Share this page
sa tafita daga jikinsa. Sosai Anwar ya tausayawa halin da yake ciki dan har ga Allah bai da niyar ya tsaya, amma da yaga halin da wannan bawan Allah yake ciki yaji zai tsaya har yasamu ɗan sauki. Wayar sa ya ɗauku ya miƙa masa yace, "Abba gashi kasanya number". Ba musu ko ya karɓa, da ƙyara yake danna wayar har yasanya ya bashi yace yakira ya faɗa musu halin da a ke ciki. Ringing da bai wuce uku ba aka dauka, Maryar namiji yaji dan haka yayi masa sallama, bayan sun gaisa yake faɗa masa Abbanka yace, "a sanar da ku yasa mu haɗari dan yanzu haka an kwantar dashi asibiti, amma da sauƙi dan har ya farfaɗo kuma shi ya bada number ka a kiraka"....tun bai kai ƙarshin zancin ba sai Marwan yafara magana cike da tashin hankali yace, "dan Allah wanne asibiti?". Wata hospital ɗin kuɗe ce ya faɗa masa, yace gasu nan zuwa yanzu. Aikuwa Marwan na gama waya da Anwar ya ƙarasa gida ciki da tashin hankali ya faɗawa Ummar su halin da ake ciki, hannun ta ɗura saman kai tafara kuka kamar ranta zai fita, da ƙyar Marwan ya rarrashe ta tayi shuru kana suka shiriya sukaje hospital ɗin. Dayake hospital ɗin da ya kaishi sannan na ce aciki garin sokoto, dan haka basusha wahala wajan gane wajan da yake ba. Suna shiga ɗakin da Abba yake suka tarar da Anwar zaune kusa dashi shiko Abba yana bacci, da sauri Umma ta ƙaraso garesa tana kuka tana faɗan, "dan Allah kar katafi ka barmu Abban Hafsat". Yana cikin bacci yaji kukanta, dan haka ya buɗe idonsa, hannu ya ɗura saman kanta, ɗagowa tayi da kanta, alamun yayi mata da tayi shuru , ba musu ko ta ɗan rage kukan da takeyi. Anwar dake zaune yanajin sun ambace Hafsat sai da gabanshi ya faɗi, shi bai san mike faruwa dashi ba, duk lokacin da yaji sunan Hafsat sai yaji faɗuwar gaba. Tashi yayi yayi musu sallama yace zuwa ajima zai dawo. Da fitarsa bai tsaya ko inaba sai wajan da a kace masa zai ga Hajara, yana isa kuma a kace yanzu suka bar wajan, yinin ranar duk inda yake tunanin zai ganta yaje amma bai ganta ba, sosai yaji zafin wannan lamar yayi danasanin zuwan sa garinnan yanzu, dan da yasan haka zata faru dashi da bai zo ba, kiran sallah da yaji anayi ne yasa yayi parking ɗin motar sa yashiga masallace, bayan an idar da sallah sai limamin wajan yayi karatu tare da karanta wasu ayoyi na alƙur'ani kuma ya fassarasu har inda ya kawo cewa duk wani bala'i ko musiba idan sun afku gareka to ka yawaita sadaka, kuma duk wani abu dakake san samu to yawaita sadaka, nan dai limamin yaci gaba da wa'azi da nuna mahin mancin sadaka, sosai Anwar ya natsu yana saurarin abinda ake magana akai, dan rabanshi da yaje wurin wa'azi ko ya saurareshi har ya manta, bayan limamin ya kammala kana a kayi sallah isha'i sannan Anwar yafito daga cikin masallacin, aikuwa bai bar unguwar da yake ba sai da yafitar da kuɗi masu yawan gaske ya fara sadaka, da yake unguwar da ya tsaya marasa ƙarfi sunfi yawa, aikuwa sai ganin mutane kake suna fitowa maza da mata yara da manya wajan karɓar sadaka. Duk kuɗin dake hannunsa sai da yara bar da su, kuma suna ƙarewa sai ga wata tshowa tazo wajansa tana faɗin, "dan Allah Alhaji ka taimaka min wallahi ƴata ce bata da lafiya kuma