Share this page
gidan sa. Koda taje sai da ta musu knocking a ƙofar gidan maigida ya buɗe ƙofa ya fito. Gasheshi tayi kana ta tambaye shi ko Anwar nanan. Yace baya gari dan ya kwana biyu baya nan,sosai taji zafin rashin samun sa dan yanzu wani son shi ne takeji wanda ji take idan bata ganshi ba zata iya mutuwa. Godiya tama Baba maigida kana ta kama hanyar makaran ta. Har akatashi shoocl bata ga Hajara ba kuma duk inda tasan zata ganta taje amma bata same taba. Ba ƙaramin tashin hankali ta shigaba lokacin da takira wayar Hajira akace kashe take. Alokacin duk wanda ya ganta yasan bata cikin natsuwar ta. Danhar Mamar ta ta tambaye ta amma sai tace wata exmas ce za suyi mai zafi shiyasa take jin tsoro. Addu'ar samun nasara Mamar ta tama ta haɗi da bata shawara. Dadare tana kwance ta kuma gwada kiran Hajara tace ko zata samu,aikuwa cikin sa'a tana kira tafara ringing. Ringing da bai wuce uku ba Hajara ta ɗauka tace, "Ya aki ciki ne Hafsat?". Sai da Hafsat ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "kina ina yanzu?". Kai tsaye tace, ina layin bugi". Sai Hafsat tace, "Subuhanallah, miyakai ki layin bugi kuma?". Sai Hajara tace, "tambayana kikayi nabaki amsa,dan haka bana sun dugon surutu". Sai Hafsat tace, "kodama numbar Jawad nake son ki bani idan kina da ita ko kimin misalin wajan da zan samun sa". Aikuwa Hajara najin me tace ta bushe da dariya haɗi da cewa,"komai kikeso nabaki ki sameni wajan da nafaɗa miki yanzu nabaki abunda kike so". Duk da dariyar da tasa mata tayi mata zafi amma sai ta dake tace, "dan Allah Hajara ki bani wallahi bazan iya zuwa layin bugi ba,bare yanzu da dare". Sai Hajara tace, "tunda abunda kike nema bai dameki ba sai anjima". Har zata katse waya sai Hafsat tace,"zanzo ki gayamin dai-dai ina zan sameki. Tace, "dakin zo kikirani zan fito". Tace kada ki kashe waya gani zuwa. "Aa bazan kasheba". Aikuwa suna gama waya jikinta har rawa yake ta shiyar taje ɗakin Mama tace zataje gidan su Safiyya ta karɓo jikarta dake hannuta dan karatu zatayi. Mama tace to taje amma kar tajima. Tana fita taje bakin ti-ti ta tare mai adai-daita ta faɗa masa sunan inda zai kaita. Bayan ƴar tafiyar da sukayi ya kaita wajan, tun abakin wajan zaka fara ganin mata da maza suna kai kawo kuma dukkan su ba mai shigar kirki. Gabanta ne ya fara faɗuwa har taso ta juya kuma ta fasa. Waya ta ɗauko takira Hajara tace gata nan ƙarasu. Bata jima da kiran Hajara ba ta ƙarasu cikin wata shiga kace ita ba ƴar muslmiba...... *#Vote* *Comment* *Shere* *©SUMY NA'IGE* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMMY M NA'IGGE✍🏼•* ```Don neman cikon labarin👇``` ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *NA 4📑* *__________📖* Shigar da Hajara tayi Hafsat tabi da kallo har ta buɗe baki zata yi magana sai Hajara tace, "zo muƙarasa daga ciki kina tawani kallona sai kace yau kika fara ganina". Sai Hafsat tace, "ni kawai kibani abunda nice dan bazan iya shaga wannan wajanba". Wani kallo Hajara tabita dashi kana tace, "abunda ki ke nemane bai dame kiba dan haka kin ga tafiya ta" . tana faɗar haka takama hanyar zuwa inda tafito. Da sauri Hafsat tabita tana kiran sunan ta amma sai tayi kamar bata san da ita. Ɗakin da taga Hajara tashiga nan ta fara ƙuƙarin shiga,warin wiwi da