Share this page
kama waje kin zauna baki damu da kowa ba shima haka, wallahi kuntafka kuskure babba, amma muna ƙara godiya ga Allah da har ya nuna muku dai-dai". Kuka Ummar Hafsat keyi kamar ranta zaifita. Kwanta uku cin garin sai ga Abban Hafsat ya zo, aikuwa shima kansa yasha faɗa a wajan iyayenshi daga baya suka haƙura suka karɓeshi, bayan komai ya lafa shima ya faɗama ƴan uwansa abinda ke faruwa, sose mahaifinshi yayi masa faɗa kana yace ba komai ya ja masa haka ba sai katse zumunci da sukayi. Da yake garin su ɗaya da Umma, bayan komai ya ɗan dai-dai ta tsakanin shi da iyayenshi kana yaje can wajan iyayen Ummar Hafsat suma suka ɗura daga wajan da iyayenshi suka tsaya. Bayan kwana biyu da zuwan sa sun ɗan huta shida Ummar Hafsat duk ida wani ɗan uwa yake sai da sukaje, haka da yayi ne Ummar Hafsat ta ɗan ji sanyi har ta fara saki jikin ta dashi, satin su uku garin dange sannan suka dawo cikin garin sokoto. Gari na waye wa Anwar ya shirya ya isa part ɗin iyayensa, koda yaje suna parlour zaune suna fira, sallamar Anwar da sukaji ne ta katse musu fira, da sauri iyayen nasa suka ɗago kai suka kallesa haɗi da mamaki a fuskukin su. Kafin suyi magana ya ƙaraso garesu yana faɗin, "Daddy , Mumy barka da safiya".....yana faɗa yana kwanciya saman cinyar mahaifiyar sa. Daddy ne ya buɗe baki yace, "Son saukar yaushe? haka akazo ko ka faɗa mana sai kayimana bazata?". Sosa ƙyar kansa ya fara kana yace, "afuwan Daddy , garin ne naji ya isheni yasa nazo tun cikin dare". Da sauri Mumy tace, "au kace tun cikin dare ka dawo". Yace, "eh Mumy, amma kuyi haƙuri gajiya nayi da garin shiyasa na dawo"....kafin ya rufe bakinsa sai Daddy yace, "Ai na ɗauka danaga ka jima acan ka samo muna sirika". Murmushi Anwar yayi amma bai ce dasu komai ba, sai can yace, "Mumy yaunwa nakeji haďamin breakfast". Tace, "tau autana taso muje dining kayi beark ɗin". Daddy yace, "tashi muje har ni muyi beark ɗin....haka sukaje dining Mumy ce tayi serving ɗin su suka fara ci. Kowa naci abinda ke gabansa amma ban da Anwar da ke jujjuya spoon ɗin dake hannusa. Mumy ce ta kula da haka dan haka tace, "auta na, mike dumunka naga komai baka ciba sai juya spoon ke yi". murmushi ya ƙaƙalo kana ya buɗa baki yace, "ba komai Mumy"....kafin ya rufe baki Daddy yace, "Son bana son karya kafaɗa muna abinda ke damunka dan tunda ka shigo na fahince akwai abinda ke damunka". Ƙyyar kansa ya fara sosa kana ya sadda kansa ƙasa yace, "Daddy ba komai, kwai wani abuki nane da bashi da lafiya kuma nake son naje dubinsa amma ina gudun kuce yawon yayi yawa bazan jeba". Kallon sa Daddy yayi yace, "hmm kai dai auta faɗi gaskiya, ai bazan ce haka ba, zaka iya zuwa dubinsa aduk lokacin da ka gadama". Murmushi yayi haɗi da godiya ga mahaifin nasa kana yace, "Daddy ba fa nan yake ba india yake". Sai Daddy yace, "a'a ba komai "dubiyace Allah dai ya baka ladar zuwa, amma dai ba jimawa zakayi ba autan Hajiya". Da ameen ya amsa kana yace, "au Daddy ba da kai ba kenan"....ya faɗa haka ashagwaɓan ce, kana ya ƙara da cewa "next week insha Allah zanje".....fatar ahairi sukayi masa haɗi da sama ɗan nasu albarka. Suna fitowa lecture