Share this page
na mai tausayi ce da kuma haƙuri kuma nasan Aunty na bata zartar da hukunci har sai tayi bincike akai, dan haka nake ruƙunki dan Allah ki tsaya ki saurareni plees". Dubanta yayi yaji miza tace amma sai yaji bata ce komai ba, irin yadda yaga tabada natsuwar ta yasan zata saurareshi. "kamar yadda kika sani ina son Hafsat so bana wasa ba dan tun lokacin da na fara haɗuwa da ita makaranta nakamu da sonta, amma itako alokacin ba soyayya ce gabanta ba kartu shine gabanta shiyasa ko saurarena bata tsayayi ba, ban jima da haɗuwa da itaba ne nazo ƙasaranan dan na yi phd, sai dai duk wani mutsi nata idan tayi sai nasani koda kuwa bani tare da ita, kuma dakika ce Hafsat yarinya tace wallahi ko ɗaya, ni banta sanin Hafsat ƴa mace ba, ke ba itaba duk wata mace babu ta inba Maryam matata ba, Aunty, Hafsat daki ka gani wata ƙaddara ce ta afka akanta, wadda duk wani musulmi mai imani ya tausaya mata, data na nigeria Allah ya haɗata da wani sheɗanin saurayi wanda ya illata mata rayuwa kuma duk da haka bai bar ta ta huta ba yaƙi ya rabu da ita, nikuma lokacin dana samu labarin haka shine nayi shige da fice har tasamu scholarship na tafiya waje karatu ko zai rabu da ita, to nayi nasar rabasu amma yanzu haka yananan yana neman ta ruwa ajallo, danshi na hanata fita makaranta kwana biyu wannda ke da ita baku san dalilil haka ba". Dubanta yayi yace, "Aunty labarin Hsfsat nada tsayi amma kiyi haƙuri sabida duk lokacin dana tuna sai nayi ƙwalla, amma wani lokaci zan baki insha Allah". Kallonsa tayi da kyau kana ta buɗa baki tace, "yanzu har kasan yadda take amma kake ƙoƙarin kajefa kanka aciki, to bari kaji koda zan yarda taci gaba da zama gidannan to bazan yarda ka aureta ba, dan da alamu ba ajinka bace, dan haka nake baka shawara tun wuri kaciri wannan so dakake mata dan gaskiya bazamu barka ka aure yarinyar da bata da kamunka ba". Yace, "Aunty kuyi haƙuri dan inaji ajikina rasa Hafsat dai-dai yake da rasa raina, Aunty bansaki da haka ba, kuma ki gayamin gaskiya, zaman da Hafsat tayi agidannan akwai abinda tayi wannda zai nuna rashin kamun kanta?". Kai ta girgiza masa alamar a'a. "Kingani dan haka Aunty kirufamin asiri karki bari kowa yaji wannan maganar kuma kitaya ni da addu'a". Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke kana tace, "na fahince ka, kuma insha Allah ba maijin wannan zance". Yace, "yauwa Aunty na, na gode sose". Murmushi tayi kana tace, "yaushe zaka zo muje muga yadda jikin nata yake?". "Sai gobe, sabida ina tunanin idan muka tafi tare da ita zamu dawo inyaso taciga da shan maganinta". Tace, "to haka yayi". Sallama yayi mata yatafi da sunan gobe zai dawo. ******* Safiyya ce kwanci ɗakinta ita kadai, ba abinda take sai aikin tunanin ƴar uwata Hafsat, tayi kuka har tagaji na rashinta, gashi har yanzu ko waya basu taɓayi ba, kuma ga Babanta har yau fushi yake dasu, duk abu yazo ya haɗe mata waje ɗaya, dan yanzu maganar da ake Baban ta yace wata biyu ya bata ta kawo masa miji dan aure zaiyi mata, kuma ita duk cikin masu sonta bataji wanda ya kwanta mata araiba, tana ciki haka taji Yayan ta Abbas na kiranta, da sauri ta tashi ta fita. Zaune ta samesu shida Mama zaune, ƙarasowa tayi ta zauna kusa da Mama tana faɗin, "gani Yaya". Wata leda