sigari ne suka bige hancin ta,aikuwa lokaci ɗaya taje da baya,dan bazata iya shaga ɗakin ba. Wayar ta ta ɗauko ta sake kiran Hajara tace, "Hajara gani ƙofar ɗakin da kika shiga, dan Allah kifito ki ba ni". Wata tsawa Hajara ta daka mata kana tace, "Idan bazaki shigo ba kina iya tafiyarki". Wani maƙaƙi ya rufe mata zuciya har taso ta tafi sai kuma wani abu ya taso mata wanda ita kanta bata san ko na meye ba. Sai da ta ɗauke sheɗar ta kana ta buɗe labulen ɗakin ta shiga. Abunda tagani ne yayi matuƙar bata tsoro da mamaki. Dan gabaki ɗaya ɗakin maza da mata ne,kuma ba mai shigar kirki a cikin su. Sosai abun yaba Hafsat tsoro dan kowane namiji rungume yake da mace. Dan ko Hajara kwance take ajikin wani sugar boy daga ita sai wata vest mai haɗe da brazier wadda ta bayanar da surar jikin ta sosai. Wani kallo tabi Hafsat dashi kana tace, "kin tsaya ma mutane akai, in bazaki shigo ba saiki tafi". Hafsat tace, "Hajara dan Allah kibani wallahi sauri na keyi". Batari da ta kalle taba tace "gashinan zuwa yace ki jirashi". aikuwa tana cewa haka sai wannan sugar boy ya yi sauri yace wa ashe itama ƴar hannuce to abamu muɗana". yana faɗa yana kallon Hafsat wadda ta haɗe fuska sai kace akwai wanda ya tilasttamata zuwa wurin Hajara hara zata buɗe baki tayi magana sai wayar ta tafara rura. Ɗauka tayi haɗe da faɗin "ka ƙarasu?". banji me akace ba a ɗayan ɓangarin iya dai tace gatanan zuwa. Kallon Hafsat tayi dake durƙushe a ƙasa tace, "kizo muje". daga haka bata sake magana ba ta fice warta. Itama Hafsat da sauri tabi bayan ta. Wajan wata mota tanufa itama Hafsat tabi bayan ta. Aikuwa suna ƙarasuwa wajan motar sai sukayi ido biyu da Anwar, lokaci ɗaya wani sanyi ya ziyar ci zuciyar ta ai bata san sanda ta faɗa jikin saba tana sauke wata sassanyar ajiyar zuciya. Jikin sa ya matse ta yana jin wani abu a zuciyar sa. Gaba ɗaya ya manta da wata Hajara dake tsaye sai da tayi gyaran murya kana ya ɗago da idanun sa waɗan da suka fara sauyawa zuwa launin ja. Tace, "kizo muyi magana dan sauri nakeyi jirana ake". Raba jikin sa da Hafsat yayi kana ya dube ta yace, "tabari na zo". Nesa kaɗan da ita suka yi kana Hajara ta dube shi tace, "Nagama aikina dan haka kabani abunda kace". Tun bata rufe baki ba ya ɗauko wasu kuɗi masu yawan gaske ya bata,aikuwa tana gani yawan kuɗin da yabata bakin ta ya kasa rufuwa sai godiya take zuba masa dan har jikin sa tasu tafaɗa ya ɗaga mata hannu alamar ka da ta soma,sosai tayi masa godiya kana ta buɗa baki tace, " duk akan Hafsat zaka bani wannan kuɗe,sai yanzu na tabbar da son da ka ke yi mata mai yawan gaske ne,amma bari gaji yadda nayi nasamu kanta". Karasuwa tayi gab da kunnin sa kana ta faɗa masa wata magana. aikuwa tana gama faɗa masa ya bita da wani kallon mamaki kana yace, "Amma gaskiya banji daɗin haka da kika yimin ba" har ya buɗa baki zai sake wata magana sai ga Hafsat ta ƙaraso wajan da suke jikin ta na karkarwa tace musu gida zata koma dan Mamar ta har takirata a waya. Sallama yayi da Hajara kan sai yakira ta,kana ya dau Hafsat ya kaita gida. To tun daga wannan lokacin duk abunda yace da Hafsat bazatayi masa musuba,sai wani son shi da kaunar sa da suka addabe ta wanda yasa takejin zata iya rabuwa da kowa akan sa. Wanda a halin yanzu ta koma kamar matar