ita da ƙawar ta Zeenatu, bayan sunyi ma juna sallama ita takama hanyar da za su haɗu da Aunty Shemah ita ko Zeenatu ta kama hanyar hostel. Wajan da sukayi parking ɗin mota ta nufa dan ita gabaki ɗaya ta manta da maganar da sukayi da Sulaiman da yace idan ta fito lecture yana nemanta. Tunda ta fito yake kallon ta tana tafiya cikin natsowa, a hankali take taka ƙafar ta har takowa gab dashi, bata ma lura da mutum ba har tazo zata wuceshi, da yaga alamun bata ganshi ba dan haka ya ɗauku waya ya danna kiran ta, tana tafiya taji wayar ta tafara ƙara, wayar dake hannuta ta duba taga wake kiranta, dan ita atunanin ta ko Aunty Shema ce? dubawar da zatayi sai taga sunan Sulaiman na yawo saman screen ɗin wayar ta, tunawa tayi da abinda yace mata, ɗagowar da zatayi sai sukayi ido huɗu dashi, zaune yake sai aikamata da wani ƙayataccin murmushi yake, wanda ke ƙarama fuskar sa kyau da annuri. Akalar tafiyar ta ta juya zuwa wajan da yake, shiko sai famar kallon ta yake kamar yau ya saba ganin ta, kallon da yake mata ne bata so, shiyasa sai famar tura baki takeyi waje, shiko hakan da take ba ƙaramin kyau yake ganin tayi ba, haka dai taci gaba da tafiya har ta ƙarasa wajan da yake. Kujera dake kusa dashi ya nuna mata yace ta zauna, kamar ba zata zauna ba sai kuma ta zauna, littafin dake hannta ya ƙarɓa ya fara dubawa har ya kammala kana ya ɗago kansa ya kalleta yace, "ba ko gaisuwa". Murmushi tayi haɗi da buɗa baki tace, "ina wuni Yaya Sulaiman".....bata kai da rufe baki ba yace, "waye yayanki hala? mama kiriƙe gaisuwar ki bana so tunda sai da na ruƙa". Murmushi tayi haɗi da faɗi, "kai mana". Yace, "a'a nikam kije kinemu Yayanki ba dai niba". Alamun kuka tayi tace, "tau shikenan bari natafi tunda kai ɗin ba yayana kaki ba". Ido ya zuba mata yana kallonta, dan yadda take magana yana masifar burgeshi, lokaci ɗaya yaji wata gogowar sonta ta ƙara laulayi zuciyar sa. Mayafinta ya riƙe yana faɗin, "sorry My kanwa, kallonta yayi yace haka yayi miki ko?". Bakinta ta cinnu gaba alamun yayi mata. har ya buɗa baki zaiyi magana sai ga Aunty Shemah ta ƙarso tana faɗin, "au nan kake tsayar min da ita kana hana ta shiga lecture ko?". Kafin yayi magana tace, "Hafsat tashi muje, idan kana son ganinta kazo gida amma adaina tsayar min da ƙanwa makaranta". Murmushi yayi haɗi da haɗi hannayi sa waje ɗaya yace, "tuba nake Aunty, insha Allah bazan koma ba, amma akowane lokaci zanzo gidan naku". Tace, "naji tana" faɗar haka suka fara tafiya. Har suka shiga mota suka tafi gida Aunty Shemah ba tace da Hafsat komai ba, bayan tayi wanka ta shirya ta fito parlour dan tayi ma Aunty magana idan akwai abinda tayi mata ya ɓata mata rai ta yafe mata, dan taga kamar fushi take da ita. Tun bata ƙarasa parlour ba sai ga Affan ɗan Aunty Shemah ya zo da gudun sa yana faɗin, "oyoyo Aunty". Hannayita ta ware shiko ya shige yana murnar ganinta. Ɗaukar sa tayi suka ƙarasa falo, zaune suka sameta tana duba wasu books ɗinta, a hankali ta zo ta zauna kusa da ita, bayan ta zauna ta gaisheta, bayan ta amsa suka ɗan jama kaɗan amma ba wanda yace ma ɗan uwansa komai, Hafsat ce ta katse shuru da faɗin, "Aunty ". Kanta ta ɗago ta kalle Hafsat tayi mata kallon ya dai. Sai da ta sadda kanta ƙasa kana tace, "Aunty dan Allah in akwai abinda nayi miki kiya femin, naga kamar fushi kikeyi dani". Sai da Aunty Shemah ta haɗi fuska kana tace, "abinda naga kinayi ɗazo shine bamin daɗi ba, ace tun yanzu har kin fara rashin shiga class, to bari kiji muddin kina son tamu tazo ɗaya sai kin aje komai ki kama karatu, bana son kiriƙa tsaye da wani makaranta da sunan wani zance, ban yadda da wanna ba koda ace Sulaiman ne ƙanena, kuma aganina karatu kika zo ba wata shiririta ba, dan haka nake haɗaki da Allah ki dana tsayi kina zance makaranta, in ma mutum yace yana sonki zaki iya bashi dama yazo nan ya sameki amma ni a makarnta bana so gaskiya, dan ko iyayenki ne baza su barki ba, kuma ni har ga Allah tunda na ganke jin kin shiga raina". Sai da ta kai ƙarshe zanci Hafsat ta ɗago da kanta tace, "kiyi haƙuri Aunty, kuma insha Allah bazan koma ba, duk da sai dana fito class ne, amma bazan sake ba koda ma can ba ra'ayi na ba ne". Nan dai suka cigaba da firar su shiko Affan sai gwalamniya yake musu kamar yana jin miso ke faɗa. Bayan kwana uku da dawowar Anwar ya fara shiri-shirin zuwa india. Tunani ya fara to idan yaje india wace makaranta Hafsat take, da yaga abin zai bashi walaha ya fara tunanin kiran Hajara dan yasan ita ce zata samu masa address ɗin duk inda take. Kwance take tana tunani Anwar da koma yadda zai shigo hannuta lokaci ɗaya, sai ji tayi wayar ta na ƙara, wayar ta ɗauka ta duba screen ɗin wayar , sunan da tagani ne yasa tayi picking bata shirya ba. A kunne ta kara wayar amma bata yi magana ba sai da ta tsaya fitar da numfashi a hankali, dan ita kanta tasan tana son Anwar so bana wasa ba. Da yaji batayi magana ba yasa ya buɗe baki yace, Hajara kin min shuru kamar baki san waya kira ba". Tambaya ta jefamasa tace, "yanzu kana ina ne". "Kaduna". haka yace da ita ata ƙaice..... kana yace da ita wani aiki nake son nasaki shine nace bari naji ko zaki iya?". Tace, "inaji faɗa idan zan iya zan faɗa idan ma bazan iya ba zan faɗa". Yace, "zaki iya, yace, address ɗin makarantar da Hafsat take nake so asamun na andia". Wata dabara ce ta faɗu mata tace, zanyi maka amma da sharaɗin".....yace, "faɗi sharaɗin naji". Tace, "a'a sa idan kazo zakaji sharaɗin". Yace, "ba damuwa idan kinsamu sai ki faɗa nazo inyaso sai ki faɗamin sharaɗin kafin ki bani address ɗin". "Naji zanje na samu, amma idan har ba ka yarda da sharaɗin ba to koda nasamu bazakaji komai daga waje na ba". Yace, "kar kidamu". haka dai suka cigaba da waya daga baya kuma sukayi sallama. Tunda lokacin Hajara ta bazama neman address ɗin Hafsat na andia.... *#Vote* *Comment* *Share* *©SUMY NA'IGE* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 25📑* *__________📖* gidan iyayen sa ya sauka ya gaishesu kana ya wuce gidansa, part ɗinsa ya wuce kai tsaye bai ma bi taka matar tashi da Baby da aka haifar masa ba ,tana parlour zaune ita da ƙanwar ta da wasu ƙawayen ta, alamun shigowarsa taji dan haka ta dube ƙawayen ta tace dasu dan Allah kujira ni ina zuwa, tana faɗar haka ta ɗau Baby ta kama hanyar part ɗinsa, duk