sai Allah yarinyar nada abin mamaki. Yaune aka daura aurena na 7 da ladidi a yanzu shekarun luba 12 itane kirjin biki anata rawar kai. Inda Allah ya taimaka bata iya rawa ba Dan haka da akace za'a yi party tace baza ayi ba dama nima banaso ladidi ce ta dage. Luba ko tace indai akayi dinner sai ta bata sauran ba'ayi ba wannan ms baza ayi ba. Dan haka aka fasa akayi Karin ango kawai aka kawo min amarya ta. LUBA'S POV Uncle aliyu kamar me aljanu da yayi aure se matar ta mutu ni da fari na dauka wasar buya suke mana ashe tafiya yama sunan wajen ? Yauwa ashe tafiya barzahu sukeyi duk sanda yayi aure toh gidansa nake weekend an hanani an hanani amma naki ji har an gaji. Aunty maryam tace AI idan ina zuwa ko wani lokaci bazaiyi dauki na ba amma nayi biris. Ba lura so suke na manta da zancen Niko kullum da na tashi daga bacci abinda nake tunawa kenan Dan bazan taba yarda suyi winning ba. Kenan fa na zama loser. Matan sa nada kirki duk sanda naje suyita bani labari muna hira tun ina kankanuwa ta. Har goyona suke aunty nafeesa kam har cemin take idan na auri uncle aliyu ni zan dinga tayata wanke wanke. Niko sai na kyalkyale da dariya Dan abin birgeni take ashe de baza tayi Nisan kwana baπŸ₯Ί nati kewarta. Wasu idan aka fada musu cewa zai aureni da fari basa yarda amma idan suka ga banida matsala shikenan sai mu dinke Dan ni inason aiki sosai komai na gani sai na taba ko anyi shara sai nayi nima. Gani da surutu ba comma bare full stop. Satin bikin uncle aliyu da aunty ladidi na shigowa na soma dauki, nayi can nayi can dukda yanzu shekarata 12 na soma game kishi amma ban damu saboda na Saba ganinshi da Mata. Bari na Baku labari in kuka ganni zakuce nakai shekaru 15 Dan mugun girma nayi. Dinki naje karbowa dukda anyi anyi na bari a karbo naki Dan nasan telan Dan jagwal ne. Aiko koda naje ya yanka be dinka ba. Tada ma yan shagon hankali nayi sanda akayi a take aka bani ba zuburo Bali da yasha Jan baki sosai na dau ledar kayana na bashi 1500 nace yasin Rabin kudin zan biya saboda an bata min rai. Kamar uwarsa jiki na ruwa yace jeki ba matsala kai ilu tara Mata me adaidaita sahu. Jiki na rawa kuwa ya tara mini ina tafiya suka Nemo ruwa da sobo suka kora Dan na caja musu kai ba kadan ba. Ina dawowa naji ana wani batu wai za'a yi party nace in anyi shegiya nake. AI da gangan ake cewa za'ayi bayan ansan cewa ban iya rawa ba. Amma usilin zance babu rawar da ban iya ba tunba na bazo bazo ba. Kawai banish ayi party ne Dan a islamiya ance mana babu kyau amma nasan da na fadi wannan za'a kafa mini hujja da abinda nayi ina yarinya Wanda nasan abin ya faru amma na mance da abubuwa sosai bazan iya hada labarin ba saide a takaice. Aiko da alamu uncle aliyun ma bayaso Dan babu wasting time yace angama uwani AI abinda kike so shi za'ayi. Nasan gatse yayi min a wasa mikewa nayi ina tsalle zan fice nace haka nakeson ji ubale na. BIYONI yayi da gudu na arce ina dariya. Karin ango Akazo yi da shike maman su uncle ABBA ne shuwa shiyasa uncle Ali ya Dan dauki haskenta yayinda uncle abban yadau duhun mahaifinsu Wanda yake kanuri gaba da baya hakan yasa ba Karin angon da hausawa keyi akayi ba. Kaulu akayi