tukunna na
rakasu
Koda na dawo liffayar ladidi na gani akan gado yana reto Dan murmushi nayi a raina nace ita
kuma har an shiga kintsawa ba kunya ne? Dagawa nayi Dan na gyara naji kamshi ya daki hanci
na rikewa nayi ina shinshina ina jiran ra fito nima na shiga alwala amma me ? Tana fitowa na
ganta da gyalen ta kanta kuma babu alamun alwala a fuskarta.
Nace a ah hajiyata ashe ba gyalenki bane wannan? To ko wata kawar ki ce tayi mantuwa?
Nadau gyalenki ne ma ashe ga naki... wani harara ta balla min tace dalla malam kamin shiru
idan ba renin hankali ba sarai kana ganin gyalen yar iskar yarinyar nan ce zaka wani ce kawata
tayi mantuwa? Kuma sarai AI kaga gyalen dake kaina sanda akayi sayan baki...
Da yake inada Ilimi nasan yan Mata basu iya magana ba kawai nayi murmushi nace Allah sarki
aiko bakin nan ansiyo mini shi ina Dan dariya... toh ke banda abinki ai kaina na kasa ban lura
da gyalen ba kuma wace yar iska kike nufi?
Tace duba ka gani dakyau... kallon liffayar nayi dakyau sai yanzu na tuna inda na Ganshi nace
au ashe ma na luba AI sai yanzu na tuna dazu na ganta dashi a wajen Kari na.
Tace zama ka karashe sauran zance wato ma matar da zaka aura ce baka sanar dani ba?
Ajiyar zuciya na sauke nace yanzu dai muje muyi alwala muyi sallah zan fada miki komai. Turo
baki tayi kamin de ta juya....
Haka mukayi sallah muna cin abinci ina fada Mata yadda akayi zan auri luba tunda matarka
abokiyarka ai babu aibu idan na fada Mata kuma babu wacce ta taba tambaya ta a mata na
shiyasa ma ban fada musu ba aiko ta nuna fahimta sosai naji dadin haka muka kwanta ban
Mata komai ba banda rungumarta da nayi ina shinshinan kamshinta na tuno na luba murmushi
kawai nayi har bacci ya dauke mu...
LADIDI'S POV
Koda mukayi sallah muna cin abinci ya labarta min yadda yar iskan yarinyar nan ta bi min miji...
aiko nace in tasan wata batasan wata ba a gabansa in nuna komai kalau da ya juya ko inci
ubanta taci sa'a ma bazamu dinga haduwa ba da na gasa yar banza.
Duk rashin mutunci Dana buga masa baya nuna damuwa nasan sarai bai kulani bane Dan
yanason ya shiga kasan Dan kamfai na Niko nace nasan maganinsa ga mamaki na babu
abinda yayi min. Inaji shi daya yana murmushi har ya fara sauke numfashi, nina da tunane
tunane na nayi bacci.
LUBA'S POV
Cikin dare na tashi yunwa na kwakulata na nufi kitchen anan na Sami kirjin kaza da guntun
madara dasu dabino harda fruit na dauko nazo na naje ciki na hanka abina yo zan cucina kaina
ne ince wani wai ni yar Gaye? Ko wanke hannu banyi ba na koma bacci.
Da safe wajen karfe 8 na tashi Dan wata yunwar nakeji wanka nayi banida wani kaya kwai sai
nasa half vest Dina da da leggings Wanda nasa kasan lace Dina na fice Dan ban tsammaci su
fito yanzu ba kitchen na shiga babu abinci na leka store aiko ga su bakilawa,su doughnuts da
cake na dibo Abu na tun a kitchen na fara hankama... da uncle Aliyu nayi karo yana dawowa
daga waje har kunya nadan ji na Dan haka nayi sauri na buya bayan labule.....
Bude labulen yayi ya yaba minnwani Abu a gashi na yana min dariyar mugunta... lakatowa nayi
naga kakashi yamutse fuska nayi nace uncle aliyu ka bata min gashina. Dauke doughnut daya
yayi daga kwano na yana fadin bashi na biya daga yanzu na daina kyaleki kiyimin tsiya son
ranki tunda kin fara girma.
