Share this page
da ɗaure mata fuska,dan duk ihu da take ba mai jinta har suka tada mota suka bar makaranta,Basu tsaya da ita ko ina ba sai wani gidan. Tunda sukayi packing ɗin motar gaban ta ke famar dukan uku-uku,ina ba ambatun Allah ba ba abinda takeyi a ranta,tanaji suka ɓuɗe marfin motar suka fitar da ita,sai da suka isa da ita parlour gida kana suka kwance mata fuska haɗe da buɗe mata baki. Aikuwa tana ɗago idonta wazata gani inba Anwar ba,wani uban zabura da tayi kamar bata ɗauke da komai ajikin ta. Nunisa da ɗan yatsa ta farayi har tasamu ta ɓuɗa baki tace, "Anwar dama kaine kasa a ɗaukoni?minayi ma Anwar? mikake nema dani?dan Allah kabarni hakanan na huta,wallahi ina cikin gararin rayuwa,wadda sabida kai na faɗa acikin ta,duk abinda kayimin baiyi isheka ba sai ka kasheni ne!to gani kashini,macuci azalumin,kayimin ciki kuma karabarni,sanidiyar ka nabar iyayena"....ai tun bata kai da rufe baki ba ya wanke ta da mari har guda biyu,wanda lokaci ɗaya ta rasa inda kanta yake. Nunin ta ya farayi da ɗan yatsa kana yace, "waye sa'arki da zaki riƙa buɗe baki kina faɗi masa magana sun ranki ehh?Narabaki da iyayenki kuma yanzu zan rabaki da wadda kika fiso dan haka wallahi sai kinyi dana sanin faɗamin maganar daki kayi" ..yana faɗa yana nuninta da ɗan yatsa. Waɗanda suka kamuta ya duba kana yace,"koje ko nemunin Safiyya duk inda take,kuma nabaku zowa nan da gobe"....ai tun bai kai da rufe baki ba,cikin hanzari da kaɗuwa da maganar sa tafaɗa jikin sa tana faɗin,"Anwar dan Allah kada kayi min haka wallahi na yarda duk abin da kakeso zamakashi amma kada kataɓa lafiyar Safiyya,dan Allah na ruƙeka"....tana faɗa tana wani kuka mai kunar zuciya. Har yaran nasa zasu tafi dan cika umarinin da ya basu sai kuma ya tsaida su yace suji rashi falo zasuyi magana da Hafsat. Bayan sunfita ne ya dubeta kana yace, "idan har baki son nataɓa lafiyar Safiyya to sai kin yarda da abinda zance,amma idan baki yarda ba wallahi ba makawa sai nasa anɗauko min ita gobe,amma idan kinyar da to ba damuwa". Kallon sa tayi kana tace, "inaji kafaɗa idan zaniya ɗan". Yace, "dole ma ki iya,kuma daga yau zaki zauna gidan nan har tsawun sati ɗaya,kuma duk abinda kikasan kina min wancan lokaci zakiyi min shi a yanzu, dan haka idan har kin yarda to amma idan baki yarda ba sai nasa su ɗaukomin ita gobe". Idontane ya cigaba da fitar da hawaye kana tace, "dan Allah kayi haƙuri Anwar kabarni na koma gida, na yarda sai na riƙa zowa har sati ya cika"....tun bata rufe bakin taba ya kwalama yaransa kira yace gobe su ɗauko mishi Safiyya. Cikin hanzari ta faɗa jikin haɗi da faɗin, "na yarda Anwar duk abinda kakeso zan maka amma kada kataɓa lafiyar Safiyya,amma kasani yanzu bani da wata isassar lafiyar da zan riƙa abinda nake maka a da,dan kasan cikin dake jikina baya bani lafiya"....tana faɗa tana share hayen ta. Wani kallo yake jifa ta dashi kana yace, "yanzu kina nufi har yanzu biki zobar da wannan cikin ba? to bari kiji daki zobar da karki zobar duk ɗaya suke a wajena dan sai kinyi abinda nace kiyi"...yana faɗin haka ya kama hanyar bedroom ɗinsa batare da yasake magana. Itako faɗuwa tayi saman kujerar parlour ta fara rera kuka kamar ranta zai fita,tana kuka tana ruƙun Allah