dake gabansa yace, "gashi kije ki kawa Umma, kice ina gaisheta anjima zanzo". Karɓa tayi tace tau bari nasa hijab ɗina". Tana sawa ta ɗauka tafice Mama tace tana gaisheta.... *#VOTE COMMENT SHARE* *SHAFI NA 28📑* *__________📖* Koda taje gidan su Hafsat, sose Umma taji daɗin ganin ta tace, "Umma gashi inji Yaya yace na kawo miki yana gasheki kuma anjima zai zo". Sai da Umma ta karɓa tace, "to mungode, ai yanzu bashi ba ko ke kin daina zuwa, yanzu nida Mamarku kaɗai ke zumunci, amma kema dan ƴar uwarki bata nanne, nasan da kinzo". Sai da Safiyya ta sadda kanta ƙasa kana tace, "a'a Umma yanzu ba ko ina nake zuwa ba sabida bana jin daɗin fitar". Ta kai ƙarshin zanci kamar tayi kuka. Dubanta Umma tayi da alamun tausayawa tace, "wai Safiyya har yanzu baki samu ko number wayar taba? wallahi yanzu haka sabida baƙincikin rashin ta har na kamu da matsalar ido, dan yanzu ba komai nake gani sose ba, Safiyya dan Allah ki ƙara bincika muna koda mai number ta yabamu, dan kwannan ina yawan mafarkinta tana kuka". Magana take amma hawaye na zuba a idonta. Safiyya ma da taga Umma na kuka itama bata san lokacin da yazo mata ba, cikin kuka tace, "Umma insha Allah gobe zanje makaranta na ƙara bincike koda Allah zai sa musamu number ta". Godiya Umma tayi mata haɗi da sanya mata albarka. Safiyya tashi tayi ta taya Umma sauran aikace-aikacin gida daga baya tayi tafiyar ta. ******* Saida su Hajara sukayi kwana biyu police station sannan akafito dasu dumin atambaye su daga ina suke?. Wani ɗan ƙaramin ɗakine mai kama da akurkin kaji wannda ko mutum ɗaya yace ya zauna sai ya wahala bare mutum biyu, shi aka buɗe suka fito daga ciki kamar wasu ƴa yunwa, sabida kwana biyun da sukayi har sun fara zanja kala. Gaban DpO aka tisasu, sai da yagama yimusu kallon tsaf kana yace, "watu kune ke fitowa dan kulalata muna ƙasa ko?". A wahalce, "Hajara ta buɗa baki tace, "wallahi a'a asali mu ƴan makarantane". DpO yace, "wace alama zangani wadda zata tabbatar min ku ƴan makaran tane". Jiki na karkarwa ta buɗe jika ta ɗauku l. D card ɗinta na makaranta ta nuna masa. Karɓa yaya kana ya duba yace, "to mi yafitar duku cikin dare?". Rasa mizata ce tayi sai can tace, "Kakatace kuma ita kaɗai ta ragemin aka bugu min waya akaci ta rasu shine na ce sai naje ita kuma ƙwata tace nabiri da safe muje nace a'a to shine tace zata rakani, muna fitowa muka samu ɗan acaɓa to yana shigowa damu cikin garin sai yatusamu wajan da kuka ganmu". Takai karshin maganar tana kuka sose. Bayan dpo yagama ƴan rubuce² sa ya sallamesu tare da jamusu kunne sose, kana suka kama hanyar fita. Bayan sun fito kallon-kallon suka farayi tsakanin su sai Zahara ta buɗa baki tace, "to yanzu ina zamuje?". Sai Hajara tace, "muƙarasa wajan gidan Malam, dan wallahi wannan uwar wahalar da muka sha bazata tashi abanza ba sai munɗau fansa akan Anwar da Hafsat". Sai zahara tace, "da muntafi gida zai fi". Hajara tace, a'a gaskiya ni ba inda zanje, sai inke zaki tafi na tarar miki napep kije". Tace, "a'a tare muka zo kuma tare zamu koma, haka suka ƙarasa cikin garin da Malamin yake, wani gida suka yadda zango kuma suka ruƙesu nan zasu zauna har lokaci da zasu je wajan Malam yacika, bamusu ko suka yardar musu har lakaci ya cika. Ƙarfe ukun dare nayi