Biyoshi nayi kamar zaki ina kukan ya bani abinci na kawai ladidi ta fito tana hamma tace nawan
wai wake sallama ne. Wasu flask ya nuna Mata yana fadin baki fada min anan su luba suka
kwana kallona tayi da sauri kamin tayi murmushi tace au mancewa nati kwi yadau zafi bari
nakai abincin kitchen ko? Shiga daki yayi yayinda ta kalleni kamar zata gutsireni tace Dan
ubanki wa yace ku kwana mun a gida kuma fa nan ba gidan karuwai bane da zaki samin
tsinannun kayan nan. Kodan banyi mamaki ba abinda mutum yasha a nono.
Iya haushi naji haushi amma sai na godewa Allah da ya bani wayo sai nace Allah sarki yayata
kinsan fa anko mukayi dake. Tace kan bala'I bala'I wato yayarki ok? irin nono daya muka sha
ko? Wato a wajen uwata kika gado? Toh zan ci......... kuma ni banason sata!
Gwaliyo nayi Mata ta nufi kitchen tana fadin zan hadu dake bayan ta dawo ta ganni bakin fridge
ina kora lemo zatayi magana uncle aliyu ya fito ya dauketa yana fadin in kika biye wannan
acikin hira baya kare Mata zo ni in baki wani labari sannan sukayi ciki. Nikam wani juice din na
dauka nasa a hanata bayan Wanda ke hannuna sannan na wuce daki don bawa su nana labari
bayan na karo doughnut daya Wanda uncle aliyu ya dauke min.
TOH FA GASKIYA A GIDAN UNCLE ALIYU ZA'AYI SHAGALI BA KADAN BA! NIDE KU BIYONI
KUJI YADDA ZASU KASANCE.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
miss untichlobanty ๐
20th June,2020.
[6/21, 3:48 PM] My Samsung: *๐๐YARINYAR CE TAYI MIN FYADE๐๐*
๐ฅ *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* ๐ฅ
๐นby miss untichlobanty ๐น
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
๐ *CHAPTER 18*๐
AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....
*Not edited*
AHALI NA DA MASOYA LUBA NA WATTPAD WANNAN PAGE DIN NAKUNE DUK WANDA
YAYI KOKARIN YI MUKU KEACE KU HADASHI DA YAN SANDA๐
ALIYU'S POV.
Ko da nayi sallar asuba dawowa nayi na samu ladidi na sallah Dan haka na koma na kwanta
abina. Inaji ta kwanta a baya na tana me sakale hannunta ta ciki na kamawa nayi na rike a haka
mukayi bacci... wayata da aka Kira ya tashe ni wai aunty maryam ce ta aiko mana abinci....
Lokaci na duba naga 8 da rabi ma ta wuce Dan haka na fito naje na karbo ina shigowa naji kara
a kitchen Wanda nasan tabbas ba ladidi bace danko ladidi tana bacci lekawa nayi naga fara ce
tafi ladidi haske da siririntaka nasan ba ko wa bace sai luba amma abinda yadan mota ni shine
kayan dake jikinta.
Tanaso ta ballowa ladidi jagwal danni ka ida ta idan na auri mace ranan farko bazan miki komai
ba saboda kidan Saba kar a hada miki zafi bibbiyu sannan kar ma ki dauka na aureni ne Dan
wannan Dan haka inde bawai naga alamun kema kinaso ba toh ranan farko kinyi escape
saboda nasan yadda ake tsinka musu gaba.
Gashinta dake tsefe bata daure bane idona ya fada akai rabon da na ganta babu lillibi tun ranar
da aka kamamu na ganta da Dan kamfai daga ranan da kaya me mutunci nake ganinta harda
hula.... sanda ta soma girma kuwa harda hijab.