ya kawo mata mafita. Koda suka kawo bakin gate ɗin makaranta tsit yake sai ɗai-ɗaikun mutane dake wucewa amma ba alamar wata bus. Cikin makaranta sukayi packing ɗin motar su,cikin hanzari Safiyya ta fito ta nufe class ɗinsu,koda ta ƙarasa ba kowa aciki dan haka da sauri ta wuce hostel wajan abukan karatunta,abukiyar karatun ta Maryam ta fara cin karu da ita, Safiyya tace, "yauwa Maryam, nace Hafsat tashigo makaran ta yau kowa?". Sai Maryam tace, "eh ta shigo dan kusa dini ma ta zauna har aka gama luctura". Safiyya tace, "wallahi ita nake nema dan har yanzu bata koma gida ba". "Aikuwa ana gama lecture tace bari tayi saura tashiga bus dan bata son magirb tayi mata kan hanya"...cewar Maryam. Har Safiyya zata wuce sai ga Saratu ko ita abukiyar karatun suce, har zata wuce taji suna zanci Hafsat dan haka ta ƙarasu garesu tace, "Safiyya Hafsat kam tajima da tafiya dan gaban idona ma tashiga wata mota baƙa ita da wata yarinya,amma ban san yariyar ba, ina dai yawan gani yarinyar tare da Hajara". Gaban Safiyya ne ya bada dummmmm,lokaci guda jikin Safiyya yayi sanyi,dan da ƙyar tasamu ta ɓuɗa baki tace musu, "nagode bari na koma gida wata ƙila ta isa"....tana faɗar haka ta kama hanyar da zata kaita wajan da tabar Baban ta. Tana isa wajan sa ta ɓuɗe mota tashiga tana mai faɗin, "Baba muje ƙila ta isa gida,dan antabbartarmin da tashiga mota". Tana faɗin haka bai tsaya wani jiraba ya tada mota suka bar makarantar. Koda suka isa gida akace bata dawo ba,sosai hankalin Baban Safiyya ya tashi,irin tashin hankalin da Safiyya taga yashiga ne dan haka taje wajan da yake tsaye tace, Baba ka daina tada hankalinka akan ɓatan Hafsat,Hafsat bata ɓace ba, ta dai je gidan saurayin ta wanda yayi mata ciki,abinda yasa nace haka sabida ko jiya da dare bayan mun kwanta, dan ita atunanin ta bacci nake, inajin abinda tace dashi,naso nayi mata magana tunjiya amma na fasa nace sai naga tasake wayar dashi....sai da ta numfasa tace, zan yarda wancan lokacin asiri yayi mata amma yanzu nasan bawani asiri atare da ita.....nan dai tagaya musu asirin da Anwar yayi mata a wancan lokaci. Baban Safiyya ya kalle Safiyya jikin sa asanyaye yace, "zaki iya gane gidan nasa kikai ni gobe?". Shuru tayi bata bashi amsaba,kafin ta buɗa baki tayi magan Yace, "dole gobe ki kaini gidan, dan bazan iya barin ta awajansa ba,amana na ɗauko ta fa,dan haka ko ina Hafsat take sai na nemuta,dan ban sani ba ko yanzu asiri ne yayi mata"....yana faɗin haka ya fice daga gidan gabaki ɗaya. Kukan datayi ne har ya saukar mata da zazzaɓi mai tsanani dan koda yafito daga bedroom ɗinsa kwance yasame ta saman kujera jikin ta sai famar karkarwa yake saboda zazzaɓi. Hankali ya ƙarasu gareta,hannunsa ya kai jikinta lokaci ɗaya ya ɗauke yana mai faɗin, meke damun ki hala naji jikin ki da zafi?". Komai bata ce dashi ba sabida ko bakinta ta ga-gare ɓuɗewa bare tayi magana. Dayaga alamun bazatayi magana ba yace, "wallahi ba ruwana da wani zazzaɓi, duk baki tashi kika fara aikin ki ba wallahi gobe sai anzomin da Safiyya"....aikuwa tana jin furicin sa,da sauri ta zabura ta miƙi zaune haɗi da faɗin, "nashirya mi zanyi maka yanzu"....abinda tayi ne ya bashi dariya dan haka ba san lokacin da yayi dariya