likitoci sunce sai ammata aiki kuma wallahi bamu dasu dan yariyar marainiya ce". Tafaɗi haka hawaye na zuba a idonta. Rasa mai zaiyi yayi dan kuɗin dake hannunsa sun ƙare dan haka yaje mota ya ɗauko cheque, rabin million ya rubuta mata yace gasu ayi haƙuri, sosai ƴar tsohor nan taji daɗi lokaci ɗaya ta fara suburbuɗu masa da addu'oi tana faɗin, yadda kayaye min wannan baƙinciki kaima Allah yaya ye makashi haka ta cigaba da kwararo masa addu'a har yabar wajan. Masalacin da yayi sallah ya koma, limamin masallacin ya je sukayi magana dashi a kan zai gyara masallacin, dan masallacin yana son gyara sosai, dan haka ba ɓata lokaci ya rubuta cheque ɗin million ɗaya ya bayar yace a gyara masallaci, sosai sukayi masa addu'a daga baya ya shigo mota ya dawo hospital dan yaga ya mai jiki. Tuƙi yake amma sai jinsa yake kamar anɗauke masa wani abu aka. Koda yaje asibiti jikin Abba Alhmdulillah dan sosai yasamu sauki dan shi abin har mamaki ya bashi, gaishesu yayi kana ya aje musu abinda ya sayo musu sannan yayi musu sallama kan sai da safe idan ya dawo, sosai suka yi masa godiya irin yadda yatsa ya jajirce akan ciyon Abba, dan yanzu sau tari mutum ya bige mutum amma ba zai tsaya ba bare ya bashi kulawa, wani ko ya tsaya da zaran ya kai shi asibiti zai gudu, amma shi ya tsaya har yana faɗin gobe zai dawo, tunanin da Ummar Hafsat keyi kenan. Yana fita daga ɗakin sai ga Safiyya tazo ita da iyayenta da Yayan ta, Allah ne kawai bai haɗasu ba, dan saura kaɗan suyi karo da Yayan Safiyya akan hanya. Yana fitowa a hospital bai tsaya ko ina ba sai ma saukin sa, yana shiga bayan yayi parking ɗin motar yafito bai tsaya ko ina ba sai falon gidan, zama yayi saman kujera three seated ya ɗan huta, dan yanzu ji yake kamar an ɗauke masa wani abu kai, wanka yaje yayi sannan ya kwanta, wayar sa ya ɗauku ya kira iyayensa ya shaida musu wani uzuri ya kamashi na gaugawa yanzu haka yana sokoto, basuce dashi komai ba sai fatan alhairi. ___________________ Suna gama waya da Anwar wata ƙawarta takirata tace, "wai hala Hajara baza kizo birthday ɗina ba, kuma kinsa za'ayi casu". Aikuwa Hajara najin haka tace, "kar ki samu damuwa yanzu zaki ganni". Tana gama faɗar haka ta tashi tashiga toilet tayi wanka, sosai ta ɗan ɗasa kwaliya kamar wani abu bai same taba. Kallon Zahara tayi dake zaune tace, "Zahara zaki rakani shukura hotel wajan birthday ɗin ƙawata?". "A'a bazanje ba dan kinsan ba wajan zuwa nane ba". Cewar Zahara. Tace, "ba damuwa ni zanje sabida nasan akwai harka". Tana faɗar haka ta kama hanyar fita daga ɗakin. Zahara tace, "ki tsaya mufita tare inyaso kowa yaje wurin da zashi. Haka kuwa sukayi dan suna kawowa bakin ti-ti ko wace ta tsayar da mai napep ta faɗa masa wajan da zai kai ta. Dai-dai shukura hotel aka aje Hajara, kuɗinsa ta bashi kana ta ƙarasa daga ciki, tun bata ƙarasa ba ta fara jin kiɗa natashi kamar zai tsaga ƙasa, koda ta ƙarasu wajan da aka kiɗan yacika sosai, maza da mata kuwa sai rawa yake kuma cikinsu ba mai shigar kirki, kace su duk ɗiyan arnane. Tana cikin tafiya taji an rungumuta ta baya, juyuwar da zatayi dan taga kowaye, bashiri taji bakinta cikin nasa, a hankali yake tafiya da ita