suka fito suka tafi wajan Malamin can saman wani dutsi, kuma koda suka je wajan cike yake da mutane duk wannda ke wajan burisa ya ƙarasa wajan bokan nasu. Sai wajan ƙarfe huɗu su Hajara suka samu shiga, bayan sun shiga basu wani jama ba suka fito ɗauke da murmushi afusakar su, waje suka samu suka zauna har inda gari yayi haske sannan suka kamu hanyar gida ciki da farin ciki a zukatansu. Hafsat tana hospital kwance tana bacci, kanata take gargizawa tana so ta tashi amma takasa, sai can ta samu ta buɗa baki ta ambace sunan Allah, aikuwa tana faɗin haka ta farka cikin razana sai haki take kamar wanda tayi tsarar gudu. Ba ɓata lokaci ta tashi tashga toilet ɗin dake cikin ɗakin, alwala ta ɗuru tazo ta tada sallar nafila. Haka ce ta faru wajan Ummar Hafsat itama wani mugun mafarki tayi kuma akan Hafsat, ba ɓata lokaci taje ta ɗuru alwala ta tada sallah tana kai kukanta wajan Allah. Hafsat tana gama sallah ta ɗauku wayar ta ƙur'ani dake kan wayar ta ta buɗe ta fara karatu, sai datayi karatu sose tafara koro addu'oi tana kuka tana faɗin, _Lailahailla anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin._ _Hasbiyal lahu lailaha illahuwa alaihi tawakkaltu wahuwa Rabbul arshil azeem._ Haka take ta mai-mai tawa tana kuka sose, dan baƙaramin tashin hankali tashigaba gami da wannan mafarki, tana kan sallaya har akayi kiran sallah ta gabatar da sallah tana cikin tasbihi bacci mai nauyi ya ɗauke ta. Gyafin Umma ma haka ta kasance. Kusan ƙarfe goma sai ga sulaiman yazo wajan Aunty Shemah dan su yake suje suga ya jikin nata. Bai jima da tahuwa ba sukaje wannan karum har da Affan. Koda suka isa wajanta sai bacci take, mutsin da tajine shi ya farkar da ita daga baccin da take, ahankali ta buɗe idonta, wayar dake kusa da ita ne ta ɗauku ta duba lokaci, sose tayi mamakin wannan baccin da tayi, kuma yanzu wasai take jin jikinta kamar bata taɓa ciyo ba,juyawar da zatayi sai ganin Aunty da Sulaiman tayi suna mata murmushi, martanin murmushin ta mayar musu kana tace, "Aunty ku ƙaraso". Affan ne ya antayo da gudu ya faɗa jikinta yana faɗi, "missing you Aunty na". Murmushi tayi kana tace, "missing too Affan". Tana faɗa tana jan kuma tunsa. Har zai sake magana Aunty tace, "kada kacika mu da surutu nan ba gida mukeba hospital muke". Murmushi Hafsat tayi haɗi da gaishesu. Amsawa sukayi sannan sukayi mata yajiki?. Tace, "gaskiya ni yanzu ba abinda ke damuna, ni kwai mu koma gida". Sulaiman yace, "bari naje naji mi zasu ce idan suntabbatar da kin ji sauƙi sai muwuce gida. Bai jima da fitar sa sai gashi ya dawo tare da faɗin, "Aunty sunce zamu iya tafiya dan duk wani bincike sun mata kuma sunce yanzu bawani matsala sai dai takiyaye shan magani". Aunty tace, "insha Allahu zata kiyaye". Daga haka suka juyo zuwa gidan Aunty Shemah. ***** Tunda ya tashi bacci yaji sabon al'amari ajikinsa, dan jiyake kamar bashi ba, ya kasa tsaye ya kasa zaune, shidai burinsa yaganshi a sokoto yanzu. Wayar sa ya ɗauka ya dan yakirata kuzai samu natsuwar abinda yakeji.... *#VOTE COMMENT SHERA* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 28📑* *__________📖* Koda taje gidan su Hafsat, sosai Umma taji daɗin ganin ta tace, "Umma gashi inji Yaya yace na kawo miki yana gasheki kuma anjima zai zo". Sai