ba... *#Vote* *Comment* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 16📑* *__________*📖 Nuni ya yi mata da ta zauna saman cinyar sa, ba musu ko ta tashi ta zauna,tana zama ya sanya wata sassanyar ajiyar zuciya,ɓsabida jin fatar shi da ta ta sun haɗu waje ɗaya, shi kansa ya san yana son Hafsat so ba nawasa ba amma a zahirin gaskiya ba za'iya auren ta ba duk son daya kemata,kuma ba dan komai ba sabida yariga da yasanta ƴa mace,kuma da ta yarda zata zubar da cikin wata ƙila ya yarda ya aure ta. Jikinsa ya ƙara sanya ta, kana ya fara shaƙar ƙamshin dake fita jikinta, hannun sa ya kai saman sassan jikin ta ya fara shafar ta, lokaci ɗaya yaji wani sanye ya mamaye zuciyar sa,sosai yake son taraiya da Hafsat ba dan komai ba sai dan yadda ya ke samun natsuwa da ita sose. Ita kowa tunda taji ta saman jikin sa wasu hawaye masu zafi suka fara fita a idon ta,uwa uba lokacin da ya ɗora hannusa saman jikin ta,jikin ta ne ya fara karkarwa sabida baƙin cikin ɗaura hannusa da ya yi kuma ga ciyo da ke ɗawai niya da ita. Bukinsa ya fara ƙoƙarin ɗaurawa saman nata, lokaci ɗaya ta fara ka-karin amai haɗi da sauka saman jikinsa, Wani baƙin ciki ne ya rufe shi bai san lokacin da ya kifeta da mari ba kana yace, "Wallahi Hafsat muddin ki na buƙatar kanki da lafiya ki bi abinda nake so, dan wallahi ko aman jini ki kai sai nayi yarda nake so dake ko nayi miki abinda har ki mutu bazaki mantani ba,dan haka maza kije ki gyara jikin ki ki sameni bedroom yanzu nan". Yana faɗa yana kama hanyar da zata sada shi bedroom. Sanin halinsa da tayi dan haka ta tashi taje ta gyara jikin ta kana ta sameshi a bedroom ɗin sa. Koda ta shiga ɗakin yana waya yana faɗin, "My love kin san na kusa dawowa kuwa?,dan haka ki fara shirin, dan kin san dana dawo ba jimawa za'ayi aure na dake". Daya ke hands-free yasa dan haka tana jin dun abinda suke fada. tace, "hmm My dear har kasa naji ƙunya". Murmushi ya yi kana yace, "kada ki damu ba jimawa zan cire wannan kunyar take dan ni tana cutar dani". Mumushi tayi mai ɗan sauti kana tace, "yaushe zaka dawo ina son na kasance cikin shiri?". Yace,"a'a bazan faɗa ba akoda yaushe dai ki kasance cikin shiri kinji tawa". Tace "to tace dashi". Haka dai suka cigaba da waya cikin so da ƙaunar junan su. Bayan sun kammala wayar ne ya kai duban sa ga Hafsat dake tsaye kamar wadda aka da sa kana yace, "kinyi min tsaye akai, ki ƙaraso mana". Jikin ta a sanyaye ta ƙaraso gareshi, Tana ƙarasowa ya jawuta jikinsa haɗi da sanya bakin sa cikin nata,to fah daga nan labari ya sauya. Washe gari tunda safe Baban Safiyya yace suje ta gwada masa gidan Anwar, hijab ɗinta ta saka batare da tayi ko beark ba suka kama hanyar gidan Anwar. Sun sha wuya kafin ta gano gidan dan har za su juyo su dawo gida sai tagane gida,amma kuma ganin gidan da sukayi baiyi affani ba dan gidan kulle yake kuma ko da suka tambaya akace mai gidan ya jima da barin garin. Sosai hankalin Baban Safiyya ya tashi na rashin ganin Hafsat, dan koda suka dawo gida ba inda ba suneme ta ba amma basu ganta ba,dan haka Baban Safiyya ya yanke shawarar yaje ya sanar da Baban Hafsat abinda ake ciki duk da yasan bai rasa jin ɓatan Hafsat a unguwa amma gwanda yaje ya ƙara sanar dashi koda ya sani. Da