da bata da cikakin sanin da zata ce shine amma jikinta har wani karkarwa yeke burinta ita dai ta ganshi gata gashi. Yana isa part ɗinsa, ko kayan jikinsa ba tsaya yarage ba ya ɗau waya yakira Aunty Shemah, bayan ta ɗauka sun gaisa yake tambayar ta Hafsat, sai da ta wani haɗe rai kana tace, "ai kana da number ta". Yace, "na ɗauka kuna tare ne amma kiyi hakuri naji kamar ranki ya ɓaci". Tace, "a'a ba haka bane kawai naga ko iyayena baka bari na ji lafiyar su sai ka ɗauku min wani zance". "kiyi haƙuri Aunty na". Tace, "ba komai, ka kirata kaji dan naga yau kamar bata jin daɗi"..... ai tun bata kai ƙarshin zancin ba ya datse kiran nata. Number ta ya kamu ya saka kira, kwanci take kamar mai bacci amma ba bacci take ba, tunanin mafarkin datayi jiyane takeyi, wayar tace da ta shiga rura ta mai data daga duniyar tunani, wayar ta ɗauku haɗi da danna picking ta kara a kunni ta. Sallama tayi masa ya amsa, bayan ta gasheshi haɗi da masa ban gajiya kana yace, "naji muryarki kamar mara lafiya?". Murmushi tayi kana tace, "lafiya ta ƙalau ya Baby tah". karki tambayeni dan sai da nace kizo ki ganta kikace a'a, kin ga ko ba dole na faɗamiki ya Baby take ba". Tace, "kayi haƙuri Babban Yayana". har zayi magana sai aka turu ƙofar ɗaki, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai yaci gaba da firarsa. Jikita a sanyaye ta fara takawa har ta kawo wajan da yake kwance, Baby ta aje kusa dashi kana ta zauna zaman jiran ya gama waya, baya ya gama kana ta ƙaraso kusa da shi tana faɗan, "Baban Baby barka da zuwa". Sai da ya ɗau Baby kana ya amsa mata haɗi da tambayar ta lafiyar ta. Baby ya zubama ido wadda tunda ya ɗauke ta yaji sonta na shiga zuciyar sa, huɗuba yayi mata yana gamawa sai Maryam ta dubeshi tace, "wani suna zaka saka mata?". Batari da wani tunani ba yace, Hafsat". Dubansa tayi da kyau tace, "kenan ka canja suna dan na zata sunan Mumy zaka sa". Yace, "a'a sai wani lokaci nasa insha Allah". Haka dai ya daure yana fira da ita kana ya tashi yaje yayi wanka ta kawu masa abinci yaci, amma duk abinda yake ɗiyar na hannusa, wanka ne kawa da zaiyi ya ijeta. Yana cikin haka sai akaturu ƙofa, abukin sa Jabir yagani tsaye yana masa wani kallo, a hankali ya buɗe baki yace minayi zaka yimin wannan kallon haka". Kafin ya bashi amsa Maryam ta gashe da Jabir kana ta ɗau Baby ta fice. Bai ce dashi komai ba sai da ya shigo cikin parlour yace, "wai yaushe zaka gama course ɗin da kajeyi ne?". Sai Sulaiman yace, "sai ta gama ". Jabir yace, "wallahi ni nasan bawani course da kaje, kajene dan kayi tsaron ta, to bari kaji wallahi baka isa ka tsareta ba, dan yanzu kazo nan amma bakasan meke faruwa acan ba, ni dai shawara ta gareka ka dawo kacigaba da aikin ka kuma kariƙe matar ka duk yafiye maka bin sauran wani".....tun bai kai ƙarshe ba ya ɗaga masa hannu yace, "Jabir daka ta!". Idonsa ya ɗago ya kalleshi waɗan da saka sauya lokaci ɗaya yace, "bari kaji Jabir wallahi ko ɗa ɗay-ɗaya har ashirin Hafsat ta haifa tare da Anwar ba ta hanyar aure ba wallahi sai na aure ta muddin tace ta amice da haka". Jabir yace, "har yanzu baka san waye Anwar ba, kuma waye Hafsat ba, kuma