Gashinta ya kara cika da tsayi Dan yanzu yakai tsayin wajen bra strap. Amma fa ghar tanzi
baiyi baki ba kuma ni nafison shi a haka... dungure kaina nayi ina cewa kaji shirme yarinya ma
ke damunta da tayi wayo zata ce bataso dama nima ba sonta nake ba Dan ci ne da ita kamar
gara amma bata kiba. Cikinnan kamar faranti... tunowa nayi da iskancin sa tayi min jiya aiko
dama na daure guntun karkashin hiya na ajiye Dan na Rama... daukowa nayi naje na dauko
flask din Dana ajiye bakin kofa na ajiye kan centre table na parlour fitowa tayi bakinta a cike
amma a haka tana kokarin tura wani cake.
Tana ganina ta shige bayan labule da alamu taji kunyar yadda na ganta ne bude bayan labulen
nayi tana shirin kutsiran doughnut haka kawai naji nima inason ci Dan haka ina Mata wani
murmushin mugunta Dan nasan me zanyi na dauki daya.... kanta yana kasa tayi tsimu tsimu
kamar kulya da ruwa yayi wa duka amma da shike akan abinci ne da sauri ta dago tana turo
baki matsa Mata karkashin nayi kuma da alamu ta wanke gashin lakatowa tayi ta gani kuma
gashi na dauka Mata doughnut biyoni tayi zata kwace bayan tayi min raki cewa na bata Mata
gashi.
Ladidi ce ta fito ni daga nan na nuna Mata abincin na shige ciki danko luba ta tsokalo min
haja.... jin shiri ladidi bata dawo ba gashi a matse nake yasa na fito da alamu surutun nan na
tsiya luba ke Mata. Dauketa nayi ina fadin in ta biye wa luba hira bazai kare ba tazo na bata
wani labari aiko muna shiga daki na canja salon labarin.....
AUNTY MARYAM'S POV
Tun jiya da daddare aka nemi su luba aka rasa an Kira wayar su duka uku amma a kashe sarai
nasan bazai wuce gidan aliyu suka tafi ba dukda na hanasu Dan haka na jira su dawo bayan
siyan bakin amma shiru har 12 wayar aliyu zan Kira na tuna yayi aure yanzu bai dace na kirasa
ba.
Samir na kira nan yake tabbatar min AI shi ya kaisu ma amma a dawowa bai gansu ba ya
dauka sun dawo da wuri ne. Nace masa babu matsala toh sannan na kashe wayar bazan
nemosu ba su da kansu zasu dawo su sameni.
Washe gari ma aika akai abincin su Aliyu ina tsammanin ko zasu biyo shi amma shiru... nidai na
baza ido naga sanda zasu dawo in basu dawo Dan Allah ba AI sa dawo Dan Kayan su.
LUBA'S POV
bayan na shiga daki na samu mama ta shi nana muka make Dan itace sarki bacci kuma
munada style din tashin ta tare zamu daga hannu muka balance sannan mu lafta Mata duka.
Wanka sukayi mukaje kitchen abincin da ladidi ta ajiye muka dibo mukayi shagali abin mu.
Shiru basu fito ba har azhar ta kusa kuma inason daukar liffaya ta... knocking nayi naji shiru
Dana gaji kawai na shigewata. Cikin bargo na gansu suna murkususu take suka dago suna
harbo min wata kallo nikam tabe baki nayi na bude drower aiko naga liffaya ta. Juyawa nayi zan
fice uncle aliyu yace ke luba kanki daya kuwa? Ya zaki tsirmo dakin mutane babu sallama?
Tabe baki nayi nace da farko de nayi knocking har na gaji na biyu kuma wata tsiyar kuke da
kake haki kamar kayi dambe da zaki?
Ranshi ne ya baci sosai amma dinshi kawai ke fadin haka yace abinda kikeso na miki sanda
kike karama muke ko zaki jona mu ne? AI da gudu na fita danko an Dan bani katin haske akan
abun kuma ba'aso ko maganarta anayi rashin kunya ne inji ummi sannan masu aure keyi. AI ko
kirjina kamar zai fado sanda na isa wajen su nana dan aunty maryam tace in mutum yaje yayi
ko maganar abin ne mutuwa zaiyi cab bab shirya mutuwa ba da din ma yarinta ke damuna.