har ya ƙarasa gaban musu kiɗa, a hankali ya cire ta daga jikinsa, da sauri ta ɗago ido ta kalloshi dan taga kowaye, murmushi ya sakar mata itama ta mai dar masa da martani, dan ta gane kowaye, lokaci ɗaya a ka cigaba da kiɗa suna rawa ciki da shauƙi. Bayan angama kiɗa da raye-raye kuwa yazo ya zauna a ka kawo abin mutsa baki, suna cikin haka ita dashi sai ga wasu ƙawayen su sun zo suka ci tazo minti biyu, ba musu ko ta tashe taje, wani ɗaki suka shiga da ita, zama sukayi saman kujerun dake jere a cikin ɗakin, basu jima da zama ba sai ga wata ƙawar su tafito tana tafe tana rangwaɗa kamar wata arniya, gaban Hajara tazo wani ƙofi ta miƙo mata tace, "karfi ki shanye dan ke kaɗai zan ba, kinsan kayan harka ba kuwa a ke baiwa ba". Tafaɗa haka murmushi ɗauke a fuskarta. Ba ɓata lokaci Hajara ta ƙarɓa ta kafa kai tanasha. tunda ta fara sha suka fara wani murmushi mai ɗauke da ma'anuni da dama. Bata ɗauke kai ba sai da ta shanye. Ƙofin ta miƙo mata tana murmushin jin daɗi. Fira suka tsayayi daga baya suka fito dan kowa yaje wajan da zashi. Koda suka fito mafi yawan cin mutane duk sun watse dan suna can suna fira mutane har sun fara tafiya. Koda Hajara ta zo wajan da suke zaune har wannan mutum yayi tafiyar sa. Wajan ƙawayen ta taje suka cigaba da fira daga baya kowa ya kama gabansa. Sabida dare yayi Hajara bata tsaya komai ba tadawo ɗakinsu sabida bata jin daɗin jikinta. Tana zuwa ko ta kan Zahara bata biba tayi kwanciyar ta. Tana cikin bacci taji kamar wani abu yana murɗarta, lokaci ɗaya ta sanya wata ƙara wadda yasa duk wanda ke layin sai da ya farka, Zahara dake ɗaki ɗaya da ita ciki matsanancin tsoro ta faraka haɗi da ƙarasawa wajan ta, ido tazara tare da ɗaura hannu a kai tana faɗin, "nashiga uku Hajara mi yasa meki haka?". ******* Sulaman tun daga lokacin bai sake kiran Hafsat ba, amma sai famar nemar mata aiki yake sabida baya son ya bar ƙasa batare da ta fara aiki ba, dan idan tana aiki albashinta zai isheta har tariƙe kanta batare da ta nemi taimakon kowa ba, kuma cikin ikon Allah ya samar mata aiki a wata asibiti, sosai taji daɗin haka dan haka tace zata cigaba da zama gidan Aunty shemah batare da ta koma hostel ba. Sai da yaga komai ya dai-data wajan aikin ta sannan ya tattaru nashi da nashi ya dawo ƙasar shi ta haihuwa ciki da kyawar ta. Ita ma haka ta kasance gareta da har kuka sa da tayi lokacin tafiyarsa. Haka dai tacigaba da karatu kuma tana zuwa wajan aikin ta, batada wata matsala ko damuwa, matsalar ta itace yanzu Ummar ta take yauwan mafarki a ko da yaushe, dan tunda tazo bata taɓa kewar gida ba sai wannan lokaci, kuma bataji zata iya tafiya ba har sai ta ida phd, dan yanzu shekara ɗaya ce ta rage mata ..... *#VOTE COMMENT SHERE* *©SUMY NA'IGE* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 31📑* *__________📖* Soyayya mai ƙarfin gaske tashi tsakanin Hafsat da Sulamai, wanda a yanzu ji suke in ba ɗaya guda bazai iya rayuwa ba, kuma duk wani ɗan uwa Sulaiman yasa Hafsat, dan har waya sukeyi da iyayenshi, sosai suke sonta itama haka, kuma yanzu kowani burinsa yaga ya mallaki ɗan uwansa, ita kanta Aunty Shemah har mamaki take a kan wannan soyayya tasu, jira