nasa ko yanzu Anwar yaje ga Hafsat zata yarda dashi dan tana masa son bana wasa ba". Irin yadda yada yaga bacin rai afusakar Sulaiman dan haka ya tashi ya kama hanyar fita, sai da ya kawo gab da ƙofa kana yace, "nasan baka san me nasani ba gami da Anwar ba, to bari kaji yanzu haka Anwar yahe india". yana faɗar haka ya rufe ƙofar ɗakin da ƙarfi kana ya bar gidan ciki da ƙunar zuciya. Aikuwa Sulaiman najin haka basan lokacin da ya tashi zaune ba, "yana faɗin wallahi ƙarya ne". Ba tsaya wata-wata ba ya ɗau kye ɗin motar ya bar gidan, School ɗin su Hafsat yaje neman Safiyya da ƙawar ta Naja'atu. Shiko Jabir ba abunda ya tsana kamar yaji abukin sa yace zai aure Hafsat, dan shi aganinshi bata dace da Sulaiman ba, dan shi abinda yafi tsana hulɗa da talaka. Koda ya isa school ɗin ba kowa ya samu ba, sai ɗai-ɗaiku, sabida ana weekend dan haka ya samu wata cikin ƴan makarantar taje hostel take ki rumasa Naja, amma koda taje Naja batanan taje gida weekend. Koda ta zo ta gaya masa hauka ne kawai baiyi ba, kuma gashi bai san gida ko ɗaya daga cikin su ba, dan haka ya shigo mota ya dawo gida, Allah ne ya kaishi gida lafiya dan yadda yake gudu kamar ya gaji da ransa. Yana zuwa gida ya kasa zama ya kasa tsaye, dan haka ya shiga mota ya kama hanyar gidan iyayen sa. Parlour ya tarar da Mumy sa da Abbansa, tunda ya shigo suka zuba masa ido suna kallon sa, Abban sane ya fara magana yace, "Yaro na mike damun ka na ganka haka kamar kana cikin tashin hankali?". Sai da ya sauke ajiyar zuciya yace, "eh to Abba dan akwai wani abinda ya taso gami da karatun da naje can india shine nake son gobe na koma"......tun bai rufe baki ba Mumy sa tace, "kar kasoma dan idan ka ga ka bar ƙasar nan to anyi suna, na gaji da wannan ƙaƙale-ƙaƙale naka fa, tunda akayi auren nan baka zauna ba bare ku fahinci juna kai da Maryam, dan haka ba inda zaka je". Sai da ta gama Abban sa ya dube shi kana yace, "my Son kaje kashirya idan Allah ya kaimu gobe sai kaje ɗin". Har Mumy zatayi magana Abba ya ɗaga mata hannu haɗi da faɗin "fatar alhairi kawai nakeson kiyi masa". Ba dan ranta yaso ba tayi masa fatan alhairi haɗi jadda da masa yaje ya tambaye Maryam duk abinda bata da tagaya masa. Yace tom haɗi da tashi dan yaje ya fara shirin komawa, har zai fita Abbansa yace, "son wani suna kake so asawa yarinyar nan". Sai da ya sosa ƙyya kana yace, "Hafsat". Yana faɗa ya fice bai jira cewar su ba. Wani sanye daɗi ne ya mamaye Mumy ita da Abba, sai Abba yace "mun gode da wannan kyautar". Ita Mumy kasa magana tayi sabida daɗi, dan sunan mahaifiyar ta ne, kuma tunda ɗiya ta taso asa mata amma ƴan uwan Abba suka hana sai yanzu da Allah ya yarda asa ga jikar ta. Kafin ya koma gida sai da ya tabbatar da ya samu bisa da duk wani abun da yake buƙata. Lokacin da ya faɗawa Maryam tafiyar sa, har kuka sai da tayi amma dayake mai sanye ce daga baya tayi masa addu'ar tafi lafiya da dawo lafiya. Tun shida na safe jirginsu ya ɗaga zuwa india, sune basu sauka ba sai cikin dare. Koda ya isa masaukin sa sose yagaji dan haka ya watsa ruwa ya kwanta. ***** Tunda tayi sallah asuba bata sake kwanciya ba, gyaran gida tayi kana