wato original din na kanurai. Karkashi ne za'a Dama ka lakata ka taba ma ango a hannu kayi masa addu'a sai ka lika kudi. Niko abin yanamin dadi lokacin muna shiri Dan ango ya kusa zama. Su nana sonata hura hanci wai na janyo baza'ayi party ba nace nifa rawa ce banyi gaban maza amma ina zuwa aunty maryam na samu tana cikin mutane sunanta korafin yadda ka biye min aka ki yin Partyn tana bada hakuri. Koda na shigo akan hanci suke kallo na suna bata rai shan kanshi na fara tare da dage kai ina hura hanci na jujjuya musu mazaunai na da basu zauna ba Dan ni albarka kirji gareni amma mazaunai na basuda girma na bazo a gani daidai kamar na kowa ne. Gefe naja aunty maryam nace so Nike a Kira mini ma kadan fada ayi mana ganga kura (ganga kura shine kidan da kanurai keyi wadda yawanci suke hawa kan layi ko sahu a taka rawa iri daya bawai a girgije Dan mu a tsarin kanuri babu rawar girgiza. Ada kakannin my kanurai suna ganin kowa Arne Dan lokacin a borno empire kadai akeda musulunci tun kamin ya shiga su sokoto. Any way ba historynazo Baku ba wannan ma wani fanni ne na dabanπŸ˜‰) Tace toh babu matsala komawa mukayi na daura liffaya ta blue wato shudi (ba lafaya ba and also kurkum not kurkur, Dilke not dilka fatan mun gane?πŸ’ƒπŸ») muka fito anata shan kamshi kamar iyayen Mata. Fili aka buda mini dan dama nasa an sanar da abokan ango cewa da na fito susa a bude min fili. Dangwala nayi amma memakon na shafa masa a hannu sai na muka masa a gemu sannan na ciro bandir din 50 wato dubu 5 na cire hularsa nasa aciki harara ta yayi nayi masa gwalo yayinda abokansa suka saki baki suna kallon mu uku Niko kara dage gira nake Dan karma suyi shawagin cewa suna sona kuma abinda zai baka haushi ko kwalliya bamuyi ba Dan ni ka'idata ban kwalliya bawai Dan inada kyau yasa nake haka ba sai Dan ba kowa ya dace yaga kwalliyata ba! Nafi karfin wannan. Bayan mun dawo cikin gida ne na kyalkyale da dariya Dan nasan yadda uncle aliyu keson gemunsa Kamar me. Masu ganga ne suka iso aka sanar wa maza suka shigo sannan akyi rawa ta al'ada karfe biyar ummi tayi mana surprise da masu kidan kwarya Dan haka maza suka fice waje inda ake Kari tare da me ganga yayinda Mata suka rufe kofa bayan an tabbatar babu namiji muka girgije nan na naje na karkade jiki su nana sai makemin mazaunai suke wai haka ne rashin iya rawa. Nide nace kanku. Da daddare ne akace ankai amarya aiko ni da nana da mama mukace toh muma can zamu kwana aka hanamu. Mama ce ta samu uncle Samir ta roka mana shi Dan taga alamun sa Santa yake amma bai fadi ba saboda karantarta shekarunta Goma ne. Aiko babu wata wata ya yarda ya daukemu mu uku a Motansa ya kaimu muku muka saka wayar mu a plane mode toh amma ba zuwan ba abinda muka tarar ne yasa zan iya ce muku ana gwarama ko kuma akwai kura hajiya! UHM IKO SAI ALLAH KO MECECE KURAR NAN? NIDE BARI NA SAMU BAKIN GADO NAYI SHIRU SANNAN NAJI DAGA GAREKU! AFWAN KUN JINI SHIRU WAYATA TA DAN SAMI MATSALA NE AMMA ALHMDLLH KOMAI YA DAWO NORMAL DAN HAKA ACI GABA DA GASHI KAWAI. TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO Miss untichlobanty πŸ’• 18th June,2020. [6/20, 9:16 PM] My Samsung: *πŸ†πŸ†YARINYAR CE