suke Hafsat ta ida karatunta sannan aje ayi maganar aure gidan su. ****** Bayan kwana biyu Abba yaji sauƙi sosai dan har an salame shi yadawo gida, kuma duk da haka Anwar yana kula da su sosai, dan tunda yazo gidan yaga halin da suke ciki suka bashi tausayi dan haka duk bayan kwana biyu ya kanzo yaga yaya suke, kuma sosai yake taimaka musu, dan yanzu har makaranta ya maida su Marwa, Abba ko ya samar masa aiki a company siminti, kuma yanzu alhmdullih komai na Abba ya fara dawo ahankali, kuma ko Yayan Safiyya ba'abarshi a baya ba dan shima sosai yake kula da su Umma. *A gurguje* Zahar ciki da fargaba ta ƙaraso wajan da Hajara ke kwanace wadda ta naɗe waje ɗaya kamar ranta zaifi, lokaci ɗaya kamanunta suka canja, ba abinda ke fita bakin ta sai wasu yawu masu yauƙi, knocking ɗin ƙofar Zahara da akeyi ne ya fargar da ita, cikin tsoro da fargaba ta ƙaraso wajan ƙofar ɗakin tana faɗi, "waye?". Muryar ƴan layinsu taji dan haka da sauri ta ƙarasa jikin ƙofara taɓuɗe musu. Ko magana basuyi mata ba suka shigo ɗaki dan suga mike faruwa? Hajara da suka gani kwance sai birgima take kamar ranta zai fita. Ɗayan wanda suka shigo ɗakin ya dube Zahara yace, "Zahara mike faruwa da ƙawarki?". Jiki na ƙarƙarawa tace, "wallahi bansani ba koni haka na ganta". Sai ɗayar mace tace, "to wallahi tun bata mutuba ki samu mai napep ya kaita can layi buge ya aje dan wallahi ta mutu ɗakin nan sai ƴan sanda sun tambaye ki". Sosai Zahara tashiga ruɗuwa, jiki na karkawa tace, "to yanzu ina zan samu mai napep cikin wannan dare?". Sai ɗayar mace tace, "kizo muje ɗakin Yawale idan zai yadda sai ya ɗauko motarsa ya kaiki inyaso da kun aje ta kujuyu". Haka ko ta kasance, dan da ƙyara Yawale ya yarda suka je, koda suka je mutane basu fara fitowa ba, dan haka suka ajeta dai-dai bakin ƙofar wani ɗaki suka tahowar su. Koda mutane suka fito sukaganta yasha da ƙasa, waɗan da suka santa su sukaje school ɗinsu aka nemu ƴan garinsu aka haɗata dasu, su sukayi duk yadda za suyi aka kata gidansu, sosai iyayenta suka shiga tashin hankali lokacin da aka kawo musu ita, ita ba matattaba, ita ba mai rai ba, dan sose take jin jiki. Koda labari yariske saurayinta, sosai hankalinsa ya tashi kuma duk wani bincike yayi amma bai ganu kamai gami da lamarin ba, dan ko ƙawayen ta antambaya amma bawani abu da akasamu wanda zai nuna ambata. ******** Suna tashi daga wajan aiki yashigo mota, bai tsaya ko ina ba sai bakin ƙofar gidansu Hafsat, yana fitowa ƙanninta suka fara yimasa oyoyo sabida yanzu jinshi suke kamar wani ɗan uwansu, bai ma tsaya wani neman izini ba ya shiga cikin gida bakinsa ɗauke da sallama. Ummu dake tsakar gida tana girki ta karɓa masa murmushi ɗauke a fuskar ta, kujera da ya gani ce ya zauna kana ya gashe da Umma. Bayan ta amsa ya tambaye ta Abba, tun kam ta buɗe baki tayi magana suka jiyo sallamar Abba. Amsa suka yi haɗi da gaisheshi. Anwar da ya ganine ya faɗaɗa murmushin sa, hannu ya miƙo masa sukayi musabaha kana suka cigaba da firarsu. Suna cikin haka har Umma ta kammala abinci ta kawo musu shida Abba suka ci, bayan sunci sun ƙoshi suka koma ɗura wata fira, suna cikin haka sai ga Safiyya ta shigo gidan ɗauke da