ta hada musu beark, bayan ta kammala taje tayi wanka tashiriya, cikin sauri tayi beark sannan tazo ɗakin Aunty Shemah tace zata tafi sabida lectura ne da ita da safen nan, key ɗin mota Aunty Shemah ta bata haɗi da iyimata adawo lafiya sabida ita yau bazata je ba. Karɓa tayi da sauri ta ƙarasa wajan aje mota, tana shiga tayi mata key ta fice da sauri sabida gab take da ta makara. Anwar tunda yayi sallah asuba ya tashi ya shirya dan tun yau yake son ya fara ne manta, sabida bashi da lokaci, dudu sati ɗaya ne zaiyi ƙasar, abukin sa na shiryawa suka fita zuwa cikin makarantar. Sulaiman sabida ya gaji bai farka da wuri ba, dan ko sallah yau sai da ya makara baiyi ba, kuma yana gama sallah sai da ya kwanta, aikuwa koda ya farka rana ta fara fitowa, cikin hanzari ya shirya ko beark bai tsaya yayi ba ya kama hanyar gidan Aunty Shemah. Koda yaje parlor ya tarar da ita tana beark, sallama yayi kana ya shigo, ido da baki ta zuba masa sai kallon sa take kamar yau ta fara ganin sa. Ƙarasowa yayi ya zauna kana ya gaisheta, ba ta karɓa ba sai jefa masa tambayar da tayi "miya dawo da kai yanzu?". Sai da ya ɗau kofin tea kana yace, "akwa abinda ya mai dani, Aunty ina Hafsat?". "Hafsat ta mai daka ko". A'a Aunty, su Mumy na gaisheki kuma sunci kin daina kiransu". Shareshi tayi dan sose ya bata haushe ace ya dawo jiya. Sai da ya ta kurata da tambaya tace, "taje makaranta". Ƙofin dake hannunsa ya aje yace bari nazo. Mamaki ya cika ta, dan haka takasa baki sai kallon sa takeyi, dan ta lura yadda yadamu da Hafsat ita bata damu da shi ba, sai ma gani take kamar batasan yana son ta ba. Tanayin parking ta fito haɗi da kulle motar, tana cikin haka sai ga ƙawar ta Zeenatu ta ƙaraso tace, "kizo muyi sauri mutafi dan munkusa mu makara, "tace to muje" . Tafiya suke suna fira har suka kusa kai class. Anwar da abukinsa sai sauri suke su isa wajan da suke tunanin zasu ganta, tafiya suke ita da Zeenatu, shiko Anwar yana bayan su shida abukinsa, dan har yasu ya ijesu ya wuce sabida basa sauri sai wata tafiya suke kamar basa son taka ƙasa, kuma ga hanyar da zata sada su class ɗinsu akwai cinko so da yawa, abukinsa ne ya riƙeshi yace mubi komai cikin natsowa insha Allahu zaka ganta". Badan yaso ba suka biyewa tafiyar su har suka kawo hanyar da zata sada su class kana suka raba hanya. ******** Kamar wadda aka koro sai gata tashigo ɗakin tana faɗin, "Zahara! Zahara!. Da sauri ta fito daga toilet tana faɗin, "Hajara lafiya kuwa kikazo min haka?". Tace, "ina lafiya tunda Anwar ya asirceni duk abinda yace namasa shi zan masa, amma ni duk abinda na nuna masa ina so wallahi bayayimin, gashi yanzu nabashi address ɗin shegiyar yarinyar nan, dan haka nake son ƙarfe ukun dare ki rakani muje wajam Malam kinga sai na kwanan anan iyaso lokaci nayi muje". Sai Zahara tace, "to mi kike son iya gami dashi Anwar da Hafast ". Hajara tace, "ni so nake iya masa abinda baya ganin kowa sani, sannan ita ko akorota daga karatun da take a india, dan na tsane jin tana can , kinga idan ta dawo tana gani tana ji muyi Aure da Anwar inya so tazo tanamuna wanki da wanke-wanke". Tafawa sukayi haɗi da sanya dariya mai ciki da ma'anuni da yawa. Tun biyu da rabi na dare suka tashi suka shirya kana suka ɗau hanyar gidan Malamin su.... *#Vote* *Comment* *Share* *°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°* *1441H/2020M.