sa, dan sai yadda yace da ita.... *Cigaban labari* Bayan Safiyya ta fita taci gaba da shirin ta bayan ta kammala tafito domin ta gaida iyayanta. Bayan ta gaishe su kana tayi beark bayan ta kammala Mama ta dube ta tace, "Hafsat anjima zan aikeki gidan Hajiya tah ki ƙarɓomin saƙo daga can ki gaya mata zaki koma makaranta sai kun gama jarabawa". Tace, "tau Mama Allah ya kaimu ajima lafiya"nan suka cigaba da firar su. Suna cikin fira wayar ta tafara rura,sunan da taga ya baiyana saman screen ɗin yasa da sauri ta saka wayar slient,sai da ta tsinke kana tayi sauri ta mike taje ɗakin ta haɗe da cema Mama tabari tazo Safiyya ce zata gayama sunan wani book wanda zata nemu mata shine za ta je ɗakin ta dubu dan yana cikin jikar ta kuma ta manta sunan shi. Komai Mama bata ce da itaba har ta fice. Tana shiga ɗakin ta ya koma kira,da sauri ta ɗauka haɗe da faɗin "Hayateey kayi haƙuri wallahi muna tare da Mama ne shiyasa ban ɗauka ba" . yadda ta ke maganar kamar tana gaban sa. Yace, "naji amma anjima zaki dawo ko?". Cikin muryar rarrashi tace, "kayi haƙura zuwa Monday na dawo, dan anjima Mama tace zata aikeni shine ma nake sun na kiraka na faɗama kayar da naje?". Ataƙai ce yace, "ban aminta ba kuma anjima nake son ki dawo dan ina buƙatar ki" yana kai ƙarshin zancin ya datse kiran bata ri da yaji me zata ceba. Wayar dake hannuta ta fara kallo dan ita bata ma san me zata cewa Mama ba. Dabara ce ta faɗu mata dan haka ta hau gado tayi kwanciyar ta har lokacin da za'a aikin ta ya yi. Kiran ta Mama ta farayi amma tanaji taki ta karɓa har Mama tagaji ta shigo ɗaki. Tasheta Mama ta farayi dan a tunanin ta bacci take bata san ko idon ta biyu ba,tayi hakan ne dan kada taje aikin da za'ayi mata. Kanta ta ɗago kamar mai bacci gaske Mama tace,"Hafsat ki tashi kije rana tafito sosai kinji". Magana tayi mata cikin muryar marasa lafiya tace, "Mama kiyi hakuri ki aike su Marwan wallahi kaina ke ciyo" ta faɗa haka kamar tayi kuka. Sannu Mama ta fara jeramata haɗi da kawu mata magani dan tasha. Aken da bata zoba kenan sai da Mama takira Abban su Hafsat tace masa yayi mata izine taje wurin Hajiyar ta karɓu saƙo. Aikuwa Mama nafita Hafsat tamiƙe kamar ba itace ke sheiɗa ɗaya-ɗaya ba. Koda Mama ta dawo Hafsat tace taji sauki dan kan ya daina ciyo. Dare nayi ta fara tunanin yadda zata cewa Mama zata tafi makaranta. Dan ya da meta da kira kuma ta rasa yazata cewa Mama. Wanka tayi ta shirya ta kama hanyar ɗakin Mama dan ta gaya mata zata koma makaranta..... *#Vote* *Comment* *Shere* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *SHAFI NA 5📑* *__________📖* Labulen ƙofar ta ya ye kana ta shiga ɗakin. Saman sallaya ta same Mama dan haka ta ƙaraso a hankali ta samu waje ta zauna tana jiran Mama ta shafa. Bayan Mama ta shafa itama Hafsat ta shafa haɗi da gaishe da Mamar ta. Bayan Mana ta amsa sai Hafsat ta ɗagi da kanta ta ce, " Mama yanzu abokiyar karatuna ta kirani tace Malamin mu ya bada wani Asignmen tun Jumu'a bayan fitowarmu kuma yace Monday za'ayi summitng kuma ni ban masani ba sai yanzu kuma yace a makin teat ɗin mu ne, kuma rashin yin sa gareni babbar matsala ce. Sai da ta kai ƙarshin zancin mama ta ɗago ta dubeta kana tace, "Kina nufin yanzu na barki kije?". Kai ta ɗaga ma mama alamar " eh". Sai