TAYI MIN FYADEπŸ†πŸ†* πŸ₯‡ *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* πŸ₯‡ 🌹by miss untichlobanty 🌹 Feel free to contact me on : WATTPAD miss_untichlobanty INSTAGRAM miss_untichlobanty TWITTER, miss_untichlobanty TELEGRAM miss_untichlobanty Your little sis loves you and don't forget to follow me! *Indai sunanki maman wani ko ummu wata toh wannan page din naki ne, da Wanda sunasu ya fara daga A-Z wannan shafin naku ne kuma* Allah yabar kauna πŸ€ *CHAPTER 17*πŸ€ AFWAN FOR THE TYPING ERRORS.... Not edited LUBA'S POV Muna isa muka fara kalle kalle , shikam uncle aliyu baya gajiya duk sanda zai sake aure sai ya canja pant na gidansa. Kuma cikin matan daya aura wannan yama sunanta? Ladidi tafi sauran kudi Dan kayanta masu kyau. Nide had yau bani taba magana ba banda gaisuwa Dan bama haduwa ma bansan ko gudu na take ba. Shiga dakin amarya mukayi kamar yadda muka saba direct gado muka nufa matan dake dakin suna binmu da kallo. Wata me kananun ido tace ku kuma fa? Zaku wani shigo ku ajiye mutane kazamin ...... a gado? Nana ce tace sai akace naki yafi namu? Nikam gyara zama nayi na ware su liffaya ta Dan zafi nakeji ashar ta dirma Zara yo kaina ladidi ta fito a nayi ta hura hanci meke faruwa ake min hargagi a gidan miji nifa kar ku sake kimin fada Dan zanci....... mutum ne. Wannan me kananun idon ne tace AI da fada muke da sauki.... dubi fa kallona tayi ta danyi murmushi tace to AI su luba ne yayan shi ne fa.....suma sakin fuska sukayi sukace au AI mun dauka gaiyar sodi ne. Mama ce tace ni da nana ne yayan sa amma sis luba matar da zai aura ne.... da sauri ladidi ta juyo tace ban gane ba. Nace zama ki gane da alamu kece wacce be fadawa ba toh aunty ladidi tun ina yar karama akayi alkawarin sure tsakanin mu..... wani ashar ta lailayo tace Sam bazai sabu ba. Wato abinda yake ta cewa zai fadamin kenan? AI yasin bazan zauna da me kama da ifiritai ba. Jimin yarinya daga kirji sai hanci kamar tsinke saura jiki kuwa kamar an fere tsabar siriranta ace inyi kishi da ita? Kallonmu tayi tace ku Dan ...... ku fita min a daki. Sauka su nana sukayi Niko na koma bangaren dama na gadon na kwanta.. kallona suka tsaya yi nace gurin mijina na kwanta ba naki ba danko nasan barni dama yakeson kwanciya. Tace toh sannu shegiya karuwa zanko ci..... Wata ce ta shigo tana fadin angwaye sun iso Dan haka muka fice muka buya kar uncle aliyu yasa a mayar damu gida hakan yasa ladidi tasha ban mayar Mata da magana ba. Ni yasin gashinta nikeji kuma saina fadawa uncle aliyu abinda tayi min. Munajin shewarsu da alamu kudi aka basu can muka jiyo hayaniya kamin ta lafa da alamu sun tafi ne mukam muna dayan dakin Dan dakuna 3 ne a gidan sai parlour biyu madaidaita. Neman liffayata na soma yi lokacin da zamu kwanta akan sai in rufu dashi amma ban Ganshi ba sai lokacin na tuna da cewa yana dakin ladidi tsaki naja na kwanta abina. ALIYU'S POV Kaina a kasa bance komai ba aka gama duk hirar abokan ango da kawaye danni kunya nakeji kuma idan Baku sani ba ladidi shekarunta 19 ne dukda bannwani girmeta and azo a gani ba amma ni AI nayi aure dayawa ba wannan ne na fari ba. Sanda suka tashi tafiya

Chapter 6 of 15