yamma bayan ya dawo daga kasuwa ya shirya yaje wajan Baban Hafsat. Koda yaje wajan Baban Hafsat,bayan sun gaisa kana Baban Safiyya ya faɗa masa abinda ke faruwa gami da ɓatan Hafsat. Sai da Baban Hafsat ya numfasa kana yace, "Alhaji Aliyu to miyasa zaka tare ni da wannan magana bayan tun wancan lokaci na shaida maka na fitar da Hafsat daga cikin ƴaƴana,amma kuma yanzu kazomin da wannan zanci,dan haka bana son wannan zanci dan Allah daga yau kada ka ƙara haɗani da ita". Har Baban Safiyya zaiyi magana sai Baban Hafsat yace, "a'a kada kasoma, kai kaji zaka iya riƙunta kuma yanzu tace bata so duniya take so tabi dan haka ka kyale ta ga duniyar nan ta ishe ta riga da wando". Yana faɗar haka ya shigewar sa gida ransa a ɓace. Haka baban Safiyya ya dawo gida jikinsa a sanyaye kamar ba lakka ajikinsa. Haka dai suka canye kwana biyu suna neman ta amma basu ganta ba,daga baya sukayi haƙuri suka cigaba da addu'a Allah ya bayya nata. Tunda sallah asuba da ta farka tayi wanka haɗi da ɗuru alwala tayi raka atanin fajar kana tayi sallah asuba,tajima zaune tana istigifari da hailala da addu'a nema tsari daga sharin mutum da aljan. Bakwai saura ya farka haɗi da wata irin miki,gyafin da take ya kalla kana ya buɗa baki yace, "waya baki umarnin ki tashi daga nan ehh?". Ko kanta bata ɗago daga ƙasa ba tace, "lokaci sallah ne ya bani umarnin tashi". Aikuwa cikin hanzari ya sauka daga kan gadon ya ƙaraso gaban ta yana nunin ta da ɗan yatsa kana yace,"saki faɗin abinda kika ce?". Irin yadda yake mata maganar ko ita ta tsora ta sosai dan haka bata ce komai ba taci gaba da lazumin ta amma gaban ta sai dukan uku-uku yake. Magana yayi mata cikin tsawa yace taje ta haɗa masa beark,aikuwa ba musu ta tashi taje kitchen ta fara haɗa masa abinda yake so. Tana tashi yabita da kallo haɗi dayi mata kwafa kana yace,"zanyi maganin ki,nan ba da jimawa ba". Yana faɗin haka ya kama hanyar da zata sadashi da toilet. Ita ko badan komai ta tashi tashiga kitchen ba sai dan kar ya hanata zowa makaranta. Agurguje yayi wanka ya fito dan so yake yaje gun Hajara ta rakashi wajan malamin da yayi masa aiki akan Hafsat a wancan lokaci dan ko yanzu so yake ayi masa aki a kanta,dan yaga yanzu sai wata gardama take mishi idan yace tayi masa abu saɓanin da. Koda ya zo parlour tana kitchen bata ƙarasa aiki ba dan haka ya sameta kitchen ɗin yace, "ya fita yadawo yanzu". Bai jira cewar taba yafita yana ta sauri kamar wanda akayi ma kyata zata tsere masa. Key yayi ma motar sa, kana ya kama hanyar da zata sada shi da layin buge,dai-dai kan kwanar gidan yayi packing ɗin motar sa. Yana fitowa a mota ba abinda ya fara cin karo dashi ina ba condoms ba, tsaki yayi kana yace, "shiya bana sun zuwa wannan unguwar sabida haka". Kwanar ya shiga,aikuwa yana shiga sai ga ƴan mata da samari sai fitowa suke cikin ɗakunan da suka kwana,wasu da alamu ma matan aure ne dan ga sunan har da goyon su,abin dai sai wanda yagani,yana ƙara tafiya sai yaga wata yarinya ita da wani saurayi za su shiga wani ɗaki, kuma daka ganta ita ƴar makaran tace dan ga kayan makaranta nan ajikin ta na secondary school, ɗaki suka buɗe suka shiga kana suka rufe ƙofa. Gab da zai shiga ɗakin Hajara yaga wasu samari su biyu sai