da Umma ta karɓa tace, "to mungode, ai yanzu bashi ba ko ke kin daina zuwa, yanzu ni da Mamarku kaɗai ke zumunci, amma kema dan ƴar uwarki bata nan ne, nasan da kin zo". Sai da Safiyya ta sadda kanta ƙasa kana tace, "a'a Umma yanzu ba ko ina nake zuwa ba sabida bana jin daɗin fitar". Ta kai ƙarshin zanci kamar tayi kuka. Dubanta Umma tayi da alamun tausayawa tace, "wai Safiyya har yanzu baki samu ko number wayar taba? wallahi yanzu haka sabida baƙin cikin rashin ta har na kamu da matsalar ido, dan yanzu ba komai nake gani sosai ba, Safiyya dan Allah ki ƙara bin cika muna koda mai number ta yabamu, dan kwannan ina yawan mafarkinta tana kuka". Magana ta ke amma hawaye na zuba a idonta. Safiyya ma da ta ga Umma na kuka itama bata san lokacin da yazo mata ba, cikin kuka tace, "Umma insha Allah gobe zanje makaranta na ƙara bin cike koda Allah zai sa musamu number ta". Godiya Umma tayi mata haɗi da sanya mata albarka. Safiyya tashi tayi ta taya Umma sauran aikace-aikacin gida daga baya tayi tafiyar ta. ******* Saida su Hajara sukayi kwana biyu police station sannan akafito dasu dumin atambaye su daga ina suke?. Wani ɗan ƙaramin ɗakine mai kama da akurkin kaji wannda ko mutum ɗaya yace ya zauna sai ya wahala bare mutum biyu, shi aka buɗe suka fito daga ciki kamar wasu ƴa yunwa, sabida kwana biyun da sukayi har sun fara zanja kala. Gaban DpO aka tisasu, sai da yagama yimusu kallon tsaf kana yace, "watu kune ke fitowa dan kulalata muna ƙasa ko?". A wahalce, "Hajara ta buɗa baki tace, "wallahi a'a asali mu ƴan makarantane". DpO yace, "wace alama zangani wadda zata tabbatar min ku ƴan makaran tane". Jiki na karkarwa ta buɗe jika ta ɗauku l. D card ɗinta na makaranta ta nuna masa. Karɓa yaya kana ya duba yace, "to mi yafitar duku cikin dare?". Rasa mizata ce tayi sai can tace, "Kakatace kuma ita kaɗai ta ragemin aka bugu min waya akaci ta rasu shine na ce sai naje ita kuma ƙwata tace nabiri da safe muje nace a'a to shine tace zata rakani, muna fitowa muka samu ɗan acaɓa to yana shigowa damu cikin garin sai yatusamu wajan da kuka ganmu". Takai karshin maganar tana kuka sose. Bayan dpo yagama ƴan rubuce² sa ya sallamesu tare da jamusu kunne sose, kana suka kama hanyar fita. Bayan sun fito kallon-kallon suka farayi tsakanin su sai Zahara ta buɗa baki tace, "to yanzu ina zamuje?". Sai Hajara tace, "muƙarasa wajan gidan Malam, dan wallahi wannan uwar wahalar da muka sha bazata tashi abanza ba sai munɗau fansa akan Anwar da Hafsat". Sai zahara tace, "da muntafi gida zai fi". Hajara tace, a'a gaskiya ni ba inda zanje, sai inke zaki tafi na tarar miki napep kije". Tace, "a'a tare muka zo kuma tare zamu koma, haka suka ƙarasa cikin garin da Malamin yake, wani gida suka yadda zango kuma suka ruƙesu nan zasu zauna har lokaci da zasu je wajan Malam yacika, bamusu ko suka yardar musu har lakaci ya cika. Ƙarfe ukun dare nayi suka fito suka tafi wajan Malamin can saman wani dutsi, kuma koda suka je wajan cike yake da mutane duk wannda ke wajan burisa ya ƙarasa wajan bokan nasu. Sai wajan ƙarfe huɗu su Hajara suka samu shiga, bayan sun shiga basu wani jama ba suka fito ɗauke da murmushi afusakar su, waje suka samu suka zauna har inda gari yayi haske sannan suka kamu hanyar gida