sallama a bakin ta, gaishe da Umma tayi kana ta ƙasara wajan Abba dan ta gaisheshi, har ta buɗe baki tace, "Abba ina wuni"....bata kai da ƙarasawa ba sabida ganin Anwar da tayi zaune gaban Abba, cikin tashin hankali ta buɗe baki tace, mugu mika zoyi muna agida? ina ka kaimin ƴar uwata!". Tana faɗar haka tazo gareshi haɗi da cungumo masa rifa tana faɗi, "wallahi sai ka nemun ƴar uwa". Irin yadda yayi mata shuru bai ce komai ba, yasa ta raramu wani icci dan ta buga masa, da sauri Abba dake zaune wanda mamaki yaci kasa ya tashi ya karɓe iccin dake hannuta, amma duk da haka sai da ya shafe wani sashe na jikinsa. Komawa tayi kamar wata zararriya, koma ɗauko wani tayi dan ta buga masa da ƙyar Umma da Abba suka shawu kanta ta ɗan natsu, lokaci ɗaya ta fara kuka tana faɗin, "mi kazoyi gidan nan? Ko ka ɗauka ta nan ka karasamin ita?". Gabaki ɗaya kan Anwar ya ɗauri, ga mamaki wanda ya a ddabe shi a zuciya, ahankali ya ɗago idonsa waɗan da sukayi jajar yace, "Safiyya dan Allah kiyi haƙuri ki nunamin wajan da take wallahi da gaske ina sonta, kuma ashirye nake dan na aure ta". Wata harara ta antayo masa sannan ta fara kici niya ta ƙwace daga riƙon da Abba da Umma sukayi mata, suna cikin haka sai ga Yayan ta Abbas yashigo gidan, aikuwa kamar kar yashigo ta ƙwace daga riƙon da su Umma suka yimata ta faɗa jikinsa sannan tace, "Yaya Abbas ga wanda ya lalatamin Hafsat, shi ne sanadin rushi duk wani jin daɗinta, kuma shine yayi mata ciki kuma daga baya ya guje ta.... aitun bata kai ƙarshin zanci ba sai ga Abbas gaban Anwar zai kai masa naushe, da sauri Abba yace, "Abbas kada kasuma wallahi zan ɓata maka rai!!". Faɗa Abba ya fara yi masu sosai sannan suka natsu, bayan komai ya lafa nan Safiyya ta faɗa musu komai wanda tasani tsakanin Anwar da Hafsat, sosai su Abba da Umma ransu ya baci, dan ita Umma sabida baƙin ciƙi kasa magana tayi ba abinda take sai kuka baƙin ciki. Abbane ya dube Anwar da kansa ke ƙasa ba abinda yake sai dana sani da zubar da hawaye yace, "ashe dama haka rayuwar ka take? to ina maka nasiha da kaji tsoron Allah, kasani duk abinda kake Allah na kallon ka, kuma ba abinda zance da kai sai dai nace kaje na barka da Allah". Tun Abba bai kai da rufe baki ba Anwar ya durƙusa gaban Abba yana kuka kamar ransa zai fita yana faɗin, "wallahi Abba na tuba kodama sharin shaiɗan ne amma wallahi son gaskiya nake mata"....tun bai ka da rufe baki ba Abba da Umma suka shige ɗakinsu suka kulle ransu amatuƙar ɓace. Abbas nagani haka ya tasa ƙeyar Anwar gaba yace ya bar musu gidansu kuma yaja masa kunne akan kar ya kuskura ya kuma dawo gidan. Ciki da rashi abinyi Anwar yaja motar sa ya bar unguwar. Allah ne ya kawoshi ma saukin sa, dan yadda yake jan motar ko gani bai yi, yana yin parking ɗin motar yayi haka ya buɗe marfi motar ya fito wani abu yaji ya dakar masa zuciya, lokaci ɗaya ya dafe ƙijinsa, cikin ƙarfin hali ya fito daga cikin motar dan ya ƙarsa falon gidan, ta ko ɗaya zuwa biyu ya faɗi a farfajiyar wajan lokaci ɗaya numfashinsa ya ɗauke. Mai gida da ya gama rufe gate yazo ya shiga ɗakinsa yaga Anwar yashe a ƙasa kamar bashi da rai, da gudunsa yazo gareshi, rasa mi zaiyi yayi