tunkuɗar wata yarinya suke suna faɗin, "wallahi yau sai kin bari muna ɗaki tunda ba ubanki ne ya bamu kuɗin da zamu biya ba". Ita ko sai turjiya take wai ba inda zata je. Da suka ga zata ɓata musu lokaci suka tisa ƙyayar ta gaba suna faɗin,"shigiya jarababba wallahi mungaji dake dan haka yau sai kin bar muna ɗakin mu". Yarinya ta sosai dan idan ka ganta bazaka ce tasan wani abu ɗa namiji ba,tsaki yayi haɗi da ƙarasawa ɗakin Hajara. Yana zuwa ba Knocking ba komai yatura ƙofar ɗakin ya shiga. Cikin sa'a koda ya shiga ba kowa aciki dan ko ita tana toilet tana wanka,koshi dan yaji motsin ruwa ne ya tabbatar da haka. Zama yayi sama katifar dake ya she a ɗakin yana jiran ta. Bai jima da zaman ba sai gata tafito daga ita sai wani ƙaramin towel da bai rufe cinyar taba. Bata ma lura dashi ba sai da yayi gyaran murya kana ta san da zaman sa. Aikuwa suna haɗa ido dashi wani sanyi daɗi ne ya ziyarci zuciyar ta lokaci ɗaya,dan haka bata san lokacin da ta faɗa jikin sa ba. Ƙoƙarin raba ta da jikinsa ya fara amma sai ya tuna da akin da zatayi masa dan haka ya kyale ta,jikin sa ta fara shafa duk da baya so amma abinda ya keson tayi masa ya hana ya dakatar da ita. Ita ko da taga bai da katar da itaba yasa ta kai bakin ta zuwa nasa ta fara kissing ɗinsa,ba yadda ya iya haka yabiye mata har suka samu biyan buƙata kana ya jawo ta jikin sa haɗi da kai mata kiss a baki kana yace, "My dear na,ina so ki kaini wajan malamin da ya taɓa yimin akin akan Hafsat".....ai tun bai rufe baki ba ta ɗago kanta da sauri ta dube isa kana tace, " nifa bana sun kana min maganar ta dan a rayuwa ba ƴar da na tsana kamar ta". Da ƙyar dai yasha kanta ta yarda zata kai shi amma sai laraba da ƙarfe uku na dare yazo su tafi dan lokaci ne ake zowa wajan malamin. Yace, "to sai yazo". Yana faɗa yatashi ya shiga toilet yayi wanka,jikin sa ta goge masa haɗi da tayashi sanya kayan sa. Har mota tarakashi gab da zai shiga mota ya juyo ya kalle ta kana yace, "Hajara yanzu shikenan kin bar hostel kin dawo nan dazama ko". murmushi tayi haɗi da faɗin,"sai mun haɗu ko". tana faɗar haka ta wuce ta barsa batare da taji mi zai ce ba. Key yayiwa motar sa kana ya dawo gida, koda ya shigo zaune ya same ta tashirya tana zaman jiran dawowar sa. Kallon ta yayi yace, "ina beark yunwa nakeji". "yana dining". Tafaɗa haka ataƙaice. Sai da tabari yagama beark tazo tace mishi makarnta take sun zuwa sabida lecture ne da ita ƙarfe goma. Wani kallo yabita dashi kana yace, "bawani makaranta so dai kike ki tsere,amma kisani bana gudun ki gudu dan na san da kanki zaki dawo gareni, kana yace zaki iya tafiya". Yana faɗin haka takama hanyar fati,har zata ɓuɗe ƙofa ya dakatar da ita yace ta bari yazo ya kaita da kansa kuma zai jiri da tagama abinda take ta dawo in kuma ba haka tasan sauran. Ba musu ta tsaya har ya kammala abinda yake yazo ya kaita makaranta. Da shigar ta school bata tsaya ko ina ba sai office ɗin shugaban makaran ta. shugaban makartar ya bata wata takarda wadda akayi ma signing yace taje ta kaima iyayen ta su sa hannu,idan sun sa sai ta kawo dan wani sati za suwu ce abuja daga can kuma kowace a bata ƙasar da zata je karatu. Bayan ta fito ɗakin shugaban makaran ta tashi ga class ɗinsu,bayan