ciki da farin ciki a zukatansu. Hafsat tana hospital kwance tana bacci, kanata take gargizawa tana so ta tashi amma takasa, sai can ta samu ta buɗa baki ta ambace sunan Allah, aikuwa tana faɗin haka ta farka cikin razana sai haki take kamar wanda tayi tsarar gudu. Ba ɓata lokaci ta tashi tashga toilet ɗin dake cikin ɗakin, alwala ta ɗuru tazo ta tada sallar nafila. Haka ce ta faru wajan Ummar Hafsat itama wani mugun mafarki tayi kuma akan Hafsat, ba ɓata lokaci taje ta ɗuru alwala ta tada sallah tana kai kukanta wajan Allah. Hafsat tana gama sallah ta ɗauku wayar ta ƙur'ani dake kan wayar ta ta buɗe ta fara karatu, sai datayi karatu sose tafara koro addu'oi tana kuka tana faɗin, _Lailahailla anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin._ _Hasbiyal lahu lailaha illahuwa alaihi tawakkaltu wahuwa Rabbul arshil azeem._ Haka take ta mai-mai tawa tana kuka sose, dan baƙaramin tashin hankali tashigaba gami da wannan mafarki, tana kan sallaya har akayi kiran sallah ta gabatar da sallah tana cikin tasbihi bacci mai nauyi ya ɗauke ta. Gyafin Umma ma haka ta kasance. Kusan ƙarfe goma sai ga sulaiman yazo wajan Aunty Shemah dan su yake suje suga ya jikin nata. Bai jima da tahuwa ba sukaje wannan karum har da Affan. Koda suka isa wajanta sai bacci take, mutsin da tajine shi ya farkar da ita daga baccin da take, ahankali ta buɗe idonta, wayar dake kusa da ita ne ta ɗauku ta duba lokaci, sose tayi mamakin wannan baccin da tayi, kuma yanzu wasai take jin jikinta kamar bata taɓa ciyo ba,juyawar da zatayi sai ganin Aunty da Sulaiman tayi suna mata murmushi, martanin murmushin ta mayar musu kana tace, "Aunty ku ƙaraso". Affan ne ya antayo da gudu ya faɗa jikinta yana faɗi, "missing you Aunty na". Murmushi tayi kana tace, "missing too Affan". Tana faɗa tana jan kuma tunsa. Har zai sake magana Aunty tace, "kada kacika mu da surutu nan ba gida mukeba hospital muke". Murmushi Hafsat tayi haɗi da gaishesu. Amsawa sukayi sannan sukayi mata yajiki?. Tace, "gaskiya ni yanzu ba abinda ke damuna, ni kwai mu koma gida". Sulaiman yace, "bari naje naji mi zasu ce idan suntabbatar da kin ji sauƙi sai muwuce gida. Bai jima da fitar sa sai gashi ya dawo tare da faɗin, "Aunty sunce zamu iya tafiya dan duk wani bincike sun mata kuma sunce yanzu bawani matsala sai dai takiyaye shan magani". Aunty tace, "insha Allahu zata kiyaye". Daga haka suka juyo zuwa gidan Aunty Shemah. ***** Tunda ya tashi bacci yaji sabon al'amari ajikinsa, dan jiyake kamar bashi ba, ya kasa tsaye ya kasa zaune, shidai burinsa yaganshi a sokoto yanzu. Wayar sa ya ɗauka ya dan yakirata kuzai samu natsuwar abinda yakeji.... *#VOTE COMMENT SHERA* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 29📑* *__________📖* Tana kwance ɗakin su Zahara, dan tunda suka dawo bata koma ɗakinta ba, bari tayi har ta ɗan dawo dai-dai, dan ta san da taje can ɗakinsu zasu cikita da tambaya miya faru da ita, tana cikin wannan tunanin taji wayar ta na ƙara, tsaki taja sannan ta ɗauka daniyar tayi piking, aikuwa sunan da taga ya bai yana kan screen ɗin wayar ai bata san lokaci da ta tashi zaune ba haɗi da faɗi, "Zahara zo kigani". Tafaɗi haka ciki da farin ciki. Zahara da ke toilet da sauri ta fito, kafin tayi magana Hajara ta