mama tace, " Tare da Safiya zaku je?". Sai Hafsat tace, " a'a Mama kinsan ba department ɗin mu ɗaya da ita ba". Sai Mama tace, " to gaskiya Hafsat abar wannan tafiya har da safe" har zata koma wata magana sai ga Abban Hafsat ya dawo daga masalaci. Bayan ya shigo ya zauna san gama gaisheshi kana Mama tayi masa bayanin da Hafast tama ta, kuma tafi ɗa masa yadda tace da Hafast . Bayan ta gama yace, " a'a baza mu hanamata zuwaba, kuma kinsan wannan karatun da takeyi yana buƙatar kula sosai dan haka tashi ga kuɗi kije kinji ƴar Abba ". yana faɗa yana dubanta. Sai Mama tace, " Kafison ta tafi?". Yace, "eh haka yafi abunda na ke so shine muyi mata fatan alhairi". Bayan Abba ya bata kuɗi ta ɗau kayan ta tayi musu sallama tafice. Bayan tafiyarta Mma ta dube Abba kamar tayi kuka tace, " yanzu karatun Hafsat bana son shi dan gabana yana yawan faɗuwa akan karatun Hafsat shiyasa yanzu bani da wata natsuwa akanta". Sosai Abba ya yi mata magana akan ta aje wannan maganar gyafe kawai suyi mata fatan alhairi. Tana fita takirashi tace ina yake gata ta tafito. Faɗa mata wurin ya yi , ba ɓata lokaci taje ta sameahi. Tana shiga mitar shiko ya yaja suka tafi. Ti-ti taga ya miƙe yana ta tafiya dan ba hanyar gidansa ce taga ya bi ba, dan haka ta dubeahi tace, Hayati naga sai miƙi ti-ti kake hala ina zamu je?". Batare da ya ɗago ya dubeta ba yace, " Zamfara". " Yanzu da dare nan hayet?". Yace, " eh yanzu nake da ra'ayin zuwa, in bazaki je ba na saukeki". Tace, "a'a kayi haƙuri idan na ɓata ma". Ta faɗi haka ciki da ƙanƙan da kai da tsoro. Bai sake cewa da ita komai ba har suka isa Zamfara. Hotel suka sauka ɗaki ɗaya ya kama musu , bayan sunyi wanka sunci abinci kana ya bata wasu ƙananun kayan bacci ya umarceta da sa su, jiki ta narawa ta saka su waɗanda da su da babu duk ɗaya suke a jikinta. Jikinshi ya jawota ya rungumeta haɗi da shaƙar ƙamshin jikin ta, lokaci ɗaya ya fara romance ɗinta. Hannunsa yasa ya fara shafar duk wani ilahirin sassan jikinta. Sosai take jin daɗin abinda yake mata dan haka ta ba da kai sai yadda ya yayi da ita, sosai ya bata wuya a daren ranar, dan sune basu kwanta ba sai biyar saura na asuba. Kuma asuba nayi ta farka tayi sallah kana tazo tana kwanta. Shima yana gama sallah ya kwanta haɗi da jawo ta jikin sa , romance ɗinta ya fara duk da yanzu bata so amma saboda jiya ba ƙaramar wahala ya bata ba, amma bazata iya ce masa bata so dan kar ransa ya ɓace. Sai bakwai da wani ya barta, kushi ba dan ya gaji ba sai dan meeting ɗin da yake dashi 7:30. Wanka ya yi kana ya yi beark yayi mata sallama ya tafi yace sai ya dawo. A dawo lafiya tayi masa haɗi da addu'a sai kace mijinta😏. Yana fita tayi wanka ta shirya tabi lafiyar gado dan bacci ne a idon ta sosai. Haka suka cigaba da zama garin Zamfara har tsawon kwana biyar. Zaune suke saman kujera ita dashi sai wayarta ta fara kaɗawa, har taso ta ƙi ɗauka kuma sai ta ɗauka, tana karawa kan kunninta ba abinda aka fara ce da ita sai, " kina ina?". Sai Hafsat tace, ina ruwanki da inda nake". Sai Safiyya tace, " to wallahi bari kiji yau zuwa gobe na baki , duk inda kike ki dawo , kuma inba haka ba zanje gida na faɗamusu abunda ake ciki, dan na gaji da ganinki cikin wannan muguwar rayuwa". tana faɗar haka ta datse kiran saboda wani