dan haka da gudun sa yaje wajan wani maƙocinsa ya faɗa masa halin da ake ciki, daya ke koshi abukin Anwar ne dan haka da sauri yazo suka ɗauke shi suka kaishi hospital. Abbas yana ganin Anwar ya tafi shima ya kama hanyar gida, Safiyya ko ta zauna taci gaba da kuka, Umma ko sai da ciyon ta yatashi sosai tasha wahala kafin ya lafa. Iyayen Anwar da suka ji Anwar shuru dan haka suka kira wayar sa amma bata shiga dan haka hankalin iyayensa ya tashi sosai, dan haka ba ɓata lokaci suka kama hanyar sokoto dan suje suga ko lafiya ɗan su yake. Koda suka isa garin sokoto suka samu labarin abinda ya same ɗan su, dan haka basu tsaya ɓata lokaci ba su tafi hospital ɗin da yake, da ƙyar suka samu aka bari suka ganshi sabida har yau bai farfaɗo ba, sosai hankalinsu ya tashi ganin halin da ɗansu ke ciki kuma autan su. Koda suka tambaye doctor da ke kala dashi dan suji mike damun ɗan nasu, sai doctor ya shaida musu cewa ya kamu da ciyon zuciya saka makon wani abun da yake so ya samu amma bai samu ba, kuma likitan ya shaida musu suyi ƙoƙari su bashi abinda yake so inhar suna son yaci gaba da shaƙar numfashi a durun ƙasa. Hankalinsu ya tashi sosai, haka dan mahaifiyarshi taji har kuka sai da tayi. Kwanan su uku sannan Anwar ya farfaɗo daga dogon suman da yayi, bayan ya farfaɗo suka sake yi masa allurar bacci, sai da ya kwana huɗu sannan iyayenshi suka samu ganawa dashi. Aikuwa yana ganinsu ya fashe da kuka yana faɗin, "Daddy zan mutu, ku taimaka min kuce su bani ita wallahi inasota sharin shaiɗan ne yashiga tsakanin mu amma wallahi har cikin zuciyata ina sonta....tari ya farayi mai haɗi da jini aciki, ruɗewa iyayensa sukayi dan haka da sauri suka kira likita suka shaida masa halin da ake ciki, da sauri suka zo suka fara bashi taimakon gaugawa. Mahaifayar Anwar kuka take ba ƙau-ƙautawa, sabida halin da taga ɗanta keci, ƴa-ƴanta mata tayi ma waya tace su zo suga Anwar dan yayi nisa. Sosai hankalinsu ya tashi dan haka su huɗu suka shigo jirgi zuwa sokoto. koda suka zo suka ga halin da Anwar yake ciki hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, dan haka su yanke shawara zasu fita dashi waje a duba musu lafiyar sa, musamman halin da suka ga iyayayesu sun shiga, dan haka ba ɓata lokaci akayi masa base zuwa ƙasar india. Yayan su Aminu ɗan Yayan Daddy suka kira suka faɗi masa halin da ake ciki dan haka yace to su haɗu acan india dan yanzu haka baya nigeria. Cikin kwana ɗaya akayi musu base suka wuce ƙasar india, kuma cikin ikon Allah sai gashi ankawoshi hospital ɗin da take aiki. Dayaki yanzu suna shiri-shirin kammala karatunsu, dan abu mai wuya ne kesa tayi wata ɗaya ƙasa, dan ita inbanda Sulaiman da gaskiya sai ta ƙara wasu watanni, amma tasan bazai bar ta taƙara koda kwana ɗaya ba bare wata ɗaya dan shi burishi a yanzu duk bai wuce ace ya mallake ta ba amatsayin matar sa. Zaune take laptop na gabanta tana wani bincike gami da karatun, wayar tace tayi ƙara, kamar bazata ɗauka ba kuma sai ta ɗauku, sunan da taga yana yawo kan screen ɗin wayar ne yasa ta sanya wani murmushi wanda ya ƙarama fuskarta kyau da annuri, ɗauka tayi haɗi da karawa akunnin ta, sallama tayi masa amsawa yayi tare