sun gama lecture tana sauri ta fito ne sai ta haɗu da ƙawar ta Maryam. Hafsat bata ma ganta ba sai Maryam tace, "Hafsat ran jumu'a yaushe kika koma gida dan naga Safiyya sai nemanki take?". Murmushi Hafsat ta ƙaƙalo kana tace,"tana fita niko na koma". Sai Maryam tace, "gaskiya Hafsat Safiyya na son ki da yawa kinga yarda tabi tarikice kuwa". Mumushi Hafsat tayi haɗi da cewa, "bari na wuce sai gobe idan na shigo". Tana faɗar haka tafice batare da ta tsaya jin me zata ce ba. Da sauri take tafi har tafita daga makarantar, bakin gate ta ganshi yana jiran ta dan haka bata tsaya komai ba tashiga motar sa suka wuce. Tana wucewa Safiyya na fitowa daga class ɗinsu,Maryam tagani zata wuce hostel dan haka da sauri taje gare ta tayi mata magana. Juyuwa Maryam tayi haɗi da yimata murmushi kana tace, "Safiyya Hafsat kike nema ne hala". Sai tace,"eh wallahi har yanzu bamu ganta ba". Tace, "yanzu fah naga Hafsat kuma tare muke har aka gama lecture". Safiyya tace, "yanzu!". Ta faɗa haɗi da zari ido. Suna cikin wannan maganar sai ga ƙawar su Saratu tazo tace, "nima naga Hafsat yanzu bakin gate tashiga wata mota". Wani baƙin ciki ne ya turnuƙata,tace kena Hafsat su ta rainama hankali tana gidan saurayin ta. Tayi wannan maganar a zuciyar ta. Kallon su tayi tace, "oky nagode sai anjima". Tana faɗar haka takama hanyar fita makaranta,sosai ran ta ya ɓace wato Hafsat suta mayar ƴan isaka wanɗanda basu da aikin yi, to daga yau ba mai koma shiga harkar ta inta iya ta tabbata tare dashi. Gida ta koma dan ko lecture da zatayi bata tsayayi ba sabida ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba. Cikin sa'a koda ta isa gida Baban ta bai fita ba,bayan ta zauna sai Mamar ta ce, "har kin dawo ne?". Sai tace, "eh Mama". Sai ta kalle Baban ta da idon ta da sukayi ja-jir tace, "Baba Hafsat fa bata ɓata ba"......nan dai ta faɗa musu abinda tasani. Ko Baban Safiyya ranshi ba ƙaramin ɓaci yayi ba amma bai ce komai ba sai Allah kashirya. Mama ko inda take fita ba nan take sauka ba kuma tace wallahi ko Hafsat tadawo baza ta zauna gidan ba. Ko Yayan Safiyya shima yayi faɗa kamar ya shaƙo Safiyya tunda itace mafarin zuwan ta gidan. Tunda Hafsat tashiga makaranta duk abinda take akan idon sa har maganar da sukayi da Maryam,abin da kwai bai sani ba shine shigar ta office ɗin shugaban makaranta. haka ya dawo da ita gidan sa ba abinda take masa sai aikin bauta amma yana kai ta makaran ta tayi abin da zatayi ya mai data har akazo darin da za su je wajan malamin su shi da Hajara. Tun shabiyun dare ya fara jin cikin sa na murɗawa har akazo lokacin da sukayi yazo sutafi,kuma lokacin ne ma cikin nasa ya fara yimasa wata murɗa wada yasa yafita haiya cinsa lokaci ɗaya. Ita ko bata masan abinda ake ciki ba sai gab da asuba tana tashi ta ganshi cikin wannan halin sosai hankalin ta ya tashi dan haka cikin hanzari ta ɗauko wayar sa,kuma sai tara waza ta kira tunda bata san kowa nasa ba. Har aka gama sallah asuba tarasa ya zatayi sai can ta tuna da akwai mai gadi gida,dan haka da gudu taje ta sanar da mai gadi abin da ke faru,aikuwa mai gadi na shiga cikin gidan ita ko ta lallaɓa ta ɗau kayan ta na makaran ta ta gudu. Cikin sa'a tana fita tasamu dan acaɓa ta faɗa masa