kukan baƙin ciki da yazo mata. Tana kuka tana faɗin, " me Hafsat ta nemi ta nema ta rasa da da zata riƙa bibiyarshi kamar mijinta". Kuka tashiga rairawa kamar ta cire zuciyar ta jefar saboda baƙin ciki kuma ba abinda yafi ƙona mata rai gashi yanzu saura sati ɗaya a fara exmas amma ita Hafsat ba itace gaban taba. Tunda suka gama wayar da safiyya jikinta tane ya yi sanyi sosai kan ta ɗago ta dubeshi dan shima ita yake kallo kana ta buɗe baki tace, Safiyya ce takirani har tana yiminbarazanar zata gayawa su Mama bana schocl, kuma nasan tunda tace zatq faɗa to sai ta faɗa, dan Allah kayi haƙuri mu koma dan nasan halin Abba ko kasheni zai iya yi". Ta faɗi haka hawaye na fita a idonta. Haɗi fuska ya yi haɗi da goge mata hawaye dake fita a idonta yace, " Dan takiraki ta gaya miki haka shine harda wani tada hankali, aikinsan duk bazata faɗa ba saboda tana faɗa za'a dakatar da karatun ku , kuma ai zata fiki jin haushi tunda tafiki son karatun". haka yaci gaba da yi mata faɗa da daɗin baki ƙarshe ma ya umarce ta data kashe wayar ta dan ko an koa kiranta baza'a same taba. Dan yace bazaiyi komai ba sai yagama aikin da ya kawoshi. Tun daga lokacin Safiyya ko ta kira wayar Hafsat kashe take, sosai hankalinta ya ƙara tashi dan har gadin sa taje amma mai gida yace ya yi tafiya , tunda taji haka gaba ɗaya ta rasa natsuwar ta har dai lokacin da Mamar Hafsat ta kirata tace takira wayar Hafsat kashe ko lafiya?. Tace eh mama karatu ne yayi mata yawa dan har saƙo tabank na faɗa muku to nima ban dawo ba saboda hostel nake kwana. Aikuwa Mama Hafsat na jin tare da Safiyya suke ta samu natsuwa kana tayi musu fatan alhairi..... *SUMMY M NA'IGE* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *SHAFI NA 6📑* *__________📖* Bayan ya kammala abunda zai kaishi suka dawo gida da sati ɗaya taneme ya barta dan taje school dan Monday za su fara exams. Yace ta shirya ya kai ta amma kafin ya dawo gida ta tabbatar da tadawo dan baya son yadawo babu abunda zaici. School ɗin ya aje ta kana ya ƙarasa wurin aikin sa. Class ɗin su taje bata jima da zuwa ba aka fara lectura. 2 dai-dai suka gama lectures ďinsu,kuma suna fitowa bata tsaya komai ba ta kama hanyar fita. Har zata fita daga cikin makarantar sai Safiyya ta ganta tana ta sauri,da saura Safiyya tayi ƙarasa gare ta. Mayafin ta ta riƙo,lokacin da take daf da fita school ɗin. Safiyya tace, "ina zakije dakike ta wannan sauri haka?". Kallon sama da ƙasa tayi mata kana tace, "wurin da kika aikeni zan je" tana faɗa tana hararar ta. Sai Safiyya tace, "koma dai me yau ba inda zaki dan Mama na can hankalin ta tashe tana sun ganin ki dan haka yau gida zamuje ta gannki ko tasamu natsuwa". Hafsat tace, "Safiyya har sau uku taki ra sunan ta, bana son kina shiga rayuwa ta Safiyya kirabu dani nayi rayuwata,ki barni rayuwar ki ko tawa? kuma bazan je gidan ba inki haihu da uwarki kije kifaɗa ɗin ina gidan saurayi na". Tana faɗar haka ta kama hanyar fita ta bar Safiyya sake da baki tana kallon ikon Allah. Har zata fice sai ta dawo,gaban Safiyya ta ƙarasu kana tace, "daga yau kada ki kara shiga rayuwa ta dan ni tunda jimawa nafitar dake rayuwa ta dan haka kema ki barni bana son sa idon". Mai adai-daita ta tara kana ta faɗa masa unguwar da zai kaita. ita ko Safiyya gaba ki