nuna mata wayar ta da ke rura, sunan da taganine yasa tayi guɗa haɗi da ta ka rawa, sannan tace, "kada ki ɗauka barshi har sai ya kawo kanshi". Hajara tace, "ko dama bani daniyar ɗauka, aikuwa haka tayi ta ƙarar har yagaji da kira ya aje wayar zuwa ajima ya koma kira ko zai ta ɗauka. Anashi ɓangare ba ƙaramin haushi yaji na rashin ɗaukar wayar da batayi ba, lokaci ɗaya yaji gwara yaje da iran yadda yakeji shi baya iya zama bai gantaba, part ɗin iyayensa ya nufa cikin sa'a koda yaje lokacin suka fito dan yin beark, ƙarasowa yayi wajansu kujrar dinning yajewo ya zauna sannan ya gaishesu, bayan sun amsa sai Mumy ta dube Anwar da kyau, kana tace , "Autana, wai mike dumunka naganka yau duk kawani ya mutse kamar ba kaiba". Sai Daddy sa yace, wallahi tunda yaje sokoto ya dawo nake ganinsa haka, kafaɗamuna idan akwai abinda ke damunka muji idan zamu iya baka taimako sai mu baka, amma katsaya kana tawani ɓoye muna abu, gaskiya bamasan haka". Yakai ƙarshin maganar yana dubin Anwar ranshi kamar a ɗan ɓace. Jikinsa a sannyaye yace, "a'a Daddy ba abunda ke damuna gaskiya, kuma da kukace duk na yamutse, ai kwanan ina fama da zazzɓi ne shiya kawo min haka amma yanzu alhmadulillah". Ba dan sun yarda ba suka ce to Allah ya ƙara lafiya. Daddy yasake magana haɗi da duban Anwar yace, "kuma kashin sati nasama za'aje neman aurenka da Saudat, ƴar gidan Alhaji Sambo". Da dauri Anwar ya ɗago kansa yace, "mikace Abba!. "Abinda kunnenka yaji shi nace". Yace, "gaskiya Daddy ni ba ita nake so ba". Ai Daddy da Mumy lokaci ɗaya suka ɗau salati kana suka ce atare, "baka sonta!!. "Eh" yace dasu, ai tun bai rufe baki ba Daddy yace, "wallahi Anwar karya kasha kuma baka isaba dan bazaka maidani ƙaramin mutum ba, farko kace kana so yanzu kuma kace baka so, to bari kaji wallahi ba gudu baja da baya in har kaga ba iyiba to ɗayan mune bashi da rai". Yana faɗar haka suka tashi domin su bar wajan ransu amatuƙar ɓace, wato su Anwar zai rainawa da hankali ya maidasu ƙananan mutane. Shima ɗin ranshi amatuƙar ɓace ya tashi ya je ɗakinsa, key ɗin motar sa ya ɗauka, ai fusace yazo ya fige motar ya kama hanyar garin sokoto. Gudu yake kamar ya fira sama cikin awa huɗu sai gashi yazo garin sokoto, hanyar da zata sadashi da unguwar da Hajara take zaune ya ɗauka, gudu yake ko kallon gabansa bayayi, kwatsam gaji abu yaba da gab gab, har yaso yaƙi tsayawa, amma irin yadda yaga mutane sun taso masa yasa ya tsaya amma ba dan ransa yaso ba. Kuda yafito cikin motar yazo wajan dan yaga waya bige, wani mutum shi ba tsofo ba kuma shi ba yaro ba, yagani kwance da alamu ko numfashi bayayi, aikuwa Anwar na ganin haka hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba, cikin hanzari yasa wasu daga cikin mutanin aka ɗaukeshi a kasa mota kana suka wuce hospital. ******* Kwance take kamar mai bacci amma ba bacci take ba, dan gabaki ɗaya hankalinta baya jikinta, wayar tace ta fara rura, ɗauka tayi batare da ta buɗe ido ba bare ta duba wake kiranta, muryarsa ce dataji yasa ta shaidashi . Sallama yayi mata kana ta karɓa sannan ta gaisheshi, shuru ne ya biyu baya sai can yayi magana cikin kasalaliyar murya yace, "Hafsat". Da taji haka sai da taji wani abu ajikinta kana ta buɗe baki can ƙasan maƙoshi tace, "na'am Yaya". Sai