* *NA MARUBUCIYA:-* *SUMY M NA'IGGE✍🏼•* ~~WattpadSummy M Na'ige~ *SHAFI NA 24📑* *__________📖* Bayan kwana biyu suna zaune da Aunty Shemah parlour suna fira sai suka jiyo sallama bakin ƙofar parlour, tun kan su ƙarɓa sai affan ya zo da gudu yana faɗin, uncle, uncle". Sulaman hannayensa ya ware Affan ya shiga jikin sa yana faɗin, "my son lafiya kake?". Sai da suka ƙaraso cikin parlour kana Affan yace, "eh uncle". surutu ya fara mishi amma Sulaiman bai kulashi ba ya kai dubansa ga Aunty yace, "My Aunty ya kuke ya gida?". Kafin ta amsa masa ya kai dubansa ga wajan da Hafsat ke zaune duk ta ta kura, dan ba wani kayan kirki ne ajikinta ba kuma gashi yayi musu bazata, tana so ta gaisheshi amma ta kasa sabida yadda ya kifeta da ido, shiko yaƙi ya janye idon sa, sai jira yake ta gaisheshi, ita ko ta kasa buɗa baki ta gaisheshi, muryar Aunty Shemah ce da yaji ta amsa masa haɗi da tambayar sa yaushe zai je gida, sannan ya mai da duban sa ga Aunty Shemah yace, "wata ƙila gobe na wuce". Tace, "bawani wata ƙila dole gobe kaje, sabida zuwanka dole ne dan inba kaje ba sai aɗauka dan baka sonta ne zaka ƙin zuwa". Suna cikin firar sai Hafsat ta sulale tayi ɗakin ta. Duban Aunty yayi da kyau kana yace, "kada ki damu Aunty insha Allahu gobe zanje". haka suka cigaba da fira har wani lokaci. Duban wajan da Hafsat take zaune yayi, amma sai yaga bata wajan, dubar parlour ya fara amma bai ganta ba, lura da haka da Aunty Shemah da tayi sai tace, "wai Sulaiman me ke son afkuwa ne gareka gami da Hafsat?". murmushi yayi haɗi da sose ƙyyar kansa, bata jira cewar saba tace, "bari na turumaka ita". tana faɗar haka ta tashi taje ɗakin Hafsat. Bata jima da tafiya ba sai ga Hafsat tazo parlour sanye da wata atamfa wadda akayi ma ɗikin riga da sikit, sose kayan suka karɓe ta duk da ba wata kwaliya tayi ba. Zama tayi kan kujera da ke nasa dashi kaɗan kana tace, "ina wuni Yaya Sulaiman". Bai amsa ba sai ido da ya zuba mata yana kallonta kamar yau ya fara ganin ta. Har zata sake maga yace, "ƴan matan Aunty ya karatu". Murmushi tayi haɗi da sadda kanta ƙasa kana tace, "alhamdullah". Shuru ya biyu baya sai can tace, "ashe Yaya munsamu ƙaruwa, Allah ya raya akan sunnanh". da yake matar shi ta haihu shine Aunty Shemah ta gaya mata kuma dan haka ma zai koma najeria yayi weekend ya dawo dan iyayen sa sun da meshi akan sai yaje, kuma in bai jeba za suga kamar dan bai son matar ne yaƙi zuwa, ba dan ranshi yaso ba ya amnci zai je. Kallon ta yayi yace, "ko zaki je gobe muje tare in zan dawo sai mudawa tare?".... kafin ya kai k'arshin maganar tace, "a'a ni ba inda zanje sai na kammala karatuna gaba ki ɗaya". kallon baki isaba yayi mata kana yace, "idan ƙarshin shekara tayi naga mai barikin anan". Murmushi tayi tace, "Yaya Sulaman ai nasan ko kai bazaka bari na koma najeria ba sai na kammala". Yace, "hmmm nasan ko yanzu aikwai abinda ya hana ki zuwa, da ko dan

Chapter 9 of 13