ɗaya mamaki da tsoro sun da baibaye zuciyar ta,dan gani take kamar ba kai sake Hafsat ke gaya mata wannan maganar ba,amma a ko da yaushe tana wa Hafsat fatar shiriya itada kullihin musulmi. Bayan ta dawo daga school wanka tayi kana ta gabatar da sallah sannan tazo ta fara gyaran gida,tana kammalawa ta ɗura sanwa. Saura ƙiris ta kammala sai gashi yadawo,aikuwa tunda taji horn ɗin motar sa gaban ta ya bada dummmm,saboda bata kammala girgin taba kuma tasan halin sa sarai baya sun jira. Tana cikin wannan tunani tafara jin knocking ɗinsa. Da sauri taje ta buɗe masa ƙofa dan kar ta ƙara ma kanta wani laifi. Ƙarɓar jakar dake hannun sa tayi haɗi dayi masa sannu da zuwa. Karɓawa yayi haɗi da ƙarasuwa daga ciki. Ruwan wanka ta haɗa masa,bayan yayi wanka ya fito, ta tayashi shiri,bayan ya kammala shirinsa parlour ya fito dan yaci abinci dan ya kwasu yunwa yau. Komai bai gani ba a dinning, dan haka ya ƙwala mata kira,ita ko tana can tana sauri taga komai ya kammala amma ina dan tana cikin haka taji yana kiran ta. Da hanzari tazo gareshi,aikuwa tunda ta ƙarasu ya jefeta da wani kallo wanda yasa cikin ta juyawa lokaci ɗaya. Tambayar ta ya farayi yace, "ina abinci na?". Jikin tane ya fara karkarwa tace, "kayi haƙuri nakusa kammalawa". Sai da yajefe ta dawani kallo kana yace, "sai yanzu kika dawo kenan?". Kai ta fara girgiza masa tace, "a'a muna gama lectures na dawo wallahi ko ina banje ba". Tsawa ya da kamata haɗe da cewa karya kikeyi kin dai tsaya iskancin kine shiya sa baki dawo ba" nan ya dinga cin zarafin ta har da kukan ta tana bashi haƙuri amma yaƙi ko saurarin ta,daga ƙarshe ma key ɗin motar sa ya ɗauka yafi ce a gidan. Har ya fita ya dawo ya ƙwala mata kira, da sauri tafito daga kiching haɗi da durƙusawa gaban sa. Tun bata kai da durƙusawa ba yace ta haɗa kayan ta tabar masa gidan sa. Aikuwa yana faɗar haka da sauri ta faɗa jikinsa tana bashi haƙura,amma ina baya ko saurarin ta dan da ƙarfi yajaye ta jikin sa ya kifeta da wani azaftaccin mari har guda biyu kana yace, "kuma wallahi kafin na dawo kinbar gidan nan tunda ba na ubanki neba" yana faɗar haka ya ficewar sa yana huci". Kuka takeyi kamar ranta zaifita dan ita ba komai yafi ƙona mata raiba irin yadda yace tabar masa gida, to ina zata je?. Wani tunani ya faɗu mata arai aikuwa da sauri ta miƙe daga durkushin da take ta koma kiching taci gaba da aikin ta. Bayan ta kammala girki, sosai ta fara gyaran gida,bayan ta kammala tasaka turare mai ƙamshin gaske wanda lokaci ɗaya yasa gida yabada wani ƙamshi mai sanyaya zuciya. Toilet taje tayi wanka,bayan ta fito ta shafe jikin ta da ma yukka masu ƙamshi haɗi da hummara ta musamman,dressing ɗin english wears tayi masa wanda tasan yafi so sosai. Tana gamawa ta ɗauko wasu turarukka ta feshe jikin ta dasu. Tarigi ya ta ɗauru alwala,sallah magarb da isha'i ta gabatar kana ta fito parlour ta zauna zaman dawowar sa. Batayi minti biyar da zama ba sai ga horn ɗin motar sa. Aikuwa da sauri ta ƙara feshi jikin ta da turare haɗi da dauko lollipop tasaka a baki, ta fara tsutsu sai kace wata ƴar yarinya. Bai ma tsaya wani knocking ba yasa key ya buɗe ƙofar. Tsaye ya ganta tana masa murmushi haɗi dayi masa wani kallo mai ciki da so da ƙauna. Jikin sa tafaɗa haɗi da faɗin "My Hubby nah, sannu