da ya sauke ajiyar zuciya kana yace, "yajiƙin naki, ina fatar kinsamu sauƙi". Tace, "sosai kuwa dan yanzu wasai nake jina kamar banyi ciyo ba". murmushi yayi kana yace, "kodama nace bari na gayamin ko zakije gida kiyi hutun ƙarshin shekara a can? inyaso idan hutu ya ƙare sai nabiya miki kuɗin jirgi ki dawo". Tun bai kai ƙarshin zancen ba tace, "Aunty Shema zata je ne". Yace, "a'a ita sai ta kammala zata koma dan kwanannan mai gidanta zai zo". To nima gaskiya bazanje ba, dan koni bazan sake komawa gida ba sai na gama karatu gabaki ɗaya, amma inaso idan kaje kayi min abu ɗaya, ka karɓumin number Safiyya da Naja'atu please". Rasa mi zaice da ita yayi, dan haka yace, "tom naji, ƙoƙari datse kiran ya fara, sai tayi saurin faɗin, "in ba damuwa inaso na koma hostel da zama tunda mijin Aunty zai zo ka ga kar na takurasu". Kasa magana yayi sai can yace duk yadda kikayi dai-dai ne". Yafaɗi haka ransa a ɓace yana faɗa ya datse kiran batare da ya ji mizata sake faɗa ba. Tanajin yadda yayi maganar tasan baiji daɗin abinda tace ba, amma ita gaskiya ji take idan yazo yatar da ita gidan kamar ta takurashi dan haka ma yasa tayi wannan tunanin. Ummar Hafsat ce zaune tayi tagumi abin duniya duk yabi ya dameta ga Baban Hafsat tun safe yafita har yanzu bai dawo gida ba, kuma takira wayarsa amma ance kashe take, kuma gashi su Marwan har yanzu basu dawo ba bare tace su nemumatashi wata ƙila yaje wurin aikin sane, dan yanzu gabaki ɗaya duniya tayi musu zafi dan tun wancan watan aka sallame Abban Hafsat daga aiki, sabida wata sata da a kayiwa , company kuma a kace sai sun biya, haka Abban Hafsat ya tattara duk wata ƙadara tashi ya sayar yabiya su kuma suka sallameshi daga aiki, a cewarsu har dashi cikin masu yimusu sata, abubuwa duk sun tsaya dan ko karatun su Marwa ya tsaya sabida ba abinda za ayi afani dashi wajan cigaban karatunsu, abun dai sai wanda ya gani danshi yanzu sai sun fita kasuwa sunyi dako sannan zasu samun abinda suka ci, ko Baban Safiya yayi musu aike ko Abbas Yayan Safiya. Yau ma kamar kullum akatashi ba komai a gidan, dan ko abin da zasu karya babu kuma gashi Abban Hafsat ko kwabo baya da, dan haka yace a bari yazo, fita yayi yaje wajan wani abokinsa ko da zai samu rance, to yana kan hanyar tafiyane ya kawo dan ya tsallake ti-ti bai san da wani abin hawa ba, dan haka yazo dan ya tsallaka, aikuwa yana dab da tsallakewa yaji wani abu yabashi gab-gab...... *#VOTE COMMENT SHERA* *©SUMY NA'IGE* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~VOTE & FOLLOW 4~ ~Wattpad Summy M Na'ige~ *SHAFI NA 30📑* *__________📖* Tun lokacin bai saike sanin inda kansa yake ba sai a gadon hospital, lokacin da ya farko, da ƙyar ya buɗe bakin sa ba abinda yake ambatowa sai sunayin Allah, yana cikin haka sai ga Anwar ya shigo, da sauri ya karasa gareshi yana faɗin, "Abba sannu ka farka? ya kakeji yanzu?". Bai ce dashi komai ba, sai da ya kuma wata magana yace, "Abba ko kana da waya a kira iyalinka a shaida musu halin da ake ciki?". Sai da Abban Hafsat yaji an ambace iyalinsa sannan ya ɗago da kansa ya buɗe baki da ƙayar yace, " ina tunanin banzo da waya ba, amma idan kana da ita sai nasaka number yarona ko mai ɗakina ka kira". Yayi wannan maganar kamar sheɗar

Chapter 11 of 13