Hanya muka kama har gida su nana na fadin madam kode uncle aliyu ya biyoki da wuka ne. Irin
wannan gumi da kike haka? Kasa cewa komai ma nayi.... me napep ne ya nemi ya kawo mana
shirme wai kudin da muka bashi yayi kadan Dan rainin hankali dari dari ake kaiwa mu uku mun
bashi dari biyar zai mana hauka aiko mu uku muka dunkule hannu yadda super heroes na
cartoon keyi mukace ko yabar kofar gidan mu ko mu canja masa halitta.
Hmm ashe Dan daba ne ba kawai mutuminka ya sauko ba man kace me ya zaro wuka... take
cikin su nana ya duri ruwa da gudu suka shige gida nima na tsure amma Nasan idan ban saita
shi ba zai iya dawowa Dan nasan halin yan shaye shaye.
Hade fuska nayi ya kasa gane meke raina Dan baiga alamun tsoro a idona ba sai hargagi yake
yayinda cikina har kugi takeyi Dan tsoro ina nazarin barkonon tsohuwa wato tiya gas da almajiri
ya koya min jiya bayan mun cashe. Toh na hada gwanin farko amma bansan tayi daidai koko da
matsala ba. Kut!! Na hadiya yawu nayi shahada kawai zaro na fasa mai a fuska sannan na
warce woman bayan na rushe hanci na da liffaya ta.
Yankar sa nayi da wukar nace kai Dan mahaukaciya nima nan da kake gani na dabancin nan
Yinsa nake, yasin ko ta anguwar na ka sake bi saina zaro yayan hanjin ka na wulla masa
wukarsa na gudu. Tun daga bakin gate na fara tari Dan duk dabarata na shaki gas din kawai de
banason ya gane ne ya kawomin wargi aiko abinda ban sani ba shine ya mugun tsorata da
yaga tiya gas din bata min komai ba gashi akwai yuwuwar idonsa ta Sami matsala.
Ina shigowa su aunty maryam suna fitowa a haukace Dan yadda su nana suka fada Mata Dan
daba ne har wuka gareshi ta tsorata. Ganin na shigo a jigace yasa akayi ciki dani nasha su
ruwa bayan tari da hawayen da nake ya lafa kawai na fara dariya. Tsayawa kallona sukayi
waiko kan da kwalabe ne?
Nan na basu labarin yadda akayi ina dariya aunty maryam tayi ta fada wai na dena fada da
maza sannan uban wa yace na kiyi hada barkonon tsohuwa kuma me zanyi dashi. Tsilli tsilli
nayi daidai lokacin wayar aunty maryam tayi ruri dagawa tayi tana fadin ango kasha kamshi
take naji wani kullu a cikina jin yadda yake daga murya bai gama ba aunty maryam ta kashe
wayar tare da sambodomin wani kallo.....๐ณ
TOH ANAN ZAN BARKU KUYI MANAGE DA WANNAN. KAR KU MANTA KU SAMBADO MIN
COMMENT DAN NAJI DADIN BAKU UPDATE DA WURWURI. YAN WATTPAD KAR A MANTA
DA VOTE FA! INA YINKU KAMR BA GOBE.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty ๐
21st June,2020.
[6/22, 10:10 PM] My Samsung: *๐๐YARINYAR CE TAYI MIN FYADE๐๐*
๐ฅ *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* ๐ฅ
๐นby miss untichlobanty ๐น
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
๐ *CHAPTER 19*๐
AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....
*Not edited*
LUBA'S POV
Wayar caja ta janyo ta fara tsulani aiko take na soma kuka ina burbuwa itako fadi take da izinin
wa kukaje gidan aliyu harda kwana? Ke Dan iskanci da rashin sanin ya kamata kika fada musu
daki kai tsaye kaman gidan ubanki, su nana ta cafko ta hada dasu tayi mana tas tas sannan
sannan ta kora mu daki..... tana zaune ta ganni da jaka niki niki dama yanzu nafi dadewa a
gidanta amma tunda nasha assauda nace babu dawowa.