da faɗin amarya ta, i miss you". Yafaɗi haka tare da rufe idonsa. Sai da ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "miss you too angona". Shuru ne yabiyu baya, sai can yace, satin nan ne za'ayi bikinku ko?". "A'a sai wani sati". Haka tace dashi ata ƙaice. Gaskiya bazan iya jirin har wani sati ban ganki ba, dan haka ki shiya tarbona daga gobe zuwa jibi". "Da gaske?". "Ki zuba ido zaki sha mamaki, wani sanyin daɗine ya mamaye mata zuciya sannan ta buɗe baki cikin marai-rai cewa tace, "My ango nah". Amsawa yayi yana mai jin wani sanyi azuciyar sa. Tace, "idan ban saka aiki ba ina so dan Allah".... kuma sai tayi shuru ta ƙasa ƙarasawa . Yace, "ƙarasa mana ina ji". Yafaɗa haka da sigar rarrashi. Tace, "koda-kodama ina so in ba damuwa zan turu maka address ɗin gidansu Safiyya ka dubumin ita da iyayen ta dan Allah ba danni ba". Ta karasa maganar kamar zatayi kuka. "Dan wannan ne kike so kimin asarar hawayenki to karki suma, yanzu ki turumin anjima zanje insha Allah". Wani murmushi jin daɗi ta sanye har shi kansa sai da yaji sautin murmushi, kana tace, yanzu zan turum ma". Tana faɗa ta da tseki. Kominti uku ba'ayi ba ta tura masa. Aikuwa zuwa yamma ya shirya yabi address ɗin da ta bashi har ya kawo gidan su Safiyya. Yaro aika yace yakira masa Safiyya, Ko da yaro yaje Safiyya na zaune sai aikin tunani take musamman yanzu da Babban ta ya matsa mata sai ta fitar da miji dan aure yake son yayi mata. Tana cikin haka taji ance ana sallama da Safiyya, gabanta ne ya bada dummm, dan ita batayi dakowa yazo wajan taba. Mamar tace ace gata zuwa, kallon Safiyya dake zaune Mama tayi tace. "to maza ki tashi kije kin bar mutum waje yana jiranki". Dan kar ma tayi mata magana yasa tana faɗar haka ta haɗi fuska. Safiyya da taga alamu haka ba musu ta sanya hijab ɗinta ta kama hanyar waja. Tsaye ta ganshi nesa da gidan su kaɗan, dan haka ta ƙarasa gareshi bakin ta ɗauke da sallama. Amsawa yayi sannan tace, "bangane ka ba". Sai da yayi murmushi yace ko gaisuwa babu? ina fatar kece Safiyya". Yafaɗi haka ajere. Kai ta girgiza masa alamar eh". Sai da ya numfasa sannan yashiga yimata bayani dallah-dallah har sai da ya kammala. Kuka ta sanya masa sannan ta durƙusa gabansa tace, "dan Allah ka taimaka min ka kaini wajan ta dan girman Allah". Magana take hawaye sai famar zuba yake akan kuncin ta. Magana yayi mata yace in har iyayen ki zasu yarda to zai kai ki har wajan Hafsat, sosai taji daɗin abinda yace da ita dan haka tace yazo suje ta kaishi wajan iyayen Hafsat yayi musu bayani ko za su samu natsuwa atare dasu. Ba musu ko yayarda yaje yayi musu bayanin inda Hafsat take kuma da wajan da take zaune, godiya sukayiwa Allah kana sukayi masa godiya sannan suka ce in akwai yadda za'ayi suna son suje suga ƴar su, yace kar su damu su shirya zuwa jibe sai suwace. Haba murna tsakanin Umma da Abba ba'a magana dan kamar anyi musu albishir da shiga aljannanh. Koda Baban Safiyya ya dawo Abban Hafsat ya gaya masa, sosai yayi farin ciki yace shima yana son yaje yaga ƴarsa. Cikin kwana uku aka yimusu base suka wuce india..... to asauka lafiya. *Wai nagaji🤦‍♀️* *SAURA KUKI COMMEN AIKO NIK'I

Chapter 12 of 13