da zuwa". Har ya buɗa baki yayi magana sai tayi sauri ta haɗa bakin sa da nata tana shayar da shi lolopop ɗin da ke bakin sa. Aikuwa tuni jikinsa ya karɓi saƙon da take bashi haɗi da shaƙar ƙamshin da ke fita a jikin ta. Bare abu ga ma abuci son ƙamshi,sosai ta mantar dashi fushin da yakeyi da ita,tsayowar ce ta gagaresu dan haka cak ya ɗauke ta zowa bedroom ɗinshi. Sai da komai ya lafa kana ya jawuta jikin sa sosai kana yafara magana ahankali yace, "My love jibi ne ta fiyar dan haka ki kasan ce cikin shiri dan tafiyar safe zamuyi". Gabanta ne ya faɗi dan ita har ta manta da wata tafi ashe tafiyar na nan kuma gashi Monday za su fara exmas. Jikin ta asanyaye tace, "Allah ya kaimu jibi lafiya". "Ameen" yace da ita haɗi da kai bakin shi da nata ya fara kissing ɗin ta. Duk abunda yake mata bata wani jin daɗin sa saboda tunda yayi maganar tafiyar jikin ta yayi sanyi dan tunani take anya zata bishi tabar exmas ɗinta?kum gashi aski yazo gaban goshi dan daf take da ta kammala degree ta afannin gaenacology kuma da bata ci wannan exmas ba zasu iya withdraw ďinta kuma gashi tana da carryover har guda biyu. Suna cikin haka tace, "a'a gaskiya bazan jeba". Ahankali yace, "mikika ce?". Tace, "aa ba da kai naki ba". ************* Yau takama Monday kuma yau zasuyi tafi kuma yau zasuyi exmas..... Wani zatayi tafiya ko exmas...... *__________📖* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~ *SHAFI NA 7📑* *__________📖* Yana gama shiri yafito dumin su tafi dan baya sun suyi rana. Kiran ta ya farayi,ita ko tana can tana tunani ta tafi ko karta tafi,rasa me zatayi tayi,gashi tana tsoro rashin yin exmas ɗinta, kuma tana tsoron ɓacin ransa. Kiran da taji yana mata yasa gabanta dukan uku-uku,alamun zai shigo ɗaki data ke ciki taji dan haka da sauri ta fara haɗa kayan ta cikin jikar da zata tafi da ita. Koda ya shigo har tasa tufafin ta tana yafa mayafin ta,amma fuskar ta a ɗaure kamar tayi kuka. Magana yayi mata yace, "kefa nake jira". Tace,"nashirya mutafi" tafaɗa haka kamar tayi kuka. Fitowa tayi ɗauke da jika a hannunta,jikin ta a sanyaye ta rasa ya zatayi,tana cikin haka taji yace, "muje zan kulle ƙofa". Fita tayi ya kulle ƙofa kana ya shiga mota ya tada. Gabanta ne ya tsanan ta faɗuwa sosai, lokaci ɗaya wasu hawaye suka fara fita a idon ta. Magana yayi mata yace ta shigo sutafi. Kamar bata ji shiba tayi sai da yayi magana cikin faɗa-faɗa kana tabuɗe motar tashiga tana mai saka kuka kamar wani yayi mata dole sai taje😏. Aikuwa yana tada mota kukan da takeyi ya tsanan ta. Dubanta yayi kana yace, "mi akayi miki da zaki saka min kuka,ko tafiyar ce bazakiyi ba ne?". Kanta ta fara girgiza masa kana tace, "a'a kayi haƙuri na daina". Yace, "to ki shafe hawayin ki dan bana son jin kuka kinji ko". Hawayen ta tashafe haɗi da cemasa "to". Tunda suka kama hanyar tafiya gaba kiɗaya hankalin ta atashe yake, dan tunda take dashi bata taɓa jin irin wannan tashi hankali ba kamar na yau,amma kuma bazata iya ce masa baza ta jeba,har suka fara fita daga cikin gari ba wanda ya cema ɗan uwansa komai. Saura minti biyar afara exmas sai Safiyya tazo bakin class ɗinsu taga ko Hafsat tazo,aikuwa tana ƙarasuwa taga class ďin kowa yazo amma sit ɗin Hafsat wayam,gaban Safiyya ne ya bada dummm da

Chapter 2 of 13