Ganin ina saukowa da jaka niki niki yasa tace ina zuwa? Cikin bacin rai na abinda aliyu da
aunty maryam suka min nace gidan ubana inda zan fada ko ina ba tare da anga laifina ba. Baki
ta saka Dan ban taba Mata rashin kunya ba saide taurin kai..... take taji wani iri a zuciyar ta Dan
tunda na fada mata magana kuma na tafi toh naji haushi... kila ina da gaskiya da ta
tambayeni....
Kiran sunana ta soma nikam kara sauri nayi Dan banaso na dawo gidan. Direct gidan mu na
nufa ko napep din banhau ba jakata na daura aka... ummi na gani na da kaya da hawaye ta
taso tana salati... luba yar umminta ya akayi? Rungume ta nayi ina kuka wiwi ta zaunar dani a
kujera dama tasan abinda ke sani farin ciki... ABINCI amm da ta bani ko kalla banyi ba har juice
ta bani na dauke kai toh tasan maganar ta girmama.
Gaba daya ta rikice tace luba hankalina yana tashi me akayi miki ? Fada Mata komai nayi
amma na tsallake fada ta da ladidi tayi ajiyar zuciya tace kema de luba harda laifinki ya zaki
fada musu daki ? Nace toh ummi sanda nayi knocking sosai fa amma ba'ayi magana ba sai na
dauka ko basanan ne.... race toh nikam bance miki akwai abinda Mata da miji keyi Wanda
ba'ason kowa yaji ko ya gani ba? Nace kin fada kince za'a mutu tace yauwa toh nan gaba indai
suna daki a tare karki sake shiga kinji daga kai nayi badan na hakura ba.
Kwakulo tasono nayi zankai baki ta make hannu na tace kede kin shiga uku katuwa dake na
dauka an dena halin ta canja zani ashe da saura ? Kai aliyu yanada aiki... turo baki nayi nace ni
kar ki kara min maganar sa. Tace au yanzu zancen aliyun ma bakya so?
Tashi nayi na tafi dakina tace aiko yarinya kina ruwa tunda shi zaki aura kaji min shirmen banza.
Dauko wayata nayi na fara kiransa har sau uku bai dauka ba aiko na cika na batse Dan dama
so Nike na dan masa rashin kunya na basa haushi.
ALIYU'S POV
Bayan na Kira aunty maryam na sanar da ita abinda luba tayi min... da ina Dan tunanin in yarda
in aureta amma yanzu ta sa na soma sanja tunani. Yarinya ahaka in ka ganta kamar sallah ashe
ko alwala babu? son kowa kin Wanda ya rasa yar budurwa amma da ka kwankwashi hankalinta
sai kaji shiru kamar mushriki yaci shirwa yasha ruwa?
Yar amarya ta ladidi ne ta fito an karya dankwalin nan gwanin ban sha'awa flask din abinci ta
dauko mana ta kawo tana budewa mukaga an sande mu yan iskan yaran nan sun cinye.
Murmushi tayi tace laa kilan su luba najin yunwa yasa suka ci bara na daura mana wani.
Kawai binta nayi da kallo ina fadin Allah na gode ma ka bani Mata kyakkyawa ga hankali kuma
yar karama abinta.
Abincin ta kawo mukaci muka shiga hira anan ne
LADIDI'S POV
Lokacin da ya Kira aunty maryam zai bata rahoto dadi naji a raina Dan dama nice na rigashi da
dabara nace masa ya fada Mata abinda luba tayi kar abar yarinya ta tashi ba gwaba kuma AI in
ta Sami tarbiyya mu keda riba tunda mu zamu zauna da ita aiko ya dauka shine fa ya fada
Mata.
Wanka nayi na sheka ado kamin na dauko mana abinci tun a kitchen din nasan sun taba danko
naji nauyin ya canja hakan yasa na bude na gani murmushi nayi Dan ko gyara kaina zanyi.
Budewa nayi kamr bansan me ya faru ba nace laa kila su luba ne kemin yunwa sukaci bari na
daura mana wani abin. Irin kallon da yake bina dashi nasan na burgeshi ne. Wata kwarkwasa
nasa har kitchen inajin haushi danko abincin ya biya raina guntun na sude dan yunwa nakeji
saboda kwakulata da mai gidana yayi.