suna unguwar su suka kama hanya..... *#Vote* *Comment* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 17📑* *__________*📃 Bakin ƙofar gidan tace ya sauke ta, kuɗi tabashi haɗi dayi masa godiya,dan ƙuɗin da ta bashi sunfi hakanan amma ya amsa baice da ita komai ba, gidan ta kaman hanyar shiga har ta shigar da ƙafar ta ɗaya sai Yayan Safiyya Abbas yazo da sauri ya tare ƙofa haɗi da antayamata wani kallo kana yace,"wallahi ba inda zaki shiga dan ba gidan ubanki bane, sai da kika gama lalacin ki zaki ɗauko wasu shegun ƙafafunki kice kizo gidan ubanki ko?, To barikiji tun wuri ki kama gabanki tun ban illatakiba". Haƙuri ta fara bashi tace, "wallahi Yaya ba inda naje sune suka saceni"....tun bata rufe baki ba ya wanke ta da wani mari wanda yasa ƙiris kaɗan ta kai ƙasa. Suna cikin haka sai ga Mama ta fito taga wake musu hayaniya bakin ƙofar gida. Hafsat tagani tana ƙoƙarin tashigo shiko Abbas ya hanata shigowa,aikuwa da sauri Mama ta ƙarasa wurin tana kunfar baki tace, "wallahi baki isa kishigo gidannan ba,tunda ba ubanki ne ya gina munashi ba". Roƙun Mama Hafsat tafariyi amma Mama taƙi koda saurarin ta,daga ƙarshe ma Mama komawa tayi gida ta ɗauko mata kayan ta ta jefomata su waja. Mazan dake zaune bakin ƙofar gidane suka taso suna ba Mama haƙuri amma ko kallo basu ishetaba,kuma gashi Baban Safiyya bayanan yayi tafiya tun jiya,kuma Safiyya ma batanan jiya gidan gwaggon ta ta kwana. Mutanin dake wajan da suka ga Mama taki haƙura ita da yaranta sai ɗaya daga cikinsu ya dube Hafsat kana yace,"kinga tunda sunce baziki shigar musu gidaba to kije ki koma gidan iyayenki zaifimiki".....tun bai rufe bakiba sai ga Ammar ƙanin ta yazo wajan,da sauri ya ƙarasa gareta yana faɗin,"Aunty daina kuka zo muje gida kinji,ai kema kinada gidan uba dan ba shegiya ceke ba". Kai ta fara girgiza masa kana tace, "a'a Ammar kaji ne bazanje ba"....jikar kayanta ya ɗauka haɗi da jan hannunta yace dole sai sun tafi,ba yadda ta iya haka suka tafi gidansu. Suna isa gidan har zasu shiga sai ga Baban ta ya fito domin ya tafi wajan aiki sai yayi arba da su,wani kallo yayiwa Ammar shida yake riƙi da hannuta da jikar ta kana yace, "wazan gani a gidana?, wallahi muddin kana son kankai da lafiya kabata kayan ta ta ɓacemin da gani".....tun bai rufe bakinsa ba ta durƙusa gabansa tana kuka tace, "Baba dan Allah kayimin haƙuri wallahi ba lafina bane dan Allah Abba ka koma bani wata dama".....wata uwar tsawa ya daka mata wadda yasa ta haɗe sauran maganar da zata faɗa bata shirya ba. Tswar da yayi ne yasa Ummar Hafsat fitowa bata shirya ba. Hafsat tagani durƙushe da ƙasa ita da Ammar suna ba Baba haƙuri,da sauri ta ƙaraso garesu kana tace, "Hafsat lafiya waya taɓamin ke"....tsawa Abban Hafsat yayi mata haɗi da yimata nuni da ta koma cikin gida. Gabansa tafaɗi tana kuka tana faɗi, "dan Allah Abban Hafsat ki barmin ƴata "......kallon da yayi mata ne haɗi da wata tswa wadda tasa ta komawa cikin gida bata shirya ba. Yana ganin Ummar Hafsat ta koma gida yayi ma Ammar nuni da yashiga gida,ba musu ko yashiga ita ko Hafsat ya nuna mata hanya kana yace, "tunda duniya kike so to gaki gata".. ...yana faɗar haka ya maida ƙofar gida ya rufe yabar Hafsat durkushe da

Chapter 6 of 13