Bread da kwai nayi mana sannan nakai masa na basa abaki daga nan muka shiga hira cikin so
da kauna.
LUBA'S POV
Kuka nasha abina na huce haushi sannan na kwanta bacci ya daukeni ina cikin bacci naji waya
na ringing...nana ce dauka nayi tana kuka tana rokon sister Dan Allah kar kice bazaki dawo ba
kar abinda akayi miki yasa kiyi zuciya na rikeni da Allah ki dawo kinji sis Dina? Nace naji zanyi
tunani na kashe wayan batare da na saurare me zata sake cewa ba.
Message na gani daga uncle aliyu wai
"yan Mata me yasa ake rangaba min Kira ko bata show din bai isa bane sai kuma an hada da
kira?๐ " tsaki naja na rafka masa Kira aiko yana dauka na fashe da kuka nace abinda kayi ka
kyauta dukda cewa ina da laifi Wanda ba da gangan nayi ba... bai dace ka fadawa aunty
maryam har kasa tayi min birtsi birtsi da bulala ba, na dauka inada darajar da nafi karfin
wulakanci a Wawrinka ashe abin ba haka bane... ok wani abin nayi ma kamata yayi ka kirani ka
zaunar dani bawai kayi min cin mutunci ba toh bari kaji indan nace kai nakeso yasa kake min
haka toh kaje gaka ga ladidi.... ni dama akwai wani mai gadi kuma yanaso kawai nice naki
yarda amma bari kaji ni luba daya daya ka rubuta ka ajiye NA FASA AURENKA!... in ga uban
da zai tursasa ni.
AFWAN AFWAN NAYI LATTI YAU AYI MANAGE DA WANNAN GOBE DA WURI ZAKU JINI
INSHA ALLAH.
KAI TSAYA ASHE FA AN BALLO WANI JAGWAL KO? TOH LUBA DE TACE TA FASA KO
SHIN ABIN ZAI YIWA ALIYU DADI? KOKO SABANIN HAKA NE?
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty ๐
23rd June,2020.
[6/23, 3:19 PM] Miss Untichlobanty๐: [6/23, 3:10 PM] My Samsung: *๐๐YARINYAR CE TAYI
MIN FYADE๐๐*
๐ฅ *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* ๐ฅ
๐นby miss untichlobanty ๐น
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
๐ *CHAPTER 20*๐
AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....
*Not edited*
AishaIsmail625 , aysherahmaddanlami, wannan shafin naku ne Allah yabar kauna
ALIYU'S POV
Bayan na fito masallati ne nayi ma luba message saboda dazu naga kiranta ina tare da ladidi
kamin na shige masallati ina fitowa kiranta ya shigo ina dagawa cikin murmushi zan tsokaneta
Dan na dauka ma hakuri zata bani na kuskuren sa tayi sannan tamin godiya na gyaran da nasa
akayi Mata banci mutunci ta gaban ladidi ba kawai sai naji sabanin haka.
Ta inda take shiga ba tanan take fita ba Abu kamar wasa sai na bude baki zanyi magana sai
naji ta daura magana. Jikina ne yayi sanyi Dan ban kyauta Mata ba amma ni ba da wata niya
nayi ba banaso naci mutuncinta gaban ladidi yasa na gasata da aunty maryam tayi Mata
magana ta Mata toh menene kuma na duka.
Tunani na ya datse sanda tace ta fasa auren kuma zata bawa me gadi dama a raina nace
masha Allah dama nasan yarinta ke damunta.... amma dakata! Ta fasa aure na saboda me
gadi? Me take nufi wato ya fini ko me ? Toh dukda banason ta saina AURETA ba ita uwar taurin
kai ba? Ko me akayi in bataso ta tada bori? Toh AI in tasan wata batasan wata ba zan AURETA
dan in kure taurin kan muga abinda zatayi.
Kiran wayar nayi taki ta daga daga baya ma naji switched off. Gida na shiga abina ina shirya
bomb din da zan Mata Dan jira zanyi ladidi ta Dan shekara sai nasa luba ma daga ciki.
Ya Allah ka jarabce ni da rasa Mata na nayi kuma karbi kaddarata ya Allah na rokeka saboda
tawakkalin da nayi kar ka kashemin wadannan kar ka rabani dasu. Shafawa nayi kamin nabar
kofan masallatin.
LUBA'S POV
Ummi na samu nace Mata ummi nifa wallahi azo a sake zama na fasa auren uncle aliyu bige
min baki tayi tace sannu shashasha kawai Dan yabaki haushi sai akace ki fasa aure? Haka
zakiyi bayan auren da an bata miki rai kice sake ki? Zama nayi a kasa Wanda ummi tasan
abinda zai biyo shine bori tace toh karma ki fara kinga yanzu SS3 kike ki rufe ido kiyi karatu kina
gamawa lokacin kin kusa shekaru 17 ayi miki aurenki.
Bori na fara nifa Allah in aliyu za a aurenin yasin ko karatun bazaiyi ba. Ummi tace subhanallah
yau ko uncle din babu ? Kuma da kike batun bazakiyi karatu ba wa jahilci zai kashe ? Ki auri
aliyun ki a gidansa sai kiyi university ko ya kikace. Mikewa nayi nace toh ai sai muga yadda zan
aureshi ni dama can nasan ba sona ake a gidannan ba. A fito a fadamin ko tsintata akayi yasa
za'amin auren dole.
Bulala ummi ta dauko ta biyoni zonan yar banza in dauki cikinki wata 9 harda sati 2 awanni 13
nayi ina nakudar ki shine zakice tsintar ki akayi toh sai kin auri aliyun tukunna ma in baki
aureshi ba wa zaki aura? Manna Mata nayi ta bankado labulen dakina ta shigo.... Luna wai
meke damunki ne? meyasa kikeson bamu ciwon kai? Me yasa kikeson maida daddynki karamin
mutum?
Maganarnan an gamata ke da kanki kikace a aura miki aliyu yanzu kice kin fasa? Ki bari idan
kin huce ki sake tunani... turo baki nayi nace nide acewa abba na na fasa. Toh ai shikenan.
Abinda ta fada kenan kamin ta sauke ajiyar zuciya ta fice.
Da daddare ummi ta samu daddy ta fada masa kamin ta karashe ya daga Mata hannu yace
kiramin yarinyar. Kwala min Kira tayi na shigo parlourn ina wani mika da hamma daddy yace in
baki warware ba zan ware ki da Mari tsam na mutsu na zauna yace wani shiririta nakeji wai kin
fasa aure?
Nace nifa daddy ba aure na fasa ba uncle aliyun ne banaso! Ke dalla rufemin baki lokacin da
mukayi justin duniya ki hakura burus kikayi mana kikace sai shi yanzu kuma kina wani magana
da batada kan gado? Toh bari kiji gara ki sani aure ba fashi. Kuma in bakida hankali ki kawomin
kasa da credit shida gidannan saina ballaki.
Mikewa nayi na koma daki ina fadin zakusha mamaki, sannan na fada kan gado na sai bacci.
Washe gari da asuba ummi ta tashi zata tasheni sallar asuba taga empty! Ban daki ko ina ta
duba babu ni babu alamata sai ta dauka ko zuciya nayi na tafi gidan aunty maryam toh amma
da asuba kuma? Daddy na ta fadawa aka Kira su aunty maryam sukace banzo ba.
Uncle Aliyu aka kira shima yace bai ganni ba nan cikinsu ya duri ruwa aka fara cigiya ta a
unguwa amma babu alamata.
Abinda ya faru kuwa shine tun da magrib ina waya da nana nake fada Mata nifa idan aka ki
yarda guduwa zanyi tace yayi mutuniyata toh amma in kin gudu ina zakije? Nace nima ban sani
ba. Maama tace toh me zai hana tazo nan ba tare da sanin kowa ba sai musa ta a BQ ko ya
kukace mu dinga bata su abinci daga nan.
Nace toh amma masu gadi zasu fada ai nana tace karki damu zan rufe musu baki aiko tunda
daddyna bai yadda ba karfe uku nayi sneaking dama already nana ta sanar da masu gadi zuwa
na Dan haka suka budemin kofa.
Inaji da safe
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 15